Showing 210001 words to 213000 words out of 467220 words

Chapter 71 - MATAR MUTUM COMPLETED 1-3 BY MARYAM FARUK.doc

23 Sep 2025

12136

karSa ba dan yasha ya kawo mata abu yace a mayar ya?i karSa sedai ya kalallameshi da magana yace ko babu soyayya tsakaninsu Baffa Babansa ne zeyi mata komai saboda shi. Wannan ya rushe batun zuwanta Biki wanda daman ko da an barta a karan kanta ba zata so taje ba, to wai se taje a matsayinta nawa???

An dai yi biki a gidan Alhajin Bechi lafiya duk kalen bala'in Hajia da yan korarta dole suka kama kansu domin Yan uwan Momy da ?awayenta wannan karon basu zo da wasa ba. Yanda Hajiyar ta saba musu idan ana biki ba yarta ba amma komai yana hannu ta se abinda tace se yanda ta tsara za'ayi wannan karon basu bari ba. Basu saurari Alhajin ba kansa Ahmad da Sarki sun share mata hawayen komai domin duk halinsa shima wannan karon Ahmad ya shawo kansa sun fitarda mahaifiyarsu kunya ba tareda sunyi jiran kowa ba. Anyi biki lafiya Amare sun tare Hafsatu an tafi Abuja Aslamiyyah na nan Kano se Amaryar Yakubu shima da Allah yayi bana yayi auran tsalle tsalle ya ?are dukda seda Alhajin yayi masa barazana da ze saukeshi daga Acting Account General dan har yanzu ba'ayi confirming nasa ba kafin ya kawo matar akayi Bikin.

Afeeyah kuwa Rikicewa ta ringayi harta fara zaton WhatsApp Winta ya samu matsala saboda status Win Ahmad da Jay da suka zama iri Waya tunda aka fara bikin har aka gama seta yi tunanin repeating sukeyi taga kamar ana Jay dan komai ma gizon sunansa yake mata yanzu. Ko kusa bata kawo cewar Jay ze iya haWa wata ala?a da Ahamd ba shiyasa ma bata tsawaita tunani ko bincike ba ganin kuma komai ya koma normal shikenan ta manta. Ada bata fiya wani duba status ba amma haWuwarta da Jay kusan kullum seta duba update Winsa wanda duk akanta yakeyi. Yace mata yaso yazo Nigeria abinda ya hanashi zuwa contract Winsa da Arsenal taje ?arshe, Clubs da yawa suna zawarcinsa har yanzu kuma beyi finalizing inda ze koma ba yana so se yayi sealing deal Win kafin yaje wani guri. Ya tura maata da sabon Field name Winsa, a maimakon JAY its going to be AJAY. Yace A for AFEEYAH and JAY remain for the JAFAR bata yarda da gaske yake ba har se ranar da yayi sealing deal da PSG sabuwar rigarsa da AJAY aka bugata.

Ta ringa murmushi kamar wawiya sanda take kallon Interview Winsa, an tambayeshi me yasa ya canza suna kuma me A take nufi yace it remains secret lokacin da ze bayyana yana zuwa. Tana jin Yah Malam Winsu da Abokinsa Sani da tsabar yanda yake son Jay sunansa ya koma Jay ranar sunata magana. Ance Initial Win budurwarsa ne, wasu sunce Initial Win Yayansa ne da yake bala'in so kowa dai da abinda yake faWi. Kamar taje ta gaya musu gaskiya se kuma ta kama bakinta. Anty Sauda tayiwa Umma zancen itama bata bada goyon baya na cewa ma tayi karsu bari Baffa yaji dan ranta ne ze Saci. Ya za'ayi tsayin lokacin nan ta dawo tace wani daban ba Ahmad ba itama tasan wasa takeyi. A ranta ko babu gudu babu ja da baya tasan kuma Baffa baze taSa bin ta tasu ba ya aura mata abinda bata so. Ai da bakinta bata taSa cewa wani tana son Ahmad ba ko zata aureshi su suke kiWansu suna rawarsu dan haka babu wata hujja da za'a kafa da zata rabata da wanda take so, badai yace ya kusa zuwa Nigeria ba yana zuwa zata kaishi gidan ayita ta ?are da haka suka cinye hutun session daya ritsa da Strike kusan watansu uku a gidan kafin suka koma School First semester Four hundred level.
*Assalamu alaikum*
*Ina matan suke, Manyan mata yan kwalisa da suka amsa sunansu na Mata ba muna mata ba Kawayen Binta gumama?*

