Showing 69001 words to 72000 words out of 467220 words

Chapter 24 - MATAR MUTUM COMPLETED 1-3 BY MARYAM FARUK.doc

23 Sep 2025

12394

yayi wanka ya shirya, kai tsaye gidan Ali ya fara zuwa suka hade a waje Alin na shirin fita ya kuma tabbatar masa Binta bataje gidan ba dan babu inda zata buya da ze kasa ganinta.
"Dan girman Allah kazo ka rakani Kaduna" ya roqi Alin
"Kai yanzu? Ina babu wannan magana, ai yanda ka tirko rigimarka se ka san ta yanda zaka kasheta. Amma fa ban taba dauka da gaske kaci kai ba Audu se yanzu, duk matan da suke garin nan yayan mutunchi ka rasa wadda ta burgeka se wannan yarinyar? Kodai Asirinsu tayi amfani dashi ta zarge zuciyarka?" Ali ya fada yana tsareshi da ido. Audu yaja tsaki kafin ya shige mota ya daga ba tare da ya bashi amsa ba

Yau dinma Musbahu yaje ya dauka suka tafi Kaduna, seda ya isa qofar gidan kuma ya fara tunanin me zece musu idan ya shiga? Seda sukayi sallar La'asar da Magriba da suka riskesu a hanya kafin ya saka kai cikin gidan. Ko ina tarwai da haske, Tun daga Get suka fara gaisawa da ma'aikatan gidan harya isa qofar falo. Ta ciki Munira ta hangoshi, ta kwasa da gudu tayi daki ta fadawa Binta da tunda tayi wanka taci abinci take rama baccin da batayi jiya ba.
"Wlh ko me za'ayi karki koma ai raini nema kamar ke ace a miki kishiya bayan duk fafutukar da daukar hakkin da mukayi muka fitar da waccen shine za'a dakko miki alaqaqai to babu wannan maganar" Muniran ta qara zugata.

Tun daga yanda Alhaji ya amsa masa gaisuwarsa yaji guiwoyinsa sun qarayin sanyi dama Mama tana musu iso a tsayw suka gaisa ta shige ciki, yau ko Kayan Alatun da ake tarbarshi dasu be samu ba Ruwa da Lemo ma Alhajin ne yayi magana aka kawo musu.
"Bansan ta taho ba Alhaji, na dawo daga sallar Asuba kawai na tarar bata nan" Audu ya fada bayan dogon shirun da sukayi kowanne kamar ya rasa abin fada.

Alhaji ya nisa yana kallonsa yace
"Me ya hadaku da har yasa ta baro gidan ba tareda saninka ba?".
Be boye masa komai ba ya bashi labarin Auran da yayi wanda yake ganin shiya tunzurata ta baro gidan, ya rufe da qaryar cewa
"Bansan cewa zasu daura Auran ba saboda tambaya kawai akaje".

Shiru Alhaji ya sakeyi yana kallonsa kafin yace
"Menene gaskiyar maganara data fada na cewar Yarinyar Karuwa ce?" Seda ya daga kai ya kalli Alhajin saboda kalmar daya fada din se yaga kamar tayi girma musamman ana maganar matarsa ne ina laifin yace tsohuwa, wannan ya tunzuro zuciyarsa ta raya masa ci masa mutunchi Alhajin ya tashi yi amma ya danne dan ko ya masa qarya bashida amfani tunda har magana ta fito amma a ina Binta taji wannan batun?

"Kayi shiru" Alhaji ya katseshi, kansa na qasa yace
"Gaskiya ne, amma ban aureta ba seda na maidata gaban iyayenta tayi Istibra'i kamar yanda shari'a ta tanadar"

"To akan me ka daki Mamana har kaji mata ciwuka a jiki?" Alhajin ya fadi ainihin abinda yafi damunsa a duk cikin maganar, se Audu ya daga kai da sauri ya kalleshi jin abinda ya fada.

"Wlh Mari daya nayi mata, shima kuma cin kwalata tayi a gaban yan uwana da sukazo fadamun an daura aure ta labe harta tsinci maganar shine ta shaqemun wuya nace ta sakeni taqi ni kuma zuciya tasa na mareta bayan nan ko yatsa ban nuna mata ba wlh" ya fada cikin kare kai. Alhaji bece komai ba yaja Intercom ya kira cikin gida kan Binta tazo, ba'a dauki lokaci ba ta fito tana jan qafa fuskar nan kamar dafaffen Kunu ta zauna kusada qafar Alhajin tana hararar Audu wanda ke kallonta yana mamakin abinda ya karceta a fuska kamar sunyi dambe da Mage.

