Showing 138001 words to 141000 words out of 467220 words

Chapter 47 - MATAR MUTUM COMPLETED 1-3 BY MARYAM FARUK.doc

23 Sep 2025

12125

KUMA MAI KANKAT DAN UWAR GIDA TA TURARA GIDANTA JIKINTA DAMA KAYAN SAWARTA ITA DA YARANTA,,HARMA ZAWARAWA DUK MUN TANADI KOMAI*
*DOMINSU SUMA*

*-MUNADA SHOES AND BAGS SBD ISASSUN MATAN DA SUKA AMSA SUNANSU MATA*=?
?
*- MAKEUP NA BRIDAL ND CASUAL...*

*IDAN KINSAN KINAJIN LABARIN SHAGON SALOON NA AFINTY QUEENS AMMA BAKI TABBATAR DA YADDA AIKINSU YAKE BA TO YAR UWA GADAMA TASAMU MEZAKI TSAYA JIRA MAZA KEMA KI ZARGAYO SHAGONMU DAZAN JERA MIKI ADDRESS DINSHI A KASA DOMIN KEMA KI TABBATAR DA KALAR IRIN NAMU KWAZON DA MUKA KWARE AKANSHI GURIN GYARAN JIKIN YAN UWANMU MATA KUMA MUKE GABATAR MUSU DA JAKUNKUNA DA TAKALMA HARMA DA TURARUKAN WUTA DANA SHAFAMA JIKINSU DON NISHADIN ZUCIYARSU DANA MAZAJENSU....*

*AFINTY QUEENS DISCOVER BLISS IN BEAUTY =؅?=د?*

*Address =?G?=?G?:*
*KU ZIYARCE MU A SHOP NO.9&10 SHEMA PLAZA,BEHIND SHEMA FILLING STATION KASUWAN BACCI KADUNA*
*TEL:08133379628.*

*MATAR MUTUM*
*NA MARYAM FAROUK (UMMU MAHEER*

*FIKRA WRITERS ASSOCIATION*

*LITTAFIN KUDI NE*
*PAY 500 A ASUSUN*
*7061838488*
*OPAY DIGITAL SERVICES*
*MARYAM FAROUK*
OR
*0709290797*
*ACCESS BANK*
*SE A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488*
*IDAN KATINE A DAUKI HOTONSA A TURA ZUWA LAMBAR SAMA VTU KUMA A TURA A 08142548705*

*Kuyi following dina a Arewabooks @Maryamfarouk01 inda zaku karanta wannan littafin tareda sauran littattafaina*
*NAGODE*

*BOOK 2*
*PAGE 1*


"Alhaji! Alhaji!! Alhaji!!!" Taratsi da kwaroroton Binta ya maido shi daga cikin duniyar tunanin daya lula. Ya yun?ura ya zauna da kyau yana cije baki saboda yanda bayansa ya ?age, baya iya dogon zama tun Hatsarin daya samu shekaru goma da suka wuce a hanyarsa ta zuwa Kaduna Jana'izar Alhaji Zakariyya Mahaifin Binta shikenan yake fama da Baya dukda iyakar bincike ance babu abinda ya samu bayan nasa amma kam yana ji a jikinsa ga kuma shekaru da suka mi?a wannan yana daga abinda yake ?ara ta'azzara masa ciwon.

"Alhaji lafiya kuwa? Nakusa minti goma tsaye akanka ina magana kayi shiru badan idonka a buWe yake bama ai Wauka zanyi ka mutu" Bintan ta sake faWa tana zama a gefensa. Ya tsura mata ido, ya rasa dalilin daya saka ranar Allah ba zata fito ta koma ba tareda Binta ta kawo zancen mutuwarsa ba, ya rasa meya tsare mata a duniya da take cike da burin taga ya kau.

"Kaci abinci ma kuwa? Koda yake la'asar sakaliya yaci ace kaci abincin rana ai" tayi tambaya kuma ta bawa kanta amsa tana tashi tsaye ta nufi firjin dake cikin Makeken Bedroom Winsa me kama da Turakar wani sarki. Ruwan gora ta Wauko da Kofin tangaran da suke jere a saman firjin ta dawo ta zauna tana tsiyaya masa data gama ta mi?a masa babu musu ya karba dan yana bu?atar ruwan.

