Showing 186001 words to 189000 words out of 467220 words

Chapter 63 - MATAR MUTUM COMPLETED 1-3 BY MARYAM FARUK.doc

23 Sep 2025

12371

faWi kawai tayi seta daki garwa. Ya saki murmushi yace
"You know nothing about my family kar kuma kice zakiyi judging da abinda kike ji a bakin mutane. Babu wata mace da aka taSa aurowa a gidanmu akace ba zatayi karatu ko aiki ba, duk wadda kikaga bata aiki bata da ra'ayi ne, amma dai ni in particular bazan yi miki ?arya ba tun yanzu ki sani idan har Allah ya sa ka munyi aure babu maganar aiki ba zakiyi ba. Ba zan yarda Matata ta ringa yawo a gari da sunan aiki a ?ar?ashin wasu ?atti ba. Business dai wannan idan zakiyi zan baki jari daga naira Wya har zuwa Miliyan Wari ya danganta da abinda zaki siyar amma ban miki ?aryar zakiyi aiki ba" ya faWa da iyakar gaskiyarsa.

Duk yanda yaso ya sha kanta akan ta bashi dama ya tura, ya yarda aje ayi magana idan yaso a saka rana sanda zata gama Makarantar idan haka ne burinta amma ta tubure ita ba haka ba. Cikin yanayin dayake nuna ransa ya Saci da rashin samun amincewar tata ya maidasu Makaranta, be tsaya ba yace mata Bukar ze maido mata da Flask gobe be taho dasu ba shi Asubanci zeyi ya wuce Kano.
"Idan yazo Badar ce zata karSo ba keba" ya faWa da sigar umarni. Cikin wasa Badar ta Sata fuska tace
"Wato ni mara galihu tunda bani da tsayaye ko"
"Kika sani ko ya zama tsayayyen?" Ya tsokaneta. Bundle Win 1k ya bawa Badar yace
"Tukuicin Tuwo, yayi daWi da alama ke kikayi"
"Afeeya ce wlh" ta faWa bayan data dafe kuWin, ya juya mota yana cewa
"Idan ta amine da muradi ma zan haWa na bata tukuicin a tare" yaja ya tafi babu wata profer sallama da suka sabayi.

"Alamu sun nuna kin kwafsa Afeeyah,wai dan girman Allah se yaushe Ahnad zezo Zaria ya koma da farin cikinki ne?" Badar ta faWa suna shiga Hostel.
"Hmmm" ta bata amsa dan ita da kanta taji rashin daWin yanayin daya tafi, duk shanye fushinsa yau seda fuskarsa ta nuna, amma ya zatayi toh?
A rabon Maman Minal ta yafita mata Kaza taci dan da Badar rantsewa tayi ba zataci ba tunda bata da mutunchi.
Harta kwanta wayarta ta fara ?ara, International number ce, kwana uku kenan ana kiranta da ita kullum kuma ko ta tsinke kafin ta ansa ko kuma taga miss call ita kuma ta san bata da wani a ?asar waje da ze kirata shi yasa bata taSa bin baya ba ta yuwu ma scammers ne.

Ta amsa wayar ta saka a kunne ba tareda tayi magana ba, kusan minti guda ita shiru haka wanda ya kira shima beyi magana ba daga can ?asa dai tana jiyo maganganu alamar yana kusada inda ake hayaniya. Suka ci minti uku, harta yanke shawarar kashe qayar dan ba zata fara magana ba ta yuwu wand aaka ce suna tsotse jinin mutane ta waya ne suna jira tayi magana su gama da ita, harta zareta daga kunne taji wani sauti daya saka zuciyarta tsayaqa na wasu seconds kafin taci gaba da aiki

"AFEEEYAAAAHHH!" Yaja sunanta, bata iya amsawa ba se sunayen Allah da take maimaitawa a ranta ?irjinta na lugude.
"Afeeya!" Me kiran ya sake maimaitawa, bugun ?irjinta ya tsananta zufa ta fara tsassafo mata haka numfashinta ya shiga yi kamar ze tsaya tamkar wadda take cikin matsanancin tsoro kuma kamar wadda aka kafe ta kasa cire wayar daga kunnenta se kokawa take da numfashinta dake barazanar tafiya hutu saboda tasirin da muryar wanda batasan ko waye ba yayi a kanta.

