Showing 60001 words to 63000 words out of 467220 words

Chapter 21 - MATAR MUTUM COMPLETED 1-3 BY MARYAM FARUK.doc

23 Sep 2025

12178

bakin mota gaba dayansu, Bashir sunyi fada da Karuwar daya kwana da ita har taji masa ciwo da kwalba ya mata dukan mutuwa wannan fushin ya saka ya fasa qara kwanan da yayi niyya yace su tafi shi Ali daman harya fara cigiyar inda ze samu motar Kano yaga sun fito. Bashir na sallama da jama'ar sa Audu har ya shiga mazaunin Direba dan shi ze jasu saboda ciwon hannun Bashir sega Zubaida ta fito daga gidan taci kwalliya daurin nan kamar ze fadi saboda yanda ta tsikara shi hannu ta riqe da jaka madaidaiciya da zata ci kala a qalla Kala uku se qaranar jakar mata a daya hannun da alama wani gurin zataje kuma tafiyar kwana ce.

"Yar dagwas, an sauka daga sarautar kenan" Bashir ya fada yana kallonta, tayi far da ido, cikin yanga da iyayi tace
"Eh, ina kayi? Naga kamar tafiya zakayi ko?"
"Kano na nufa, kefa na ganki da jaka da alama balaguro zakiyi"
"Zan sauka a Zariya" ta fada tana wucewa motar, ta aje jakarta akan Boot ta wuce ta bude gaba ta shige kai kace motar tace. Bashir ne ya saka mata motar a Boot haka suka kamo hanya, duk yanda take daurewa seda ta biyesu ta shiga hirar, sun tsaya a hanya zasuyi sallah Audu ya samu damar yi mata magana shida ita.

"Kaga malam, nifa ba irin sauran masu Arhar da kuka saba tayawa bace" ta bashi amsa tana farfara ido ta wuce ta barshi a gurin yana murmushi kamar wawa. Dagaske sonta yake, irin soyayyar nan ma me zafi. Har qofar gidan da zataje suka sauketa a Zariya dukda tace su ajiyeta tun akan hanya.
"Nan ne sabuwar maboyar taki kenan? To sena rako Abokina" Bashir ya tsokaneta, ta harare shi kafin ta Audu tana taunar cingam qas qasa tace
"Nagode Samari, se wani jiqon"
"Shege Abokina wlh ka samu shiga, kasan uban nacin da nayi akan yarinyar nan kuwa amma taqi bani fuska? Kai bani kadai ba kowa mararinta yakeyi amma yarinyar nan yanda kasan kudi wahalar samu ne da ita, daga qusoahin gwamnati se Sarakuna take kulawa" Bashir ya fada yana dukan kafadar Audu.

Ali yaja tsaki yace
"Wlh kayiwa kanka fada karka kuskura ka bari shaidan ya maka ingiza me kantu nidai babu ruwana daga yau ma in sha Allah bazan sake binku fita irin wannan ba"
"Nifa na gaya maka sonta nakeyi dagaske" Audu ya fada bayan sun hau titi. Bashir ya ringa dariyar iskanci yana cewa
"A sannu dai duk zasu hau saiti, wato ina gaya muku dadin duniya a sha ruwa ga mata, kai Allah ka yafe mana kurakurenmu".
Haka har suka iso Kano.

Ba'a rufa sati ba ya kama hanyar Zariya ba tareda ya sanarwa da Abokanansa ba saboda yanda tunanin Zuby ya addabeshi, yaje gidan da suka ajiyeta wanda se sannan ya gane nan ma gidanmata masu zaman kansu ne, ya rasa ta inda ze fara nemanta. Har gurin Magajiyar gidan aka kaishi tace babu Zubaida a gidan haka ya haqura ya dawo Kano da qunar zuciya sedai duk yanda yayi akan ya yakiceta ya haqura da tunaninta abin yaci tura. Gaba daya ya shiga damuwa ya zaman har walwalarsa ta ragu. Da Binta ta matsa masa da tambaya se ya ce mata Asara yayi, aiko ta si ta fishi shiga tashin hankali ma dan Binta na son kudi, dukiyar Audu kuwa jinta take kamar tsokar jikinta a kullum zancenta Duk abinda yake dashi nata ne tunda itace sila shiyasa take baqin ciki idan yayi Alkhairi wa wasu, ta bangarenta kuwa duk abinda take dashi ko take samu babu me ci, hatta a karan kanta mugunta takeyiwa kanta dan da wani ya mori abu tareda ita gara ta haqura da abun itama.

