Showing 447001 words to 450000 words out of 467220 words

Chapter 150 - MATAR MUTUM COMPLETED 1-3 BY MARYAM FARUK.doc

23 Sep 2025

12111

yawa zancen referal da ake ta faWa shi yake saryar muku da guiwa da shiga META FORCE, to bari kiji yar uwa idan har kinyi register cikin Team me karfi tamkar na MAMAN NASREEN zaki dara. Team ne dake Wauke da mutane da suka daWe da wayewa a digital marketing. Bakya bu?atar lallai se kin kawo referals kafin spill over ta tarar dake sedai idan kin so kiyi sharing abin alkhairi daya sameki tareda yan uwa da abokanan arzi?i. Ga yanda tsarin yake*

*META FORCE*

*A yanzu babu wani business dayake bada kudade a duniya yanzu irin crypto currency, akwai Project dayawa acikin META FORCE wanda akayi lunching da wadanda ba ayiba amma za ayi nan bada jimawa ba. Guda uku da aka rigada akayi lunching sune*
*TACTILE*
*Uniteverse*
*Royalty Nft*
*1 Tactile : matakin farko kenan dole idan zaki shiga meta force sai ka arayin registration a tactile sannan zakasamu damar shiga kayi joning sauran programs din. Tactile yanada levels guda 12 kowane level da kudinshi*
*Level 1 5 dollars*
*Level 2 10 dollars*
*Level 3 20 dollars*
*Level 4 40 dollars*
*Level 5 80 dolllars*

*Spillover*da*over flow*
*Sune kuWin da kamfani yake biya na aikin da team sukayi, hajiya kina zaune ko baki kawo kowa ba spill over zata tarar dake idan har TEAM Winki is active ma'ana suna aiki sosai kamar dai team Win MAMAN NASREEN, abun kuma yana ?ara armashi idan ya zama kema kin kawo wani yayi register a ?asan ki amma fa ba dole bane, kowa ya sani dai ko wanne kasuwanci yana ci gaba ne daga yawan traffic da yake akansa dan haka yawan jama'ar team Win ku yawan yanda kamfani zatayi appreciating naku ta ringa watsa muku ruwan spill over kamar a August*
*Uniteverse*
*idan kashiga uniteverse munada tier 1 to 9*
*Tier 1 50$*
*Tier 2 100$*
*Tier 3 200$*
*Tier 4 400$*
*Tier 5 800$*
*Tier 6 1600$*
*Tier 7 3200$*
*Tier 8 6400$*
*Tier 9 12800$*

*Royalty* NFT

*level 0-Zero NFT*
*level 1-Activator*
*level 2-Supervisor*
*level 3-Manager*
*level 4-Pro-manager*
*level 5-Pacesetter*
*level 6-Ambassador*
*level 7-Millionaire s club member*
*Masu NFT ana biyansu albashi duk wata wani lokacin ma sau 2 a wata kuma salary dinka yadanganta da level Win da kake*
*Nasan yan baiwa sun san me ake nufi da NFT kati me daraja kenan wanda shi kaWai idan kika siyar ze kawo miki kuWaWe da se kinyi kukan farin ciki ga wadda ta shirya bin jirgin tsira jirgin Alkhairi ta tuntuSe mu kai tsaye akan 09046470308*
*META FORCE tafiyar da babu nadama da yardar Allah*

*MATAR MUTUM*
*NA MARYAM FAROUK (UMMU MAHEER*

*FIKRA WRITERS ASSOCIATION*

*LITTAFIN KUDI NE*
*PAY 500 A ASUSUN*
*7061838488*
*OPAY DIGITAL SERVICES*
*MARYAM FAROUK*
OR
*0709290797*
*ACCESS BANK*
*SE A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488*
*IDAN KATINE A DAUKI HOTONSA A TURA ZUWA LAMBAR SAMA VTU KUMA A TURA A 08142548705*

*Kuyi following dina a Arewabooks @Maryamfarouk01 inda zaku karanta wannan littafin tareda sauran littattafaina*
*NAGODE*

