Showing 312001 words to 315000 words out of 467220 words

Chapter 105 - MATAR MUTUM COMPLETED 1-3 BY MARYAM FARUK.doc

23 Sep 2025

12177

suka ringa mata dan gaba Waya ta koma kalar majiyantan itama ta samu guri ta zauna jin cewar har sannan Ahmad Win be farka ba amma dai Dr Hassan yace musu babu komai Allura suka masa me ?arfi saboda jikinsa ya huta dan bayan Momy tazo tayi masa bayanin da Ahmad ya mata na jiya yace babu komai suna kan bincike akan abinda yake damunsa da zarar ya kammala koma menene in sha Allah za'a shawo kan matsala.

Se guraren uku na rana ya farka jikin kuma da sau?i sosai dan bayan an cire masa ?arin ruwa da kansa ya shiga banWaki yayi wanka da alwala yayi sallar Azahar kafin ya dan ci faten dankalin da Momy ta saka Maimuna tayi masa da kunun gyada, yanda yake ?arfafa jikinsa yake abubuwa harda dai son ya kwantar musu da hankali su bar damuwar da suke ciki. Seda suka tabbatar da jikin nasa yayi kyau bayan magriba kafin su Momy suka wuce gida suka bar Fatima, suna tafiya kuma se ga Ummanta tareda Baffa, Umman ce ta fara shiga ita kaWai har tace ma sun haWu a ?ofar Asibitin sun gaisa.

"Rubutun ne be kammala ba se yanzu aka kawo kuma bana so muzo ba tare dashi ba shiyasa muka jinkirta" Umma ta faWa bayan sun gaisa, ta mi?a mata madaidaiciyar jarka cike da ruwan tawada ruwan zuma me haske sannan ta bata wani ?aramin gorar faro tana sake cewa

"Ruwan zamzam Win da Sauda ta kawo mun ne wanda tayi dawafi dashi, yasha ya shafe jikinsa Alfarmar annabi da alkur'ani ze samu afuwar duk abinda yake damunsa" ita da Ahmad suka haWa bakin gurin godiya se ga Baffanta tareda Baba Al?ali da Dr Hassan sunyi sallama. Cikin mutuntawa Umman suka gaisa da Baba Al?ali da Dr Hassan Baffa kuma ya shiga yiwa Ahmad ya jiki, basu jima sosai ba sukayi musu sallama suka tafi Baba Al?ali ma ya fita tareda Dr Hassan Win se lokacin ta samu sararin sakewa ta kwanta jikinsa ta fashe masa da kuka.

"Ke kam so kike hawayenki su ?are ne? Tum safe fa kike kuka, badai gashi na samu lafiya ba dama fa Wan mild ciwon ciki ne duk kika rikita kanki kiketa koke koke gashi duk kin tayar ma da kowa hankali" ya faWa yana shafa kanta seta rage kukan ta Waga kai ta kalleshi, yanda yake maganar wai mild ciwon ciki kuma ta tayarwa da kanta hankali ta tada na wasu, wato shi da sau?i ya Wauki abun

"Irin wannan kallon da kikeyi mun maida wu?ar cigaba da kukanki gara ma kiyi yanzu ki ha?ura ko zuciyarki ta dangana" ya sake faWa yana mayar da kanta ?irjinsa seta fizge ta tashi zaune tana kallon cikin idonsa tace

"Ahmad me kake Soye mun?"
"Ahmad kai tsaye babu ko bismillah?" Ya faWa cikin wasa yana buWe mata ido seta tamke fuskarta amma tana buWe baki da niyyar magana kuka ya sake ?wace mata,

"Ikon Allah, daga cewa kuma kiyi kukan ke baki san wasa ba?" Ya faWa yana rungume ta, tana jin yanda zuciyarsa take bugawa fat fat, seda tayi kukan me isarta kafin ya saketa dalilin Nurse data shigo zata sake maida masa ruwa yace ta jira yayi sallar isha'i, seda yayi sallar kuwa kafin aka maida masa ruwan babu jimawa bacci yayi awon ga??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????ba dashi.

