Showing 414001 words to 417000 words out of 467220 words

Chapter 139 - MATAR MUTUM COMPLETED 1-3 BY MARYAM FARUK.doc

23 Sep 2025

12180

ta karSa ni bana son jidali" Momy ta faWa tana ajiye masa kason hajiya daga nan suka masa sallama kowacce ta wuce Sangarenta tana danne abinda yake ranta. Wato irin rawar ?afa da zirgillin da yakeyi akan auran nasa ko budurwa ze Wakko fil a leda se haka, Hajiya Rabi tacewa Momy tayiwa hajiya uzuri domin yanda Alhaji yakeyi badan tana kai zuciya nesa ba da itama kishi seya zautar da ita.
"Ita ta zauna da ita ta santa dole hankalinta ya tashi Momy, ni wlh tsoro nakeji kar ta dawo ta ?arasa wargaza mana Wan zaman lafiyar da mukeyi dan duk abinda ya gigita Hajiya ai an san ba ?aramin al'amari bane".
Ita dai Momy murmushi kawai tayi tace mata
"Karki wani damu babu komai da yardar Allah ai kinji abinda Hajiya Balaraba ta faWa in sha Allahu lafiya lau zamu zauna Hajiya kuma wannan tsakaninsu ne ai dole ta firgice domin bata san da kalar ramuwar gayyar da zata zo mata ba mu namu ido ne ai in dai baka shiga sabgar mutum ba ai baze shiga taka ba".

Hajiya na Waki bata san wainar da ake toyawa ba se ?arfe tara Alhajin yasa aka kirata ya bata kuWi kamar na sauran sannan ya gaya mata yau zasu wuce Umarah da Zubaidah. Bata iya Soye kishi da hassadarta ba ta saka masa kuka tana cewa ai gashi nan tun bata dawo ha ya fara gwada rashin adalci shidai ya tsallake ya fice ranta ya sake Saci ganin Rabi da Aisha sun shigo kowacce ta sha kwalliya ta alfarma su suka rakashi har mota da yar jakarta ita aka barta a falo tana sharSar kuka data koma Waki shine ta shiga kiran Jafar tunda Alhaji ze bar ?asar kafin ya dawo zatayi executing plan Win ta tayi ta kira bata same shi ba seta kom kiran Fatiyyah taji ita idan akwai alamun nasara cikin maganar da sukayi jiya.

Ta kasa zaune ta kasa tsaye, abu goma da ashirin ga ba?in kishin Zubaida da yake cin zuciyarta. Bayan Bara'atu macen data tabbatar Audu na so kamar rai Zubaida ita ce ta biyu data tsana saboda tana da duk wata sufa da kissa irin waccen Audun yake so a gurin mace. Bata manta karon su ba ko a wancan zamanin sa'a da take da ita ce tasa har tayi galaba akan Zubaidan bata fayanyta sake samun damar da zataji daWin Audu tana ba?in cikin ta sake dawowa cikin gidansu dukda tasan ba haihuwa zata zo tayi ba amma dukda haka tana ba?in cikin tumunin takabar da zata zo a kasa da ita. Da so samu ne duk su watse, yaya dai sun haifa ba yanda ta iya zasuci gadon ubansu amma tumunin takaba tana harin ita kaWai zata ci ba kuma ta cire rai da hakan ba.

KADUNA
Babu yanda ta iya ta sake shiga motarsa a karo na biyu saboda yanda Badar da Nurain suka haWa kai kamar zasu cinyeta da magiya. Tayi kicin kicin da fuska bayan ta zauna a cikin motar kawai Badar ta wani fara Waukansu hoto wai sunyi kyau musamman da aka samu arashi atamfar atamfar data saka dark blue ne yafen light blue a jiki tayi matching da yar ubansun shadda light blue daya saka ya kafa hula kamar Angon gaske ga askin da yayi yasa yayi kyau ita da kanta duk yanda takeji se????####### #
# # #
################### #!#"###$#%#&#'#(#)#*#+#,#-#.#/#0#1#2#3#4#5#6#7#8#9#:#;#<#=#>#?#@#A#B#C#D#E#F#G#H#I#J#K#L#M#N#O#P#Q#R#S#T#U#V#W#X#Y#Z#[#\#]#^#_#`#a#b#c#d#e#f#g#h#i#j#k#l#m#n#o#p#q#r#s#t#u#v#w#x#y#z#{#|#}#~##?#da ta yaba shi a ranta. Tafiya sukeyi shiru babu me cewa wani ?ala baka jin komai a motar se ?arar ace, yanda turarukansu suka haWe suka samar da wani yanayi me saukar da nutsuwa cikin zuciyar wanda ya sha?i sabon ?amshin da suka samar hakan ya bawa zuciyoyinsu damar yin nutsu cikin kogin tunani mabanbanta.