Ce mata yayi ta maimaita duk abinda ta fada cewar Audu ya mata, tana kuka ta shiga shiryosu harma da abinda dazun bata fada ba na cewar daman Audun ya dade yana yawon ta zubar dinsa har kwanaki yake tafiya yayi acan in ya dawo kuma tayi magana ya zageta koya hada mata da duka qarshema tace idan ta fita har gidan yake kawo mata shidai kasa cewa komai yayi saboda mamaki, maganganunta kuma babu yanda za'ayi ace qarya takeyi tunda tabbas yana yawace yawaceb har yaje ya kwanan amma ai ba abinda take fada yakeyi ba sedai kuma waye ze bada shaidar hakan?

Shidai Alhaji na jinta yana kuma kallon Audu daya kasa rufe bakinsa seda tayi shiru kafin ya kalleta yace

"Kinaji ko Mamana, duk wani Aure da kika gani tattare yake da qalubale muddin kuma ba ma'aurata sun bude cikinsu ba bazaka taba sani ba dan haka kowa haquri yakeyi kamar yanda kika faro haqurin kici gaba dayi kuma tunda ya auro yarinyar da take dauke masa hankali a wajen ai magana ta qare se ayi fatan kuma Allah ya hada kanku ya bada zaman lafiya. Kaikuma abinda nake so na gaya maka shine ka tabbatar kayi na farko kuma kayi na qarshe da zaka dora hannu da sunan duka a jikin Mamana, zan manta da duk wata alaqa dake tsakaninmu na maka ka a Kotu domin bana hada kowa da yayana, ban daki yar kowa ba dan haka babu hujjar da zata saka wani ya dakar mun yata. Idan tayi maka laifin da ba zau iya sasantawa a tsakaninku ba ka kawo mun qararta nizan hukuntata amma bazan lamunchi duka ba ina fatan ka gane?"

Kunya, nauyi da takaici suka rufe Audu gaba daya ya rasa ma abinda zeyi, Alhaji yaci gaba da cewa
"Idan Allah ya kaimu gobe yanda kikazo da sassafen nan ki tattara ku koma aje aci gaba da haquri kuma na kashe maganar nan, Aure kuma dakayi Allah ya sanya Alkhairi ya baka ladan Jihadi"

"Wlh bazan koma ba, babu yanda za'ayi nayi zamab kishi da Karuwa Dady kawai kace masa ya saketa idan ba haka ba bazan koma gidan ba" ta fada cikin kuka tana bubbuga qafa.https://chat.whatsapp.com/I8xKHGurk7EBf5ZqQdxHKG

*MATAR MUTUM*
*NA MARYAM FAROUK (UMMU MAHEER*

*FIKRA WRITERS ASSOCIATION*

*LITTAFIN KUDI NE*
*PAY 500 A ASUSUN*
*7061838488*
*OPAY DIGITAL SERVICES*
*MARYAM FAROUK*
OR
*0709290797*
*ACCESS BANK*
*SE A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488*
*IDAN KATINE A DAUKI HOTONSA A TURA ZUWA LAMBAR SAMA VTU KUMA A TURA A 08142548705*

*Kuyi following dina a Arewabooks @Maryamfarouk01 inda zaku karanta wannan littafin tareda sauran littattafaina*
*NAGODE*

*PAGE17*


Badan Audu yaso ba sedan Yaya Baba dayace muddin ba sanarwa da Yakubu ba bazasuje masa neman Aure ba tilas ya kirashi ta wayar Landilayin wadda ya hada a gidansa shima kuma Yakubun suna da ita a Ofishin da yake aiki dan haka ya kirashi.

