Showing 303001 words to 306000 words out of 467220 words

Chapter 102 - MATAR MUTUM COMPLETED 1-3 BY MARYAM FARUK.doc

23 Sep 2025

12165

Alkhairi ya fashe damu baki daya*

https://t.me/tapswap_bot?start=r_6046431979

Tun tana budurwa akwai lokacin da wata ?asar Mamansu taje gidan suna hira taji tana gayawa Maman sirrin mallaka tace mata
"Babu boka babu Malam zaka mallakeshi kai ba shi kaWai ba duk wanda kika so se yanda kikayi dashi, abu ne me sau?i duk in zakiyi girki ki kuskure bakinki ki zuba ruwan a abincin ina tabbatar miki duk wanda yaci yawunki tofa duk maganar da kika gaya masa ta zauna, idan ma kina son aiki me sauri kuma me daWewa to idan kika tashi da Asuba karkiyiwa kowa magana ki karanta wannan addu'ar ki ri ga tara yawun a roba kina dafa masa abinci wlh kin gama dashi".

Littafi ta nema da biro ta rubuce komai da ?awar Maman ta faWa tamkar ita aka gayawa dukda yaji Maman a lokacin tace ba zatayi ba kuma tayiwa ?awar nasiha da taji tsoron Allah itama ta dena saboda cutarwa ne har Binta ta ringa gulmar Maman a ranta akan me zata ce ba zatayi ba, taso ta gayawa yayyenta a sannan se kuma taji tsoron kar zance ya komawa Maman ta tuhumi a ina taji daga nan ta gane bata dena yi mata laSen data saba yi ba, ba kuma zasu kwashe sa daWi ba wannan tasa tayi shiru ta adana abin a ranta har zuwa sanda Allah haWa Audu da Mahaifinsu.

Da fari ta tsani Audun tun kafin ta kai ga ganinsa, yanda Mahaifinsu ya Waukake shi daga baya ya saka tunaninta ya canza akansa harta raya a ranta zata aureshi badan tana son sa ba sedan tana hango irin rayuwar da take fata a tattare dashi bugu da ?ari kuma yanda mahaifinta ya jashi jikinsa ya Worashi akan dukiyarsa yasa taji ba zata iya bari wasu can ai amfana da Arzi?in ubanta ba wannan tasata ta nuna masa soyayya akayi dace kuma ya amince har sukayi aure sirrin datayi satar ji gurin ?awar Mama ya zame mata makamin ?are dangi, haka take kuskure baki tana zuba musu a abinci sannan ta tara yawun baccinta bayan ta karanta abubuwan da tace wannan Audun kaWai yake zubawa ya cinye ta kuma samu kansa ta yanda ko Yayan data haifa basa jin maganarta tamkar shi.

Tsayin shekarun da abinda take ta?ama kenan se yanzu da mahassada suka tasota a gaba ne suke neman lalata mata shirinta a sanda tazo daidai kan gaSar shan romon damakaraWiyya.

Seda tayi kuka ta godewa Allah kafin ta share hawayenta, damuwarta yanda zata wanke kanta a guri Audu dan tasan yanziu shegiyar Saran nan ta fallasa komai dole kuma zargi ya darsu a ransa, Turan da take ta?ama da ita yanzu ga yanda take bayan ita kuma bata da wani guri da zataje ta buWe cikinta balle a tayata neman mafita.
Hajiya Zainab
?awarta ta faWo mata a rai, hatsabibiyace dan harta fi Turai iya shige shige. Ita sam ta manta da ita ma saboda sun jima basu haWu ba haka ko rasuwar Mijin Turai bata zo musu gaisuwa ba Allah besa kuma duk sun tuna da ita ba a lokacin se yanzu da take neman ruwan kashe gobara.

Watarta ta raruma ta shiga binciken lambar Haj Zainab Win ta kira wayar ta ?araci ringing ba'a amsa ba bata ha?ura ba ta sake kira tana dabda katsewa aka Waga a maimakon muryar Mace se Namiji taji yayi mata sallama.
"Zainab nake nema, kace mata Bintace ta Alhaji Audu" ta faWa bayan gajeriyar gaisawar da sukayi da wanda ya amsa kiran.

