Showing 363001 words to 366000 words out of 467220 words

Chapter 122 - MATAR MUTUM COMPLETED 1-3 BY MARYAM FARUK.doc

23 Sep 2025

12171

kafin suka wuce gidan, Ahmad ya rigada yayi bacci tunda ya mayar dashi aka bashi abinci yaci aka masa wanka shikenan yayi bacci abinsa dan daman ba wani damunsa Nono yayi ba.

Yana rungume dashi yace su shiga su kirawo wani ya karSe shi, Fatima na zaune a falo ta baje takaddu tana dubawa, watanninta biyu da komawa makaranta kenan, tayi registration latti dan lectures har sunzo ?arshe ana shirin fara jarabawa shiyasa duk abin ya rikice mata. Ta zura dogon Hijabi kan kayan jikinta ta fita amso Ahmad Win ba tare da ta tambayesu waya dawo dasu ba tasan dai baze wuce Salim ba dama kuma so take su haWu fuska da fuska ta shata masa layi akan abinda ta kira rashin hankali da yakeyi mata.

Wai kamar ita Salim yake aikawa da sa?onnin soyayya tsabagen baya tsoron Allah kuma bashi da kunya. Fuska a haWe kamar wadda zata fita ya?i ta buWe ?ofar gidan, Jafar daya bata baya ya juya suka haWa ido su biyun kowa ya wani tamke fuska kamar yaga abinda baya so.

Tsayawa tayi a inda take ta?i karasawa kissafinta yazo ya kawo mata shi, gane hakan yasa shima ya jingina da jikin mota ya kalli gefe yana sake tamke fuska. Tsayuwar kusan minti biyar tayi beko sake kallonta ba balle yaje inda takez zuciya tazo mata wuya, indai har yana nufin ita zataje inda yake to kuwa sedai ya juya da yaron. Ciki ta shige bam ta bugo ?ofa, yajin haka shima ya buWe motarsa ya shiga hankali kwance ya kwantar da sit ya kishingiWe abinsa. Gida zashi daga nan balle yace ze Sata lokaci, daga nan har 10 idan taga dama ta fito ta amshe shi.

Har bacci ya fara Waukar sa bugun da akewa gilashin motar ya farkar dashi, yanda ya buWe gilas Win yaso ace itace babu abinda ze hanashi fasa mata baki amma se yaga Baffa ne. Saurin kintsa kansa yayi ya sakko daga motar yana gaishe shi Baffan yace
"Ashe kana nan, naga shigowarka fa ni kuma mun fita mun le?a wata dubiya ne bayan layi ashe kana nan da abokinka har yayi bacci ma".

Shafa kansa yayi yace
"Na rasa wanda zan aika ciki ne".
"Se kace wani ba?o? Sallama kawai zakayi a baka izini ka shiga, kuma daka kirata a waya ai da tuni ma ta karSe shi kayi tafiyarka bismillah muje" Baffa ya faWa yanayin gaba ya bishi a baya. Tun daga get Win ya fara jiyo kukan Amal ga muryar Fatiman dukda ba'ajin me take cewa amma yasan masifa takewa yarinyar, a bakin falon ya tsaya Baffa ya shiga ciki yana mata magana tayi shiru se gata kamar an jehota ta fito yanda ta fizgi Ahmad Win badan da idon Baffa ba tabbas seya kwarfeta sannan ya rufeta da duka amma dukda beyi hakan ba seda ya cafki tsintsiyar hannunta cikin tsantar mugunta, ga ihun da Ahmad ya fasa saboda yanda ta firgitashi a baccinsa ga azabar ri?on da yayi mata. A cikin abinda befi sakan biyar ba ya tara mata jini a fata hannu, a kunnenta ya raWa mata

"Ki tabbatar wannan ya zama karo na ?arshe, duk idan kika sake gwada gangancin nan sena nuna miki haukata tafi taki" ya saki hannunta tareda ingizata yanda yasan ba zasu faWi ba ya juya ya fice ba tareda yayiwa Baffa sallama ba dan ransa ya baci da abinda tayi.

