Showing 183001 words to 186000 words out of 467220 words

Chapter 62 - MATAR MUTUM COMPLETED 1-3 BY MARYAM FARUK.doc

23 Sep 2025

12173

ba tsarana bane, ire irenki ne m daidai dashi, matsayi da Arziqin iyayenku yayi kamanceceniya kinga babu me ganin cewar Alfarma yayi miki idan yayi tarayya dake" Afeeya ta faWa zafafe tana barin Wakin saboda gajiya da maganganun Badar dukda yanda Maman Minal da Ummi suke mata magana akan tayi shiru amma ta?i, dagaske neman fitinarta takeyi yau amma ba zata biye mata ba gara ta fita.

"Saboda ina sonki na damu dake ina miki burin ki auri Mijin da yake sonki kiji daWi shine kike gaya mun haka ko Afeeya?" Ta faWa tana ?an?ancr ido. Fes Afeeyan ta kalleta tace
"Kinji abinda na faWa ai, Ahmad ne bana sonsa bazan aure shi ba kuma fatan da kike mun baze kamani ba Allah ze kawo mun Miji Talaka daidaini na aura wanda babu me saka mana ido ballantana a ringa fassara duk wani motsina akan sa da sunan na butulcewa ni'imar ubangiji".

"Meye haka Afeeya?" Maman Minal ta dakatar da ita, ta kalleta da idonta da suka fara canza kala tace
"To akan me Anty Zahra? Duk sanda magana zata haWo akan Ahamd se Badar ta yimun gori a fakaice tace yafi ?arfi na? ni na janyo shi nace ya soni ko yaya? Da yana da zuciya ma ai da bamu kai haka tare ba saboda na nuna masa bana muradinsa ta duk hanyar data dace amma ya nace ya kafe so takeyi na aureshi Alhalin danginsa basa ?aunata? Ba'a a kunnenta ?aninsa yayi mun cin mutunchi ya zagi iyayena sannan ta dage sena cusa kaina inda Allah be kaini ba saboda kwadayin abin duniya?

Toni kudinsa ko wani matsayi nasa ba zasu rufe mun ido ba su sa na jefa rayuwata cikin ?unci na rayu da mutanen da basa so na, idan tana sonsa gashi nan na bar mata ta aureshi itace daidaishi" ta ?arasa tana ?o?arin ri?e kukan daya taho mata amma ta kasa dole ta sakeshi ta doshi ?ofa zata fita amma mutanen da suka tsatstsaya munafunci yasa ta fasa fitar ta shige bayan Ummi da ke zaune ta kasa cewa komai ta kwanta tana kuka.
Maman Minal ta kulle ?ofar jiki a sanyaye kafin ta zauna tana cewa
"Daga zancen tuwo shikenan se tashin hankali? da alama sheWan ya shigo ya laSe a Wakin nan shiya haWa komai kuma bazeyi nasara ba in sha Allah".

Badar da jikinta yayi sanyi la?was ta zauna daga tsayuwar da tayi ta kasa cigaba da masifar tata. Har ga Allah ita batayi magana da manufar da Afeeya ta Wauka ba, ta ri?i Afeeyar a matsayin yar uwa shiyasa har take son cigabanta take kuma son ta da Ahmad ganin cewar mutumin kirkine ya na da duk wasu qualities da mace zata so a gurin Namiji gashi yana sonta baya ga haka wlh ita bata da wata manufa ta daban akan maganar.

Dakin ya Wauki shiru se shashe?ar kukan Afeeya, kowa da tunanin da take a ranta wayarta ta sake Waukar ?ara lambar dazun ce bacin ran da take ciki yasa ta kashe wayar gaba Waya ba tareda na amsa kiran ba. Ranar har dare dukkansu basu da walwala shiru Wakin kamar anyi mutuwa, tsakaninta da Badar kuwa se kallo seda Baffa ya kira wayarta akan be samu ta Afeeyan ba sannan nema ta tuna data kashe wayar tata, data mi?a mata bata kar Sa ba, ta kunna tata ta kirashi.

Sururat ce ta saka su shirin dole cikin daren bayan ta dawo Ummi da Maman Minal suka tsara mata abinda ya faru ta ringa masifa ta kuma Worawa Afeeya laifi kacokan wannan yasa suma sauran suka buWe baki tare da nuna cewar ita ce bata kyauta ba su da kyakykyawar niyya suke tare da ita kuma wannan tasa har suke son abinda suke ganin ze zamar mata Alkhairi ba wani abu ba.