Wata biyu Audu ya kwashe yana dakon soyayyar Zuby, dayaga abin baze fita daga ransa ba tilas ya samu Bashir ya roqeshi akan ya nemo masa ita.
"Wlh sonta nake Bashir kuma da Aure" ya fadawa Bashir din.

"Amma dai Audu baka da hankali, to ai koni da nake cikakken dan Bariki iyakata da Karuwa na biya buqata ta mu rabu a gurin duk matan da suke yawo a garin nan ka rasa wa zuciyarka zata so se Karuwa? Hauka kake ko shaye shaye ka fara?" Bashir ya fada cikin madaukakin mamaki.

"Nidai idan zaka nemo mun ita kawai ka nemota Malam babu ruwanka ko Magajiya ce a hakan naji na gani kuma ina sonta in har ta amince kuma auranta zanyi" Audu ya bashi amsa cikin tsare gida. Bashir ya kunna sigarinsa yana zuga yace

"Babu shakka Haqqin Bara'atu ya fara dabaibayeka tun ba aje ko ina ba, ka saki yar gidan mutunchi me Cikakken Asali zaka maye gurbinta da Karuwa to Allah ya kyauta ka shirya gobe muje Zariyan, da kace musu Yar Dagwas da tuni an nemo maka ita sedai kuma idan suna ta canza a can dan halin matan Bariki ne basa amfani da sunansu na Ainihi.

*MATAR MUTUM*
*NA MARYAM FAROUK (UMMU MAHEER*

*FIKRA WRITERS ASSOCIATION*

*LITTAFIN KUDI NE*
*PAY 500 A ASUSUN*
*7061838488*
*OPAY DIGITAL SERVICES*
*MARYAM FAROUK*
OR
*0709290797*
*ACCESS BANK*
*SE A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488*
*IDAN KATINE A DAUKI HOTONSA A TURA ZUWA LAMBAR SAMA VTU KUMA A TURA A 08142548705*

*Kuyi following dina a Arewabooks @Maryamfarouk01 inda zaku karanta wannan littafin tareda sauran littattafaina*
*NAGODE*

*PAGE 16*

Kamar yanda Bashir ya fada suna isa suka tambayi yar dagwas se gasu a dakinta aka rakasu. Zubaidan na kwance kamar mara lafiya suka shiga, ta ringa kallonsu da mamaki dan bata gane Audu bama Bashir dai data fi waya shi ta gane.
"Lafiya? Tara ko bashi?" Ta fada cikin tsiwarsu irin ta yan Bariki bayan data miqe tsaye. Audu dai se binta yake da kallo Bashir yace

"Ai kya bamu gurin zama musha ruwa tukunna yar dagwas", tayi gatsine kafin ta dauki wani siririn mayafi ta yafa a kanta da babu dankwali ta fita tana tafiya a hankali.
"Duk yanda akayi dan Hau ta hadu dashi ya lakada mata na jaki shiyasa ka ganta haka" Bashir ya radawa Audu. Wani duumm yaji a zuciyarsa, shikam So be kyauta masa ba ya rasa macen da ze zargo masa se yar bariki wadda jikinta bashida shamaki da Maza.

Zuby ta dawo da kwalabe uku a hannunta, biyu na Giya is Coca cola daya ta ajiye a gabansu.
"Ga naka nan wadannan nawa ne" Bashir ya fada yana tura masa Coke din. Seda ya zuqe kwalba guda kafin ya kalli Zubaida dake zaune daga gefe ta jingina tana kada qafa yace
"Tafiyar ta Aboki na ce, kwanaki ma yazo yayi ta bulayi ni ban ma san ya akayi yasan sunanki Zubaida ba yazo haka ya koma ba tareda ya sameki ba, bari na baku guri na dan nemi inda zan rage lokaci" ya fada yana miqewa da dayar kwalbar a hannunsa.

