Showing 213001 words to 216000 words out of 467220 words

Chapter 72 - MATAR MUTUM COMPLETED 1-3 BY MARYAM FARUK.doc

23 Sep 2025

12503

wuce Wakinta. Baffa ya sake duban Afeeyah, yanda taji muryarsa ta tabbata ransa a Sace yake ta san kuma fushi ba Wabi'arsa bace tabbas ta kaishi bango ne dan haka yana sake maimaita mata tambayar jiki na rawa taja baya daga kusa dashi kafin tace

"Ni daman Baffa ban taSa cewa ina sonsa ba kawai bazan iya wula?antashi bane amma duk wata alama da ya kamata na nuna masa nayi amma ya?i ya ha?ura".

Baffa ya ringa kallonta har tayi shiru, yafi minti goma kafin ya iya cewa
"Kina nufin tsayin shekara uku da yaron nan yake bibiyarki yana wahalta miki duk ya tashi a banza yanzu zakice ba sonsa kikeyi ba?"

"Wlh Baffa ni ban taSa cewa yayi mun abu ba, kuma ai ko kai kana hanashi amma se ya dage se yayi kuma ni ina gaya masa ya dena kawai shine baya ji"

Umma ta le?o a fusace tace
"Dan ubanko dole yanzu kice bakya sonsa mana kuma bake kika saka ya ringa miki wahala ba, Kare ne shi da ze shekara uku saboda rashin zuciya yana tare dake kina nuna masa rashin So kuma yaci gaba da zama dake? Kin gama yaudarar sa kin Sata masa lokaci saboda baki da mutunchi yanzu zakice bakya Son sa me yasa tun farko baki faWawa Malam Win ba shi da kansa ya kirashi ya sallame shi se yanzu da koWaWWiyar fuskarki zakicewa mutane ke daman bakya son sa to wlh baki isa ba" Umma ta shiga sababi harta manta darene ta muryarta a sama.

Baffa daya kasa magana tuntuni ya kalli Fatima yace ta wuce Waki, sum sum ta shige tana jin kamar an sauke mata wani nauyi daga kanta tunda har ta iya furtawa Baffa bata ra'ayin Ahmad tasan magana ta ?are. A Waki Umma ta warwarewa Baffa komai game da zancen Yaron da Afeeyah take so wato Jay Wan ?wallo.
"A ina suka haWu?" Ya tambayi Umman, ta watsa hannu kafin tace
"Wai acan makarantarsu, Malam ka sanarwa Yaron nan kawai ya turo Iyayensa suzo a Waura musu aure kawai idan yaso ta mutu ?arshen rashin Son Sa".

"Ba za'ayi haka ba, za'a bi komai a hankali, magita zata samu da yardar Allah" inji Baffa. Daren raba shi yayi yana sallah da addu'oi, ya kasance me yawan tsayuwar dare amma yau Umma tasan sallar tasa harda ta neman Wauki gurin Allah kan wannan abin daya tunkaro shi. Baffa na Son Afeeyah, amma abu Waya da tayi imani dashi shine baze bi Son rai ya zubar da ?imar sa ba shiyasa ya maida lamarin ga buwayin sarki gagara Misali wanda duk hukuncin daya yanke babu wanda ya isa yayi inkari akai.

Kwanaki uku Baffa ya jera yana Istikara cikin tareda tsananta Addu'a da ro?on ubangiji akan Al'amarin, Afeeyah kuwa rai fes dan Ahmad be sake kiranta ba tunda ya tafi kuma ta furta abinda yake ranta dan tasan Umma ta gayawa Baffa zancen Jay babban abinda ya sakat nishaWi da farin ciki kuma shaida mata da Jay yayi yana tafe Nigeria nan da sati biyu masu zuwa. Saura kwana biyar su koma makaranta semester ?arshe ce babu Lectures da yawa se aikin project da abinda baza'a rasa ba dan haka ta yanke ba zata koma bahar se yazo tukunna abinda bata taSayi ba ?arin hutu tunda ta fara University.

Ta gayawa Badar Jay yana tafe, Badar nason Jay da Afeeyah amma ba kamar yanda take sonta da Ahmad ba kamar yanda take ce mata Ahmad Mijin Aurene Jay kuma na rage lokaci da neman suna domin ita dai bataji a jikinta Jay auran Afeeyah zeyi har yanzu ba duk kuwa da tarin ?aunar da yake nuna mata akan haka har faWa suka sakeyi ta dai rabu da ita tana kuma yi mata addu'a a matsayinta na ?awarta.