"Ya kukayi to? An samu kuWin sun fito?" Ta jefa masa ainihin maganar data shigar da ita gurin nasa. Ya kurSe ruwan yana gyara zama yace
"Ba'a samu ba, yace besan inda suka shiga ba kuma na yarda Aminu baze yimun sata ba dan haka maganar ta ?are dukma wanda yayi sama da faWi dasu shida Allah kuma a sannu wata rana asirinsa ze tonu"

"Kace me? Miliyan dubu dari biyun harda Wori kake cewa kabar mutum da Allah akanta Lallai ma Alhaji, tsaya ma, yanzu kai har kana da bakinda zaka shaidi Aminu? Yaushe ka zauna dashi da har kasan halinsa da zakace bazeyi maka sata ba?" Binta tayi maganar a zabure. Alhaji Audu ya kalleta she?e?e yace

"Waini nawane kasonki cikin kuWin nan Binta da duk kika bi kika tashi hankalinki kamar ma kin fini damuwa da abinda ya faru?"

"Ni kuwa nake da kaso a ciki, karka manta Yara goma na ?yan?yashe maka a gidan nan ga Takwas nan a raye cikinsu kuma Zarata shida duk mazane kaga kuwa ni nake da Kaso a cikin dukiyarka kuma bazan zuba ido ina kallo a ringa damfararmu sannan kayi shiru kace ka bar mutum da Allah ba" ta bashi amsa tana kaWa jiki tareda juya ido kamar wata ?aramar yarinya, ya buWe baki ze bata amsa sallamar Momy ta dakatar dashi seya haWiye abinda yayi niyyar faWa Win ya amsa sallamar ta ?araso ciki hannunta Wauke da ?aton Try. Akan Centre table dake tsakiyar Wakin ba tareda ta nuna tasan da zaman Binta a gurin ba ta kalli Alhajin fuska babu yabo babu fallasa tace

"Ai bansan ka dawo ba seda nake nake cewa shiru kace kuma ba daWewa zakayi ba sannan Baba Bilki tace ai ko taji shigowarka tunWazun ta zata na sani shiyasa batayi mun magana ba" abincin ta shiga zubawa ta gama jere komai ta sauke kulolin daga kan Teburin sannan ta tura masa shi gabansa yanda zeji dadin cin Abincin. Wani ruwan ta sake dakkowa daga firji ta ajiye masa Binta dai kallonta take tana zare ido a ranta tana tunanin wai ya akayi ta gaza korar wannan sailubar matar har suke dosar shekaru Arba'in tare a matsayin Kishiyoyi?

"Bari nayi sallar La'asar se naci abincin" Alhaji Audu ya faWa kafin ya yun?ura ya shige banWakin dake manne da Wakin barcin nasa. Momy ta zauna kan doguwar kujera kwaya Waya dake cikin Wakin Hajiya kuma har sannna tana zaune kan gado tana ?arewa Momyn kallo kamae wata farin shigar Maita har Audu ya fito ya tada sallah ya idar ya hau kan abincinsa Binta na zaune ita kuma Momy bata ce mata ta fita ba dukda zaman nata ya Sata mata rai. Har a yanzu da shekaru suka mi?a tsakanin ita ko Rabi babu wadda ta isa ta shiga Turakar Alhajin a ranakun girkin Hajiya Binta amma ita ko a kwance suke tana iya faWo musu a yanzu ne kuma Alhaji Audun yake son ya gyara wannan barakar har yake ?o?arin taka mata burki wasu lokutan sedai a banza domin ta rigada ta raina shi, bashi da wani kwarjini ko Martaba a idonta da zw ce tayi abu tayi ko ya hanata ta hanu har ila yau kuma zancen tayi laifi ya mata faWa kamar yanda yake musu fa babu shi, ita lamarin Alhaji da Hajiya Binta ma har rasa matsayin da zata ajiye shi takeyi dan ko a labarai bata taSa cin karo da Macen da take zuba sharafi a gidan Auranta irin Hakiya Bintan ba.

"Ina kin gaka abinda ya kawoki?" Muryar Audu ta ratsa kunnuwansu, Momy na danna waya ta Wago so take ta fahimci dawa yake a cikinsu? Ita me girki ko kuwa Binta data zo ta tasasu gaba? Hamsha?iyar kuwa ?ara gyara zama tayo dan a tsammaninta da Aishar yake seda ya sake maimaita maganar yana kallon idonta kafin ta ankare, ta buWe baki zata faWa masa ba dadi se kuma ta gimtse data tuna tanada shirin da take so ta cimma seta mi?e tsaye tana murmushi tace

"Ai to bari naje, duk na shafa'a ne wlh se naga kamar a ?akina nake". Tana dafda fita daga Wakin wayar Momy tayi ?ara alamar shigowar kira, Hajiya ta fice amma ta coge a bakin ?ofa ta kasa kunne, abin ya rigada ya zame mata ?abi'a ko ace ciwo, gulma da LaSe, tsabar yanda ta Worawa kanta bala'i ko a hanya take tafe taji wasu na ?us?us seta dakata ta kasa kunne ko ba zataji ko ta fahimci abinda suke faWi ba, ga zargi da tsarguwa ko yayan cikinta taga suna magana seta tsargu da ita suke ko wani abun suke shiryawa.