"Kaga jashi ku tafi ni ba lafiya ta isheni ba kuma ko qalau nake kasan tsadata ba haka nan ake fado mun ba kamar wata mara Aji" ta dakatar da Bashir din, se yayi murmushi yace
"Al'amarin da yake tafe dashi yafi wannan kedai ki saurareshi kawai" daga haka ya fita ya barsu.
Audu ya muskuta yana kallonta soyayyarta na qara huda zuciyarsa yace
"Bakida lafiya ne"
"Matsala aka samu nayi ciki, uban yace ze karba kuma naga kar daga baya yazo ya mun Akuya na zubar" ta fada masa kai tsaye kamar wadda ta aikata abin kirki, is ya kasa cewa komai ya zuba mata ido kawai zuciyarsa na bugawa.

Ina jinka fadi abinda ya kawoka dan kwanciya nake so nayi" ta sake fada tana gyara zama, zaman shima ya gyara ya fuskanceta dakyau kafin ya shiga zayyano mata abinda yake cikin zuciyarsa dan ya gaza dannewa,
"Kuma ni da Aure nake sonki, ina so ki bar wannan rayuwar ki koma gida gaban iyayenki wannan rayuwar bata dace da Mace kamarki ba, ki je kiyi Istibra'i zan aureki".

A duk maganganunsa fadar ta koma gida gaban iyayenta ne ya jefata a wani hali ya tado mata da tsohon mikin dake zuciyarta nan da nana hawaye suka wanke mata fuska. Kewar gidan da Mahaifanta ya taso mata se gani yayi ta hade kai da guiwa tana kuka wiwi. Hankalinsa ya tashi da kukan da take ya kuma shiga mamakin me ya sakata kuka, shidai ba wa'azi yayi mata ba balle ace tsoron Allah ne ya ratsata kawai ya gaya mata yana sonta ne ze Aureta amma take wannan kukan kamar wadda zata mutu take.

"Ki dena kuka dan Allah" ya fada cikin rabewar murya.
"Ka tashi ka fita" ta bashi amsa cikin bada umarni. Ya tsaya amma tsaqar data buga masa tasa dole ya fita cike da mamakinta ya zauna a qofar dakin.

Zubaida kuwa tana kuka ta koma tunanin Baya, gida take tunuwa da mahaifiyarta tareda sauran yan uwanta da kuma dalilin daya fito da ita. Duk ranar da aka ambaci Iyaye ko Gida se tayi irin kukan nan, tana so ta sake ganin nata amma bata da hali. Kalaman Mahaifinta suka dawo mata sanda yake korarta daga gida.
"Ki tafi, idan kika sake waiwayarmu Allah ya isa iyakar abin kunyar da kika jamun ya isa ki tafi duk inda zakije Zubaida na yafeki daga cikin Yayana".

Cikin dare ya koreta, ba tareda yayi tunanin ina zataje ba wane hannu zata fada kuma ya gaya mata karta kuskura taje gurin danginsa kona mahaifiyarsu. Hatta da yan unguwa da suka tausaya mata suka so bata mafaka Tijara yayi musu yace ze hada duk wanda ya shigar masa hurumin gida da hukuma haka ya koreta se tasha taje ta samu mafaka duk akan dalilin Qaddarar data fada mata wadda shine sila. A dalilin kasa sauke nauyinsu da Allah ya dora masa na ciyarwa da sauran buqatu ya tilasta mahaifiyarta fara dora mata tallan shinkafa da wake tana kaiwa Bakin Kasuwa kuma a nan ne qaddara ta hauta wani Azzalumi yayi mata wayo yayi mata fyade, shekararta goma a sannan, ya gana mata Azabar data fitar da ita daga hayyacinta qarshe ta farka ta ganta a gidansu Kwance ga Mahaifiyarta na Kuka Mahaifinta kuma na Sababi kamar zeyi Aman wuta.

