Showing 90001 words to 93000 words out of 467220 words

Chapter 31 - MATAR MUTUM COMPLETED 1-3 BY MARYAM FARUK.doc

23 Sep 2025

12114

wasar zata kaya.

Audu bece komai ba ya wuce samansa, jiki a sanyaye Zubaida ta miqe ta shiga tattara abubuwanta Binta natsaye tana zubda mata habaici,
"Ke kin dauka zaki kawo mana shege wato kici bulus bamu gane ba? To qaryarki tasha qarya wlh tun wuri ma ki nemo farkan daya dibga miki ciki ki nana masa abinsa badai a gidan nanba kar muke kallonki"

"Wlh Binta ki tsoraci gamuwarki da Allah" Zubaidan ta fada hawaye na sakko mata, Binta tayi shewa tace
"Nan da sati i yanzu ina gaban Ka'aba yarinya in shafata in roqi Allah yayi gaggawar tona miki asiri ki tattara ya naki ki barmin gida gayyar tsiya gayyar na'ayya"

"Allah baya bacci" Zubaidan ta sake fada daga haka ta shige dakinta. Tana zaune Audu ya shiga ya zauna akan Kujera yana fuskantar ta, irin zaman da yayi yass gabanta ya shiga faduwa, cikin kaushin murya yace
"Zan sake tambayarki bana buqatar qarya ko wani alaye ki fada mun gaskiyar magana Cikin da kikace kin zubar dagaske kike ko kuwa kwantar dashi kikayi?"

Kuka ta fashe dashi ba tareda ta sgirya ba tace
"Yanzu ka dauki maganar da take fada dagaske kenan? A ina ka taba ganin an kwantar da ciki? Idan ma anayi tayaya ciki ze kwanta tsayin sama da shekara daya a Jikina ace baka lura ba wai me yasa akai baka amfani da kwakwalwarka se abinda matarka ta kitsa maka ba tareda bincike ba ka hau kai kawai ka zauna?"

"Nine bana amfani da kwakwalwata?" Ya fada yana nuna kansa, a duk maganganun babu abinda ya tsinta se wannan, ta miqe cikin kuka tace
"Kwarai, kwakwalwarka hotoce Audu domin bata aiki se abinda wani ya kitsa maka dashi kake tunani. Ya za'ayi ka kasa tantance gaskiya da qarya? Se yaushe idonka ze bude ka gane tuggu da makircin da matarka take shirayawa a cikin gidan nan? Ta laqawa uwargidanka sharrin Kisa shine zata shegantaka maka Da ko Ya ka hau kai ka zauna?
To wlh na gaji bazan iya wannan rayuwar ba, ba zan zauna da mutumin da besan daidai ko abinda ya kamata yayi a matsayinsa na Namiji ba, bazan cigaba da zama ace Kishiya ita zata tsara mun irin zaman quncin da zanyi a cikin gidan aurena ba.

Ka fito fili ka fadi abinda yake ranka ka fadi cewar kana kokwanton cikin jikina karka sake sakayawa ko ka titsiyeni da tambayar abinda ya shafi rayuwata ta baya, ka fadi kai tsaye Matarka ta kitsa maka cewar cikin jikina ba naka bane kuma ka hau ka zauna babu abinda zance maka kuma banida amsar da zan baka a yanzu se dai nace maka mu jira lokaci, ubangijin daya wanzar da samuqar cikin ze qarware duk wani qulli da ake qoqarin laqaba masa amma kafin nan ka sani bazan iya cigaba da zama da kai ha Audu gidanmu zan tafi zanje na qarasa rainon cikina a can har Allah ya saukeni lafiya abinda na haifa ya raba gardamar zargin da kake neman laqabamun" tana gama fadar haka ta shige daki tana Kuka ta hau hada kaya.

Laqwas yayi akan Kujera kamar kazar dataji ruwan zafi, ya yunqura ze miqe kenan Burum Binta ta fado dakin tana cewa
"Babu shakka daman ance tabarmar kunya da hauka ake nadeta kana zaune tayi maka wasan kwaikwayo da salonso na Tsofaffin kikali ko? To ai idan kina da gaskiya fitowa zakiyi ki kare kanki baqai ki hau koke koke kina hada kaya ba kaga magana ta tabba da ciki aka shomigo mana so take ta tafi se ta koma inda za'a rufe maka baki ruf ka kasa cewa komai koda yake yanzun ma naga kamar bakin naka a rufe yake ai"

"Banida lokacinki ki kuma jirayi sakamakonki komai nisan tsahon zamani" Zubaida data fito da jaka ta fada tana gotata. Tana fita Audu da Bintan suka rufa mata baya Binta na shewa kamar sabon shigan hauka tana tafa hannu.