A cikin Wakin kuwa a speaker Momy ta saka wayar saboda kunnenta dake mata ciwo kwana biyu bata kara wata a kunnen muryar Ahmad ta ratso wayar yana cewa
"Momy, kin masa maganar kuwa?"
"Tukunna dai, wai idan sauri kakeyi haka ka tareshi da kanka kayi masa maganar mana seni zaka mayar yar aikenka" ta bashi amsa. Daga waje Binta ta sake manna kunne a jikin ?ofa tunda taji muryar Ahmad da kuma cewar anyi magana wace maganace? Abinda take so kunnuwanta su zu?o mata kenan.

Ahmad ya sake marairaicewa Momy yana cewa
"Haba sweet mother, haba rabin raina kinsan dai bazan iya tunkararsa ba kuma na gaya miki Jafar ya masa magana yace he will get back to us yanzun kusan one month kenan bamuji komai daga gareshi ba and time is really against me Momy, idan baze samu ta hanyar sa ba na sani na nemi wani Alternative Win kinji Mamana? Ya ?arasa maganar kamar ze saka mata kuka yana idarwa kuma tari ya sar?e shi"

"Bakaje Asibitin da nace kaje ba kenan?" Ta jefa masa tambaya ba tareda tabi ta kan maganar da suka fara ba, Ahmad da tarin ya tsagaita masa yace
"Naje wlh Momy an rubutamun magani na ma farasha, kiyi masa maganar yanzu dan Allah kinji"

"Zanyi" ta faWa a ta?aice daga nan ta kashe wayar. Alh Audu na cin abincinsa kuma yana sauraron duk wayar da sukeyi tuni kuma ya fahimci zancen da tunin da Ahmad Win yake magiyar tayi masa. Ruwa yasha yana kallonta yace
"Shi baze iya zuwa ya sameni muyi magana ba se ya ringa turomun yan aike?"

"Wane shi? Wannan ai se Yayan gida Yayan So" ta bashi amsa hankalinta na kan wayarta se yayi shiru yana kallonta, a yan shekarun nan Aishar ta fara canzawa, idan tayi wani abun se yaga kamar ta fara gajiyawa dashi ne kamar me neman wani dalili da ze janyo saSani a tsakaninsu. Ajiyar rai yayi yace

"Ai shikenan, kice masa gobe ya sameni a gidan Gona na Kwanar Dawaki se mu tattauna maganar kuma yazo da takaddun"

"Baka da lambar wayarsa kaima kenan?" Ta faWa tana tsareshi da ido, tamke fuska yayi be kuma bata amsa ba ya shige banWaki wanko hannu.
Tayi tsaki a ranta wani abu me Waci yana taso mata seta mi?e ta shiga tattara kwanukan daya gama dasu ta Wora akan Try Win data kawo su ta fita. A bakin ?ofa sukayi kiciSus da Hajiya dake dakon jiran a faWi gundarin abinda take so taji bu?atar da Ahmad Win yake nema a gurin Alhajin da har yace ya sameshi a gidan Gona.

Kardai fa tufka take ta baya tana warwarewa tana nan tana ha?ilon ganin sun danne komai Aisha ta ringa mata zagon ?asa suna wawasa ita da Yayanta? Dole ta ?ara saka idanu kenan akan harkar shige da ficen gidan da duk abinda yake faruwa wannan maganar ma da ba'a ?arasa ba seta bi diddiginta tunda sunan Jafar ya fito a ciki shi zata tambaya dukda dai shegen Yaro ne ba lallai ya faWa mata ba tunda sirrin ubansa Ahmad ne. Tana ganin Momyn ta Wan diririce se kuma ta waske ta tura ?ofar irin dawowa ta sakeyi zata shiga. Momyn ta kaWa kai kawai ta wuce, ba yau Hajiyar ta sababa LaSe ya zame mata Wabi'a.

