Showing 255001 words to 258000 words out of 467220 words

Chapter 86 - MATAR MUTUM COMPLETED 1-3 BY MARYAM FARUK.doc

23 Sep 2025

12145

hannun yaro, lefe gangariya suke haWawa suma Ahmad ya saki bakin Aljihu sosai suna abinda ya dace tun bayan daya tabbatar da Alhaji ze basu gidaje wanda seda akayi ?warbai da Hajiya Binta Al?ali yazo har gida yayi mata cin mutinci kafinaka samu magana ta mutu. Tun bayan daya wa Alhaji Audun zancen ya bawa Ahamd gida lokacinma maganar Jay bata tashi ba bece masa komai ba, ana kai KuWin auran Jay Hajiyar ta shiga ta fita akan ai se Alhaji ya bashi gida dukda dai ba zama zeyi ba amma ya zama idan yazo yana da muhallin da ze sauka da iyalansa. Ta kwarkwanceshi tas kamar kuma yanda aka saba yabi ta tatan yace Naziru ya duba masa duk gidan da yayi ya shiga ya zauna labari na isa kunnen Al?ali ya wanko ?afa yazk har gida yayiwa Audun tatas yace

"Wato ana zatonkura tayi lafiya ashe kama kan bakanka na nuna banbanci a tsakanin Yayan cikinka ko Audu? Shi Ahmad Agolansa Aisha ta kawo maka da tunda mukayi maganar gidansa da kai baka ce komai ba se ?an da Binta ta haifa shi ne cikakken ?a a gurinka da zakayi masa abinda ya dace uba yayi? To ahir Winka, karka kuskura ka lalata tsaftatacciyar Ala?ar da ita kaWai tayi saura a gidanka, karka janyo abinda ze kawo rabuwar kai tsakanin Ahmad da Jafar, karka yarda Ahmad ya fara tunanin ka faifita Jafar akansa domin muddin ya juya maka baya ba zakaji daWi ba, duk wata sa'ida da salama da kake ji a cikin gidan nan yanzu dalilin yaron nan ne, shi yakw faWi tashi gurin ganin gidanka ya saitu to wlh karka bari komai ya lalace".



"To ai uwarsa tace ya fara gini har ya kusa kammalawa sun siyi fili shida ?an uwan nasa ya fara gina nasa tunda shi wancan ba shiga ciki zeyi yanzu ba" Alhaji Audu ya faWa tamkar duk beji kashedin da Al?ali yayi masa ba. Cikin takaici Al?ali yace
"Ai saboda shi ba me matacciyar zuciya bane kuma be dogara da kowa ba shiyasa ya tsaya da ?afafunsa yake abubuwansa da guminsa, to a matsayinka na ubansa nace ka kira Ahmad ka bashi damar ya zaSi duk gidan da yayi masa daga jerin gidajenkana Kano ko duk State Win da yayi ra'ayi se ya zaSa sa'annan ka baiwa Jafar dama shima ya Wauka dominAhmad na gaba dashi, umarni ne ba shawara ba idan kuma ban isa ba se in sani" yana gama faWar haka ya tafi abinsa dake da sauran burbuWin girma da mutunchinsa da yake gani se kuwa gashi yaji maganar.



Washe gari ya cewa Ahmad yaje bayan Sufi mart, da akwai gidaje da aka gina an gama komai abinda ya saura ba shida yawa, fentin katangar waje ne se saka kayan wuta wanda komai yana nan a ajiye daman. Gidaje ne gida biyu aka gina masa su, gini badai gini ba, duk sanda ya zagaya yaga gidan nan har wani nishaWi yake ji a ransa se yaji kamar ya samo wata yar shawalwalar yarinya ya cike ta huWu da ita ya samu inda ze ringa zuwa yana hutawa da kayaniyar duniya shine fa da Hajiya ta samu labari ta ringa tashin hankali tana tijata akan me za'a bawa Ahmad gida kuma wannan gidan da ita da yayanta duk bin ?wa?w?wafinsu basu san dasu ba ba'a isa ba ta ringa rashin mutunchi shi kuma Alhajin kamar wanda ta Waurewa baki ya gagara cewa komai be dai ce ya fasa kyautar ba kuma bece ba haka ba da abu ya?i ci ya?i cinyewa Hajiya Rabi ta kora Hajiya Balaraba a waya ta ce dan Allah ta cewa Al?ali yazo gidansu babu lafiya saboda Hajiyar shiga tayi har falon Momy tana zaginta tana cewa seta warware tsafin da taje tayi daya saka Alhaji yake Waukar abubuwansa masu Daraja ba tareda shawara da kowa ba ya mallakawa Ahmad.