Bata so aja maganar da tsaho dan haka nace taji ta kuma bawa Badar ha?uri kamar yanda Sururat tayi insisting.

"Wlh Afeeya ina jinki kamar Yah Yusra, idan har zan iya aure ko soyayya da Mijinta to zanyi da Ahmad. Son da yake miki da kamalarsa tasa har nake miki sha'awar auransa dan nasan irinsa basu da yawa a duniyar yanzu amma tunda har zuciyarki tana raya miki wani abu daban akan niyyata in sha Allahu zan kama kaina, bazan sake yi miki wata magana data shafeshi ko ma akan saurayi ba gaba Waya. Zanci gaba dayi miki Addu'a Allah ya zaSa miki abinda yafi Alkhairi" Badar din ta faWa bayan da Afeeya ta bata ha?urin,

jikinta yayi sanyi ganin yanda idonta ke zubar kwalla sanda take maganar, ta tabbata har ranta gaskiya take faWa kuma Badar na sonta kamar yanda ita ma take sonta amma abune yazo da rashin fahimta dukkan su kowa tana da dalilanta na so ko ?in tarayyata da Ahmad amma ta haWiye nata za kuma ta cigaba da addu'a Allah ya fiddo mata da Mijinta daidai ita ya fiye mata sau?i.

Saboda ta tabbatar musu maganar ta wuce yasa washe gari suna gama Lectures tacewa Badar suje kasuwa ayi cefanen, ta kuwa ji daWi sosai dan da sunta share juna amma daga zuwa kasuwar komai ya wuce aka dawo daidai
Harda kayan zoSo suka siyo, sesaga baya kuma Badar tace su siya Kunun Ayar Shinkafi kawai ba se anyi ZoSon ba.

"Bari na kira Salima Nasir ta zo manada snacks gobe se a hada masa ko?" Badar ta sake faWa. Dole Afeeya ta amsa gudun karta ?ara laifi a gurin Badar data saki ranta dalilin za'ayiwa ?anin Dadynta girki. Sunyi markaWen stwe a Kasuwa dan haka suna komawa suka Wora girki suna hira kamar ba abinda ya faru jiya.

Washe gari haka Afeeya ta tu?a tuwon rabin kwano tayi miyar kukar da ?amshinta ya karaWe duka block Winsu ya buwayi hancin kowa. A Set din food flask da suka Wakko da safe a gidan Maman Minal ta saka masa tuwon Miyar aka barta a tukunya akan seya zo se a sake dumamawa a zuba a flask din. Kayan da zan saka ko Badar ta turarasu ya kai sau uku, jikinta har rawa yake idan Ahmad zezo musamman wannan karon, sunyi waya da Afeeya ya gaya mata be taso da wuri na ze kai zuwa uku kafin ya sauka dan haka zuwa biyu ta gama komai tayi wanka suka zauna suna ta labarai. Biyu da rabi ya kirata akan ya shigo zaria.

"Na gaji da yawa ni nayi driving zan wuce nayi Lodging hotel idan na huta da Magriba sena shigo kuma bani kaWai bane tare muke da mutumin Badar" ya faWa mata. Har zatace masa toh ta tuna da Tuwon data gama shan wahalar tu?awa hannayenta duk sun sage tafin se radadi yake mata Allah ma yasa kar nayi kanta. Da shagwabar da bata san tayi ba tace masa
"Toh Abincin fa? Shima se da magribar zaka ci?"
"Wane Abinci?" Ya tambayeta cikin rashin fahimta se sannan ta tuna da bata gaya masa tayi masa tuwon ba dan haka tace
"Girki mukayi shine na Wibar maka ko bazaka ciba?"
"Nidin banza, gani nan yanzu kuwa zanzo na karba kamar kinsan yunwa nakeji ko breakfast banyi dakyau ba saboda dokin son ganinki"
Guntun murmushi tayi kafin suka aje waya. Miyar aka sake Wumamawa Maman Minal tayi masa zubi me kyau duk ta kwashe Albarkatun cikin miyar ta bar musu saura. Hijabi ta Wakko cikin na *UMMU-MAHEER 07061838488)* wankakke gogagge ta Wora akan doguwar rigar jikinta Badar ta kwaso Ashar ta watsamata ta haWiye dan daman ta san se sunyi.

