Showing 381001 words to 384000 words out of 467220 words

Chapter 128 - MATAR MUTUM COMPLETED 1-3 BY MARYAM FARUK.doc

23 Sep 2025

12151

ra'ayi kan hakan ko bashi da? Dan ya so ta a baya ai ba lallai ya zama har yanzu tana ransa ba duba da yanda al'amura suka faru sannan kuma koda Ahmad ya bar wasiyya idan Allah be ?addara aure a tsakaninsu ba haka nan za'a ha?uri ta auri wani daban maganar munafunci ai duk bata taso ba" Al?ali ya tare Alhajin.

Maimakon yayi ?asa sema sake hasala yayi yace
"To idan ba munafunci ba naga yarinyar ba kai kace dama can budurwarsa bace? Ina nan har ciwo ka ringa kwanta mana saboda ita? Duk a saboda me ya takure rayuwar sa ya Wauki ?unci ka Worawa ranka saboda duk ba dan ya rasata bane shine yanzu za'a ringa binsa ana lallaminshi akanta se kace an gaya masa ta rasa masu sonta da aure ne?
Wlh ni badan wasiyya Ahmad ya bari akan al'amarin nan ba kai baka isa kasa na maimaita maka magana sau biyu ba, ko da kaga na dakatar da Salim kawai saboda na cikawa Ahmad muradin sa ne kuma Allah ya gani nayi iya yina, tunda kaga ba zaka iya rufawa Wan uwanka asiri ba se kaje ka ?arata, daWin ta Allah ya bamu yaya maza da yawa, ga saurayi ma yace yana sonta kuma idan Allah ya kaimu gobe da kaina zanje na tambayowa Asharab auranta in sha Allahu kuma bazan baro gidansu ba har se ta tabbata a matarsa, tashi ka bani guri dama ai seda nace karka kirashi ka?i ji ai gashi nan ka gani".

Ko gezau Jafar beyi ba yana zaune kamar an dasashi zuciyarsa banda bugawa da ?arfi babu abinda takeyi. Yasan Alhaji kaifi Waya ne, yanda yace ze nemawa Asharab auranta ba wai barazana bace dagaske yakeyi to shi kuwa idan haka takasance wace gadar ya kamata ya hau ya faWo ya dagargaje kawai kowa ya huta? Ya za'ayi ma yana raye ya sake saka ido ta auri wani cikin Ahalinsu? Ai wlh sedai kowa ya rasa, in har be sameta ba to kuwa babu wanda ya isa ya mallaketa.

"Ba zaka tashi ba sena buge ka?" Alhajin ya sake daka masa tsawa yana janyo wani ?wagiri da yake ri?ewa idan ciwon ?afarsa ya motsa. Ya Waga kai ya kalli Alhajin idanunsa kamar zasu zubo da wuta saboda yanda suka kaWa sannan ya kalli Baba Al?ali murya a dakushe yace
"Hajiya tace bata yafe mun idan har na sake maganar auranta".
"Ita Bintan tace haka?" Baba Al?ali ya tambayeshi, ya gyaWa masa kai alamar eh se ya sake cewa
"Idan ba dan ta hana ba kana sonta kenan?"

Seda ya kalli Alhaji dake girgiza ?afa ya kumbura yayi suntum da fushi kafin yace
"Ina sonta Baba"
"Kaje ka kawo sadaki da kuWin aure dan sisi bazan biya maka ba ba auren fari bane kuma ka nemi inda zaka ajiyeta idan kuma a gidanta zata zauna se ayiwa gidan kuWi ka ringa biyansu haya nan da sati huWu in sha Allahu za'ayi komai a gama" Alhajin ya faWa kamar me jiran yaji amsar sa. Ya buWe ido yana kallonsa, yama za'ayi haka ta yuwu? Ce masa fa yayi Hajiya ta hana bata yafe ba tace zata tsine masa kuma yace nan da sati huWu ze masa aure ita kuma Hajiyar ayi yaya da maganarta?

"Amma Alhaji tace fa zata tsinemun, wlh na gaji, rayuwata kullum sake shiga ?unci takeyi kuma nasan hakan yana da nasaba da irin kalaman da kulkum Hajiya takeyi akaina ina so nayi mata abinda take so idan har hakan ze sakata farin ciki ta cigaba da saka mun albarka yanda takeyi da na shirya na hakura da komai. Tunda na rasa Yah Ahmad na cigaba da rayuwa to ni me yayi mun saura kuma?