Abinda be taSa faruwa ba se gashi Momyn ta biye mata suna faWi in faWa Hajiya har tana cewa zata daketa tace da rabon idan batayi kwanan Kabari ba yau zatayi na Asibiti idan kuma tana musu ta gwada kai hannu jikinta. Muryoyinsu har Baban Compound ga Alhaji baya nan babu kuma wani takamaiman tsayayyen Namiji da ze iya tsawatar musu seda Al?ali yazo ya tarasu yaji ba'asi nan ya buWrwa Binta wuta ya mata kaca kaca yace tunda Ake fifita Yayanta ana musu abubuwa waya taSa Waga ido ya kalla se itace da hassada ta cikawa zuciya bata da burin sedai ita ko Yayanta su mori Audu shine yasa zatazo tana tada masifa akan dukiyar da ba ta ta ba
"Amma ubane sila" ta faWi abinda ta saba duk sanda aka sako zancen dukiyar Audu. Al?ali yace

"Allah ne ya bashi ubanki ne sila amma da guminsa ya tattalata harta kai haka ko kuwa taki ya ringa zubawa abinda uban naki ya bashi yayi ta yaWo yana ?ara yawa? Ke matsalata dake bama mutum ya tsaya yana magana dake ba ba fahimta zakiyi ba dan kin rigada kinci kai inyi miki ta yan zamani, to wlh ko ki bari hankali ya kwanta ko kuma ayi tashin hankalin na gaske. Yakubu, Zakariyyah da Naziru duk se sun fita daga gidajen da suke zaune tunda na Audu ne na sani sarai domin koda sakarai ne amma be manta ni ?an uwansa bane baya Soye mun komai daya ke ciki, su fita idan yaso ku jira idan ya mutu aka raba gado kowa seya amfana da rabonsa" ya mata fes ta fita tana kuka sannan ya juya kan Momy itama ya mata faWan biyewa Hajiya.

"?ureni tayi, amma nayi nadama kuma bazan sake ba in sha Allahu" ta faWa ya sallameta ya tafi shikenan magana ta mutu amma Binta bata ha?ura ba har seda aka bawa Jafar gidan da yake jere dana Ahmad Win dan dama guda biyu ne dukda sun rigada sun zaSar masa wani katafare a cikin Nasarawa GRA wanda ya shallake zaman Matashi me mace Waya dai Mansion ne dan?arere har an canza takardu shikenan Jay ya ci tudu biyu abinsa. Da taso mugunta se cewa tayi wai gidajen sun zarce ya basu kyautarsu sedai Aro shida Jafar Win duk wanda yake so ya mallaki nasa ya ringa biyansa a hankali dan baze yuwu ya ringa kwashe kadarorinsa yana kyauta dasu ba babu Adalci tunda beyiwa sauran Yayan ba yace mata Toh.

Kwanaki na tafiya sati na wucewa a kace duk abinda aka sakawa rana ze zo se gashi anci watanni uku lokaci yayi su Fatima sun kammala makaranta wanda kuma yayi daidai da wata uku kenan saura kwanakin auransu da aka saka. Zuwa sannan za'ace an samu cigaba sosai tsakaninta da Ahmad domin tayi surrender, takanyi iyakar yinta gurin kwatanta bashi kulawar da ya kamata ace ya samu a gurinta. Dukda cewar Ahmad Win bana da bane domin shima ya canza, ya rage rawar jiki akanta ya koyi kamewa da jan aji. Wannan lako lakon da maida kansa kamar wani sakarai da yakeyi mata ya dena, a yanzu idan ya kirata ta bashi uzurin tana wani abu ze barta amma fa baze sake kiranta ba har se idan ita da kanta ta kirashi sannan zasu cigaba da abinda suke kai. Sannan yawan zuwa gidansu akai akai da yakeyi a baya shima ya dena, koda ta dawo gida a yayi ?o?ari jaye sau biyu cikin sati, tun abin baya damunta harya fara ci mata rai ga kwanakin aure suna matsowa tunani takeyi karfa ace lambo lambo Ahmad ya mata a baya, yanzu da ya tabbataemr da zata zama tasa shine ze fara fito mata da true color nasa idan ya zamana bayan sunyi aure yace ze rama irin cin kashin data masa tsayin shekaru uku ai ta shiga uku ta lalace bata hango inda zata tsoma kanta taji sanyi ba.

