Showing 411001 words to 414000 words out of 467220 words

Chapter 138 - MATAR MUTUM COMPLETED 1-3 BY MARYAM FARUK.doc

23 Sep 2025

12154

su na fi ?arfinsu dasu da duk masu tayasu".

Fatiyyah ta saka kuka, muryar hajiyar har tsakar gida tana zazzaga shi dai ya tsaya Sacin rai ya hanashi ya zauna kuma ya kasa tafiya. Fatiyyah ta figi jakarta tana kuka ta fita suka kusa cin karo da Naziru daya faWo falon tamkar an jefo shi kana ganinsa kasan hankalinsa a matu?ar tashe, ta matsa masa ya shiga a maimakon ta fita kamar yanda tayi niyya seta coge a bakin ?ofa tana so taji dame yazo shi kuma tsawar da Jay ya fafara mata tasa ta fita babu shiri tana haWa hanya. Tamkar zararre Nazirun ya cewa Hajiya
"Tashi mu tafi?"
"Mu tafi ina?" Ta tambaye shi itama tana zare ido dan tsorata tayi da yanda ya faWo falon. Ya mi?e tsaye ya nufi Wakin ajiyarsa yana cewa
"Sun san kuWin nan suna nan gidan kowanne lokaci kuma zasu iya biyo sahu kuma kamani zasuyi shiyasa zan bar ?asar, kizo mu tafi kawai".

Tsaki hajiyar taja tabi bayansa da?yar take tafiya tana cewa
"Ji wani zancen banza sun daWe basu biyo sawun su ba da gumin ubansu aka nemi kuWin ko yaya da zasu soka idonsu akai? Babu inda zakan je sata nayi ko fashi da makami? Kaima ba inda zakaje se kace abin rashin gaskiya su idan basu da kunya su shigo gidan nan suce zasu Wauki wani abu mana ba EFCC ba ko Shugaban ?asan ne da kansa yazo ze gane na fishi ta'addanci" ta shiga Wakin ta tsaya kan Naziru dake Wiban bandir na daloli yana sokewa a aljihunan jikinsa ya gama ya raSe ta gefenta ya fito ta biyoshi bayan ta kullo Wakin ganin jikinsa har rawa yakeyi tace

"Kai wai dan ubanka EFCC kake tsoro ji yanda kake tsuma se kace wanda aka kama da kan mutane. Idan ba zaka iya zama a gidanka ba kazo nan ni zan tare maka duk tsiyarsu daidai nake da su" be kulata ba seda yaje kusada Jafar yace
"Bani key Win motar ka"
"Ina zakaje?" Jafar ya tambayeshi a maimakon ya bashi abinda ya bu?ata. Yaja tsaki ya wuce Wakin hajiya ya fito da mu?ullin mota tana ganinsa tace
"Mayar, Faisal ne ya fito da ita jiyan nan aka dawo da ita daga savice da ita ze ci angwanci" be tsaya ba ya nufi ?ofa yana cewa
"Kiyi mun addu'a, na tafi Libia".
"Niger?" Ta faWa da ?arfi tana dage ?irji, Jafar da hankalinsa ya gagara kwanciya da irin gaggawar da Nazirun yakeyi ya bi bayansa yana tambayar sa wai lafiya amma ya?i tanka masa. Seda ya bar gidan a motar daya Wauka Jafar ya karSi mu?ullin tasa da yazo a ciki wadda ya bari a kunne a compound Win security ne ya kasheta ya bawa Jay key Win ya koma gurin hajiya yana tambayar ta kuWin menene ya ajiye a Wakin?

Mantaqa tayi da masifar da takeyi kafin Naziru ya shigo tace masa "Kasan ai yana ha?an zinare, shine fa magauta suka tasashi a gaba akayi masa shunen EFCC suna ta bibiyar account Win sa daga ?arshe ya kwashe komai ya kawo su nan ya ajiye ashe basu ha?ura ba, ni ko naga Wan shegiyar da ze zo gidan nan yace ya biyo kuWi. Dama rabi dukiyata ce shima macuci ya handame ai shigo shigo na masa nace ya kawo su nan ya ajiye ba inda za'a sake fita dasu". Jay ya mi?e ya nufi Wakin yana cewa

