Showing 327001 words to 330000 words out of 467220 words

Chapter 110 - MATAR MUTUM COMPLETED 1-3 BY MARYAM FARUK.doc

23 Sep 2025

12209

gafarceni Yah Ahmad karka kamani da laifin son macen data kasance taka, wlh, daga sanda na fahimci Afeeyah itace Fatiman ka na ha?ura da ita kuma koda ace Allah ya ?addara na aure ta daga baya na gane bazan iya zama da ita ba tilas na rabu da ita domin a kullum ina Addu'a kar Allah ya jarabce mu ni da kai da son abu guda da ba zamu iya mallakarsa a tare ba.

Duk abinda ya faru a baya na Wauke shi a matsayin ishara, izgilin da nayi maka akanta ne Allah ya kwatanta mun. Kasha gaya mun so ba ruwansa da kyau, matsayi ko nasaba abune da ubangiji yake kinsawa bayansa a zuciya ba wai zaSi bane amma na gagara fahimtar haka. Ban santa ba ban taSa ganinta ba amma na zargeta da asiri tayi maka, har ?azafin maita na Wora mata dan a lokacin ina ganin waWanda abubuwa guda biyu ne kawai zasu saka mutum kamarka yaso macen da ba kowa ba irinta. Na ci zarafinta ma zagi iyayen ta da basuji ba basu gani ba se gashi lokaci Waya Allah ya kamani ya jarabceni akan abinda na ke tsoro. Ka yafe mun Yah Ahmad kuma Allah shine shaidana tun daga sanda ta zama matarka ban sake kallonta da wani abu da ya danganci soyayya ba. Kawai na kasa sakewa ne, zuciyata ta gagara karSar ?addarar data afka mata na kuma karSi hakan a matsayin sakayya, rayuwar ?unci da ba?in cikin da na ringa nanata zan jefata muddin ta kuskura ta aureka se gashi ni na ?are a cikinta" Jafar ya ?arasa hawaye na ziraro masa.

"To kuma hawayen badai yanzu komai ya rigada ya wuce ba?
Kasan ko, sanda aka tabbatar mun inada ciwon nan har na kai mataki na biyu ina shirin zuwa na uku, hankali na ya tashi matu?a da gaske. Na san mutuwa dole ce koda ciwo ko babu idan lokacinta yazo tilas ne na tafi to amma abinda na ringa tunani makomar Matata da kuma zumunchin gidanmu amma idan na tuna inada kai se naji komai yayi mun sau?i daga sanda na san wacece Fatima a gurinka na sake fahimtar tabbas komai yana faruwa bisa wata sila. Allah shi yasan abinda ya tsara a gaba fatana koma menene ya kasance Alkhairi a rayuwar mu baki Waya" Ahmad ya faWa cikin ?arfin hali yana kallon Jafar daya haWa kai da gado yana kuka kamar mace. Yar dariya yayi kafin ya sake ce masa

"Ni yanzu damuwata ma guda Waya ce, yanzu idan munje Aljanna ma wa zata zaSa a tsakaninmu, ni data fara aura ko kuma kai da zaka yimun fashin mata? Koda yake ma nasan ?arshe nine zanci girma na bar maka. Babu komai na samu wata zukekiyar hurul'aini da Sata taSa zaman Najeriya ba mu cigaba da kurSar romon damakaraWiyyar soyayya muna tsinkar inibin ?auna, ashe dai rabon zamana da Fatima ba me tsayi bane ba shiyasa na kasa ha?uri, duk wuya da daWi na jure amma ko a yanzu Alhamdulillah na godewa Allah bisa ni'imomin da yayi mun a rayuwa".

Mi?ewa Jafar yayi ya fice daga Wakin gaba Waya, can ya samu guri yayi kuka ya godewa Allah kafin ya rarrashi kansa ya koma Wakin ya tarar Ahmad Win ya koma bacci likitan dake dubashi tareda nurses gida biyu akansa suna ta turanci ya juya ze fita likitan ya dakatar dashi yana ce masa sun gama ze iya zama. Besan bacci ya kwashe shi ba se farkawa kawai yayi yaga karfe Waya har sannan kuma Ahmad be tashi ba.