Har Badar tayiwa maganar akan sauyin Ahmad
"Badar tsoro nakeji kar ya ?ullaceni jira yakeyi daman ya samu damar da ze rama abinda na masa a baya"

"Haba dai ni nasan Ahmad mutum ne me kyakykyawar zuciya baze taSa kwatanta rama sharri da sharri ba, kawai dai nasan ya fahimci keWin zuma ce seda wuta saboda idan ya Wauke miki ai kina shiga taitayinki ki nemoshi kuma gara ya fara shata miki layi karki zata idan kukayi aure haka zakije ki cigaba da masa shirmen da kika saba gara ki sani da da yanzu akwai banbanci Mijinki yake shirin zama na random saurayi da kika sani a baya ba, amma wlh da ace ma da gaske tama ki yakeyi da naji daWi domin kin azabtar da bawan Allahn nan koda yake Allahnsa ya rama masa kiyi addu'a Allah yasa abin ya tsaya iyakar haka" amsar da Badar ta bata kenan.

Biki ya rage sauran sati huWu aka kai lefe kowanne gefe, na Jafar aka fara kaiwa Akwati iyakar ganinka gasu nan sha?e da kaya saitin gwal biyar aka zuba wanda tsofaffin na Binta wanda Turai ta yi ya?i ta bayar dasu aka narka akayo mata sababbin designs ta sake jaSe su ta ajiye a ciki aka Wiba aka bata kuWin rabi kyauta dai haka akayi mata fahin kayanta. Tsabar zirgilli cewa tayi da ita za'aje dukda ba can Abuja aka kai kayan ba Adamawa aka kai can ne Asalin garin mahaifin Fatiyyan dan auran ma acan za'a Wauro shi daga ?arshe dai wayo aka mata aka gudu aka barta ai kuwa har kuka tayi, a waya Lawan ya ringa nuna mata videos dake trending dan su Fatiyyah fa bada wasa suke ba ita da ?awayenta sun gama gigita Social media da zancen Auran tun ana saura wata biyu aka fara save the date dan ma Angon ya?i bada haWin kai yanda ya kamata shiya ragewa abin Armashi dan cewa yayi ma se biki ya rage sati ze dawo da ?yar ya maida shi sati uku.

Kwana biyu da aka kai lefen Jay aka kai na Ahmad, Lefe na mutunchi shima dukda babu tarkacen akwatuna kamar na Jay amma babu wanda ya isa ya raina lefensa ita kanta Hajiyar duk hassadarta da aka buWe musu suka gani seda tace
"Ai daman Amadu badai zuciya ba ita dai yar Bakanike shar da ita toh Allah sa karsu kai kwari su karyar a samu na siyan kayan Waki, daman idan tazo kafi diddigi kai ka Wauki hoton komai yanda ko tsinke ya Sace zaka gane" kowa ya mata shiru dai ba'a tanka taba. Shima dai da aka tashi kaiwa guduwa akayi aka bar Hajiya, Hajiya Ummu Yayarta da suka zo kai Lefen Jay basu koma ba dasu aka tafi kuma ita tace acewa Binta seda Yamma za'aje tunda kusan duk wanda za'aje dasu a hanya za'a haWu su da suka tashi fita sukace mata zasu shiga Kasuwa ne shikenan aka barta a gida tana sa?a irin abinda zatayi idan sunje, ta ?udiri a ranta seta kunyata Aisha, ko za'ayi auran nan ba zata bari tayi shi cikin farin ciki da daWin rai ba se gashi tana can tana sa?a mugun ?ulli taga ana shigowa da Ruwa da Lemo da Farantan kayan snacks ana kaiwa ?akin Momy.