Washe gari wuraren goma na safe aka sallame su suka wuce gida saboda uzzurawar da yayiwa Dr Hassan kuma ganin jikinsa yayi kyau sannan a gwaje gwajen da sukayi masa na Typhoid, malaria, ulcer harda gwajin HIV dana Hepatitis duk sun nuna negetive ya dai rubuta masa magunguna da zasu taimakawa jikinsa samun kumari sannan ya ja masa kunne akan kulawa da lafiyarsa ya rage ayyukan da suke akansa ya kuma guji duk wani abu da ze zame masa damuwa sauran gwaje gwajen da sakamakon idan sun fito duk abinda ake ciki zasuyi magana.

Se bayan da suka dawo gida Alhaji Audu ya kirashi yaji ya jikin nasa, haka yan uwa da abokanan arzi?i sukayi ta tururuwar zuwa dubashi, seda ya kwashi tsayin sati biyu banda Sallah babu abinda yake fitar dashi waje yana gida tareda Fatima da ta tattara hankali da duk wata nutsuwarta akansa, lelensa takeyi tamkar wani bakwainin jinjiri. Shima yana iyakar ?o?arin sa gurin ganin ya cire damuwa daga zuciyarsa wanda ita take neman fallasa sirrin da yake ta ?o?arin binnewa. Sau tari idan zafin ciwon ya masa yawa sedai ya shiga Waki yayi kuka har se ya samu salama sannan ya fito yaci gaba da sabgoginsa tamkar babu komai sedai duk yanda yaso da ganin komai ya daidaita maimakon sau?i ya samu cikin al'amuransa se ya zama sake lalacewa yakeyi yana ramewa tamkar wanda ake Wiba ana miya dashi sannan ga damuwar daya sakawa kansa ta ganin kan yan uwansa ya haWu guri guda kuma abin ya?i yuwuwa, bashida aiki se yawo gidajensu yau yaje gurin wannan gobe yaje gurin wancan idan ya samu ya haWo nan da?yar se can ta zille duk abin ya rikice masa ya kuma rasa yanda zeyi ga damuwa ga zullumi da fargabar da take neman tarwatsa zuciyarsa.

********
Al'amarin Hajiya Binta kuwa abin ba a cewa komai bayan da suka isa akayi mata duk wasu gwaje gwaje da hotuna daga ?arshe likitoci suka ce in har tana so ta tsira da ranta da lafiyarta tofa sedai baki alaikum a yanke ?afar saboda kwayoyin cuta sun shiga akwai kuma ya?inin cewar cancer zata iya kama gurin dan haka gudun abinda ka iya biyo baya a yanke, seda ta suma sau bakwai daga ta farfaWo ta tuna wai yanke mata kafa za'ayi se ya sake sume wa seda akayi da gaske kafin jini da bugun zuciyarta da jijiyoyi ya daidaita har akayi aikin aka cire ?afar, sanda ta farfaWo bayan aikin kuwa ta tabbatar da gaske ta rasa ?afarta irin ihu da kururuwa data ringayi seda aka daddanneta akayi mata allurar bacci me ?arfin gaske kafin suka samu salama.

Jafar ne tsaye akanta, dan Yakubu da suka tafi tare tunda komai ya daidaita bayan an saka lokacin yankewa Hajiyar ?afa ya koma gida, shi kuma Zakariyya sunyi iyakar abinda zasu iyayi masa, anyi masa gashi na tsayin sati biyu Allah kuma ya taimaka ya fara iya motsa jikinsa yana tashi dakansa da saura abubuwa magana ce dai sunce babu tabbacin bakinsa se sake buduwa saboda buguwar daya samu akai ta taSa masarrafar maganarsa sannan ya rasa tunaninsa kuma ciwon mantau ne na har abada babu wani chance na cewar ze iya tuna baya.

Haka dai suka tattaro suka dawo Nigeria bayan Yakubu ya sake komawa suka taho tare shi kuma Jafar ya koma gurin neman abincinsa cike da takaicin hali irin na Hajiyarsu, a kwancen da take da ?afa Waya ta halitta Waya ta ?arfe tamkar robot amma bata hankalta ta zubar da makaman ya?in ta ba alwashi babu kalar wanda bata ciba akan mutanen da take zargin su sukayi mata asiri har wannan abin ya sameta musamman da tunda suka tafi zata iya lissafa sau nawa Alhaji Audun ya kira yaji lafiyarsu, tamkar ma dai ya manta da ita ko ya zata ta mutu, ta dawo da mugun ?uduri tareda mugun nufi a zuciyarta, lalular da Zakariyya ya samu ta sake zaburar da ita, yanzu shi ya zama mara amfani, shi kaWai ya rage mata da suke haWa kai gurin neman mafita dan haka yanzu ya?in ya zama nata ita kaWai.