A hankali ta saci kallonsa ganin ya kunna Bluetooth Win motar yana danna wayarsa da alama shirun ya ishe shi yana so ya kunna wa?a, ta mayar da kai gefe tana matse baki, jira takeyi ya kunna abinda be gamsheta ba ta samu damar cancareshi a hankali wa?ar da ta zame mata tamkar wani abun Webe kewa ta fara tashi cikin speaker Win motar, volume Win beyi ?ara da yawa ba amma se ta ringajin ?iWan har tsakiyar kanta, tsikar jikinta suka ringa zuba tun ba da ya fara bin wa?ar daidai inda mawa?i Salim smart cikin wa?ar labarina yake cewa
"Tsaya kiji labari na, ko zaki gane nufina. Sonki ya shiga raina ya wuce matakin ?auna ban da kowa bani da komai, in ba ki lallai zan rasa komai ki mun alfarmar so zana baki labari na". Bata san lokacin data Waga kai ta kalleshi ba, idanunsu suka sar?e cikin na juna. A tsaye suke cikin hold off hakan ya basu damar ri?e junansu ta hanyar kallo har seda motocin da suke bayansa suka fara fafara masa horn kafin ya ankare an samu hanya, waskewa yayi yaci gaba da tu?i itama ta mayar da kai jikin window wani abu ya tsaya mata a rai.

Mamaki ta ringayi daya sake kamo wa?ar Zuciya ta Umar M sharif, tun daga farkonta har ?arshe haka ya rera mata baitukan yana wani Waga murya dan ya isar mata sa?on da kyau. Ya gama ya koma karki manta dani, ya ringa maimaita baitin "kece ta fari, ta farin fari ta fari" ya maimaita gurin yafi sau goma har seda ta kai hannu tayi forwarding wa?ar. Abinda ta kura selection ne na wa?o?in nanaye na hausa ya haWa dan ya fitine ta dasu. Ta tuna zamanin yammatanci ta taSa cewa ya mata wa?a yace ta bishi bashi ?ila biyan bashin ne ya tashi yau. Suna shiga Jaji annashuwar da zuciyarta ta samu ta koma fushi dalilin kiransa da Fatiyyah tayi, dukda suna gab da juna bata wani fahimci abinda sukayi magana akwai ba wannan ne kuma ya Sata mata rai ta haWe fuska se bayan ya gama wayar ma sannan ya lura da canjin fuskar tata, kansa ya fasu domin ko bata faWa ba yasan kishi ne abinda tayi.

Saboda neman magana ya lalubi hannunta ya ri?e ta fuzge bayan ta balla masa harara data saka shi fashewa da dariya babu shiri yayi me isarsa kafin ya kunna wa?a ya cigaba da sharholiyarsa. Da suka shiga Kano seda ya biya mata abinci kafin ya kaita gida be shiga ba ganin mata nat shige da fice kamar ana wata hidima a gidan tana sauka ya juya ya tafi saboda kiran da Hajiya take ta ?wala masa a waya.
*MATAR MUTUM*
*NA MARYAM FAROUK (UMMU MAHEER*

*FIKRA WRITERS ASSOCIATION*

*LITTAFIN KUDI NE*
*PAY 500 A ASUSUN*
*7061838488*
*OPAY DIGITAL SERVICES*
*MARYAM FAROUK*
OR
*0709290797*
*ACCESS BANK*
*SE A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488*
*IDAN KATINE A DAUKI HOTONSA A TURA ZUWA LAMBAR SAMA VTU KUMA A TURA A 08142548705*

*Kuyi following dina a Arewabooks @Maryamfarouk01 inda zaku karanta wannan littafin tareda sauran littattafaina*
*NAGODE*

*BOOK 3*
*PAGE 41*

*Assalamu alaikum*
*Yar uwa kina da labarin UMMU_MAHEER COLLECTION kuwa?*
*Kasuwar online inda zakiyi siyayyar kayan ado da kwalliya kama daga kan suturun sakawa, mayafai, hijabai, kayan shafe shafe dana tsafta na kamfanin Oriflame, kayan yara na sakawa dana kwalli duk muna dasu masu kyau da sau?in farashi daidai da aljihunku*

