Showing 243001 words to 246000 words out of 467220 words

Chapter 82 - MATAR MUTUM COMPLETED 1-3 BY MARYAM FARUK.doc

23 Sep 2025

12213

amsa cikin yanayin irin kamar ya dameta, ya maida wayarsa yana cewa
"Wahala kike kira akan abinda ya shafeki? Idan ban hidimta miki ba neman da nakeyi bashi da amfani kenan. Nifa a rayuwata inajin daWi kawai na kyautatawa mutum koda baze gode mun ba"

Lafazinsa na ?arshe se taji kamar magana ya faWa mata ta sake cukulewa bata ce komai ba. Ya waiwaya ya kalli hanya kafin ya ciro wayarsa ya shiga kiran Jay ganin kusan minti nawa shiru babu shi babu labarinsa. A lokacin Jay nata sharara gudu a titi beji kiran ba, sau biyu ya kirashi be amsa ba ya ha?ura ya kalleta ganin tana dafe kai ya saka cikin kulawa yace mata
"Ya dai, meya faru kike ri?e kai?"
"Ciwo yakeyi mun yanzu ina tsayen nan naji ya sara" ta bashi amsa tana yatsina kamar gaske nan nan kuwa yace
"Ciwo kuma har yanzu be dena ba amma kika cemun kin warke kin sha magani?"

"Nasha kuma ya dena yanzu ne kawai ya dawo kodan na daWe a tsaye ne ban sani ba" ta faWa tana wani sake ri?e kan da hannu biyu. Burinta ya cika dan kuwa sannu ya shiga jero mata yana cewa ko zasuje Asibiti, tace
"Nafa gaya maka an bani magani daman Dr yace na dena yawan tsayuwa da shiga haske sosai su suke tayar mun da ciwon". Ya kalleta kamar me tantamar abinda ta faWa amma yace

"Shikenan ki shiga ciki, bari na sake trying number Jafar idan yazo se ki le?o ku gaisa ko yayane dan Allah kinga babu daWi ace yazo kuma baku haWu ba"
"Tam" ta bashi amsa tana ?o?arin juyawa ciki Baffa ya iso gurin, yanda kasan wanda yaga wani da suke wasa Suya haka ya sauke ido ?asa ya kasa kallon Ahmad shi kuma cikin girmamaqar daya saba yi masa ya dur?usa ya shiga gaishe shi ya wuce ciki ya barsu a tsaye.

"Kinga yau kuma Baffah surukuta yakeyi dani daga fara maganar auranmu dukda ma yace a bashi sati huWu zeyi musu magana" Ahmad ya faWa bayan da Baffah ya shige ciki, batace masa kamai ba se dafe dafenkai da yamutsar data cigaba da yi hakan ya tuna masa da ciwon da tace yana mata yace ta shiga gida ta wuce har sannan dafe da kai yana binta da sannu. Seda ta shige kafin ya sake ciro waya ya shiga kiran Jay a sannan kuma aka ce masa Call waiting tana dab da tsinkewa ya Waga muryarsa tamkar wanda yake maye ko cikin wani shau?i yace
"I'm sorry Yah Ahmad kuka ta saka mun ni kuma banma san yanda akayi ba kawai na ganni a ?ofar gidansu".

Ahmad ya buWe baki kamar yana gabansa yace
"Tafiya kayi, kuma kake cemun baka san yanda akayi ka ganka a gidansu ba ko saboda ka raina wayo ai shikenan ita kuma motar tana ina toh?"
"I'm coming back to pick you" Jay ya sake faWa da muryar da tafi ta farko zama wata iri, Ahmad yace
"Zan hau Napep, and abinda zance maka kaji tsoron Allah kabar koma menene kake aikatawa a inda kake"
"Thanks" Jay ya amsa shi kafin ya katse wayar ya bar Ahmad da waya a kunne cikin mamaki. Wato saurin da yakeyi kenan so yake yaje ya taSa yar mutane, kenan Jafar be bar halayyarsa ba har akan macen da yake i?irarin yana so ze aureta seya gwada mummunar Wabi'arsa kenan? Tunanin daya ringa masa yawo akai.