A sannu sannu ciwo ya fara cin karfin Ahmad, jikinsa ya gaza, A cikin wata guda duk dauriyarsa da Soye yanayin abinda yake tattare dashi seda ya gaza ya zama cewar ciwo ya gama fallasa kansa a jikinsa yanda ya fita a hayyacinsa ko wanda be taSa saninsa ba ya kalleshi ze tabbatar da bashi da lafiya kuma ciwo me tsanani irin me cin jiki da ruhi neyake damunsa amma taurin zuciya da kafiya irin tasa ya barwa ransa komai ya gagara furta abinda yace cin ransa tsayin shekaru sedai yanayin da yakeji kuma yake gani ya tabbatar lokaci yayi da abin ze bayyana kansa ko yaso ko ya?i.

Zuwa sannan shida kansa ya yarda baze iya shikaWai ba, yana bu?atar mataimaka amma a duk sanda ya dubi mutum biyu mafiya soyuwa a gurinsa mahaifiyarsa da matarsa, rashin sanin takamaiman damuwarsa ta jefa rayukansu cikin garari se yaji baze iya raba damuwarsa dasu ba yasan ba zasu iya Wauka ba. Basu kaWai ba hatta da yayansa ya lura rashin lafiyar sa ta fara taSa su, sunyita tambayarsa me yake damunsa? Bashida lafiya? Me yasa bazeje Asibiti da sauran tambayoyin da suke sake karya masa zuciya sannan yawan kukan da Fatiman takeyi suma sun koya muddin suna gida haka zasu tasa shi gaba idan ta bashi abinci ya?i ci tana fara kuka zasu shiga tayata wannan al'amari yana sake dugunzuma masa hankali matu?a.

Saboda yanayin tsananin da jikinsa yayi tilas ya dena fita ya saki duk wasu sabgogin sa a hannun Salim da sauran Amintattun Yaransa da Abokanansa da suke huldar cinikayya, ya dena zuwa gidansu itama Fatiman ya ya hana. A muryarsa ba zaka taSa cewa bashida lafiya ba shiyasa ba kowa ya san tsananin ciwon nasa ba se ita Fatiman dake tareda shi, tun tana kuka tana ro?onsa akan ya gaya mata me yake damunsa harta ha?ura ta fawwalawa Allah kawai ta zuba masa ido.

Momy kanta ta ha?ura da son sanin me yake damun Ahmad tunda Dr Hassan yace mata bincikensa be nuna amsa Ahmad na tareda kowanne irin ciwo ba se kawai ta ake mi?a lamuranta ga Allah ta sake yawaita sadakar da takeyi, ta gaji da surutun mutane wasu suce Asiri aka masa wasu suce mayune kowa dai da maganarsa da kuma abinda ze bata shawarar tayi amma duk tayi watsi da komai ta fawwalawa Allah, yanda Alhaji Audu yayi banza da al'amarin Ahmad Win koda wasa be taSa yi mata maganar ko ya nuna damuwar sa akai ba shi yake sake kambama damuwar ta, ta tuna yanda ya damu da Binta da Zakariyya har seda aka fita dasu kafin ya samu nutsuwa amma Ahmad tamkar ma besan halin da yake ciki ba, koda yake da wuya idan ya sani Win saboda tunda Ahmad Win ya dena zuwa gidan koda wasa be tambayi dalili ba ta yuwu amfanin da yake masa ya ?are shiyasa ya sake maidashi matsayinsa na da dashi ko babu shi duk Waya a gurinsa.

Cikin wannan yanayi Hajiya Binta suka dawo Nigeria, halin data samu gidan a ciki ya goge mata kaso hamsin cikin Wari na ba?in cikin data dawo dashi. Irin yanda ta tararda Aisha a firgice ya daWaWa mata rai, yana cikin abubuwan data ro?i malamin da sukaje gurin sa yayi mata a bazara Aisha ta rasa nutsuwa a cikin gidan daga ?arshe ma ta shiga daji sannan labarin rashin lafiyar Ahmad Win ko tamkar busharar Aljanna haka ya zame mata, shi cewa tayi a haWa shi da masifar da se ya rasa komai nasa, bata so ya mutu amma tana burin ya wula?anta ta yanda duk masu sonsa se sun gujeshi yanda ya taso taurarinsa suka dishashe na Yayan ta baki Waya a gidan tana so yayi ba?in da ko mujiya se ta fishi farin jini a cikin al'umma da alamu dai burikanta suna dab da cika.

