Showing 114001 words to 117000 words out of 467220 words

Chapter 39 - MATAR MUTUM COMPLETED 1-3 BY MARYAM FARUK.doc

23 Sep 2025

12118

tunamun gobe idan Allah ya kaimu zanje na dubo su Hassan dukda dai nayi musu aike cikin satin nan amma gara naje na ganosu da kaina" Audu ya fada dan maganarta ta qarshe yasan da Zubaidan takeyi aiko abinda ya fada ya doketa har seda ta kware da Zobon da take sha ta ringa tuttula tari yana mata sannu dakyar ya lafa mata ido yayi jajir ta ringa maida nufashi zuciya na tafarfasa.

*MAMAN MARYAM ONLINE BUSSINESS*

*Ina kuke Mata Yan kwalisa , Ina nufin isassun Mata ,Wai shin Kuna da labarin shahararren company nan namu na GHT wato good healthtreatments*
*Wanda yazo muku da fitattu Kuma* *ingantatattun suppliment ,na dukkan matsalolin ku*S'

*Ina maisan tayi kyau,irin na isassun Mata ya fitar Miki da shef dinki tayi Miki gyara in and out ,nemi royal jelly dinmu na company GHT*
*Wanda aka yishi da xuma ,kundai San amfanin Zuma basai na fada miku ba , hajiya ta kixo ki Yi gyara domin ki kerewa sa,a kije taro ko baki da ko sisi kiji Ana rangada Miki hajiya , saboda yanda Zaki Kara kwarjini ,kina walwali acikin mutane , magungunan ght anti agen ne suna maida tsohuwa* *yarinya ,yarinya Kuma ta koma jaririya*


*Muna da magunguna iri iri*

*NA GYARAN JIKI*
*NA GOGE NANKARWA*
*NA RAGE QIBA*
*NA CIRE TUMBI*
*NA QARIN HIPS*
*NA GIRMAN BREAST*
*NA QARA TSAHON GASHI*

*NA QARIN NI'IMA WANDA ZAI SAUKAR MIKI DA NI'IMA YA QARA MIKI DADI DA ZAQI A GURIN OGA*

*Muna da hadin bita zai zai ,indai kishiyar ki tana Shan magungunan GHT, tohh lallai sunan ki sorry domin kuwa tazarar dake tsakanin ku kamar tazarar sama ne da kasa*

*Muna da Wanda zai matseki ciki da waje Andai na yayin dinki uwargida*,

*Sannan company mu na GHTBai tsaya anan ba*
*Ya kawo muku maganin dukkan matsalolin ku*

*INA MASU HAWAN JINI?*
*INA MASU CIWON ZUCIYA?*
*INA MASU CIWON QODA?*
*INA MASU CIWON HANTA?*
*INA MASU SICKLER?*
*INA MASU HIV?*
*INA MASU CANCER?*
*INA MASU NEMAN HAIHUWA?*

*Tohh Ku matso GHT taxo muku da magungunan matsalolin ku*
*Kuma muna da testimonys da yawa ,na wadanda suka gwada suka da ce*

*Munanan a KANO KUNTAU*
*Kuma muna tura Kaya ko wanne gari cikin aminci da gaskiya , kuma kayan mu muna badashi ne cikin price Mai rahusa ga kyau ga inganci sannan ga Rahusa*

*Kutuntube mu ta wannan number =???08129249549*
*=???07011401314*

"Sannu bari na shiga ciki nayi wanka kafin ki gama" ya fada mata bayan da tarin ya lafa mata ya shige daki tabi bayansa da harara tamkar idanunta zasu zazzago. Tashi tayi ta hau tattare kwanuka ta sauka dasu zuciyarta fal da tunani, Wannan shi ake kira goma da Ashirin abu na nema ya hade mata biyu bata gama da wannan yar qauyen ba ya maido mata da zancen Zubaida ashe har aike yake musu yana kuma zuwa ya gansu?
Koda yake itace sakarya data manta da ita gaba daya matsalar Bara'atu tasha mata kai ta manta da batun tsinannun Tagwayen can data haifa to yanzu ita ina zata kama? Bara'atun zata bari ta koma kan Zubaida? Ko kuwa bari zatayi seta fatattaki Bara'atu sannan ta dira kan Zubaidar?