Hajiya na ganin Momy ta sauka ta juyo itama ta fice dan akwai abinda yake a gabanta yanzu kafin ta juya takan zancen Ahmad Win, Wakinta ta wuce ta tarar da YAKUBU na cin abinci, Hajiya ?arama na tsaye gaban console mirror dake falon tana gyara Waurin kallabinta. Ganinta yasaka Binta sakin fuska ta washe ha?waranta duka, guda biyu data sakawa Ha?orin Makka na zinari sunata ?yalli, Umarar Bara da sukaje ta cire Asalin guda daya na bakinta daya cinye aka saka mata biyun.

"Kinyi kyau uwar masu gida, yau zuciyar mahassada sedai ta buga dan ba?in ciki" Hajiyar ta faWa tana ?arasawa kusa da ita. Hajiya ?arama ta saki murmushi kafin ta shiga juyawa dan ta nunawa Hajiyar kwalliyarta dakyau, Fitted gown ce ta wani cotton London Brocade a jikinta dark blue me zanen flower sea green da fari a jiki, kudinsa ya tasamma dubu sittin, Jafar ne ya aikowa da Hajiyar su sun kai guda goma yace a Winka mata dogayen riguna saboda laushinsa yasan zeyi dadin sakawa shine Hajiya ?aramar ta kwashe uku dan tasan ba Winkawa Hajiyar zatayi ba ta kai aka mata lalatattun dinkuna a ciki wannan fitted gown din itace me Wan dama dama dan ta rufe mata jiki gaba daya illarta kawai shape dinta daya bayyana ?arara.

"Kin fa gama haWewa Yar nan babu makusa" Hajiyar ta sake faWa tana bata hannu suka kashe daidai nan wayarta tayi ?ara, sunan Abba Tee ya bayyana akan screen Win. Tsanar dadi harda wani ma?ale hannaye Hajiya tayi sama kamar Kangaroo bakin nan ko har ma?ogaronta ana hangowa, Hajiya ?arama ta amsa wayar cikin muryar shagwaSa kamar zata fashe da kuka tace

"Harka iso"
"Yes Babe, ina waje" ya bata amsa daga cikin wayar, ta sake narkewa tana cewa
"Baka shigo ciki ba? Issa baya nan ne? Kayi horn ze buWe maka Get ya shogar dakai palour kafin na fito"

"He isn't here, oh kamar gashi nan wani Buzu ko? ya buWe Get Win bari na shigo"
" Saurayin ya sake FaWa kafin ya katse wayar.

Hajiya ta sake bata hannu suka kashe tana cewa
"Wai, Allah ya taimakemu, maza kije ki ?ara turare, duba Wakina akwai wannan Disaina da kike nacin na baki na gurin Yayanki ki Wauka, bari na duba abincin idan sun kammala"

"An gama kumai har na shirya a Try kaowa kawai za'ayi" Inji Hajiya ?arama
"Yauwa yar gari, jeki to kar yayita zama Allah ya bada sa'a" cewar Binta. Hajiya ?arama ta wuce Waki ta ?aro turare kamar yanda Binta tace ta fito tana takun yau?i Albarkatun jikinta na motsawa danma kayan jikin nata sun matseta kam hakan ya rage musu samun damar rangaji yanda ya kamata.

Yanda Yaran Alhaji Audu Maza suke Dogaye ginannu idan ka cire Ahmad daya Wauki Jikin Aisha bashida ?iba sam haka beyi irin tsahonsu ba to Matan ma duk haka suke dogaye masu cikakken jiki, Allah ya taimake su da ?ira mai kyau ta jiki data fuska musamman da dukansu se akayi katari suka Wauko fuskar Dada, Farare tas Win cikinsu Amina, Aslmaiyya da Hajiya ?arama da yan Biyun Hajiya Rabi Baba Bilki takance kamanninsu kwabo da kwabo da Dadarsu.

"Yauwa, saura kuma ki sake maimaita abinda kikayi wancan karon kika saka yayi fushi, kina kallo dai har dubuta dari Turai ta damfareni, koda yake kwalliya ta biya kuWin sabulu tunda an janyoshi yazo, soyayyar nan ta zamani ke sekace ba wayayya ba da ita ake kama samarin nan, banda abinki waye ze kwasheki haka siWan ba tareda ya tabbatar kin iya kalar soyayyar da yake da bu?ata ba, yar rungumar nan da kis ne dai Allah na tuba ai ba wani abu bane, ban dai ce kije ki buWe kafa ba ki saka mu shiga uku kuma kuyi a hankali Alhaji ma sama ze iya saukowa kowan...."

