Showing 45001 words to 48000 words out of 467220 words

Chapter 16 - MATAR MUTUM COMPLETED 1-3 BY MARYAM FARUK.doc

23 Sep 2025

12121

ta tayar da sallah. Harta idar da shafa'i da wutri ta zauna zaman lazumi babu Audu babu labarinsa har ta jiyo an fara labaran qarfe tara abinda ya saka ta shafa addu'arta ta fito tsakar gida kenan ta leqa Abdullahi taga harya kwanta shima ya kashe musu fitila alamar ya dade da dawowa kenan.

Mamakin inda Audu ya tsaya takeyi, duk zamansu daga sallar Isha baya zuwa ko ina a gida ze zauna suyita hira har lokacin bacci yayi kuma da Binta tazoma be fasa ba daya dawo daga Isha ze garqame qofar gida to yau ina yayi kuma.
Zaure ta leqa, mamakinta ya ninku ganin qofar a kulle da sakata, ya shigo har ya kulle kenan to ina ya shiga
"Gurin Amaryarsa mana" zuciyarta ta bata amsa. Gabbanta suka qara yin sanyi ta koma ciki tana ayyana wato wannan ne abinda mutane sukayita hango mata amma wauta da yarinta ta hanata fuskanta, so da yardar da tayi da Audu yasa bata taba hasaso ze iya wofantar da ita akan wata mace ba koda yake Amarya ance kota Kare ce ana dokinta sedai shi nasa zirgillin yayi yawa bata tsammanin haka sauran maza da suka qara aure sukeyi tun ba'a je ko ina ba su fara nuna da uwargidansu da bola babu banbanci a gurinsu.

Yunwar data kusan wuni da ita tana aikace aikace ta sakata zuba funkason ta shiga ci badan dadi ba sedan maganin yunwa zuciyarta cunkushe da tunani. Wa zata kaiwa kukanta ya bata mafita dan ita a iya wayo da dabararta bata san me zatayi ta kaucewa afkawa wannan wawakeken ramin dake a gabanta ba. Makirci da tuggun da Binta ta tsiro dashi ga kuma megidan dataga alamar sam ba zasu daidaitaba. Domin bashi da fahimta, ta sani a koda yaushe hasashe da maganarsa itace daidai babu ruwansa da jin bangare domin yin alqalanci akan abu wannan halin ko akan yaran yana gwadawa duk wanda ya fara kawo masa qara yakan bashi gaskiya ba tareda ya tsananta binciken bin ba'asin ainihin abinda ya faru ba ta sani yanzu koda zata fada masa abinda Binta tayi mata a bayan idonsa baze taba yarda ba, tunda bata san meta gaya masa dazun da har yake mata fadan ta barta ita kadai zaune ba.

Ta gama cin abinci ta matsar masa da nasa gefe ta fita da kwano ta daurayo bakinta kafin ta shiga shirin kwanciya itama. Tana tsaka da shafe jikinta da Addu'a ya shigo tayi saurin jan bargo ta rufa har kai a zuwan bacci take tana jinza yana kiran sunanta taqi amsawa saga kwancen da take tana iya shaqar qamshin turaren Binta tamkar jiya, wani abu me daci ya taso mata se hawaye suka shiga zubar mata ya fita daga dakin yana cewa
"Har kinyi bacci bari naci abinci toh"
Siririn kuka ta saki murya bata fita. Wannan wani irin abu ne? Sati daya da qara auren har zata fara karbar wannan wulaqancin haka, jiya be shigo da wuri ba da safe tazo ta kasa ta tsare bata barsu ko gaisuwar kirki sunyi ba sannan yanzu ta janye shi se yanzu ya dawo shin shi be san abinda yakeyi babu kyau ba idan ita tanayi da gayya da mugunta ne shi ya kamata ya biye mata su shiga haqqinta?

Tana sharar hawaye ya gama cin abincinsa da duk uzurin da zeyi kafin ya kwanta a bayanta. Wani kuka ya sake taso mata sanda ya jata jikinsa tana jin qamshin turaren Bintan a ainihin fatarsa da alama jiki suka hada. Ya dade yana koya mata abubuwa wanda se tayi da gaske take iya maida masa da martani saboda kunya yau kam bata da qarfin jiki dana zuciyar da zata kulashi. Tana jinsa yana zabga tsaki bayan daya samu nutsuwa, be ko jira ta saka musu ruwan zafi ba ya fice ko ya dumama koda na sanyi yayi oho ita dai seda ta fara jin saukar numfashinsa alamar bacci ya kwashe shi kafin ta fita ta saka ruwa tayi wankanta.