Babu kalar Allah ya isan da batayi masa ba sanda ta samu ta lallaSa Ahmad ya koma bacci ta shiga jinyar hannunta da take jinsa kamar ba'a jikinta ba. Shatin inda ya ri?e yayi jajir jini ya kwanta kamar wadda ya Waure da cable, da safe da Umma taga hannun ta tambayeta meya sameta dan daren jiyan da wuri ta kwanta tasha maganin mura ce mata kawai tayi itama bata sani ba haka ta tashi taga hannun.

"Ya zakice baki sani ba, kalli fa se kace wadda aka Waure da igiya?"Umman ta faWa tana sake duban hannun. Idonta ya kawo hawaye, tasan ma idan ta gayawa Umma ba tausayin ta zataji ba ?arshe ta bita da ba?ar magana dan haka tayi shiru.

Jafar kuwa jirgin sassafe yabi zuwa Abuja, ya samu tarba me kyau ya samu daga Fatiyyan kamar zata haWiye shi, yanda ta ringa masa seka rantse ba zata sake Sata masa rai a duniya ba amma yasan sedai idan wata aka canza ba Fatiyyah daya sani ba, wuyarta dai su koma gida ta haWu da Hajiya. Be ?wari kansa ba a Sangaren ba?in data gyara masa Waki suka baje soyayya har seda kowannensu ya gamsu da kewar Wan uwansa da yayi kafin suka kwanta sukayi baccin daya janyo suka rasa jirgin ?arfe Waya da yayi musu booking dan niyyarsa da yaje zasu dawo ne ba zama zeyi ba dole se canzawa sukayi zuwa jirgin tara na dare saboda sa?o da mamanta tace an taho kawo mata daga Kaduna basu zata ranar zasu juya ba da se tace kawai a kai mata can Kanon.

Bayan dogon Jan kunnen da Abbanta yayi mata da gargaWi ya kwasota suka dawo gida, sha biyu ma ta gota sanda suka sauka saboda latti da jirgin yayi dan haka suna zuwa gida bacci kawai sukayi washe gari ma haka ya lalace a gida tare da ita se yamma lis suka fita tare, can gida suka fara zuwa ta gaida Hajiya da ta ringa wani sha mata ?amshi. A can sukayi sallar magriba sannan suka kama hanyar gida. Wayarsa na hannun Fatiyyan ta Wauke su hotuna tana dubawa kira ya shiga. Ta gwale ido tana karanta sunan dake yawo akan screen Win, 'Afeeyah' da jerin emojis na zuciya da ko ita bata samu darajar su a nata sunan ba.

Ashariya me mai?o ta auna ya juya da sauri ya kalleta dan wayar a silent take dan haka besan me ta gani ba, a fusace ya mata tsawa yana cewa
"Wane irin rashin hankali ne a motata kike mun zagi se kace wata yar tasha?"
"Yanzun ko za kaga tashanci ganin idonka Jay, wato duk tsayin lokacin nan daka jinginar dani ashe kana tare da wannan yar iskar mayya karuwar me bin mazan mutane da aurenta, ko kuwa ta kaso auranta ne kun sake jonewa bani da labari?" Ta faWa tana kanga masa screen Win wayar da wani kiran ya sake shigowa. Da sauri ya taka burki, Allah yasa babu wata motar a bayansu da se anyi Satacciya.

Da hannu Waya ya bige nata hannun wayar ta faWi ?asa dukda zafin da taji bata ha?ura ta rarumo wayar data rigada ta amsa kiran ta saka a speaker muryar Amal ta ratsa kunnuwansu tana cewa
"Hello Dady kana ina Momy bata da lafiya kuma Umma bata nan, cikinta ne yakeyin ciwo kuma tayi amai sau biyu" ta kashe wayar yanda tayi maganar zaka fahimci sauri takeyi kar me wayar ta kamata.

"Ashe yau za'ayi abu ta kazan uba Jafar me naji ban gane ba? Cin amanata kake yi Jafar? Dadiro ka ajiye har kuka haifi ya da ita ban sani ba? Fatiyyan ta faWa tana huci kamar wata kumurci. Tsabar yanda ransa yake tafarfasa be ce mata komai ba ya kai hannu ze Wauki wayarsa ta dafe, a zafafe ya sauke mata marin daya saka hancinta fara yoyon jini nan take, ta fasa ihun gigita, ko a jikinsa ya Wauki wayarsa ya saka a cikin aljihu sannan ya taka motar ya shiga fella gudu kamar zasu tashi sama. Daya tsaya a kofar gida tayar har ?auri takeyi ya cire lock Win kofofin ya kalleta idanu jajir yace
"Fitar mun daga mota, kuma wallahil azim kira Waya daga gurin Hajiya igiyar aurenki kenan" ya faWa mata maganar data fi marin Wazu gigitata.


