Showing 39001 words to 42000 words out of 467220 words

Chapter 14 - MATAR MUTUM COMPLETED 1-3 BY MARYAM FARUK.doc

23 Sep 2025

12248

namu nawa suke? A bariki fa sa'anninsu har yanzu suna gaban iyayensu ana musu kallon qananan yara kai ko me yasa ba zaka barta taci arziqin da kuka tara tare cikin kwanciyar hankali ba?" Yakubu ya fada.

Audu ya karkace, shi fa a yanzu Jin Binta yake kamar daga sama aka yo masa wahayinta tsabar so. Ba wai ya dena son Bara'atu bane Aa, yanda Bintan ta iya magana da tattala Namiji idan yaje Kaduna har ya dawo Kano yayi satittika kafin ya sake komawa cike yake da bege da shauqin kalaman data ciko shi dasu. Ga tarin wasiqu datake rubuta masa masu dauke da kalamai masu gigita tunani, haka ze ringa dauka kullum yana karantawa idan sun qara ya ringa maimaitawa har se yaje ta sake hadoshi da wasu ya dawo yaci gaba da tisa karatun kalaman soyayya. Irin wadannan abubuwan yasa ya fara ganin baiken Bara'atu wadda bata san komai ba bata kuma iya komai ba se abinda ya koya mata ko ya nuna mata.

Ya kasa gane banbancinta da Binta wadda ta kereta a shekaru, sannan ta bangaren wayewarsu babu hadi Binta haihuwar cikin Turawa girman Kaduna zagaye take da gogaggun yan Boko yan uwa da qawaye baya ga haka ita din tana cikin mutane da Allah yayi masu dan banzan wayo da iya magana. Duk dakiyar mutum tana iya canza masa akala a cikin ruwan sanyi yayi abinda take so ba tareda ya ankare ba. Tana da wayo kamar me, ga kissa kamar rainon Tsofaffi da wadannan halayen ta sake kanainaye shi yanda take nuna masa yafi kowa a duniya ya kai matsayin da shi da kansa yasan qaryane be kai dinba kambama shi kawai take amma da yake shi mutum nr me Izza da kuma son a girmamashi a yabe shi hawa yake ya zauna kan duk abinda ta fada baya ko tunanin Izgilanci take masa domin ta fishi ta kowacce fuska amma take nuna masa ita din banza ce akan sa.

Gyara zama yayi ya kalli Yakubu da yayi shiru cikin mamakin abinda Audun yazo dashi yace
"To amma da farko akwai haramci a cikin abinda nazo dashine? Naga qarin auran nan halal ne. Dafa ba'a qara aure da ba'a haife mu ba domin mahaifiyarmu a ta biyu taje gidan Baban mu sannan ita Bintar nan ka san komai game da Alkhairin da mahaifinta yayi mun. Kana kallon laimar Arziqin daya lulluba mun a cikin watanni kadan na damu abinda na shekara goma ina fafutuka ban samu ba meye aibu idan na karbi tukuicin auran yarsa wanda ita tayi mun tayin haka da kanta baka tunin zan zama butulu mara godiyar Allah idan nace zan qita?

Tunda har su basu dubi matsayinsu da nawa ba suka amince zasu bani auran yarsu aikuwa ni bai kamata nace Aa ba kaima kuma be kamata kaqi abin ba domin Alkhairin da yake tattare dashi ba iyakar kaina ze tsaya ba gaba daya ya shafe mu. Kuma ni Bara'atu bani da matsala da ita, mun samu fahintar juna domin ban boye mata komai ba tun farkon maganar kuma ta amince dan haka yanzu abinda ya rage kawai zamuje can Bechi mu sanar dasu Yaya Baba idan yaso se a saka rana da zakuje ku nema mun auran. Ni yanzun duk bama wannan ya dameni ba, tunanin gurin da zan ajiyeta nakeyi".

