Showing 279001 words to 282000 words out of 467220 words

Chapter 94 - MATAR MUTUM COMPLETED 1-3 BY MARYAM FARUK.doc

23 Sep 2025

12112

jira har sanda Allah ya nufa ya bashi wata matar kamarta sannan yayi auransa haka nan ya kwasowa kansa wannan yarinya da bata san me takeyi ba?

Takamaimai babu wani abu da ze Waga tattare da ita yace na cikakkiyar mace data san kanta, banda tayi wanka da kwalliya ta kame akan kujera tayita Waukar hoto da waya da ?awaye babu abinda ta iya, babu ruwanta dashi, yaci abinci be ci ba duk ba damuwarta bace ba, daman daga can gidan Alhaji ake kawo musu abinci safe rana dare wanda Hajiya ta saka akeyi a cewarta surukarta ba kalar wahala bace ta huta kafin a kawo mata yan aikin da akace zasu zo, idan aka kawo yanda suka ajiye Shi a Dining sefai idan yaga dama ya fita ya Wiba yaci kuma wanda yayi saura ba zata killaceshi ba nan zata bar na safe se an kawo na rana su kwashe kwanukan babu wanki su tafi dasu haka na ranar in an kawo na dare a Wauka naa daren kuwa haka ze kwana sesa safe shima za'a Waukeshi.
Ko ba?i akayi yan zuwa ganin Waki toh fa sedai tace su shiga kitchen su sama wa kansu abinda zasu ci ba zata iya tashi ta basu ba, Shara kuwa gidan bega tsintsiya ba se ranar data kwana huWu sannan aka kawo mata yan aiki mutum uku, Shi dake ba wani daWi yake ji ba shiyasa bebi ta kanta ba ya barta ne kawai zuwa su koma Paris a can ze saita mata hankali.

Hajiya dai duk irin ?orafin da masu zuwa gidan Jafar Win suke kawo mata ko a jikinta, da Munira tayi ?orafin yanda ake dawo da kwanuka daga gidan Jafar Win cewa tayi
"Kin san dai yarinyar nan ba kalar wahala bace ba na san a gidansu bata san wani abu wanke wanke ba akan me zatayi a nan? Ita dai waccen yar matsiyatan dake an saba da wahala kina gani washe garin da aka kawosu ta Wora tukunya ana Allah Allah anga na banza aci daWi bayan ko ?wayar hatsi basu kawo mata gara ba, aidai wlh Aisha sakaryace koda yake Allah ya ?ara yanzu dai kiga uban zannuwan da aka kawomun a cikin gara kinga ribar auran yayan masu dashi kenan".

Cikin tsananin takaici Muniran tace mata
"Wlh bansan sanda zaki canza ba Binta halayenki ko wacceta fito daga gidan tantagaryar tsiya Albarka wlh, yanzu har wata tsiya ce uban Fatiyyah, idan ana lissafin masu kuWi waya sanshi waya san da zamansa? Sufa ya kamata suyi murna yarsu tayi aure a gidan Audu Bechi amma yanda kike abu se kace wacce aka auro yar gidan ?aruna aka akawo, kece kai musu abinci, tunda tazo ko sau Waya banga ta kiraki a waya ba amma ke tsabar iya zubar da mutunchi ke kike kiranta kiji ya take me take bu?ata kina ganin irin rashin mutunchin da takeyi duk wanda yaje gidan gaisuwa se wanda yacika mata ido take gaidawa idan ta raina mutum kuwa iskar Fanka ta fishi a gurinta, nan kafin Yan Bechi sukoma seda Ahmad ya kawo matarsa ta musu bangajiya dukda sunje musu amma ke da Jafar yace zasu zo hanawa kikayi daman da sukaje rashin mutunchi ta musu duk ana gaya miki amma kin toshe kunne kin bi bayan rashin gaskiya ina jiye miki randa zata kware miki zanin rashin mutunchin ?ila sannan zaki dawo hayyacinki kisan me kikeyi.