*Muna da kayan back to school wato dangin su Lunch box, school bag, lunch pack da sauransu*

*Sannan akwai kayan kwalliyar Waki, muna yin gadaje, kujeru da duk wani abu daya danganci gida se wanda kika zaba kuma wanda kudinki ya baki*

*Kayanmu garantee ne, idan kinyi kasuwanci damu zaki dawo har ki kawo wasu da yardar Allah. Muna kano muna kuma tura kaya ko ina a faWin cikin ?asar nan da wajenta*
*Kai tsaye kiyi joining WhatsApp group dinmu ta kan wannan link Win*
https://chat.whatsapp.com/FKsWield4wPKepHDZwtPUP
*Ko kuma ayi mun magana akan number 07061838488*
*Nagode*

GIDAN ALHAJI AUDU
Ana kiran sallar la'asar Fatiyyah ta shiga gidan ta tarar da hajiya na safa da marwa daga farko zuwa ?arshen falonta kallo Waya zaka mata ka tabbatar da hankalinta a matu?ar tashe yake yanda kasan wadda ta aro jinjiri aka sace. Fatiyyan ta shiga Wakin fuskarta ji?e da hawayen da ta Waura aure dasu. A fusace Hajiya ta kalleta tace
"Se yanzu kikaga damar zuwa kenan?" Itama cikin makamancin lafazin hajiyar ta mayar mata da cewa
"To yanzun kika san ta yaya na fito? Ina a gabanki yayi mun iyaka da taka ko ?ofar gida ai baki ce masa komai ba". Hajiya tayi mata kallon zamu gauraya kafin tace
"Ba wannan ba, yanzu ina maganar mu ta kwana? Kin samu kinyi yanda nace miki?" Hawaye ya sake tsinkewa Fatiyya tace
"Ko Wazu kafin ya tafi seda ya sake maimaita mun idan har naga be aureta ba to tabbas mutuwa yayi, kuma ma wlh an gaya mun ?arya yakeyi ba Abuja ya tafi ba yana Kaduna yaje Wakko ta dama ai ya kaita gidan ?awarta ranar juma'a" ta ?arasa da kuka me haWe da shashshe?a.

Hajiya Binta ta zuba mata ido tana mata kallon tsantsar ba?in ciki da takaici kafin tayi ?wafa tace
"Ai nidai a duniya ban taSa ganin sakaryar mace da bata san kanta ba irinki Fatiyyah, Jafar dai beyi sa'ar mace ba, aba kamar Namiji babu kissa babu kisisina ballantana kisan lagon namiji kisakashi yayi abu ko beyi niyya ba? Tir da halinki Fatiyyah wlh kin Wuma asara".

Kallon ?asa ?asa Fatiyyan ta mata na raini, so take tace mata ai basu hassana da hussaina suke tare suka tafka asarar. Ita da ta iya kissar me ya hana bata hana faruwar abun ba, amma ta Winke bakinta domin tafi kowa sanin me hakan ze haifar. Hajiya ta zauna tana zabga tsaki tace
"To bari kiji, billahillazi muddin kika bari akayi auran nan ki tabbata a bakin naki igiyoyin auran domin baki da amfani, se ki zaSa, auranki ko ko kisan duk ma yanda zakiyi ki lalata nata zaSi ya rage naki kuma".
Tsoro, firgici da mamaki suka dirarwa Fatiyyah. Toronta furucin hajiyar na idan har ta bari Jafar ya auri Fatima a bakin auranta, tasani muddin tayi niyya babu wanda ya isa ya hanata aiwatar Jafar kuma bazeyi in kari ba domin akan tsini yake da ita, neman hanyar hukuntata akan laifukanta yakeyi kuma shi da kansa ya gindaya mata sharaWin sakin idan bata bi umarninsa ba tasan baze ?i tayin hajiya ba, sakinta zeyi without second thought tunda ya faWa mata akan Fateemah ya shirya rabuwa da kowa muddin ba mahaifansa bane. Duk yanda ta shiga Wimuwa data tuna wani abu se kalaman hajiyar suka juye mata zuwa mamaki ko ma tace dariya dan haka ta saka hannu biyu tana share hawayen fuskarta cike da izgili tace

