Showing 237001 words to 240000 words out of 467220 words

Chapter 80 - MATAR MUTUM COMPLETED 1-3 BY MARYAM FARUK.doc

23 Sep 2025

12144

yake ?o?arin ganin ta samu cikar muradinta badan haka tasa zuciyar taso ba Umma kuwa ta juya zuciyarta baibai ta?i fahimtarta ta yaya zatace ta zare hannunta daga Al'amuranta? Tana fatan ace barazana takeyi mata saboda ta fasa abinda tayi niyya dan in da gaskene ina zata kama tayaya ma koda ace burinta ya cika na zama matar Jay zata samu farin ciki da nutsuwa alhalin Ummanta tana fushi da ita??
Haka ta raba dare tana koke koke daga ?arshe taci galaba akan shaiWanin da yake neman nesantata daga neman Wauki gurin ubangijinta ta fita tayo Alwala ta ringa jera salloli, a baya koda babu yawa takan tashi tayi sallah ta kaiwa Allah kokenta da bu?atunta amma tun da suka fara raba dare suna zuba sharafin soyayya da Jay shaiWan yayi kinini ya samu abinda yake so. Sanda ya kamata ta tashi tayi sallolin se baccin da batayi da wuri ba da gajiyar data kwasa a yinin su danneta, sallar Asuba ita da take tashin yan Wakinsu ya zama yanzu ita ake tashi duk free time da take zama ta jaddada kusancinta da mahaliccinta soyayyar Jay ta cinye yau da duniyar ta mata zafi ta ko ina gashi take karSa dole ta fuskanci mai duka ta kai amsa kukanta.

A baya takan yawaita addu'ar neman zaSin Allah a cikin lamuran rayuwarta gaba Waya, yanda Ahmad ya kasa samun matsuguni a zuciyarta duk kuwa da tarin kyawawan halayensa yasa kawai ta yankewa ranta ba Alkhairinta babe shiyasa ubangiji be haWa zuciyoyinsu guri guda ba, da Jay ya afko mata yanda ya shiga ranta farat Waya nan kuma ta yanke shine cikar burin datake jira Allah ya aiko mata. Bata nemi zaSin Allah ba kawai ta yanke shiWinne kamar yanda bata nema akan Ahmad ba ta yanke bashi bane.

Ance ba'ayin aure salin alin amma kuma bata tsammaci auran da ze saka ta samu tangarWa da iyayenta ba ze zamo Alkhairi a rayuwarta ta yaya ma haka zata faru?? Umma tace ta zare hannu a al'amarinta ta ina zata ga haske a gidan Jay?? Toh amma idan ta ha?ura dashi yaya rayuwarta zata kasance? Ta tabbatar babu ita babu farin ciki a gidan auran da ba Jay bane ze kasance Mamallakinta, shi take So, shi zuciyarta ta aminta dashi amma kuma Albarkar iyayenta nada muhimmanci da tasiri a cikin rayuwar da zata gabatar tare dashi.

Ta ringa jera sallah tana kuka wiwi tareda kwashe mintoci masu yawa a sujjadarta tana kaiwa Allah kokenta da neman agajinsa a wannan siraWi da take kai, seda taji sallar Asuba kafin bacci ya kwasheta bata jima ba cikin baccin ta ringajin ?arar wayarta data ajiye dabda kanta bayan ta duba lokaci kafin baccin ya kwasheta. Tayi firgigit ta farka, mafarki take wai Jay yazo a fusace ya Waga hannu ze kwasa mata mari be kai ga aiwatar da nufinsa ba ta farka tana zare ido, akan me Jay ze mareta a mafarki? Koda yake da fushinta ya tafi jiya ?ila ya huce ne shine ma yake kiranta yanzu da wannan tunanin ta janyo wayar da azama ta duba.

Sunana Ahmad ta gani da manyan ba?i suna yawo a kan wayar, ta ringa maimaita sunan a ranta tamkar ranar ta fara ganin kalmar.
"Allah ka haskamun abinda yafi zama Alkhairi a rayuwata, Allah karkasa aurena ya zama silar gamuwata da mahaifana" Addu'ar data ringa nanatawa a sujjadarta tana bin bayanta da sunayen Allah tsarkaka tare da cikakken ya?inin samun biyan bu?ata. Ahmad da ta manta rabon da suyi magana a waya dashi tun kafin dawowar Jay kamar tun ranar da Anty Sauda ta tilasta mata kiransa ta bashi ha?uri shine yake kiranta yau da farar safiyar nan?