Tana hada abubuwan da zatayi amfani dasu a dakinsa take wannan lissafin a ranta, ta gama ta dauki ledar data zuba kayan, Nazirun na saman har yayi bacci Zakariyya kuma dasu Babangida zasu fita ya bisu yanzu da bata gama yanke yanda zatayi da Bara'atun ba tana bar mata yaron ya kwana da yan uwansa ranakun girkinta dan haka ta rufe qofarta ta koma Saman Audun tana ayyana matsalar Bara'atu zata fara kaudawa, zata bar Zubaidan tukunna dan tata me sauqi ce take ganin.

"Wai ni watannin Yan biyun nawa nawane yanzu?" Ta daure ta tambayi Audun bayan sun kwanta, ya danyi lissafi akansa kafin ya kalleta yace
"Kamar Goma kenan ko? Ki lissafa tafiyarki Hajji yanzu watan sama kwanansa goma Azumi saura kwana Ashirin ko sha tara kinga a wata na Tara suke sun shiga na goma"

"Haka ne" ta fada daga nan ta maida kai ta kwanta tana ayyana dole ma ya karbosu sannan ya nemo me masa hidima dasu yawwa. Haka dai tayi baccin daren babu nutsuwar zuciya, tunanin yanda zata qulla can ta rushe can kawai takeyi, tana jinsa yana jan minshari hawaye ya silalo mata, kamar ta zabga masa mari taji, duk akansa take wannan fadi tashin.

BARA'ATU
Washe gari da Audu ya fito ze tafi Kamfani ya shiga yi mata sallama bayan sun sake gaisawa bayan wadda sukayi da Asuba, cikin risilama ta maido masa da maganar jiyan saboda tace tana da magana idan ya dawo yace ta fada sannan babu damuwa.

"Se naga kamar dakunanmu sirrinmu ne sannan gyaran daki akwai wanda zakaga yafi so yayi da kansa yafi ganin komai yayi masa daidai kamar dai ni, shiyasa zakaga ko dakinka duk sanda nake ciki se na sake gyarawa koda ace Maman Zakariyya tayi gyaran dan bana jin komai ya mun idan ba da kaina nayi ba" Bara'atun ta fada masa da yanayin da take ganin ze fahimta. Ya ringa jjjiga kai irin ya fahimce ta din nan sannan yace ze yiwa Bintan magana.

Seda da dare bayan ya dawo ya ya gama cin abinci ya sanarwa da Binta yanda sukayi da Bara'atun, daman tasha kwanan baqin ciki da yinin takaici dan zancen Zubaida da yayanta ya maqale mata a zuciya yaqi wucewa duk haka ta wuni babu walwala qyashi da hassada ya cikata ta ringa hasaso abinda Audun yake kai musu waya sani ko itama gidan ya gina musu irin nasu Bara'atu tunda itama a gidan Laka suke ga Damuna kar yace ze rufto akan Yayansa.

Seda ta gama sauraron Audun tsaf kafin ta narke fuska ta samu mafaka abin kuma yazo a daidai yanda take so dan haka tace
"Ka ga magana ta ta fito ko? Jiya mena fada maka? Ai nace maganar batayi mata ba tayi shiru me yasa tuna gurin ba zata fadi nata ra'ayin ba se dai ta jaka gefe ta gaya maka, yanzu ai se aga kamar cutarta nakeyi shiyasa ba zata yi magana a gabana ba. Ni ina so muyi zaman lafiya da ita amma kaga abinda ta bullo dashi a taqaice dai tana nufin ni qazama ce banida tsaftar da zan iya yi mata gyaran daki ashe duk wanda nake maka ma in tazo seta sakeyi shikenan tunda haka ta zaba se mu zuba mu gani nida ita aga wanda ze sare in har tashin hankali take neman kai ka sani na iyashi wlh banda ma Allahya doramun qaunarta da son muyi zaman lafiya da ita meye ze hadani da wata Bara'atu ka bata labarin yanda muka gwabza da Gogaggiyar Karuwa ma balle ita karan kada miya" nan ta fara qoqarin tayar masa da Jidalinta.