Duk yanda Yakubu yaso fahimtar da Audu abu yaci tura dole ya haqura tunda dai kamar yanda Audun ya fada abinda yake shirin yi ba haramun bane sedai shima ba qarin auransa ne baya so ba, Audu qaninsa ne kuma Aboki koma yace Amini, duk wani sirrin junansu sun sani yasan da cewar Audu baze iya zama da mace daya ba kuma irin Bara'atu saboda tayi masa kadan sannan a tsari na halitta har yanzu bata kai cikar da yake fata ba amma yaso ace idan ma auran zeyi ya nemo daidai dashi ko a can gida ko a nan cikin Kanon amma dai ya samu yarinya yar Talakawa irinsa da zasu yi zaman lafiya ba irin wannan aure daya gingimo ba. Shi gaba daya ma gani yake abin kamar da wani qulli ciki, tayaya mutum daga haduwar hanya ze ringa masa irin wannan hidima haka sannan har ya dauki ya ya bashi Aure bayan matsayinsa be wuci na me gadi ko share sharen gidansa ba.

Sanda yayiwa Balaraba zancen yanda ta firgice seka rantse ita aka ce za'a wa kishiyar, ta ringa masifa tana Bala'i wa Bara'atu daga qarshe dai dole ta barta tunda ita da za'ayiwa kishiyar ko a jikinta ina dalilintana daukar dumi?
A can Bechi ma haka Bilki ta ringa fada akan me Audu ze qara aure me Bara'atu tayi masa, amma tunda dai duk basu za'ayiwa kishiyar ba kuma me zama da ita tace taji ta gani dole suka haqura suka zubawa sarautar Allah ido.

Anje an tambayowa Audu Aure, Yaya Baba, Hashimu da Aminu se Yakubu sukaje Kaduna bisa jagorancin Audu. Tarba ta mutunchi akayi musu, basu taso ba seda aka tsaida ranar Aure watanni uku masu zuwa suka dawo kowa na jinjina gidan da Audu yaje neman auran. Hashimu ya ringa yawo a gari yana cewa Auran kwadayi zeyi tunda gashi tun be aureta ba ubanta ya gina gidan mai ya bashi gaba kuma ba'asan me zeyi masa ba. Takanas ya samu Baban Bara'atu akan seya tursasawa Audu ya sakar masa yarsa domin qarshe boyi boyi zata zama a gidan daya auro wannan yar Attajiran Azabatar masa da Ya kawai zasuyi hankalin Inna Hajara ya tashi sanda ta samu labarin irin Amaryar da ake shirin yiwo wa yarta, takanas ta tashi qanwar Bara'atun ta turata tace idan ta samu sarari tazo Bechi tana son magana da ita.

Haka kuwa akayi ta gayawa Audu yayi mata shiri kamar yanda ya saba duk sanda zataje gida ta tafi, Innarta ta ringa nuna mata qalubalen dake cikin auran da yake shirin yi amma se tayi murmushi tace
"Duk hasashe kukeyi Inna kuma Audu yana qaunata na tabbata babu wata mace da ze aura da zata zarceni a zuciyarsa sannan ita kanta da kuke magana tana da kirki. Tun yanzu bakiga yanda duk sanda yaje seta hadoshi da abin Arziqi ya kawowa yara ba dani kaina kuma ya fada mun sam bata da matsala dan haka kuyi mana Addu'a kawai Allah ya bamu zama lafiya" da haka ta kashe bakin Innarta da duk wani dake shirin saka mata rudu a zuciya.

Ba kuma wai bata damu ko kuma bata kishin Auran da Audun yake shirin yi ba, ta damu kwarai dan tana son mijinta, irin rawar qafar da yakeyi akan Amaryar tasa na daga mata hankali amma ta yarda da cewar Damuwarta ba zata saka a fasa abinda Allah ya hukunta ba sannan meye ribar ta tayar da hankali ta rasa mutunchinta da qimarta a gurinsa kuma daga qarshe yayi auran su zauna? Shiyasa ta maida komai ga Allah shi take roqo kullum dare da rana akan duk fitinar dake cikin aura Allah ya kade musu ita ya sanya zaman lafiya da fahimta a tsakaninsu kuma wannan haqurin da tayi da ake mata kallon wawiya ko yarinta ce take damunta ya saka Audun ya mayar da ita Abokiyar shawara akan duk wani abu da zeyi ko yake shirin yi. Daidai da zancen muhalli ita ya tuntuba akan yanda take ganin za'ayi.