Ita yar matsiyatan da kike cewa babu wanda yaje ya dawo ya faWi aibunta dangin Ubansu kowa da yabon kirkinta ya tafi ana tsinewa taki surukar so kikeyi itama ki mayar da ita mujiya a cikin dangi irin sauran pAce ke duk surukanki babu ta kirki me hankalin ciki kin ?warzabeta itace yar iska a gurinki to wlh ki canza tunda wuri kafin lokaci ya ?ure miki, sannan abinda yafi damuna yanda kowa in yayi aure kumari yake yayi haske amma banda Jafar duk ya rame kina kallonsa kinsan yana da damuwa amma ko a jikinki seta waccen fitsararriyar me ido a tsakiyar ka kike ba zaki ji meye damuwar Wanki ba to tun wuri dai ki gyara wlh kafin kizo kina dana sani mara amfani".
Idan nace zan rubuta komai da komai to wannan page din ba zai isheni ba ,Amma ga masu sha'awar siyan kayana Zaku iya mun magana Kai tsaye ta wannan number, haka masu sha'awa su dinga ganin kalolin kayana a status sumin magana ta wannan number sai nayi seving numbers dinki ta hakan ne Zaku dinga ganin kalolin kayana idan na daura*
http://wa.me/+2347069711327

*Ina maraba da Mai siyan Daya ko sari Dr maman Yusuf likitar mata sokoto*

*MATAR MUTUM*
*NA MARYAM FAROUK (UMMU MAHEER*

*FIKRA WRITERS ASSOCIATION*

*LITTAFIN KUDI NE*
*PAY 500 A ASUSUN*
*7061838488*
*OPAY DIGITAL SERVICES*
*MARYAM FAROUK*
OR
*0709290797*
*ACCESS BANK*
*SE A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488*
*IDAN KATINE A DAUKI HOTONSA A TURA ZUWA LAMBAR SAMA VTU KUMA A TURA A 08142548705*

*Kuyi following dina a Arewabooks @Maryamfarouk01 inda zaku karanta wannan littafin tareda sauran littattafaina*
*NAGODE*

*BOOK 3*
*PAGE 7*

Seda sukayi sati biyu da tarewarsu kafin Amaren suka sake junansu a ido, tun safe daman Ahmad ya shaidawa Fatima bayan magrib zasuje gidan Alhaji Audu da gidan Baba Al?ali dan haka da wuri ta gama duk abinda zatayi sanda ya dawo daga sallar Magrib Win hatta da jakarta na ri?e a hannunta da alamun shi kawai take jira dan fashin sallah takeyi a sannan, a Wan zamansu ta karanci abubuwa da yawa akansa daga wanda yake so har zuwa wanda baya so kuma tana kuma ?o?arin kiyayewa, baya wasa da lokaci, idan yace ?arfe kaza zeyi abu to kuwa da wuya ya wuce hakan. Idanu cike da so tareda bege ya kama hannayenta yana juyata yace

"Kinyi kyau". Doguwar riga ta saka ta Leshi A line tayi simple Wauri sannan ta yafa gyalenta akai ta fito sak cikakkiyar matar bahaushe, shigar ta fito da kamalarta sosai, tayi murmushi tana shafa fuskarsa tace
"Kaima kayi kyau Habibi I'm jealous karma wata ta kallemu kai a hanya"
Ya matseta a jikinsa har seda tayi yar ?arar wasa kafin bakinsa akan kunnenta yace
"Dagaske kina kishi na Faty?"
Cikin salon da bata taSa zaton zata gwada akan wanin Jafar wanda ta koya saboda shi ba ta juyo suka fuskanci juna numfashinsu na gauraya, da wani salon murya tace
"Ba zan iya kwatanta yanayin da nakeji akanka ba a yanzu, abinda na zani zan iya yarda a rabani da komi amma banda kai, in rayu dakai in mutu na barka shine burina dan idan ka rigani mutuwa bansan wacce Al?ibla rayuwata zata kalla ba".

Cikin wani irin sauri da zumuWi ya haWe bakinsa da nata ?arar fashewar abunda basu san ko menene ba ya katse musu hanzari, a tare suka kalli ?ofa inda sukaji ?arar, Jafar ya dur?usa ya shiga tattara pieces Win tsadaddiyar wayarsa data dagargaje a ?asa sakamon suSucewar da tayi daga hannunsa ta daki marbles dake shimfiWe a palour, da sauri Ahmad ya saki Fatima data saki tsaki me ?arfi, bata san sanda tayi Shi ba ba kuma tasan dalilin yinsa ba kuma daga Ahmad Win har Jafar sun jita, cikin jin haushi ta zauna akan kujera tana girgiza ?afa, Ahmad ya isa gurinsa yana cewa

"A garin yaya? Yaushe ma ka shigo bamu ji motsinka ba?"
Murya a cunkushe kamar wanda aka cusawa tsumma a baki Jafar yace
"Nayita kiran wayarka baka amsa ba, ?ofan kuma a buWe yake nayi sallama ai bakuji ba".
"To yanzu a garin yaya wayarka ta faWi haka? Yanda ta fashe bana zaton zata sake tashi kalli komi fa ya fice daga jikin Wan uwansa" Ahmad ya sake faWa, Jay ya tsinci Sim card Winsa kafin ya juya yana cewa
"Dare ya farayi"
"Muje Wife" Ahmad ya faWa yana kallon Fatima dake kumbura kamar fulawar data ji yeast.