Takanas taje gidan Anty Sauda tace mata nan zata fara kawo Jay kafin Umma ta sauka daga fushin da takeyi da ita tukunna se ta kaishi gidan.
"Yanzu kina ganin abinda kika zaSawa kanki daidai ne Afeeyah?" Anty Sauda wadda Umma ta gaya mata duk abinda ya faru ta tambayeta.
"Haba Anty dan Allah wai ana aure dole ne? Naga kema zaSi aka baki kika kawo wanda kike so me yasa ni ake nema a tauye mun ha??i?" Ta jefawa Anty Saudan tambaya. Seta girgiza kai kawai tace mata Allah ya kawo Jafar Win lafiya, bata wani jima ba ta koma gida dukda zaman gidan ba wani daWi yake mata ba yanzu saboda yanda Umma ta canza mata. Daga ita har Baffa babu wanda ya mata zancen ganinbata koma makaranta bama se Yah Malam daya zo hutu ne yace ya ya ganta a gida tace se wani satin zata koma. Baffabe canza mata kamar Umma ba dan ze amsa gaisuwarta har ya sakata aikace aikace kamar yanda ya saba amma Umma ko gaiseta tayi da harara take amsa mata tti duk yanda zatayi Umman ta sakko amma abu yaci tura tasan dai fushin Umma akan Ahmad ne addu'a takeyi Allahya kawo Jafar wanda yace zuwa Waya zeyi kafin yayi na biyu za'a tambaya masa auranta dan ya matsu.

"Yah Ahmad ka dena sona wlh, yanzu ace zanzo gida amma babu wani murna ko Wokin gani na daka sabayi kawai Allah ya kaimu shikenan abinda zaka ce?" Jafar ya dasawa Ahmad mita akan beyi murna daya ce masa zezo gida ba. Ahmad daya kwanta zazzaSin malaria kamar yanda yayiwa Momy ?arya amma gaskiyar abinda yake damunsa Love sickness ne. Tun ranar daya baro gidansu Fatiman damuwa ta saukar masa da ciwon kai da zazzaSi me zafi amma haka yake bankar Anti Malaria da Momy tasa dole yaje asibiti aka rubuto masa.

"I told you bani da lafiya Jafar amma kana ta so se ka sakani magana"
"Ni ai bazanyi maka sannu ba saboda wannan ciwon kai ka Worawa kanka, let me ask you please, is this Fatima made of Gold or some sort of precious stone da tayi deserving wannan soyayyar da kakeyi mata?
Yah Ahmad me yake damunka? For heaven sake kana nema ka kashe kanka akan wata banzar mace? Is she the only living woman on earth? Ko dai asiri tayi maka? Oh na manta mayyace believe me ta cinye maka zuciya kuma wlh bata isa ba. Ko waye ubanta she must leave you, seta fita a rayuwanka let me come back first I'm going to deal with her personally, se ta gane bata da hankali wlh" ya ringa sababi kamar ze aro baki daman kuskure Ahmad yayi daya taso masa da maganar gashi yana neman ya sake ?ara masa ciwo.

"I love her, kuma banajin zan iya dena sonta idan da abinda zakayi kasa ta soni i will appreciate it more zaginta da kakeyi dan baka san abinda nake ji bane ba nidai idan kana sona da gaske just help me fight na samu Fatima" Ahmad ya faWa. Jafar yayi shiruj irin wanda takaici ya gama ti?ewa kafin yace

"Indai haka ne ze sa ka yarda Ina sonka then I don't love you Yah Ahmad and i will never love you indai se naso wannan yarinyar ne ka cireni a jerin ?annenka, i hate her, i hate her with all my life kuma ko Allah yasa ka aureta bazan taSa shiga gidanka ba" yana gama magana ya kashe wayansa yanda Ahmad ya jishi yasan ba ?aramin zafi ya Wauka ba. Yayi murmushi, yasan rigimar Jafar na lokaci ne zuwa anjima ze sake kiransa kawai dai wannan ?iyayyar da yakeyi mata me zafi ce ya rasa dalilinta, saboda shine kuma yanzu so yakeyi ya ha?ura da ita ba shikenan ba.

