Showing 360001 words to 363000 words out of 467220 words

Chapter 121 - MATAR MUTUM COMPLETED 1-3 BY MARYAM FARUK.doc

23 Sep 2025

12106

ai kaja lokaci. Bafa kafi shekara sha bakwai ba ka fara buga ?wallon professionally kusan shekaru ashirin ba wasa ba anyi abinda akayi Allah ya sa albarka amma dai za'a buga kofin duniya da kai kafin kayi ritayar ko?" Alhaji Babannan ya tambayeshi, kafin ya bashi amsa Alhaji Audu da wasu Abokanan kasuwancinsa suka fito daga ?aramin falo inda suka tattauna hakan yasa suka mimmi?e suka gaishe su cikin mutuntawa abin yayiwa Alhajin daWi kamar ya taka rawa. Ya yafici Alhaji Babangida suka fita tare raka mutanen tare Baba Al?ali kuma ya zauna gurin yayan nasa yana kallonsu yana murmushi.

Ashe irin ranar zata zo nan kusa? Seda su Alhajin suka dawo kafin aka buWe taro da addu'a. Zance guda Waya dai shi aka sake maimaitawa, su ri?e zumunchi su kyautata mu'amala a tsakaninsu ya rufe da nuna farin cikin yanda suka shirya zuwa gidan ba tareda kowa ya gayyato su ba da fatan kuma hakan ta ringa kasancewa sa'i da lokaci kafin shima Alhajin yayi musu nasa bayanin ya rufe yana cewa
"Akwai magana guda Waya da take da akwai, daga baya na samu labarin wasiyya da Wan uwanku ya bari ta hannun Al?ali, ina so naji, nan cikinku akwai wanda yake da muradin auran tsohuwar iyalin Ahmad ne ko kuwa... Tarin da Jafar ya sar?e dashi ya hanashi cigaba da maganar, aka bashi ruwa suka rufu akansa suna masa sannu kamar ma da gayya yake tarin se sake janyo shi yakeyi kusan minti biy??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????ar yana abu Waya kafin yayi shiru, Alhaji Audu dai kallonsa yake, jin yayi shiru ya saki murmushi mai ma'anoni dayawa kafin yace

"Yawwa kamar yanda nake cewa akwai wanda yake da ra'ayin hakan a cikinku ne?".

Shiru falon ya Wauka kamar babu kowa a ciki, da dai ace kunnuwansu na da ?arfin ji da tabbas babu abinda ze hanasu jiyo irin kiWan luguden da zuciyar Jafar takeyi, ?asa yayi da idanunsa yana jin sanyi na ratsa sassan jikinsa. Wato shirun da yayi be amsawa Alhajin sa?on daya aika masa dashi tun da daWewa ba shine yasa ya biyo masa ta haka.

Alhaji Babangida ya katse shirun da cewa
"Ai ina ganin koda ace akwai me wata niyya akan hakan baze iya faWa a nan ba, da cewa akayi duk wanda yake so yaje an bashi dama ?ila za'a fi samun ?arfin guiwa"

"Daman dai ni ina ciki" Salim ya saki maganar da se bayan furtata shi da kansa yayi da na sanin hakan saboda yanda idanu sukayi masa caaa kamar zasu cinye shi Wanye, babban abinda ya saryar masa da guiwa wani kallo da Alhajin da kansa ya jefa masa.

A hankali Jafar ya mi?e, Al?ali ya kalle shi yace
"Ina zakaje?"
"Kirana akeyi a waya" ya bashi amsa kansa na kallon ?asa.
"Ka saka wayar a silent ko ka kasheta koma wanene yake kira ya jira muna abu me muhimmanci ne a nan gurin" Alhaji Audu ya faWa cikin sigar umarni. Yayi jumm a tsaye, so ake ya zauna a faWi abinda ze sa ya haWiyi zuciya ya mutu amma kuma baze ?etare umarnin Alhajin ba dan haka ya koma a sanyaye ya zauna ba tare da ya kalli kowa ba.

