Showing 234001 words to 237000 words out of 467220 words

Chapter 79 - MATAR MUTUM COMPLETED 1-3 BY MARYAM FARUK.doc

23 Sep 2025

12138

harya harbo jirginki da wurwuri ya fahimci mayadariya ce ke kuma makwaWaiciya. Shi dayake free ne gashi nan ya buWe miki ai ya nuna miki kar yake kallonki tunda dai yaga ubanki ya san bashi yake miki hidimar da tasa kike jin kanki kina goga kafaWa da waWanda suka tsere miki ba kinga ko auransa kikayi yasan ba dan Allah bane kin aureshi ne saboda abin hannunsa. Ko da dai banga wata sufa ta rashin da'a a tattare dashi ba amma ki sani inda kaso dari ya yarda dake daga kalamansa kin rasa kaso hamsin na ?ima da darajar da yake kallonki dasu ada in ma be zarce hakan ba.

Ga wanda kika daWe tare dashi yana bauta miki yanzu da kika hango kazar data fishi mai?o shine kika tubure akan kw baki taSa cewa kina sonsa ba ai shikenan ni babu abinda zance miki tunda ubaki ya tsaya miki, Allah ya shige gaba" Umma ta faWa kafin ta maida hankalinta kan Film Win Hausan da aka fara a Arewa. Afeeyah na tsaye tana hawaye, jin Umman tayi shiru ta fahimci ta gama maganarta. Wai dan Allah da wane yare zata fahimtar da Umma? Abinda take tambayar kanta bata da amsa dan haka cikin muryar kuka tace

"Kiyi ha?uri Umma"
"Da kika mun me ni kuma? Ai ke ya kamata na bawa ha?urin shiga rayuwarki da nakeyi, ni ai babu abinda zan sake cewa kuma Afeeyah ai magana ta ?are tunda har kin turoshi kenan ba gudu ba jada baya kina kan bakanki shima kuma Malam naji ya bashi sati biyu ya turo, to dai ku tsananta bincike kar azo ayi abinda daga baya za'a ringa wlh tallahi" Umman ta sake magana, yanda tayi seka rantse da wata ?awa ko yar uwarta suke shawara akan auran wata, tamkar ba auran yar cikinta ake magana ba wai su tsananta bincike ita da Baffa kenan ta zame hannunta a ciki kai se a bar Umma dai.

Kuka Afeeyah ta fashe mata dashi tana zama a gurin
"Umma magana kikeyi fa tamkar kin zare hannunki daga cikin sabgata kina nufin nayi gaban kaina?" Ta faWa cikin kuka, Umma tace
"Au wai baki sani ba tuntuni? Ai ni tun daga randa kika nuna mun kin girma, kin isa ki yankewa kanki hukunci na zare hannuna daga sabgarki Afeeya ai yanzu kece uwar kanki, abinda kike so ne kuma na barki da zaSinki
Ke bakiyi ko rabin tashen da nayi a zamanin ?uruciyata ba, ko rantsuwa nayi bazanyi kaffara ba soyayyar da kike i?irarin kinawa wancan yaron batavkai zafin wadda nayiwa nawa muradin ran ba, da ace na zamo me kafiya da taurin kai irinki da ban auri ubanki ba har nazo na haifeki kika tsaya gabana kina faWin ke ga wanda ranki yake so.

Ban fara son ubanki ba seda na zauna dashi domin daya ganni yace yana sona ya samu Mahaifina uffan ban tofa ba nabi abinda nawa uban ya zaSar mun gashi naga ribar biyayyar danayi masa saboda shekara talatin da biyar Alhamdulillahi babu abinda zancewa ubangiji se godiya domin matsalolin aure sedai naji su gurin mutane badai a cikin gidana ba, ?ila dana bijire nabi zaSin raina kamar yanda kike shirin aikatawa Allah kaWai yasan takaicin da zan kwasa a tsayin shekarun nan" Umma tayi maganar cikin zafin rai. Afeeyah dai se kuka take Umman ta mi?e ta nufi ?ofa tana cewa

"Kukan daWi kikeyi, Allah ya gani iyakar yi mun kare mutunchinmu, se ki zuba ruwa a ?asa kisha kin jawo mana abinda za'a yi damu, ba unguwar nan ba na tabbatar duk wanda yaji labarinmu seya zagemu shekara uku kina cinyewa yaro kuWi yana miki hidima rana tsaka kice baki san zance ba Allah yasa yazo yace a biya shi se ki san ta inda zaki fara tattaro masa kaya da kuWaWen daya kashe miki"