****************

"Alhaji, ni tun kwanaki naji kana zancen Amadu ya samu mata ko? Ashe ma ya taSa kaiwa Ummu ita, se jiya da muke magana Jafaru yace daya zo za'aje masa neman aure shine tace mun zancen ai taga budurwar Amadun ma ya Waukota daga makaranta suka biya gidanta wai ya karSowa Aisha Leshi, wai a Zaria take makaranta, nace Yayan masu kuWi suna zuwa wannan makarantar kuwa?"

Alhaji Audu na kurSar ba?in shayi daya sha spices, Girkin Hajiya Rabi ne ita ta dafa masa tana kawowa Hajiya Bintan tazo ta kankane gurin dole ta fita ta bata guri dan har ta fara sakar mata maganganu tana ci mata zarafi shi kuma Gwankin na zaune shirim bece komai ba. Ya gama sauraron Hajiyar kafin yace
"Oh ya samu mata kenan da yake ke zaki nemo masa auran shiyasa ya fara sanar dake?"

"Shi wa? Ummu nace maka ni a suwa Amadu ze faWamun ya samu Matar Aure Aisha ce ni kowa?" Ta faWa tana wani taSe baki. Alhaji ya sake zuba shayinsa yana sha yace
"Shi ?an naki nake magana"
"Wai Jafaru? Dama idan be gaya mun ba toh wa kake so yaje ya fara sanarwa ko yana da wata uwar ne bayan ni a duniya?"
"Aa bance ba, shi Ahmad Win dake ya Waukeni uba ai tun fara neman yarinyar da yakeyi ya sanar dani, kawai inda ya nemo auran ne be gama kwanta mun a rai ba shiyasa ma kika ga an kawo yanzu maganar bata tashi ba amma yafi shekara da sanar dani".

Har wani zullo tayi kamar zata kwanta a gabansa tace
"Ashe maganar ta daWe? Daman Ummu tace anfi wata shida da zuwan nasu tun kafin lokacin bikin su Hafsatu to ashema ka sani toh naji kace gidan daya nemo auran ne beyi maka ba, da akwai matsala kenan?"

Da zuciya Waya yace mata
"Yar wani Bakanike ce yarinyar Malam Hafizu akace sunansa a Alfindiki yake, a binciken da na saka akayimun dai Mahaifin yarinyar nace bashi da matsala mutumin kirki ne toh amma ita yarinyarce surutu yayi yawa akan yanda Samari suke zuwa gurinta wannan yazo wannan ya tafi gashi a matsayin mahaifinta irin rayuwar da akace tanayi ta wadata ya zarce ace shi yakeyi mata, kinsan yaran yanzu, zakiga Iyaye suna iyakacin ?o?arinsu gurin tarbiyya amma idan sun fita se abinda hali yayi musamman masu tafiya karatu wasu garuruwan ba gaban Iyayen nasu ba to wannan yasa na dakata kuma shima Ahmad Win tun maganar farko da mukayi be sake tayar mun da zancen ba dukda dai ina da labarin suna tare haryanzu kuma ita kaWai yake kulawa ta yuwu yana jira ta kammala makaranta ne tunda ance shekarar ?arshe take".

Tamkar me Waukar karatu haka Hajiya ta naba'a tana sauraron Alhaji se gyaWa kai takeyi har ya kai aya kafin cikin Jimami tace
"Ikon Allah, shi kuma Amadu inda ya tafi kenan? Nida nake ta sauraro naji ya samo yar gidan ?angwate ko BUA tunda suke abokanan goga kafaWarka a ?asar nan seya Sige da yar gidan Bakanike? Toh Allah ya rufa asiri, ita dai ta Jafaru ance Balarabiya ce dan ya turawa da Munirah hotonta wai irin wanda ake kalla sau Waya ne shiyasa bata kwafa ba ta ajiye mana. Todai daya zo koma ya ake ciki zamuji, seka fara shirya wa'inda zasu nemo masa auran inajin dai baze wuce a Saudi Arebia ba ko Dubai"

Alhaji yace mata
"Toh, Allah ya kawo shi lafiya"
"Toh amma Alhaji ina da wata magana idan babu damuwa kuma ka bani dama in faWa" yanda tayi maganar yasa ya tattara hankalinsa akanta dan yaji me zatace. Hajiya ta gyara zama kamar gaske kai a ?asa tace
"Dama Alhaji akan mu'amalarka da yaran gidan nan ne naga ya kamata a gyara wasu abubuwan, ina nufin su Alhaji Babangida da sauran yaran da basa cikin gidan nan. Bana jin daWin yanda kowa idan ya tashi yake Wora mun laifi a ringa cewa ni ce na rabaka da yayanka.

