Showing 258001 words to 261000 words out of 467220 words

Chapter 87 - MATAR MUTUM COMPLETED 1-3 BY MARYAM FARUK.doc

23 Sep 2025

12143

raji'un" Afeeyah ta ?arasa tana fashewa da kuka kamar wadda akayiwa mutuwa.

Shiru Badar tayi tana sauraronta, duk kanta ya ?ulle itama ta yanda abunuwan suka faru sedai abu guda take da tabbaci akai shine koda ace Knowingly Jay ya zowa Afeeyah domin cimma wata manufa tashi akanta to tabbas babu saka hannu Ahmad. Ta na da tabbacin Ahmad baze taSa haWa baki dashi su yaudari Afeeyah ba, idan kuma ba shirin shi Jay bane to wani Al'amari ne daga Allah kuma shi kaWai yasan dalilin faruwar hakan

"Kiyi shiru Afeeyah ki dena kuka haka, ni wlh na rasa ma me zance abin ya bani mamaki yanda bakiyi tunani ba, amma wai daman tunda kuke rigima da Jafar ?anin Ahmad ke baki taSa ganinsa a fili bane ko a picture? Sannan shima kuma be sanki ba?" Badar ta tambayeta. Afeeyah ta tsagaita da kukanta tana jan hanci tace

"Ban taSa ganinsa ba Badar ban sani ba, banida tabbaci akan shi ya sanni ko akasin haka, kai tayaya ma zeyuwu ace shima be sanni a hoto ba? Definitely wannan abun shiri ne , it can't be a coincidence. Daman sun shirya abinsu ne nice sukayiwa wasa da hankali" seta sake Sarkewa da kuka Badar tace

"Ikon Allah, kuma fa Afeeyah suna kama, se dana gansu tare a picture na tabbatar da jini ba ?arya ba, kuma kinsan idan na ga picture Jay na kan rasa dawa yake yanayi wanda na sani se yanzu na gane ashe Ahmad ne, they have this unique eye shape and color ya kamata ace tunda wuri munyi hasashen haka"

"Muryansu ma yana shige, har tafiyansu maganansu duk yana shige se na ringa tunanin ido nane ko kawai tunanin Ahmad nakeyi shi yasa nake ganin kamanninsa da Jay ashe da gaske ne ba hasashe bane ba" Afeeyah ma ta faWa. Badar tace
"Kuma ke baki taSa tunanin ki tambayi wani a cikinsu ko ya san Wayan ba? ko ba close relation ba akwai kamannin da idan kika gani zaki san tabbas mutum sun haWa jini koda ba a kurkusa ba beside Jafar brother Ahmad kince shima ?an ?wallo ne ni se yanzu ma na tuna, amma ace ke tunaninki be taSa kawo miki haka zata iya kasancewa ba? Over 3 years kina tare da Ahmad ace baki san brothers Winsa ba musamman Jafar da suka fi sha?uwa ba haba Afeeyah wlh kema harda ke, sakarcinki ya fiya yawa. Yanzu waye ze yarda kan baki sani ba?
Wlh duk wanda yaji maganar nan ma cewa zeyi kina sane kika gwara kan yan gida Waya kawai yaudararsu kikayi".

"Badar ki barni naji da abinda ya dameni, ki kyaleni nayi tunanin makomata a yanzu" Afeeyah ta faWa cikin kuka, Badar bata sake cewa komai ba ba kuma ta ajiye wayar ba tana jiyo kukan Afeeyah me tafe da shashshe?a yanda take kukan zaka fahimci ba ?aramin Al'amari bane a zuciyarta. A hankali cikin tausasawa Badar tace

"Ki dena kuka, Allah yaga zuciyarki, idan har wannan abinda ya faru shiri ne koma wanene yake da saka hannu a ciki Allah baze bashi nasara akanki ba, idan kuma shirin Allah ne ina fatan hakan ya zame miki haske a cikin rayuwarki, in Allah ya yarda babu abinda ze biyo bayan wannan al'amarin se Alkhairi amma abinda nake so dake yanzu kiyi shiru kiyi ha?uri kuma muci gaba da addu'a, nidai ina ganin da ace wannan abun set up ne kuma da saka hannun Ahmad Afeeyah da baze kawo lefe gidanku ba. Yanda lokaci guda Jay ya barki da a wannan lokacin shima tafiya zeyi ba zaki sake ganinsu ba balle kiji labarinsu amma kina gani daga sannan nema abubuwa suka sake ?arfi a tsakaninku.