"Allah ya sanya Alkhairi yasa ayi a sa'a" abinda Yakubun ya fada masa kenan bayan daya shaida masa zancen Auran se kuma yaji babu dadi dan haka yace masa
"Amma zaka zo ko? Saboda ina tunanin a daura Auran kawai idan an kai kudin"
"Ina da Ayyuka da yawa a gabana bana jin zan samu halarta sedai daga baya nazo naga Amarya amma a ina ka samo matar?" Yakubu ya tambayeshi, Audu yayi shiru kamar mara gaskiya kafin yace

"Amm yar nan cikin gari ce unguwar Alkantara, yarinyar nada hankali da nutsuwa sosai se ka ganta ma"

"Amma da zan baka shawara ka dauka da nace kayi haquri ka maido da Bara'atu kodan darajar yayanta ka dubi rayuwar da zasuyi a Bechi babu wadataccen Ilimin Islamiyy ada Boko"

"To ya kake so nayi da wannan din bayan na sanarwa da Iyayenta zan turo so kake na zama qaramin mutum?" Audu ya fada a dake dan ya gaji da maganar ya maido Bara'atu da suka dameshi da ita, Yakubu yayi murmushi yace

"Bance ka fasa ba kana iya hadasu su ukun ai Alhamdulillahi Allah ya hore maka abinda zaka iya riqe su nidai yaranka nake dubawa saboda zuwan nan da nayi na gansu banji dadin yanda suka koma ba gashi sun fara tasawa"

"Naga muma a Bechin nan aka haifemu muka girma, yanzu kai bada shekarunka ba harda Aure ka kammala sakandire ka tafi Jami'a? Suma idan sun girma sun kai munzalin da zasu iya wahaltawa kansu se su dawo nan gidan su zauna yanzu dai ba wannan maganar mukeyi ba ka daure dan Allah kazo kasan dai nan duniya bani da kamarka" Audu ya fada. Yakubu yayi dariyar takaici yace

"Zanyi maka Addu'a daga nan kuma da ace abinda ka fada da gaske be baka da kamata da baka qi karbar shawarata ba muddin ba cutar da kai nayi niyya ba, yanzu ina aiki ne zamu sake magana idan na samu lokaci" daga haka ya ajiye waya ya bar Audu sororo da waya a hannu seda ya kashe ma sannan ya tuna dayar maganar da yake so ya masa ta jin dalilin daya saka ya dauki Baballiya ya tafi da shi Lagos zeyi hutu ba tareda su. Sanar masa ba seda sukayi magana da Alhaji Zakariyya yake gaya masa dan a gidan Baballiyan yake zama idan sun samu hutu yanzu haka yana ma yana shekararsa ta qarshe shirye shiryen fita sukeyi.

Duk yanda Audu yayi da Yakubu akan yazo Auransa qi yayi dole ya haqura badan yaso ba kuma har ransa yaji rashin jin dadin hakan saboda bashi da tamkar Yakubu sannan ya rasa abinda yasa Yakubu ya dauki wannan fushin dashi. Yanzu kenan yana so ya nuna Bara'atu ta fishi a gurinsa kenan?
Haka nan ya tura su Yaya Baba da wasu Abokanansa sukaje masa neman Auran wanda ba'a tashi daga gurin ba seda aka daura shi. Yana gida ranar be fita ba yana tsammatar dawowarsu Binta natayi masa gwalgwaso ta aje wannan ta kawar da wancan surutu kuwa har kunnensa ya gaji ga babu halin yace tayi shiru ko ta fita ta barshi ya huta.

Lantana ce ta kwankwasa musu qofar saman, rawar kan matar ya zarce misali seda Binta ta taka mata burki sannan ta dena zirgillin shigar mata turakar Miji. Bintan ce ta bude qofar ta leqa fuska a hade tana cewa
"Meye? Wai sau nawa zanja kunnenki akan tako benen nan ballantana kiyi tunanin shiga dakin nan? Ke wace irin daqiqiyar mace ce ne Lantana?"

"Kiyi haquri Hajia, baqi kukayi shine nace bari nazo na sanar miki" Lantana ta fada cikin qasqantar da kai amma a ranta zagin Binta takeyi.

Binta ta yatsina fuska tace "Baqi kuma daga ina? Ni yau babu wan???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?da babu wanda nayi da ita zatazo"
"Ai Hajiya Maza ne ba mata ba kuma kamar yan Uwan Alhaji ne dan naga wasu suna yanayi dashi"

Tsaki me qarfi Binta taja, ta tsani wannan zaryar maukar da yan uwan Audu suke musu. Ba'a rufa sati se wani yazo daga Bechi badan ta taka burki bama har kwana suke so su ringayi amma duk zatayi maganinsu dan ba zata dauki wannan abun ba suzo su dabaibayeshi su cinye musu dukiya to bada ita ba. Ciki ta juya ba tareda tacewa Lantana komai ba, Audu na kwance kan kujera tace