Ya aje wayar cikin rashin jin daWin abin ga ciwon kan daya tasowa Fatima a gefe duk suka dagula masa lissafi suka kore farin cikin daya ke ciki a daren. Titi ya fita ya tare Adaidaita da ze kaishi gida, da ace yasan gidan su Budurwar Jafar Win can zeje da ace kuma ya san abinda zeje aikatawa kenan da be barshi ya tafi shi kaWai ba, dole ma ya kaiwa Baba Al?ali ?arar Jay akan ire iren abubuwan nan da yake aikatawa, idan aure yake so yayi kawai ?ila ya shiga hankalinsa ya dena wannan shirmen.

A Sangaren Jay kuwa tafiya ya ringayi a motar ba tareda yasan inda ya nufa ba, seda yayi tafiya me nisa ya bi titin bypass kamar me shirin tafiya Bechi a daren seda ya wuce guraren cunkoson mutane kafin ya samu gefen titi ya gangara ya tsaya ba tareda ya kashe motar ba yayi parking kawai ya kwantar da kansa akan steery. Ya kasa relating abu, Fatiman Yah Ahmad itace Afeeyarsa, Afeeyarsa ita ce Fatiman Yah Ahmad a garin yaya? Ya akayi haka ta faru? Tunani ya shigayi na haWuwarsa da Afeeyah har zuwa yau, babu wata kafa ko siga da zata saka ya zargi wani abu akanta, babu abinda be sani akanta ba amma koda wasa zuciyarsa bata taSa kwatanta cewar zata iya zama ita ce Fatiman Yah Ahmad ba, abinda yake so ya fahimta yanzu shin Coincidence ne ko kuma Set up plan?

Arashine ko ita ta shirya komai ta haWa soyayyarsa data ?an uwansa mafi soyuwa a gareshi guri Waya? Idan shiri ne menene ribarta akanyin haka? Me suka mata data zaSi hukunta zukatansu da hukunci mafi muni irin wannan?
Yana bu?atar sanin amsar waWannan tambayoyin kafin sanin abin da zeyi a gaba.

Wani abu yakeji a zuciyarsa, ya zarce ya ce zafi yakeji ko ciwo koma menene besan me ze kirashi ba. Ta yaya za'ayi suyi tarayya cikin Son abu Waya shida Yah Ahmad? Tilas wannan ya kasan ce shiri dukda ya sani Allah babu yanda baya sanya Al'amura su kasance amma yana da ya?inin ubangiji baze tagayyara zumunchin da yake tsakaninsa da Yah Ahmad.

Ya saka hannun akan fuskarsa yana goge danshin dayaji yana bin kuncinsa, shi kansa yayi mamakin kansa Hawaye ne wanda fitarsa ke cakuWe da dalilai da yawa, Allah ya sani be taSa jin son wata Mace a duniya irin yanda yakeji akan yarinyar nan ba, zuwansa Kaduna gurin Anty Ummu Yayar Hajiya Binta yaje saboda a kaf dangin mahaifiyarsa ita kaWaice yake da tabbacin zata iya tarar gaban Hajiyar ta feWe mata gaskiya komai Wacinta kuma itace yake da ya?inin zata bashi goyon baya akan auran Afeeyah. Hajiya Ummu ta goyi bayansa dukda ta jinjina Al'amarin domin burin Hajiya sananne ne ga kowa akan sa. Kowa yasan tanadin da take dashi akan Matar auransa. Ita kanta Hajiya Ummun yarta Samiha ta soshi kuma da ace yana da ra'ayin auran Zumunchi daya auri Samiha kodan Anty Ummun amma haka Hajiya ta shafawa idonta kwalli ta manta cewar Ummu ce ta saki Nono ta kama a gaban kowa tace me uban Samiha yake dashi da zata haWa surukuta da yarsa?

Abinda Anty Ummu ta fara masa bayan daya mata bayanin komai tace "Allah ne ya kama Binta, burin data ci akanka baze zamo gaskiya ba, kanaji ko Jafar idan har kana son wannan yarinyar kar kaji komai kar kuma wani abu ya baka tsoro ka tafi kanka tsaye ka nemi auranta. Karka bi takan Binta ko Mahaifinku domin bakin ganga ne se yanda ta kaWashi ka tafi kai tsaye ka samu Al?ali nasan in sha Allahu zeyiwa duk wata Saraka da ka iya tasowa togaciya tunda wuri, kuskuren da Ahmad yayi kenan amma tunda Al?ali ya karSi maganar wa ka sake jin yace wani abu akai?"