*BOOK 3*
*PAGE 46*

A falo ya samu Alhaji tare da Hajiya Rabi bayan ya raka hajiyar Wakin ta. Suka gaisa da Antyn tana tambayar sa me jiki tace ai basu san yau ki za'a sallamota ba dan yanzu suke shirin sake zuwa su dubata ma, ganin kamar magana yake so suyi da Alhajin yasa ta fita ta basu guri. Alhaji Audu yaci gaba da duba takardun gabansa kamar baya sauraron Jafar dake masa magana har seda yaji yayi shiru kafin ya Waga kai ya kalleshi yace
"Ya ka dakata?" Jafar yayi ?asa da kai ba tareda yace komai ba, Alhaji yayi ?wafa yace
"Wato kai koda yaushe laifina kake gani akan lamarin uwarka kenan. Kai baka san saboda zaman tare da zuri'ar dana duba yasa na barta haka ba? Wlh da ace nabi ta zuciya da ce musu zanyi harda ita a harkar suje can su gar?ameta har ?arshen zamani amma banyi haka ba, na nema mata sassauci amma shine saboda baka da kunya zaka zo kana mun wasu surutai na saketan idan da abinda zaka iya bismillah". Shiru Jay yayi kansa a ?asa, tabbas yasan Alhaji yana ha?uri amma ya zata tunda har ya iya jure shekarun baya me yasa ya kasa yi mata uzuri yanzun da ya tabbatar ba zasu maimaita zaman da sukayi a baya ba? A hankali yace

"Kayi ha?uri Alhaji ba abinda nake nufi na kenan ni tunanina"
"Ka adana tunaninka wa kanka kai kaWai kaji, ni yanzun tattala lafiyata nakeyi dan haka kayi ha?uri ka barni karka janyo abinda zan Sata maka rai. Kuma yarinyar da kaje ka aje hotel ba zaman kanta takeyi ba, ka nema mata gida ta tare kamar kowacce macen aure idan kuma huWubar uwarka ce take tasiri akanka ka sawwa?e mata ta nemi miji da ze ri?e ta tsakani da Allah, duk ni na ja mata dana tilasta ka ka aureta shiyasa ka ?i bata daraja irin ta kowacce macen aure. Ita kuma Binta bani da damuwa da ita, taci gaba da zama a Wakinta kuma duk wani abu dana saba yi musu baza'a cireta daga ciki ba, kawai dai ku ja mata kunne ta kama kanta bana son tashin hankali ko wani jidali a cikin gida na yawwa" Alhaji Audu ya faWa daga nan ya wuce sama ya bar Jay a zaune cike da mamakin ya akayi yasan ya aje Afeeyah a hotel? Wato lamarin Naziru ya koya masa hankali kenan bibiyarsu yakeyi duk inda suka shiga. Jiki ba laka ya bar gidan. Yana hanya Fatiyyah ta kirashi, harya koma hotel Win suna waya tana ta nanata masa yanda tayi missing Win sa tareda surprise Win da tace zata zo masa dashi goben.

Ya daWe zaune a mota har kusan sha Waya suna waya kafin sukayi sallama ya fita, zuciyarsa cike da tunanin abinda ya kamata yayi ya isa Wakin. Fathiyyah zata dawo, kenan dole ze raba kwana tsakanin matan nasa yanzu tunanin sa yanda zeyi da Afeeyah. Yanzu dai da kunya yace ta koma gidansu ya ringa musu zarya yana Waukar ta kuma idan yace taci gaba da zama a hotel har a kammala gyaran gidan shima be mata adalci ba, idan kuma yace ta tare a gidan da Fathiyyah take nan ma se ya zama wani abu, kamar ya shiga ha??in kowacce a cikinsu. Tunanin abinda yakamata yayi ya ringayi amam ya rasa option Win ?arshe kawai ya gani a matsayin mafita tunda gidansa ne, kuma duka matansa ne inda ace bashi da wadatar raba musu muhalli ko samar musu wanda yafi wannan Win yalwa ai a hakan zasu zauna. Da wannan shawarar yayi na'am.

Sanda ya shiga Wakin ya tarar da har tayi bacci ga dai abinci nan ta ajiye masa da alama gajiya tayi da jiransa tayi baccin se kuma yaji babu daWi. Haka ya cuccusa abincin saboda yunwar da yakeji ya kwanta bayan daya jata jikinsa, Wumi ko yace zafin jikinta ya ringa ratsashi tun yana masa daWi harya fara damunsa ya shiga tunanin kodai zazzabi takeyi dan a kwanakin dama temperature jikin nata tana zarce ta baya hawa amma kuma dayaga baccinta take yi hankali kwance se kawai ya Wauka ko sanyin Ac ne yasa dan haka ya rage musu kafin ya samu bacci ya Wauke shi.