Ni yanzu ba auren Afeeyah bane abinda nake bu?ata, nafi so ku taimaka mun Hajiya ta yarda na karSi su Layla koda hakan ze zama fansar soyayyata na amince dan nafi bu?atarsu a yanzu sama da zama da ita"

"Tashi ka bamu guri" Alhaji Audu ya faWa cikin yanayin da dole ya tashin ya wuce yana waiwayen Baba Al?ali fuskarsa na alamun neman Wauki.

*Assalamu alaikum*
*Yar uwa kina da labarin UMMU_MAHEER COLLECTION kuwa?*
*Kasuwar online inda zakiyi siyayyar kayan ado da kwalliya kama daga kan suturun sakawa, mayafai, hijabai, kayan shafe shafe dana tsafta na kamfanin Oriflame, kayan yara na sakawa dana kwalli duk muna dasu masu kyau da sau?in farashi daidai da aljihunku*

*Muna da kayan back to school wato dangin su Lunch box, school bag, lunch pack da sauransu*

*Sannan akwai kayan kwalliyar Waki, muna yin gadaje, kujeru da duk wani abu daya danganci gida se wanda kika zaba kuma wanda kudinki ya baki*

*Kayanmu garantee ne, idan kinyi kasuwanci damu zaki dawo har ki kawo wasu da yardar Allah. Muna kano muna kuma tura kaya ko ina a faWin cikin ?asar nan da wajenta*
*Kai tsaye kiyi joining WhatsApp group dinmu ta kan wannan link Win*
https://chat.whatsapp.com/FKsWield4wPKepHDZwtPUP
*Ko kuma ayi mun magana akan number 07061838488*
*Nagode*

*MATAR MUTUM*
*NA MARYAM FAROUK (UMMU MAHEER*

*FIKRA WRITERS ASSOCIATION*

*LITTAFIN KUDI NE*
*PAY 500 A ASUSUN*
*7061838488*
*OPAY DIGITAL SERVICES*
*MARYAM FAROUK*
OR
*0709290797*
*ACCESS BANK*
*SE A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488*
*IDAN KATINE A DAUKI HOTONSA A TURA ZUWA LAMBAR SAMA VTU KUMA A TURA A 08142548705*

*Kuyi following dina a Arewabooks @Maryamfarouk01 inda zaku karanta wannan littafin tareda sauran littattafaina*
*NAGODE*

*BOOK 3*
*PAGE 35*

Kwana uku a tsakani Baba Al?ali, Alhaji Abdullahi, Alhaji Babangida da Alhaji Zakariyyah sukaje gidan Malam Hafizu nemarwa Jafar Auran Afeeyah bisa umarnin Alhaji Audu. Tun saura kwana biyu suje Baba Al?ali ya kirawo Baffan akan zeje, be kawo komai a ransa ba saboda Al?alin ya kan je lokaci lokaci ya duba su Layla suyi hirar duniya ya tafi koda yagaya masa zuwan da wuri yayi tunanin saboda wani sa'in sunayin saSani yaje gidan shi kuma ya fita, ?ila akwai abinda yake so su tattauna shiyasa ya sanar dashi da wuri. Yanda yace Win kuwa ranar guraren sha Waya na safe sukaje, Baffa yayi mamakin ganinsa bashi kaWai ba sedai bece komai ba, yayi musu iso cikin gida a ?aramin falonsa da yake a waje suka zauna Umma ta gabatar musu da ruwa da zobo da lemon roba se cincin da dubulan da akayiwa Anty Sauda ba'a kai mata ba ta Wibar musu a ciki dan shirin da tayi na zuwan Al?ali ne kawai kamar yanda Baffan ya gaya mata, sunyi awara da safe da ita suka karya ta rage akan zata soya maaa idan yazo se gasu kuma da yawa seda ta sallame su ta wuce Wakin ta tana mamakin me suka zo yi haka su da yawa kuma?

