Showing 261001 words to 264000 words out of 467220 words

Chapter 88 - MATAR MUTUM COMPLETED 1-3 BY MARYAM FARUK.doc

23 Sep 2025

12160

DIGITAL SERVICES*
*MARYAM FAROUK*
OR
*0709290797*
*ACCESS BANK*
*SE A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488*
*IDAN KATINE A DAUKI HOTONSA A TURA ZUWA LAMBAR SAMA VTU KUMA A TURA A 08142548705*

*Kuyi following dina a Arewabooks @Maryamfarouk01 inda zaku karanta wannan littafin tareda sauran littattafaina*
*NAGODE*

*BOOK 3*
*PAGE 2*

"Kawai ji nakeyi kamar na fasa auran nan, banajinsa sam ina tsoron kar na auri Fatiyyah kuma na kasa bata farin cikin da ya kamata ta samu da ace za'a fahimce ni dana ro?i koda ba'a fasa ba a ?aramun lokaci zuwa sanda zanji I'm fully ready" Jafar ya faWa cikin wani yanayi da alama akwai wani abu da yake Soyewa can ?asan ransa.

Ahmad ya zauna kusa dashi ya kama hannayensa biyu cikin nasa yana kallonsa yace
"Tell me Jafar menene matsalarka? Tun waccen ranar ka canza, daga wancan lokacin komai ya birkice maka, akwai maganganu da yawa a bakinka amma ka kasa furtasu. Jikinka da fuskarka sun rigada sun fallasa abinda kake rufewa a zuciyarka, ka dubi Allah idan har ka yarda ni jininka ne kuma zan iya share maka hawaye ka faWamun mecece damuwarka koda kana tunanin bani da magani ka gaya mun na sanyaka a addu'a".

A hankali Jafar ya zare hannunsa yana ?a?alo murmushin dole yace
"Babu komai Yah Ahmad ka yarda dani kawai dai auran ne nakejin bana so nayi yanzu kamar kuma ita Fatiyyan ce bata gama kwanta mun a zuciya ba"

"Ina Afeeyah?" Ahmad ya sake jefa masa tambayar yana tsatstsareshi da ido yaga sanda Adams Apple Win Jay yayi sama ya koma ?asa kamar wanda ya haWiyi wani abu me tauri, idan beyi ?arya ba har hawaye yaga ya taru a idonsa ma, sau biyu yana buWe baki da niyyar yin magana amma ya kasa se kawai ya mi?e daga kan gadon.

"I'm asking you ina Afeeyah? In har ba mutuwa tayi ba ko kuma aure tayi ka maidota ta cike gurbin data bar maka ya zame maka ciwo a zuciyarka, it won't be so easy, amma in har iyayenta sun yarda zasu aurar da ita in two weeks time ni Ahmad nayi maka Al?awarin samar maka da cikar farin cikinka" Ahmad ya sake faWa daidai sanda Jafar ya isa ?ofar toilet, a sanyaye ya waigo ya kalli Ahmad Win yayi murmushi a zuciyarsa yana ayyana cewa

"Cikar burina na nufin rugujewar naka farin cikin Yah Ahmad, ni zan iya dannewa amma kai ba zaka iya ba" a fili kuma yace
"Ka jirani bari na watsa ruwa muje".

Tafiya sukeyi tamkar kurame kowanne da tunanikan da suke yawo a cikin zuciyarsa, har sun kama hanyar gidansu Fatiman, Alisco Tailor da Ahmad ya bawa Winkunansu na fitar biki ya kirashi se kawai ya juya akalar motar suka tafi gurinsa, a can suka bata lokaci gurin gwaji kusan an gama na Ahmad se abinda baza'a rasa ba na Jafar ne ba'a fara haWewa bama saboda beje yayi fittings ba se lokacin aka Wauki measurement Winsa. Kayane sunfi kala 20 kowannensu kuma duk iri Waya Ahmad Win yayi musu. Ya nunawa Jafar wata Musulmar Shadda se ?yalli take tana haske ido yace

"Alhaji ne ya bamu 20yrds yace ita zamu saka ranar dinner, suma Matan an siya musu Fabric iri Waya"

"Uhm" Jay ya bashi amsa dan tunda ya taso masa da maganar Afeeyah Wan ragowar ?arfin halin da yake yi nema yake ya gagareshi yayi breaking down.