"Subhanallahi me yake faruwa haka" suka tsinkayi muryar Yakubu da shigarsa gidan kenan yana fada, Zubaidan taci burki kuka yana sake kwace mata Binta ta gyara tsayuwa murya a sama tace
"Me fa ya faru Yaya Yakubu? Abin kunya tayi asirinta ya tonu kuma shine take mana qaramin hauka".

Zuciyar Yakubu ta tsinke ya tafi wani tunani na daban seya kalli Audu dake nan tsaye qato dashi kamar wanda kwakwalwarsa ta bata se zare ido yake yace
"Me ya faru? Ban fahimci abinda take cewa ba?"

"In maka gwari gwari Yaya Yakubu, ciki. Shege tayo take neman laqawa qaninka ta gurbata muku Zuri'a" Binta ta sakeyin caraf ta amshe tamkar sunanta ya koma Audu.
"Hasbunallahu wani'imal wakeel, Audu dagaske ne abinda take fada?" Yakubu ya fada yana ja da baya dan ya samu balance sosai jin wannan babbar magana.

https://chat.whatsapp.com/I8xKHGurk7EBf5ZqQdxHKG

*MATAR MUTUM*
*NA MARYAM FAROUK (UMMU MAHEER*

*FIKRA WRITERS ASSOCIATION*

*LITTAFIN KUDI NE*
*PAY 500 A ASUSUN*
*7061838488*
*OPAY DIGITAL SERVICES*
*MARYAM FAROUK*
OR
*0709290797*
*ACCESS BANK*
*SE A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488*
*IDAN KATINE A DAUKI HOTONSA A TURA ZUWA LAMBAR SAMA VTU KUMA A TURA A 08142548705*

*Kuyi following dina a Arewabooks @Maryamfarouk01 inda zaku karanta wannan littafin tareda sauran littattafaina*
*NAGODE*

*PAGE 22*

Wuta ta daukewa Yakubu sanda Binta ta gama rattaba masa abinda ya faru dan ita ta zama bakin Audu yau. Ya ringa kallon Audun yana jira yaji ya qaryata ko ya fadi akasin abinda Bintan ta fada amma yaga yadauke kai gefe yana wani cin magani se ya maida kallonsa kan Zubaida dake irin kukan nan da meyinsa ya gaji dayi, tausayinta ya rufeshi gefe daya takaici da tsanat Bi ta me girma tareda qyamatar Hali irin na dan dan uwansa suka kamashi.

"Ku Fita ki bamu guri" ya fadawa Binta da Zubaida.
Zubaida ta miqe ya kalleta yace
"Kar kije ko ina ki koma dakinki" ta juya ta fita Binta ko ta gyara zama, cikin kaushin murya yace mata
"Zaki fita ko sena kwasa miki mari a nan gurin?"
shidin ba ma'abocin zafi bane amma bashida wasa musamman a gurinta sam basa ga maciji yanda kuma ya hade gida ya tabbatar mata ze iya kwasa mata mari idan bata tashi ba kamar yanda ya bara umarni dan haka ta miqe tana qunquni.

"Nayi maka uzuri domin bayan Kaidin Mace Jahilci da duhun kai suna dawainiya dakai Audu lokaci yayi daya kamata ace ka koma Makaranta Both Islamiyya da Boko" Yakubun ya fada bayan fitar Binta wadda ta labe a bakin qofa ta kasa kunne tana jiran taji me zasu tattauna. A zabure Audu ya kalle shi yace
"Ni kake kira jahili?"
"Qasurgumi ma kuwa" Yakubun ya bashi amsa idonsa fes a kansa kafin yaci gaba da cewa

"Banda kai wawane wanda bashida tunanin kansa se abinda aka kitsa masa kuma Jahilci yana dawainiya da kai ta yaya Mace zata zo maka da irin wannan maganar shirme wadda ko yaro qarami aka gayawa dariya zeyi amma ka hau kai ka zauna harka sheganta cikinka da kanka wane kalar wawanci ne yake damunka Audu? Binta ce ta auro maka Zubaida da zatayi maka lissafin cikinta ka yarda ko kuwa? Watanta nawa yau a gidanka? A lissafin watan sama auranku ya shiga wata na goma ma kaga kenan cikinta har yazarce watannin da Da yakeyi kafin a haife shi kuma da zata ce maka Da ciki ta shigo kwantar dashi tayi kai mahaukacine da ka kwashe tsayin lokaci tare da Mace da ciki amma baka gane ba ko kuwa akanta ka fara Aure balle kace baka san yanda alamar ciki take ba?