Yana ganin kuma ta farka be duba komai ba yace ta tashi ta fitar masa daga gida, a fadar sa daman an sha gaya masa ana ganinta a shagunan Maza, ko a sannan din be yarda Fyade akayi mata ba, a yanda wanda suka tsinto ta suka gaya masa wai ciki ta zubar, wanda ya bata maganin ya gudu se ita suka tsinto cikin Jini a wani kango. Babu dogon tunani babu komai Mahaifinta ya yanke wannan danyan hukunci na korarta a cikin dare. Beyi tsinkayen cewa a sannan ko Al'ada bata fara ba ballantana ace ta dauki ciki, yayi mata korar kare cikin rashin Imani, Mahaifiyarta da qannenta naji suna gani tabar gidan shekaru goma kenan kuma kamar yanda ya fada bata sake koda taka qafarta a qasar Kano ba da Asuba tabi wata mata Mai siyar da Abinci a tasha daman ta santa idan ta kawo tallah tana gaisheta matar tasan abinda ya faru da Zubaidan dan haka data ganta cikin daren bata tambayi ba'asi ba kawai ta dauketa ta kaita dan dakinta na langa langa dake cikin Tashar. A nan ta gyarata tayi mata wanka ta kuma bata Abinci washe gari da Asuba suka hau mota suka bar Kano dan dama taga matar ta hada kayanta tsaf da alama zatayi Balaguro, bata tsinci kanta a ko ina ba se a Kwantagora, da fari Abinci suke siyarwa da giya a nan gidan daga matar ta ingizata zuwa ga wannan rayuwar da take nadama da dana sanin shigarta.

Takanyi kuka tace me yasa bata tsaya ba Babanta ya halakata tunda yace idan bata fita ba seya kasheta? Data sani ta zauna ya kashe ta ta mutu tun sannan qila da tana Aljanna abinta da wannan qazamar rayuwar data jefa kanta a ciki.

Audu na qofar dakin yana jiyo kukan ta daga ciki, kasa daurewa yayi ya koma ya tsaya akanta yana ganin yanda take kuka har jikinta na jijjiga.
"Dan girman Allah kiyi shiru, idanhar maganar so ko aure danayi miki ce ta sakaki wannan kukan na janye na haqura ke dena Kukan haka" ya fada cikin sigar lallashi. Bata bari ba, haka ya kai tsugunne ya ringa lallashinta da kalamai masu kwantar da hankali. Shida kansa yayi mamakin inda ya iyasu, be haqura ba har seda ta dena kukan tana ajiyar rai da jan majina.

"Kiyi tunani akan maganata" ya sake fada mata ba tareda ya sare ba.
"Ta yaya mutum kamarka me kamala, na fahimci ba halinka daya da Abokinka ba ya za'ayi kace zaka auri Karuwa kamata wadda bata da mutunchi ballantana daraja?" Ta fada hawaye na sake sakko mata.

Audu ya zauna da kyau ganin ta sakko tana so suyi magana yace
"Nima ban sani ba, amma na tabbatar qila Allah ne yaso dana zama silar fitar dake daga wannan rayuwar shiyasa ya doramun sonki. Sannan maganar Mutunchi ko Daraja, ban sanki ba bansan daga inda kika fito ba amma na tabbatar koma daga ina kike kin kasance Mace me Mutunchi da Daraja a baya, qaddara ce ta kawoki nan domin mata kadan ne suk shiga Bariki da son ransu, mafi aka sari Qaddara ce take afka musu wadda mutane suke kasa yi musu uzuri harsu ingizasu ga zuwa abinda yafi wanda ya same su a baya muni.

"Duk abinda dan Adam yake aikatawa muddin be mutu ba yana da damar shiriya ya nemi yafiyar ubangijinsa, kema lokaci be qure miki ba. Ki bar wannan rayuwar da babu komai cikinta se qasqanci, ki koma gida wlh da gaske nakeyi zan aureki bada wasa nake sonki ba".

"Mahaifina ya koreni, yace karna sake komawa gidansa idan har naje be yafe mun ba. Ina so naje, ina kewar mahaifiyata amma bana son na sake shiga wani fushin nasa akan wanda nake ciki" ta fada cikin sauti me ban tausayi.

"Ke din yar wane gari ce? Kuma meya fito dake daga gida?" Audu ya tambayeta. Bata boye masa komai ba na daga labarin rayuwarta ta gaya masa gaskiya, yaji tausayinta kwarai dagaske ya kuma ga baiken Mahaifinta. Irin wannan qaddarar ta fadawa mata da yawa, idan da ace iyaye suna taya Yayansu karban qaddararsu a yanda tazo musu da an samu raguwar masu fantsama Bariki. Da yawan iyaye Sukan manta cewar Abin kunyar da suke tunqahon yayan sun jawo musu har yasa suka kada su duniya kadan ne akan rayuwar da suke jefasu suyi, ga dakon zunubi domin duk abinda suka aikata na barna tare za'a raba musu Sakamakon da iyayen saboda sune suka turasu zuwa ga barnar. A tunanisa da a ringa zunden mutum ana cewa yarsa ta zama Karuwa gara a kira shi uban wadda aka tabayiwa Fyade ko tayi cikin shege ya barta a gabansa ta shiryu har ya aurar da ita wannan haqurin da mutum yayi se ubangiji ya dubeshi ya shirya masa zuri'a amma korar yara akan wata qaddara mara kyau ba daidai bane, su kansu Iyayen sunyi bankwana da kwanciyar hankali daga ranar da suka kori Yayan nasu basa sake samun nutsuwa.