*SODAH GENERAL ENTERPRISES ce tazo da kanta ba aike ba tana kuma shaida mutu da cewar zafafan kaya sun sauka, kamar yanda kuka sani tana kawo muku suturu na sakawa kama daga kan Atamfa, Laces da dangoginsu*

*Wannan karon ta sake taho muku da tsarabar Supplements ingantattu wato Original bawai copy ba. Ku sani bayan abinci jiki yana da buqatar qarin wasu sinadarai da zasu taimakawa ginuwar jikin da lafiyar kowanne bangare na jikin, SODAH ENTERPRISES tana da General Supplements ma'ana wanda suke tattare da Vitamins da dukkan jiki yake buqata sannan tana da special supplements wanda HQ wato gidan mutunchi yake buqata domin sake tsare qima.*

*Ina wadda take fama da skin nata yaqi dadin azanci? Fata ta bushe tayi dabbara dabbara ta shafa mai duk a banza se qara lalacewa tayi? To maza ki leqa gurin SODAH ENTERPRISES domin tana da sabulu me kyau da inganci me gyara fata tayi kyau ta goge tayi sulbi baya saka Fari asalin kalarki ze sake fiddo miki ya kuna goge duk wasu tabo ko rashes da suke hanaki walwala, sabulunta babu chemical ba kuma na bleaching bane yawwa karki tsammaci da zakiyi haske Aa sedai glowing kalarki ta ainihi ze fitarda.*

*A tuntubeta kai tsaye akan 08137145294*
*Ko ki danna wannan link kai tsaye domin magana da ita*
https://wa.link/wwvjr3
*Location Kano, tana Nation wide delivery*

*MATAR MUTUM*
*NA MARYAM FAROUK (UMMU MAHEER*

*FIKRA WRITERS ASSOCIATION*

*LITTAFIN KUDI NE*
*PAY 500 A ASUSUN*
*7061838488*
*OPAY DIGITAL SERVICES*
*MARYAM FAROUK*
OR
*0709290797*
*ACCESS BANK*
*SE A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488*
*IDAN KATINE A DAUKI HOTONSA A TURA ZUWA LAMBAR SAMA VTU KUMA A TURA A 08142548705*

*Kuyi following dina a Arewabooks @Maryamfarouk01 inda zaku karanta wannan littafin tareda sauran littattafaina*
*NAGODE*

*BOOK 2*
*PAGE 16*

Rayuwa ta shuWa, soyayyar Afeeyah da Jay tana ?ara ?arfi inda al'amarinta tsakaninta da Ahmad yake sake taSaSarewa. Zywa yanzu ya gama tabbatarwa Fatima bata ta tashi da gaske wani ya masa shigar sauri kuma ya sure Imaninta. Ya sake tsananta Addu'a akan Al'amarin amma mainakon rangwame se sake jinta yakeyi a zuciyarsa kamar ture. Damuwar da yake ciki da ayyuka da suka masa yawa yasa duk ya sake figewa ya fita a hayyacinsa. Kowa a gidan yaro da babba ya shaida Ahmad yana da damuwa hatta Hajiya kuwa seda ranar ta tsare shi tace

"Kai Amadu anya magauta basu danneka ba? Wannan uwar rama haka kamar wanda ake Wiba ayi miya kullum? Koda yake jarabar neman kuWi daka saka a ranka ai dole ka?i abin kirki, ni na rasa ma me kake nema ko kuwa so kake se ka yi gasa da ?aninka ne? Shidai kasan yan guje guje kawai zeyi a fili ya dirim Miliyoyi sun shiga akawun, shiyasa yake mulla ?ibarsa kai kuwa kana ta fama da dogon wuya kamar tsohon ra?umi takwaran ubanka". A ?ofar Wakinta take maganar ga Hajiya bata rage Volume dan haka hatta Momy dake cikin falonta suna magana da Baba Bilki sun jiyota. Baba Bilki ta girgiza kai tace

"Yau rashin mutunchin Binta ya motsa kenan, daWina da ita bata bar kowa ba, kinji Mijinku ne takwaran tsohon ra?umi. Amma fa maganar gaskiya ki matsa Babana ya gaya miki me yake damunsa da gaske wannan ramar tasa tayi yawa, ni dana tambayesa yace wai aiki ne amma kuma wane aiki ne haka damuwarsa zata nuna har a fuskar mutum? Amadi da ko yaushe fuskarsa take a washe ga barkwanci amma yanzu se a wuni baka ga murmushinsa ba gaskiya ya kamata kiji damuwar yaron nan idan kuma naje Bechi daman zan karSo masa taimako dan dole mahassada suyi masa caaa irin wannan buWi da ubangiji yayi masa kiga komai yaro ya taSa se ya zama kuWi".