Wato ita da yan uwanta sun laqabawa Bara'atu sharrin kisan kai sunci banza shine yanzu ta sake fitowa da wannan sigar kai kuma ga Raqumi se yanda aka juya akalarka ta fada ka hau ka zauna akai..."

"To ai ba qarya Binta ta fada ba hakan zata yiwu tunda ita Zubaidan da bakinta ta gaya mun tayi ciki tun kafin na dawo da ita gidansu kuma ni ban tabbatar da tace ta zubar dagaske ne ko qarya takeyi ba. Sannan ba Binta kadai ba har Bilki seda na tambaya ta tabbatar mun ana iya kwantar da ciki yafi shekara sannan a tayar dashi idan ba haka ba tayaya za'ayi ace ciki yayi wannan girman a wata daya" Audun ya fada a fusace zuciyarsa na tafarfasa na yanda Yakubun ya zageshi ya kirashi Jahili. A fusace shima Yakubun yace

"Ta yanda Allah ya rangwanta maka hankali da tunani kake kasa banbance tsakanin daidai da rashi Sa ta haka yayi ikonsa ya girmar da ciki a wata daya, Kai wane irin mutum ne Audu? Anya kwakwalwarka a daidai aka dasa maka ita kuwa?"

"Karka sake zagina kuma karka sake dangantani da hauka" Ya fada yana miqewa tsaye,

"Idan na kuma zaginka zaka rama ne? Na fada kai wawane shashasha wanda bashida tunanin kansa se abinda waccen yar iskar Yarinyar da idan tayi wasa ba zataga annabi ba ta shirya maka. Ka auro shaidaniyar Mace tana neman ta Halakar da kai, to bari kaji ka farka tun kana da sauran lokaci idan ba haka ba kana ji kana gani zaka tafi lahira yanda haqqi ze kaita wuta haka zata kama hannunka ku shiga tare...."

"Na shiga uku ni kake kake cewa yar wuta Yaya Yakubu?" Binta ta fado musu hannu aka tana kwakwazo, cikin daga murya Yakubun yace
"Ke munafuka ce, munafuki kuma Allah da manzonsa sun rigada sun fada mana makomarsa idan har ya mutu be tuba ba. Cikin Halayan manyan munafukai wannene bakiyi?
Qarya, Ha'inci, Zalunci, Annamimanci sannan ga tulin haqqin mutane da kika dauka dana Aure da kika lalata kina tsammatar idan baki nemi yafiyar wadanda kika zalunta ba zaki wanye lafiya da duniya ne?

To dakai da ita kar ku fasa duk abinda kukeyi duniya ce gaku gata nan kuma kanku kuke rusawa, Zubaida kuma babu infa zataje a gidan nan zata haife abinda yake cikinta tunda kai baka san shari'a ba bari na gaya maka koda ciki ta shigo gidanka muddin ta yi watanni shida kafin ta haihu Shari'a ta baka Dan koda kana kokwanton ba naka bane balle kuma wane tabbaci zamu samu idan ma da cikin Tazo ace ba naka bane tunda a yawon tambadanci daman kuka hadu? Baka ga komai bama tukunna Abdulwahab kabi duniya a sannu idan ba haka ba ranar kuka na tafe" yana gama fadar haka ya fice daga falon.

Seda Binta ta tabbatar da ya sauka qasa kafin ta kalli Audu tace
"Lallai wannan shi ake kira ga Mari ga tsinka jaka, yanzu shi Yaya Yakubu saboda qin Allah shine ze ringa fadar maganganun nan saboda ba shi ake shirin liqawa shege ba? Ni anya kuwa cikinku daya da Yaya Yakubu nan?"