*ASSALAMU ALAIKUM*
*Matan kwarai matab albarka ina gaisuwa. To kunsan dai ba iya shafa mai fata yai kyalli shine cikar kyawun mace ba, a ganki dumur-mur, jiki duk tsoka jiki duk laushi ko ina oga ya kama yaji shi tibis shi ne magana.*

*Ina farin cikin gabatar muku da ingantacciyar SABAYA wadda zata cike miki gurbin wannan ramar ta kuma tabbatar miki da mafarkinki na zamtowa matar sakawa a gaban mota*

*Kiran waya kawai zakiyi ko chat, a tuntubi Maman khadijah mai garin kunun sabaya, tana Palladan anguwan Fulani Zaria Kaduna state tana kuma aika sa?o duk inda kuke a faWin tarayyar Nigeria, kar a manta siyan na gari mayar da kuWi gida*

*Phone no.-08033411249 OR 07037777442*
*MATAR MUTUM*
*NA MARYAM FAROUK (UMMU MAHEER*

*FIKRA WRITERS ASSOCIATION*

*LITTAFIN KUDI NE*
*PAY 500 A ASUSUN*
*7061838488*
*OPAY DIGITAL SERVICES*
*MARYAM FAROUK*
OR
*0709290797*
*ACCESS BANK*
*SE A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488*
*IDAN KATINE A DAUKI HOTONSA A TURA ZUWA LAMBAR SAMA VTU KUMA A TURA A 08142548705*

*Kuyi following dina a Arewabooks @Maryamfarouk01 inda zaku karanta wannan littafin tareda sauran littattafaina*
*NAGODE*

*BOOK 3*
*PAGE 32*

Seda ta kai tsakiyar falonta kafin ta rushe da kuka me tsanani kamar wadda aka cewa mamanta ta mutu, zuciyarta ta shiga ingizata akan ta kira Hajiyar, kurarin banza yakeyi ta laluba sedai gigita tasa bata Wakko jakarta daga motar ba. Ta ringa rusa kuka a ranta tana ayyano yana can gurin Afeeyah, ashe yana tare da ita, shi yasa rayuwar auranta ta?i daidaitar mata yanda take so. Duk uban kuWin da take kashewa a banza babu biyan bu?ata kullum se ?arya malamai suke mata akan zata mallakeshi ze zo hannunta se yanda tayi dashi amma bata ga alamar hakan ba. A falon ta zauna dan bata ji zata iya motsawa ko nan da can ba har se ya dawo sun kwashi tsiyar da zasuyi dan ta rantse ba zata bar maganar ba, duk kuma inda take seta lalubota a wannan karon sunyi faWan ?arshe gara ace rasa shi tayi gaba Waya data zauna wata can a waje tana buga wasan gare gare da rayuwar auranta.

Jafar kuwa cike da Sacin rai ya kama hanyar gidansu Fatiman, yana isa layin yaci karo da abinda yafi wanda ya baro muni da girgiza masa zuciya. Fatiman ya gani wani da be gane ko waye ha ya tarairayota yana ?o?arin sakata a mota yanda ta saki jiki kamar wata matacciya ya bawa wancan Win damar zagaye hannayensa jikinta ya rungumeta gaSa Waya a sharrin idanunsa ma gani ya ringari kamar hannayen mutumin suna mazanunin da bai kama ace sun taSa ba. Cike da bala'i ya juya motar, ya manta a lungu yake babu kuma wadataccen fili kauuu ya fashe bombar tsadaddiyar motarsa da katangar gidan bayansa, be damu ba haka ya gurje motar ya juya ya fice Jafar dake ri?e da Fatima yabi motar da kallo kamar yanda sauran mutane dake zirga zirga cikin layin duk suka tsaya suna kallon ikon Allah ita dai bata ma san me yake faruwa ba ta kanta takeyi haka nan taje taci kwaWon zogale a makaranta gashi ya zame mata masifa tun rana take gudawa zuwa yamma kuma se amai kafin ace me jiki ya rikice ga gida ita kaWai se su Amal da suka dawo daga islamiyya suka tarar da ita Allah ne ya aiko mata Yah Jafar Win yanzun shine ze kaita Asibiti Umma bata nan sun tafi ?auye gaisuwa basu dawo ba.

