Showing 216001 words to 219000 words out of 467220 words

Chapter 73 - MATAR MUTUM COMPLETED 1-3 BY MARYAM FARUK.doc

23 Sep 2025

12137

da tayi musu har gobe yana addu'ar kafin ta mutu in sha Allahu seta WanWani sama da ba?in cikin data shayar dasu. Matan da akace banda su dalilin irin wannan taro da ba'a taSa yin irinsa ba suka san lallai da akwai wani babban Al'amari a ?asa wannan tasa kowacce ta wanko ?afarta ta taho ranar taron. Momy da Hajiya Rabi basu san wainar da ake toyawa ba har s ana i gobe taron da suka tsinkayi muryar Hajiya Binta na bada umarnin abinda za'a girka gobe da yawan wanda za'ayi. Lokacin Salim na falon Momyn yana cin abinci yayi tsaki yace
"Wai me matar nan take shiryawa ne? Dan dai Alhaji bashida wata shawara tasa ta kansa se abinda tace masa"

"Wani abu ya faru ne?" Momy ta tambayeshi shine ya faWa mata kiran da Alhajin yayi musu. Tayi shiru, ita tayi girki jiya yauma itace amma ace Alhajin bega ya kamata ya sanar mata da komai ba ai shikkenan. Bata masa zancen ba har washe gari da Asuba kafin ta baro bangaren nasa taji yana waya da wani abokinsa yana sanar masa baze samu zuwa wani Waurin aure ba shine bayan ya gama yake ce mata wai ze gana da Yayansa duka akan maganar aurab Ahmad.

Cikin mamaki tace "maganar auran Ahmad kuma? Yaushe zancen ya taso da ni ban sani ba? Sannan naji kace zaka tattauna da Yayanka akan maganar daman haka kakeyi idan auran yayan naka ya tashi ko kuwa wani sabon salo ne ka tsiro dashi da za'a fara akan Ahmad?"

"Ya zaki ringa min wasu tambayoyi se kace wani Wanki? Tsakanin nida ke waye yafi zamarwa dole daya san maganar auran Ahmad ko kuwa ke zakije ki tambayo masa auran?" Alhajin ya faWa yana wani zare mata ido irin ta zo masa da raini. Zuciyarta ta harzu?a domin ta tabbatar wata ma?ar?ashiyar ce aka shiryota kuma Binta ce idan ba haka ba ita dashi basu taSa zancen auran Ahmad ba, tabbas Ahmad ya gaya mata iyayen yarinyar sun bashi izinin ya turo magabatansa har yace tayiwa Alhajin magana tace ba zatayi ba ya same shi da kansa bayan nan kuma ya fara rashin lafiya ta tabbatar da ace sunyi magana da Alhajin tilas seya gaya mata yanda sukayi domin a ko ina zata shaideshi baya abu gaban kansa ba tareda yayi shawara da ita ba kuma duk yanda ake ciki seya koma ya gaya mata ta sake bashi haske akan abinda ya kamata yayi.

To ace ma Ahmad ya masa magana sun tattauna shiya manta be koma ya gaya mata ba ai shi Alhajin a matsayinta na uwar Ahmad tana da ha??in ya sanar mata da zancen auransa ba wai taji a sama yaje ya shawarta da wadda a kullum bata da burin da taga kasawarsu. Ta sani ya fayyacewa Binta inda Ahmad ya nemo aure shine zatayi amfani da hakan dan ta tozarta yarinyar da iyayenta toh kuwa Allah ya fita ba zata taSa cin galaba ba.

"Ai ko ri?on Ahmad nakeyi ba wai ni na haifeshi ba ya kamata a fitar mun da ladan wahalata a sanar mun da zeyi aure, kuma a gidan nan baka taSa haWa taro dan wani ?a zeyi aure ba akan me za'a farashi akan Ahmad? Saboda shi me biyayya ne duk yanda aka bi dashi zece toh shi yasa kake so ka tauye masa ha??i ko yaya?"