Jim yayi kafin yace mata
"Amma kin jima baki nemeta ba ko?"
"Gaskiya dai rabona da ita za'a Shekara biyar haka da Allah bata wayar da sauri uzurine dani babba bana son jan magana ka bata waya" ta hayayya?owa mutumin, shiru tayi kamar ruwa ya cinyeta sanda taji yace

"Wata biyar kenan Allah yayi mata rasuwa bayan tasha jinya, hatsarin mota tayi a hanyarta zataje wani ?auye babu wanda yayi zaton zata ?ara ko minti biyar a raye saboda irin damejin da jikinta yayi amma da Allah yaso seda ta kwashe wata takwas a kwance cikin yanayin da ita da kanta ta ringa fatan Allah ya Wauki ranta ta huta da azabar da take ciki, wata biyar kenan yanzu data mutu kuma zanyi miki nasiha idan har kina cikin ?awayenta da kuke yawon bin bokaye kuna cutar da bayin Allah ki tuba tun kina da sauran lokaci domin da ace kin samu ganinta a halin jinya na tabbatar rayuwarta seta zame miki ishara".

Haka nan Hajiya ta zauna ta buga tagumi kusan minti nawa ta rasa ma abinda zata sa?a a ranta, Turai na Asibitin mahaukata Zainab ta mutu yanzu ina zata tsoma ranta taji sanyi? Wa zata kamanya samar mata da mafita a halin da take ciki?"

Ranar wuni tayi sur a Waki kamar Amarya ta gagara le?awa waje abin duniya ya haWu ya mata yawa se washe gari da safe ta samu ?warin guiwa bayan data ?arfafa kanta ta kuma shafawa idonta toka ta tunkari Alhajin domin da asara gara gidadanci kuma ita tabarmar kunya ai da hauka ake naWeta gara suyi wadda zasuyi kawai.

Ko a fuska Alhajin be nuna mata komai ba sanda ta shigama a zaune yake yana cin abincin da Hajiya Rabi ta shirya masa harda tambayarta ina ta shige tun jiya ne sake jin Wuriyarta ba hakan ya bata kwarin guiwa ta zauna ta fara rera masa zance ta zarce ta bashi ha?uri akan kuskuren da tayi na saka masa kanwa a Abinci.

"A gabanka Bilki ta faWi cewar kanwa tana saukar da jini idan anyi amfani da ita yan daya dace to wlh ni yar kaWan nake sakawa waccen shashaahar yarinyar tunda bana nan daga nace ta saka kaWan shine ta ringa kunzumata harta muce ?a'ida amma an auna arzi?i tunda Allah ya ta?aita wahala barka" ta marairaice tana faWa shidai ya cigaba da cin abincinsa yana amsa ta sama sama harya gama sega Ahmad da Aminu sunyi sallama.

Ganin Ahmad be gigitata ba kamar ganin Aminun, bakinta har rawa yake ba tareda ta amsa gaisuwar da sukeyi mata ba ta shiga tambayarsa abinda ya kawo shi gidan.

"Yanzu mutum da gidan ubansa Binta har kya tambayeshi me yazo yi?" Alhaji ya faWa yana kallonta fuskarsa kadaran kada han seta wayance tana cewa

"Kuma fa hakane, mamaki nayi ne naga kusan shekara nawa rabon daya tako cikin gidan nan, tun sanda aka nemi kuWi aka rasa a kamfani to ko an gansu ne yanzun dan dai nasan ba zaka yafe kudin nan ba bare har ka bashi damar tako maka cikin falo" ta ?arasa tana wat sariya kamar wadda ta zare, Ahmad da Aminu dai basu ce komai ba suna zaune suna sauraronta Alhajin ma jim yayi yana kallonta kamar zeyi magana se kuma ya fasa yace mata

"Ki Wan bamu guri zamuyi magana idan kin shiga ciki kuma ki turomun Aisha". Jiki ba nauyi ta mi?e domin dai iya muzanta tayi idan kuma tace zata tsaya bata san me ze biyo baya ba, yi tayi kamar ta fitan amma ta laSe a bayan ?ofa ta kasa kunne dan koma menene se taji.

Alhaji Audu ya kalli Ahmad daya jinginar da kansa jikin kujera idanunsa a rufe yace
"Ya jikin naka? Kaje kaga Charles Win me yace maka?"