A maimakon ta amsa wayar se kawai ta kifeta ta fashe da kuka kamar wadda aka mara ta ringayi harda shashshe?a shi kuwa kamar yasan meke faruwa ya ringa kira har seda ta amsa ba tareda ta bar kukan da takeyi ba.

AHMAD
A gigice ya mi?e tsaye bayan da Fatima ta amsa wayarz kira uku ya mata kafin ta amsa ana huWun ya raya a ransa bacci takeyi amma kuma abinda yakeji a ransa game da ita yasa ya kasa ha?ura da kiran har seda ta amsa.
"Lafiya Fatima, meya sameki? Meya faru kike kuka?" Ya jera mata tambayoyi a rikice, daga can gefen ta sake kecewa da kukan daya fi na farko ba tareda ta bashi amsa ba, ya wuce ya buWe wardrobe inda Jallabiyyunsa suke yake dubawa da alamu ya manta da wata a jikinsa saboda ruWewa

"Dan girman Allah ki faWamun meya faru? Me yasa kike irin wannan kukan?" Ya sake faWi yana zaro riga ya shiga kici kicin sakata akan ta jikinsa.

"Bani da lafiya, ?irjina ciwo yakeyi" ta faWa tana jan numfashi kamar zata shiWe, yaja salati ya dire kafin ya saki rigar hannunsa ya nufi ?ofa se kuma ya dawo da sauri ya shiga jijjiga Jay da tun fara wayar daya ambaci sunanta ya kasa kunne yana jinsa dan baccin nasa beyi nisa ba.
"Meye kuma?" Ya faWa yana mi?a kamar sannan ya tashi. Ahmad ya latse wayar ya kashe kafin yace masa
"Ka tashi muje, Fatima ce bata da lafiya"
"Alhamdulillahi Allah yasa ta mutu kowa ya huta" Jay ya faWa kafin ya juya abinda ya kwanta harda jan Duvet ya rufe har kansa. Ahmad yayi kasa?e yana kallonsa kafin kuma ya tuna abinda yake gabansa ya sauke ajiyar zuciya me ?arfi ya fice.

Dake safiya ce ko bakwai batayi kuma ana hutun makaranta dan haka babu cinkoso akan titi nan da nan ya isa unguwarsu Fatima. Ko buWe We ?ofa basuyi ba ko kuma sakayota akayi oho ya niyyata ze buga kenan ya hango Baffah yana tahowa da carbi a hannunsa da alama sannan ya fito daga masallaci.

Mamaki bayyane akan fuskarsa yake kallon Ahmad sanda ya dur?usa yana gaisheshi dan daga nesa be gane shi bane ko kuma be kawo ze ganshi a irin lokacin bane yasa be kawo shiWin bane.

"Fatima ce na kirata tana kuka tace mun bata da lafiya" Ahmad ya bawa Baffah daya tambayeshi ko lafiya ySa ganshi yanzu amsa. Baffah yayi shiru kafin ya tura ?ofar yayi ciki yana ce masa
"Bismillah"
"Aa Baffah ta fito muje Asibiti kawai kar a Sata lokaci" ya bashi amsa kai a ?asa. Baffah ya shige ciki ya tarar da Umma a tsakar gida tana yan kaye kayenta.
"Ina Afeeyah?" Ya tambayeta, ta nuna masa Wakin Afeeyar da hannu dan haushinsa takeji seda suka tafka mahawara jiya kafin sukayi bacci. Wai ya bawa Jafar sati biyu ya turo, data tambayeshi yasan shi ne ko yayi bincike a kansa da zece ya turo maganar aure sati biyu se yace mata

"Banji a jikina yaron nan ze aureta ba koda yana sonta shiyasa nayi musu haka kinga daga ita harshi babu wanda zece an tauye masa ha??i. Yace sunan mahaifinsa Abdullahi Tijjani ?an kasuwane kuma a unguwar Hotoro suke zaune zan sanarwa Malam Saminu seya bincika shine me mutane a shiyyar dan binciken Ahmad ma kinga shi yayi"