Audu kuwa yaji dadin zaman lafiya baze so abinda ze tarwatsa masa kan gidan daya fara haduwa ba kuma se yaga zancen Binta gaskiya ne Bara'atu bata so ayi zaman lafiya shiyasa zata bullo da wannan maganar inda taso ayi yanda Bintan tace in yaso duk abinda yayi mata badaidai ba ta gyara daga baya baki alaikum.

"Yanzu dai kiyi haquri, zanyi mata magana babu wani tashin hankali ko rigima daze bullo a gidan nan zaku cigaba da zamanku lafiya yanda kuka fara" Audun ya tausheta, se ta fara magana kafinta kai qarshe ta saki kuka tana cewa

"Ni idan zan fada maka wani abu daya shafeta ai a gabanta nakeyi bana munafunci me yasa ita se a gefe zakuyi magana ta da ita? Allah kadai yasan me take gaya maka akai na shiyasa naga kwanakin nan duk ka canza mun kuma ko rantsuwa nayi bazanyi kaffara ba waccen me kama da Zabiyar ta gidan Yakubu ce ta zugota zuwan da kukayi to nidai tunda naga alamun hade mun kai zakuyi tunda ita yar garinku ce ni kuma bare gara nasan nayi tunda sauran mutunchina kafin ka kunyatani ace qaramar Yarinya ta koreni daga gidan Miji"

"Wace irin magana kikeyi haka Binta? Daga zancen shara seki fara sako wani soki burutsu meye wannnan? bana son irin haka kin sani ko? Bari na kirata to tazo ayi maganar a gabanki zan yanke hukunci kuma dole kowa yabi abinda nace" Audun ya fada yana miqewa se ta tareshi da cewa

"Hukuncin me zaka yanke? Bayanta zaka bi ko?"
"Se ki jira kiji tukunna" ya bata amsa fuuuu ya wuce kiran Bara'atu. Da gudu Binta ta shige bandaki ta wanko fuska tana qyalqyala dariya, ta gama tsanewa ta murza hoda da Gazal kafin ta ware dankwalinta ta gyara daurin tayi fes abinta kamar ba ita ta gama kuka yanzun ba.

Bara'atu na zaune da yara Abdullahi ne yace su kwaso Littattafansu a duba saboda an kusa komawa makaranta saura sati daya. Ba sanin abinda sukeyi tayi ba dan haka tana zaune kan Kujera kawai tana kallonsu tana kuma kwabar wanda taga ze bata littafinsa da zane musamman Zakariyya da ya fiya qiriniya se qoqarin batawa Yayyen littafi yakeyi da fensir Audu ya fada dakin sallama ciki ciki yana muzurai.

"Ina son magana dake" ya fada ya juya, tabi bayansa da kallo kafin ta miqe a sanyaya tana tunanin to meya faru kuma? Hijabi ta dora kan Baqar doguwar rigar jikinta ta bi bayansa, shi kadai ta tarar a falon se Naziru dake ta rarrafe a qasa ta daukeshi ganin ya nufi qofar da bata rufe dakyau ba ta zauna kan kujera tana masa wasa yana dariya, satar kallon Audun tayi taga ya tamke fuska yana muzurai zatayi magana kenan Binta ta fito daga daki tana masa magana ganinta yasa ta katse tace