"Ki fita kuma ?arfe goma ne taron, umarni ne na baki ba wai shawara ba ki kasance a gurin" ya bata amsa cikin halin ko in kula ba tareda ya bi ta kan maganganunta ba. Hawayen takaici suka zubo mata ta share ta fice daga Wakin, tana can ?uryar Wakinta ta kira Yar uwarta Maimuna ta gaya mata abinda ake ciki.
"Kije ki zauna a gurin saura kuma ki zama hoto kiyi shirun da kika saba a zartar da abinda ba haka ba dan nasan munafunci yasa aka shiryi wannan zaman ba wai dan Allah bane" Maimuna ta gaya mata. Tana shirya masa abin kari Hajiya Rabi ta shiga Falonta. Suka gaisa take tambayarta zaman da Alhaji ya kirata a waya yanzu yace mata wai ?arfe goma.

"Nima da Asubar nan ya gaya mun wai akan Ahmad ne, amma ita hamsha?iyar ai tasan da komai tunda tun jiya naga tana bada umarnin abincin da za'a dafa" Momy ta bata amsa tana murmushin takaici. Hajiya Rabi cikin jimami tace
"Ahmad kuma? Nasan dai ba laifi yayi ba koma menene Allah yasa Alkhairi ne, bari naje na shirya toh" daga haka ta wuce tana ta lissafin to wane irin abu kuma Ahmad yayi ko zeyi da har se an masa taron dangi haka?
Tun tara Iyalan Alhaji Audu suka fara hallara a gidan. Wasu su kaWai suka zo wasu tareda yayayensu da matansu dan haka gidan ya cika hayaniyar jikoki kota ina tashi takeyi suna ta guje guje. ?arfe goma Mazan suka hallara cikin babban falon da ke bangarensa a ?asa gaba Wayansu Jafar ne kawai babu a gurin.

Bayan an buWe taro da Addu'a tareda jawabin maraba daga uban garken, babu Sata lokaci ya shiga zayyano musu ma?asudin kiransu wannan taro.
Shiru falon ya Wauka banda ?arar Ac bakajin komai se salallamin da Hajiya Binta takeyi murya a sama tamkar wadda aka aikowa da mutuwar iyayenta dare Waya, yanda takeyi seka rantse da Allah yanzu ta fara jin maganar, tamkar bada ita ta tsarawa Alhajin daya tara su ba domin ta ?addamar da wani shiri nata. Can kuma ta zabura ta mi?e tsaye idonta akan Ahmad daya sunkuyar da kai ?asa, abinda yake ji a zuciyarsa baze misaltu ba, wai duk akanme? A ina aka taSa haka? Shi yaushe ya cewa Alhajin maganar aurensa ta tashi? Auran da yake ?o?arin yakicewa ya ha?ura da yarinyar shine aka zo ana masa wannan taron dangin akansa?

"Amadu ashe baka da hankali ban sani ba? Wayonka da nake gani na banza da wofi ne baka san komai ba se neman kuWi kamar ?arawo?" Hajiya Bintan ta faWa, Momy ta Wago a karon farko tun zamanta a falon ta kalleta jin kalmar data jiSanci gudan jinin nata da ita wai ?arawo ita kuwa Hajiya bata dakata ba a fusace taci gaba da cewa

"Wallahi tallahi ko sama da ?asa zata haWe banga uban daya isa ya ?ulla auran nan ba, yar Bakanike Amadu? Mu zamu haWa surukuta da Bakanike kuma Sadaka yallah mayu? to idan ita uwarka sallamammiya ce komai aka ce bata musawa ni bazan lamunta ba. Iyakar irin tsiyar da aka Wakko mana sun isa ba se an haWo mana da wanda zasu zo suna mana Wauki WaiWai suna ciyayya ba" Hajiyar ta kai aya tsabar masifa numfashinta har neman sar?ewa yakeyi.

Alhaji Audu dake kishingiWe akan kujera ya nisa yace "Duk wannan a ganina ba wani abun azo ana tayar da jijiyar wuya akai bane, magana ce ta aure kuma shi ma'auri yace yaji ya gani sannan ni da kaina nayi binciken iyayenta kuma ban samu wani abun ?i da ze saka a hana shi auranta ba, ni kiram da nayi muku na taraku ne dan muyi shawara akan yanda za'abi gurin neman auran, suwa za'a wakilta suje".
Momy da Anty Amarya suka kalleshi kamar yanda da yawan yayayensa dake zaune duk suka kalleshin. Harara Hajiya Binta ta maka masa kamar wani Wanta tace
"Lallai Alhaji, ya kake nema ka canza magana koda yake kwanakin nan ka zama me fuska biyu daman"
Mamaki kamar ya sha?esu jin abinda Hajiyar ta faWa masa, kunne, baki da hanci duk suka zuba suna jiran suga matakin da ze Wauka amma sukaji mu?us ko tari Alhajin beyi ba sema Hajiya data ci gaba da sababinta tana cewa

"Da zakace bakaga wani aibu da ze hanashi auranta ba ai kuwa ita keda babban aibu, Talaka yar talaka jikar talaka kuma Mayya".