"Lallai Malam, wato bakaji a jikinka auranta zeyi ba? To idan kuma ya ?aryata jin naka ya turo magabatansa se ayi yaya?" Umman da mamaki ya cikata fal ta faWa Malam ya sake tamke mata kai daya ce
"Ru?ayya, duk wanda yake shine Alkhairi a gareta Allah ya tabbatar mata, Allah yaga zuciyata, idan son rai na ne Ahmad shi ze zama Mijin Mamana amma tace ba haka ba, bazan mata dole ba zan cigaba da bibiyar lamarinta da addu'a Allah ya zaSar mata wanda yafi Alkhairi a cikinsu". Tsabar yanda ya kasheta da mamaki yasa ta gagara ce masa komai se kallonsa da ta ringayi, wato baze mata dole ba
"Ai shikenan" ta faWi ta maida kai ta kwanta ranta fal da mamakin Malam Hafizu. Da sanin yau ta masa se tace kwaWayin matsayin sabon yaron da Afeeyar ta kawo ne ya jashi to amma idan Arzi?ine a Nigeria dai ai ba'a gayawa Audu Bechi uban Ahmad ba. Ta yuwu makauniyar soyayyar Uba da Ya ce tasa ze zama sullutu ya biyewa Afeeyar ta mayar dashi ?aramin mutum. Ta raya a ranta zata saka musu ido shi da yar tasa ne taga gudun ruwansu ba zata sake cewa komai akai ba, da wannan haushin ta kwana shi yasa da safiyar da yake tambayarta ina Afeeyar ta masa nuni da Wakinta kawai taci gaba da sabgar gabanta.

Baffah ya kada baki ya kira Afeeyah dake kwance wurjajan tana kuka jin daWi, yo jin daWi mana babu duka babu zagi mutum ya ?ule a Waki yana kuka ai se wanda daWi yaiwa yawa. Ta amsa tana goge hawayenta kafin ta fito tana kare fuskarta da Hijabi. Saboda karma Umma taji abinda ze hasalata yasa ta shigi kitchen ta basu guri, tana jin Malam na tambayar Afeeyah me yake damunta?
"Ahmad na tarar a waje yace kunyi waya yanzu kince masa baki da lafiya meya sameki" inji Baffah. Ta kalleshi da mamaki tana maimaita "Ahmad kuma?" A fili yace
"Eh shi, ko bakuyi waya ba"
"Munyi, amma ai bace masa nayi yazo ba kuma ni lafiya ta ?alau" ta faWa a sanyaye.

"Se kije ai ki sallameshi gashi can duk hankalinsa a tashe, wlh yaron nan tausayi yake bani Jarabta a so babban abu ne me wahalar gaske" Malam ya faWi yana wucewa Wakinsa Umma data fito da tukunya zata tari ruwa a famfo ta koma kitchen ba tareda ta kalli inda take bama ita kuma Afeeyah tsoron abinda Umman zatace ya hanata tashi daga inda take har seda Malam ya sake mata magana.
Ahmad na jingine da ?ofar gidan, daka ganshi kasan yana cikin damuwa duk yayi wani iri yanajin an taSa ?ofar ya juya da sauri sukayi ido huWu.

Gabanta ya yanke ya faWi ba tareda wani dalili ba, kai a ?asa kamar wata farin shigar munafurci ta gaishe shi,
"Muje Asibiti Fatima me yake damunki?" Ya faWa yana matsawa gabanta. Ta girgiza masa kai idonta na tara ?walla tace
"Ciwon kai ne daman kuma ya sauka"
"Ciwon kan kikewa kuka haka Fatima? kalli fa yanda fuskarki ta koWe yanayinki ya nuna ba lafiya ba sannan kice ciwon kaine kuma ya sauka" Ahmad ya faWa yana ?are mata kallo.

"Dagaske nakeyi maka ciwon kaina yana da zafi sosai har nakan gwammace nayi zazzaSi akanshi"
"Kinga kenan kina bu?atar Dr's attention dan haka muje Asibiti kawai"
"Dagaske na warke nasa magananin da aka bani akan duk sanda ya motsa mun nasha Migraine ne" ta sake faWa cikin tabbatarwa. Se tayi murmushi kallonta yace

"Kodai biko na kikeyi shine kika fake da ciwo saboda ki tasoni ko ban shirya ba?"
Tamkar tace masa tayi bikonsa a saboda me se kuma tayi shiru tana wasa da yatsunta murmushi ya kwafsa mata ta hanyar sakin kansa ba tareda ta shiryawa hakan ba. Ahmad yayi murmushi yana gyara tsayuwarsa yace

"Duk sanda nafara fitar da rai da tsammanin samunki se Allahya kawo silar da zata sake maido ni rayuwarki bakya ganin hakan bayinmu bane yin Allah ne? Ta yuwu akwai wani tanadi da yayi mana amma zukatanmu na nesan tamu da riskar wannan tanadin akan lokaci?"