"Karki kuskura ki zagarmun Dan uwa babu ruwanki duk abinda ya fada a kaina dan ya isa ne" Audun ya dakatar da ita cikin kaushi idanunsa sun kada sunyi jajir saboda bacin rai, ta sunkuyar da kai irin na shahararrun Makirai tace
"Allah ya baka haquri ai ba wani abu nale nufi ba kawai dai gani nayi kamata yayi ace ya tayaka qyamatar wannan abin ba wai ya goyi bayan a cuceka ba amma kayi haquri idan ba bata maka rai" sum sum ta fice daga dakin itama zuciya fari qal dan tasan ko iya tijarar da Yakubu yayi masa dalilin Zubaida ta isa ta qara tunzurashi tunda shi mutum ne me Izza da tsananin son girma.

Bayan fitar Yakubu daga Bangaren Audu dakin Zubaida ya nufa, tana zaune bakin qofa tayi tagumi bata ko bude ba balle ta shiga cikin ta zauna kamar yanda ya ce mata ganinsa yasa ta miqe tsaye a yanayi na bacin ran da yake ciki ya ce mata
"Bude qofar ina son magana dake"
Ta bude suka shiga ya zauna akan kujera ita kuma ta zauna a qasa sukayi shiru na dan wani lokacin kafin ya nisa yace

"Ina so ki gaya mun tsakaninki da Allah shin da akwai wani abu da kika aikata da har ya sakawa Audu kokonton cikin jikinki a ransa"

Tayi raurau tana shirin fashewa da kuka, abin ya hade mata biyu ga damuwa ga yanayi na ciki Yakubun yayi saurin cewa
"Ki bar koke koken nan haka kodan lafiyar abinda yake cikin ki kiyi mun magana kawai"

"Allah shine shaidata babu abinda nayi wanda har ze cefa kokontona a zuciyar Audu. Haduwata da shi zuwa maidoni gida da yayi gaba daya ya faru a dan taqin lokaci shi shaidane akan cewar tunda na dawo gidan mu nayi tuba na gaske babu inda nake zuwa babu wanda yake zuwana wata magana bata qara hadani da Namiji ba idan ka cire mahaifina she shi Audun ballantana har wani mugun Al'amari ya faru har aka daura mana aure na tare a gidansa, kuma a cikin gidan nan ma nayi Al'ada balle yace da ciki na shigo kuma har sanda cikin ya bayyana duk be nuna wata damuwa akai ba seda Matarsa ta dawo daga gidansu sannan abubuwan suka canza"

"Ita ta kitsa maganar kenan, Binta! Binta! Wannan yarinya anyi shaidaniya amma babu komai karki saka damuwar komai a ranki ki kyalesu daga shi har itan kici gaba da kula da kanki da abinda yake cikinki. Idan kinji gidan ya miki qunci ki taho gidanmu tare mukazo da Balaraba kuma zata jima a nan dan zan tafi na barsu se na dawo sallah sannan zamu koma baki daya sannan dan Allah maganar nan ta tsaya ikar cikin gidan nan karki gayawa kowa in sha Allahu komai ze warware kansa kinji" Yakubu ya fada mata cikin lallashi. Ta share kwalla tace

"Shikenan zan zauna kamar yanda kace zan kuma cigaba da roqon Allah daya zabamun mafi Alkhairi, tabbas nayi dana sanin Auran Audu saboda bansan haka yake ba. Ban taba tsammanin bayan tsamoni da yayi daga rayuwata ta baya ba kuma zeyi amfani da hakan ya rusamun rayuwar dana ke qoqarin ginawa a gaba. Yanzu idan yaqi karbar dan da zan haifa ya zanyi? Da wane ido duniya zata kalleni?"

"Karki sake fadar haka babu abinda ze faru da kuma halastacce da ne da kansa ze amshe shi ba tare da wani ya tilasta masa ba, kedai Allah ya sauke ki lafiya kawai kinji kiyi haquri kuma kici gaba da Addu'a" daga haka yayi mata sallama ya tafi ta maida jakarta daki amma bata bude ta ba domin har zuciyarta bata aminta zata iya cigaba da zama da Audu ba. Bata shiryi qare rayuwarta cikin qunci da baqin cikin Miji da kishiya ba. Ta sani daman dole zata riski qalubale masu tarin yawa a rayuwarta amma bata tsammaci ta haka zasu bullo mata ba.

