Showing 240001 words to 243000 words out of 467220 words

Chapter 81 - MATAR MUTUM COMPLETED 1-3 BY MARYAM FARUK.doc

23 Sep 2025

12113

ta sharfaWo ?aryar da ita kanta se bayan ta dire maganar kunyar kanta ta dabaibayeta.

"Kinci darajar Son da nake miki shiyasa na kasa daurewa amma da wlh nayi niyyar bazan sake kiranki ba har se bayan anzo an tambayan mun auranki but i couldn't, my heart is going crazy about you ji nakeyi kamar nayi hauka just a day banji muryaki ba". Ina ruwa Afeeyah ta buga tsalle ta faWa dajin ba ha?ura Jay yayi da ita ba kuma ba fasa auranta yayi ba ashe punishing nata yakeyi da ?in kiranta aiko ta ladabtu.

"Kayi ha?uri" ta faWa cikin wata lallausar murya, Jay ya saki murmushi yace
"Zan ha?ura but let me see ur face first, oh na manta kin cire Sim daga wancan wayan ko? Then zanzo anjima zan taho miki da wani wayan amma ba fa jimawa zanyi ba dan ban gama hucewa ba, zan baki waya ne kawai na tafi"

Cike da zumuWi kamar zata taka rawa tace
"Allah ya kawo ka lafiya"
"Aiit, take care I love you" ya faWa, ta mayar masa da
"I love you more and i miss you" daga nan suka aje waya. Ya kalli Ahmad dake cin abinci yace
"Yau zamuje gurin Afeeyah"
"Wacece haka?" Ahmad ya tambaya, Jafar ya Sata fuska yace
"Soyayyata"
"Soyayyarka da kake mun boye boye akanta ko? Aje lafiya nima yau gurin Babyta zanje mun shirya".

"Kayi ha?uri, i promise you idan muka dawo zan gaya maka komai ba abinda kake tunani bane"
"Bana so kuma ba zanje ba na gaya maka gurin Babyta zanje nima" Ahmad ya faWa shima yana kumbura fuska kamar gaske Jafar yace
"How about ka rakani nima na rakaka? Amma gurin Soyayyata za'a fara zuwa"

"Then if you mean ita muje amma gurin Fatima zamu fara zuwa nine babba kaga matata tana gaba da taka kuma nasan wayo kake so kayi mu fara zuwa naka daga nan ka zame ka barni" inji Ahmad. Jay ya yamutsa fuska, kamar yasan abinda ya niyyata zeyi kenan, bashida zaSi tunda yana so Yah Ahmad ya rakashi gurin Afeeyah dole ya yarda da tsarinsa koda yake gara ma yaje face to face ya zazzagewa Wannan Fatiman abubuwan da suke a ransa, wato ta mayar da Ahmad kamar wani Toy tayi wasa dashi sanda taso ta yar sanda taso to yau kuwa ze buWe mata aiki.

Suka shirya bayan da akayi sallar magriba suka kama hanya. Jay ne yake tu?i, suna fita Ahmad ya kira Fatima danya shaida mata bashi kaWai bane kuma sun taho. Ita shaf ta manta ma da zuwan Ahmad tunda Jay yace mata zezo ta kasa zaune ta kasa tsaye, ta zabari mayafi ta tafi kusadasu aka mata ba?in lalle ranar daya fara zuwa yace mata yana so da yake da wuta nan da nan ta wanke kanta ta busar da Dryer ta tayi styling nasa da adon da ze bayyana sanna ta turara kayan da zata saka Two piece Gown and V Hijab data siya a gurin Ummu-Maheer (07061838488), yadi ne me sau?in kuWi amma kyakykyawan Winkin daya samu yasa idan ta sakasu ake Wauka tafiyayyen ne daga Egypt haka Hijabanta.
Umma nata kallon ikon Allah amma bata ce mata komai ba tasan sunyi waya da Ahmad amma bata zaton zuwansa takewa wannan shirin haka.