Gida ya wuce da sauri, seda ya tsaya ya karSar mata abinci kafin ya shiga ya le?a Wakin da take itama ya tarar da ita tana sharar bacci se kawai ya ajiye abincin ya rubuta mata gajeran sa?o ya fita, da akwai wani Abokinsa Dan chaina daya je ya duba Ahmad har yayi mishi al?awarin ze karSo masa wani maganin gargajiya irin nasu yana fitowa daga gidan se gashi kuwa ya kirashi ya faWa masa kwatancen gidan wata yayarsa akan yaje ya karSi maganin jiya ta dawo daga china shi baya gari shiyasa baze iya amsowa ya kai masa ba. A sanyaye yake komai maganganun da sukayi Wazun da Ahmad Win duk sun sake kassara masa jiki.

*********
Fatima kuwa sanda ta isa bata tarar da Jafar ba se Ahmad da Nurse Win da take kula dashi yana zaune sun ta hira duk tarkacen wayoyin da suke jikinsa an cire, abinda yake danyatsansa ne kawai se ledar ?arin jinin da basa gajiya da saka masa. Wani lokacin ya shiga wani lokacin ya ki shiga ko kuma idan ya shigan ma daga baya haka ze ringa gangarowa yana dawowa waje.

"Nayi kewarki ina kika tafi kika barni?" Ya faWa yana mi?a mata hannu. Ta isa gareshi ya Wora kansa akan cikinta daya la?ume yana cewa
"Dan uwana Jafar ya kake?"
"Jafar kuma?" Ta faWa tana kallonsa, ya muskuta yana matsa baki kafin yace mata
"Na manta ban gaya miki ba ko? Indai kika haifi Namiji Jafar sunansa idan kuma macece Fatima".

Shiru ta masa ta zauna kawai, Nurse Win ta fita ta barsu ya kalleta cike da tsokana yace
"Maman Jafar"
"Ka bari bana so" ta faWa tana harararshi seya fashe da dariyar da ta manta rabon da yayi irinta yana cewa

"Yaushe rabon da ki harareni? Dan Allah ki Wan yimun tsiwar nan taki nayi kewarta sosai kinji"

A maimakon tayi abinda yace se ta shiga share hawayen da ba zatace ga dalilin su ba se yayi saurin tsayar da dariyar yana ce mata

"To me kuma nayi miki zakiyi kuka? Dan Allah ki dena bana so".

Goge hawayen ta ringayi da hannu bibbiyu ba tareda tace komai ba, kallon kafarsa tayi saboda bargon kan gadon da taga ya zamo yana jan ?asa seta mi?e ta tattareshi ta mayar kan gadon sannan ta gyara masa ?afar, nauyi taki ?afafunsa sunyi da kuma sanyi, seda ta gyara masa zamansa sosai yana ta binta da kallo kafin take ta rage sanyin Ac Wakin ta koma ta zauna.

"Dabino nake so naci" ya faWa yana kallonta, ta sake mi?e wa ta shiga duba durowar da take ajiye masa dabinon da ruwan zam zam da take tofa masa ayatushshifa ta duba tsaf amma babu dabinon seta kalleshi a hankali tace
"Ya ?are kayi ha?uri idan Jafar ya dawo seya siyo wani"

"Kunyi magana dasu Yaya Hassan kuwa sun sauka gida?" Ya sake tambayar ta ta amsa masa da
"Eh, munyi magana da Momy Wazu tace suna Legas,

"Allah sarki Allah ya saka musu da alkiya basu ladan zumunchi" ya faWa yana lumshe idonsa wani sirin hawaye ya ziraro da sauri ta matsa kusa dashi tana cewa

"Menene?"
"Dabino zanci" ya sake maimaita mata ba tareda ya buWe idonsa ba. Yar jakarta ta buWe ta dau?i kudi tace masa bari taje ta siyo, harta kai ?ofa gabanta ya tsinke ya faWi da sauri ta tsaya ta dage ?irji kafin ta waiwaya ta kalleshi idanunsa kur akanta ya mi?a mata hannu alamar taje seta koma da sauri. Da hannu Waya ya Wora kanta a kirjinsa ya sumbaci goshinta yace
"Allah yayi miki Albarka nagode da kulawa" kafin ya saketa a hankali ya runtse idanunsa da taga kamar sun juye, haka nan ta gagara motsawa ta zuba masa ido kawai tana kallonsa yana motsa bakinsa har tana jin sautin hailalar da yakeyi kaWan kaWan duk se taji ta kasa tafiya nemo masa dabinon, tsoron da bata san na menene ba ya dirar mata.