Afeeyah ta fita makaranta dan haka ta shige Wakin ta inda Ahmad yake bacci ta kira Sauda ta gaya mata abinda yake faruwa.
"Amma ko jiya mun daWe muna waya da ita da daddare amma bata ce mun zasu zo ba. Nice ma nake nuna mata babu komai ta amince ta aure shi saboda ta haka ne kawai zata rayu da yaranta Umma amma tace Aa ita babu aure ma a lissafinta to bansan ya akayi ba kuma ko kuma dai su daga can suka shirya abinsu tunda dai ko waya ita basayi dashi balle ace da saninta" Saudan ta faWa. Umma tace

"Lallai Sauda, wato kece ma kike bata shawarar ta auri Jafar duk kin manta irin cin mutunchi da tozarcin da uwarsa ta ke mana ?iri-?iri ta nuna bata ?aunar mu, menene bata zo cikin gidan nan ta faWa ba? Har maita ta Wora mana shine har zakiyi mata sha'awar ta auri Wanta amma dai wlh kema kin bani mamaki. Ina laifin ma ace wata daban ce cikin matan gidan uwarsa amma badai waccen mahaukaciyar matar ba bazan taSa yarda da wannan haWin ba".

"Ni wlh Umma ba wani abu nake dubawa ba se rayuwar yaranta su nake tausayi Jafar Win dai shi kaWai ne wanda zasu rayu dashi su ringaji tamkar suna tare da mahaifinsu. Yanzu Umma waye ze aureta da yaya huWu? Ko ta samu ma kinsan dai bazasu taSa bari yaransu suje agolanci ba kuma ba zasu yarda ta barsu a hannunki ba. Ko ba wannan yaranta Mata ne Umma, zefi kyau ta rayu tareda su ta tarbiyyantar dasu da kanta tunda dai da ranta kuma tana da damar yin hakan. Nidai in dai har dagaske tambayar auren sukazo babu wani jeka ka dawo kawai Umma a amince. Ni kaina da ina ?in abin amma da Abban su Huzaifa ya fahimtar dani na gane hakan shine rufin asirinsu baki Waya.
Tana sonsa yana sonta, matsalar uwarsa can ita ta sani hakan ma wata ishara ce Allah ze nuna mata idan abin ya tabbata talakan da bata so ta auri Wanta waya sani ma ko da rabo tsakaninsu kinga seta haWiyi zuciya ta mutu Afeeyah ta haifar mata jika" Sauda ta sake faWa.

Umma tayi shiru, akwai gaskiya cikin maganganun Sauda itama tana yawan tunanin makomar su Amal domin dai kamar yanda sukace sun bar mata su ne zuwa ta tashi yin aure dole zasu karSe su idan ma sun bar mata a wannan zamanin babu wanda ze aureta da yara huWu sedai dan abin hannunta ba kuma ze yuwu ta tauye rayuwarta ta zauna tace ba zata sake aure ba saboda su tabbas auran na gidan shine maslaha amma gaskiya tana da ja akan Jafar, gara koma wanene cikin sauran yaran gidan, ai ga Salim shima ya nuna yana ra'ayinta gara Shi dai akan Jafar Win dan gaskiya ita bata son tashin hankali halin uwar Jafar ba abin so bane.

Tana ta sa?a da warwara har ba?in suka tafi Baffa ya sameta a Waki ya ajiye mata kuWi. Ta kalleshi ta kalli kuWin fuskar sa babu walwala yace
"Wai kuWin aure ne da sadaki suka kawo" ta gyara zama da sauri tace
"Na me?"
"Na Afeeyah suna nemawa Jafar auranta" ya bata amsa.
Tayi shiru kusan minti biyu kafin ta sake cewa
"Daman kunyi akan zasu zo neman auren ne amma shine baka gaya mun ba?"

"Wace irin magana ce kikeyi haka? Ina muna zaune dake ya kirani yace yau ze zo? Idan nasan zancen neman aure ne ze kawo su zan zauna ni kaWai ne ba zan kira waWanda zasu tayani karSar maganar ba? Nima yanzu suka zo mun da batun duk kuma yanda zanyi na kaucewa hakan banyi nasara ba. Allah ya sani ba dan son zuciya ko wani abu ya saka na amsa musu ba se dan naji nauyin na kasa basu damar cika wasiyyar da suka ce Ahmad ya bari. Sannan na yanke hukuncin kai tsaye ne dan nasan itama ba zata ?i ba kuma duk cikin manemanta na yanzu babu wanda ya kaishi nagarta mun sanshi mun san asalinsa fatana hakan ya kasance alkhairi ga rayuwarsu baki Waya, duk wanu hasashen abu mara daWi da mukeyi Allah ya musanyashi da abinda yafi zamowa alkhairi.