Tana rufe baki ya shiga falon da sallama ?asa ?asa, suka bishi da kallo harya zauna kusada ?afafun Momyn. Murmushin ya?e yayi ganin yanda suka zuba masa ido yace
"Lafiya dai Innata da Momy kuke kallona haka kamar kunga ba?o?" Inna yake kiran Baba Bilkin Jafar ma ya kama saSanin sauran da Manyan suce mata Hajiya ragowar Baba.

"Ai dole mu kalleka Ahmad, kana duban kanka a Mirror kuwa? Wannan ?asumbar da gashin daka tara a kanka na magani da menene?" Momy ta tambaya tana dafa kan nasa. Ya shafa gashin shima yace
"Lokaci ne ban samu naje aski ba amma yanzu idan na fita zanyi"
"Gara dai kayi ko ka koma hayyacinka amma fuska gashi biya biya kuma ba'a kintse ba ai babu kyau" Baba Bilki data mi?e ta sake faWa yayi murmushi yana tambayarta fita zatayi tace masa Bechi zata tafi kwana biyu bataje ba sati zatayi kafin ta dawo.

"Da bana komai ai da na kaiki"
"Aa yi zamanka, tare zamu tafi da Yaya Yakubu ai can gidan nasa ma zan tafi yanzu"
"Toh Allah ya kiyaye hanya ki gaidasu" sukayi mata bankwana. Bayan fitarta Momy ta fuskance shi dakyau tace
"Karka boyemun komai ka faWamun gaskiyar abinda yake damunka Ahmad".

Ya nisa kamar bazeyi magana ba se kuma yace
"Momy Fatima ce na kasa gane kanta"
"Matsala kuka samu?" Ta tambayeshi tana nazartarsa. Ya karkace kamar zeyi mata kuka yace
"Ni dai babu abinda nayi mata Momy itace dai bansan ko na mata wani abu ba. Gaba Waya ta canza duk na kasa gane kanta".

"Ahmad kama Addu'a kuwa akan lamarin yarinyar nan?" Ta tambayeshi, yaja rantsuwa yace
"Wlh ina yi Momy, ko jiya kwana nayi ina sallah ina addu'ar neman zaSin Allah amma wlh kamar an ?aramun sonta a maimakon ya ragu a zuciyata"

"Kuma ba addu'ar son rai kakeyi ba? Kana cewa kana neman zaSin Allah amma kuma ranka ba haka bane ka rigada ka zaSarwa kanka abinda kake so?" Momy ta sake faWa tana dubansa yace
"Momy shekara uku fa kenan, na san ba nacina ko dagiyata ce zata bani abinda nale so ba amma kuma Allah na barwa zaSina ina ganin da inada wani haske daban bayan ita da yanzu na ganshi amma Momy ita Win dai ita na gani nake kuma ji a jikina itace matata".

"Toh addu'ar dai ita zamu cigaba dayi akan koma menene Allah ya warware sannan damuwar daka saka a ranka ba zata amfana maka komai ba kayi ?o?ari ka cireta, duk abinda Allahya saka cewar rabon bawa ne a duniya seya same shi idan kuma ba rabonka bane duk wuya haka zaka ha?ura domin ba zaka sameshi ba. Sannan kuma ni ina ganin cewar harda halinka yasa yarinyar nan take maka koma menene"
Ya zabura yace

"Halina kuma Momy? Me nakeyi?" Momy tace
"Shekara uku kace da bakinka yanzu, wace irin soyayya ce haka har yanzu da za'ace ba za'ayi aure ba? Kaida bakinka kace mun mahaifinta yace maka ko tana cikin makaranta idan ka shirya aurar da ita zeyi to me kake jira har yanzu? Kana tsammanin zata cigaba da zaunawa tana Sata lokaci dakai ne Alhalin ?ila tana da wasu masoyan da suka fika himma?"