"Tsabar iskanci in gama shan wahalar turara miki kaya ki wani kwashi Hijabi kamar me takaba ki saka" ta faWa a fusace tana neman fizge hijabin. Maman Minal tace
"Ki barta ai ze dawo anjima se tayi kwalliyar sannan".
"Masifaffiyar banza kawai" Afeeya ta faWa ?asa ?asa. Sururat ce ta tayata Waukan Basket da suka zuba abincin.

Kallon da bata so ya kafeta dashi tun daga corridor harta fita wajen hakan da yayi yasa hankulan mutane da yawa yayiwo kanta har suka ?arasa gabansa yana ta sakin murmushi kamar wani wawa.

Kallonsa tayi taga ya sake zama wani dan tsurut musamman daya saka ?ananan kaya se taga ma har tsakiyar kansa tana kallo tsanar sharri, murmushi tayi itama ta shiga gaishe su shida Abokinsa da kana ganinsa kaga Kanuri. Wani Ba?i dashi hausar ma se a hankali se surutu kamar ya ?one a kai.

"Gaskiya Amaryarmu ba kalar rana bace, dan haka kodai ka nemi inuwa ku zauna ko kuma ka barta ta koma ciki an jima idan gari yayi sanyi seka dawo. Ni ganin basket Win nan ma gaba Waya ya sake tadomun da yunwa" Bukar ya faWa ga surutu ga saurin baki.
Kanta na ?asa tana wasa da zoben hannunta duk kallon da Ahmda ya kafeta dashi ya takurata,

"Bari muje Fatima anjima se na dawo bayan La'asar ko?" Ya faWa cikin sigar tambaya ta Waga masa kai ta ce
"Toh".
Abokin ne ya karSi basket ya saka a mota Ahmad ya bishi ya Wakko wata leda me tambarin super market dinsa BECHI STORES ya mi?a mata ta karSa ta Wan rusuna tace
"Nagode"
"Tsarabarki ce, tukuicin girki kuma se naci naji ?anWanon sa tukunna"

Murmushi tayi, ya langwaSe kai ya jingina da mota yace
"Kamar karna tafi, kinyi kyau sosai Fatima Hijab suna miki kyau" Ya?e kawai takeyi Abokinsa ya le?o daga mota yace
"Kodai na zuba na fara ci ne in ba yanzu zamu tafi ba?"

"Kaga kun kwaso gajiya, kodan saboda dashi kuje Anjiman se ku dawo" ta faWa, seya gyara tsayuwarsa yana cewa
"Naga hannunki"

?irjinta ya buga, me ze gani a hannunta kuma? Amma haka ta daure ta mi?a masa hannun da daga wrist zuwa fingers Win ne a buWe,
"Masha Allah ya faWa" kafin ya juya yana Waga mata hannu da cewar
Se ta dawo ita ma ta Waga masa. Ta tsallaka ta shige hostel tana ta mamakin dalilin son ganin hannunta da yayi.
Tuwo ta tarar suna ci ta wanke hannu ta zauna, tunda ta gama taso taci jarabar Badar ta hanata wai bakinta zeyi warin daddawa se kace idan ta wanke baze fita ba. Seda suka qoshi ?at kafin a zazzage ledar tsarabar.

Wata Arniyar Turkish gown ce Material me sharashara Amma tana da landing Dark blue ce da flowers Yellow da fari da dan yarfin ja kadan. Irin design da ake sakawa roba a waist ta matse ta sama ?asan kuma ya buWe ce se mayafai Medium guda biyu plain da kana ganinsu kasan suma daga Turkey suke saboda samfurin jikinsu, takalmi loafers dark blue qafa daya se Wani kwali ?arami na turarene babu suna a jiki hakan ya tabbatar mata da sabone basu luncher shi ba testing ya kawo mata kamar yanda ya saba tunda suka haWu, Ahmad yanayin Designer perfumes kuma duk sanda sukayi sabon Turare kafin a fitar dashi seya kawo mata.

Company haWin guiwa ne da wasu Abokanansa da sukayi karatu tare a Paris Asalin kamfanin yake amma a Dubai suke operating.

Tarkacen Chocolate na yan gayu birjik su su Badar suka Wiba ragowar kayan ta watsa su a kan gado. Ahnad baya gajiyawa kullum cikin hidimta mata yake. Idan ya tashi siya mata kaya tamkar besan zafin kuWi ba daidai da Slippers yanda yake saka Designer haka yake siya mata tun Baffa da Umma na faWa har suka ha?ura suka zuba masa ido kyautar KuWi ce dai Baffa ya dakatar shine yace idan an hanata karSan kuWi ai ba za'a hanata kaya ba dukda haka kuma idan zata koma school seya tura mata kuWi masu nauyi sedai taji dirim.