"Haba Ru?ayya shin wai maganar nan ba zata mutu haka ba?" Baffa da tun daga soro ya tsinkayi mitar Umman ya faWa bayan dayayi sallama. Ta kalleshi kafin tayi murmushi irin na zallar takaici tace
"Malam kenan, ai ba'a ma haifi maganar ba balle ta mutu, yanda mutanen unguwar nan basa raina abin magana idan bamuyi wasa ba ai fita seta gagaremu na wani lokaci saboda yanda za'a ringa zunWen mu. A haka ma meye ba'a cewa duk akanta balle kuma aji wannan shegantakar Allah dai ya rufa asiri" ta fice daga falon ta barsu shida Afeeyah dake aikin kuka har sannan.

"Tashi kije ki kwanta" ya faWa mata a sanyaye, tabbas Umman batayi ?arya ba, tarayyar Afeeyah da Ahmad ba abinda mutanen unguwa basa faWi wasu ma cewa suke lalatarsu kawai sukeyi amma idan ba haka ba ?anin uwarta ne kona ubanta ze ringa mata hidima haka?.

Jay kuwa da tunani kala kala fal kansa ya bar gidansu Afeeyah, ya ringa bulayi a loko dan ya manta ta inda suka shiga kuma shi kaWai ya fito, daidai Allah yasa ya ganshi a titi sedai ya banbanta da inda ya ajiye motarsa dakyar da tambaya ya koma kan Titin daya ajiyeta ya figi motar a tsiyace ya bar unguwar.
Abu goma da ashirin haka ya ringa sa?a da warwara. Be taSa koda a hasashe hango Afeeyah ta fito daga irin low class family haka ba. Dukda bata yi masa ?aryar ita yar masu Arzi?i bace dan ko magana sukeyi takan nuna masa batasan abubuwa da yawa da yake maganarsu ba seya Wauka wasa takeyi seyau ya tabbatar ya kuma ganewa idanuwansa.

Asalinta ko matsayin mahaifinta be girgiza komai daga Son da yakeyi mata ba amma ?aryar daya kamata dumu tayi masa ita ta hasalashi, seda ya tambayeta idan da wanda yake nemanta har iyayenta sun sani ta gaya masa tace babu. A duniya idan akwai abinda ya tsana be wuci wula?anci da ?arya ba gashi ya kama wadda yake mutuwar so da dukka laifukan saboda shi ta masa ?arya ta kuma wula?anta koma wanene take tare dashi bayan tsayin lokaci daya Wauka lokaci yana hidima da ita, daga irin suturun da take sakawa kai ko fatarta ka kalla kasanba ?aramar kulawa take samu ba ta mayuka masu inganci tabbacin koma wanene yana da buruka masu yawa akanta shiyasa baya ?yashin kashe mata ko nawa ne amma ace lokaci Waya ta sutaleshi.

Tabbacin da yake dashi shine tana sonsa tunda gashi har mahaifinta ya faWa shima kuma ya yarda da hakan domin ya gani a idonta ya kuma fahimci hakan daga ayyukanta badan haka ba shima ze ce tana da target akansa idan ta samu wanda ya fishi watsar dashi zatayi. Allah kenan, wato tasu ?addarar kenan shida Yah Ahmad soyayya da irin waWannan yaran. Dalilin abinda yakeji akan Afeeyah yasa yaji ya farayiwa Ahmad uzuri bisa jure cin kashin da Fatima takeyi masa domin yanda yakejin Afeeyah a ransa ya tabbatar shidai baze zama sullutu irin Ahmad ba amma fa ko ta?i Allah ko bata sonsa se ya aureta a hakan sedai ta mutu tunda dai ya samu cikar burinsa amma shi ya zauna yana lallaSata tana wula?antashi bayan yana da makaman da ze iya juya komai dasu se yanda ya tsara za'ayi.
*MATAR MUTUM*
*NA MARYAM FAROUK (UMMU MAHEER*

*FIKRA WRITERS ASSOCIATION*

*LITTAFIN KUDI NE*
*PAY 500 A ASUSUN*
*7061838488*
*OPAY DIGITAL SERVICES*
*MARYAM FAROUK*
OR
*0709290797*
*ACCESS BANK*
*SE A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488*
*IDAN KATINE A DAUKI HOTONSA A TURA ZUWA LAMBAR SAMA VTU KUMA A TURA A 08142548705*