Haka taje ta dirawa Alhaji Kuka wai Aisha ta wula?antata an kai lefen Ahmad banda ita bayan ita a na Jafar sune kan gaba cewa akayi ita zata wakilceta shi kuma, besan ya akayi ba be kuma bi ba'asi ba ya kira Aishar ya mata tatas akan me zatayi haka ta karya masa doka bayan ya kafa cewar duk sabgar ?a ko Yar wanda ta tashi sauran Kishiyoyinta ne zasu wakilceta a gurin ita dai bata tanka ba domin tayi rantsuwar ba zata bati Binta taci galaba akanta ta hanata jin daWin auran sanyin Idaniyarta ba.

Rabon da Afeeyah ta shiga Social Media harda WhatsApp kuwa ta manta, fin watanni uku, kai tun bayan data yarda da gaske Jay ya barta ta cirewa kan lasisin duba Social Media ta sauke komai daga kan wayarta ta zama sedai tayi kira a kirata kawai saboda bata so taci karo da wani abu daya dangance shi, ko me suna Jafar aka kira a kusa da ita a ranar se tayi kuka balle kuma tun mugun ganin da tayi shida wannan yarinyar daya haWa sunansa da nata har ya iya posting nata a private account Winsa ta tabbatar dagaske ne ya barta.

Dalilin shirin bikinta Badar ta uzzura mata seta bude WhatsApp da IG, tuntuni ta buWe musu group acan anan suke ta shiri da sauran ?awayensu amma babu Amarya a ciki, data rasa uzurin da zata bayar se tace bata da waya. Ita ta fitar da Ankon Yini da Kamu wanda zasuyi na gidansu Ahmad yace zasuyi dinner wannan mutum goma suka ware masu Anko dan karsuyi yawa musamman da bikin biyu ne, bisa uzzurawar Badar da take cewa
"You are getting married in to Bechi Family Afeeyah bafa wani karabitin Family bane ya kama muma mu motsa asan da anayi" Tilas ta koma kan Network ta saita komai da dare ranar bayan sun gama waya tana gaya mata mitar da mutane suke tayi ya za'ayi ace ana ta shiri ba'ajin ta bakin Amarya kuma shine ta gaji ya koma. Bayan sun gama maganganunsu a WhatsApp harta kwanta zuciyarta ta ringa Azazzalarta akan ta shiga IG, ta tashi ta kunna Data ta shiga, A jejjere duka bloggers da take bi taga sukayi posting hotonsu, ta ringayin ?asa idanuwanta kamar zasu cire su diro ?asa, jikinta tamkar mazari haka yake rawa gaf gaf wayar ma ?o?arin suSuce mata takeyi, garin babi zafi sam domin yanayin sanyi ya fara shigowa ita da yake kumamace ma har safa ta saka saboda sanyin data ji bayan tayi Alwalar Isha'i se gashi lokaci gida Zufa ta wanke har kayan jikinta na naso.

Ta dinga duba hotunan kamar zararra ta shiga wannan page ta fito ta shoga na ?asansa domin kamar da gayya ake posting abun saboda ta gani. Su biyun babu wanda kamanninsa ze Sace mata duk wuya duk daWi haka kuma ba zatace gizo bane ko kuma ?wa?walwarta ce bata fassara mata daidai ba. Dadai taga kallon pictures Wim baze kaita ba ta shiga duna caption Win da yake akan duka pages Win,
*_"Latest grooms in town, the Bechi brothers"_*.

Comment section ta shiga domin har sannan bata gama tantance abinda ta karanta ba, ta ringa scrolling yau idanunta sun zama kamar wasu scanner a seconds take karance abinda aka rubuta, ashe ba ita kaWai ce cike da mamaki ba, kusan tambayar da kowa yakeyi 'Daman Jay ?an Bechi ne?'
Su nasu iyakar mamaki ne sedai ita ta shiga gigita, tashin hankali, Wimuwa kai babu abinda ma bata shiga ba, Jay shine Jafar Win Ahmad kuma shine Jay Winta?