Saboda takalar tsiya Alhajin beyi shiru ba yana nuna Jafar yace
"Kafin Ahmad su tafi ya barwa Al?ali wasiyyar idan be dawo ba Jafar ya auri matarsa kuma ya ri?e masa yaransa, Hassan ya tabbatar mun har akan gadon mutuwarsa ya sake jaddada hakan, yau shekarar Ahmad guda da rasuwa abinda yasa na ja lokaci saboda a bawa yarinyar lokaci da zata manta ta baya harta shirya tarbar wata rayuwar ta gaba. Labari ya zo mun cewa manema sun fara kai mata caffa hakan yasa naji tsoron karta amince da wani Allah ze kamamu da laifin rashin cika al?awari da gayya.

Gashi nan, nayi masa magana har karo uku shirunsa ya tabbatar mun da baya ra'ayi ba kuma ze iya cika wasiyyar Wan uwansa ba shiyasa nake tambaya a cikinku ko da akwai wanda zeyiwa Ahmad wannan alfarmar ya auri matarsa ya ri?e masa yayansa su tashi tare da uwarsu amma banda kai Salim".

Shirun da falon yayi yafi na farko aka ringa kallon kallo a tsakani, Jafar dai kansa yana ?asa gaba Waya ji yake duniyar ta masa Wumi. Ranar da Alhajin ya fara kiransa akan maganar ji yayi kamar ya Sace kawai yabi iska, be kuma bashi amsa ba Alhajin be ha?ura ba sau uku yana tuntuSarsa akan maganar koda yaushe kuma shiru yakeyi baya ce masa komai, to me zece?

"Kafin nan ina so kusan cewa Jafar da Ahmad sun taSa haWa neman ita aur....."

"Nidai bani da ra'ayin ?ara wata mace a yanzu, idan har saboda yara ne ai ku kuka ce na bar mata su idan zata yi aure za'a maido mun dasu akan haka mukayi yarjejeniya babu ruwan kowa tayi auranta ta bamu yara kawai ni abinda na sani kenan" Jafar yayi fargigit ya katse tafka-tafkar da Alhaji Audu yake shirin tafkawa kafin ya mi?e tsaye yana muzurai kamar wani zaki yace

"Duk wanda yake so yaje ya aureta ita kaWai banda yarana" daga nan ya saka kai ya fice daga falon.

Wani arnen murmushi Alhaji Audu ya saki kafin ya mi?e shima yana cewa
"Zaku iya tafiya, Hussani ka sameni a sama" ya wuce abinsa. Baba Al?ali ya dube su yace
"Kowa yayi ta kansa kuna dai gani babu sarari a guri idan kuma mutum ya matsa tsaf ze fito da bindiga nidai babu ruwana".

**********
Naziru, Zakariyya se Faisal zaune gaban Hajiya bayan tashi daga taron sunje kai mata kanun rahoto, Yakubu dama ko gidan be shiga ba ya wuce sabgarsa dan shi daman ba'a wannan zaman dashi. Ta gallawa Hajiya ?arama dake kwance a falon harara kafin tace

"Tashi ki fita munafuka" ta cicciSa ta fice daga falon ta tafi Wakin Anty inda duk yaya da surukan gidan suka tare. Tun jiya da tazo Hajiyar ta hanata motsawa ko ina hatta Alhaji bata bari taje ta gaishe shi ba saboda kar a ga yanda ta koma, ga tsohon ciki ga masifar miji sa uwarsa idan ka ganta a lokacin dole ka tausaya mata.

"Kun sakani a gaba kuna zare idanu nace wane munafunci kuma aka sake ?ullawa?"
Zakariyya ya gyara zama zeyi magana ta tareshi tace
"Aa dakata yi ta kanka dan Allah ka bari masu lafiya sumin bayani"

"Dama ai ce miki zanyi ki tambayesu ni na manta me aka ce" ya faWa yana Sata rai, tayi tagumi, al'amarin Zakariyya dai se godiyar Allah ya zama wani shi ba mahaukaci ba shu ba yaro ba, se yana tsaka da magana zeyi shiru yace ya manta abinda ake cewa dama babu zancen a faWa masa magana ba tunawa zeyi ba. Shi yanzu ya zamar musu nauyi ne kawai baya cas baya as sedai kullum yazo ya tasata gaba yana caza mata kai.

Mi?ewa Naziru yayi ya shige Wakin da ajiyar sa take, Faisal yayi ?asa da murya yace
"Wai fa Hajiya Alhaji ne yake tambaya a cikinmu idan da akwai wanda ze auri matar Yah Ahmad".