"Wane irin kuWi hajiya? Ke kin buWe kinga kuWaWe ne da har kika yarda aka ajiye su a gidan nan kuma Alhaji ya sani?"
"Ai fa na manta kaima Wan uba ne na buWe maka cikina, to be sani ba kuma billahillazi naji maganar a wajen Wakin nan tsakanina dai se na mugun saSa maka Jafar. Karka zata na bar waccen maganar da muka fara ne, dama kasan abinyi ko ni ko ita domin ba ha?ura nayi ba idan kaga dama kaje ka sake yin sanadin da aure na ze ?arasa mutuwa" ta faWa cikin tsananin fushi. Ya dakata a ?ofar Wakin yama rasa me ya kamata yayi. Kwata kwata hankalinsa be kwanta da zancen kuWin da aka ajiye a Wakin ba, idan har da gaske kuWin ne kuma silar su Naziru ze bar ?asa ai kuwa akwai gagarumar matsala. Be damu da zancenta na ?arshe ba ya juya yana kallonta yace
"Hajiya ki buWe naga kuWin nan da kika ce sam hankali na be kama zancen nan ba"
"To dama ya shafeka ne balle ka nutsu dasu? Zo ka fitar mun daga Waki ma ka kuma ji abinda na faWa" ta bashi amsa tana hararsa. Duk yanda yaso data buWe masa Wakin ta?i daga ?arshe ta fitittike ta shiga zaginsa dole ya tafi amma har ransa be aminta da kuWin ba, zuciyarsa ta ringa raya masa ya sanarwa Alhaji sedai tsoron tijarar hajiyar da dama akan tsini take yasa ya gagara yin hakan. Ya kira Faisal ya tambayeshi ko ya san kuWin meye yace masa

Irin kuWaWen da suka sata ma kamfani ne fa shine suka ajiye su a Wakin daga ita se shi suke shiga suk naci na haka na ha?ura gara kaima ka barsu yanda ka gansu dan kuWin cizo ne" amsar da Faisal ya bashi kenan hakan seya samar masa da yar nutsuwa jin ba wasu kuWaWe bane na daban amma duk da haka ze bincika dalilin daya saka Naziru ze tsallake ya tafi wani guri.
Har ya shiga mota sannan ya tuna da Ahmad yazo ya sauka ya koma cikin gidan a falon Momy ya Wauke shi ya bata uzurin yana so ya mayar dashi da wuri akwai in da zeje. Momy dai murmushi kawai tayi tana tambayarsa mamansa fa? Idan ya koma yace ta kirata ta nemi wayarta bata samu ba. Ya ringa sunkuyar da kai yace mata toh.

A hanya ya shiga sake gwada wayar Afeeyah da tun daren jiya bayan ya koma gida yake kira amma a kashe, yanzun ma a kashen take. A maimakon ya mayar dashi gida ya zarce ya tarar da Fatiyyah da ?awarta Adasiyyah a waje da alama rakota tayi zata tafi idanunt sunyi luhu luhu fuskarta duk tayi ja alamaun tasha kuka ta gode Allah ya wuce su ya shiga ciki a ransa yana mamakin damuwar data sakawa ranta dalilin Afeeyah. A farkon auransu har cewa takeyi ita da zata ga Afeeyar seta tayashi ro?on data amince ta aureshi ashe duk ?arya takeyi saboda ba zata gantan bane take faWar haka banda dai sakawa kai damuwa tasan dai ba zasu samu matsala da Fatima ba lafiya lau zasu zauna idan ta kwantar da hankalinta amma ta gagara yin hakan.