Seda sukayi sallar magriba kafin suka kama hanyar Alfindiki, garin sanyi nan da nan duhu yakeyi dan haka kafin su isa gidansu Afeeyar dare ya rufa, inda Ahmad ya saba parking ya ajiye mota suka tattaka, tun suna hanya daman ya kirata akan gasu nan zuwa ya kuma jaddada mata da karta manta da list Win da yace mata tayi yaji muryarta babu daWi amma be wani mayar da hankali ba dan yanzu yayi karatu akanta ya fahimci sanda yake ?o?arin nuna mata damuwarsa sannan take zuge masa zogalen rashin mutunchi amma idan ya kama kansa sunfi daidai tawa.

Akan dakalin ?ofar gidansu Afeeyah Jay ya zauna saboda tsayuwar ba zata yuwu masa ba ya gode Allah daya kasance basu da wuta, ya sake gyara zaman hukar dake haWe da rigar sanyin jikinsa ya jata sosai ta rufe masa rabin fuska Already ga uban face mask ya saka, bazeso suyi creating wani scene a gaban Ahmad ba, koda ze warware mata to daga shi se ita se yasa yayi shiri da kyau domin baya so ya bayyanar da fushin fuskarsa harta samu damar da zata takaleshi.

A gefen Fatima kuwa yinin ranar zir cikin damuwa da zullumi tareda sharar hawaye tayishi, Badar ta sake kiranta ta kwantar mata da hankali tareda sake jaddada mata akan kartayi maganar da kowa tukunna su jira su ga abinda hali zeyi.
"Ki kwantar da hankalinki muci gaba shirin biki dan Allah, ya kamata ma zuwa yanzu ace Ahmad ya sallame mu, kiyi masa magana saboda mu samu mu tsara komai da zamuyi akan lokaci ga Winkunanki ma an gama duka wannan Fabric Win na Dinner ne kawai yayi saura yace zan tura miki da bill Win" cewar Badar. Suna gama maganar Ahmad ya kirata yace zezo, kamar tace masa ya bari se gobe dan dan ita yanzu bata san ma da yaya zata kalleshi ba se kuma ta daure kawai tace masa toh, seda ya ce mata gasu a waje kafin ta tashi daga gurin da tayi sallah ta canza Hijabin jikinta kawai fuska jeme jeme ta fita, harta kai soro tunanin gasu, shi da wa kenan yake nufi? Ya dakatar da ita.

Wani bugu zuciyarta ta shigayi tamkar numfashinta ze Wauke sanda take ayyano shida Jafar ?ila yake nufi,
"Bashi bane, Ammar ne ko Bunu Abokanasa da yace mata zasu zo tare saboda suna ta damunsa akan suna so suga Amarya da ?awayenta suji tsare tsaren da suke dashi na biki da wannan ta samu ?arfin guiwar fita dukda jikinta a sanyaye yake murya kamar ta munafukai tayi musu sallama sanda ta isa ?ofar gidan.

"Barka da fitowa Amarya" Ahmad ya faWa bayan daya amsa mata sallamar. Kanta a ?asa tana wasa da yatsunta ta gaidashi, ya amsa kafin ya juya inda Jay yake zaune yana cewa

"Wai bakaga Yayarka ta fito bane kana zaune ba zaka taso ta kama Sannu da fito...." Maganarsa ta katse sanda ya lura Jay baya gurin, se ya shiga waige waige, daga can kan layin ya hangoshi ya juya baya waya kare a kunnensa seya girgiza kai kawai yana kallonta yace
"Shifa haka yake da satar jiki ba zakiji motsin shiga ko fitarsa ba sedai kawai ka nemeshi ka rasa, toh ya kike? Ya Amarci? duk ki cika atmosphere Win gurin nan da ?amshin Amarci ya kamata nima ki samminko?"