Ta lailayo ashariya me mai?o tace
"Se kuka ce me?" Yanda ta harzu?a ya saka Faisal saurin ce mata
"Salim ne yace yana sonta, shi kuma Alhajin yace Aa banda shi".

"Gayyar na ayya gayyar tsiya can su ?arata, inq Jafar ko banda shi akayi zaman?"
"Harda shi" Faisal ya faWa, kafin ya bada jawabi Naziru ya fito Waga daki alamar yayi shiru ya masa yana zare ido hakan tasa ya canza abinda yayi niyyar cewa daban yace
"amma be zauna ba ana gama yin addu'r ya tafi wai wani yana jiransa".

"Ina dai be ji wannan mummunan tayin ba?" Ta sake tambaya, ya gyaWa mata kai cikin tabbatarwa yace
"Beji ba gaskiya se bayan ya tafi ma akayi maganar". Shiru tayi tana kaWa kafarta me lafiya.

******
Jafar kuwa bayan ya bar gidan gudu ya ringa shararawa a mota kamar ze bar gari, me yasa Alhaji zeyi haka? Yanzu idan wani a gidan ya zagaya yaje gurinta kuma fa? Tunanin da yake yi a zuciyarsa kenan. Ya samu guri yayi parking ya kifa kansa a jikin sitiyari, ya ha?ura da ita, tunda ta auri Ahmad ya goge bu?atuwar zaman aure da ita amma kuma baze iya zuba ido wani cikin ahalin gidansu ya sake mallakarta a matsayin mata ba base yu ba.

Wayarsa tayi ?ara ya cirota idanunsa jajir ya duba, Fatiyyah ce, a rana bata kirashi ba ta kira sau goma tunda ya tafi kuma watanni goma kenan ko sau Waya be amsa wayarta ba har gara text message yana mayar mata da amsa. Yayi magana sa mahaifinta ya gaya masa abinda ya saka ya barta a gida kuma Babanta ya fahimce shi ya goya masa baya.

Kamar baze Waga wayar ba se kuma ya amsa, daga irin sa?onnin da take aika masa da nacin kiran waya yasan ta ladabtu kuma yanzu ze lan?wasata ya biyar da ita yanda yake so. Kuka ta saka masa, se kuma yaji tausayinta ya kamashi. Ya sani Fatiyyah tana sonsa, matsalar ta Waya rashin tunani akayi sa'a ta sake samun goyon baya gurin Hajiyarsa amma yana fatan komai ze gyaru yanzu.

"Na tuba Jay, dan Allah ka yafe mun" ta faWa cikin kuka. Shiru yayi kafin a hankali yace mata
"Ki shirya gobe zanzo mu taho", daga muryarta ya karanci tsantsar farin cikin da maganar sa ta sakata tace
"Dagaske Jaayy?"
"Ina miki wasa ne?" Ya tambayeta yana wani Waure fuska kamar yana gabanta tayi saurin cewa
"Aa, me zan tanadar maka?"
"Kanki" ya bata amsa dashi da yayi maganar da ita da yayiwa duk seda ba?on yanayi ya ziyarce su, tayi murmushi a hankali tace
"Allah ya kawo ka lafiya" ya amsa da "amin" ya katse wayar.

Jingina yayi jikin kujera ya lumshe idonsa saboda abinda yaji yana taso masa babu zato. Rabonsa da jin bu?atuwar mace a karan kansa tun ranar daya san Ahmad yana Asibiti, tunda ya rasu komai sedai yayi saboda gudun shiga ha??inta, wata shida kenan yanzu rabon da ko a ido ya ganta balle ya sauke mata ha??i shima kuma yana da bu?atar hakan. Windo ya kalla kawai yaga motar Salim ta gifta, asali motar Ahmad ce data fito a gadon Momy yayi mamaki ?warai ranar daya dawo yaga motar a parking space ya tambayi me akeyi da ita a gurin aka ce masa Salim ne yake hawa, ganin motar kaWai seda ya jefashi cikin yanayin da har ?walla ya zubar amma shi Salim ko a jikinsa yake iya hawa motar ganin da yayi masa yanzu ya tuna masa da abinda ya baro a gida, a fusace ya tayar da motar kawai yabi bayan sa.