Bata taSa katari da Bakin daya iya furta sunanta, ya bawa kowanne harafi ha??insa kamar me wa?a.
"Afuwan, Assalamu alaikum" ya sake faWa cikin wani sauti me haWe da irin ?aramar dariyar nan, take ta kware da yawun bakinta ta shiga tari tul tul Ummi data fi kusa da ita ta mi?a mata ruwa tasha tana maida numfashi har sannan kuma be kashe wayar ba, kwakwalwata ta ayyano mata me wannan muryar, sallamar da yanayin da yayinta ya tuna mata da jinjirin Samudawan da tayi gamo dashi ranar Monday.

"Sannu, badai loman abinci kikeyi ya ?warar dake ba?" Ya sake tambayeta se kawai taji bakinta ya saki tsaki kafin ta zare wayar ta kasheta tareda ajiwa batama lura da yanda yan Wakin sukayi shiru tareda zuba mata ido ba se sannan.
"Afeeya meya faru? Kinga fuskarki kuwa se kace wadda Fulanin Daji suka kira?" Maman Minal ta faWa, ta shafa fuskar da hannu, Badar tace
"Meya tsorataki? Kin kara waya a kunne kusan minti goma bamuji kince komai ba lafiya ko wani abun ne ya faru?"

"Uhm" kawai tace ta mi?e tareda Waukar Wankwalinta ta fita ba tareda ta amsa tambayar ba har sannan kuma zuciyarta bata bar bugawa ba kamar yanda jikinta yake rawa. Last floor ta haye ta tsaya tana kallon 90s mutane nata karaina surutu duk ya cika gurin, tunani takeyi shi Win ne ko ba shi ba? Idan shine a ina ya samu number ta sannan kiran me yake mata?
Zancen Sahid dayace ya bawa wani number ta ya faWo mata to ko shi yake nufi a gurinsa ya samu number wayata tunda ta faWa mata sunanta daman?

"Afeee" aka ?wala mata kira daga ?asa, tayi firgigit daga tunanin da take ta kalli inda taji sautin na tasowa tsabar wula?anci Nurain ne yake kwala mata kira daga cikin 90s, bata amsa ba ta harareshi ya Wago mata Kwalin popcorn yana cewa
"Kinyi kyau, zaki ci popcorn?" Still da ?arfi yayi maganar abinda ya janyo hankulan waWanda ke kusa dashi suka kalli gurin dan ganin dawa yake tana ganin haka tayi saurin sauka ta koma Floor Winsu dukda haka tana hango su se shegiyar dariyarsa yakeyi tana shiga Badar tace

"Cin kan Bestin naki ya motsa yau"
"Ke kuma sweetynki ba" tabata amsa tana ?o?arin cire rigar jikinta wayarta ta shiga ringing, data Badar a tare ta Waga ganin Ahmad ke kira bayan ta haye kan gado, hira suka shigayi ya saki kamar bashi ya tafi fuska babu walwala ba, Bashi da ru?o, yana daga cikin kyawawan halayensa se santin kwalliyarta yakeyi har yana cewa saura ?iris yayi abin kunya next time karta sake saka Red Lipstick idan zata masa kwalliya har se ta zama matarsa.

Sedata kashe wayar ta kura Badar ta fita Ruth tace mata sun fita da Ummi Nurain ne ya kirata
"Gulma, ana so ana kaiwa kasuwa" ta faWa,daga nan ta gyara kwanciyarta ta bhau WhatsApp.


Lambar Basamude ta gani a farko yayi mata magana
"Why did you hang my call and you hissed at me? Not even in your dream you try that again" Ta maimaita sa?onbabu Adadi Mamaki ya kasheta, a fili tace
"Ikon Allah, ji wata magana kamar wani uban mutane, wannan yana da lafiya kuwa?" a maimakon ta amsa se ta shiga profile Winsa, Hoton Jessy ne akai ta Yan Ball kalar Red da white no 9 an rubuta *JAY* a jiki, batasan ko ta wanne club bace ba abinda ta sani dangane da yan Ball.
Tayi tsaki na fita daga chat Win tana jinjina ?arfin halinsa, status ta fara kallo kira ya shigo video call tayi rejecting wannan mutum ko maye ne ai se haka wannan Naci har ina?