Jikina yana bani idan har set up ne kamar yanda kikace to shirin Jay ne kuma yaga babu yanda zeyi ya shiga tsakaninki da Ahmad shiyasa yayi giving up ya barki, ba?in cikinsa baya sonki da Ahmad shiyasa ya shigo rayuwarki don ya rabaku ko yanzu kika duba abinda ya faru ki godewa Allah domin beyi nasara ba shiyasa ma ya rabu dake kinga kenan Allah na sonki da Ahmad kuma Al'amarinku tabbatacce ne in sha Allah. Abinda nake so dake yanzu maganar nan ta tsaya iyakanmu, na san bayan yan gidanku ni da Islam ne se Sururat muka san relationship Winki da Jafar, ina da tabbaci akan zasu rufe mana wannan sirrin ina so kema ki binne komai a zuciyarki, karki bari kowa yasan abinda yake faruwa, zamuyi bincike mu gane komi daya faru we will watch both their steps idan har da wani abu in sha Allah we will find it sooner kafin ace an fara hidiman auranku ina addu'ar ma ya zamana babu komai and Jay kuma we must surely deal with him, we will give him a taste of his own medicine. Yanaji yana gani zakuyi aure da Ahmad ku rayu cikin aminci sedai ba?in ciki ya kashe shi".

Banda kuka babu abinda Afeeyah takeyi har Badar ta kai ?arshen maganarta taci gaba da rarrashinta tana ?o?arin nuna mata babu komai in Allah ya yarda.

"Ni Badar duk ba wannan ne matsalana ba ya zama da sanin Ahmad ko babu saninsa abunda yake damuna ta yaya za'ayi ace Ahmad da Jay are brothers? Badar kin manta irin son da na yiwa Jay ne? Do you think i can still live with Ahmad while my heart once belong to his blood brother?
Badar har raina na tsani Jafar, knowing his true identity now make me hate him much more than i do before amma kuma bana jin zan iya auran Ahmad na zauna dashi kuma naci gaba da ganin Jafar i just can't Badar" Afeeyah ta faWa cikin matsanancin kuka, Badar tayi shiru, she is confused, bata gane inda maganar Afeeyan ta dosa ba. Is she trying to say she is still in love with Jay despite abinda ya faru?

"Bangane abinda kike nufi ba Afeeyah, ki fahimtar dani" Badar ta faWa, cikin kukan Afeeyah ta sake cewa
"Ba zaki gane ba Badar kawai ki tayani da addu'a"
"Allah ya kawo mafita toh" Badar ta faWa cikin sanyi kafin ta ajiye waya.

Afeeyah kuwa seda taji kanta na barazanar tarwatsewa kafin ta ha?urtar da kanta tayi shiru. Tana kwance lamo Anty Sauda ta shiga Wakin, dawowarsu daga kasuwa kenan ita da Anty Hauwa Babbar Yar Umma FaWima yayar Baffansu suna ta zaryar zuwa ?araso siyayyar kayan kitchen da sauran abubuwan da basu ?arasa ba.

"Uhm kina Waka a kwance mu muna yawo a rana saboda ke ko?" Anty Saudan ta faWa daga bakin ?ofa, bata motsa ba se Anty Hauwan ce ta tare mata tana cewa
"To idan bata kwanta ba me kike so tayi? Amaryace fa dole ta huta kema lokacinki yi miki akayi kikaje gidanki kika tarar da komai a jere dan haka yanzu dole ki maida zubin Adashi"
"Ai shikenan, wlh na gaji Allah dai yasa mun gama daga yau se kuma a shiga jere tashi kiga wannan tukunyar ita ce wadda kike faWa ko?" Anty Sauda data zauna bakin katifar Afeeyan ta sake faWa.