"Kayi baqi"
Da gaggawa ya miqe kamar wani mara gaskiya, be ko tambayeta su waye ba ya shige daki ya zuro rigar wandon jikinsa ya sauka qasan seta bishi da sauri dan se anyi komai a gabanta. Haka take duk sanda yan uwansa suka zo seta kasa ta tsare komai zasu fada ko ya basu seta gani idan akayi dace kuwa saqo ya biyo ta hannunta daman se abinda mutum ya gani. Qannensa Mata dai da suke ciki daya tun fitar Bara'atu babu wadda ta sake taka qafarta gidan se yan dakin Goggo Maryo ne suke zaryar zuwa ko gajiya basayi da wulaqancin Binta dan Mazan sun fisu kamewa da wadatar zuci muddin sukaje to dole ce ta saka ko kuma maganar Gonarsa wadda Aminu da Yaya Baba ne suke kula masa dasu yanzu.

Bayan Audu ya sauka qasa a tsakar gida ya tarar da Baqin nasa a tsaitsaye.
"Bismilla muje can falon" ya fada yana musu jagora zuwa falon da Bara'atu ta fita can ya gyara ya saka kujeru yake sauke baqinsa amma haka Binta zata bisu har can din. Suna zama tana shiga ko gyale bata yafo ba ta dirirce ganin harda Yaya Baba ko babu komai shidin babbane a cikinsu yanayin rayuwa yasa take ganin kamar ma ze girmin Dadynta dan wahala tasa tsufa ya masa sammako banda yanzu da Al'amura suka fara daidaitar musu ya dawo hayyacinsa dalilin Alkhairan da yake samu daga kula da Gonar da yakewa Audu amma da kam anji jiki ga tarin iyali ga Abinda suka Dogara dashi na Noma Hashimu ya ringa Ha'intarsu yana Azurta kansa su da wahala amma shine cikin walwala da jin dadi wannan ya saka suka yada makaman yaqinsu suka rungumi su Audun hannu bibbiyu gashi kuwa suna sharbar romon damakaradiyya har ya sauke farali a dalilin hakan.

"Au kune sannunku da zuwa ina wuninku?" ta fada tana jada baya tareda sunne kai, suka amsa mata a tare, ta tsaya daga qofa bata fita ba bata shoga ciki sosai ba Audu ya kalleta yace
"Kawo musu ruwa mana"
"Ayyo toh, bari a kawo" ta fada ta juya tana dannan masa Ashar a ranta. Mairo ta kwalawa kira ta gaya mata ta kawo ruwa tayi sauri ta koma bakin qofar ta labe.
"Munje kuma Babanta ya sanar mana da daman kun gama magana shiyasa bamuyi gardama ba dayace a Daura auran, to Alhamdulillahi anyi komai kamar yanda shari'a ta koyar yanzu ya rage kuma ka saka ranar da matarka zata tare, Allah ya sanya Alkhairi ya sa Abokiyar arziqi ce" Yaya Baba ya fada.

Ihun da Binta ta fasa ya hanshi yin magana se ya miqe da sauri ya fita suka rufo masa baya kowa da tunanin abind aya sameta, tana tsaye ta dora hannuwa biyu a kai, ganinsu yasa ta qara fashewa da ihu me firgitarwa da tayar da hankali har tana dira qafafu kamar qaramar yarinya.
"Lafiyarki? Meya sameki? Ko kunama ce ta harbrki?" Audu ya jera mata tambayoyin cikin rikicewa yana qoqarin riqeta amma taqi tsayawa, ihu take tsalawa duk qarfinta kuma taqi magana haka nan bata dena dire diren ba.

"Kodai shafar jinnu ne tana dasu?" Yaya Baba ya tambaya yana ja baya, takaici ya qume Audu na abinda takeyi ya juya yana ce musu
"Muje dan Allah lafiyarta qalau wulaqancine da rashin son a zauna lafiya ya sakata haka" seta ruqo rigarsa ta baya cikin gunjin kuka tace
"Wlh baka isa, idanna yarda shegiya uwata ta haifeni aure? Aure fa naji suna zancen an daura maka ni zaka munafunta kayi mun kishiya da kudin ubana har yaushe ka nemi auran ban sani ba? Na rantse da Allah kayi kadan" ta fada tana cukuikuye masa riga, bayaninta ya fahimtar dasu dalilin kukan, Yaya Babba ya baza riga yace

"To mu bari mu wuce dan me motar daya kawomu yana waje dama yana jiranmu, Allah ya zaunar lafiya ya kade fitina idan an tsaida ranar Biki ka sanar mana mu shirya a can ai za'a kai Amaryar kamar wannan itama ko?" Ya qarasa yana nuna Binta.