"A hankali ya buWe idonsa da sukayi jajir ya kalli Alhajin kafin ya sauke su yace
"Da sau?i, sunyi mun gwaje gwaje ne yace amse zuwa sati Waya zasu fito amma ya bani maganibda zansha kafin fitowar sakamakon"

"Allah ya sauwa?a ya ?aro afuwa, Malam Aminu ya duniya? Shekaru da yawa ina aka Soye ne?" Alhajin ya faWa, Aminu yayi ?aramin murmushi kafin yace

"Muna nan Alhaji, ya ?arfin jimi kuma?"
"Jiki ya warware, ina Wan uwan naka na ganka kai kaWai?" Ya sake tambayarsa

"Rasuwa akayi, Mahaifin matarsa ne ya rasu muma daga gurin jana'izar muke mun baroshi acan saboda kusan shine madadin Da Namiji a gidan tunda duk mata ne ?annen matar tasa to shi yake kula da komai"

"Toh, Alhaji Namadi ya rasu Allah ya gafarta masa" Alhaji Audun ya faWa yanayin fuskarsa na canzawa kafin ya kuma cewa
"Layi yana ta tafiya ko yaushe zata zo kanmu oho?"

"Duk ita muke jira ai Alhaji se dai muyi fatan Allah yasa mu cika da imani" Ahmad ya faWa daga nan sukayi shiru na kusan minti goma kafin Alhajin ya sake cewa Aminu

"Ka shiga ciki ka kirawo mun Aisha babu lallai waccen ta gaya mata" Alhaji ya faWa yana kallon Ahmad dake gyangyadi a zaune se yayi firgigit kafin ya tsallake ya wuce cikin gidan abin dariya suka kusa cin karo da Hajiya dake tsaye tana dakon jin abinda zasu tattauna tayi gaba ya bita a baya har cikin gidan. Kafin Ahmad ya dawo har Alhajin ya gama tattauna dalilin kiran Aminu da yayi, yana sane da Bintan bata tafi ba, shima kuma Ahmad dayace ya je ya kirawo Momy ya fahimci me Alhajin yake nufi dan haka daya shiga ya zauna har seda ya daidai ci sun gama tattaunawar kafin ya dawo har Alhajin ya sallami Aminu ya tafi.

"Baka samu Baba da Yusuf Win ba kenan?" Alhaji ya tambayeshi. Cikin yanayi ma gajiya Ahmad Win yace

"Babban Yaya baya nan yaje Germany shi kuma Yaya Babannan duk yanda zanyi nayi amma ya?i saurarata, har Babban Yayan seda yayi masa magana daga ?arshe yace karna sake zuwa gidansa kuma yayi blocking Wina sannan kona kirashi da ba?uwar lamba bana samunsa"

Shiru Alhajin yayi kafin murya a karye yace
"Yusuf yana da kafiya da ru?o, duk cikin yayana shine ya kwaso mafi yawan muguwar halayyata ta kafiya da ru?o, da ace ba Bara'atu ce ta haifeshi ba ban san me ze zama ba. Yaushe Babaan yace ze dawo?"

"Nan da sati biyu yace, ina ganin dawowar tasu ma tazo lokaci Waya da Yaya Hussain" Ahmad ya bashi. Murmushi Alhajin yayi yace

"Hussaini rigima kenan, a gidansa uwar tasu take ko a gidan Hassan?"

"Aa tana nan Kano gidan Dr, amma bata nan yanzu tare suka tafi da familyn Yah Hussain Win hutu Landan"

"Toh su Zubaida mutanen Landan ashe dai har yanzu da sauran ?uruciyarta lallai za'a sha gayu a Landan" Alhajin ya faWa yana murmushi harda kama baki, Ahmad dai ya tsaya yana kallonsa kawai gashi ya gaji so yakeyi yaje gida ya kwanta ya huta, tunda Alhajin ya Wora masa aikin haWo masa kan yayansa Waki Waki duk bashi da nutsuwa. Alhajin ya Wora masa aiki me nauyi dukda abu ne da yake da burin aiwatarwa fatansa kenan samuwar daidaito a gidansu amma kuma ya fara sarewa da abin dan yana neman yafi karfinsa.

Duk yanda yake zaton abin zezo da sau?i ya wuce haka da?yar, ro?o tareda magiya ya samu Aminu da Wan uwansa Aliyu suka amince zasu amsa gayyatar Alhajin yau Win da suka shiryi zuwa kuma sirikin Aliyun ya rasu shine suka taho babu shi dan Aminun ma yaso ya zame seda yayi kamar ze masa kuka kafin ya yarda suka zo a ?alla hakan ya ?ara masa ?arfin guiwa ze kuma sake jajircewa ya shanye duk wani zagi da tijara da sauran zasuyi masa har se ya cimma burinsa sunzo gaban Alhajin kamar yanda ya bu?ata domin koda ace Shi yayi musu laifi matsayin mahaifi yake a gurinsu su ya cancanci su dur?usa a gabansa bashi ze bisu inda suke ba.