"Uhm" kawai tace kanta a ?asa har sannan haka kuma harshenta yayi mata nauyi ta kasa tambayar wanene suka zo tare. Magana yaci gaba da yi mata tana bashi amsa a ta?aice,

"Yau dai ga Abokin rigimarki Jafar na kawo miki" ya faWa yana kallonta, take ta ?ware da miyan bakinta, abin ya zamar mata biyu ga wani mahaukacin bugu da zuciyarta ta shigayi kamar zata huda ?irjinta ta fito ta ringa tuttula tari tamkar zata shiWe duk Ahmad ya rikice ya rasa me zeyi se sannu yake jera mata daidai nan Jay daya gama tattara duk wani ?arfin guiwa da yake dashi ya ?araso gurin,

"Shiga ciki dan Allah ka amso ruwa a bata" Ahmad ya faWa masa, wani kallo me kama da ka rainamun wayau ya watsawa Ahmad Win gane hakan yasa shi da kansa be jira komai ba ya shige gidan a rikice dan yanda take tuttula tari kamar zata shiWe abin ba kyau. Yana shiga aka kawo wuta, ringa rafka sallama a tsakar gidan amma shiru babu kowa, ruWewar da yayi tasa beko tuna da freezer Umma dake cikin barander ba balle ya Wauka ruwan ya tafi ya tsaya yana ta jera sallama.

A waje kuwa Ahmad na shigewa Jay ya matsa kusa da ita yana ?are mata kallo cikin hasken fitilar data dakke ?ofar gidan, Afeeyah da tarin ya lafa mata itaka ta Waga kanta sukayi ido huWu dana Jay da suka kaWa suka canza kala sukayi mici mici kamar zasu fesar da wuta, irin kallon da yakeyi mata ya saka hantar cikinta kaWawa, zuciyarta ta tsinke sauran tarin da takeyi ya kama gabansa

"Ma?aryaciya, Mayaudariya, Muguwa, Azzaluma, Macuciya, in fact babu wani suna da zan kirayeki dashi da ze saka zuciyata tayi sanyi akan abinda nakeji a yanzu, Kin cutar dani Afeeyah, kin cutar da zuciyar Wan uwana da babu komai cikinta se sonki da burin kyautata miki me mukayi miki da mukayi deserving wannan sakayyar daga gareki?

Koda yake i will not demand any explanation from you now, abu biyu nake so na gaya miki, na farko, not in your weirdest dream zakiyi tunanin sanar da Yah Ahmad wani abu daya faru tsakanina dake a past, i dare you to break my brother heart wlh a lokacin zaki san cewa you have messed with the wrong guy sannan kar kiyi tunanin cewar yanzun ma zaki tafi free no, kin tuna Al?awarin da nayi miki a baya? Zan cika miki su. Fatima I'm going to make your marriage life miserable, i will be your worst nighmare bazan taSa hutawa ba har sena SalSalta rayuwarki na lalatata ta yanda harki mutu na zaki dena nadamar shiga cikin Ahalinmu ba this is my promise to you, farin cikin da kike tunanin zaki samu bayan cutar da zuciyoyin da suka so ki tsakani da Allah baze tabbata ba"

"Kai har kana da bakin da zaka gayamun wata magana Jafar? Daman akwai sauran mugu kuma azzalumi a duniyar nan bayan kai? Tun asali na tsaneka Jafar na tsani duk wani wanda ya raSu da kai. A yanzu tsanar da nayi maka ta sake nunkuwa, wlh ko me sunanka bana so naji an ambata balle ace kaida kanka zan gani a gabana, Wlh badan ina tsoron Allah ya kamani da ha??in Ahmad ba da a yanzu zan ce na fasa auransa kuma a hakan ma zanyi addu'a na nemi zaSin Allah idan har babu Alkhairi a rayuwata dashi Allah ya musanya mun da wanda ya fishi shima Allah ya bashi wadda ta fini Alkhairi a rayuwarsa kuma wlh bazan taSa yafe maka ba, yaudarata da kayi kasa na soka se Allah ya saka mun, Allah ya isa taSanin da kayi, dama nayi zargin wani mugun nufi a ranka na kuma godewa Allah da be baka nasara akaina wani abin kaico ya faru tsakanina da kai ba kuma in sha Allahu se kaga sakayyar abinda kayi mun nan kusa ba da daWewa ba Allah ya isa" Afeeyah ta faWa cikin matsanancin kuka daidai nan Ahmad ya fito kici kici da ruwa a hannu kukan ta ya ke jiyowa daga cikin soro ya sa ya Wago ?afa yana zuba sauri ya fito.