Shiru shiru ta tsammaci Audun ze shiga ya mata masifa amma har wayewar gari bataji duriyarsa ba haka suka kwana biyu ko qofar dakinta be leqa ba se a kwana na uku da dare tana zaune ya shiga ya tsaya daga bakin qofa ya miqa mata takadda fara a linkife fuska babu Annuri ta karba ta bude bata iya karatun boko ba dan haka ta mayar ta rufe ta ajiye a gefenta ba tareda ta tankashi ba.

"Baki ce komai ba, ko bakiga abinda yake rubuce a ciki bane" ya fada cikin murya me kauri, ta daga kai ta kalleshi irin kallon nan na daidai nake da lokacinka kafin tace
"Ka rubuto mun da Ajami idan kana so na gane abinda yake ciki har na baka amsa". Yaja tsaki ya koma inda ya fito. Tun randa Yakubun yazo yake auna daya da biyu akan yuwuwar ya amince da cikin jikinta amma ya kasa, Shaidan ya rigada ya yi kane kane a zuciyarsa yana raya masa abubuwa kala kala ga qaramar shaidaniyar dake nan gefensa tana qara ingizashi, duk yanda yaso daya daure yayi mata uzuri ya kasa musamman idan ya tuna dalilinta Yakubu ya yaba masa baqaqen maganganu ya kirashi jahili se yaji babu abinda zeyi ya huce irin ya saketa kawai hakan ko yayi ya rubuta mata saki har biyu a takarda ya linke ko Binta bata san da ya rubuta sakin ba se da kuma ya bata sannan yaji cewar yayi wauta data bude yaga babu damuwa ko kidima a fuskarta. Tuna masa da tayi bata iya karatu ba ya sanyaya masa zuciya kenan bata san me takaddar ta qunsaa ba da wannan sanyin ya juya ya tafi yana ayyana ze dawo ya dauke takardarsa kawai ya fasa.

Safiya nayi ta shirya ranar Asabar baya fita da wuri kuma da yake yanayin sanyi ya fara kankama kowa na daki yayi luqui a ciki. Ta dauki jakar kayanta da takardar daya bata ta kama hanya, tsakaninsu da gidan Yakubu babu wata tazara me nisa dan dayan tsallaken Titin Audun ya maida masa da filin sa daya karba yayi madaidaicin gida. Ta zabi da taje gidan Yakubu ne saboda ko babu komai shidin ya jibanci lamarinta sannan tana tsoron yanda Mahaifinta ze karbi wannan Al'amarin idan taje tana buqatar wanda zeyi masa bayanin da ze sauqaqa masa tashin hankalin da komawarta gida da cikin da ubansa yake kokonto ze jefashi a ciki.

Balaraba na tsakar gida tana kauda kayan wasan yara da bata samu ta kwashe jiya da suka gama wasan ba taji ana qwanqwasa Get ta bude ganin Zubaidan ya bata mamaki sedai labarin da Yakubu ya bata na abinda ke faruwa a gidan Audun ya kauda mamakin nata ta matsa mata ta shigo tana mata sannu kafin ta karbi jakar hannunta. Bayan sun nutsu a falo, ta kawo mata Ruwan shayi da su madara da burodi tace

"Bari na soya dankali, bari nayi da se sun tashi a bacci tukunna"
"Ki barshi wannan dinma ya isa" Zubaidan ta fada a sanyaye amma Balaraba ta wuce kitchen tana ce mata yanzu zata gama.

Daidai wanda zataci ta soyo mata da kwai ta kawo, ta kalli kayan shayin na nan yanda ta ajiye su tace
"Na dauka kin hada shayin ya sarara kafin ma gama? To bari na hada miki"

"Baqi mukayi ne?" Suka jiyo muryar Yakubu dake fitowa daga daki yana tambaya. Balaraba ta amsa da cewar
"Baquwa dai" ya qaraso ciki yana kallon Zubaidan sam beyi mamakin ganinta ba domin yasan halin taurin da kafiya irin na dan uwansa. Yayi mamakin da har aka kwana hudu ma sannan ya ganta a gidan nasa.


*MAMAN MARYAM ONLINE BUSSINESS*

*Ina kuke Mata Yan kwalisa , Ina nufin isassun Mata ,Wai shin Kuna da labarin shahararren company nan namu na GHT wato good healthtreatments*
*Wanda yazo muku da fitattu Kuma* *ingantatattun suppliment ,na dukkan matsalolin ku*S'

*Ina maisan tayi kyau,irin na isassun Mata ya fitar Miki da shef

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login