"Hajiya!" YAKUBU da ke cin abincinsa tun shigarta be tanka maganar da sukeyi ba ya kira sunanta cikin Waga murya me kama da tsawa dan a firgice daga ita har Hajiya ?aramar suka kalleta kowacce na tsammanin da ita yake. Farantin gabansa ya ture ya mi?e tsaye fuskar sa tamkar zatayi aman bacin ran daya turnu?eshi lokaci daya.

Ya nuna Hafsatu da yatsa yana cewa
"Ashe abinda ake faWa akanki gaskiya ne? Iskancin da aka ce kinayi dagaskene saboda kin shahara yanzu har cikin gidan ubanki kika kawo saurayi zakuyi iskanci?" Kai ta shiga girgiza masa tanaja baya domin Yakubu bashida daWi, ba su ba uwar data haifeshi ma shakkarsa takeyi dan Lamarinsa me girma ne. Hajiya Binta ta dake tana hararar sa tace

"Kai bana son Wiban Albarka, a gidan uwar masu faWar aka ganta tana iskancin? Koda uban wani tayi a cikinsu da har suke bayar da shaida? Bakaji me nake faWa bane? Ce mata nake fa ta saki jiki dashi ita ai gida huma ce duk samarin da kake gani suna zuwa suna tafiya ai ?in basu fuska takeyi shi yake korarsu. Shifa wannan Win in gaya maka, Yaron Alhaji Mudi Tanko ne tsohon Senet piresiden kuma yanzu haka takarar gwamna yake a Garinsu, can kwanaki bana muku zancen sa ba har yazo sau Waya shine ya tafi be sake dawowa ba? Ai in gaya maka wannan shashashar yarinyar ce ta kusa kwafsa mana, wai fa Waukarta yayi sukaje Otal ya kama ?aki, daga cewa su shiga ciki shikenan ta gudo wai har da ce masa ita ba yar iska bace se kace yace mata wata tsiyar ze mata idan suka shiga. Shiko yayi fushi ya tafi, dakyar fa yanzu seda na baiwa Turai dubu Wari ta kaiwa Malaminta akayi aiki akansa shine fa ya zo yanzu, faWan da nake mata kenan kar a maimaita ta wnacan karon a samu a kamashi a hannu ya fito ayi zancen Auren nan masu yi mun dariya su sha kunya suji da ?aryar sarauta suzo suga Arzi?i a inda yake dan duk na samu labarim gidansu ba ?aramar wada?a ubansu yakeyi idan ya tashi Aurar da Yara ba".
Yanda take maganar hankali kwance tamkar me faWar wani abin Arzi?i, Yakubu yayi sakato yana kallonta a ransa kuwa kokwanto yakeyi akan Hajiyar ce ta haifi Hafsatu ko kuwa Ri?onta takeyi?

Anya uwa zata yiwa yarta irin wannan huWubar kuwa?
"Zatayi mana, mussamman uwa irin taku da take bautawa duniya da abinda yake cikinta" zuciyarsa ta bashi amsa. Seya ja numfashi ya furzar kafin ya zabura ya nufi ?ofa, cikin Hajiya ?arama ya kaWa, Hajiya kuwa yatsine fuska tayi tace

"Ke da Allah rabu dashi, ance masa bansan duk abinda sukeyi bane su? Duk fa haka suke lallatse yammatan suma suna basu kuWi balle ke da Aurenki ma zeyi jeki abinki manta dashi kar kuma ko manta uar soyayyar nan da ake nunawa a fim irinta zaki masa kinji ki hargitsa masa tunani yayi maza maza ya turo azo ayi magana kar zancen Auran Aslamiyya ya riga naki tashi".

A saluSe Hafsan ta fita duk karsashin da take dashi ya barta. A ?ofar fita daga ainahin cikin gidan taci karo da Ali Daya daga cikin Ma'aikatan gidan me kula da shuke shuke, da gudu ya taho badan ta matsa masa ba da tuni yayi tafiyar gari da ita.

"Yawwa Hajiya kiyi sauri, ga Alhaji Yakubu can yana dukan ba?onki" ya faWa yana haki. ?irji ta dafe tana zaro ido daga inda take kuma tana iya jiyo ihun kukan data tabbatar na Abba Tee ne da kuma hargowar Yakubu yana faWin
"Daga yau ka sake zuwa wani gida ka yi iskanci da ?anwar wasu". Da gudu ta juya ciki tana kuka tana kiran Hajiya. Binta nacan tana gyara zaman kofunan da za'a kaiwa Ba?on tana kwararaqa me aikinta Ashar akan wai bata goge su dakyau ba so take yace musu ?azamai sega Hafsa na kuka jage jage, bata ko iya sauraronta gaba daya ba tayi waje cikin tashin hankali tana

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login