Cikin gidan Jafar ya koma da sauri bayanya sakata a mota yacewa su Layla su kullo kofa kar kuma su buWewa kowa idan ba Umma ko Baffa ba sannan yaja suka tafi, emergency aka karSe ta aka saka mata ruwa da alluran tsayar da amai dana gudawar se lokacin ya kira ya kira tace ai suna tafiya Asibitin ta dawo ta taho ne ko bazasu jima ba yace ta zauna ruwa ake ?ara mata ba zasu kwana ba.

JAY
Gida ya koma kamar zeyi bindiga ya kama da wuta saboda tsabar masifar dake cin ransa har Waci bakinsa yake masa ya jefarwa da Fatiyyah jakarta a tsakiyar Wakin ya wuce sama harta tashi zata bishi yanayinsa da ta gani yasa ta dakata harya wuce kafin ta dau?i Jakarta ta shige part Winta na ?asan ta kira mamanta. Kuka ta fasa mata, maman ta ringa tambayar ta menene ta?i magana seda tayi me isarta kafin ta iya zayyana mata abinda ya faru
"Momy bakiga fuskata ba wlh har yanzu ina jij raWaWi a gurin kuma ya watsar dani a gida yayi ficewarsa dan ya tabbatar mun karuwarsa ta fini mutunchi wlh bazan yarda muna gama waya zan kira Hajiyar sa sedai kome ze faru ya faru" ta faWa tana sake kecewa da kuka.

Daga can Maman tayi tsaki tace
"Ai wlh bana ganin laifi Jafar saboda irin ?wa?walwar dake kanki dole se ana saita ta lokaci lokaci idan ba haka ba za'a samu matsala ke sa ace wannan uwar tasa ce ta haifeki ma da abin yafi daidai ce ace ke baki da lissafi a rayuwa gaki dai a fuska mace amma kwata kwata a halayya wani namijin ma ya fiki sau dubu yar kissar nan ta mata da kwantar da kai baki iya ba se masifa se zafin rai an gaya miki ko kana asiri seka haWa da kissa da kwantar dakai zakaga biyan bu?ata inda ace irin halin ki nakeyi a nawa gidan ai da banyi tsayin zaman da har zan haifeki ba kinsan dai ubanki ya ninkashi a hutsanci to ki kira uwar tasa ki kaso auranki zaman gidan kike sha'awa gaki gashi nidai bazan sake ce miki ga yanda zakiyi ba Fatiyyah kiyi duk abinda ranki ya raya miki" tana gama faWar haka ta kashe wayar".

Ta sake kira seda tayi mata missed calls biyu sannan ta Waga tana cewa
"Menene kuma? Ina kin gama tsara abinda zakiyi kuma kin gaya mun to kiran da kike sake mun na magani da menene?"

"Kiyi ha?uri Momy wlh baki san yanda zuciyata take tafarfasa ba, Momy Afeeyah fa, har yanzu yana tare da ita kuma wlh Momy har ya suka haifa ashe shiyasa be taSa nuna damuwar sa akan rashin haihuwa ta ba saboda yasan ya ajiye a wani gurin wlh wannan ba maganar da zanyi shiru bace Alhajin su ma ya kamata ya sani ba iya kar Hajiya ba"

"Nace kiyi duk yanda zakiyi ko" Momyn ta sake faWa a fusace cike da takaicin halin Fatiyyan kafin tace
"Ai ba magana kike ji ba, nan kina ganin wahalar da muka sha kafin aka ciyo kansa yazo. Ki jira akawo sa?on da Malam yace ki matsa a jikinki ina kafafunki na rawa kika bashi kanki gashi nan ko awa ashirin da huWu ba'a cika ba kin koma yar gidan jiya to bari kiji muddin ba zakiji magana idan na gaya miki abu ki bi ba zan rabu dake dabararki ta fishsheki ba kuma zan sake asarar kuWi na akan matsalarki ba. Duk kin manta da yanda aka kirashi harya aureki amma tunda kika samu guri baki shuka abin kirki ba se na tsiya to kiyi ta kanki ni na gaji".