Washe gari tunda sukayi sallar asuba su ka dan wujijjiga juna kafin suka koma bacci se guraren goma da wani abu Afeeyah ta fara farkawa dalilin wayarsa dake ta ?ara kafin ta duba wayar ya farka shima haka yasa ta wuce banWaki kawai shi kuma ya Wauki wayar. Ya buWe ido ganin missed calls Win Fatiyyah har biyar, seda ya kalli ?ofar toilet Win ya tabbatar ta rufe kafin ya kirata. Murya can ?asa yake magana saboda karta jiyoshi, daga can Sangaren cikin fushi Fathiyyah take tuhumarsa dalilin ?in amsa wayarta.
"Mun sauka na fito ban ganka ba bayan kace zaka zo ka jira saukar mu" ta faWa. Ya dafe kansa, shaf ya mantada sunyi wannan maganar shi ya manta ma jirgin safe zata biyo dan yace ta bari seda yamma ita kuma tace ba zata iya ba all his thoughts was zata ha?ura seda yamman ashe har ta tawo. A hankali yace
"Kiyi ha?uri, bacci ne yafi ?arfina i just woke up to your call".
"Kawai saboda baka bani muhimmanci bane shiyasa ka kwanta kayi bacci amma da kasan zanzo ai da kayi sallah be kamata ka koma bacci ba" ta shiga mita. Ha?uri ya sake bata kafin yace
"Why not ki hau cab kawai ta kaiki gida? Kinga zan Sata lokaci yanzu banyi wanka ba and it's kind of far daga inda nake zuwa airport kinga kar kiyita tsayuwa babu daWi".

Kuka ta fasa masa ba shiri ya shiga rarrashinta tana faWin ai da Fatima ceko daga birnin SIN ne ze taho ya Wakkota. Duk yaji babu daWi, baya so ya bawa kowacce impression Win yafi girmama bu?atar Waya akan tata domin shine mataki na farko na janyo rashin daidaito tsakanin mata hakan yasa yace mata gashi nan. Ya dafe kansa da hannu biyu bayan ya kashe wayar kafin ya yun?ura ya tashi caraf suka haWa ido da Afeeyah da tun fara wayar tasa ta fito daga banWakin dan daman fitsari ne ya matsata. Tayi masa kallo Waya kafin ta wuce ?aramin fridge dake cikin Wakin ta buWe ta Wauka madara duk se ya duburburce ya rasa me ze ce mata tunda dai yasan taji duk wayar da yayi daga yanayin dirty look Win data masa. Ganin tayi banza dashi tayi zamanta tana kurSar madara me sanyi yasa ya ari jarumta ya yafa ya tashi yana wani basarwa ya shiga wanka. Afeeyah ta shiga Wauke hawayen da suka fara mata zarya akan fuskarta, wato matarsa zata dawo amma shine be gaya mata ba to wai ita a me ya Wauke ta nema? Ya kama ace tasan wannan amsar. Tashi tayi ta shuga haWa kayanta a akwati tunda matarsa ta dawo ai nata zaman ya ?are, tana zuge akwatin ya fito daga wanka bata bari sun haWa ido ba ta shiga cire kayanta ta zubar dasu nan tsakiyar Wakin kafin ta raSe shi ta shige banWakin tana jin yanda ya bita da idanu amma bata nuna ta sani ba, tana wankan tana kuka. Ranta ya ?ara Saci sanda ta fito ta tararda baya Wakin se ?amshin turarukan sa daya bar mata.

Cikin fushi ta shirya zuciyarta har wani tu?u?i take mata taja akwatinta ta nufi ?ofa sedai duk yanda tayi ta buWe ?ofar ta?i bata haWin kai kawai seta zauna a gurin ta fara kuka. Wato kulle ta yayi baya ko tunanin wani emergency ya iya tasowa ya rufeta a Waki ita kaWai. Seda tayi kuka ta gode Allah kafin ta kwanta a gurin bacci ya kwasheta.