Yanda fuskarta tayi mata nauyi dukda bata kalli mudubi ba tasan kumbura tayi kuma tambayoyi zasu tasata dashi na jin ba'asin meya faru hakan yasa ta sake lafewa daga kwancen tace mata
"Nifa bana jin daWi marata ce take ciwo"
"Ai to sannu, se ki tashi kisha magani ai" inji Anty sauda, cikin sha?iyanci Anty Hauwa tace
"Daure yarinya saura sati biyu zaki sha babban magani keda ciwon Mara sallama" suka saka dariya ita da Anty Saudan da take cewa
"Baki da mutunchi Hauwa"
"Wlh fa, nasan kayan gyara ne suka fara aiki Kawai zata wani langwaSe tace mararta na ciwo bayan ba Al'ada takeyi ba".

Seda Hauwan ta faWi maganar kafin Afeeyan ta gano wautar da tayi na ?aryar ciwon mara dan da gaske ba Period take ba gashi yanzu ta janyowa kanta wani fejin maganar.

"Gara da kika tuna mun, ungu *TULA TULAN* nan ki fara sha" Anty Sauda ta faWa tana mi?a mata wata leda me Wauke da robobi, dole ta tashi zaune amma ta ja mayafinta ta rufe fuska, Sauda bata damu ba ta shiga cewa
"Maganin gyaran Nono ne sadidan, daga sunan sa kinsa me yakeyi dukda baki da matsalar su amma ze sake gyara miki su su tsaya ?yam su ringa she?i sannan can headquarter ma ya sake gyarata tsaf 2 in 1 ne in gaya miki tested and trusted"

"Amma yar uwa ba amana, yanzu kinada *TULA TULA* amma kika barni ina yawo da silifas a riga a group Win Ummu-Maheer nake jin ana zancen abin nan ban maida hankali ba ashe maganin matsalata ne ina nan inata fama da macutan banza masu cakuda ?wayoyi da garin Masara suna bawa mutane" Anty Hauwa ta faWa tana fizge ledar daga hannun Afeeyah ta farke ta tana cewa

"Ai kuwa sedai mu raba nima ina fara sha kafin bikin nan na samu breasatcup ya zauna mun"

"Kwantar da hankalinki ai abin ba me wahalar samu bane, nan Kaduna *Maman Ilham me TULA TULA take, yanzun nan bari a kirata ki tura kuWi ta sako miki a mota (08135613021)*" Anty Sauda ta faWa tana lalubo wayarta ta karanto mata lambar babu Sata lokaci ta dannawa me Tula Tula kira nan take suka ?ulla ciniki tace zata aiko mata kayanta Kano gobe da safe saboda ma yamma tayi ne sannan da lokacin za'a turo mata, nan suka Sarke da hirar Tula Tula, Anty Sauda da ta daWe tana amfani dashi ta shiga bata testimony na yanda yayi mata aiki bayan gyaran Nono harda maganin Infection ga saukar daka Ni'ima.

"Amma fa ba sha take magani take bane, a hankali kina sha ya huda jikinki kafin ya ?are zakiga aikinsa" cewar Anty Sauda, Hauwa tace
"Haba na sani ai, daman duk maganin gyaran Nono ko na gyaran jiki da za'ace daga kasha zakaga aikinsa sedai idan da ?wayar bature akayi shi kuma irinsu suna da illa ga lafiya, dama ai se a hankali ka kuma juri sha yanda ya kamata kafin kaga aikinsa". Wannan damar Afeeyah ta samu ta sulale ???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?tsakar gida ta shige bayan gida ta wanke fuskarta, idan ta tuna Jafar da Ahmad gidansu Waya zuciyarta wani tsalle takeyi ta buga, ta kasa fassara abun, ya akayi haka ta faru? Abu guda da takeji kuma shine matsaya a zuciyarta ko da cewar ta tsani Jay, soyayyarsu ta zama tarihi a zuciyarta amma bata jin zata iya auran Ahmad ta zauna inuwa Waya da Jay a matsayin tsohon masoyinta.

**************
GIDAN ALHAJIN BECHI
Mata nata shirye shirye daga Sangaren Hajiya zuwa na Momy manya da yara kowa yaci burin Bikin Yah Ahmad da Jay, su biyun a gidan kusan favourite Win kowa ne shiyasa a shirin bikinsu yara matan gidan suka manta da Sangaranci dukda daman su abun da sau?i a tsakaninsu kawai dai yanayin da suka tashi a gidan na kowa nasa ya sani yasa ala?ar bata da ?arfi yanda ya kamata ace ta zama, shigowarsu Anty Dada da sauran Yayan Baba Al?ali dana ragowar yan uwa cikin shirin ya ?arawa abin armashi, su da kansu suka samu Baba Al?ali akan suna so a shiryawa su Yah Ahmad dinner bayan an kawo Amare yayi na'am da shawarar tasu nan sabon shiri ya tashi na yanda abubuwan zasu kasance.