Yayi shiru dan besan bayanin da zeyiwa Momy ta fahimta ba. Baya so ya Sata Fatima a idonta ta hanyar sanar mata cewar itace har yanzu batayi na'am dashi ba kuma ita ta?i bashi damar ya tura ayi maganar auransu idan kuma yayi shiru Momy zata cigaba da bashi laifi na cewa shi yake Satawa Fatiman lokaci wannan yasa ta karkata hankalinta ga wani daya fishi himma kamar yanda tace.

"To ai Momy yanzu tana Level 4 har sun gama First semester da bari nayi tunda son zo ?arshe kawai ta ?arasa daganan se aje ayi magana"

"Oh so kakeyi harta gama makarantar tazo ta zauna sa'annan ka gama shiriritarka se aje ayi maganar aure ko? Lallai kuwa kana zaune nan zakaji wani ya aureta. Waima sanyar me kakeyi ne? Ina kace tun tuni ka sanar da Alhaji maganar nan me kake jira da ba zaka sake tayar masa da ita ba tunda ka nace lallai se shi zaka kaiwa maganar auranka?"

"Aa Momy ba haka bane ba, naga ai Alhaji ne Aha??u da na sanarwa da zancen aurena idan yaso shi kuma ya iya saka wakili ya shige mun gaba" ya bata amsa kai a ?asa. Momy ta harareshi tace
"Sannu uban fitar da ?o?on Asali, dama dai yanda kake da ?ulafucin uban nan shima haka yake ta taka amma na tabbata yanzu ya manta ma da kunyi wata magana data shafi zancen auranka dashi. Se kaje ka sake samunsa ai ka tuna masa, idan kuma yace Aa kaga aiseka fara sabon lissafi tunda ga tudun dafawar da duk yanda aka ciza ze tsaya maka kace baka san zance ba ba zakaje ta wurinsa ba".

"Ni Momy bana so a sakeyin irinta Yaya Sarki kina kallo dai Alhaji swda yayi ta faWa akan ya zameshi daga maganar auransa shiyasa amma ba wani abu ba kuma nasan ai dai ko shi na gayawa dole dai Baba Al?alin ze wakilta" ya sake faWa Momy tace

"Ai shikenan, amma dai mafita guda ce in har da gaske kake son yarinyar nan manya su shiga maganarku, kaje ka samu ubanka ka fayyace masa komai ya t???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?ura a nema maka auranta in kuma zaka zauna nu?u nu?un ne kuma shikenan"

"Toh Momy zanje" daga nan suka bar maganar suka shiga wata. Bayan fitarsa ya ringa shiryawa yana warware ta yanda ze sake tunkarar Alhaji da zancen aurensa da Fatima. Amma ta yaya ma ze taso magana alhalin ita wadda za'a aura Win bata yarje masa ba?

Ya samu jikin katanga ya lafe ya shiga kiran layinta, yanzu abin ya sake ta'azzara har rejecting take in bata ga damar amsawa ba kuma ya dameta, So hana ganin laifi haka yake jurewa domin ya yarda ?addarar sa ce Son Fatima. A kira na biyu ta amsa muryarta ta shaida masa bacci takeyi dan haka yace
"Kiyi ha?uri na tasheki a bacci"
"Babu komai ina zaune ne nima ban san baccin ya kwasheni ba, ina wuni?" Ta gaidashi. Tana da kirki, tana da tarbiyya, Mahaifanta mutane ne kai tana da duk wani quality da yake nema a gurin matar auransa baya zaton idan ya barta ze damu full option abinda yake nema a gurin mace tamkar nata ya ayyana a ransa.

"Kina free yau da dare zanzo?"
"Eh" ta bashi amsa a ta?aice, shikenan ya mata sallama akan se bayan Magriba zeje haka kuwa akayi yaje yayi aski ya Wan shiga saiti ana sallar Magriba ya sha kwalliya ya tafi gidansu. A can yayi sallar Isha a masallacinsu Baffa kafin suka ?arasa gidan tare. A ?ofar gida Baffa ya dubeshi yace
"Malam Ahmad na bawa Mamana Sa?o kusan sati nawa amma banji amsa ba".