Yana tareda Ahmad har magriba sannan yayi wanka shima yayi masa bema san ya iya yiwa yara wanka ba se lokacin ya shirya shi tsaf ya saka masa Waya daga cikin shaddojin da aka masa Winki suka yi saura, kayan sun masa kyau kuwa kamar an gwada shi se shima ya fito da irin kayan ya saka yayi musu hoto sannan ya Wauke shi suka fita jin an fara kiran sallah. A falo ya tarar da Fatiyyah a zaune da alama waya ta gamayi yanda ta gansu sun sha anko da Wan bazawarar tasa ya sake harzu?ata. Da mamanta ta gama waya wadda kullum ciki tisa mata tayi ha?uri ta Wauke kai malam yace yana nan yana aiki komai zai daidaita amma ta kasa bin maganar maman domin bata ga alamar wannan karon aikin malamin zeci ba.
Ya aje Ahmad bayan ya canza tasha zuwa cartoon network yana kallonta yace
"Gashi nan zanje nayi sallah"
"Se ka nemi me jire maka shi badai ni ba" ta bashi amsa a hasale kamar tana jiran ya kulata, seya wuce abinsa ba tareda ya tanka ba be kuma Wauke yaron ba yana jinta tana maganganu ya fita. Sanda ya dawo Ahmad kaWai ya samu yana lage cikin kujera harya fara bacci abinsa ya Wauke shi ya fice ba tareda yabi ta kanta ba. Shi da kansa baya jin daWin irin zaman da sukeyi amma ita taja, duk kuma yanda zeyi ya fahimtar da ita su zauna lafiya ta?i ta bashi haWin kai.

Yana hanya kiran hajiya ya ringa shiga wayarsa, baya raba Waya biyu Fatiyyah ce ta kirata ta gaya mata yaje da Ahmad gidan kuma sun fita dan haka ya?i Wagawa domin sabon Sacin rai ya sani ze fuskanta muddin ya amsa wayar. Bayan yayi sallar isha'i a masallacin unguwarsu y zauna a waje yana jiran Baffa da ya baro suna magana da dattijan unguwar da alama meeting suke dan sun taru da yawansu. Yana zaune cikin mota yana ta tsara abinda ze gayawa Baffa har be san ya iso inda yake ba seda ya ?wan?wasa masa glass ya fito daga motar Baffa yace su shiga ciki yana sosa kai yace
"Aa Baffa nan ma yayi, dama ha?uri nazo na bayar akan abinda ya ta gaya maka na faWa. Wlh Baffa na rasa yanda zanyi ne kawai shiyasa".

Baffa yayi murmushi yace
"Abu Waya nake so ka sani shine Jafar Allah shine shaida babu son zuciya ko kuma wani al'amari makamancin haka cikin raina kamar yanda da yawa suke tunani a kan al'amarinka kaida Afeeyah. Abu biyu ne har yasa ban zafafa ba, kai jinin Ahmad ne sannan al'amarin aure wani abu ne me wuyar sha'ani wanda ba'a zafafawa a cikinsa domin Ubangiji yana iya yin komai. Imma kaso Allah ya hana faruwarsa ko kuma ka ?i kuma ya afku dan haka tsayuwa tsaka tsaki shiyafi a komai na rayuwa kuma mutum ya ringa mi?a zaSi gurin Allah duk abinda kaga ya tabbata se ka karSa domin shine alkhairinka"

Kansa na ?asa yace
"Haka ne Baffa, wlh na sani duk wani abu da zakumin a gidan nan alfarmar Yah Ahmad ce yanzun ma kar a gaji, kaga Baffa a rayuwata tunda nayi wayo ban taSa aiwatar da wani abu ba tareda shawararsa ba shi yake sakani a hanya yanzun kuma babu shiz ban saba da rayuwar kaWaici ba shiyasa al'amura sukeyi mun wahala tunda bakiyda me saitamun hanya idan na kuskure. Shi Baba Al?ali ya sani amma ya gagara yi mun uzuri akan kuskure na nasan ai kai zaka fahimceni Baffa kuma har yanzu shi Alhaji ba wai ya sauka bane idan wani abu ya sake faruwa kowa ni zega laifi ni kuma ban san ya suke so nayi ba" ya ?arasa maganar muryarsa tana karyewa. Baffa dake kallonsa yace