Kaga girma ya cin maka, ya kamata ace zuwa yanzu ka fara sakin wasu abubuwan ka bari Manyan yayanka suyi maka".

Alhaji yayi tagumi yana kallon Hajiya Binta data sake gyara zama tana cewa
"Ba harkar kasuwancinka nake nufi ba, wannan ai kana da magada daka rigada ka koya musu komai kuma suka goge akai ina nufin kamar harkokin aure, kaga daga kai har Yakubu kun manyanta ya kamata ku zauna ku huta ku fara sakarwa Yayanku suna jan ragamar abubuwa".

"Wato ba zaki ringa karanta sunan Yakubu ba, Idan beci darajar girmata da yayi kin kirasa da Yaya ba ai kya bashi sunan da kowa yake kiransa dashi Al?ali" Alhajin ya tareta. Ta lan?washe kamar yarinya tace
"Allah baka ha?uri saboda faWa ne uffararan Baba Al?ali nake so nace, to da kai dashi duk ku huta ka kirawo Yayanka gaba Waya ka zaunar dasu kuyi maganar nan, ka ware wanda zasu ringa zuwa tambayowa Maza aure da kuma wanda zasu ringa karSan na mata idan an zo. Amma kafin nan ya kamata duk wani abu daya taso ka ringa tarasu kana shawara dasu, ta hakane zaka jasu a jiki suma su sake dakai a hankali se kaga duk sun dawo gida a dena zagina a gari ana cewa na raba yaya da ubansu".

Alhaji ya sakeyin shiru yana nazarin maganarta, Al?ali Yakubu ya taSa yi masa makamanciyar magana irin wannan, yace ya kamata ace ya ringa janyo Yaransa a jiki domin ya gyara kuskurensa na baya. Rayuwarsa ta fara zuwa gangara, be kamatu ace ya mutu ya bar kan iyalansa a rarrabe kamar yanda suke a yanzu ba. Maganar Bintan se ta sakashi Nazari, tabbas abinda ta faWa gaskiya ne domin Abokanansa masu Manyan Yaya kamar nasa da yawa yanzu a kwance suke suna hutawa komai da masuyi musu, ze gwada shawarar tata koda akan zuwa batun Neman aure ne da karSar ze saka su yasan babu wanda zece bazeyi ba a cikinsu.

"Kamar yanzu da zancen auran Ahmad dana Jafarun nan musamman na Ahmad da kake da kokwanto akan yarda ko akasin haka, ka tarasu, ka nemi shawararsu kaga zasuji daWi suga ka mutuntasu kuma su sun fika sanin kan duniya yanzu se kaga an samu maslaha ai ko?" Ta sake faWa. Alhaji ya jijjiga kai da alamar gamsuwa, tayi murmushin cin nasara sannan tace

"Toh amma fa karka gayawa matanka ko Yan uwanka shawarata ce dan ka san cewa za'ayi da wata manufa nayi ni kuma Allah yaga zuciyata babu komai face Alkhairi so nakeyi ka shirya da yayanka ka haWa kan zuri'arka", bata tashi daga gurin ba seda ta gamsar da Alhaji Alfanun abinda tace yayin ya kuma yarda da hakan. Babu Sata lokaci a daren ya kira Alhaji Babangida, umarni ya bashi akan ya haWo masa kan Yan uwansa daga Babannan zuwa Mu'allim, banda Matan da kuma Zayyad da Abdallah da basu isa ayi wannan shawarar dasu ba. Alhaji Babangida ya shiga mamakin ko lafiya wannan kira haka da Alhaji yayi musu amma babu damar tambaya. A washe gari ya sanarwa da waWanda yake da numbers Winsu a waya ta hanyar Text message yace su sanar da sauran. Ya sake kiran Alhaji domin ya manta be tambayi ranar da yake da bu?atar ganinsu ba.