"Gurin saukar baqin gidansu kadai duk unguwar nan babu gida me kyau da tsaruwarsa, gaba daya abinda ya dameni kenan yanzu inda zan ajiyeta saboda kinga ko a shari'ance be kamata ace ka dauko Mace daga cikin daula ka muzguna mata a bangaren muhalli ku sauran buqatu ba" Audu dake faman lissafin kayan lefe ya fada, Bara'atu ta hadiye yawu tace
"Gaskiya idan hakane kuwa ya kamata ace kayi mata tanadi na musamman domin nasan ba zata iya zama a cikin gidan nan ba"

"A ina ma zan ajiyeta toh?" Ya fada yana kallonta, cikin iyakar gaskiyarta tace
"Na dauka zaka toshe qofar tsakiyar dakin nan seka huda mata qofa ta wajene mu tashi da falle daya"
Daya rasa abin ce mata kawai ya fashe da dariya, ya gama rubutunsa ya tattare takaddun ya fita.

Daya tuntubi Yakubu zancen gida ce masa yayi
"Ka sakata a bangarenmu kawai"
"To ku kuma fa?" Audu ya tambayeshi,
"Wannan ba matsala bane tunda kaga idan muka tafi yanzu se mun shekara ko fi kafin muzo, zuwa sannan se musan abinyi" Yakubun ya bashi amsa. Cike da rashin jin dadi Audu yace
"Wai dagaske kake ba zaka zauna ayi Bikinnan kuna nan ba? Wai me nayi da yayi maka zafi har haka ka qullaceni?"

"Bakayi mun komai ba Audu tafiya kuma ka sani ina shekarar qarshe ya kamata ace na ninka mayar da hankali akan Karatuna sannan itama Balaraba na gaya masa tana zuwa makaranta acan to sun koma kaga be kamatu daga farawarta kuma ta ringa wasa ba. Nidai abu dayane da yake damuna na rasa dalilin da sam auran nan be kwanta mun a zuciya ba, ina tsoron ka auro matar da zata wargaza maka zaman lafiya, ta gurgubtar da kyakykyawan tushen daka soma ginawa. Haka kawai nake jin baka dace da matar Aure ba Audu amma Allah shine masanin gaibu ina kuma yi maka addu'ar Allah ya kawai da duk wani abun qi daga hadinku".


*MAMAN MARYAM ONLINE BUSSINESS*

*Ina kuke Mata Yan kwalisa , Ina nufin isassun Mata ,Wai shin Kuna da labarin shahararren company nan namu na GHT wato good healthtreatments*
*Wanda yazo muku da fitattu Kuma* *ingantatattun suppliment ,na dukkan matsalolin ku*S'

*Ina maisan tayi kyau,irin na isassun Mata ya fitar Miki da shef dinki tayi Miki gyara in and out ,nemi royal jelly dinmu na company GHT*
*Wanda aka yishi da xuma ,kundai San amfanin Zuma basai na fada miku ba , hajiya ta kixo ki Yi gyara domin ki kerewa sa,a kije taro ko baki da ko sisi kiji Ana rangada Miki hajiya , saboda yanda Zaki Kara kwarjini ,kina walwali acikin mutane , magungunan ght anti agen ne suna maida tsohuwa* *yarinya ,yarinya Kuma ta koma jaririya*


*Muna da magunguna iri iri*

*NA GYARAN JIKI*
*NA GOGE NANKARWA*
*NA RAGE QIBA*
*NA CIRE TUMBI*
*NA QARIN HIPS*
*NA GIRMAN BREAST*
*NA QARA TSAHON GASHI*

*NA QARIN NI'IMA WANDA ZAI SAUKAR MIKI DA NI'IMA YA QARA MIKI DADI DA ZAQI A GURIN OGA*

*Muna da hadin bita zai zai ,indai kishiyar ki tana Shan magungunan GHT, tohh lallai sunan ki sorry domin kuwa tazarar dake tsakanin ku kamar tazarar sama ne da kasa*

*Muna da Wanda zai matseki ciki da waje Andai na yayin dinki uwargida*,

*Sannan company mu na GHTBai tsaya anan ba*
*Ya kawo muku maganin dukkan matsalolin ku*

*INA MASU HAWAN JINI?*
*INA MASU CIWON ZUCIYA?*
*INA MASU CIWON QODA?*
*INA MASU CIWON HANTA?*
*INA MASU SICKLER?*
*INA MASU HIV?*
*INA MASU CANCER?*
*INA MASU NEMAN HAIHUWA?*