"Allah ze yi maganin koma menene Jafar aci gaba da addu'a babu abinda yafi ?arfin Ubangiji"
"Ina yi zan kuma ?ara" ya faWa a hankali. Baffa yace
"Daga Sangare na babu matsala in dai har ta amince nima na amince, kuje ku sasanta, Allah ya tabbatar da alkhari ya kaWe duk wata fitina da sharri da suke zagaye da al'amarin"
"Amma Baffa kasan halinta bata jin magana, kawai ?ara mun ciwon kai zatayi nidai Baffa in dai an ha?ura da gaske to kawai a bata umarni nasan ba zatace Aa ba" Jafar ya faWa cike da shagwaSa kamar wani yaro. Baffa yayi dariya yace
"Ai kuma idan akayi haka ba'a kyauta ba gaskiya. Ka dai je ku sasabt tsakaninku ai babu me shiga se yaji kunya". Ya shafa kansa yana tsugunnen, so yake ya sake ro?on Baffan amma kuma baya so ya si?e shi sedai yasan in har aka ce a barshi da Aafeeyah to fa kafin ta sakko daga hasalar da tayi Alhaji ze iya sake fusata ya Wauka ma shiri ne kawai sukayi. Yana shirin sake magana Baffa ya wuce yana ce masa se da safe tunda baze shiga ba. Guiwa a sanyaye ya mi?e yayi saurin ce masa

"To zan iya zuwa na Wakko ta goben?"
"Allah ya kaimu, kamar bayan azahar haka se kaje" Baffa ya bashi amsa daga nan ya shige gida shi kuma ya shiga mota ya shiga gari. Gurin da yake zuwa aski yaje akayi masa tareda wankin ?afa da gyaran ?umba, ya sakeyin fes dan damuwar da yake ciki kwana biyun tasa duk ya hargitse gashin kansa ya taru ga ?asumba da akayi masa askin aka gyara fuskar se yayi kyau sosai ya dawo Jay na gaske ba ragabzar da yake nema ya mayar da kansa ba. Seda ya sake wanka ya shirya tsaf kafin ya tafi part Win Fatiyyah, baze so ace yayi aure suna wannan yanayin ba. Yana so ta nutsu ta kwantar da hankalinta, yasan tana son sa shima kuma yana mata so daidai wanda zuciyarsa ta bata ya tabbatar da ta san kanta tana bashi irin kulawar da yake fatan samu ko be manta da Aafeeyah gaba Waya ba tunda ?addararsa ce kaso me tsoka ze ragu na sonta da kewarta da yakeyi amma sam Fatiyyah tayi wasa da damarta. A zamantakewarsu muddin ze bata kuWi ya kuma saketa tayi yawo yanda ranta yake so babu ruwanta da sabgarsa ko wata damuwarsa. Harkar waya da ?awaye kawai ta saka a gaba ya tabbatar badan halin daya tsinci kansa ba ace cikin walwala da nutsuwa yake shekaru taran da sukayi tare idan be ?ara mata ba to ze koma ruwa, biye biyen da Yah Ahmad yayi ya?i har Allah ya taimakeshi ya bari irin shakulatun Sangaron da takeyi da lamuransa muddin ba bu?atar kanta bace dole ya nema a waje amma yaci sa'a mata sun fita akansa tunda ya rabu da ?addarar sa.

Washe gari ?arfe tara ya bar Kano cike da annashuwa biyu, na farko yanda suka gudanar da daren jiya tsakaninsa da Fatiyyah bayan yashawo kanta da ?yar. Beyi mata ?arya ba ya tabbatar mata ze auri Aafeeyah saboda yana sonta babu kuma abinda ze hana faruwar hakan face mutuwa amma ya mata al?awarin baze bari wani abu ya taSa martabarta ba, zeyi iya bakin ?o?arinsa gurin ganin ya kamanta adalci a tsakaninsu fatansa ta gyara ta kama kanta karta bada wata ?ofar da ko Aafeeyan ta shigo zata fuskanci akwai Saraka a tsaninsu yana kuma fata kamar yanda ta masa al?awarin komai ya wuce hakan ta tabbata su zauna lafiya ga kuma Wokin ganin Aafifi da duk yanda ya so ya hana zuciyarsa zumuWi akan lamarinta ya gagara. Sha biyu saura ya isa, har ya Wauki hanyar gidan Badar se kuma ya fasa ya wuce wani hotel yayi lodging ya kwanta dan ba wani isashshen bacci ya samu jiyan ba kuma ya tashi ya fara shiri da wuri saboda tafiyar da zeyi.