Kusan minti biyar tana tsaye ya sake buWe ido yace mata
"Baki tafi ba?"
A hankali ta juya tana waigensa harta fice daga Wakin. Bata sha wahala ba a cikin Asibitin ta samu gurin wata mata da take jinyar mahaifiyarta a hawan da yake ?asan nasu ta fito suka haWu ta tambayeta saboda ita sun Wan jima kusan watansu biyu a Asibitin har sannan kuma Allah be yanke musu zaman ba tace mata suna dashi ta Webo mata Ajwa da yawa ta bata ta koma gurin Ahmad Win, sanda ta koma ta tarar yayi bacci ta ajiye ta tsaya akansa tana kallonsa.

Bacci yakeyi amma fuskarsa washe da murmushi me kyau se taga kamar fuskar sa ta Wan ciko ya kuma washe mugun ba?in da yayi ya ragu. Ta daWe a tsaye tana kallonsa har seda ?afafunta suka gaji kafin ta zauna ba daWewa sega Jafar ya shiga ya mata kallo Waya ya wuce gaban gadon yana duba Ahmad. Ciki ciki yace mata

"Waye ya cire masa wannan abun"
"Wanda suka saka masa" ta bashi amsa tana Waukar wayarta da tayi ?ara aiko ya banka mata harara yace
"Fita malama karki tashe shi da ?arar wannan wayar taki".

Banza ta maaa ta amsa kiran video call ne Momyn Ahmad ta kira, fuskar Momyn duk a hargitse tace mata
"Ina Ahmad Fatima?"
"Gashi bacci yakeyi Momy meya faru?" Ta faWa tana kangawa Momyn fuskarsa.

"Babu komai kawai so nakeyi na ganshi yau duk bamuyi magana ba, Jafar ne a kusa dake?" Momyn ta sake faWa. Seta ajiye wayar a gefen gadon ta inda Jafar Win yake ya Wauka bayan daya harareta ya nufi waje suna magana da Momyn, can ya dawo ya ajiye mata wayar inda ya Wauke.

Murya a ciki tace
"Aikin banza mutum ya ringa nuna shi yafi kowa iya kula da mutum amma yini guda ya kasa Kira masa mahaifiyarsa suyi magana"

Kwafa yayi be tanka mata ba, sun fi minti ashirin a zaune kowa da abinda takeyi kafin Jafar ya tashi yana kallon ledar jinin dake hannun Ahmad. Sanda ya shiga Wakin kaWan ne ya rage a ciki ya kusa ?arewa amma yanzun se ya ga ledar ta cika taf da mataccen jini ba?i??irin dashi. Da mugun sauri har yana haWawa da gudu ya fita ita bata ma lura da abinda ya gani ba tana karanta Azkar a wayarta seda ya dawo tareda likitoci guda biyu sannan suka ce ta fita, kafin ta kai ga sakin ?ofar kunnuwanta suka jiyo mata abinda yayi sanadin tsayuwar numfashinta na wucin gadi,

"Wannan ai ya daWe da rasuwa" kalmomin da taji daga bakin likitan kenan daga nan ta yanke jiki ta faWi a gurin itama.

*MATAR MUTUM*
*NA MARYAM FAROUK (UMMU MAHEER*

*FIKRA WRITERS ASSOCIATION*

*LITTAFIN KUDI NE*
*PAY 500 A ASUSUN*
*7061838488*
*OPAY DIGITAL SERVICES*
*MARYAM FAROUK*
OR
*0709290797*
*ACCESS BANK*
*SE A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488*
*IDAN KATINE A DAUKI HOTONSA A TURA ZUWA LAMBAR SAMA VTU KUMA A TURA A 08142548705*

*Kuyi following dina a Arewabooks @Maryamfarouk01 inda zaku karanta wannan littafin tareda sauran littattafaina*
*NAGODE*

*BOOK 3*
*PAGE 23*


A hankali ta buWe idanunta da takeji sun yi mata nauyi tamkar yanda kanta yayi gingirin kamar an Wora mata dutse, a dishi dishin da take gani ta fahimci a Wakin da take kwana cikin apartment Win Jafar take. Ta yun?ura zata tashi zaune, zafin da taji ya tsarga mata a hannu ya ankarar da ita karkacewar allurar ?arin ruwan da aka saka mata se tayi saurin gyara hannun ta runtse ido kafin ta zare allurar gaba Waya daga jikinta take jini ya samu hanya bata ko damu ba ta haWe hannayen ta dafe kanta dake barazanar tarwatsewa saboda Azabar ciwo.