*Tohh Ku matso GHT taxo muku da magungunan matsalolin ku*
*Kuma muna da testimonys da yawa ,na wadanda suka gwada suka da ce*

*Munanan a KANO KUNTAU*
*Kuma muna tura Kaya ko wanne gari cikin aminci da gaskiya , kuma kayan mu muna badashi ne cikin price Mai rahusa ga kyau ga inganci sannan ga Rahusa*

*Kutuntube mu ta wannan number =???08129249549*
*=???07011401314*


Biki ya rage saura wata daya, ba qaramin raraka Audu yayiwa jarinsa ba ya hadawa Binta lefe na yar gata aka kai, be bar Bara'atu a baya ba dan itama seda yayi mata lefen dukda be kai na Bintan ba, ya kuma bada aikin sababbin Gado da kujeru daze chanza mata. Yakubu sun kwashe kayansu wanda Bechi ya aika dasu Bilki ta dauki Gado Aisha Kujera ragowar tarkacen yan uwa suka raba sun rabu da Audu akan ze nemi fili nan kusa a tayar masa da wani gini domin siyan bangaren Yakubun yayi dukda Yakubu yace Aa ai gida gaba daya na Audu ne dan da kudinsa ya siyi fili ya gina amma shi yace ba haka ba koda shi ya gina kyauta ce yayiwa Yakubun dan haka yanzun siya yayi kuma in Allah ya yarda kafin su zo Kano ze maida masa da wani.

Ya tada gyaran gurin, anyi toshe toshe da liqe liqe, maginin gaske ya dakko Injiniya akayi masa aikin se ga guri ya fito fes an fitar da Sef cinten daki biyu da falo a tsakiya harda bandakin tsakar gidan aka shigar mata a daki se kitchen aka lailaye ko ina da Torazo gida dai ya fito na zamani a ganin ba za'a kushe ba dukda yasan dai a matsayin Bintan tafi haka amma ai ita tace taji ta gani ko a bukka ze ajiyeta zata zauna. Bara'atu ma ta samu arziqi an saka mata torazo a dakunanta dana su Abdullahi da tsakar gidan, Gadonta ta maida musu can aka saka mata sabon da Audu ya mata ga kujeru da kafet harda kayan Kallo se danqareriyar firiza duk a kayan fadar kishiya ita kuwa me ta manta?

Audu nata doki da murna sanda yan uwan Binta sukazo ganin guri se kuma murna ta koma ciki. Babu kara suka ringa kushe gurin da yada maganganu akan an asirce musu yar uwa banda haka me Binta zatayi dashi balle har ta yarda ta zauna a gurin da ko Boyis kwatan su Albarka. Basu kwana a gidan ba kamar yanda ya shirya musu otal suka kama washe gari suka juya sukaje can sukayi ta cece kuce da fadar maganganu abinda ya saka Mamansu magantuwa kenan saboda yanda suka fasakta muhallin Bintan abin yayi muni.?????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????? Tayi tsammanin yanda ya zage yayi lefe haka ze qerawa yarta gida kodan ya rage mata radadin auransa da bata so yar tayi, meye amfanin Kudin da Ubanta ya sakar masa domin tana da labarin qanin Kyauta yake bashi mai, idan an kai masa tanka goma kudin Biyar Alhajin yake karba haka tsayin shekara daya bata taba jin yace ga kudi Kaza na Ribar Mai da Audu ya kawo ba amma shine zeyiwa yarta wani Akurkin kaji a sakata a ciki.

Cikin fushi da tari Alhaji da maganar, takanas ya tashi Tunde suka tafi Kano kwanaki biyu bayan komawarsu su Salima a sannan Biki ya rage saura kwanaki goma se ganinsa kawai Audu yayi ba zata. Shidai Alhajin bega aibun gurin da suka ringa fada ba domin a abinda ta rasa a gidansu baze wuce girma da kuma taswirar gini ba dukda haka domin gujewa duk wasu surutai na matar tasa da bata taba qalubalantar wani hukuncinsa ba yasan tayi kawaici matuqa akan lamarin auran tunda har ta magantu yanzu tabbas abin ya kaita maqura dan haka yacewa Audu

"Me yasa baka sanar dani baka da gurin da zaka ajiye Mamana ba?"
Audu yaji wani iri, wato shima ya raina gidan kenan? Amma dai a qarfinsa sunsan yayi abinda ze iya harma ya zarta. Shiru yayi bece komai ba gudun kar zuciya ta kwashe shi ya gayawa Alhajin mara dadi dan be gama hucewa daga fushin cin zarafin da Yayansa suka masa ba daman.