"Amma Mama Ina tsoron Abinda Hajiya zata yi idan taji maganar nan daga baya shiyasa nake tunanin ki fara sanar mata a lallaSata harta amince da kanta sannan" Jay ya faWa, Hajiya Ummu tace
"Jafar kenan, shawara dai kake nema a gurin kuma na baka, wlh tallahi badai Bintar dana sani ce zata amince da maganar nan da kazo da ita ba, tunda dai ba abune daya saSawa shari'a kake shirin aikatawa ba magana ce ta aure, idan kuma daman ba son yarinyar kakeyi ba to kaitsaye ka janye kawai karma ka janyo wani abin kace nace ka jawowa yarinya suna zaune lafiya da iyayenta Jarabar Binta ta dirar musu, kaje ka samu Al?ali shi ze san duk ta yanda ze biyowa abun" Abinda Hajiya Ummu ta gaya masa kenan, Daya sake nuna mata hoton Afeeyah data bu?ata bayan ta gani tace masa

"Niko kamar nasan fuskar nan a wani guri" a lokacin yace mata
"Nafa tura miki hotonta kwanaki can Mama" ya faWa seta jijjiga kai tace
"Tabbas na tuna, gata tabarakalla, Allah yasa yanda take da kyaun fuska haka zuciyarta take" nana suka ?ar?are daita bayan ta sake jaddada masa yaje ya samu Baba Al?ali kaitsaye kar yabi ta kan Hajiyarsu, daga can ya wuce Abuja gidan Hafsatu kashe tata wutar, maganganun data zayyana masa na kalar zaman da takeyi da Abban se yaji ashe ko rabi Hajiya bata sani ba, ta bashi tausayi matu?a duk son zuciyar Hajiya nata suka ja mata, samarin Arzi?i tayi su amma ita da uwarta suka raina musu Ajawali, shi shafaffe da mai da yayi daidai da ra'ayinsu gashi nan tun ba'aje ko ina ba tana kuka da data sanin auransa, gara Hajiya raba ba?in cikin akeyi da ita, ita da take zaune dashi take kwasar kashinta a hannu ita take da abin faWa. Daya tariyo gidan Naziru, da matarsa ta rufin asiri gashi nan ya tattago matar Jaraba irin wadda Hajiyar take so shi kuma tana gasa masa Aya a hannu, Yakubu ma dai sammakal wata yar gidan da Tarbiyya bata wadata ba ya kwaso yar masu kuWi yan boko ranar nan yana ji suka kwaso rigima wai bata iya sallah ba daga ya mata magana yace a gidan ba'a sakata Islamiyyah ba ta kira Babanta tana kuka tace ya zage shi tas yace musu kafirai uban yazo yayi tijara a tsakar gidan Alhaji Audu akayi sa'a dai baya nan Hajiyar ce ta fita tana bashi ha?uri duk suna Waki suka ?i fita to irin auran da take so yayi shima kenan.

Bayan ya dawo ya ciza ya busa yaga dai shawarar Hajiya Ummu wadda kuma daman usulun abinda zuciyarsa ta ayyana masa kenan a matsayin mafita tilas ya aiwatar da hakan shine yaje ya samu Baba Al?ali Wazun ya zayyane masa komai yace kuma ya kwantar da hankaliynsa ya tambayeshi ina ne gidansu yarinyar yace zeje yau ya karSo full Address da sunan Mahaifinta akan haka suka rabu. Dalilinsa na Soyewa Ahmad komai akanta kuma kawai yana jin nauyin abubuwan daya masa akan Fatima, irin izgilancin daya masa na cewar ya rasa Macen da zeso a duniya se yar bakanike, duk matan da suke sonsa isassu bega matar aure ba se ita abin haushin ma tana wahalar dashi se gashi shima ya ?are da faWawa tarkon yar Talaka li?is da yake ganin kamar ma Mahaifin Fatiman Yah Ahmad Win zefi nata wadata, wannan tasa ya yanke hukuncin su tafi tare, yaga komai da idonsa idan yaso daga baya su tattauna domin yasan Yah Ahmad bazeyi judging nasa ba kamar yanda shi ya masa

Ashe shine babban gara a cikin wasan, shi yar bakanike ta Wanawa mugun tarko ta kamashi kuma yanda ya kamata tayi wasa da hankalinsa. Abubuwa da yawa ne cikin al'amarin, ze tabbatar da Allah ne ya kama Hajiyarsa dashi kansa dumu dumu, rainin arzi?in da yayi musu ubangiji ya tabbatar masa da ba nan take ba, ba rashin wayon Ahmad bane ya saka soyayyarta tayi galaba akansa haka duk izza da jiji da kansa gashi nan ta haushi ta tattakeshi son ranta sannan Tozarcin da Hajiyarsa ta so yiwa Ahmad ne yayi waiwayi ya diro akansa, ina zata tsoma ranta da wannan abin kunyar idan taji labarin yar bakaniken data rainawa Ajawali tayi wasa da Zuciya da ?wa?walwar Jay da take ganin kaf zuri'ar Audu Bechi babu yashi?.