"Ranar Asabar Win nan" Alhaji ya bashi amsa. Alhaji Babangida yace
Zan sanar dasu ranar, amma naji Jafar yana tafe ranar Talata, ba za'a iya Wage taron a jirayi zuwan saba?"
"Aa, duk abinda aka tattauna idan ya dawo zaku sanar dashi" da haka sukayi sallama. Ya gayawa Al?ali ze zauna da yaransa duka ya kumayi murna da hakan domin an samu cigaba kenan Alhaji Audun ya shiryi samun daidaito tsakaninsa da Iyalansa.
*Assalamu alaikum*
*Ina matan suke, Manyan mata yan kwalisa da suka amsa sunansu na Mata ba muna mata ba Kawayen Binta gumama?*

*SODAH GENERAL ENTERPRISES ce tazo da kanta ba aike ba tana kuma shaida mutu da cewar zafafan kaya sun sauka, kamar yanda kuka sani tana kawo muku suturu na sakawa kama daga kan Atamfa, Laces da dangoginsu*

*Wannan karon ta sake taho muku da tsarabar Supplements ingantattu wato Original bawai copy ba. Ku sani bayan abinci jiki yana da buqatar qarin wasu sinadarai da zasu taimakawa ginuwar jikin da lafiyar kowanne bangare na jikin, SODAH ENTERPRISES tana da General Supplements ma'ana wanda suke tattare da Vitamins da dukkan jiki yake buqata sannan tana da special supplements wanda HQ wato gidan mutunchi yake buqata domin sake tsare qima.*

*Ina wadda take fama da skin nata yaqi dadin azanci? Fata ta bushe tayi dabbara dabbara ta shafa mai duk a banza se qara lalacewa tayi? To maza ki leqa gurin SODAH ENTERPRISES domin tana da sabulu me kyau da inganci me gyara fata tayi kyau ta goge tayi sulbi baya saka Fari asalin kalarki ze sake fiddo miki ya kuna goge duk wasu tabo ko rashes da suke hanaki walwala, sabulunta babu chemical ba kuma na bleaching bane yawwa karki tsammaci da zakiyi haske Aa sedai glowing kalarki ta ainihi ze fitarda.*

*A tuntubeta kai tsaye akan 08137145294*
*Ko ki danna wannan link kai tsaye domin magana da ita*
https://wa.link/wwvjr3
*Location Kano, tana Nation wide delivery*

*MATAR MUTUM*
*NA MARYAM FAROUK (UMMU MAHEER*

*FIKRA WRITERS ASSOCIATION*

*LITTAFIN KUDI NE*
*PAY 500 A ASUSUN*
*7061838488*
*OPAY DIGITAL SERVICES*
*MARYAM FAROUK*
OR
*0709290797*
*ACCESS BANK*
*SE A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488*
*IDAN KATINE A DAUKI HOTONSA A TURA ZUWA LAMBAR SAMA VTU KUMA A TURA A 08142548705*

*Kuyi following dina a Arewabooks @Maryamfarouk01 inda zaku karanta wannan littafin tareda sauran littattafaina*
*NAGODE*

*BOOK 2*
*PAGE 17*

A bisa dole Iyalan Alhaji Audu suka amsa goron gayyatar daya aika musu dashi. Ba kalar mitar da basuyi ba amma haka suka zo domin koda basa ga maciji da mahaifin nasu sun sanshi sarai baya Waukar wargi, farillan rashin mutumchi kuwa sala sala yanadasu wanda yake amfani dasu gurin ladabtar da duk wanda yace zeyi masa giggiwa.

A cikin su daman wanda yafi kowa taurin kai Alhaji Hussaini ne, da Dr Hassan ya sanar masa da kiran Mahaifin nasu take yace masa
"Bazanzo ba, inada abubuwan da suka fi muhimmaci da sauraron kalaman son rai da wannan tsohon ze faWa mun in kuma ya fara tafiya gargara ne yake so ya bada wasiyya ka karSa harda tawa ka ri?e na bar maka in ma mutuwa yayi ni wlh na yafe gadonsa tuni". Seda Hajiya Zubaida Mahaifiyarsu tayi masa kaca kaca bayan da Dr Hassan ya sanar mata da abinda yace tace kuma tilas yaje idan kuma ya isa ya tsallake umarninta daman ita kaWai take maganin Iya shegensa, yana son mahaifiyarsu yana tausaya mata yana kuma ri?e da abinda aka labarta musu cewar Alhaji Audun yayi mata tun kafin haihuwarsu da bayan zuwansu duniya.

?wato su da yayi ya maidasu gidan ya zube su a tsakar gida shine abun daya ?ara ta'azzara tsamar dake tsakaninsu. Yanda Hajiya Binta ta ringa yi musu, kalar azabatarwar

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login