Zuciya babu daWi Jay ya bar hotel Win bayan ya kulleta ta waje ya kuma tafi da key Win dukda yasan hakan be kamata ba amma bashi da wata hanya da ze hanata tafiya idan kuma yace ze tsaya yi mata bayani yanzu ?ara complicating abun zeyi, yasan ba zata fahimcr shi ba sannan itama dake can tana jiransa ya sake kunno wata matsalar. Ya?e kawai ya ringayi yana biyewa Fatiyyah har suka isa gida. Be san yayi kewarta ba shima seda suka keSe, duk da dai wani abun sedai kawai a barwa zuciya dagaske yanzu ya fahimci abinda ake nufi da aka ce mata suna suka tara, akwai mace akwai kuma muna mata amma dai baze furta ba balle ace yace =??=??.

Yanda Fatiyyah ta ringa kanainayeshi ya shagaltar dashi be ankare da lokaci ba seda aka kira azahar. Dakyar ya samu ta barshi ya fita sallar daga masallacin kuwa jikinsa har tsuma yake ya kama hanya hankalinsa gaba Waya ya koma kan Afeeyah. Ya buWe Wakin a hankali ya shiga, tana zaune akan darduma hannunta ri?e da carbi tana ja. Kamar wani mara gaskiya haka ya ?arasa ciki da sallama yana ?o?ari dakewa irin karta kawo masa wargi. Ya zauna kan kujera yana kallonta. Seda ta shafa addu'arta kafin ta kalleshi babu yabo babu fallasa tace
"Sannu da zuwa". Kunya haWe da nauyi suka rufar masa, be yi tunanin zata tarbeshi da lumana haka ba, a hankali ya mi?e ya Wago kafin ya rungume ta a jikinsa murya can ciki yake cewa
"I'm sorry love, kiyi ha?uri kinji. Bana so zuciyarki ta sosu shiyasa na kasa gaya miki yau zata dawo".
Tayi murmushi kawai tana ?o?arin zamewa daga jikinsa ya saketa suka zauna still ya kama hannunta yana murzawa yace
"Say something mana bana son shirun nan"

"Ta dawo lafiya? Ina mata sannu da zuwa" ta faWa ba tareda ta bari sun haWa ido ba, yasake janta jikinsa yana murmushi yace
"Fushi fa baya miki kyau Afifi ki Wanyi murmushi mana ko naji sanyi, haba babylove, my zuma, my kinfi sugar" ya ?arasa yana tsunkulinta a ciki dole tayi murmushi badan taso ba, ita kaWai tasan abinda kecin zuciyarta kishinsa nr fal, musamman da ta sha?i wani ?amshi bayan wanda ya fita dashi daga jikinsa kawai daurewa takeyi tana gayawa zuciyarta gurin matarsa yaje dama kuma ba nata bane ita kaWai, bama itace asalin me shi ba saura ta samu. Rungume ta yayi ya shiga ?o?arin haWe bakinsu bata hanashi ba amma bata taimaka masa ba ya saketa fuskarsa na nuna damuwa yace
"Karki Wauka wannan halin please bazan iya jurewa ba karkizo kina zargin na juya miki baya. Kamata yayi ki ?arfafani nayi adalci a tsakanin ku, idan kika bari sonki yayi tasiri akaina muka shiga ha??in ta Allah baze barmu ba" yana gama faWar haka ya wuce cikin Waki ya barta tana binsa da kallo.

Wato idan har ana neman blackmailer aka samu Jay a tsaya iya haka, yasan takan lauya zance yasa ka zargi kanka akan abinda baka aikata ba. Yanzu tsakani da Allah saboda ta nuna kishin ta akansa shine zece tana so ya fifitata ne akan matarsa ko kar yayi adalci a tsakaninsu? Lallai halin Jafar case study ne me zaman kansa. Kusan minti goma da shigarsa Wakin kafin ya fito ya canza kayan jikinsa zuwa short da armless shirt ya wuce ?ofa ya buWe sannan ya dawo gurinta da tryn abinci. A ?asa ya zauna fuska ba wasa yace ta sauko, bata musa ba dan yunwar takeji ko karyawa batayi ba tunda ya fita ya shiga bata abincin a baki loma uku tayi tace ta ?oshi dan ji tayi abincin ya tsaya mata kwata kwata cikinta be karSe shi ba. Ya tashi ya haWo mata tea da zallar milo kamar yanda tace shi tasha da cookies bayan sun gama suka kwanta shiru yana wasa da ?ananun kalbar dake kanta. A hankali yace mata
"Ina tunanin zaki fara zama can gidan for now".