Bata ce komai ba be kuma damu da hakan ba yaci gaba da cewa
"A yanzu na rigada na buWe zuciyata, na sallamawa Ubangiji komai dukda dama a kullum cikin mi?a lamurana a gareshi nake. Tunda kince lafiyarki ?alau bari naje gida, se wani lokaci" be jira komai ba ya wuce ya barta a tsaye. Jiki ba laka ta koma ciki ta dasa jiran tsammanin samun kiran Jay amma har Azahar shiru babu shi babu labari.

Ahmad kuwa bayan ya koma gida ya tarar da Jay na shiri daya tambayeshi ina zeje yace masa Kaduna daga can ze wuce Abuja gidan Hajiya ?arama. A ta?aice yayi masa bayanin da Hajiya ta masa jiya, Ahmad ya jinjina Al'amari, Allah kenan me mutane iri iri. A haifi mutum amma tsabar shahara yace shi baze haifi wasu ba to Allah ya rufa asiri. Be ce ze bishi ba kamar yanda shima be nemi rakiyarsa ba za'a iya cewa wannan shine karo na farko da hakan ta faru ace Jay zashi wani guri ba taredaya nemi rakiyar Ahmad ba. Tareda Manager shi suka tafi shi kuma Ahmad bayan ya shiga gida sun gaisa da Momy da sauran mutane ya tafi Shago duk yanajin babu daWi. Tabbas akwai abinda yake damun Jafar, amma menene wannan da har ya gagara tattauna matsalarsa dashi?

Jiyayaje gidansu wacce yake so basu samu sunyi magana ba balle yaji yaya sukayi tunda kafin ya shigo shi yayi bacci da safe kuma ya fita to kodai shima ya samu matsala irin tasa ance ya dakata ko kuma ma dai iyayenta sun rigada sun mata Miji? Tunanin da Ahmad ya ringayi kenan yana zaune a office Winsa. Ya Wauki wayarsa ze kira Jafar sega kiran Fatima ya sake shigowa wayarsa. Mamaki kamar yayi me, Fatima dai yau meya sameta haka acw a rana da kanta ta kirashi har sau biyu wannan abu kamar Almara. Be sake rushewa da mamaki ba seda ya amsa bayan sun gaisa take tambayar ya yaje gida sannan ta bashi ha?urin tayar masa da hankali da kuma fito dashi da sassafe daga nan sukayi sallama dan ya gagara sakin jiki yayi mata wata ?wa?warar magana.

Allah sarki zuciya da abinda take so, Wan wannan kiran yasa duk ya rikice ya cigaba da Wora lissafin gobensa da Fatima, daya tashi daga Shagon da?yar ya kanne ya wuce gida dan zuciyarsa nata uzzura masa da ya sake zuwa ya ganta ya kumayi mugun ?o?ari da be kirata ba. A daren Jay ya dawo, se yaga kamar sanda ya tafi yafi nutsuwa da kwanciyar hankali akan dawowarsa duk ya wani birkice kuma bece masa komai ba still shima ya kama bakinsa be tambayeshi ba.

A Sangaren Afeeyah kuwa abu kamar almara haka aka wuni sur tun tana zaton Jay ze kirata harta fitar da rai ta shiga lalube da lissafin yanda rayuwarta zata kasance idan har da gaske Jay ya barta. Ta kirashi sau biyu wayar ta ?araci ringing ba'a amsa ba kuma be biyo baya ba har dare, A Waki ta wuni, sunyi Chat da Badar bata Soye mata komai ba akan zuwan Jay na jiya, yanda sukayi da kuman zuwan Ahmad da safe harma da Stand Win Umma akansu biyu