Audu basuje Zariya da niyar kwana ba amma Alamun cin galaba akan Zubaida daya gani ya sakashi kwana a garin. Yayi mata alqawarin ze nemo mata mahaifinta muddin yana raye ze hada su kuma koya mutu ze maida ita gida gurin ragowar yan uwanta. Ya roqeta akan ta shirya su tafi Kano tare, ze bata mafaka har zuwa sanda zata daidaita da iyayenta amma taqi, tace dai yaje ba zata dawo idan har mahaifinta ya mata izini.

Haka washe gari suka dawo Kano gaba daya Audu bashi da kuzari, Bashir nata yi masa shaqiyanci da cewar shima ya zama dan hannu dan tunda suka rabu basu hadu ba seda safe da zasu wuce Kano dan haka besan duk abinda ya faru tsakaninsa da Zubaida ba.

A gida ya tarar da Binta cikin yanayi na neman tashin hankali dan yana shiga tambayar data fara jefa masa itace
"Daga gidan uban wa kake?"
A lokacin yanayin sanyin jiki da kuma martabar mahaifinta da ya wuce ya zageshi ya saka ya qi tanka maka amma kaitsaye zuciyarsa ta ringa raya masa ya gaya mata daga gidan ubanta yake ko da abinda zatayi akai. Bata haqura ba ta bishi har daki tana ihu da hargagi tareda fadar maganganu. Baturiya matar Ali ce ta gaya mata Audun sun tafi wani gari gurin Mata tareda Bashir itama tsintar zancen tayi a gurin Mijinta yana gayawa wani Abokinsa daya je gidan shine ta wanke qafa ta tafi gidan Binta ta gaya mata ranar bata iya runtsawa ba a tsaye ta kwana tana jiran taga ta inda ze bullo amma be dawo na se yanzun.

Duk kalar rashin mutunchin data ringa zazzagawa be tanka mata ba ya shige daki ya kullo qofa ya shiga wanka. A ranar yake so yaje ya fara binciken iyayen Zubaida data gaya masa ita din haifaffiyar unguwar Alkantara ce, sanda ya fito Binta ta sauka daga saman harya fita kuma beji motsinta ba ya dauki mota ya bi kwatancen da Zubaida tayi masa besha wahala ba saboda sunan Mahaifinta data gaya masa Malam Hassan Na'ibi yana fada aka kaishi har qofar gidan lokacin qarfe biyar na yamma rana tayi sanyi a qofar gidan ya tarar da Malam Hassan din da wasu dattijai guda biyu kan tabarma suna hira.

Ya ringa kallon mutumin, kamanninsa daya da Zubaidar, sedai yanayinsa ya nuna kamar bashi da lafiya saboda a kishingide ma yake be iya zama sosai. Audu ya qarasa kan tabarmar ya zauna suka gaisa duk suna masa kallon rashin sani.
"Gurinka nazo Baba, idan babu damuwa ina so zamuyi magana ne" ya fada yana kallon Malam Hassan ganin haka ya saka ragowar suka gane baqonsa ne.


*MAMAN MARYAM ONLINE BUSSINESS*

*Ina kuke Mata Yan kwalisa , Ina nufin isassun Mata ,Wai shin Kuna da labarin shahararren company nan namu na GHT wato good healthtreatments*
*Wanda yazo muku da fitattu Kuma* *ingantatattun suppliment ,na dukkan matsalolin ku*S'

*Ina maisan tayi kyau,irin na isassun Mata ya fitar Miki da shef dinki tayi Miki gyara in and out ,nemi royal jelly dinmu na company GHT*
*Wanda aka yishi da xuma ,kundai San amfanin Zuma basai na fada miku ba , hajiya ta kixo ki Yi gyara domin ki kerewa sa,a kije taro ko baki da ko sisi kiji Ana rangada Miki hajiya , saboda yanda Zaki Kara kwarjini ,kina walwali acikin

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login