*Kuyi following dina a Arewabooks @Maryamfarouk01 inda zaku karanta wannan littafin tareda sauran littattafaina*
*NAGODE*

*BOOK 2*
*PAGE 21*
Ya isa gida yana fitowa daga mota ya hango Hajiya daga ?ofar shiga gurinsu tana tsaye kome take a daren se Allah dan goma ta gota tana hangoshi ta nufeshi da sauri.
"Hajiya lafiya? Meya fito dake a daren nan?" Ya faWa sanda suka gamu, tace
"Ina fa lafiya, tun Mangariba nake nemanka a gidannan kowa yace besan inda kake ba na kira wayarka yafi sau shurin masaki baka amsawa".

Se ya zaro wayar daga Aljihu, tunda ze shiga gidansu Afeeyah ya latseta ta shiga silent shiyasa beji kiran Hajiyar ba. Hajiya data gama ?are masa kallo daga sama zuwa ?asa tace
"Daga ina ka fito haka kaci uwar Gizina kamar wanda yaje gaisuwar surukai?"

"Sadik na raka" ya bata amsa yana shafa kai lokaci guda zuciyarsa ta shiga tsalle, tabbas da akwai gagarumar matsala domin dai ya sani ko sama da ?asa zata haWe idan shi yace yaji ya gani tofa Hajiya ba zata yarda da wannan haWin ba, a tsarin zubi na halitta Afeeyah ta dace da Matar da Hajiyar take hakaito masa sedai yasan an saSa lamba, yar talaka jikar talaka yace ze aureta tofa ya taro gagarumin ya?i ne ta shiga wanda be zamar mata dole bama tayi kane kane inaga maganarsa? Ta yuwu shi ba a gida zatayi masa nasa taron ba fili zata siya a gidan Radio ko Jarida ta wanke shi tas ta Ahalin daya ke shirin jajibo mata a matsayin surukai.
"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un" ya faWa a fili yana dafe kai, Hajiya da tayi magana harta gaji ya zuba mata ido kawai amma alamunsa sun nuna baya tareda ita, cikin hayagaga tace

"Da akayi me kake ja mana Innalillahi? Ina maka magana tuntuni ka tsareni da shegun idanunku na gado ko kuwa kana nufi kaima ba zaka shiga maganar bane?"

"Wace magana kuma Hajiya?" Ya tambaya yana dafe kansa daya shiga sara masa, hasaso Word War III ya tashi a gidan kwai yake da zarar maganar auransa ta fasu. Sati biyun da mahaifin Afeeyah ya bashi sunyi kaWan daya shirya harya saita komai bisa tsari ta yanda koda wani abu ze biyo baya ya zamana bayan cikar burinsa.

"Muje ciki na gaji, rabona da bacci me daWi har na manta ni kaWai kamar wadda ta rabawa masifu goron gayyatar biko da wannan ta fita wannan seta shigo" Inji Hajiya ta juya tana jan ?afafu. Matsalar Hajiya ?arama ce take neman zautata, Shegen Mijinta da yayi musu lamSo akayi aure tunda taje gidan nan a kullum sabon Episode yake haska musu na rashin mutunchi. Yanzu wai bata da lafiya sunje Asibiti an ce ciki ne da ita shine yace sedai a zubar ita kuma ta?i yace ta zaSa ko aurenta ko cikin wai shekararsa Ashirin da takwas be isa ya fara tara yaya su tsufar dashi ba. Tun wancan satin ake jaraba data kirata ta gaya mata tace ta je ta sanarwa Babarsa matar dake bata da mutunchi a faWar Hajiya Binta wai tacewa Hafsatun ita babu ruwanta bata shiga rayuwar yayanta yanda kowa ya ga dama haka yakeyi tunda yace baya son haihuwar yanzu seta ha?ura idan kuma zaman auren ne bata so ga hanya nan yammata da yawa ze samo wata ya aura.