"Allah na sonki Afeeyah, karki bari ki rasa damar da kike da ita a hannu wlh ba zaki maimaira kamarta ba. Bakoda yaushe abinda muke so a rayuwarmu yake zama Alkhairi ba haka kuma ba duk abinda muke ?i ne yakan zama sharri tare damu ba. Kiyiwa kanki karatun ta nutsu ki kalli gidajen aurayen da suke a zagaye dake wanda akayisu cikin daWin rai da sahalewar uwa da uba amma ba'a rabasu da ?alubale da matsaloli inaga wanda akayi kan doron fushin iyaye? Yanzu ke zaki iya zaman aure da Mijin da mahaifiyarki ta nuna bata sonsa? Bana tsammatar zaki samu cikakkiyar nutsuwa balle kwanciyar hankali nidai irina wlh ko Yan gidanmu ne suka nuna basa son mutum muddin suna da hujja me ?arfi zan ha?ura dashi saboda su dai dasu zan tattauna duk wata matsala da ka iya tasowa idan babu goyon bayansu ina zan kai kukana?

Kina gani dai kina zaune Allah ya sake turo miki Ahmad a lokacin da abinda kike ?ulafuci yake ?o?ar bari hannunki, idan kika sake kikayi wasa da damarki tana iya zama ta ?arshe dan haka kiyi tunani kuma ki tattaro ki dawo School ki fuskanci karatunki semester ?arshe muke karki bari kiyiwa kanki sawarwarar da zaki samu matsala a wannan lokacin tun wuri ki saki komai ki sake kama Allah ki kuma bar komi a hannunsa" abinda Badar ta gaya mata kenan da har yasa ta samu ?warin guiwar sake kiran Ahmad.

Jay be kirata ba se washe gari, idan kaga yanda ta fita a hayyacinta seka zata ciwo takeyi kwana guda kawai amma ji take kamar ta shekara ba taredashi ba faWar irin zafin da takeji a zuciyarta kuwa Sata lokaci ne, ashe haka Ahmad yake ji akanta shima? Tabbas So abune me ciwo da wahalarwa ta yarda yanzu da ta afka masa kuma ta dena ganin baiken masu zaucewa a soyayya domin ita kanta a yini Wayan nan da takejin kamar tayi bankwana da farin cikin rayuwarta badan tsoron abinda ze je yazo ba ware baki zatayi tayita kwarara ihu a Waki harse nauyin da zuciyarta tayi mata ya ragu amma bata isa ba Umma zataci mata uwa da uba ne tabbas a gidan shiyasa sedai ta lafe a Waki tayi kuka ta share hawayenta.

Tana tsaka da shirya kayanta dan ta himmatu gobe zata koma makaranta kafin ba?in ciki yayi Ajalinta a gidan babu jimawa sun gama magana da Ahmad dukda ba qata magana me tsayi bace ba shiya kirata yaji ya take idan babu damuwa zezo Anjima da anyi Magrib tace masa Toh shikenan sukayi sallama. Tana zuge akwati wayarta tayi ?ara ta zabura jin Ringing tune data sakawa Jay ne. A tare suka sauke ajiyar zuciya bayan data amsa wayar kafin ya kira sunanta a sanyaye bata amsa ba se kawai ta sakar masa siririn kuka daya saka ya mi?e tsaye daga kwancen da yake babu shiri

"Kuka kuma? So kike ki ?aramun damuwa akan wadda nake ciki?" Ya faWi cikin yanayin daya saka Ahmad dake cin abinci kallonsa. Basu jima da dawowa daga gidan Baba Al?ali ba koda yake Jafar ya Wakko acan besan ma yaje ba seda ya kirashi yace ya biya dan Alkah su taho tare suna shigowa kuma ya wuce gurin Momy ya karSo abinci shi Jafar yace Azumi yakeyi seda suka gama magana da Fatima kafin ya fara cin abincin.

"To ba kaine ba tun da ka tafi baka waiwayeni ba" ta faWa cikin kuka. Seya koma ya zauna yana cewa
"Kinyi mun laifi, baki kirani kin bani ha?uri ba and you are expecting me to call you kenan baki san girman lafin da kika aikata ba ko?"

"Na kiraka jiya sau biyu baka amsa ba" ta bashi amsa tana tsagaita kukanta se yace
"Jiya, wato baki damu ba na tafi cikin fushi, baki kirani tun a darenba se jiya shima da rana saboda kin lura ina sonki"

"Wlh ba haka bane ba, kai kace na cire layina daga waya na cire se da safe na samu ?arama na saka layin a ciki"

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login