Daga can gefe gaba kaWan da inda Jay yayi parking Matasa guda uku suna zaune akan Benci suna cin gyaWa. Gida daga cikinsu yace
"Waccen motar tafi minti Ashirin a tsaye anan kuma a kunne", na kusa dashi ya keSe baki kamar wata mace yace
"Kai da ganin motar ai kasan lalatattun Yayan masu kuWin nan ne baze wuce budurwa ya Wakko yazo nan yana lalubeta ba, yar iskar saboda ma bata da daraja a gunsa baze iya kama mata hotel ba a mota ze latse ta" yanda yake maganar seka rantse da Allah a idonsa yaga ana abinda yake faWar, na farko daya fara magana ya cafe yana cewa

"Kuma fa haka ne, wlh yanzu haka shegun suke daman indai kaga mota da dare me ba?in gilashi an zuge shi tsaf kuma motar a kunne to wlh Iskanci sukeyi".

Na ?arshen da tunda suka fara maganar saka musu baki ba se sannan yace
"Haba Lawan, me yasa ba zaku kyautatawa mutane zato ba? Yanzu idan ranar lahira aka tsayar dakai ta yaya zaka kare kanka akan wannan shaidar daka bayar tamkar ya faru a gabanka? Me yasa a koda yaushe zuciyoyinku suke hasaso sharri a maimakon Alkhairi a kusa? Ba ku tunanin lalura ce ta tsayar da me motar nan? Ta yuwu kiran waya ne ya shigo masa shiyasa ya tsaya dan ya amsa domin yafi Alkhairi akan ya ringa tu?i yana amsa waya.." Wanda ya kira da Lawan ya katse shi yana cewa

"Ji wannan Bashir Win wace irin wayace sama da minti ashirin kuma ya bar mota a kunne se kace a gidansu ake siyar da mai?"

"Kai kuma me wannan motar ne zaka yi tunanin mai ze zama matsalarsa kalleta fa ni banma san sunanta ba" Wanda ya fara takalo maganar ya bashi amsa, Bashir yayi murmushi yace

"To sa ace ba waya yakeyi ba idan kuma lalurace fa wani abu ne ya same shi a cikin motar?"

"Kamar yaya?" Lawan da Idris suka haWa baki gurin tambayarsa, Bashir yace
"Kwanaki naji labarin wata mata kamar haka tana tafiya a mota ta gangara gefen titi ta tsaya tun mutane basu damu da tsayuwarta ba har dai suka fara tunanin wani abu ana duba motar aka tarar ashe Allah ya mata rasuwa tana kwance kan sitiyari" Lawan ya zabura ya tashi hannu akai yana cewa

"Innalillahi muje mu duba kar gobe mu zama mu zamu bada labarin a radio" ya durfafi motar Jay Idris na take masa baya sannan Bashir. Sau biyu suka ?wan?wasa masa glass, seda ya goge fuskarsa da Tissue idanunsa sun kaWa sunyi jajir kafin ya zuge glass Win gefen da yake gaba Waya ta yanda suna iya hangen gefensa zuwa bayan motar. Bashir ya masa sallama kafin yace
"Afuwan ranka ya daWe munga kana tsaye ne tun Wazu shine mukayi zaton ko ba lafiya ba"

Murmushi Jay yayi yace
"Lafiya lau, nagode da kulawa"
"Kai wannan ai Jay ne" Idris ya faWa cikin ?araji tuni kuma Jay yaja motarsa ya bar gurin Idris da Lawan suka haukace suna cizon yatsa, Jay ne a gurin sama da minti ashirin amma basu sani ba
"Kai amma fa naga idonsa sunyi Jaa, kodai shaye shaye yake a motar?" Lawan da be daddaraba ya sake faWa.