Shida saura Ahmad ya kirata akan sun fito suna hanyar Samaru, bisa takurawar Badar Ummi tayi mata light make up ta cakare cikin Atamfa dinkin fitted straight Bubu, bata kamata tsam ba haka bata yi buhu ba tabi shape dinta ko ina ya fita masha Allah abinka da dogowar Mace na ta juya Anty Zahra tace
"Afee kinyi kyau, komai kika saka kyau yake miki".
Badar ce tayi mata Wauri me kyau daya dace da kwalliyarta

Seda aka idar da sallar magriba kafin ta fita dan bayan ya isa kirata yace ze shiga central mosque yayi sallah tukunna. Bata cika fita babu Hijabi ba infai ba Abaya ta saka ko irin Bubu plain Gown ba a hakan babu kwalliya gajiya takeyi da idanun mutane balle yau datayi shigar Atamfa harda kwalliya a fuskarta ga Waurin gaban goshi wani irin kyau tayi me sanyi da ?ayatarwa ba Maza ba hatta matan dake kaikawo a waje Hostel binta suka ringayi da kallo duk seta jita a takure shoyasa tafi gane ta suturta kanta da Hijabi Ko Abaya.

Yanda Ahmad ya saki baki yana yabon kyan da tayi ko har seda abin ya bata kunya ta sunkuyar dakai tana murmushi. Shi kaWai ya dawo Abokin nasa wai ya shiga City, a nan Basket ball court suka zauna suna hirar duniya dan a itane take sakewa dashi suyi magana ko zancen Business dan tanada sha'awar kasuwanci sosai abinda ma zata ce ya a birgeta da Ahmad kenan Business mind set, a tsaye yake da ?afafunsa kuma kullum cikin nuna mata amfanin neman na kai yakeyi. Yakan ce mata
"Ina so naga matata tana sana'a badan bazan wadata ta da komai na rayuwa ba Aa sedan ni na yarda da ko wani zeyi mun abu ya zamana nima inada abuna wanda zan kalla nace da gumi na na sameshi".

Seda aka kira yace ta kira su Badar su fita wannan daman constant ne duk sanda yazo seya fita dams yawo sun sha iska sunyi ciye ciye, tana kiranta minti goma suka fito duk a shirye harda Ruth suka zauna su huWu a baya ita a gaba banda Maman Minal suka tafi Zaria Suya kamar yanda Badar tace can za'aje sunata hira da Ahmad har suka isa.

Sunci kifi sun sha shayi sunyi take away kaza da Suya amma banda Afeeya da idanun da Ahmad ya kafeta dasu suka hanata sakat. Yau se take ganin kamar tasan wani bayan shi me irin idon, amma ta gaza tuna waye.
https://chat.whatsapp.com/FKsWield4wPKepHDZwtPUP

*ASSALAMU ALAIKUM WARAHMATULLAH*
*MUNA GABATAR MUKU DA UMMU-MAHEER COLLECTION Ita din dai kuka sani taku ta gargajiya da take kawo muku kayayyaki irin na yangayu daga kan ATAMFA, BUYERS BATIK, COTONOU BATIK, SWISS LACES, LAGOS LACES, MAYAFAI, KAYAN KWALLIYAR YARA DA SAURANSU. TA SAKE SHIRYOWA TSAF DA COLLECTION NA HIJABAI IRIN NA AFEEN JAYY FA AMMA BANA HAJJAJU BINTA GUMAMA BA*

*YI MAZA KU GARZAYO DOMIN KUYI SIYAYYAR KAYAN SALLARKU A GURINTA CIKIN RANGWAMEN FARASHI GA BIYAN BUQATA*

*DA AKWAI NORMAL HIJAB ME HANNU, MARA HANNU, POCKET HAND SE WANDA KIKA ZABA KALA KAWAI ZAKI BADA AYI MIKI AIKIN, JILBAB DINMU TAMKAR SAUKAKKE DAGA EGYPT, WANDA SUKA SIYA ZASU BAKI TABBACIN INGANCIN YADINMU. DA AKWAI NORMAL YARD, AKWAI LONDON CREP IYAKAR KUDINKI IYA SHAGALINKI*

TWO PIECES GOWN DA V HIJAB NA YARA DA MANYA HARDA MA ABUBUWAN DA BAN FADO BA ZAKI SAMUSU GURIN UMMU-MAHIR DA YARDAR ALLAH.