Dole ma yaji wane salon raini ne har haka da Salim zece yana son Fatima ze aure ta? Sunyi tafiya me nisa kafin kuma ya tsaya yana tuhumar kansa a dalilin da ze saka shi bin Salim Win, yayi tsaki ya juya motar kawai ya wuce gida. Wani kamfani ya kira suka gyara gidan ko ina ya shiga saiti, bayan sallar la'asar ya sake komawa can gidan Alhaji Audu, tun shekaran jiya daya dawo basu wani zauna da Hajiya ba. Seda ya fara shiga falon Momy kafin ya wuce gurin Hajiyar tareda Ahmad a hannunsa ya tarar da ita da wata mata, yasan matar amma ya gagara tuna sunanta ko inda ya santa ganin magana suke mai muhimmanci yasa kawai ya gaida Hajiyar ya fita akan ze dawo idan anyi magriba.

Hajiya ta taSe baki ta bishi da harara, Sahura tace
"Ikon Allah, ina ganin sitikarsa fa Labaran duk ya li?e Wakin sa dasu, girman Wan mutum babu wuya su kuke goyo sanda kuka bar gwauran dutse ko?"

"Haba, sanda muka dawo nan ai na haifi Hajiya ?arama inada cikin Faisal ma" Hajiyar ta bata amsa. Tattare kuWaWen da Hajiyar ta bata ta shigayi tana cewa
"Bari na tashi, kinsan shi Malam gajere i yanzu ne lokacin samunsa, gara in hanzarta naje idan yaso gobe se na tafi kwanar Wan gora gurin Malam Habu in shiga Zariya in kaiwa Na ta'ala nasa se in dawo nan kuma gidan me shirgi itama a kai mata nata aikin. Kinsan fa idan matsala ta girma Malami Waya baya iya maka, haWa hannu ake da yawa Malamai da yan bori shine se kiga nan da nan ?ura ta lafa".

"Ai shikenan, fatana dai naga sakamako me kyau dan billahillazi kika kai musu kuWaWe na sukaci banga aiki ba se kin biyani dan ban gaji asara ba" Hajiyar ta sake faWa. Sahura ta washe baki tace
"Hajiya kenan, kedai ki zuba ido kawai zaki ce na gaya miki. Kinsan ku Malam da kuka saba bi na masu kuWi ne idanunsu sun buWe cutarku kawai suke suna ci muku kuWi dan idan ma kun tafi wasu ne zasuje, mu kuwa namu masu neman na cefane koya kika yafa musu aiki zasu miki sadidan saboda ki kawo musu wasu. Ai matsala taso ?arshe yo Allah na tuba da tuntuni kika nemeni Hajiya ai da yanzu wani zance ake ba wannan ba" da haka ta tattara jakarta da ta cika taf da kuWe ta tafi.

Sahura Aminiyar Lantana ce mai aikin Binta tun can baya, bayan da suka baro gwauran dutse tare suke zuwa da Lantanar nan gidan kafin ciwo ya kwantar da ita har kuma Ajali ya sauka dan sanda Lantanar ta kwanta ma Sahurar taso taci gaba da zuwa tana mata aikin ta?i sam ta manta da kabarin ta a duniya ma seda gumu tayi gumu gabas da yamma ta rasa mafita ranar tana zaune kawai Sahurar ta faWo mata a rai.

Ta iya shige shige, malamai na birni dana ?auye babu wanda bata sani ba, tun sanda Hadiza ta fita ta bar Aisha ba yanda Sahurar batayi ba akan ta kaita inda Alhajin ko kallon mace be isa ya sakeyi ba balle ya yo mata kishiya amma ta?i, a lokacin gani take duk ?aryar harkar Malaman ita kuma kuWin ta bana ci bane yanzu da taga babu sarki se Allah ba shiri ta tafi unguwar tayi katarin samun Sahurar na nan da ranta shine fa ta yayibota ta gaya mata damuwoyinta ita kuma tace ta kwantar da hankali kamar tayi filo da jinjiri dan dai ta kawo kuka gidan mutuwa.

A can baya inda shuke shuke suke da kujerun hutawa Jafar ya zauna da Ahmad har aka kira sallar Magriba kafin ya mayar dashi cikin gidan ya tafi masallaci, sam bashida rigima, da aka idar da sallar be fito ba ya zauna yana kallon Alhaji Audu na hararar sa amma ya?i bari su wani haWa ido sosai, seda yayi sallar isha'i ya koma cikin gidan, Wakin Hajiya ya fara shiga tana zaune akan kafet ta mi?e ?afarta Waya daga cikin masu aikinta na shafa mata man zafi a ?afar me lafiya ya shiga ya gaisheta ta amsa a sama se yaji ba daWi amma ya zauna kawai yana tambayar meya samu ?afar tayi masa banza.