Damuwarda jama'ar gidan suke ciki tasa babu ma wanda ya lura da canjin halittar data samu, a gurin saka mata kafar anyi rashin dace aka saka mata wadda tafi ainihin ?afarta tsayi, sannan zallar karfe ce tamkar dai robot haka ?afar take a tsaye dan haka ya zama tana tasgaWawa, ainihin ?afarta se ta zama kamar ta shanye ita kuma ta ?arfen tunda bata lankwasuwa haka take jefata wata irin tafiya takeyi kakar Aljanar data shawu tayi tatil. Buri Waya kuma mafi soyuwar cika a gurinta na karkatowar hankalin Alhaji gareta shine babu alamun cewar zata samu nan kusa domin yanda taga Alhajin ya zama shima kamar wani wanda aka zarewa laka, beda aiki sena zama yayi shiru ya zurawa waje Waya ido yana tunani amma tunda waWanda suka tsole mata ido Al?iyamarsu ta tsaya a faWar ta to a juri zuwa rafi wata rana tulu ze fashe.

Daren wata Alhamis ?arfe uku na dare ciwo me tsananin gaske ya farkar da Ahmad daga baccin daya samu da?yar bayan daya sha magani, ya kamata ace ya koma ganin likitansa tun sati biyu daya wuce amma hakan bata samu ba saboda ya rigada ya sallama baya tsammanin akwai sauran saka rai cikin al'amarin sa. Da jan jiki ya shiga banWaki ya dafe sink yana sauke numfashi, ciwo yakeji irin wanda baze iya kwatantawa ba. Da?yar ya iya zaro wayarsa dake cikin aljihunsa tun cikin dare kafin baccin ya kwashe shi yake rubuta sako ze turawa Jafar ya rubuta yafi sau goma ya sharewa a yanzun ma daya ciro wayar sabucewa tayi daga hannunsa saboda yanda jikinsa yake karkarwa ta faWi ?asa ?arar faWuwarta ta farkar da Fatima da itama nata baccin ba nauyi yakeyi ba ta yun?ura da?yar ta shiga banWakin.

Hannu biyu ta aza akai ta fashe da kuka me tafe da ihu ganin jinin dake cikin sink Win harda gida guda ta tabbatar kuma daga jikinsa yake, bata tuna cewar dare bane haka ta fita tana kuka ta shiga bubbuga Wakin Liman me gadinsu shiru be amsa ba se daga baya ta tuna ai baya nan, ya tafi gida anyi musu rasuwa seta nufi get Win da gudu ta buWe ta fita, ta kalli gidan Jay dake kulle sama da shekara guda kenan rabonsu da Najeriya, gidan dake kallon nasu ta shiga bugawa tamkar bata cikin hayyacinta, masu gadin unguwar suka taho daidai nan me gidan ya buWe dan yana falonsu na ?asa ya idar da sallar nafila yana lazumi yaji bugun ?ofar sanda ya fito masu gadin sun dabaibayeta da tambayar ko lafiya amma ta kasa basu amsa se kuka kawai takeyi.

Da?yar ta iya gaya musu, Dattijon tareda masu gadi biyu suka shiga gidan se matarsa da itama bugun Fatiman ya fito da ita, a kwance suka samu Ahmad ?asan tiles Win banWakin cikin mawuyacin hali suka fita dashi.

A ?ofar ICU ta zauna ta haWe kai da guiwa tana rera kuka me ban tausayi Dattijon na tsaye kanta yana nanata Innalillahi wa'inna ilahi raji'un ya gagara ce mata komai, sama da awanni biyu har aka kira sallar Asuba likitocin da suka shiga da Ahmad basu fito ba zuwa sannan hawayenta sun bushe ta jingina kanta kawai jikin bango tayi shiru, maganar Umma a shekarun baya ta faWo mata tamkar an harbota, lokacin da take kuka akan ba zata auri Ahmad ba ranar tace mata kukan wasa takeyi sannan na gasken na tafe idan bata yi wasa ba se tayi kuka har hawayenta sun bushe gashi kuwa ranar tazo mata,