Jafar ya gyara tsayuwarsa yana jifanta da wani kallo ya sake cewa
"Kin san Allah kika tunzurani a gurin nan zan murWe miki wuya na rage mugun iri amma babu komai" yaja ?wafa, Ahmad ya kwarara masa tsawa cikin tsananin Sacin rai yace

"Dama dalilin daya saka ka yarda ka biyoni kenan saboda kazo ka zubar mun da mutunchi ka wula?anta matar da zan aura? Nagode Jafar nagode daka nuna mun iyakata" seya juya kan Fatima dake rusa kuka kamar iyayenta ne suka mutu badan sanyi yasa kowa ya shige gida ba da tabbas sun tara yan kallo a gurin. Ha?uri ya shiga bata kamar ze ari baki ita kuma kamar yana tunzurata kuka take kamar me, daman tuni Jay ya bar musu gurin saboda wani nauyi da ?irjinsa yayi masa yanda yaga Ahmad ya marairaice a gabanta yana bata ha?uri, can bakin titi ya tafi ya jingina da motarsu ya runtse ido hawaye me Wumi ya ziraro masa ta gefen kunne.

Ko ?warzane beji ya ragu daga tarin son da yakeyiwa yarinyar ba, ta yaya ze rayu da son matar ?an uwansa? Me yasa Afeeyah tayi musu haka? Me yasa ta zaSi wannan hanyar? A hankali ya kifa kansa a jikin motar be damu da cewar bakin titi yake ba ko wani abu ya baiwa hawayensa damar sauka bisa kuncinsa wasu na korar wasu. A fili ya furta
"Allah na tuba, Allah ka sassautamun wannan jarabawar tayi mun tsauri da yawa ya rabbi matar Yah Ahmad take shirin zama Allah ka ciremin son ta daga zuciya karka bari shaiWan yayi tasiri a kaina".

TaSa motar da akayi yasa ya shiga goge fuska da saurin gaske sedai fushin da Ahmad Win yakeyi be sa yama fahimci halin da yake ciki ba. A hanya kamar Ahmad ze cijeshi tsabar yanda yake masa bala'i shidai bece komai ba, ya juya ya haWe kai da gilashi abinda ke zuciyarsa kawai ma ya ishe shi. Suna isa gisa kowa ya kama hanyarsa, Ahmad ya shiga cikin gida shi kuma ya wuce Waki dan kwanciya kawai yake so yayi yasan ma seya haWa da sleeping pills in har yana so yayi baccin da ze saka ya manta da wani kaso na damuwarsa.

Yana aje ha?ar?arinsa akan gadi bayan ya rage kayan jikinsa Hajiya ta banka musu ?ofa.
"Yanzu Jafaru bana gargaWeka akan ko hanyar unguwarsu mayyar yarinyar can da Amadu ya jajibo kar naji an ganka a gurin ba shine ka faki idona ka bishi kuka tafi tun La'asar se yanzu zaku dawo kuma kazo ka kwanta ba ko ka shiga ka cemun ka dawo ba tunda daman da zaka tafi ai bakayi mun sallama ba ko?"
Cikin taratsi take maganar dan har seda ya toshe kunnensa saboda kans ada yake bala'in sara masa. Bata ko aje numfashi ba ta sake cewa
"Kuma ina ka ajiye wayarka? Ashe daka dawo baka kira wannan yarinyar ka ce mata ka sauka ba ka barta cikin zulummi se kirana take tana rusa mun kuka duk da nace mata kazo gida amma hankalinta ya kasa kwanciya banda sakarci kuka ka kwashi ?afa zalo zalo ka tafi raka wani zance"

"Hajiya Dan Allah kiyi shiru" ya faWa yana tashi zaune dafe da kai kafin ya sake cewa
"Na gaji bacci nakeji kuma indai Fatiyyah ce munyi magana da ita tun Wazu"

"Na shiga uku ni Binta badai har sun zarge maka kurwa sun fara lasarta ba? Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un billahillazi Amadu da Aisha sunyi kaWan, wlh ko zan tafi tsirara se naga bayan duk wanda yace ze taSa rayuwarka ?arya sukeyi wlh basu isa ba bari ma ka gani ina zuwa" ta faWa kafin yace wani abu tuni ta fice daga Wakin, bashi da ?warin jikin da ze bita dan haka ya koma ya kwanta cike da takaicin halin mahaifiyarsa, yanzu wane tashin hankalin zata kunno a daren nan kuma?