A jikin mota ya jingina yana maida numfashi kamar wanda yayi gudu ?wa?walwar sa da idanunsa suna tariyo masa abinda yaji da wanda yagani, tasha gaya masa ba zata iya rayuwa babu Shi ba, ta yarda ta rasa komi indai tana tare dashi kenan shi ta yaudara ko kuma Ahmad take yaudara yanzu. Ba a son ransa ba ya waiwaya sakamakon ?arar takun takalmanta da suka cika kunnensa kamar katin gayyata, a kallo Waya ya ?arewa shigarta kallo har zuwa yanda hannayensu suke sar?e ita da Ahmad.

"Ina Fatiyyan kuma?" Ahmad ya tambayeshi bayan daya kalli cikin motar be hangota ba, ya yamutsa fuska yana buWe mazaunin driver yace
"Bata shirya ba"
"Ban gane bata shirya ba Kuma shine ka fito na zaka jira ta gama ku fito tare ba?" Ahmad ya jefa masa tambayar yana kallonsa, yanda kasan wanda ya zaga haka ya hayayya?o masa yana cewa
"Tun da safe na gaya mata zamu fita saboda ta raina ni ta zauna bata aikin komi se waye wayen banza da chat sannan yanzu tace bata shirya ba wlh bazan jirata ba ai ni ba yaronta bane ba".

"Ikon Allah, amma dai akwai abinda ya Sata maka rai ba iyakar wannan bane ko?" Ahmad ya sake faWa, ya tunzura baki kamar ze taSo sama amma bece komi ba, shi kaWai yakeji a lokacin.
"Inaga mu bari muyi isha'i kawai se mu tafi, wife shiga kiyi mata magana ta shirya " Ahmad ya faWa yana kallon Fatima, ta masa murmushi ta juya ta tafi, a get suka kusa cin karo da Fatiyyah ita ta saka kai zata shiga ita kuma tana fitowa Fatiman tayi zaurin janye mata ta bata hanya dan yanda ta taho da alama in bata matsa babangajeta zatayi, a sama take itama. Kamar wadda zata bikin ?awa haka ta cakare ta saka fitted gown ta Atamfa ta kamata tsam komi ya fita fuskar nan fes da hoda da jambaki dogon gashinta me tsayi sa she?i na reto ta tsakiyar gwagwgwaron datayi ta rataya Chantilly veil daya dace da Atamfar jikinta a kafaWa Waya take ?amshinta ya karaWe gurin, ida ka ganta ba zaka taSa cewa ko tsayayyen saurayi me kishinta tana dashi ba balle ayi tunanin Matar aurece me Miji.

Gaban motar ta buWe ta shige tana taunar cingam ?a?ass, badan Maminta tace tashirya ko ya tafi ta Wauki mota tabi bayansa ba da wlh babu inda zataje, har ita ze ringayiwa ihu akai saboda tace ba zataje gidansu ba? Shi take aure ko iyayensa da zece dole se taje ta gaishe su bayan damunta da uwarsa takeyi kullum a waya akan me ba biki ba ba mutuwa ba zece se taje ta gaida su?

Ahmad da Fatima suka Shiga baya, kanta akan kafaWarsa tana shafa gemun daya fara tarawa saboda tace tana so kuma ya masa kyau suna maganganunsu ?asa ?asa, baka jin me suke cewa se sautin dariyarta dake hawarwa Jafar kai tana masa yawo kamar kiyashi, ikon Allah ne ya kaisu gidan Alhaji Audu badan yasan inda yake cilla kan motar ba, sanda sukazo fita daga mota sannan ya ankare da shigar Fatiyyan tasa, ya kwaso rantsuwa kafin ya dire Ahmad ya rufe masa baki yana cewa