"Amma Hajiya talauci fa ba fasi?anci bane, sannan baya cikin sharuWWan da suke hana aure. Kuma maita da kike jifanta da ita kin san cewar fa ba ?aramin abu bane idan sukaji zasu iya yin ?ararki akan hakan tunda baki da wata tartibiyar hujja data tabbatar da abinda kike jifansu dashi" tsautsayi ya saka Hajiya Rabi magana tamkar kuwa Hajiya Binta na jiranta daman tace

"Babu shakka Rabi dole kice talauci baya cikin abinda ze hana aure saboda kinji zaki samu ?arin yar uwa ko Ahalul fu?ara'u za'a ?ara yawaita? Koda yake ma a hakan ita ai ta fiki tunda nata uban ance yana da tsayayyar sa'ar da yake samun abun kaiwa bakin salati ba irin naki tsohon ba da se an bi gidaje anyi yawon maula kafin a tattara a kaiwa Iyali ya isa be isa ba a yayyafa aci shi kansa Alhajin daya kwaso wa kansa ?aya gashi nan kullum cikin nadama da dana sanin auranki yake, jiya farar safiya gari ko gama haske beyi ba me dattin hula ya buga mana gida wai katangarku ta faWi, daka fita ka bashi kuWin ina dawowa kayi kana mitar daka saba duk sanda yazo maka maula irin rayuwar da kake so shima Amadun ka jefa shi a ciki kenan ya ?are yana nema dangin Sadaka Yalla su dabaibayeshi su cinye sannan subi Wan naman jikin nasa ma da ba auki ne dashi ba su lashe ni daman kwanakin nan zugewar nan da yakeyi ina ganin har sun fara lasar sane wlh sun zarge kurwa tab" Hajiya Binta ta faWa tana tsaida idonta akan Alhajin.

Ba?in cikin maganganunta suka sanya Anty Amarya barin falon babu shiri saboda kukan daya taso mata, shekaru kusan Ashirin kenan babu ranar Allah da zata fito ta koma ba tareda ta goranta mata talauchin da ba ita ko iyayenta suka siyawa kansu ba, dukda tabbas Mahaifinta shi yake ?ara zubar mata da mutunchi saboda ya kasa wadata da dan Abinda Allah ya hore mata take taimakonsu dashi haka shima Alhajin ta sani iyakar ?o?ari yanayi cikin su ukun ita kaWaice duk watan duniya seya saukewa iyayenta buhunhunan Abinci da kuWin cefane duk a son Baban nata ya dena banzar Wabi'arsa ta yawon maula gidajen Masu kuWi, ya dai rage amma fa kullum yana tafe gidan Alhaji Audu, sabulun wanka omon wanke wanke ko yana da kuWin da ze siya se yazo ya roqa an bashi.

Hajiya ta bita da Harara taja tsaki ganin Mu'allim yabi bayan mahaifiyar tasa bayan daya bi Hajiyar da wani kallon Tsana idanunsa sun tara ?wallar ba?in ciki
"Umma ta gaida Ashsha, dama banga tsegumin daya kawo ku ba Alhalin baku da abin faWi" Hajiyar ta faWa tana buga cinya kamar wata yarinya.

Alhaji Babangida ne yayi gyaran murya, daga jin yanda yake magana kasan a tunzure yake yace
"Amma Hajiya Binta ni banga ta inda zancen Auran Ahmad ko wadda yake son aure ya shafeki ba tun da dai ba Wanki bane. Ita mahaifiyarsa batayi ?orafi ko nuna rashin amincewarta akan abun ba se ke meye naki a ciki? Sannan koda ace mahaifin yarinyar nan yafi kowa talauci a duniya wannan ba hujjar ace ba za'a auri yarsa ba tunda talauci ba fasadi bane"

"Nima abinda na gani kenan Yaya, duk ma ba wannan ba a gidan wa aka taSa titsiyewa akan matar da yake son aure? Ina har yar rawar Tiktok aka auro mana gashi nan ta fitini kowa tana koyawa yaranmu shaiWanci amma waya Waga kai yace wani abu kan hakan kodan saboda shi shafaffe ne da mai shiyasa ba'aga aibun abinda yayi ba se Ahmad da an san idan aka ce kar yayi ze ha?
Lura ai biyayya kuma ba hauka bace" Dr Hassan ya faWa cikin ?unar rai.