Hajiya kuwa cikin gida ta wuce kayya kayya tana surutai da zazzagar maganganu da babu wanda ya fahimci inda zancenta ya dosa. Ta wuce Wakinta ta Wakko wani magani da Turai ta taSa karSo mata na miyagu sanda aka kawo mata wata me aiki ashe mayyace ce, uhm ansha buduri dai abu ya wuce. Ta wuce tafi gefen masu aikinsu mata ta ringa surfawa Adama kira itace ta hannun damanta cikin masu aikin makwafin Lantana ce sak ta samu ita ta saka ta kwaso mata rushi a ?aton Kasko suka koma Wakinsu Jafar yana kwance yana jinyar zuciya se ji yayi yayan Aljanu na neman toshe masa ?ofofin shigar iska ya wuntsula ya tasha Hajiya na tsaye akansa tana zare ido tana watsa turare a wuta, ?a'idar turaren idan anayi ba'a magana kuma fakar mutum ake a masa saboda kar Aljanun mayun da suka dabaibayeshi su ankara su gudu shi yasa ta shigo saWaf saWaf shi kuma zurfin da yayi a tunani yasa beji motsinta be seda haya?i ya kai masa sumame.

FATIMA
Yanda ta ringa kuka tana tumami ya Wagawa Umma hankali harta fara tunanin ko gamo tayi gashi ta shige Waki ta kullo ?ofa, da Baffa ya dawo yace mata ta rabu da ita, koma menene ita da kanta zata buWi baki tayi magana, hankalin Umma be wani kwanta ba amma dai tabi ta tashi suka rabu da ita. Tun jiyan take lura da ita bata cikin walwala toh amma me ze sakata irin wannan kukan sannan yanda Ahmad ya shigo a gigice nemar mata ruwa duk meyw dalili?

Washe gari bakwai bata gama cika ba tayiwa Umman Sallama akan zata tafi gidan Anty Sauda. Tun kwana uku da suka wuce ya kamata ace ta koma can gidan an fara mata gyaran jiki amma ta?i se gashi da wuriwuri ta tattara kayanta tacewa Umman ta tafi tace mata toh koma menene dai zataji a bakin Sauda. Acan ma seda ta gama tayarwa da Anty Saudan hankali har itama ta shiga tayata kukan kafin ta iya buWe baki ta sanar mata wai Jafar ?anin Ahmad ne ta kuma gaya mata abinda ya faru jiya da sukaje. Anty Sauda ta kaWu matu?a itama harta rasa abinda zata ce mata.

Seda ta gama jimami kafin ta iya cewa
"Kaina ya ?ulle Afeeyah, ya akayi haka ta faru? Ta yaya zakiyi dating Wa da ?ani kuma kice baki sabi ba? Ai babu ma me yarda da wannan maganar"

"Wlh ban sani ba Anty, mecece ribata idan na sani kuma na aikata? Dame hakan ze ?areni?" Ta faWa cikin kuka. Anty Sauda ta sake cewa
"Toh a kullum dai cikin addu'a muke akan Allah yayi mana zaSin Alkhairi a rayuwarmu duk abinda kuma mukaga ya faru daga Allah ne, abinda zance miki kawai kici gaba da addu'a ki kuma saki zuciyarki komai ya wuce karki bari maganganunsa suyi tasiri a zuciyarki tunda dai Allah ya gani bada saninki komai ya faru ba sannan kamar yanda yace miki ne karki kuskura ki gayawa Ahmad wata magana akan abin nan, yanda Allah be saka ya sani ba ki barshi a haka Allah ya wuce gaba ya kiyaye sake afkuwar wani abu irin haka. Sakayya cema Allah yayiwa Ahmad Win, irin wahalar dashi da kikayi kema kin WanWani son wani kuma kin rasashi se ki mayar da hankali ki rungumi abinda Allah ya zaSa miki kuma ki gode masa da besa kinyi biyu babu ba".

"Nifa Anty na ha?ura, bazan iya auran Ahmad alhalin yana Yayan Jafar ba" Afeeyah ta faWa cikin kuka, Sauda ta mata kallon baki da hankali kafin tace

"Baki goge shafin Jafar daga zuciyarki na kenan? Ai

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login