A gefen iyaye mata Momy ta shirya zatayi Mothers eve, jin zancen dinner yasa suka canza shawara tunda daman sun shirya za'a Wakko Amarya tazo se suka bari kawai suyi yini a gida idan yaso a haWe shagalin duka ayi a gun Dinner, Hajiya kuwa as usual daman babu abinda ta shirya dukda ubannin Miliyoyin kuWaWen data ?wamushe a hannun Jafar da sunan zatayi hidima ta linkesu a jaka jira take Momy ta shirya biki ta sake kankanewa irin na bikinsu su Hajiya ?arama. Wani Musulmin Lace Turai ta kawo pieces uku kuWinsa ya tasamma Miliyan guda kowanne batayi shawara da Hajiya Binta ba ta kaiwa Momy duka ukun tace mata
"?awata ce Hajiya Batulu ta kawosu, bata buWe kayan ba se satin Azumi saboda tana ganin mutuncina yasa ta buWe mun naje zabar wanda zamuyi ankon dinner yaran nan shine na gano muku wannan, suke nan kalar pieces huWu ta Wauki Waya na karSo muku su kuyi anko ku uku ku saka ranar bikin nan".

Momy ta ringa juya lashin, tabbas ya haWu iyaka kuma ya mata koda talla ta kawo mata ba zata bari ya wuceta ba amma zancen Anko su uku harda Hajiya take ganin kamar baze yuwu ba dama dai ita da Hajiya Rabi ne dukda ita bata da matsala da hakan amma ta karSa da kanta ta nunawa Alhaji wanda suke sama sama tun akan zancen kai lefe se gashi ankon da zasuyi ya wanke fushin nasa cas ya cakewa Turai kuWinta kuwa ta karSi na Binta ita kuma Momy ta kaiwa Hajiya Rabi nata aka cigaba da shirin biki.

Tun ana saura kwana sha shida yan gidansu Amarya Fatiyyah suka diro Kano yiwa yarsu jere, gida daman masha Allah dayasha kayan dasuka kamatu dashi se gashi ya fito kamar a ?asar Larabawa. Babu inda basu zuba kaya ba har Sangaren da aka kulle matsayin na Ango seda suka buWe suka saka kaya pent house kaWai suka bari shima saboda kayan Gyming da suka tarar ya zuba a gurin suka gyra ko ina tsaf suka kulle gidansu suka koma Abuja. Randa akayi jeren Hajiya bata iya bacci ba bayan da taga video gidan, Turai tace mata

"Binta kinga uwa me zuciya ko? Kitchen Win yarinyar nan babu ce kawai babu na kayan Aiki, Allah dai yasa ta iya abinci shine fatan amma kam uwarta ta mata kaya in me adani ce har yayanta se ta kai musu wasu abubuwan nata wlh. Ni mantawa nayi da mun gayawa uwar yarinyar nan yanda kike kai naki Yayan a tsiyace babu kwanukan arzi?i da bata wahalar da kanta ba".

"Bana son wula?anci Turai itama rashin sanin darajar kuWi ne ya saka tayi hakan jifa wasu abun iri Waya sun kai kala uku ko fiye da haka banda Asara ba gara ta bata kuWin ta juya su ba? Ke nama tuna bari na kira wannan yaron naga alamun so yake ya rainamun hankali an fi sati yana mun wala wala kuWi fin shekara ana juyasu amma ace ba'a fara bawa mutum riba ba nifa shiyasa nafi ganewa na tasa kuWina a gaba nayita kallo haba" Inji Hajiya ta shiga neman number Naziru. Yanda ya saba bata uzururrukan Banki sun?i bari a tura kuWi masu yawa idan aka matsa EFCC zata iya tuhumar ina aka samo kuWin waya mutu waya dawo da haka ya binneta. Bayan ta gama wayar ta shiga sababi Turai tace

"Waini Binta naji ance Naziru ya buWe kamfanin haWa magunguna, wai daman abinda ya karanta kenan?"