"Kar kayi abinda zaka zubar muku da mutunchi a gaban masu aiki"
"Akwai zubar da mutunchin daya fi wannan? Kalleta fa? Ita bata da hankali bata san inda zamu zo ba zata fito a haka ko kuma haka taga AFEEYAH tayi tata shigar?" Ya faWa a hasale. Su ukun suka fara kalle kalle kamar masu neman Afeeyar daya faWa harda ita kanta Fatiman, Ahmadya saki ajiyar zuciya me ?arfi yana ri?e da hannunsa yace
"Me yasa tun a gida bakayi mata magana ta canza ba? Kayi ha?uri kawai mu shiga yanzu koma menene idan kuka koma gida se kuyi" haka suka firfito daga motar, ma'aikatan gidan suka yanyamesu ita da kanta seda taji wani iri ta shiga raSewa a bayan Fatima, dirowar Hajiya gurin kamar jifa ya ceceta, ta cakumeta da sunan runguma baki har kunne take cewa

"Oyoyo welcome my daughter you are highly welcome" se kuma ta juya kan masu aiki dake ta faman gaishe su kowa na mi?a wuya dan yaga Amare musamman Fatiyyah dan ita Fatima sun ganta
"Shegu kamar mayu to aniyar kowa ta bishi kun wani zura mata ido se kace baku taSa ganin mace ba" Hajiyar take bala'i, hannunta cikin na Fatiyyah ta ringa janta ?iii se cikin gida, Ahmad, Fatima da Jafar dake numfarfashi, masifa nacin ransa suka wuce Falon Alhaji Audu. Tareda Baba Al?ali da Alhaji Ali Mijin Turai suka sameshi, daga farkon Falon Fatima ta zauna su kuma suka wuce ciki suka shiga gaida iyayen nasu.
"Ahmad dai inaga Wurar yeast Amarya takeyi maka, kai kuma da alama da naman jikinka take miya ko?" Alhaji Ali ya faWa yana kallon su biyun, Baba Al?ali yace

"Masha Allah kam Ahmad ashe zeyi ?iba, shi kuma Malam ai baya jin daWi ne, kasan shi ya rigada ya saba da rayuwar Turai idan yazo gida naga alama takura yakeyi duk se ya tsomare kafin ya koma inda ya fito, to ai gajiyar biki ta warware seka fara shiri ka koma kafin kasa iyayenka su fara yiwa Amarya Wan biki tunda gashi Alhaji Ali ma ya fara, ina ita yar uwar taki ko ba tare kuka zo da ita ba?" Ya fara tambayar akan Fatima ya ajiyeta kan Jafar, Ahmad ya bashi amsar cewa ta shiga ciki,

"Baka jiyo hayaniyar Uwarsa ba ta fito tarar surukarta?" Alhaji Audu da se sannan ya saka musu baki ya faWa, Baba Al?ali ya kalli Fatima ya sake cewa
"?arasa ciki gurin iyayen naku, Mamanku Balaraba ma tana ciki tare muka zo"
"Daga nan fa kuma can zamuje, shikenan se muje gidan Baba Abdullahi idan yaso ma saka wata ranar muzo" Ahmad ya faWa. Cikin jin nauyi haWi da kwarjinin su daya dabaibayeta ta mi?e zata fita, Alhaji Audu ya nuna mata ?aramar ?ofar dake cikin falon yacewa Ahmad
"Kwaso mata takalmanta tabi ta nan". Kamar zata kifa haka ta wucesu, Jay ne a gefen hanyar zaman da yayi dole seda mayafin jikinta yabi ta kan fuskarsa kafin ta wuce Ahmad na biye da ita da takalmanta a hannunsa, ya sakar mata peck akan lips Winta kafin ya zube mata takalman yana cewa

"Bari muyi sallah yanzu zamu shigo be sani ba abinda yayi akan idon Jay da Alhaji Audu, tunda ta wuce Jay ya kasa hana idonsa binta da kallo shi kuma Alhajin duk motsinsa akan idonsa yakeyi shiyasa ya lura da kallon daya bi matar yayan nasa dashi.
"Bari muje muyi sallah muna hanya akayi" Ahmad ya faWa bayan daya dawo daga rakata, da sauri Jay ya mi?e dan a ?agare yake ya kuma tsargu da kallon da Iyayen nasu suke binsa dashi.