Tana ganin kiran Ahmad ta tuna da batun zuwansa, ta yi kasa?e tana tunanin mafita dan Jay ma yace mata yana hanya dukda dai yace ze biya wani guri tukunna. Da sauri ta shiga kiran layin Ahmad bayan data shirya ?aryar da zata masa da zata dakatar da zuwansa amma wayar ta?i shiga. Har wani tsirgawa cikinta ya ringayi saboda tashin hankali, ya zatayi idan Jay yazo ya tarar da Ahmad????
*MATAR MUTUM*

*NA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)*

*LITTAFIN KUDI NE*
*PAY 500 IN TO 7061838488*
*MARYAM FAROUK*
*OPAY DIGITAL SERVICE*

*IDAN KATI NE A TURA A DAUKI HOTONSA A TURA A 07061838488*
*NAGODE*

*KUYI FOLLOWING DINA @Maryamfarouk01 a Arewabooks*

*BOOK 2*
*PAGE 22*

Kiran Jay ta shigayi dan taji ya taho Winne ko yaya sedai wayar ta ?araci ringing amma be amsa ba. Idan hankalinta yayi dubu ya tashi har wani juyawa cikinta ya shigayi ta kasa zaune ta kasa tsaye. ?arinshiga tashin hankalinta data sake kiran Ahmad dan tadakatar dashi still dai shima be amsa ba. Zufa taringa keto mata dukda a tsakar gida take zaune. Ta zabura sanda wayar hannunta tayi ?ara, Ahmad ne, da sauri ta zura Hijab Win rigar jikinta har tana sha?e wuya, Umma dainata sabgoginta seka rantse bata sanda wanzuwar Afeeyar ba amma duk wani motsin da takeyi akan idonta ne.

Afeeyah kuwa soro ta wuce ba tareda ta amsa wayar dake ?ara a hannunta ba ta shiga wara ido amma bataga Ahmad ba lokacin wayar ta katse wani kiran ya sake shiga seta amsa da sauri.
"Zamuyi sallar isha'i kafin mu ?araso" ya faWa mata tayi saurin cewa
"Daman gidan Anty Sauda zan tafi, ka sameni a can kawai"
"Muna bakin titi already ki jira muyi sallah kawai sena kai ki" ya mayar mata kafin kuma ta sake cewa wani abu ya kashe.

"To ko Jafar zancewa ya sameni gidan Anty Saudan? Amma kumabme zan gayawa Umma ta barni na fita a daren nan?" Ta jerawa kant tambayoyinda bata da me amsa mata su. Kamar zata fasa kuka haka ta koma cikin gidan ta zauna tareda rafka tagumi, Jay ya?i amsa wayarta ta yuwu tu?i yakeyi Ya Allahu yau wacce irin rana ce da take neman zame mata mara sa'a? Daga shiryawarsu da Jay ya idan yazo yaga Ahmad bata san kalar tashin hankalin da zasuyi ba. Tana nan zaune har aka idar da sallar Isha'in ba tareda ita tayi ba. Tamkar an raWa mata guduma a kwakwalwa haka taji sanda wayarta ta Wauki ?ara a karo na biyu, ta mi?e ta le?a falo inda Umma take lazumi bayan ta idar da sallah tace mata

"Ahmad ne yazo yana waje"
"A dawo lafiya"Umma ta faWa ba tareda ta kalleta ba, se kace Wazu data bazama ta fita ta gaya mata inda zataje.
Afeeyah kuwa har wani sar?ewa numfashinta ya ringayi tsabar yanda take a firgice, dole ta sallami Ahmad koda kuwa ta kama data faWa masa maganar da zata saka ya tafi koda beyi niyya ba.

JAY
Suna tafe a mota suna hira gwanin sha'awa irin wadda suka sabayi da alamu yardar zeje gurin Fatima tareda Ahmad ta faranta ran Ahmad Win matu?a dan gashi nan a bayyane. Sun hau kan Gadar ?ofar Nasarawa ya tambayi Ahmad ina zasuyi.
"Mi?ewa zakayi Mandawari zamuje" Ahmad ya bashi amsa. Ya taka mota yana cewa
"Ai bansan gurin ba"
"Muje masallacin sarki idan mukayi sallar isha se na karSi tu?in" Ahmad ya sake bashi amsa. Jay yayi shiru kamar yacewa Ahmad ai nan ne unguwar su Afeeyah se kuma ya ?yale. Haka kawai yaki jikinsa ya masa wani iri, gudu yake da mota amma se gashi ya rage speed sosai ya koma tafiya a hankali har suka isa Masallacin, yanajin sanda sukayi waya da Fatiman yaja tsaki bayan da Ahmad yake ce masa wai gidan Yayarta zata tafi

"Kabarta ta tafi kawai se muje gurin my Afee, naga ta kirani ma bana so na amsa kewarta yasa na gudu na barka kace ban kyauta ba"
"Su tsuntsun soyayya, yau dai zanga wannan Afeeyah naga da wane charm ta sace zuciyarka" Ahmad ya faWa yana dariya.