"Subhallahi a garin yaya kika cire Allurar?" Muryar Jafar ta doki kunnenta, ta Waga kai suka haWa isoi, cikin da?i?a biyu ta karanci tsanani ramar da yayi babu wani abu da yayi saura a fuskars ase dogon hanci da ?wala-?walan ido tamkar wanda yayi jinyar shekara goma.

Inda take ya ?arasa ya tsugunna yana ?o?arin kama hannunta dake zubar da jini amma ta janye seya tashi ya wuce gaban mudubi kafin ya dawo da wata ?aramar akwati ya budeta ya cire auduga da fulasta, da ?arfin ya kama hannun bayan ya goge da ruwan spirit kafin ya danne da audugar ya naWe mata shi da fulaster duk fusge fusgen da takeyi be saketa na seda ya gama ya tashi ya mayar da a kwatin inda yake sannan ya kalle yace

"Ina ne yakeyi miki ciwo yanzu?" Ta runtse ido, bata ma san me takeyi ba, kamar ma dai ta rasa tunaninta haka takeji a maimakon ta bashi amsa seta sake sulalewa ta kwanta tana dafe kanta. Cikin muryar dake nuna tsantsar kulawa yace mata
"Sannu, ki dauri ki tashi kiyi wanka sannan ki rama sallolin da kika rasa, nan da awa uku zamu tafi Najeriya idan Allah ya yarda" yana gama faWar haka ya fita daga Wakin ya barta.

Najeriyar daya ambata ce ta maido mata da ?wa?walwarta saiti harta tuna ainihin abinda ya sameta, mutuwa itace kalma ta ?arshe da taji an ambata sanda take cikin hayyacinta. Ta tuna bayan sumanta na farko ta farka inda ya sake samun tabbacin Ahmad uban yayanta ne ya rasu kafin ta sake komawa wani suman da se yanzu ta sake farkawa. Agogon dake manne a bangon Wakin ta kalla, wani irin agogo ne me haWe da kalanda, kwanan wata sunan rana harda shekara. Ita da ta suma a ranar Juma'a se taga agogon yana nuna ?arfe uku da rabi na safiyar litinin. A hankali ta mayar da idanunta ta rufe wani abu me tsananin Waci da nauyi ya tsaya mata a ma?ogaro seda ta kwashi kusan minti goma kafin ruhi da gangar jikinta suka haWe harta samu damar tashi tsaye, dabin bango ta isa banWaki ta Wauraye jikinta dan ba zata kira abinda tayi da wanka ba kafin ta Wauro Alwala ta fito tana takawa a hankali.

Nurse Anna, matar da tayi jigila da jinyar Ahmad ta gani tsaye a Wakin, da sauri ta nufeta ta taro ta tana mata sannu. Ita ta taimaka mata ta zauna ta matso mata da kayan shafa seta girgiza mata kai alamar bata bu?ata, doguwar riga me dan kauri da Hijabi da ta gani a ajiye ta zura a jikinta, seda Nurse Win ta auna jininta da bugun kirjinta ta tabbatar da daidaiton komai kafin ta fita ta barta bayan ta shimfiWa mata abin sallar data bu?ata.

Tana tsaka da sallar ta koma Wakin da faranti data shiryo mata kayan abinci ganin bata idar ba yasa ta shiga tattara mata komatsanta a cikin jaka tana share hawaye dan Jafar ya gaya mata yanzun zasu wuce gida. Ba ?aramar sha?uwa tayi da Ahmad ba a Wan lokacin da yayi a Asibitin su. Ita ce take kula dashi mutuwarsa ta gigitata dan ko kafin shigowar Fatima a ranar hira sukeyi tana ce masa tayi mamakin sau?in da yake samu domin basu zaci ze ko kwana a Asibitin ba bayan da aka kawo shi yace mata harda gudummawarta a ciki kulawar da take bashi ta taimaka gurin samun lafiyarsa, Yana ta yi mata hirar yaransa, har yace idan Fatima tazo zai ce mata ta nuna mata hotunansu ashe da rabon baze samu damar hakan ba.