Magiya da ban ha?uri Fatiyyan ta ringa mata harta samu ta sakko tace jar tayi komai yanzu ta bari da safe zata kirata ta tsara mata matakan da zasu bi,
"Ki saki ranki kije ki bashi ha?uri yanzu kiyi duk yanda zakiyi ku shirya kome kuma zeyi ki kauda kai, idan komai ya tafi daidai a gaya miki akwai randa ko cewa kikayi ya zagi uwarsa baze musa miki ba. Maza kije ki lallaSa shi ku shirya yanzu zaki jini da safe" Momyn ta jadda da mata. Suna gama wayar ta shiga banWaki tana kallon fuskarta da gefe Waya ya kumbura ba?in cikin da take ji ya sake nunkuwa, ta fasa kiran Hajiya ba kuma zata tunkareshi yanzu ba amma ba abinda ze saka ta bashi ha?uri kuma be mari banza ba zata nuna masa tasan mutunchin kanta yayi na farko kuma yayi na ?arshe da ze sake saka hannunsa jikinta da sunan duka.

Wanka tayi ta gasa fuskar kafin ta kwanta tana sa?e sa?en ta inda zata fara binciko ko wace yar iskace wannan Afeeyar data zame mata ?aya a ma?oshi, tayi murmushi dalilin wani tunani daya zo mata, da wannan farin cikin samun madafa tayi bacci tana Allah Allah gari ya waye ta aiwatar da shirinta ba zata jira Momy ba dan zancen Waya ne Malamin ta zata kira yayi aikin da banda na kiranyen da akayiwa Jafar har Malam ya bata sa'a ta fita a ranar da suka haWu a gurin siyan shawarma har ya kai su ga aure se wannan karon da aka sake yi masa kiranye su kaWai ne aikin da zatace taga amfaninsu duk ubannin kuWaWen da ita da Momyn suke kashewa.

A can Wakin Jafar kuwa yana shiga ya fara fatali da kayan jikinsa kamar wani ?aramin yaro ya rage gajeran wando kawai kafin ya kwanta akan gado dukda sanyin Ac daya cika Wakin amma zufa yakeyi numfashin na neman sar?ewa se kace me cutar asthma. Rufe idonsa yayi hoton Wazu suka fara masa yawo ya buWe ya tashi ya zauna, be taSa sanin yana kishinta ba se yau duk irin yanda yake kore abin daga ransa yana ?aryata zuciyarsa akan duk wani abu daya shafeta a yau ya yarda yaudarar kansa kawai yakeyi. Ji yakeyi inama yana da bindiga yau babu abinda ze hanashi tarwatsa kan ko wane Wan banza ne wannan. Yayi tsaki a karo na babu adadi ya gyara kwanciya, tunani yayi me yasa be taSa jin irin haka idan ya ganta tareda Yah Ahmad ba a baya?

Dukda yanajin wani abu ko a lokutan bayan duk sanda ze gansu tare se wani abu ya tsaya masa a zuciya wannnan abin ne ya hanashi walwala tsayin shekaru, tana yawan faWo masa a rai duk kuma inda yake tunaninta ya riske shi da zarar ya tuna matar Yayansa ce se yaji duniyar ta masa zafi wani abu ya tsaya masa a ma?oshi ya?i wucewa irin abun yaji sanda Salim yace wai yana son ta amma wanda yaji yanzu ganinta da wani yafi kowanne azaba idan da ace ya ?arasa inda suke ya tabbatar baze iya ri?e kansa ba seya aikata abinda daga baya zeyi dana sani.
?arar wayarsa ta katse masa tunani, zuciyarsa ta buga da ?arfi ganin sunanta na yawo a screen, ko ce masa kuma za'ayi ta mutu? Ya raya a ransa. Da sauri ya Waga dukda haushin ta da yakeji muryar Amal cakwai tace

"Dady, baka zo ba gashi har an tafi kaita Asibiti".
"Wanene wannan daya rungume ta ya sakata a mota?" Bakinsa ya furta tambayar kamar

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login