Tunanin abinda ya sakashi tsakin ta ringayi, duk sharrinsa bazece yaji wani abun daban tattare da ita ba saboda gyara gangariya Innarta tayi mata ruwan Ni'ima har diqa yake a jikinta kuma ko yanzun dukda jikinta be wani karbi abinda ya mata ba amma tasan taba da ruwan da ze bashi duk nutsuwar da yake nema to kodai shirun data masa ne ya bashi haushi dan yasha gaya mata baya so tana barinsa yana abu shi kadai. Da safe ma haka ya fita yana faman daure dauren fuska, qarfe biyar na yamma Babangida ya shigo da Biskit yace mata Babansa ne ya bashi ta tambayeshi yana ina yace yana dakin Amarya, be leqasu ba seda ya dawo daga sallar isha shima daga bakin qofa yayi mata seda safe ya juya daman ko qyallin idon Binta bata gani ranar ba.

Haka al'amura suka cigaba da gudana, a watanni biyu da auran Binta Bara'atun ta fita hayyacinta seka dauka jinyar shekara tayi saboda rama da baqin da tayi. Wani irin zama sukeyi mara kan gado, Audun gaba daya kamar wanda aka sakawa hannu ya fita a sabgarta tsakaninta dashi idan yana dakinta gaisuwa ce se ranar dayayi sha'awar kulata a shimfida yayi bayaga wannan idan kaji yayi doguwar magana da ita to qorafinta Binta ta kai masa yazo yanayi mata fada wanda bata iya ce masa komai illah ta bashi haquri, to ba se ta aikata abinda ake ce masa tayin ba sannan ne har zata kare kanta. Wata irin annamimiyar matace Bintan, rashin mutunchi da Tijara se kalar wanda ta manta ne batayi mata a gidan da zarar Audun ya fita yamma nayi ta daidaici lokacin dawowarsa idan yana dakin Bara'atun kenan kuna zata sheqo wanka tazo ta kame mata a falo harya dawo sannan ta hillace shi su tafi se sanda ta ganshi a hakan kuma ze zo ya rufeta da fadan Binta tace tayi mata kaza ko tace mata kaza babu bin ba'asi babu tambayar ya akayi yanda kasan wanda Bintan ta wanke gabanta ta bashi yasha haka yake shakkarta yake jin maganarta.

Ita kuwa Binta daman a shirye ta shigo gidan Audu, bata tsarawa kanta zama da kishiya ba dan haka ta shirya ta kuma tsara komai yanda zata ringayiwa Bara'atun gashin quma har se ita da kanta ta fita ta bar mata gida. Sanda tazo taga yar yarinyar a matsayin matar Audun ma abin dariya ya bata tasan ba zata sha wahalar kada taba, tayi amfani da nakasun Audun tayi galaba akansa. Ta karanci shidin mutum ne me son a riritashi, kalar soyayyarsa da wayewarsa har mamaki abin yake bata tamkar wanda ya tashi cikin Turawa ko wasu gogaggun mutane shiyasa take qure basirarta ta tabbatar da ta tashi kansa da nata salon wayo da dabarar. Da baki kadai idan ta zauna ta ringa tsara masa zance baya sanin sanda yake aikata duk abinda ta sakashi ta kuma fahimci Bara'atun wawiyace babu abinda ta sani se Biyayya wa Audun kamar zata kwanta masa irin abubuwan da Bintan take masa yasa gaba daya ya raina Bara'atun dan qoqarinta da yake gani a baya duk ya disashe, a yanzu kuma da damuwa tayi mata yawa tasa abinda take iya tabukawar ada ma ta dena Shiyasa ya fita a sabgarta.