"Bana tsammanin zan cimma abinda nakw fata Ahmad" Alhajin ya maido Shi daga tunanin daya tafi, seya gyara zama ya kalleshi idonsa cike da rauni yace
"Me kuma ya faru Alhaji"
"Babu abinda ya faru, yace mun komai ya wuce, a yanda yace be taSa ri?ata da komai a ransa ba amma kuma ya wofantar da tayin komawa bakin aikinsa da nayi masa". A hankali Ahmad yace

"Ai dama Alhaji ba zaka tsammacin wani a cikin mu ze karSi tayin ri?on wani abu daya shafi dukiyarka ba. Shiri ya kamata ka nema da Yayanka kamar yanda kace kana so. Kawo zancen dukiya ko wani abu ze sake lalata komai ne domin kayi ha?uri Alhaji a yanzu wata dukiya bata a gaban kowannen mu, Alhamdulillah Allah ya raba ya bawa kowa daidai abinda ya tsara masa abu guda muka rasa kuma shine muke da bu?ata soyayyar mahaifi, dukda bamu sameta a sanda muke kulafucinta ba muna maraba da kwantan da zamu samu.

Ajiye komai zakayi a gefe, kuWi, matsayi da duk wani abu ka fito a mahaifi da yake burin rarrasar dan yaronsa, ka lallashe mu, ka lallaSa mu, ka tausasa kalami a garemu ka kuma nuna har zuciyarka ka karSi kuskuren da muke ganin kayi mana sannan a shirye kake da ka gyara kana kuma bu?atar mu saboda mu yayanka ne bawai dan kawai girma ya kamaka kama tunanin mutuwa tana kusantoka dan haka kake neman magajin da ze maye gurbinka bayan babu kai ba" HaSon daya Salle masa ne ya sakashi yin shiru dole,

Alhaji da yayi zukuWi kamar daliSi na sauraron ya mi?e da sauri yana cewa
"Subhallahi haSo kuma Ahmad? ?aga kanka sama ina zuwa" ya doshi firji da sauri kamar ze kifa ya Wakko ruwa me ?an?ara.

*MATAR MUTUM*
*NA MARYAM FAROUK (UMMU MAHEER*

*FIKRA WRITERS ASSOCIATION*

*LITTAFIN KUDI NE*
*PAY 500 A ASUSUN*
*7061838488*
*OPAY DIGITAL SERVICES*
*MARYAM FAROUK*
OR
*0709290797*
*ACCESS BANK*
*SE A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488*
*IDAN KATINE A DAUKI HOTONSA A TURA ZUWA LAMBAR SAMA VTU KUMA A TURA A 08142548705*

*Kuyi following dina a Arewabooks @Maryamfarouk01 inda zaku karanta wannan littafin tareda sauran littattafaina*
*NAGODE*

*BOOK 3*
*PAGE 16*

Daga wannan HaSon jikin Ahmad ya sake rikicewa dukda yana ?o?arin dakewa da nuna lafiyarsa ?alau hakan bata samu ba dan yana jin jiki sosai. Tun daya bar gidan Alhaji Audu seda yayi sati a gida yana jinya kafin yaji dama dama ya koma sabgoginsa duk kuma jinyar nan da yayi babu Wanda ya sani daga shi Fatima da kuma likitan da yake zuwa yana dubashi ya kuma gargaWeta akan karta gayawa kowa, cikin satin yanda ta birkice seka Wauka itace mara lafiyar, yana warkewa ima ta kwanta laulayi ya diro mata da zafinsa kamar aike ga Baba Bilki bata nan ta tafi Bechi kusan watanta Waya acan sau?i sau?inta daman hutun makaranta akeyi yaran suna gidan Anty Sauda amma dukda haka daga ita harshi Win sun hargitse, idan ka gansu seka rasawa zaka fara yiwa sannu.

Ita dai daman ana ganinta ansan dalilin ciwonta, duk laulayi baya sakata rama amma a wannan karon kam tayita saboda rashin nutsuwa da kwanciyar hankalin data gagara samu dalilin kasa gane ciwon da yake damun Ahmad Win.