Ahmad ya kasa zaune ya kasa tsaye a bakin Gate yana jiran dawowar Jay, baze barshi ba yau se ya masa kaca kaca , yana nan zaune bayan ya kira Fatima tace masa kan da sau?i sega motar da suka fita da ita ta kunno kai, yanda yake tu?i ya sake fusata Ahmad dan da gudu ya shiga gidan tamkar me wasan mota. Jay be lura da Ahmad ba dan haka yana kashe motar ya fito yana rangaji ya nufi bangarensu, a daidai barander Alhaji Audu juwa ta kwasheshi kamar wanda iska ta buge se ganinsa sukayi yif ya faWi a ?asa Ahmad daya taho a fusace se gashi yayi kansa da gudu cikin tashin hankali, kardai kuma shaye shaye Jay ya fara be sani ba? Tambayar da yakeyiwa kansa.

*MATAR MUTUM*
*NA MARYAM FAROUK (UMMU MAHEER*

*FIKRA WRITERS ASSOCIATION*

*LITTAFIN KUDI NE*
*PAY 500 A ASUSUN*
*7061838488*
*OPAY DIGITAL SERVICES*
*MARYAM FAROUK*
OR
*0709290797*
*ACCESS BANK*
*SE A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488*
*IDAN KATINE A DAUKI HOTONSA A TURA ZUWA LAMBAR SAMA VTU KUMA A TURA A 08142548705*

*Kuyi following dina a Arewabooks @Maryamfarouk01 inda zaku karanta wannan littafin tareda sauran littattafaina*
*NAGODE*

*BOOK 2*
*PAGE 23*
"I'm fine, i just missed a step" Jafar daya yun?ura ya tashi da taimakon Ahmad ya faWa. Ko kusa Ahmad be kama zancen wai lafiya yake ba domin idanunsa sun ?aryata hakan sannan damuwa ta nuna Saro Saro akan fuskarsa dukda a lokacin be karanci yanayin nasa a matsayin damuwa ba, to wace damuwa ce haka zata samu Jafar. Yana ri?e da hannunsa kamar yaro gudun karya sake faWuwa su ka kai Waki duk yanda Jafar ke ce masa ya barshi ze iya tafiya be saurara ba. Ahmad yayi mamakin da Alhaji be le?o ba duk salatin da ma'aikatan gidan suka ringayi kuma yana zaune a falo ya tabbatar ma ya hango me yake faruwa dan a buWe ?ofar take, Jay ya kwanta akan gado tareda juyawa Ahmad baya, gani yake idan suka cigaba da haWa ido ze karanto abinda yake ?o?arin dannewa ba kuma ya so ya fahimta.

"Meya sameka Jafar? What did you take?" Ahmad dake tsaye akansa ya tambayeshi, Jay ya juyo, kafin ya kai ga bashi amsa aka banko ?ofa, tashin muryar da sukajiyo gabanin buWe ?ofar yasa suka gane wacece
"La'ilaha illallahu shikenan magauta sunyi nasara akaina na shiga uku ni Binta na lalace jifa ya tarar da Jafaru" ta faWa hannaye biyu dafe da kai tana jijjiga. Jay ya tashi zaune Ahmad kuma ya matsa gefe can ya jingina da bango yana kallon Hajiya seta kuma juya a fusace kansa tana cewa

"Aniyarka ta bika wallahi tallahi duk wani mugun abu ya ?are akanka, wato ka ?unsheshi a Waki kana jira ya mutu seka fito dashi ko?"

"Haba Hajiya wai meye haka kikeyi? Wace irin magana kike haka dan Allah?" Jafar ya katseta cikin Wacin rai, ko wane munafuki ne yaje ya gaya mata se Allah, salon tazo ta ?ara masa damuwa kan wadda yake ciki. Hajiya ta juya kansa tana cewa

"Banza sallamamme dabe san ciwon kansa ba, wato ya tattareka ya kaika ta yuwu ma tuni ya sadaukar da kurwarka shine yau ya kai musu kai su lashe, to billahillazi kurwarka Waci ne da ita ba zata ciwo ba sedai ya musanya musu data tsohon ubanku da dama yaci yanzu ya matsa ya bar mutane su sarara, taso muje ai inada sauran Tazargade da tsakin kuka yanzu zan turara maka su koma wane shegen maye yayi gigin taSaka sedai ya cinye kurwarsa wlh" ta matsa ta shiga janyo ?afafunsa kamar wani yaro ?arami. Da iyakar ?arfinta take

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login