*SANQAMA MATA KIRA KO CHATTING AKAN 08142548705/07061838488 KO KUMA KIYI JOINING GROUP DINTA KAI TSAYE DOMIN SAMUN LATEST DESIGN AND AVAILABLE KAYA DA SUKE A QASA*
*MADALLAH DA MASU SO FISABILILLAHI IRIN NA AHMAD BECHI*

*MATAR MUTUM*
*NA MARYAM FAROUK (UMMU MAHEER*

*FIKRA WRITERS ASSOCIATION*

*LITTAFIN KUDI NE*
*PAY 500 A ASUSUN*
*7061838488*
*OPAY DIGITAL SERVICES*
*MARYAM FAROUK*
OR
*0709290797*
*ACCESS BANK*
*SE A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488*
*IDAN KATINE A DAUKI HOTONSA A TURA ZUWA LAMBAR SAMA VTU KUMA A TURA A 08142548705*

*Kuyi following dina a Arewabooks @Maryamfarouk01 inda zaku karanta wannan littafin tareda sauran littattafaina*
*NAGODE*

*BOOK 2*
*PAGE 11*


"Saura sati nawa kuyi hutu?" Ya tambayeta yana sake narkar da idanunsa a kanta. Ta lissafa a zuciyarta kafin tace
"Four weeks i think"
"Fatima" ya kira sunanta da sautin dake nuna muhimmancin maganar da zasuyi, ta gyara zamanta ta saci kallonsa yaci gaba da cewa
"Shekara biyu kenan since i meat you. Banyi zaton zan ?ara wata shida ba daga ranar dana haWu dake ba tare da kin zama matata ba amma se gashi har an tafi shekaru which kece kika jawo hakan, please Fatima, i will ask you again ki aureni, last week na je na samu Baffa akan ina so na turo magabatana yace na nemi Amincewarki tukunna, idan kin yarda ko yaushe na shirya na tura ayi magana.

Bansan me kike jira ba, Fatima Aure baze hanaki ?arasa karatunki ba tunda shine maganarki kullum ke kinfi so ki gama makaranta ni bazan hanaki karatu ba idan kin gama wannan kina so kici gaba wallahi ko a Nigera ko wata ?asa ni zan tsaya miki har se ke da kanki kince karatun ya ishe ki tukunna kawai ki Amince mun ki bani dama na tura Iyayena ayi maganar auran mu saboda wlh Ha?uri na ya fara ?arewa Aure nake so Fatima"

Shiru tayi masa kuma kunyar kalamansa na ?arshe ne ya assasa shirun wai Aure yake so, matso da kujerar sa yayi kusa da tata kamar ze haWe su yana cewa
"Talk to me Fatima bana son shirun nan naki menene matsalarki bayan maganar karatu? Idan da akwai wani abu daban let me know please"

Kamar tace masa "shi Win ne bata ra'ayin aure se kuma ta canza maganar dan ko babu komai kirkin Ahmad ya wuce tayi masa irin wannan cin fuskar. Kora da hali dai ba wadda bata masa baa baya amma ya ?ifahimta to ya yake so tayi dan Allah? Gyara zama tayi ta dan ja baya saboda kusancin nasu yayi yawa kafin tace.

"Nidai Ahmad nafi so na kammala karatuna tukunna in so samu harma nayi NYSC kafin nayi aure, sannan kana cewa muyi aure naci gaba da karatu na tayaya hakan zata faru bayan Matan gidanku bas karatu?"
BuWe ido yayi irin na mamaki ya kalleta kafin yace"Waya gaya miki haka?"

"Haka naji a gari" ta bashi amsa tana sauke ido ta saboda yanda ya saka mata nasa, cikin taushi yace
"Fatima abin harda sharri? A wane gatin kikaji? Waya ce miki matan gidanmu basa karatu?
Matan Yayyena harda me Phd Matar Dr Hassan tana aiki Lecturer ce, inaga a cikin sauran babu wadda batada Degree, idan kuka ?annena kike nufi Aslamiyya da Hajiya ?arama Level 2 suke kowacce kuma Next two month aka saka ranar Auransu kowacce zata gama Karatun a gidan Mijinta ya za'ayi kice ba'a karatu a gidanmu kodan kinga Alhajin mu ba ?an Boko bane?"

"Ni bance haka ba, to inaga qadda ta gaya munce bata ji daidai ba" ta faWa cikin kare kai shaci

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login