Yana shiga Wakin kiran Hajiya ya shiga wayarsa, tun jiya ya?i amsa wayarta yayi shahada dai ya Waga a ta?aice ta amsa gaisuwarsa tace
"Kana ina Jafar?" Ya kalli Wakin da yake ciki kamar me tsoron kar wani yaji ?aryar da zeyi kafin yace mata
"Ina Abuja hajiya".
"Abuja? Me kaje yi Abuja? " Ta tambaya kamar bata yarda ba. Ya kwanta akan gado yana ce mata
"Daga head quarter neakayi kirana ina ga maganar gasar kofin duniya ne kin san ban rigada nayi submitting retirement letter ba inaga shiyasa suke so su tuntuSe ni" ya gaya mata abinda ya gayawa Fatiyyah. Tayi shiru kafin tace

"Yaushe zaka dawo kenan?"
"Idan na gama da wuri a yau zan dawo in Allah ya yarda"
"Shikenan ina jiranka komai dare idan ka dawo kazo, idan ma se goben dai ka sauka a nan" hajiyar ta faWa daga nan ta katse wayar kiran Ashrab da tun fara wayarsu da hajiya yake kira ya sake shiga. Yayi tsaki, shifa duk shirin da suke da Ashrab tunda yace yana son Aafeeyah ya fita a sabgarsa shi kuma se nace masa yake kamar besan ya masa ba daidai ba. Rai a haWe kamar yana gabansa ya amsa wayar, daga can murya a washe Ashrab yace
"Ango na Fatiyyah da Fatima".
"Ko yan ba?in ciki basa so" Jay ya bashi amsa. Ashrab ya ringa dariya kafin yace
"Ko sun so ko basu so ba tunda Allah yayi ai dole su ha?ura, ina maka murna toh Ubangiji ya tabbatar da alkhairi ya kaWe fiti na" ya amsa masa da
"Amin nagode, kaima ya kamata ka tsayar da idonka guri Waya dai haka dan gane ganen naka ya wuce na shari'a kuma".

Shi Ashrab bema fahimci magana ya gaya masa ba saboda zancen yana son Fatima shiryashi akayi dan a hasala Jay amma shi be san anyi ba dan haka yace masa
"Kai dai tunda ka iya shigen layi dama ai shikenan, muna tafe in sha Allah jinkirin alkhairi ne. Congratulations once again" daga nan sukayi sallama a ransa yana mitar gulma ce tasa ze kirashi kawai seya kashe wayar gaba Waya ma yayi sallar azahar sannan ya kwanta se guraren uku da rabi ya farka ya ringa salati zuciyarsa na bugawa kar ace fa ta tafi. Hankalinsa be kwanta ba seda ya kunna wayar sa ya lalubo number Badar daya Wauka a wayarta ya kira ya samu tabbacin bata tafi ba kamar yanda ta sanar masa ta dai gama shiryawa Nurain suke jira zasu kaita park dan haka yace ta ri?e masa ita gashi nan zuwa gidan ya shirya a gaggauce yayi checking out ya tafi.

GIDAN ALHAJI AUDU
Wayewar garin lahadi aka tashi da hidimar girkin Waurin auran daya zo musu a ba zata dan se da Asuba Alhajin ya kira Momy da Hajiya Rabi ya gaya musu aure biyu za'a Waura, idan shi nasa kishi yasa sun ce ba zasuyi komai ba ai na Wan su dai ba sa ?iyi ba. Hajiya Rabin ce abin ya zowa a mamaki dan ita Momy tun daren jiya Ummansu Fatima ta kirata ta gaya mata zancen sedai bata zata lahadin washe garin take nufi ba musamman da sukayi bacci ?alau babu wata hatsaniya daga gefen Hajiya Binta amma data tuna a last strike take se abin be bata mamaki ba, sukayi fatan alkhairi Alhajin ya kawo kuWaWe masu yawa ya bawa kowacce sannan ya bawa Momy na Hajiya ta kai mata ya shaida musu an samu canji ?arfe sha biyu da rabi jirginsu ze tashi dan haka idan ya fita yanzu babu lallai ya samu sukunin dawowa gidan kafin su tashi se bayan sati biyu. Sun fasa tafiya Abuja Saudia zasuje suyi umarah da amarci na sati biyu kamar yanda Momy ta bashi shawara kan yafi ace Umarah ya tafi akan wata Abuja idan yaso kafin su dawo an gama gyara mata guri ta tare shikenan.

"Amma dai da ka kai mata da kanka ko ka kira

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login