"Ina ganin zan saka a duba gida ginanne idan yaso se a siya a sakata ciki ko ya ka gani?" Alhajin ya sake fada se sannan Audu ya daga kai ya kalleshi. Wato zancen Labahani gaskiya ne da yake cewa idan ka auri yar masu kudi rainin arziqi se abinda ka gani sannan su zasu ringa yi maka iko da gida to idan kuwa haka ne shi ba za'ayi akansa ba, baze bada qofa ba balle daga baya idan ya hana ace yayi Butulci.

"Kayi haquri Alhaji ba ina nufin raini a gareka ba amma maganar gaskiya wannan ne muhallin da nake dashi da zan saka Binta a ciki. Ka sanni ka san Asalina haka itama tun gabanin tafiya tayi nisa a tsakaninmu tasan komai a kaina kuma ta yarda da hakan zata zauna dani a kowanne. Kayi haquri ka barni na ajiyeta a inda Allah ya horemun a yanzu, ina fatan zuwa gaba na gina mata daidai da tsarinta amma a yanzu abinda ya sawwaqa kenan".

Badan Alhaji yaso ba gudun kuma karya takurashi yaga kamar ya masa kutse a cikin lamarin gidansa yasa ya haqura ya tafi kuma kamar yanda Audun ya fada ita Bintan taji ta gani dan ya zaunar da ita kafin a kawo kudin Aure ya tambayeta ta amice tace koda can Qauyensu ze kaita tana sonsa a haka zata aureshi.

Haka akayi Biki Amarya ta tare, iyayenta sun zuba mata abinda dakin ze iya dauka. Danma kuma babu laifi ginin an fitar da dakunan da baga dan haka sun dauke gadajenta Biyu kantama kantama yan Dubai. Kujerune dai seda aka canzo ainin wanda aka siya mata saboda falon ya matse ga Divida bango guda yar waje kujerun ma irin bajaj din nan ne 1 sitter su takai girman two sitter matsakaitan kujeru dan haka suka matse matuqa dole aka mayar aka canzo mata wanda gurin ze dauka. Kwana biyu yan uwanta sukayi suka juya dalilin seda suka kaita Bechi wanda basu kwana ba ko banda ruwan gora da aka basu babu abinda suka iyaci na daga abincin tarbar Amarya yamma lis suka tada jaraba seda aka kaisu Kano gidan Amarya dan sunce ba zasu iya bacci a garin ba wannan Abu ya qona ran Yan uwan Audu ya ku.a darsa tsanar Binta a ransu duk da ba ita ta musu ba amma sun ce itama haka halinta yake kenan tunda bata hana yan uwan nata yar musu da magana da izgilanci ba

Audu kansa ya qara hasala wannan karon dan haka babu wata sallamar Arziqi suka koma Kaduna suka yita fadar qarya da gaskiyar abinda ya faru na wai an aura masa ita buqata ta niya ya fara musu rashin mutunchi. Todai babu yanda suka iya aure ya qullu Amarya da Ango na son junansu sedai fatan a zauna lafiya.

Sati gudan da Audu yawa Amarya Binta an barji soyayya irin wadda ya dauka a fina finan turawa kadai ake irinta. Baiwar Allah Bara'atu aikinta ta dafa abinci wanda take qure duk basirarta da abubuwan da Balaraba take koya mata idan sunzo tayi musu takai musu idan sunci ta debo kwanuka safe rana dare haka take wannan Bauta tsakaninta da Audu kuwa da safe idan ya dawo sallar Asuba ze shiga ya duba su shikenan se wata safiyar ko idan taje kai musu abinci baya fita ko ina yana daki suna barzar Amarci a haka ya kwashe sati dayansa gurin Amarya wadda zuwa sannan ba zatace ta mata wani

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login