A ganinsa baqin kishi ta saka a ranta shiya hanata walwa ta takura kanta shi kuwa bashi da lokacin da ze zauna yana lallashinta ko tambayarta me take so tu da dai be tauyeta da komai ba yanzu da budi ya qarar masa ma jin dadi da abubuwan mora rayuwa sedai suyi Kyautarsu amma dukda haka a maimakon ta saki ranta taci arziqi Aa se rama take tana qara qarmashewa tana ja masa zagi dan duk wanda ya ganta se ya zargi wani mugun abun sukeyi mata da ya saka ta fita hayyacinta.

Bara'atu bata sake shiga uku ba seda Binta ta fara laulayi, duk wata hidimar Bintan kanta ta koma bisa umarnin Audu, haka zata kwanta kamar ruwa idan yana gida tayita malele kuwa ita a dole ciwo take daidai da dan kamfai idan ta cire Bara'atun ce zata wanke mata girki kuwa se tayi kala uku a rana kuma taqi ci idan ya dawo tace masa ai ta fada mata abinda take so taci taqiyi haka ze hau kanta da fada da bala'i baiwar Allah sedai tayita kuka tana kuma kaiwa Allah kokenta gashi ya hanata zuwa Bechi a fadarsa idan ta tafi waze kula da Binta tunda shi yanzu sabgogi sun masa yawa dan har tafiye tafiye ya fara.

Wannan bala'i yasa ta qara figewa tayi zuru zuru. Ana haka ya tada zancen gyaran gida saboda ya samu isassun kudin da zasu gina masa abinda yake so. Sunyi shawara da Binta akan Bangaren Bara'atu za'a rushe tunda shine gefen hanya zefi kyau ya zama fuskar gida dan haka ya samu Bara'atu da zancen murna kamar ta fasa ihu sanda yace mata zata tafi Bechi ta zauna na wani lokaci kafin a gama gyaran gidan, a cikin sati daya suka tattara ita da Yaran suka tafi Bechi, cikin bangaren Yakubu na da suka zauna wanda Audun ya saka aka gyare shi daman idan sunje can suke sauka nan fa gulma ta ringa yawo a gari kan cewar auren ta ne ya mutu. Ramar da tayi ta qara bawa mutane abin fadi aka ringa yawo da zance kala kala kowa da irin abinda yake fadi.

Hankalin Bilki ya tashi da ganin Bara'atun, ita kadai ta iya budewa cikinta ta fada mata halin da take ciki a gidan dan uwanta dan hatta da Innarta duk yanda tayi da tasan me yake damunta qin fada mata tayi kawai tace mata rashin lafiya tayi amma ta samu sauqi. Ran Bilki ya baci da labarin da Bara'atu ta bata, ta ringa fada qarshe ta dora mata laifin cewar koma menene ita ta jawa kanta da tun farko ta basu damar yi mata rashin mutunchi.
"Akan me zaki zauna kinemi ki kashe kanki da damuwa? shi Yaya Audun mala'ika ne da bazaki iya kallinsa ki gaya masa abinda yake ranki ba. Kin zauna kin bari zuciyarki ta cika da tsoro mara dalili kina cutar da kanki to wlh idan kika cigaba da wannan salibancin kina ji kina gani seta rabaki da gidan kamar yanda ta fada" Bilkin ta fada cikin qunar rai.

Zamanta a Bechi se yafi mata kwanciyar hankali da nutsuwa, a qasa da wata daya ta fara maida jikinta ta murmure to bata da matsalar komai, ga kayan abinci nan jibgi ya ajiye musu haka kudin kashewa ya bata isassu tayi bacci cikin nutsuwa ta farka tayi abinda zatayi ta fita gurin Goggo Fadi suyi hira da Amaryar da Aminu yayi ya ajiyeta nan suke zaune tareda Goggo Fadin saboda qafa data sakata a gaba, idan kuma taji marmarin fita ta tafi gidansu ta wuni can dare yayi ta koma gida a haka suka ci wata daya sannan Audu ya je musu kwanansa biyu ya juya haka kuma yaci gaba dayi duk qarshen wata zeje yayi musu kwana biyu har suka shafe watanni hudu a Bechi.