Be manta hanyar daya bi har zuwa bakin titin da ya jira Malam yazo ya tafi dashi ba wannan tasa mamaki ya kamashi sanda yaga bayan sun isa Mandawari Ahmad ya karkata ya shiga titin unguwar su Afeeyah, kasa ha?uri yayi har seda yace masa
"Wai nan ne unguwar su Fatiman?"
"Nan ne, ko kana zaton wata GRA zamuje? To a nan lungun tawa Babyn data sace zuciyata take kuma wlh karka kuskura muje kace zakayi mata izgilanci domin dai ka sani Arzi?i da Talauci duk na Allah ne kuma a aure Tarbiyyar mace ake dubawa bawai girman gidan data fito ba".

Sam bama sauraron Ahmad yake ba illah baza idanu da yayi dakyau yana so ya gane layin da suka shiga da Malam. Akwai wani gida me rumfar langa langa doguwa a daidai kan layin mutane suna zama gurin ya zama kamar masallaci ma dan har butuci ya gani da drum na ruwa a gurin ranar daya zo wannan ya ri?e a ransa matsayin alamar daze ringa gane mashigar lokon nasu dukda idan ya shiga ciki babu tabbacin ya kai kansa saboda zurfin gurin.

Zuciyarsa ta buga Dumm sanda Ahmad yayi parking a daidai spot Win daya haddace a ransa. Ya ringa kallonsa sanda yake ce masa
"Da yar tafiya daga nan zadai ka iya ko?" Se ya ?a?alo murmushin dole yace
"Nida nake zagaye field sau babu adadi kake cewa zan iya wani Wan trecking kaWan". Ya fita yanajin wani sanyi na raysa gaSSansa dukda cewar zafi akeyi, ya ringa kallon gurin kamar meson yaga ya canza masa daga abinda zuciyarsa take hasaso ma, suka tsallaka yana biye da Ahmad a baya suka shiga cikin lokon

"Ba lallai abinda kake hasashe ya zama gaskiya ba, ?addarah bazatayi muku haka ba, baza ta saka ku Son abu Waya wanda baze yuwu ku mallakeshi a tare ba" zuciyarsa ta ringa ?arfafa masa guiwa. Ahmad dake masa hira jin baya amsawa ya saka shi kama bakinsa suka ci gaba da tafiya. Jay da yake tunanin idan ya dawo baze iya sake maida kansa gidansu Afeeyah ba se gashi taswirar Lokon na zuwar masa kamar zane a ?wa?walwarsa, bugun zuciyarsa ya tsananta sanda yaga dagaske sun tasarma layin da gidan Malam Hafizu mahaifin Afeeyah yake ciki, akan kwana yaci burki Ahmad ya kalleshi yace
"Ya akayi naga ka tsaya"
"Nasan Afeeyah tana can tana jirana, so nakeyi na kirata na gaya mata zanyi latti kartaji shiru kayi gaba zan biyo ka" ya rattabo masa ?aryar da yake ganin ita zata fitar dashi. Ahmad yace

"Ga gidan can ai mu ?arasa seka kirata ko sarki me Afeeyah" ba tareda ya kalli gidan daya nuna masa ba ya shiga shafa Aljihunsa yana laluben waya amma be jita ba ya saki ajiyar zuciya kafin yace masa

"Wayar na mota"
Dan Allah muje Jafar na sani daman se munyi haka dakai kuma tunda muka zo nan dai ya kamata ka daure kawai mu ?arasa yau Waya kaga Fatima na tabbatar duk wani grudges dake tsakaninku yau zaku warware shi muje please".

"Wannen ne gidan?" Jafar ya tambayeshi a ransa yana fatan ya nuna lungun daya mi?e yace a ciki gidansu Fatiman yake, kai shi da zata yuwu ma Ahmad yace makuwa yayi ba nan unguwar zasu zo ba saboda abubuwan da zuciyarsa take raya masa sunyi muni da yawa baya fatan ace hakan kuma ta zama gaskiya