"To amma hajiya da alama kin manta, jiya ai naji kina cewa kema akwai sharaWin sakin akanki. Idan har naji da kyau cewa kikayi Alhaji yace idan kikayi amfani da ?arfin ikonki kika hana auran a bakin naki igiyoyin, ina matsayin waccen maganar kenan idan kika angizani nayi abinda ya janyo aka fasa auran yaya kenan?".
"Tsam Hajiya Binta tayi tana kallonta kamar me nazarin wani abu,bata san a gidan uban da Fatiyyah taji maganar nan ba domin jiya ai kafin ta ?arasa faWa Jafar ya dakatar da ita banda munafuka ce ita ta yaya ta sani ko shi Jafar Win ne da suka koma gida ya gaya mata? Kawai se ta fashe da kuka kamar yar yarinya tana cewa
"Wannan masifa har ina wannan bala'i dame yayi kama? Wlh bazan yarda ba, babu yanda za'ayi a gurbata mun zuri'a da jinin talaka jinin mayu ba. Haka kawai muna zaman zamanmu Aisha ta haifo mana jaraba yaje ya kwaso mana annoba ta kashe shi zata biyo mu muma ta kashe mu, ban shirya zawarci da shekaru sittin da biyar ba amma wlh bazan zuba ido a Waura auran nan ba. Idan har ni na haifi Jafar dole dole koma ta halin yaya ya fasa auran nan" ta Wora hannaye biyu aka tana cewa "Innalillhi wa'inna ilaihi raji'un wannan yarinta ta zame mun masifa Ahmad ka cuceni ka shigo mana da Anno ba Ahali".

Ita dai Fatiyyah kallonta kawai takeyi kamar ta samu tv zuciyarta a jagule. Nata taSa zaton abin ze kai haka ba, tunda kuma har hajiya ta gagara maganin matsalar ta sare ta sani aure babu fashi sedai ko zata yi me ba zata taSa bari Fatima ta samu nutsuwa ko zaman lafiya da mijinta ba, da tsiya da bala'i seta gasa mata aya a hannu ta yanda da kanta zata zaSi rabuwa dashi bata damu ba koda zasu rasa su duka ta yarda. Babu yanda za'ayi ta rayu da Ahmad cikin mutuntawa da soyayya sannan ace ta sake samun wata rayuwar tareda Jafar bayan ita ce silar da ita bata mori nata auren ba"
Sallamar da akayi ta saka Hajiyar dake kuka da Fatiyyan suka kalli ?ofa a tare, hajiya ta zabura tayi baya kukan ta ya tsaya tana kallonsa tace
"Innahu min sulaimanu, Satan hanya kayi kome da zaka shigo mun Waki?"
Hussani Bechi ya tattara babbar rigar farar shaddar dake jikinsa ya zauna kan kujera bayan daya nunawa abokanansa biyu da suka shiga falon tare guri suma suka zauna suna danne dariyar sata kamasu saboda yanda hajiyar tayi tamkar wadda tayi gamo da aljanu. Seda ya sake karkata hularsa da yayiwa sawar ?wan?wararrun yan duniya tayi gefe can kamar zata faWi ?asa, cike da sha?iyanci yace

"Hajjaju ina wuni? Ya taro kuma? To Allah ya sanya alkhairi ya haWa kawunan ku" ya nunawa abokanansa hajiyar yana cewa
"Ita ce matar Alhajin mu ta biyu, asalin uwar gidan ta mutu yanzu da a ta?aice ita ce uwargida ku gaishe ta" suka haWa baki gurin gaida hajiya da kallonsu kawai take bata amsa gaisuwar da yayi mata bama balle tasu. Har ga Allah ta tsorata da ganin Hussanin a Wakin ta, abinda ya fara zuwar mata yazo mata tijara ne kan zuwan da tayi ta zagi uwarsa tunda ba mutunchi ne dashi ba. ?aya daga cikin abokanan ne yace
"Itace maman Jay kenan? Naga suna kama" Hussani yace
"Ita ce, Jafar ango, ai ga tasa uwar gidan nan ma wannan ce matarsa" ya nuna Fatiyyah da tayi tsilli tsilli tana kallonsu bakinta na rawa ta gaishe su se Hussanin yace
"Allah yasa ba huWubar tsiya kika zo take miki ba? In baki shawara yarinya karki yarda wannan matar ta kaiki ta baro ki. Yanda ta ringa haWa gurmi da husuma a gidan nan tana jin daWi gashi Allah be kasheta ba a sannu komai yana warwarewa to wlh kika biye mata se kin fita shiga uku dan Jafar ba Alhaji bane ubanki ze ci kuma muma nan ba irin Al?ali bane balle mu zuba miki ido kina ?wallo da Wan uwanmu dukan tsiya zan miki kika kawo mana hauka a gida yarinya tunda matar ?anina ce ke tsaf zan hukuntaki a matsayin ?anwata ko ita da kika ga taci banza dan ba'a haifi irina a gidansu Alhajin bane da ze ringa saita mata hanya to ki shiga hankalinki ku zauna lafiya da abokiyar zamanki dan ita dai har Ahmad ya mutu be taSa kaiwa wani ?arar ta ba".