*MATAR MUTUM*
*NA MARYAM FAROUK (UMMU MAHEER*

*FIKRA WRITERS ASSOCIATION*

*LITTAFIN KUDI NE*
*PAY 500 A ASUSUN*
*7061838488*
*OPAY DIGITAL SERVICES*
*MARYAM FAROUK*
OR
*0709290797*
*ACCESS BANK*
*SE A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488*
*IDAN KATINE A DAUKI HOTONSA A TURA ZUWA LAMBAR SAMA VTU KUMA A TURA A 08142548705*

*Kuyi following dina a Arewabooks @Maryamfarouk01 inda zaku karanta wannan littafin tareda sauran littattafaina*
*NAGODE*

*BOOK 3*
*PAGE 19*

Alhaji Munzali banda innalillahi wa'inna ilahi raji'un babu abinda yake maimaitawa a fili har likitan daya duba Ahmad ya gama yi masa bayani.
"Se ha?uri Baba, Addu'a kawai yake bu?ata a yanzu domin magannar gaskiya babu wani abu da wani likita ze iyayi masa sedai fatan jinya ta zame masa kaffara kawai ayi ha?uri" Likitan ya faWa cikin kwantar da murya saboda ganin yanda Alhaji Munzalin ya rikice se zufa yakeyi dukda Wakin sanyi ?alau yake.

"Dan Allah Dr zan nemi alfarma koda wasa kar ka bari yarinyar nan matarsa tasan abinda ake ciki, ku bari a fara sanarwa da iyayensa, akwai abokina da yake da ala?ar kasuwanci da mahaifinsa bari na kirawoshi idan yaso se ya bada number da za'a sami wani nashi dan bana tsammanin ta fito da waya saboda a kidime take" Alhaji Munzalin ya faWa yana laluben Aljihunsa.

Da mamaki likitan yace
"Kenan bakai ne Mahaifin sa ba?"
"Makwafci nane* ya bashi amsa yana mi?ewa tsaye ya shiga kiran layin Abokinsa da ya san yana da ala?a da Alhaji Audu Bechi sedai akayi rashin sa'a wayar a kashe. Shida ma bata gama cika cif na a sannan dan haka beyi mmakin rashin samunsa a waya ba. Maida wayar yayi Aljihunsa yana cewa

"Ban sameshi ba amma bari naje na san gidan Mahaifinsa yanzu zan dawo" be jira jin abinda likitan zece ba ya fita har yana haWa hanya saboda kiWima da tashin hankalin daya tsinci kansa a ciki. Ahmad yaro ne me matu?ar kirki da girmama na gaba dashi, kullum ta Allah tare suke sallar Asuba da kuma Magriba da Isha idan ya dawo gida da wuri. Kowa ya shakdeshi da halin kwarai da karamci ga kyauta babu ruwansa da tunanin kusan duk mazauna gurin nada wadata idan ma beyiwa mutum kai tsaye ba to zeyiwa yaronsa.

Ya dai daWe yana hasashen Ahmad Win bashida lafiya, tunda daman ba mutum bane me kuzari sosai duk Abinda yayi tunani ko sickler ne ashe babbar jarabawa ubangiji ya haWashi da ita, tausayinsa me tsanani tareda tausayin yayansa ya kamashi, kalar tasu ?addarar kenan.
Yana tunane tunanen ya isa ?ofar gidan Alhaji Audu Bechi, daga gefe yayi parking yana tsayawa kuwa securities biyu suka taso kansa suna tambayar lafiya da sassafen nan me yake nema a gurin. A ta?aice yace musu gurin Alhaji yazo, suka shiga ?are masa kallo dukda ba a wula?ance yake ba amma beyi kalar wanda kai tsaye zece gurin Alhaji yazo babu appointment babu komai ba.

"Uzuri ne na ujila, base na shiga gidan ba. Ni makwafcin yaransa Ahmad da Jafar ne, abinda naso faWa masa yanzu haka Ahmad yana Asibiti a kwance jikinsa ya tsananta babu kowa a tare dashi se matarsa itama kuma tana cikin yanayin da take bu?atar wanda ze kula da ita ne dan haka a sanar da mutanen gidan" Alhaji Munzali ya faWa, ai sunan Ahmad daya ambata yasa duk suka shiga hankalinsu suka fara jera salati Issa ya kwasa da gudu ya shiga cikin gidan Alhaji Audu na kishingide a kan carpet, tun daren jiya jikinsa babu daWi, be iya bacci bama seda Dr Charles yazo ya auna jininsa

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login