Yau taje gidan Turai suka tattauna shine tace ta samu cikin su Naziru ta saka wani ya kirashi ya masa magana dan tasan Alhaji dai baze shiga wannan batu ba ?arshe kwancewa kanta zani zatayi a kasuwa kowa yasan halin da ake ciki to ta kira Naziru???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~? yace baya Gari, Zakariyyah yace yaron bashida mutunchi baze kirashi ya zageshi a banza ba Yakubu kuwa da tasu a tsakani daman bazata sako shi ba shine take ta neman Jafar wai shi ya shiga ya sasanta dan yanda Hafsatun tace tun jiya ya bar ?asar ya tafi Dubai bisa rakiyar wata budurwarsa da har gida ta biyo masa suka tafi daman kuma ba ba?on abu bane ?awayensa mata sunfi Maza zuwa gidan haka zasu wuni a part Winsa idan tayi magana in be dake ta ba se ya gaya mata maganar da zata gwammaci dukan da ita.

"Zan kirashi da safe Hajiya" Jay faWa bayan daya gama sauraronta. Ta muskuta tace
"Gara dai ka kira shi, ta yaya za'ayi banda shi ba Wan Arzi?i bane yace baza'a haihu ba? Dan uwarsa da ba'a haihuwa shi zezo duniyar ne ko kuwa da ba'a haihuwa da yawa layi zezo na haifa masa yar ya aura ya ringa zuga mata rashin mutunchi? Billahillazi se tayi dozen kuma a ?alla ciki maza takwas koma goma duk wannan jiji da kan da uwar sa takeyi dan ta haifi Namiji Waya tal se mun sauke mata shi Hafsatu zata cika gida musu gida da Yaya ta yanda in ubansu ya mutu aka tashi rabon gado za'a haWa harda su".

Cike da mamaki yace
"Hajiya, ina kika taSa ganin jika ya gaki Kakansa?"
"Za'a fara akansu" ta faWi irin ko a jikinta seya mi?e bayan daya ce "Allah ya rufa asiri bari naje na kwanta"
'Kai wai se yaushe zaka nunamun surukar tawa ne? Kuma yar wace ?asace? Ya kamata fa azo ayi abinda za'ayi tunda wuri dan auranka so nakeyi nayi biki na kece raini Wanda ba'a taSa kamarsa a faWin Najeriya ba" Hajiya ta dakatar dashi seya koma ya zauna ya lalubo wayarsa daga Aljihu, cikin hotunan da yayiwa Afeeyah ranar dayaje gidan Anty Sauda ya buWe kunno mata Waya, ta fito sosai a tsaye dukda fuskarta babu fara'a amma tayi kyau kwarjininta ya fito sosai.
"Kai kai kai zankaWi zu?i, Jafaru a ina ka samo wannan ta Gabas ce ko Yamma?" Hajiya ta faWa tana zooming hoton kafin tayi gaba tana kallon ragowar da sukayi tare, akan wanda ya rungumeta gaba Waya a jikinsa kanta na kafaWarsa dan haka rabin fuskarta ne ya fito Hajiyar ta tsaya, kamar idanunta zasu faWo haka take kallon wayar tace

"Kyau iya kyau gaskiya kun dace, turamun wannan shi zan nunasu Turai" ya karSi wayar da take mi?a masa, kunyar kansa ta kamashi da yaga hoton ita kuwa Hajiya kacaniyar nemo wayarta takeyi tana maimaita a tura mata zata aikawa su Turai suga surukarsu
"Wayar ba caji zan tura miki da safe" ya mi?e,
"Ai shikenan Allah ya kaimu, kai zan iya bacci kuwa? Ganin wannan yarinyar ya wankemun haushin shegen Yaron can ma wlh. Kai Allah dai yayi maka Albarka kai kaWai ko yaushe baka bani kunya kana biye da tsarina yanda ya kamata.

Sanda yaje Waki ya tarar Ahmad har yayi bacci, tun daya sahalewa kansa waccen mayyar yake bacci sosai da kuwa seya raba dare yana tsammatar kiranta kuma ba zata kira ba. Ya gama abinda zeyi ya kwanta sedai bacci ya gagara zuwar masa. Tunani kala kala suka addabeshi, laifin da Afeeyah ta masa na boye masa tana da wani bayan shi amma a yanzu damuwar Hajiya ta shafe wannan. Ta yaya ze sanar da saSanin abinda take hasashe kuma irin abinda yasan zata gwammaci jin komai dashi wato ace shi Jafar data ciwa burin duniya kan matar auransa take zakwaWin zuwan lokaci se kurum taji akasin abinda take buri wato dai a maimakon taji za'a tafi gidan Tayis Ac sama da ?asa se a shige Lokon Alfindiki gidan laka shi ya tabbatar yar Bakamiken da Yah Ahmad ya kwaso in ba'ayi wasa ba tafi Afeeyah galihu.