Be ha?ura ba ya sake kiranta voice call ta sake rejecting, seda ya kira sau uku ana huWun ta amsa tun kafin tayi magana yace
"Wallahi Afeeya, if reject my call again I'm going to deal with you"
"Malam kanka guda kuwa? Who are you? Are you suppose to tell me what to do or what?" Ta bashi amsa a haslae jin abin nasa ze zarce ganga da makaWi.

Tana ji yaja numfashi kafin ya sassauta murya yace
"Baki san abinda nake ji a zuciyana bane, 3 days i have been calling but you are not answering, na sameki yau and you hanged on me haba Afee bakida tausayi ne?"

"Don't call me that again" ta faWa jinyanda Afee daya kirata ya saka tsikar jikinta zuba,
Tanaji yayi wani mayaudarin murmushi yace
"*AFEEYAH* God i love the name, gaskiya Dadynki ya kyauta daya saka miki suna me daWi da Ma'ana, idan munyi aure nima zaki haifarmun tawa Little Cute Afeeya like you ko?"

"Qit" takashe wayar,, koda wanda ta sani bata wannan zancen shirmen ballantana da stranger wanda bata san mutum bane ko Aljan. Seda ta kashe Data ta saka wayar a Silent kamar yanda takeyi idan zata kwanta kafin tayi addu'a ta rufe idonta amma bacci yace be san zance ba, dakyar da taimakon Allah ya saceata. Kwana tayi tana mafarkin mutumin wai suna tafiya akan Gajimaren suna tsinkar furen soyayya.

Da Asuba ta samu tsarki tayi wanka tana Azkar Ahmad ya kirata suka gaisa ya gaya mata yanzu ze tafi Kano.
"Da wurwuri haka?" Ta tambayeshi, tana ji yana warming mota yace
"Alhaji ne ya kirani zan takashi Hadeja ?aurin Aure kinga dole na tafi da wurwuri karna Sata masa lokaci"
"Haka ne, Allah ya tsare hanya ya kaika lafiya" tayi masa Addu'a ya amsa da "Amin" kafin sukayi sallama ta kashe wayar ta juya da niyyar maida kai taui bacci aka sake kiranta.

"Jarabar duniya" ta furta a fili ganin me kiran da farar Asubar nan se kace wanda yake binta bashi ze fara kira wannan wane irin mutum ne mara lissafi ta shiga mita a ranta amma hakan besa ta?i amsa wayar ba dan harga Allah can ?asan ranta har wani daWi taji daya kira.

Cikin dakakkiyar muryarsa ta Maza irin wadda zakaji kamar har echo tke yi yayi mata sallama ta amsa tana jin wani sabon yanayi yana mamayarta.
"Jiya kika kashe waya kuma bayan nace bana so, kuma nayita kira baki amsa ba why?" ya faWa a tausashe kamar bacci be gama sakin muryarsa ba hakan ya sa muryar tayi wani amo na daban me tsinka jini, numfashi taja ta fesar amma batace komai ba yaci gaba da magana yana cewa
"Bana so, don't you ever hang on me again gara ki gayamun ni na kashe wayana da kaina if you don't want to talk to me, raini ne wannan kuma bana so".

Ta shagala da sauraron Muryarsa se kuna ta zabura tace
"Wai kai a matsayinka nawa ne da zaka ringa kafa mun sharaWi?"

"Ina son tsiwa, amma bana son rashin kunya, idan kika ci gaba sena fasa miki baki, then i will keep kissing it har se ciwon ya warke" ya bata amsa seta hangame baki ta kasa cewa komai, baccin da take tattalawa ya kama gabansa.
"Afeeyah, i hate it when someone hisses at me, karki sake" ya sake cewa

"Waye kai?" Ta samu kanta da tambaya dan wannan gadarar tasa ta shallake ta masu hankali kuma,
"I will call you by 10am, kina free?" Be bata amsar tata tambayar ba ya jefa mata tasa
Ta wurga ido kamar yana gabanta kafin tace
"No, i have class by that time"
"2pm?" Ya sake faWa se ta karkace tace
"That will be my resting time"
"In the evening?" Be ha?ura ba ya sake tambaya ba kai tsaye tace masa
"Kasan me, ina da lokaci amma ba naka bane so you better respect your self and stop calling me talk less of Bossing around kana wani gayawa mutum abunda zeyi da wanda ba zeyi ba"

"Idan na kira karki daga kinji" ya faWa yanda kasan wani Baffanta kafin kuma tace wani abu ya kashe wayarsa ya barta da baki a gantale.