"Wancan me Ash paint da ba?ar ?ofa daidai inda Solar ??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????take" Ahmad ya sake nuna masa gidan da kwatancen da duk yanda yaso da kautar da gaskiya dole ya shige shi. Ya zurawa gidan ido kamar me son gano inda aka ha?o ?asar da akayi ginin gidan da ita. Ahmad ya cigaba da tafiya yana ce masa
"Muje mana"
"Zan zo Yah Ahmad Allah bana son rigimar Afeeyah kaga ban gaya mata zan biya wani guri ba kuma na bar wayana a mota kar tayita kira taji shiru kaja mun tayi fushi" ya sake faWi, yanda yayi maganar da ace Ahmad ya mayar da hankali ze fahimci akwai abinda yake dannewa. Ahmad ya girgiza kai yace

"Shikenan, amma wlh idan baka dawo ba Allah ka shirya tarbar rashin mutunchin da zanyi maka" Ahnad ya sake faWa yana jefa masa key Win mota seya cafe yana murmushin da gara ace kuka ya fasa dashi kafin ya juya yana cewa
"Zan dawo".
Wucewa Ahmad yayi abinsa ya tsaya a ?ofar gidan kafin ya rangaWawa Fatima kira a waya, Jay kuwa baya yayi amma be tafi ba, so yakeyi ya tabbatar da gaske wancan gidan Yah Ahmad yake nufi sannan yana so yaga wacece. Fatima a gidan. Indai baya samu makuwar tunani ba wannan shine gidan daya zo shekaran jiya waccen gurin Afeeyah. Irin kallon daya yiwa gidan yasa ko a mafarki baya zaton ze kasa tantance shi balle a zahiri sedai idan kuma gizo idanuwansa sukeyi masa. Bayan fitilar Solar dake kafe a ?ofar fidan wadda haskenta har tsakar gida yake haska musu da akwai wutar nepa dan haka gurin tarwai yake ta yanda ko abun mutum ne ya faWi ze iya ganinsa.

Yana jingine jikin katangar daya lafe dan bazeyi gigin tsayuwa akan ?afafuwansa kaWai ba, yaga sanda Ahmad ya saka waya a kunne da alamu ita ya kira kafin ya ajiye mintinu kamar huWu tsakani ?ofar dake rufe ta buWe cikin ?asa da sakanni biyar Fatima ta bayyana. Tarwai yake hango fuskarta daga inda yake tsaye wadda yake ganin zanen fuskar Afeeyarsa akanta. Irin Doguwar riga Omo blue da farin V hijab da Afeeyah ta tura masa da hotonsu Wazun a matsayin kayan da zata masa kwalliya dasu ne a jikinta. Daga inda yake tsaya yana iya hango fuskarta da take kicin kicin babu ko Wigon fara'a inda ta Ahmad ke washe kamar yaron daya tsinci ha?orin makkah.

Bazece ga lokacin daya Wauka a gurin ba haka kuma baze iya wassafa tunanin da uake zarya a zuciyarsa ba ?afafunsa da sukayi sanyi har suka kusan kayar dashi a ?asane suka ankarar dashi bu?atar ya bar gurin da yake. Tafiya kawai yakeyi bisa jagorancin ?afafuwansa ba tareda linzamin idanu ko zuciyarsa ba har Allah ya fitar dashi bakin titin lafiya. Yayi diri diri domin besan ina ze dosa ba. Daga cikin barandar da mutanen nan ke zaune ya hango wasu mutum biyu sun haWa sahu suna sallah da alama makararrune, shidai baze ce ga yanda akayi ba ya tsinci kansa tsakiyarsu bayan daya saSule takalmansa, mutanen sukayi raka'a biyu suka sallame Jay ya mi?e ya cigaba da sallah. Tun suna tsammanin ze sallame bayan rama raka'a biyu da be samu tare dasu ba a zatonsu sallar isha'i ce se gashi suna lissafa masa raka'a takwas a jere, ya tashi ze kai ta tara wani dattijo ya ri?e shi yana cewa