Bayan fitar su Ahmad Alhaji Audu na kallon Wan uwansa yace
"Wannan yaron akwai abinda yake damunsa ba rashin lafiya bace"
"Yanzu dai mu fara kashe wutar da take a gaban mu kafin mu sake tado da wata, yanzu kai menene maganar ka anan?" Baba Al?ali ya maida shi kan abinda suke tattaunawa kafin shigowarsu Ahmad. Muryarsa na bayyanar da Sacin rai yace

"Ina kan maganata, muddin bincike ya tabbatar sa gaskiya ne abinda aka faWa wlh da hannuna zan basu shi, duk irin Wauke kan sa nayi akan dukiyata dana sha wahala na tara na barsu suke yanda suka ga dama da ita amma hakan beyi masa base ya janyo abinda ze rusa mu? To wlh sedai shida uwarsa da take goya masa baya su WanWani ba?in cikin abinda yake shirin tattagowa, nagodewa Allah daya azurtani da wasu yayan, da ace su kaWai na haifa da yanzu ban kawo haka ba nasan da ba?in cikinsu ya daWe dayin Ajalina"
"Audu kenan, Allah yasa mu dace kawai amma son rai ne zesa ka ringa SaSatu da faWe faWe akan abinda kai ka siyo shi da kuWinka, muyi addu'a kawai Allah ya rufa asiri amma kuskure kam anyi sedai fatan Allah ya duba, yanzu dai ayi ?o?ari a sameshi a waya, wannan gudun da yakeyi Shi ze saka zargi ya tabbata akansa, idan har yana da gaskiya kamar yanda yace ya fito yayi musu bayani ya kuma basu abinda suka bu?ata shikenan hankalin kowa ya kwanta" Alhaji Ali ya faWa. Baba Al?ali yayi murmushi domin kuwa harbi ne bayan hari ?anin nasa yakeyi, daman duk wanda ya siyi rariya ai yasan zata zubda ruwa,

"Idan suka kama uwarsa ai ze fito daga duk inda ma ya Soye ko?" Alhaji Audun ya sake faWa cikin Sacin rai.

A cikin gida kuwa kamar jariri sabuwar haihuwa haka Hajiya takr ririta Fatiyyah, abinci dana sha babu adadi tasa aka jere mata, tun safe da Jafar yace mata zasu zo ta aksa zaune ta kasa tsaye, tun Hajiya ?arama data yiwo yaji na tayataharta zame dan abin Hajiyar ya wuce na hankali ko yanzu ranta a cukule da yanda Hajiyar take ta rawar jiki da Fatiyyan ita kuma se wani yatsina take tana gwalangwaso, yanda ta amsa mata gaisuwar data mata a watsene ya tunzurta ta fice ma ta bar musu falon tana ji Hajiyar na kiranta akan tazo ta zubawa Fatiyyah abinci ta share dan tsaf zata iya sharara mata mari idan taci gaba dayi mata kallon rainin da take mata, badan zubar da kai irin na Hajiya ba a gidan Audu Bechi har Fatiyyah wata abar tsiyace? Duk rawar kanta seda ta tsinewa shigar Fatiyyan a matsayin ta na musuluma matar aure kuma wadda tazo gaida surukanta, a tsakar gida ta haWu da Fatima suka sakarwa Juna murmushi.

Tun washe garin da aka kawo su sukaje musu gaba Wayansu harda yayan gidan Baba Al?ali kafin kowacce ta wuce garin da take aure amma tana ganinta ta ganeta saboda fara'arta.
"Sannu da zuwa Matar Yah Ahmad" Hajiya ?araman ta faWa tana mat side hug, suka gaisa a mutunche kafin tace mata
"Muje na rakaki gurin Momy dan nasan tsayuwar da kikayi a nan kin kasa tuna inane part Winta ne" murmushi Fatima ta sakeyi suna fara tafiya Hajiya data gaji ta kiran Hajiya ?arama ta le?o, smoothie tasa ta haWawa Fatiyyah koda zata so abu me ruwa ruwa to yanzu ta kalli duk abinda aka girka tace basu mata ba bata ci an duba fridge Win kitchen kuma ba'a ganshi ba, ashariya me mai?o ta lailayo ta direwa Hajiya ?aramar, Fatima ta zabura dan kamar dirar aradu muryar Hajiyar tazo mata dan haka ta rikice ta shiga gaisheta

"Bakaniken ubanki da wannan koWaWWiyar sadakayallar nan kika gaida a tsaye, ke kuma zakizo ki Wakko mun abinda na sakaki ko se nici uwarki tukunna" ta juya kan Hajiya

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login