"Afee don do new catch" Sururat ta faWa teasingly, takaicin daya cikata ya sa bata tanka mata ba tana jin Badar na cewa
"Tun jiya take wata waya kamar ta munafukai koma wanene yayi ta kansa wlh dan ina gani babu wanda ya isa yayiwa Ahmad over taking".

Kwanciya tayi cike da jin haushin kanta da biyewa mutumin har ya samu damar raina mata hankali.
"Amma ya haWu, haka take son tsayayyen namiji, ta tabbayar da Ahmad ne sedai yayita lallaSata yana cewa tayi ha?uri".

AHMAD
?rfe Tara da mintina ya isa Kano dalilin Hold up daya samu a Kwanar ?angora wata babbar Mota ta faWi a tsakiyar Titi wannan ya kawo cin koson ababen hawa a titin dan se zagaye suka ringayi suka kaucewa inda hanyar ta rufe ma. A ?ofar Katafaren Get Win gidan Alhaji Audu Bechi ya tsaya yana danna Horn, Issa ya tsallako da gudu daga gidan dake kallon nasu inda suke zaune da sauran masu gadin gidajen layin ciki. girmamawa yake masa sannu da zuwa
"Yi sauri Issa, na makara Alhaji yana jirana" ya faWa ganin Issan ya tsaya Sata masa lokaci da gaisuwa da sannu da zuwa hakan yasa ya wangale masa Get ya shiga.

Cikin Rumfunan da aka tanada domin Ajiye mota yayi parking, motoci ne birjik a gurin yanda kasan kamfanin saidasu, cike da murna ma'aikatan dake kaikawo a Kantamemen compound Win suka nufeshi suna masa maraba, duk saurin da yake haka ya tsaya yana basu hannu, babu kyama balle nuna banbancin kasancewar Barorin gidansu ne su yake mu'amalantarsu wannan ?abi'a tasa ta karrama ?an Adam yasa yake da farin jini matu?a gurin mutane.

Junaidu daya daga cikin masu kula da shara ya Waukar masa ?aramar Akwatin da kayansa suke ciki, har ya nufi bangarensu na Mazan gidan yayi burki ya juya zuwa ainihin cikin gidan.

Da sallama ya shiga tsakar gidan shiru babu kowa kai tsaye ya doshi Falon Momy, ya kai tsakiya ya tsinkayi muryar Hajiya a bayansa tana cewa
"Aa, su uban Bilki an dawo kenan?" (Baba Bilki tana kiransa Babanta saboda Tace Asalin sunan Tijjani Amadu ne dan haka da Babangida da Ahmad duk sunan Malam Babansu sukaci shine Hajiya ta samu idan iskancinta ya tashi take ce masa Uban Bilki) Jiya ?an uwanka yake cewa kace masa zaka daWe a Habujan se gaka kuma da Sassafe lafiya dai ko?"

Birki yaci yana cije lebensa, ya tsani sunan nan data ke kiransa kuma a duk sanda tayi hakan tana nufin zagin Baba Bilki ne ta yuwu sunyi hatsaniya shine zata fake da haka ta zageta da alama kuma yau da SurSushin mutunchi tunda har ta kira Jafar da ?an uwansa
Seda ya daidaita fuskarsa kafin ya waiwaya ya kalleta, babu yabo babu fallasa ya dur?usahar ?asa kamar yanda yake gaida Mahaifiyarsa yace

"Hajiya Ina kwana?"
Tana ?ara matsowa ta amsa masa da lafiya tana sake maimaita tambayar dalilin dawowarsa da safiyar nan da be bata amsa ba. ?atuwar Robar hannunta ya kalla ya girgiza kai, Nama ne sha?e a ciki yau Juma'a da alama tayi halin, zuwa take ta zaftare naman Abincin sadaka da akeyi duk ranar Juma'ar, tun suna yara haka Hajiyan takeyi ko ran girkinta ko ba nata ba se taje ???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?ta kwashe Naman kuma babu wanda ya isa yace dan me hatta kuwa da me bada kuWin Naman wato Alhajin gidan.