"Oh ni Turai kema cikin sahun yan ba?in cikin zaki shiga kome? Se mutum ya karanci abu sannan zeyi sana'a dashi? Kuma fa kamfanin nan bashi kaWai bane haWin guiwa ne da wasu Abokanansa turawa shi kawai lasisi ya samo musu da filin da suka gina gurin fili kuma nawane ma ina sane na basu saboda wata rana zan iya tuburewa ince gurin duka ma nawane tunda dai suna nane akan takaddun fili" Hajiya ta faWa murya a sama. Turai ta sauke numfashi tace

"Maganganun da nakeji akan kamfanin ne sunyi yawa, har Ali seda yamun zancen zarge zargen da ake musu fa ya kamata ki matsa shi kiji ainihin abinda mutanen sukeyi dai saboda gudun abunda kaje ka dawo wata rana musamman da ba siyar musu da gurin nan kikayi ba duk inda bincike ya tashi ta kan Asalin mamallakin muhallin za'a faro"

"Allah ya tsinewa duk wanda bezo ya bincike su ba, paracetamol da chloroquine Win da suke yi su karyar dasu a farashi me sau?i ake ba?in cikin cinikin da sukeyi kome? Lallai ma Turai to an daWe ba'a zarge su ba nace Allah ya tsinewa uban duk shegen da be zargesu ba" daga man zaman ya watse dan duk yanda Turai taso data fahimtar da Binta jita jitar da akeyi a gari ta?i sauraronta.

Biki ya rage saura sati biyu Ango Jay ya diro Kano bisa tursasawar Ahmad dan shi a yanda yaso se ana saura kwana biyu ?aurin aure ze dawo, Amaryar ma tayi nacinta ta gama akan yazo suyi pre-wedding pictures yace ba za'ayi ba, ya dai bata kuWaWe masu nauyi da suka zarce bu?atunta akan tayi hidimar biki suna kuma waya duk abinda take ciki tana sanar masa dukda dai he is not feeling the weeding yanda ya kamata ita ma kuma ta lura da hakan har mita tayi masa akan be damu ba baya wani Wokin auransu yace mata kawai gajiya ce, a tsakanin lokacin suna da wasanni da yawa kullum a gajiye yake.

Dawowansa me be gaya mata ba, a Lagos ya sauka ya bi jirgi zuwa Kano inda Ahmad yake jiransa a Airport shida Asharab Autan Baba Al?ali, shi yayi musu hoto yayi ya Wora a Ig kafin kace me bloggers sun kwasa sun fara yawo dashi har ya kai ga idon Afeeyah.

Da yamma Jay na kwance akan Gado tunda suka dawo ya shiga cikin gida suka gaisa ya fito ya kwanta ko abinci ya kasa ci, gaba Waya ya canza ya zama wani shiru shiru kuma yayi rama, Ahmad na tsaye gaban wardrobe yana fitar da kayan da ze saka ya kalleshi yace
"Wai meya me yake damunka ne haka nayi tunanin gajiya ne amma kuma yanayinka yana sake lalacewa duk se wani sakeyin laushi kake Kodai tsoron Auran kakeyi?" Ya ?arasa cikin sigar
tsokana, Jay yayi murmushi yace

"Akwai gajiyan jikina kuma bayayimun daWi amma idan nayi bacci zan warware"
"Ba zaka rakani na kenan" Ahmad ya sake faWa se Jay yayi saurin jan Blanket yana cewa
"Not today Yah Ahmad daga dawowana already daman banajin daWi kuma zaka jani ka sake kaini inda zan samu wani ciwon".

Cikin haWe fuska Ahnad yace
"Amma mun rigada munyi magana ko?"

Cikin salon canza maganar tasu Jay yace
"Yah Ahmad inajin kamar i rushed my self lokacin daya kamata nayi aure beyi ba ko?"

"Kamar yaya?" Ahmad ya faWa yana ajiye brush daya taje kansa ya mayar da hankalinsa gaba Waya kan Jafar kamar yanda shima ya tashi zaune dakyau yana kallon Ahmad Win yace
*MATAR MUTUM*
*NA MARYAM FAROUK (UMMU MAHEER*

*FIKRA WRITERS ASSOCIATION*

*LITTAFIN KUDI NE*
*PAY 500 A ASUSUN*
*7061838488*
*OPAY

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login