Hajiya ta harari Alhaji Babangida, koda ta girme shi amma shakkarsa takeyi ta san ko shi Alhajin yana bashi darajar kasancewarsa ?a na fari a gidan, maganar Hassan ce tasa tayi kasa?e tana kallonsa. Naziru ya zaburo masa yana cewa
"Ka kira sunana kai tsaye ka dena wani kwane kwane, kuma na auri yar Tiktok Win koda abinda zakayi akai?"
"Yi shiru da bakinka Naziru barni dashi" Hajiya ta gyara zamanta taci gaba da cewa
"Yanzu kai Hassan tsabar baka da kunya ana maganar matar aure me Asali da tushe daga babban gida har ka saka baki? Koda yake kana da hujjar bin bayan Al'amarin, tunda uwarku ta auru a matsayinta na Tubabbiyar Karuwa ai dole kace wannan ma ba......"

Tsawar da Hussaini ya daka mata me kama d??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????a saukar Aradu ta saka sauran maganganun bakinta ma?alewa. Cikin yanayin da yake nuna ?ololuwar Sacin ransa dan hatta da jijiyoyin kansa daya sha askin Skin sun fito ruWu ruWu haka idonsa ya rikiWa yayi jajir ya nuna ta yana cewa
"Akul Binta, duk abinda kike ji dashi ya tsaya kan waWanda kika raina karki yi kuskuren sako mahaifiyarmu a shirginki domin yanzu ba da bace idan kuma ba haka ba...."
"Idan ba haka ba me zakayi?" Alhaji Zakariyya ya diro gabansa kamar wanda aka harbo da kwari da baka yana huci, Hajiya da tsoron Hussainin ya cikata jikinta har Sari yake ta ja hannunsa Zakariyyah tana cewa
"Barshi Ubana kasan Wan hau ne"

"Ki ?yaleni Hajiya ku kuke nuna kuna tsoronsa a gidan nan idan zafin kai da ?waya yake ji dasu shi ?aramin ?warone kansa baze Wauki ko rabin chajin da nakeyi ba an faWa ance Yayan Tubabbiyar Karuwa kayi abinda zak...."

Marin da Hussanin ya Waukeshi da shi irin me jirkita ?wa?walwar nan ya sakashi wuntsilawa gefe dafe da fuska yana raba idon, Hajiya Binta ta fasa ihu tayi kansa ganin yanda yake zare ido kamar tunaninsa ya kauce, a fusace shi kuma Naziru ya cakumi kwalar Hussanin ya kai masa naushi a fuska yana cewa
"Wlh baka mari banza ba sena rama masa" kafin kace me dambe ya sar?e a tsakaninsu kowanne ya shiga kaiwa Wan uwansa mugun hari da yake jikinsu iri Waya ne, dukkaninsu sangangan suke irin jikin Audu Bechi wannan ya ?arawa Damben nasu armashi dan kowa ya gagara kai Wan uwansa ?asa amma dai Hussainin yafi kai hari a zuciye.

Ahmad, Momy da Dr Hassan ne suka shiga ?o?arin raba su sauran jama'ar falon kuwa seka rantse a Tv suke kallon wannan Al'amari babu wanda ma ya motsa balle ya kai agaji sema tattare ?afafunsu da sukayi dan kar a faWo musu. Hajiya na gefen Alhaji Zakariyyah dake kururuwa kamar mace sakamakon yanda Marin ya shammaceshi ya shige shi dagaske ga ha?orinsa Waya daya turguWe a ?asa, ihu Hajiyar take itama tana Zagin Hussaini, jafa'in duniya babu wanda bata janyo masa ba dashi da Hassan Winsa harda uwarsu dake can gida bata san wainar da ake toyawa ba ta karSi rabonta se abi da Hajiyar ta manta ne bata ambata ba.