"Dama Hajiya ina so gobe naje na dawo da Fatiyyah" ya faWa yana kallonta. Ta Waga kai ta harareshi tace
"Ai ido ma zura maka naga gudun ruwanka. Da zaka jingine ta a gida uwar me tayi maka bani ce na maka faWa ba saboda itace marainiyar wayonka seka sauke fushinka akanta ko? To karma ka dawo da ita Win ka barta tayi ta zama ku ta shafa bani ba" ta fizge man zafin daga hannun yarinyar tana ganin haka ta fice ta basu guri. Seda ya gama nanata abinda ze gaya mata a zuciyarsa kafin a hankali yace

"Ina so na nemi alfarma a gurinki Hajiya, dan Allah ki fita a sabgar Fatiyyah bana son wannan haWa kan da kikeyi da ita kuna abinda be dace ba wlh Hajiya rainaki zatayi ko yanzu baki ga illar abin ba a gaba zaki ce na gaya miki sannan nima kina ?ara jawowa tana rainani duk umarnin da nayi mata ba zata ji ba saboda kina goya mata baya akan rashin gaskiya".

Mici mici tayi da ido tana kallonsa harya kai ?arshe ta buWe baki zatayi magana se kuma tayi shiru kawai tayi ?wafa ta tashi daga ?asan da take ta koma kan kujera tana kallonsa, shima shirun yayi, kusan minti biyar ya kalli agogon sa sannan ya mi?e cikin fushi tace
"Ina zakaje? Ko har ka gama ?are mun tanadin ubana zaka tafi?"

"Yanzu dan Allah menene abin laifi kuma a maganata Hajiya?" Ya tambayeta kamar zeyi kuka. Cikin faWa tace
"Dama ina zaka ga abin laifi a ciki Jafar? Yanzu ni ba wannan maganar ce a gabana ba, Wazu ubanku ya tara yan uwanka yana faWa musu wata magana mara kan gado" kome ta tuna se kuma tayi shiru. Ya koma ya zauna yana kallonta yace
"Wace magana kuma Hajiya?"
"Aa shikenan, na manta an ce baka gurin maimaitata bashida amfani tashi ka tafi kawai" ta faWa tana wani haWa rai.

Dariya ma ta bashi se kawai ya tashi yayi mata sai da safe ya fita ta rakashi da harara tana cewa
"Zanje nawa kaina kasassaSa tunda dai Allah yasa baya gurin ai shikenan, maganar ma ba zata sake tashi ba badai wani a cikin gidan nan ya auri yarinyar nan ba kuma taje can alo tsiya wani ya kwasa".

Kusan duk abinda ta faWa ya jita dan yana dur?ushe yana saka takalmi a ?ofar Wakin, yana shiga falon Momy ya tarar da Amal a kwance a ?asa tana birgima fuska face face da hawaye tana ganinsa ta mi?e da gudu ta Wane shi"

"Me kuma ya faru?" Ya tambaya se lokacin ya lura da Salim dake tsaye yace
"Kawai dan zan mayar dasu gida shine takewa mutane wannan kukan kamar wadda za'a yanka". ?auke kansa yayi kamar beji abinda Salim Win ya faWa ba ya kalli Anty Halima ?anwar Momy yace
"Me akeyi mata Anty?"

"Yo wannan har se anyi mata wani abu Jafar? Rigimarta bata sallah. Daga dai cewa suzo a kai su gida gobe da makaranta shikenan ta hau mana bori"
Momy tace
"Duk ga wanda ya gigitata nan ai, ina jinku seda tace ita Dadynsu ne yace ze mayar dasu ya tsaya yana zare mata ido harda cewa ze zaneta idan bata tashi ba, to kafin a dake tan ne ta fara rage kuka".

Kallo me kama da harara Jafar Win ya jefawa Salim kafin ya juya yana cewa
"Bari na mi?a su Momy, seda safe". Da Allah ya taimaka har suka fice Hajiya dake can Wakin ajiyar Naziru bata sani ba. Seda yayi musu siyayyar kayan ?walama

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login