Dan Allah ina ro?on ki karkice zaki tayar da fitina ko wani abu akan al'amarin nan Rukayyah, kiyi ha?uri da duk abinda ya faru Allah ne kaWai yasan dalilin faruwar komai ba kuma mu isa mu canza ?addara ba. Ki daure ki nuna mata alfanun dake tattare da haWin ba sharrin da yakw cikinsa ba ko badan komai ba ku dubi rayuwar waWannan marayun na sani kin sani duk waWannan zawarawan da suke zuwa suna nuna mata suna ?aunar yayanta ba har zuciyarsu bane, idan ma akwai wanda yakeyi tsakani da Allah to fa baze taSa sonsu tamkar Jafar ba uwarsa kuma taci gaba da addu'a babu abinda yafi ?arfin Allahu in sha Allah zata samu rinjaye akanta".

Kasa cewa komai Umma tayi, to me ma zata ce bayan aikin gama ya gama. Seda Baffan ya mi?e ze fita kafin ta iya ce masa
"To wata nawa aka tsayar da lokacin?" Ya juya ya kalleta da Wan murmushi yace
"Dafa wai wannan Juma'ar sukace, ashe shima Alhaji Audun aure ze ?ara, akwai matarsa uwar waWannan tagwayen zasu mayar da aure shine wai da a haWa to dai mace musu suyi ha?uri tana jarabawa yanzu a bari ta gama tukunna ko zuwa nan da sati huWu"

Umma tace "ikon Allah aure kuma? To Allah ya sanya alkhairi" ya amsa da
"Amin" ya fita. Ta ringa jimamin zancen auren Jafar da Afeeyah a ranta, ita dai abin ya gagara kwanta mata seta tashi ta goya Ahmad ta kulle gidan ta tafi gidan Umma FaWima yayar Baffa. Bata da wadda ta Wauka yar uwa kuma Aminiya kamarta. Yan uwanta sun mata nisa koda suna kusa ma tasan karshen abinda zasu mata shi Umma FaWima take mata. Ta Wauke ta tamkar ita ce ?anwarta na Baffan ba abinda kuma yake ?ara haWa su faWa da Umma Halima kenan tana ganin ta shanye mata yayye duk se yanda tayi dasu.

JAFAR
Tun da ya bar gurin Alhaji waccen ranar sallah ce kaWai take fitar dashi daga gida da yaje yayi kuma ze koma ya kwanta gaba Waya ya rasa me yake masa daWi a duniya. Besan me Alhaji zeyi ba, idan ya kafe akan seya auri Afeeyah yanzu yaya zaiyi? Wa zeyiwa biyayya a cikinsu wa ze bijirewa?

Idan maganar gaskiya akeyi Alhaji shine akan layi kwata kwata Hajiya tana kan layin son zuciya ne domin bai ga dalilin da ze saka ta hanashi kulawa da yayan Wan uwansa na jini ba ko ta hanashi auran wacce yake so amma kuma ita Win mahaifiya ce, bashi da hujjar bijire mata kai tsaye. Dole yana da bu?atar ya fahimtar da ita ta fuskanci gaskiya a yanda take sannan ya lallaSa ta harta sakko ta amince masa to amma a yanda Alhaji ya tunzura baya zaton ze bashi wannan damar idan kuma yace shima ze gwada masa ?arfin zasu sakashi a tsakiya ta ko ina ya rasa inda ze kama yaji sanyi kuma komai ze sake lalacewa ne maimakon ya samu mafitar da yake fata.

Kullum cikin tunanin da yake kenan, wayoyinsa ma kashe su yayi dan baya bu?atar kowa ya kirashi. Randa ya kwana uku be fita ba yana kwance a falo kan kujera Fatiyyah na dur?ushe gabansa tana haWa masa shayi tana masa hira. Ranta fes domin Momyn ta ta gaya mata malam ya bata tabbacin badai Jafar ya sake kallon wata ya mace ta burgeshi ba. Ita kaWai ze ringayiwa kallon mace, duk wadda ze gani ita da gardi basu da maraba a idonsa. Tun ranar da yaje gidan Alhajin ya dawo ya kwanta data gaya wa Maman tace mata aikin da akayi ne yake nu?ur?usarsa ze ware ita karta bari tayi nisa dashi ta sake shiga jikinsa sosai a lokacin daka kuma ta aiko mata da abubuwan da zatayi amfani dasu duk tayi tasan kuma indai zancen Afeeyah ko wata mace a rayuwar jay ta wuce gurin.