Sanda Fatiman ta suma ma bayan ta farfaWo ita ta cewa Jafar su wuto gida kawai zata zauna da ita, a kwana biyun ita take zaune da itan shi kuma yana can Asibitin ya tare a mutuware kan gawar Ahmad yana karanta masa Alkur'ani mai girma sallah ce kaWai take tayar dashi ba yanda mahukuntan gurin basuyi ba tilas suka kyale shi musamman daya samu goyan bayan musulman cikin su. Sunyi bala'in tausaya masa kuma sun jinjina masa ta yanda ya karSi sa?on rashin mutumin da sukayi amanna yana ?auna da gasken gaske da cikakken tawakkali ya burge su.

Bayan ta idar da sallar ta jingina kanta jikin gado tana jan carbi ba tareda ta ko kalli abincin da aka ajiye mata ba, cikin gajiyayyar muryarsa yayi sallama ta amsa a zuciya, a kusa da ita ya tsaya yana mi?a mata waya yace
"Ummanki ce"
"Sannu Fatima kin tashi Ashe" Umman ta faWa bayan data amsa sallamar da tayi mata. Da "eh" kawai ta amsa mata daga can Umman ta sake cewa
"Kiyi ha?uri kinji muma duk dakon jiranta mukeyi, muna nan muna jiranku duka harsu Badariyyah gasu muna tare anan gidan tun ranar da akayi rasuwar tazo, Allah ya kawo ku lafiya kiyi ha?uri kinji"
Da "toh Umma" ta amsa mata dan kalaman bakin ta sun tafi hutu seda taji wayar ta katse kafin ta zareta daga kunnenta ta mi?a masa ba tareda ta kalleshi ba.

"Kwananki biyu a kwance bakici komai ba se ruwa da ake saka miki, ko babu yawa ko Waure ki saka wani abu a cikin ki" ya faWa yana du?awa ya ajiye farantin abincin a gabanta seta kawar da kai gefw tana cewa
"Na ?oshi"
"Kici ko kaWan ne" ya sake faWa mata cikin lallashi, musun bashida wata fa'ida dan haka ta karSi kofin daya zuba dafaffiyar madara a ciki ya mi?a mata. Tamkar tana shan maWaci haka ta ringa runtse ido harta shanye saboda yanda ya sakata a gaba ya sake tsiyaya wani a kofin ta toshe baki da hannunta tana cewa

"Zanyi amai idan na sake shan wani abu"
"Idan kin gama ki fito" ya faWa yana mi?ewa ya kwashe kwanukan ya fita dasu a maimakon ta tashi se ta mayar da kanta jikin gado hawaye masu Wumi suna gangaro mata. Ta kasa gasgata al'amarin, ta kasa yarda da gaske wai Ahmad ya rasu ji takeyi tamkar rayuwarta ta kife baibai me yasa Ahmad ze tafi ya barta a yanzu data fi bu?atar rayuwa dashi sama da kowa da komai a faWin duniya?
Seda ya sake shiga ya maimaita mata zasu makara kafin ta rarrashi kanta ta bi bayansa suka fita.

Se bayan da suka zauna a cikin Jirgi kafin Jafar ya gaya mata gawar Ahmad zata rigasu isa Najeriya da kusan awanni biyu, ita dai tunda ta kwantar da kanta jikin wundo bata sake cewa komai ba har bacci ya Wauke ta dalilin maganin daya tilasta mata tasha bata kuma farka ba seda jirginsu ya sauka a Legas.

Al?ali Yakubu, Alhaji Babangida, Alhaji Abdullahi, Sarki se yan uwan Momy guda biyu tareda Salim da Dr Hassan suka tarar suna jiransu har sun karSi gawar su kaWai suke jira. Dr Hassan da Salim suna dab da shiga jirgin da ze kaisu Kano labarin rasuwar Ahmad ya riske su dan Hassan Win kaWai Jafar ya iya kira ya sanar masa daga nan kuma ya kashe wayarsa seda aka kwana sannan ya kunnata saboda ya sanar musu da sun samu da jirgi da wuri zasu taho gida.

A private jet Win Alhaji Audu suka taho Kanon, seda suka sauka sannan taga akwatin da gawar take ciki ana ?o?arin sakashi a motar ambulan, tayi tsaye tana kallonsu sam bata ji maganar

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login