Jikin Fatiyyah har rawa yake da jin wannan ?an?ararriyar tijara, tana jinsa yaci gaba da cewa
"Kema dai ba'a taSa kawo ?arar ki ba amma tunda na ganki gaban hajiya nasan huWubar tsiya take miki to ki watsar mata da abarta anan ki tafi ki rungumi ?addara kinga dai ke ba haihuwa kikeyi ba, kiyi ha?uri kawai idan tazo ta haihu kema kya samu Wa, kuyi zamanku lafiya amma muddin kika biye mata kina ruwa wlh".

Hajiya tayi ?arfin halin hararasa tace
"Bana son rashin albarka Usaini, saboda kai baka gaji arzi?i ba ka shigo har Waki na ka ringa zagina? To tashi ka fita tun baka hasalani na maka rashin mutunchi ba". Dariyar rashin mutunchi yayi yana dirza ?afar sa da be cire takalmi ba akan carpet yace
"Ai ko da kikaga bana shigowa gidan nan saboda babu uwata ne a ciki ba zanzo na ringa raSe raSe na rasa inda zan zauna ba yanzun kuwa har kan gadonki idan naga dama zan hau in zauna babu kuma yanda kika iya dani Wan gida ne ni me cikakken yanci yanzu kuma Wan amarya kinga da ta?ama ta zan ringa shigowa cikin gidan nan nayi abinda naga dama" ya mi?e tsaye yana gyara hularsa yace
"Dama kawo su nayi su miki ala sanyan alkhairi ku tashi muje"

"Ala sanya alkhairin uwarka? Ni nayi aure da zaka kwaso mun yan hau irinka ka shigo mun dasu falo suna kallon mutane kamar wasu namun daji" ta faWa a hasale itama tana mi?ewa tsaye, ya Wage kafaWa irin ko a jikinsa kafin yace
"Bana uwar tawa ba wannan can muka fara zuwa suka mata na ?anina da aka Waurawa aure ni kuma naga ya dace na kawo su gurinki tunda kece uwarsa tunda ban miki abin arzi?i ba shikenan" ya kaWa rigarsa abokansa suka take masa baya suka bar Hajiya da Fatiyyah tsakanin su biyun baka tantance wadda tafi wata shiga Wimuwa.
"Kinji abinda ya faWa ko kunne nane?" Hajiya ta faWa tana kallon Fatiyyah da kamar tana jiran tayi mata magana ta zube a inda take ta fashe da kuka tana cewa
"Aure yace an Waurawa Jafar, dama Saluhu ya gaya mun na ?aryata shi ashe da gaske" ta fashe da kuka kamar zata shiWe. Hajiya ta zauna daSas tana kallonta in disbelief tace
"Wa aka Waurawa auren? Wane Saluhun ne ya gaya miki?"

Fatiyyah na kuka tace
"Wannan me kantin na kan layin su Fatiman, shi na bawa kuWi yake gayamun duk wani motsinta Wazu da safe ya kirani yace mun yaji ana sanar da Waurin aure ?arfe goma da rabi kawai nace masa toh dan ban kawo dagaske yakeyi ba ashe kuwa hakane".
Hajiya ta ringa sauke ajiyar zuciya kamar wadda ta farka daga dogon suma tayi shiru takasa cewa komai, ga kishiya ga surukar data ?i jini a duniyar ta tabbas Audu ya shammaceta". Fatiyyah na kuka ta dau?i jakarta ta fice daga falon ganin hajiya ta zubawa guri Waya ido bata cewa komai, waje ta haWu dasu Khadija, duk a ba zata labarin auran Jafar ya isar musu basu kuma yi ?asa a guiwa ba suka rankayo suka taho ko kulasu batayi ba ta shige motarta Maimuna na mata magana Sarah ta taSe baki tace
"Kema kinso Sata bakinki ne tana wannan kukan ta yaya zata kulaki?" Suka wuce ciki abinsu.

Suna shiga falon hajiya ta mi?e ta shige uwar Wakin ta tana tafiya kamar zata kifa, seda ta zauna a

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login