Kusan koda yaushe bashi da lafiya, idan ba zazzabi ba mura idan babu mura a wayi gari jiki yayi ?ulalai kamar wanda ya bige can ya kumbura gobe ya sace can ya sake Wauka haka dai yake ta fama ko kuma kawai hanci ya fara jini daman ba'a maganar gajiya kullum cikinta yake yayita ?orafin ciwon jiki wani sa'ilin tana lura dashi idanunsa har ?walla suke tarawa idan ya dawo gida a gajiye se yayi wanka ta daddanna masa jikin ya kuma sha yan kwayoyi kafin yake samun salama yin duniya kuma yaje Asibiti a dubashi sosai ya?i, sedai fa idan ciwon ya matsa masa wani likita daya samu wai Dr Sadi yazo gidan ya dubashi sannan ya ja mata kunne akan sake kaiwa Momy ?arar sa tun wancan karon data saka shi a gana kamar yaro ta kaishi Asibiti haka nan suke zaune, ga matsalar yan uwasa saya Wauka ya aza a kansa bashi da wata hira yanzu seta yanda zeyi ya taimakawa Alhaji kan zuri'arsu ta haWu guri guda.

Sosai take tausaya masa ganin yanda Shi kaWai yake ha?ilo gurin tattaro kawunansu, ya kira wancan yake gidan wancan wani sa'ilin yazo fuska da walwala yana jin daWi idan kuma beyi nasarar zuwan ba daman daga yanayinsa zata gane dan duk zamansu har yanzun be taSa buWa baki ya gaya mata wata matsala ta cikin gidansu ba ita ma bata taSa tambaya ko nuna masa tasan wani abu ba, yanda dai ya damu da yan uwansa yana masa Addu'ar Allah ya bashi nasarar cika burinsa na haWa su ko ta samu hankalinsa ya nutsu guri guda.

Sannan ta lura yanzun wani shiri ya ?ullu tsakaninsa da Alhajin nasu idan basuyi waya ba to zeje gidan wani lokacin ma idan ya fita ta sabgoginsa idan sukayi waya zece mata yana gurin Alhaji ko yanzu zeje gurinsa ko idan ya dawo yace daga gurin Alhajin yake shiri dai sukeyi sosai yanzu sun zama kamar wasu Abokanai duk inda kuma Alhajin zeje ze kirashi ya rakashi dan ma yanayin lafiyarsa yana kawo tsaiko shi kansa Alhajin kullum faWan sa kenan me yake damunsa me ya saka a ransa yake ?arar dashi kamar kudin guzuri?

A gidan Alhaji Audu kuwa za'a iya cewa sau?i ya samu dan tun faruwar wancan al'amarin bayan da girki ya sake zagayowa kan Hajiya yanda ta shirya wa Alhajin Abinci ta kai masa haka yasa aka kwaso aka mayar dashi cikin gidan ?arin ba?in ciki da abin kunya a kan idonta masu aiki suka juye abincin a shara dan har Waya tana cewa a bawa karnuka Wayar tace mata Aa, suma rai ne dasu wayasan mugun abin da yake ciki.

Ranar duk iya masifa da tijararta se gashi lu?us ta gagarayi sema Waki data shige ranta na zafi, da aka kwana biyu kuma taga an tada aiki a gidan gaba Waya akayi musu gyare gyare akayi fenti sannan yasa aka kwashe kayan falukansu aka zuba musu sababbi, da sanda duniya na hannunta ne da ita za'a shawarta komai ta sa ayi abinda tayi niyya ta hana Wanda bata so ba kuma ta karSi kuWaWe makudai tasha sharafinta, daga baya sega wani zindi?in ?ato an kawo da sunan kukun da ze ringa dafawa Alhajin abinci an gyara kitchen Win da yake Sangaren sa wanda daman tun asali dalilin yin kitchen Win kenan dan babu shi daga baya yayi shi ya kuma ce ze Wakko kuku da ze ringayi masa abinci daidai da Abinda jikinsa yake bu?ata amma tayi kinini ta hana kuma ya hanun yanzun kuwa cikin sharudanda Baba Al?ali ya kafa masa kenan haramta mas acin duk wani abu daya fito daga hannun Binta, da kansa ya samo masa yar dajje kuma gwani akan fannin girki da shi kaWai ze ringa yiwa an hutashshe da matan dukansu.

Tabbas tana cikin tsaka me wuya ba kuma tada matai maki a yanzu Turai ce daman

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login