Wannan al'amarin kacokan yana ganin ishara ce Allah ya gwada musu daga shi har Hajiyar, dukda shi bece ya tsani Talaka ba kuma be taSa inkarin cewar baze auri Wiyar Talaka ba ta yuwu izgilancin daya ke yiwa Ahmad ne kan zuciyarsa bata san abinda ya kamata dashi ba duk matan Kano ya rasa wadda ze so se yar Bakanike se gashi ubangiji ya masa talala ya jefashi a komar wadda yake ga nata uban ko Tartibiyar Sana'a bashi da ita.

Ya shafa ?eya jin a garin lissafi ya sake tafka wata SaranSaramar, ya za'ayi kai tsaye ya yanke Babanta bashida sana'a dame yake ciyar dasu sedai in Sarawo ne ko Wan Maula irin Babansu Anty Rabi.
"Allah na tuba" ya faWa a fili jin shaiWan na sake ingizashi izgilancin nasa na neman tsallakawa kan Baban Hajiya Rabi kuma.

"Meya faru?" Ahmad da yayi juyi a bacci ya tambayeshi, bashi da nauyin bacci ko yaya akayi magana yanaji.
"Zancen zuci ne ya fito fili, sorry na tasheka" Jay ya faWa yana gyara kwanciya Ahmad ma baccinsa ya koma ya barshi yana cigaba da sa?a da warwara. Yayi tunanin ya Soye wa Hajiya Asalin Afeeyah ayi komai a sirrance tunda dai yasan Baba Al?ali baze kware masa baya ba, shima kuma Alhajin ko ya samu labari baze sake ?ai?ayin bakin gayawa Hajiyar ba dan silar na Ahmad har yau be gama komawa daidai maganganun da Yayansa suka sossoka masa ba basu gama sakinsa ba to amma kuma hakan bashida Fa'ida, duk yanda akayi daga baya magana seta fasu kuma abinda Hajiyar zatayi ta yuwu seya zarce wanda zatayi idan tasan komai tun daga mafari. Ko bayan wannan ma shi baze yarda ya gina wata mu'amala tasa da ?arya ko yaudara ba musamman maganar aure, to shi yaya zeyi yanzu? Yana son Afeeyah so me tsanani cewar ya rabu da ita bama abu ne me yuwuwa ba to ya kuma zeyi da mahaifiyarsa da a duniya babu abinda ta tsana irin Talaka da Talauci??

Bacci Sarawo ne yayi nasarar sace shi da Asuba kuwa ya farka da ciwon kai dan be daWe da baccin ba Ahmad ya tashe shi Asuba tayi ga tunani daya raba dare yanayi. Be iya dogon zaman lazumin da Ahmad yake tilasta masa yi ba idan yazo gida ya bi lafiyar gado saboda bacci da ciwon da kansa yake masa, lura da kamar baya jin daWi dan har idanunsa sun nuna hakan yasaka Ahmad be matsa masa ba shidai yaci gaba da jan carbinsa. Tun jiya yake fama da faWuwar gaba daya rasa ta mecece ga tunanin Fatima daya masa sau?i kwana biyu ya juyo dan seda yayi dagaske jiya kafin ya iya dakatar da kansa daga kiranta. Tunda Baba Al?ali ya shaida masa Baffah yace su dakata da zuwa daga nan ya sare daga lamarinta ya tabbata ya rasata kenan tun sannan kuma ya tilasta kansa ha?uri da al'amuranta, ko dar beji sonta ya ragu a ransa ba amma ya taushi zuciyarsa ta karSi ?addarar cewa Fatima ba matarsa bace, yana tsaka da jinyar zuciyarsa kuma sabon abu ya fara bijiro masa daga jiya zuwa yau Win tamkar ana masa kiranye haka yakejin so me zafi yana Azalzakar zuciyarsa, kasa dakatar da kansa yayi yabi umarnin zuciyarsa ya cire wayarsa dake jikin chaji ya doka mata kira.

FATIMA
Tana kwance kan abin sallah wand kusan akansa ta kwana, tun bayan da Umma ta gama soka mata maganganu jiya ta shiga Waki ta ringa kuka, Allahn daya jarabci zuciyarta da soyayya shi kaWai yasan halin da take ciki se Baffah da ya tausaya mata

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login