A bangaren Audu da Binta kuwa filin gida suka samu suna zuba sharafin soyayya babu kama hannun yaro. Ginin daya tayar kuma yayi nisa, ginin Bene ne akeyi na zamani taswira me kyau da qawatarwa qasan na Mandiya Binta ne se Benen da aka dora da zata zama turakar me gidan bangaren da Bintan take ciki yanzu kuma ya barshi akan Bara'atu seta koma can dukda Binta a ranta ta quduri cewar Bara'atun ta tafi kenan ba zata dawo mata cikin gida ba. Kwana biyu da yake zuwa yi musu qarshen wata seda yayi da gaske Binta ta barshi, Allah ya sani bawai baya son Bara'atu bane Aa mugayen halaye data tsiro dasu ne suke bashi a ganinsa Kishi ne yake damunta ya hanata walwala.

https://chat.whatsapp.com/I8xKHGurk7EBf5ZqQdxHKG

*MATAR MUTUM*
*NA MARYAM FAROUK (UMMU MAHEER*

*MARUBUCIYAR*
*WATA KISHIYAR*
*RUBUTACCIYAR QADDARAH*
*HALIN KISHI*

*FIKRA WRITERS ASSOCIATION*

*LITTAFIN KUDI NE*
*PAY 400 (PROMO PRICE BAYAN KAMMALA FREE PAGES ZE KOMA 500) A ASUSUN*
*7061838488*
*OPAY DIGITAL SERVICES*
*MARYAM FAROUK*
OR
*0709290797*
*ACCESS BANK*
*SE A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488*
*IDAN KATINE A DAUKI HOTONSA A TURA ZUWA LAMBAR SAMA VTU KUMA A TURA A 08142548705*

*Kuyi following dina a Arewabooks @Maryamfarouk01 inda zaku karanta wannan littafin tareda sauran littattafaina*
*NAGODE*

*FREE PAGE 13*

Gini ya kammalu har Binta ta tattara ta koma sabon bangarenta. Sababbin kayan daki Babanta yayi mata jere na garari irin wanda ba'a samu filin yi a wancan dakin ba se yanzu saboda wannan me yalwa sosai akqa debe su dan har rabin Filin maqocinsu da suke jingine ya siya ya shigo dashi shiyasa ta samu maka makan dakuna biyu ga Falo da kitchen da sto???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?re, an rushe katangar tsakiyar bangarorin gidan ya hade se ya sake tada daki babba a tsakar gida guda daya aka kumayi Kitchen shima na tsakar gidan se Bandaki.

Tsaf aka fente ko Ina har inda Bintan ta tashi dukda babu abinda gurin yayi amma yaga be kamata Bara'atu ta shiga a haka ba. Ya sake aiya mata gado daya tunda daya take dashi nan kuma daki biyu ne yasa aka kwaso kayanta ta aka ajiye a store din gidan Alhaji Idi gidan qawarta qwara daya duk unguwar, da ita kadai ta iya sakewa ragowar dai idan sabga ta tashi aka gayyaceta zataje amma bata shiga gidan kowa suma tun suna shigo mata ganin bata sakewa yasa suka bari. Binta na zuwa suka ringa shishige mata duk suka zama yan korarta dan ta wuce da Ajin ace qawayenta ne, amma da yake yawancinsu gulma ce wasu kuma kwadayi ya sakasu neman qawancen haka suke jure duk izgilancinta suna manne da ita.

Ranar da aka maido kayan Bara'atu Binta bata tare suka fita da Audu ya ajiyeta a Gadon qaya dan ya siyi mota a tsukin. Gidan wani sabon Abokinsa Mustapha shima harkar Mai yake dan haka yanzu Audun yana mu'amala sosai da su dan qungiya guda garesu. A Asibiti suka hadu da Matarsa Baturiya gurin awo, hali yazo daya aka qulla qawance. Se daga baya suka fahimci sudin matan Abokanai ne shikenan zumunchi ya qullu har ta gabatar da ita ga sauran matan Abokanan mazajen nasu dan suma guruf suke dashi kowacce naji da kanta Mijinta hamshaqi.