Da rashin fahimta ya dubi Baffan kafin cikin girmamawa yace
"Ina ganin ta sha'afa ne Baffa ko kuma nine na manta da ta gayamun amma wace magana ce?"
Baffa yayi murmushi yace
"Dama maganar zuwan magabatanka ne nace lokaci yayi daya kamata ace manya sun shiga cikin maganar nan, ni badan ka buye ta tata ba kace a barta ta gama karatun kamar yanda take so ai da tuni kuma ka huta da biyo dare kana ma?alewa jikin katanga" Baffa yayi masa barkwanci. Yayi yar dariya yana sosa ?eya, Baffa ya sake cewa

"To ina sake maimaita maka tunda da alama ta sha'afa kamar yanda kace, a sanar musu saboda a san abinda ake ciki"
"In sha Allahu Baffa zan sanar musu" ya faWa kai a ?asa, Baffa ya wuce ciki yana masa Addu'a da fatan Alkhairi. Shiya turo masa Fatima wadda ta manta da batun zuwan Ahmad Winma seda Baffa yace mata yana waje. Dogon Hijab ta saka, bata shafa ko hoda ba ta fito tana bulbula ?amshin designer perfumes Win da yake kai mata akai akai. Ta gaishe shi ya ringa kallonta kullum ya ganta ?ara sonta yakeyi, jinta yakeyi har tsakiyar ransa shi be taSa sanin haka So yake ba seda ya afkawa kogin ?aunar Fatima.

"Yanzu Baffa yake cemun ya baki sa?o amma baki gaya mun ba" ya faWa yana kallonta. Ta juya ido abinda ya sake kashe shi kafin tace
"Wane sa?o kenan?"
"Ya wuce ai tunda ya faWa mun da kansa. Magana ce akan turo magabata na ayi maganar auranmu, na so na gaya masa har yanzu bamu samu fahimtar juna nida ke ba amma kuma na kasa".

Ta ringa kallonsa babu ?yaftawa harya kai aya kafin ta sauke kanta jikinta nayin sanyi kamar wadda rana ta daka, Ahmad ya harWe hannu a ?irji yana kallo ta ya sake cewa
"Baffa da kansa ya mun magana na turo neman auranki, kar kisa ya Waukeni a mutumin banza idan na gaza cika umarninsa. Fatima me kike da bu?ata? Ki gaya mun dan Allah me nene dalilin daya saka ba zaki bani dama na shiga rayuwarki ba?"

A maimakon tayi masa magana kawai se gani yayi hawaye ya fara mata tsere dan da hasken Nepa tar a ?ofar gidan, ya buWe baki yana kallonta da mamaki kafin yayi magana ta juya da sauri ta shige gida tana cigaba da kukan. Yayi kasa?e a gurin, shi ba abin ya bita ciki ba mamakin dalilin kukanta ya rufeshi. Yana tsaye Baffa ya fito be ankate ba seda ya kira sunansa.
"Malam Ahmad lafiya kuwa naga ta shiga gida tana kuka ko wani abu ne ya faru?" Baffan ya tambayeshi. To shi me zece masa yanzu? Gaskiya ze faWa masa ko kuwa yayi shiru Baffan ya zargi wani abun yayiwa yarsa?

"Wlh Baffa babu abinda ya faru, tambayarta kawai nayi ta amince na turo iyayena shine ta fara kuka ko magana batayi bama ta wuce ciki" ya faWa cikin rawar murya. Baffa yayi ajiyar zuciya yace
"Kayi tafiyarka kayi abinda nace maka in har da gaske kake son aurenta ka turo magabatanka"
"Nagode Baffa in sha Allahu zaka jini bada daWewa ba" daga nan yayiwa Baffa Sallama ya wuce, farin cikin daya samu dalilin ganinta ya gushe, har wani ciwon kai yaji yana neman kamashi kukan Fatima ya tabbatar masa da gaske bata sonsa tilas ya ha?ura da wannan yarinyar muddin ba rabuwa da ita ne Ajalinta ba.

A can gidansu Fatima kuwa bayan Baffa ya koma ciki tarar da ita yayi tana sharSar kuka Umma na tsaye kanta tana faWa kamar zata rufeta da duka.
"Ya isa Zara'u rabu da ita" Baffa ya faWawa Umman, ta zauna tana tsaki, ji take kamar ta rufe Afeeyar da duka ko zata maidata cikin hayyacinta.

"Duk menene dalilin wannan abun? Me ya sakaki kuka daga yace ze turo magabatansa dama bakya sonsa ne ko kuwa ra'ayi kika canza?" Baffa ya tambayeta. Bata amsashi ba se kuka da takeyi ?asa ?asa. Umma ta jefeta da takalmi tana cewa
"Ba magana ake miki ba kinaji kinyi shiru?"
"Nace ki barta Zara'u ko?" Baffa ya faWa a Wan fusace. Umma tayi ?wafa ta

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login