Ta mi?a masa tea Win ya karSa ya shiga sha a hankali ta zauna yace ta Wakko masa wayarsa a sama bayan ta kawo masa yace ta kunna. Wayar na kunnuwa kira ya shigo dan haka ta mi?a masa ganin Baba Al?ali ne ya ke kira ta kwashe kayan shayin ta wuce kitchen dasu. A speaker ya saka wayar dan bashida ?arfin ri?eta a kunnensa, suka gaisa Baba Al?ali yace
"Kai kuma shiru shiru baka kawo kuWin ba kodai kawai akaiwa Wan uwan naka ka bashi gari?".

Shiru yayi be ce komai ba, Baba Al?ali yayi murmushi me sauti yace
"Wato baka da lokaci na balle ka bani amsa ko? Ai shikenan. Babanka ya matsa, dan haka nidai na ranta maka dubu Wari uku munje mun kai, Wari biyu kuWin aure Wari kuma sadaki kuma an tsayar da rana sati huWu dan haka..." Kafin Al?alin ya gama bayani ya katse wayar a garajen hakan ruwan shayin ya kelaye masa a jiki gashi da zafi sosai dan bata surka ba, a tafashen sa haka ta haWa masa amma duk beji zafin ba saboda yanda maganar Baba Al?alin ta rikitashi numfashinsa har wani Wumi yayi kansa yayi dummm ya shiga zare idanu yana duba ta inda ze hango Fatiyyah daidai nan ta fito daga kitchen ta kalli rigarsa data ji?e ga kofin shayi da sauran sun zube akan carpet tace

"Babe zubewa shayin yayi?" Kamar ta tunawa fatarsa nan da nan ta aika sa?on zafin daya ziyarceta zuwa ?wa?walwar sa, jikinsa ya dauki raWaWi, ya dafe inda ruwan ya zube yana cije baki yace
"Ban san baki surka ba nasha shine ya zube".

"Wayyo Allah, bari na kawo maka ruwan ?an?ara sannu" ta faWa da sauri tana komawa kitchen kafin ta dawo harya haye sama yana cije baki dan da gaske yake jin zafi yanzun, ta bishi da ruwan ya cire rigarsa fatar cikin har tayi ja ta shiga shafaasa ruwa me sanyi a gurin tana masa sannu, wayarsa daya ajiye kan gado ta sake yin ?ara. Kusan kamar a tsorace ya tureta ya Wauki wayar har seda ruwan hannunta suka zube be ko bi takanta ba ya shige banWaki da sauri.
Da mamaki Fatiyyah ta bishi da kallo cikin ranta kuma ta tabbatar akwai abinda yake Soyewa, tayi ?wafa ta fice daga Wakin ba taredata gyara inda ruwan ya zube ba.

Jafar kuwa wanka yayi bayan ya sake kashe wayarsa, gaba Waya ji yake kamar komai na juya masa takamaimai ma be san me ya kamata yaji ba, daWi ko akasin haka?
A ta?aice yayi wanka ya shirya a gurguje be ko nemi Fatiyyah ba ya fita. Seda yayi nisa da gidan ya samu guri ya tsaya sannan ya sake kunna wayar ya kira Baba Al?ali.
"Ina magana ai naji ka kashe" Al?alin ya faWa. Ya shafa kansa dake sara masa yace
"Chaji ne ya ?are ban ma ji abinda kake cewa Wazun ba".

"Allah sarki, cewa nayi mun kai maka kuWin aure Wazu kuma an tsayar da rana nan da sati huWu masu zuwa idan muna raye" Baba Al?ali ya maimaita masa, yayi shiru kafin ya sauke ajiyar zuciya a hankali yace
"Amma Baba Hajiya ta sani?"
"To gaskiya bani da masaniya akai dan nima shekaran jiya Audun ya ce mun na kira Malam Hafizun na gaya masa zamuje, ban sani ba ko ya sanar mata ko yaya sukayi oho. Kai baka shiga gidan bane ba?" Al?ali ya bashi amsa.

"Toh amma Baba ita Afeeyar ta amince ne?" Ya sake tambayar sa se Al?alin yace
"Baka da lambar wayar tane Jafar? Ka kirata mana kaji, mudai mahaifinta ya karSi magana ya bamu lokaci wannan kuma tsakaninka da ita ai ku ta shafa ko? Kaga se anjima ana kirana

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login