Dishi dishi take ganin screen Win ma a zaune take amma juwa ke neman kwantar da ita. Ta shiga call log, she needs to call someone that will wake her and tell her that it was all a dream abinda ya faru a baya ba gaskiya bane ko kuma abinda take gani a yanzu shine mafarki ba gaskiya ba. Rikicewar da tayi ta saka ta kasa fahimtar kira ya shigo wayarta wanda Badar ce take kira, a kusan lokaci Waya suka ga hoton, Badar tasan Jay zeyi aure domin dai duk me shiga Social media tuni ya haddace ?irgen Kwanakin auran Jay da suka rage wanda ze kama rana Waya dana Afeeyah, yana daga dalilin daya saka bata damu sosai da barinta hawa social media ba domin tasan sanin abinda yake faruwa ze iya rusa shirin da sukeyi na ganin sunyi bikin farin ciki. Ko yau WhatsApp tace tayi downloading ita kanta bata san sanda ta shiga kiran Afeeyar ba bayan data ga wannan twist Win domin a rikice take, Jay ?anin Ahmad ne kenan Afeeyah tayi soyayya da Yaya da ?ani tana sane ko kuwa Arashi aka samu abinda take so ta tambayeta kenan.

"Afeeyah Ahmad and Jafar are brithers yanzu na gani a IG"
"Badar Ahmad and Jay are brothers tell me this is not true Badar ki cemun hallucination nakeyi" Afeeyah da Badar suka haWa baki gurin faWi kana iya tantance tashin hankalin dake cikin muryoyinsu karma ta Afeeyah taji labari.

*END OF BOOK 2*

*RAMADAN MUBARAK*
*TA?ABBALALLAHU MINNAH WA MINKUM*

*UBANGIJI YA HA?A FUSKOKINMU DA ALKHAIRI, ALLAH YASA MUYI AZUMI LAFIYA MU GAMA LAFIYA,*

*DUK WANDA YAJI DADIN LABARIN NAN KARYA MANTANI A ADDU'ARSA, ALLAH YA FINI SANIN BU?ATUNA, UBANGIJI YA AMSA MANA BU?ATUNMU NA ALKHAIRI YA MUSANYA MANA AKASINSU DA ABINDA YAFI ZAMA ALKHAIRI A RAYUWARMU,*

*YA YAR UWA KARKI MANTA DUK SANDA KIKA ?AGA HANNU ZAKI RO?AWA YAYANKI SHIRIYA A GURIN UBANGIJI KI HA?A DANA SAURAN AL'UMMAR MUSULMI, SIRRI NE BABBA*

*RANAR SALLAH ZAMU CIGABA DA YARDAR ALLAH*
*MATAR MUTUM*
*NA MARYAM FAROUK (UMMU MAHEER*

*FIKRA WRITERS ASSOCIATION*

*LITTAFIN KUDI NE*
*PAY 500 A ASUSUN*
*7061838488*
*OPAY DIGITAL SERVICES*
*MARYAM FAROUK*
OR
*0709290797*
*ACCESS BANK*
*SE A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488*
*IDAN KATINE A DAUKI HOTONSA A TURA ZUWA LAMBAR SAMA VTU KUMA A TURA A 08142548705*

*Kuyi following dina a Arewabooks @Maryamfarouk01 inda zaku karanta wannan littafin tareda sauran littattafaina*
*NAGODE*

*BOOK 3*
*PAGE 1*

Tun kusan two weeks ago nake ganin pictures Win Jay da yarinyar da ze aura se yanzun kawai naga wannan, Afeeyah I'm confused, ta yaya Ahmad da Jay suka zama brothers? And do you know about it ko kema yanzu kika sani" Badar ta sake faWa cikin Jimami. Afeeyah bata iya sake cewa komai ba se kawai ta fashe da kuka, kukan da dalilan yinsu yake da yawa.

"Ta yaya zakiyi tsammanin na sani Bafar, ace nasan Ahmad da Jay brothers ne kuma nayi dating nasa. Kima ture yan uwantakansu, Badar Jafar fa mutumin dana tsana sama da kowa a duniya ace shine ya rikida ya zama abinda nafi so dama da komai a yanzu nake dakon sonsa dan har yanzun ba wai ya fita daga raina bane saboda babu yanda zanyi ne kawai na ha?ura dashi shikenan lokaci guda azo a ce shida Ahmad yan uwane kenan ma duk abinda ya faru set up ne.
They set me up Badar, daman ya daWe yana shan Alwashi akaina gashi nan ya cika Ahnad da ?aninsa used me Badar, daman ai na faWa miki zuciyata ta kasa kwanciya kan Ahmad na cewar bashida wani shirin rama abinda nayi masa a baya yanzu ga magana ta fito, sun yaudareni shida ?aninshi Innalillahi wa'inna ilaihi

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login