"Wane gidan?" Ta tambaya tana kallonsa, ya shafa fuskarta yace
"Gidan da Fathiyyah take. Seki zauna a dakina just for a mean time kafin a gama gyaran inda zaki zauna".
Strictly tace
"No". Ya juyota suka fuskanci juna yace
"I have no option for now, ba daWewa zakiyi ba fa, just few days kafin mu koma UK. Bansan ya akayi Alhaji yasan muna nan ba yayi mun magana idan kuma banyi wani abu ba kinsan halinsa se yace na?i jin maganarsa" banda "hmmm" babu abinda tace masa ta juya masa baya babu daWewa kuma bacci ya kwasheta a jikinsa. Seda aka kira la'asar kafin ya kwantar da ita ya sake wanka ya fita bayan ya barmata short note akan ta shirya idan ya dawo zasu fita. Tana idar da sallah taci abinci sannan ta kira Anty Sauda, bata rage komai ba ta gaya mata dawowar Fathiyyah da abinda yace. Anty Saudan tace mata
"Babu wannan maganar, ko ze haWa ku gida Waya badai irin wannan zaman ba. Wannan ai cin fuska ne ma a gurinta ita Fathiyyah, indai be shirya inda zaki zauna ba ki dawo gida kawai. Shegen zirgillin ki ya ja miki ai, ba jan aji ba komai kika kama kika bishi ai gashi nan, dama illar mace ta bawa miji kanta kenan kafin ta tare, wula?anci se wanda kika gani tunda ya rigada ya samu abinda yake marari".

Ita dai tayi shiru dan bata da bakin kare kanta. Biyar da rabi ya dawo tana kwance bacci na neman yafi ?arfinta yace ta tashi su fita. Sukuku take jinta, Hijabi kawai ta zura akan doguwar rigar jikinta a mota ya ringa mata mitar wai duk kishi ya saka a yini Waya ta firgice. Ya ringa cewa wai fuskarta tayi fayau ?ila da tayi wanka ko mai bata shafa ba waya mutu waya tashi ita dai jinsa kawai takeyi bata ce masa ?ala ba har suka isa Sokoto road, ta ringa kallon gidajen da suke wucewa a layin daya shiga har suka isa ?ofar wani gida da shi kaWai ne ba'a kammala a gidajen dake layin ba. Ta ringa kallon ginin a zuciyarta ta yabawa architecture daya zana ginin yayi ?o?ari taswirar gidan ta fita babu kwalliya ta hayaniya ko ?yale-?yale gini ne na masu aji da baka bu?atar a gaya masa naira tayi kuka kafin samuwarsa. Seda ya daidaita tsayuwar motar kafin suka fita tana biyr dashi a baya har suka shiga compound Win gidan da be cika girma sosai can amma yana da yalwa dan a kalla ze Wauki motoci shida zuwa sama. Kai tsaye suka shiga main building Win gidan ?aton falo yayi musu maraba, wani irin gini akayiwa falon tamkar palace, tsayin katangarsa tsayin ginin gidan gaba Waya daga sama har ?asa ga matakalar bene a tsakiyarsa guda biyu sun harWe juna. A cikin falon akwai ?ofofi guda uku. ?aya daga hagu, Waya dama se guda daya daga can gefe ga kuma wata ?ofar glass ta Sangaren inda take zaton dining area ne ?ofar kuma ta kitchen. Kusan an gama komai na falon harda penti se Wan abinda ba'a rasa ba.

?ofar dake hannun dama ya buWe suka shiga, part ne guda a gurin me Wauke da bedroom guda uku da kitchen se wani ?aramin Waki da za'a iya yin falo dashi ko study room. Tana tsaye ya gama magana da ma'aikatan dake ?arasa penti kafin ya kalleta yace
"Gurin yayi miki?"
Tayi murmushi tace masa
"Yayi" to idan ma beyi ba me yake tunanin zata ce?.
Sama suka hau nan ma part biyu ne komai iri Waya two bedroom da parlour wanda yake ta Sangaren part Win da suka shiga na ?asa yace nata, daga nan suka shiga wani Waki da gaba Wayansa akayi shi da glass, ta buWe baki tana kallon bayan gidan da mamaki ta cikin glass Win. Bayan garden da swimming pool harda mini football pitch daga

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login