Gaba yayi yana ce mata
"Wlh Alhaji ne yayi mun kiran gaggawa zan rakashi Hadeja, yanzu ma sauri nakeyi nasan ya shirya ni yake jira". Ya lura da yanda murmushin kan fuskarta ya Sace Sat kamar Waukewar wutar Nepa hakan kuma nada nasabada jin cewar Alhaji ne ya kirashi.

Wucewa yayi ya barta nan a tsaye,
Da sallama ya shiga falon Mony wanda ya tarar da ?ofar a buWe, Momy na zaune a ?asa tareda ?anwarta Anty Maimuna da bata fi minti Goma sha biyar itama da shigowa Kanon ba daga Katsina inda take aure suna karyawa Ahmad ya shiga. Seda ya cire takalminsa sau ciki a baqin wajen kafin ya shiga yana sake nanata sallamarsa Momy da Anty Maimuna suka Wago a tare kowacce fuskarta washe suna amsa masa ya zube a gabansu yana kallon Antyn nasa dake masa oyoyo kamar wani Wan yaro yayi dariya yace
"Anty saukar yanzu ko nan kika kwana? Koda yake munyi waya da Momy dazun bata ce mun kina nan ba kenan yanzu kika zo".

"Zuwana " kenan Amadi ban daWe ba, kayan lefe nazo haWawa ?nin Baban Sayyid nayi waya da shagon da zan siyi kayan basu fito ba shiyasa nayo nan na karya tukunna" ta bashi amsa seya ?ara washe baki yana gaisheta tareda tambayar Yaranta tace duk suna gida suna gaishesu kafin ya juya ya fuskanci Momy da murmushin kan fuskarta ya gagara gushewa saboda farin cikin ganinsa. Cikeda tsantsar ladabi ya gaisheta ta amsa tana tura masa plate din gabanta tace
"Nasan baka karya ba"
"Kai Momy, so kike Alhaji yamun faWa kenan ?arfe tara fa yace zamu tafi gashi yanzu goma ake magana" ya faWa yana mi?ewa tsaye, Momy ta goge hannunta da tissue tana cewa

"Dana ji shiru ma na zata har ka shigo kun tafi dan tun Wazun dana kai masa abin kari naji kuna waya yace ka kusa gida da ai da Takwaran Al?ali zasu je ban san ya akayi tafiyar ta juyo kanka ba"

"Haba dai, kina da rai na taho daga wani gari na shigo har cikin gidan nan na fita ba tareda nazo na ganki kin saka mun Albarka ba ai ko bakida rai na shigo na kalli Wakinki nayi miki Addu'a Momy" Ahmad ya faWa, wani murmushi me nuna irin Alfaharin da Momyn keyi da kasancewar sa Wanta tayi kafin ta mi?e tana cewa
"Ka hanzarta dan nasan yaji shigowarka karka ja yayi maka suruti" seya rusuna a gabanta yana cewa
"Zan fita"
"To ?an Albarka, Allah ya kaiku lafiya ya dawo daku lafiya Allah kuma ya tsare ku daga sharrin ?arfe" Momyn ta faWa tana dafa kansa kamar ?aramin yaro ya mi?e yana murmushi yacewa Anty Maimunan ya tafi itama tayi masa Addu'a kafin ya zura takalmin sa rabi ya fita da sauri jin agogo yana buga goma.

Anty Maimuna ta rakashi da murmushi kafin ta kalli Momy tace
"Allah kenan, idan ya baka dubu masu bata maka se ya baka Waya da ze wanke maka takaicin duka dubun nan. Yanzu ki gani har qofar dakin nan Salim yazo keda kika haifeshi baki isa ya le?o yace ya kika tashi ba balleni ba?uwa zuwan yanzu kuma ba kunya ya karSi abinci yayi tafiyarsa.

Momy ta kai zaune tana cewa
"Ai Maimuna Al'amarin Salim a kullum maimakon yayi sau?i ?ara ta'azzara yakeyi. Ba Salim kadai ba ni yanzu Yayansu shi yafi damuna, ace mutum beyi shashanci ba da ?uruciya se yanzu daya fara tara iyali? Kuma wannan ?allababbiyar sabgar siyasar da ya shiga ita take neman canza masa al?ibla, daman ni sam abin be kwanta mun ba. Tunda ya fara yake sakani magana, kullum matarsa na hanyar kawo ?ararsa.

Yanzu shekaran Jiya seda sukazo sulhu da saboda tsabar wula?anci Yaron nan

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login