Data dawo gidan bata ma lura da an zuba kaya ba tunda qofar a kulle take, taci gaba da sabgoginta. Washe gari Audu yace mata gobe zeje Bechi. A fili tayi masa fatan zuwa da dawowa lafiya a zuciyarta kuwa tace
"A haka dai Auran ze balbalce badai ta dawo gidan nan ba".
Da Asuba bayan sun tashi kuma yace mata ta shirya kayanta kala biyu su tafi tare saboda duk sanda yaje se yan uwansa sunyi qorafin rashin zuwanta kuma ya manta Gobe daurin Auran Saleh Yaron Yaya Baba na Biyu. Rabonta da Bechin tunda aka kaita tana Amarya se zuwa daya da sukayi gaisuwar rasuwar Wan Baban Bara'atu shima a tsaitsaye ba kwana tayi ba watanni takwas kenan.

"Yanzu a sanyin nan kake so na tafi qauye?" Ta fada tana kumbura baki sanda yace ta shirya din, Audu ya kalleta yace
"Gida fa zamuje ba Jeji ba balle kice zakiji sanyi. Yaushe ma rabonki da can? Karki manta Bechi tushe na ne. Badan iyayenmu basu da rai ba kin san baki isa ki kwashi wata daya ba ba tareda munje kin gaishe su ba, ko yanzun ayyuka ne suke shan kaina su hanani zuwa ziyara akai akai amma ina ganin zan nemi direba wanda ze ri ga kaiku duk hidima Biki ko suna be kamata ace kuna qin halarta ba tunda ba kullum bane sannan tunanin da nakeyi zan gyara gidan mu nacan duk sallah mu ringa tafiya munayi tareda yan uwa"

"Tabdi" ta fada a ranta, a fili kuma ganin yanayin da yayi maganae kamar ransa a bace yake yasa tace masa
"Nima bawai ina nufin wani abu bane kawai dai saboda cikin jikina kaga ya girma be kamata na ringa dogayen tafiye tafiye ba"
"Kwananki nawa da dawowa daga Kaduna? Bechin ta kai nisan can ne? Ko da qafa zaki tafi? Kinga karki bata mun rai idan ba zakije ba ki zauna" ya fada yana ficewa daga dakin.

Ita da take neman hanyar da zata kama shi a hannu ina ita ina neman fitinarsa shiyasa ta tashi ta shiga shirya kayan kamar yanda yace a ranta kuma tana ayyana irin abinda zatayi idan taje. Ta tsani qauyen da mutanen cikinsa. Su ba kowan komai ba se Izza da girman kai ya yayan Sarakai wannan shegiyar Bilkin ko nan Kanon tazo haka take mata rashin mutunchi Audun na kallo ba zece komai ba ti duk zatayi maganinsu. Ta shirya kala biyun kamar yanda yace sannan ta kwashi kayan shayi, Biskit da cincin din da Mero matar da ta samo tana mata girki tayi mata harda dubulan se Sauran Miya duk ta hada kamar me zuwa wata qasar. Audu be shigo ba se gurin takwas lokacin har tayi wanka ta karya da Mairo da Lantana ita kuma share share take mata duk da suka zo cewa tayi su tafi se bayan kwana biyu zasuje qauye. Ganin ta shirya ya saka shima shiga wanka a gaggauce ya shirya suka kulle gidan suka tafi.

Sun isa Bechi ana ta hidimar daurin auren da za'ayi washe gari. Gaisuwar ma kamar sun roqa haka tayiwa wanda taga zata iya. Wadanda ta raina kuwa ko kallon Arziqi basu samu ba. Bara'atu na cike da murnar zuwan Audu sedai ganinsa da Bara'atu ya saka duk karsashin ya barta, gabanta ya ringa faduwa dan ita tsoronta takeyi ko kuma tace tsoron kaidinta. Ita wlh daze barta a nan Bechin yaci gaba da zuwa koda ba duk sati ba zata yarda. A zaman da tayi harta murmure tayi tas abinta babu damuwar Miji babu ta kishiya kuma idan yazo mata kwana biyun sosai yake tarairayarta yana riritata sabanin a Kano da a suna ne kadai take da girki dan ko Binta ta barshi ya kwanta a dakinta to fa ba zasuyi bacci zur ba tareda tazo ta tashe su ba da sunan ciwo na damunta wanda se a ranakun girkin Bara'atun take ciwo. Audun da kansa yake ce mata idan a can yake watara ta kwanta ko farkawa batayi se Asuba.

A dakin Bara'atun Binta ta sauka kamar yanda ya tsaya. Ta haye mata

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login