"Ku koma ciki Yaya bamu gama magana ba ke kuma sakeni" ya fada yana qoqarim banbare hannunta daga rigarsa amma ta qara riqewa tam tana qara tabbata masa idan ta sake shi shegiya take.

"Kaga ka kashe wannan wutar tukunna bari muje Allah ya rufa Asiri" daga haka suka fice suna waiwayen Binta dake ihu tana qara maimaitawa Audu be isa ya mata kishiya da kudin ubanta ba.
Mari me kyau ya kwasa mata bayan fitarsu daya saka ta sakeshi babu shiri. Ya nuna ta da yatsa yana cewa
"Kinyi na farko kinyo na qarshe ni ba sakarai bane da zaki cimun kwala a gaban mutane, Aure kuma nayi, ba'a qaro mata ke na Auroki ko ba wata kika tarar a gidan ba? To ki kiyayeni wlh" yana gama fadar haka fuuuu ya wuce cikin gida ya barta a tsaye taba sharbar kuka.

A haukace ta zari mayafi tabar gidan bata ko dauki Zakariyya ba ta tafi gidan Turai can ta tarar da ita a wani birkitaccen yanayi dan itama gyale ne a hannunta da alama fita zatayi qiris ya rage suci karo kowacce taja baya. Binta ta fashe da sabon kuka tana shigewa cikin falon Turai tabi bayanta tana cewa
"Gidanki zani"
"Ai gani nazo, Turai ni Audu ze wulaqanta a duniyar nan ni ya tozarta yayi mun kishiya ban sani ba da kudin ubana?"

"Danqari, Binta amma Audu ya shammace mu kuma wlh ko a bakin Ali banji zancen auran nan ba se yau, to ya akayi haka? Kin ma san wadda ya aura wai?" Turai ta fada cikin Tashin hankali. Binta na sharar hawaye da Majina tace
"Ina na sani, badan nabi bayansa bama da yan uwansa sukazo da qila sedai naji ana gafara za'a shigo da Amarya ki taimaka mun Turai ya zanyi? Wlh bazan dauki wannan wulaqancin ba Audu be isa ya tozartani a duniya ba yayi kadan har marina fa yayi yanzun me kike tsammanin zeyi mun idan matar ta shigo".

"Uhm Binta kenan, nifa Auran Audu bashi ya daga mun hankali ba kamar wadda ya auro din, Kilaki fa ya kwaso miki a matsayin kishiya, idan har Auran nan ya tabbata ai kin gama yawo Binta wlh kashinki ya bushe kishi da Karuwa"

Sakare Binta tayi kukan ya tsaya mata kamar anyi ruwa an dauke kafin ta lailayo wata Ashariya me maiqo ta maka tana cewa
"Kilaki? Ni aka aurowa karuwa a matsayin kishiya? Ashe barinkin Audu har tayi qaurin da ze auro Karuwa ya kawo cikin gidana? Lallai kuwa be siyo zaman lafiya ba ze kuma san ya tsokana tsuliyar Dodo, na rantse da Allah daga ita harshi se sun gane kurensu, zasu san ni Binta ba kanwar lasa bace" yeeyeyey ta cigaba da kuka.

Turai ta sauke tagumi tareda yin Ajiyar zuciya me qarfi tace
"Qawata wannan Al'amarin fa ya zarce yanda kike tsammani, duk fa iya kissa da manaqisarmu bamu isa mu kama qafar matan bariki ba. Ke iya qoqarinda tayi har ya Aureta ai kinsan ba qaramar kai bace wannan tararta se anyi babban shiri" ta matsa kusada Bi ta dake kuka ta dafata taci gaba da cewa

"Kina ji qawata, yanzu dai tunda me afkuwa ta rigada ta afku mataki biyu ne zamu iya dauka a kai,ta siyasa zamu bullowa abun kuma ba mu zamuyi yaqin da kanmu ba, na tabbata yan uwansa basu san waya aura ba dan haka farke mata laya zamuyi duk wanda ya isa ya fada aji a danginsa ki sameshi ki gaya masa wacce Audun ya auro sannan ki sanar

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login