"Bawan Allah wace irin sallah ce wannan raka'a goma fa kayi tahiya Waya, ai ko sallar Asham ce ba haka akeyinta ba". Be ja ba ya sallame sallar be kuma tanka mutumin ba ya mi?e ya kwashi takalmansa a hannu ya tsallake titi ya tsaya ganin motar Ahmad ya saka ya tuna a mota suka zo harga mu?ullin ma a aljihunsa seya zaro shi ya buWe ya shiga mutanen nan dai suka bishi da idanunu baki harma da hanci wasu na cewa
"Da alamu kan ba ?alau ba". Wani yace
"Gaskiya babu alamar hauka a tattare dashi idan dai aka ce damuwace ko firgici ya sakashi aikata hakan bazan musa ba"
"Shiko har wace kalar damuwa ko firgici ze sakashi jera raka'a goma har yana shirin Worawa ba dan an ri?e shi ba? Wai ba tare suke da yaron nan me zuwa gurin yar gidan Malam Hafizu ba? Su suka tsaya a waccen motar tare kuma suka tsallako yauwa ka gani ma gashi nan ya shiga motar ta yuwu wlh kara zube yake ba ilimin muhammadiyya kasan fa yayan masu kuWin nan se a hankali da yawansu sallah kawai sukeyi amma basu san me suke yi ba" wani zguduj?uri ya koro jawabin, oho Jay dai tuni ya bawa mota wuta yai reverse ya fice daga titin ba tare da sanin ina zashi ba.

A can ?ofar gidan Malam Hafizu kuwa bayan fitowar Fatima Ahmad ya kalleta cikin shau?in So, Allah ne ya jarabce shi da ita dan haka masu ganin baikensa su dena. Fuska a washe kamar kullum yana kallonta bayan daya amsa gaisuwar data masa a da?ile kamar an mata dole yace
"Kinyi kyau" tace
"Uhm" tana wani sake tamke fuska shiko be dameshi ba, ya daWe da sakawa a ransa Fatima tana cikin jerin mutane marasa yawan fara'a shiyasa haWe fuskarta ya dena bashi haushi. Ya gyara tsayuwarsa yana ce mata

"Yasu Baffah da Umma?"
"Lafiya lau suke" ta bashi gajeriyar amaa tana duba wayarta, ya sake mata murmushi yana jingina da bango yace
"Da Sabuwar Fatiman nayi magana a waya kwanakin nan, ina ta zumuWin nazo na tarar da ita se kuma naci sa'ar samun tsohuwar Sarauniya Fatima na nan tana cigaba da zuba mulkinta".

Tayi murmushin nan me kama da taSe baki bata dai ce komai ba shi kuwa yace
"Tare muke da Jafar yau dai abokanan faWa zasu ga junansu". Da sauri ta kalleshi jin sunan daya ambata tace
"Ashe ya dawo kenan?"
"Gobe satinsa Waya da dawowa shima soyayyarsa ce ta azalzaloshi ya taho yanda kuma suke buga wasan da zafi ina tsoron karfa suyi mana over taking" ya bata amsa yana kallon fuskarta kamar yanda itama take kallonsa, ta wani yamutsa baki kafin tace
"Allah sarki"
"Dan Allah idan yazo kar kiyi abinda ze sa ku raba hali, gaisawa kawai zakuyi ku maida komai daya wuce ba komai ba already na masa magana nasan shidai baze fara takalarki ba" Ahmad ya faWa cikin sigar lallashi.

Ta harareshi a fakaice kafin tace
"Wato nice ma zan takale shi na janyo abinda zamu raba hali? Kuma da zaka ce abinda ya wuce ya wuce harda zagin mun uba kana zaton yaci banza kenan? Ni bazan iya pretending naso mutumin daya rigada ya furta da bakinsa baya ?aunata ba kaima kawai neman tada zaune tsayene ya saka ka taho dashi, ni wlh dana san shine ba?on da kake nufin zaku zo tare bazan ma jiraka ba tafiyata zanyi dan inada abu me muhimmanci a gabana na aje na zauna jiranka" ta ?arasa tana sakin ?aramin tsaki.

?arara fuskarsa ta nuna rashin jin abinda abinda ta faWa ta gani kuma amma ta Wauke kai tana cigaba da duba Keypad wayar hannunta tana kallon lokaci kafin ta sake duban hanyar tahowa a ranta tana addu'ar Allah yasa ma yaji haushi ya tafi kafin ya dama mata salalan tsiya.

Ahmad kuwa haka ya haWiye abinda ya taso masa cikin sanyi ya kalli wayar da take ta juyawa a hannunta yace
"Meya samu wayarki na ganki da wannan?"
"Babu komai chaji ne babu na cire Sim Win" ta bashi amsa ba tareda ta kalle shi ba seya zaro wayarsa daga aljihu ya nuna mata yana cewa
"Ya kamata ma a canza ta tunda anyi lunching sabuwa tuntuni, IPhone Win kike so ko kina son Samsung irin wannan last week nima na canzata?"

"Waccen ma ta isheni na gode base ka wahalar da kanka ba" ta bashi

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login