Momy ta kalli Alhaji Audu dake zaune akan kujera tamkar gunki cikin kuka tace
"Kana kallo Alhaji, jira kake se Waya ya kashe Waya kafin ka tsawatar musu? Wannan shine daidaiton da kake fatan samuwarsa cikin zuri'arka? Anya kuwa Alhaji ka shiryi tarar da ubangijinka cikin salama kamar yanda kowanne musulmi yake fata?" Tana gama faWar haka cikin kuka ta fice daga falon, a bakin ?ofa taci karo da yayansu Mata a tsaitsaye cikin tashin hankali. Hajiya ?arama datafi kusa da ita tacewa

"Kira Babanku Al?ali ki gaya masa yazo babu lafiya a gidan nan" ta shige cikin gida tabar Hajiya ?arama na ?o?arin kiran Baba Al?ali amma sau biyu wayar na suSuce mata saboda yanda jikinta yake rawa da?yar ta iya danna kiran.
Momy kuwa harta isa Wakinta hawaye be tsaya mata ba, ba kuma tasan ranar da zata dena zubar dasu ba hawayen ba?in ciki, takaici da dana sanin auran wannan mutumin da sam bata san me zata kirashi ba. Son zuciyane ko kuwa tsabar ?in Allah ya saka Alhajin yin abubuwan da yakeyi bata sani ba amma koma menene ta tabbata muddin be tuba ya gyara ala?arsa da Ahalinsa ba ya mutu a haka tabbas baze kwanta cikin salama a Kabarinsa ba.

A can falon kuwa Hussaini ya mazge Hassan Winsa daya cukumi cikinsa yana ?o?arin janyeshi kafin ya kaiwa Ahmad ?afa amma ya goce ba shiri suka matsa daga rabon damben suka barsu zuwa sannan Hussainin keda nasara dan ya kai Naziru ?asa ya masa lilis har ya kai baya iya maida martani se ?o?arin kare kansa kawai yake amma Hussaini be ha?ura ba yaci gaba da jibgarsa kamar Allah ya aiko shi. Dama ce irin wadda ya daWe yana fatan samu da ze huce kaWan daga irin takaicin da Hajiya Binta da Yayanta suka ?unsa musu a rayuwa. Lokacin yarinta tsoron hukuncin da Alhaji zeyi musu da izayar da zasu sha a hannun Hajiyar tasa yake ha?ura idan zuciyarsa ta raya masa daya jibgi yayanta in suka musu abu, yasha ya kwatanta ya dake sun in yaso ya gudu ya bar gidan amma yasan Hassanbaze yarda ya bishi ba, saboda shi ya shanye duk wani wula?anci a gidan yanzu kuwa Allah ya bashi damar da duk wanda yace ze shigarwa Nazirun seya haWa dashi ya zane.

Seda Hussani gama yayiwa Nazirun casar gero kafin Allah ya bawa Alhaji Audu ikon yun?urawa daga zaunen da yake tamkar wanda ya tafi hutu wata duniyar na wucin gadi ya dawo haka ya shiga jan numfashi kamar me Asthma. Ahmad yayi kansa yana cewa
"kun gani ko ku bari idan ba kashe shi kuke so kuyi ba".

Hussaini daya gama aikin Allah ya tsugunna ya Wauki Agogon Azurfarsa daya tsinke a garin dambe bayan daya gaji da jibgar Naziru ya kalli Ahmad yace
"Toh ya mutu mana, dama wa rayuwarsa ta dama bare idan ya mutu yayi ba?in ciki? ?ilan ku da su daya Wauka Yaya ya fifitasu akan kowa sune zasu shiga uku duk ranar da aka ce babu shi" sannan ya kalli Hajiya Binta da idanunsa da suka koma abin tsoro yace
"Nan gaba idan wani daga cikin marasa kunyar Yayanki yayi niyyar tsoma baki a sabgata ki gargaWeshi, idan ba haka ba zanci gaba da nuna muku abun da ?an Tubabbiyar karuwa ze iya aikatawa" yana gama faWar haka ya fice daga falon a fusace fuuuu kamar kububuwa.

Maganganun Hussaini sun daki ?irjin Alhajin kamar shigar bullet, ya yun?ura cikin wani yanayi ya tashi tsaye dan bakinsa kamar an li?e masa shi da glue yake ji yana tsayuwa akan ?afafunsa jiri ya kwasheshi ya koma kan kujerar Yaraf kamar wata gingimemiyar giwa ta faWi. Ahmad da Hassan suka rufu akansa, Hassan Win ya kalli Ahmad yace
"Ri?eshi, bari na Wakko Kit

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login