"Au kece? Yau kinzo hira da kanki kenan ba tare da an kiraki ba"
"Uhm" kawai Bara'atu tace kafin ta gaisheta ta amsa tana zaunawa tana sake cewa Audu
"Kaga abin mamaki yau Bara'atu tazo hira damu"
"Ni na kirata" ya fada fuska a daure qasan ransa yana mamakin yanda tayi kamar bata san yaje kiran Bara'atun ba,

"Koda naji, nidai nasan badai Bara'atun dana sani ba" ta sake fada. Audu ya gyara zama yana kallonsu duka yace
"Na gayawa Binta saqonki sedai bataji dadin abinda kika fada ba kuma kamar yanda ta fada abinda kika bullo dashi so kikeyi ki ruguza mana zaman lafiyar da muka fara samu a gidan nan dan haka ni a matsayina na wanda ya ajiye ku duka zan yanke hukunci, kamar yanda muka tattauna jiya magana tana nan zaku ringa ayyukanku kan yanda muka tsara babu wani ja inja ba kuma nason na sakejin wata magana daga kowanne bangare".

Abin be wani bawa Bara'atu mamaki ba domin tasan za'a rina wai an saci zanin Mahaukaciya wannan ba sabon abu bane a gurinta kuma yanzu ta tabbatar da zarginta na cewar Binta na nan kan halinta babu abinda ya canza kuma nemanta takeyi da sharri shiyasa ta kawo wannan tsari to amma ba zata zauna ta zama sakarya ba a wannan karon ma, dole ta fadi ra'ayinta koda kuwa Audun zeyi masifa bazata yarda taci gaba da zama yar amshin shata a gidan ba.

Ta kalli Binta dake murmushi tana lada qafa kafin ta fara magana ba tareda ta kalle shi ba tace
"A gaskiya kayi haquri nidai na yafe sharar dakina zan ringayin abata da kaina kuma ina roqar Alfarmar itama ka daukemun ta dakinta, na yarda ta canza mun da wani abun daban da zan ringayi mata amma banda sharar daki"

"Yanzu Bara'atu har kinyi kaurin wuyan da zan fadi magana ki musamun ni zan zartar da hukunci a gidana kice ba haka za'ayi ba?" Audu ya fada a fusace cikin tsawa yana kallonta, bata son fada sannan ya za'ayi a tauyeta kuma tayi magana ya nuna ta masa rashin kunya dan ta nemi haqqinta wannan ya karya mata zuciya Kwalla ta taran mata a ido amma ta kasa magana dan tana bufe baki tasan kuka zata saki, Binta da taji kamar ta taka rawar murna ce ta katseshi da cewa

"Haba Yallabai, haba ranka ya dade Allah ya huci zuciyarka ungo karbi ruwa kasha" ta miqa masa ruwa be karba se huci yake yana hura hanci ta sake marairaicewa tana cewa

"Haba mana Sadauki ni banga abin bacin rai a maganar nan ba kowaccen mu fa tana da damar da zata fadi ra'ayinta shiyasa tun jiya naso ta bude baki ta fadi abinda yake ranta take yanke da bamu zo yanzu ana bacin rai ba amma dukda haka daman maganar nan nina kawota tunda kuma a maimakon samun daidaito tana nema ta haddasa fitina na janye, zan saka a nemo mun wata me aikin kawai taci gaba da taimaka mun itama idan tana so a samo mata in kuma bata so taci gaba da aikinta yanda ta saba shi kenan magana ta wuce kowa yayi haquri".

"Bata isa ba wlh ita tayi kadan ta kawo mun tsarin da zanbi a cikin gidana yanda na tsara haka za'ayi" ya sake fada a zabure, Bara'atu ta kalleshi, yanda yake magana tamkar shiya kawo dokar tun Asali kamar ba Shirin Bintan bane ita ta kawo nata tsarin ya hau ya zauna ita kuma da bada sadaki ya aurota ba saboda ana so ayi mata rashin Adalci taqi shine yake wannan kumfar bakin.

"To bari na nemi alfarma, tunda tace abar mata sharar dakinta zatayi ni kuma nawa na canza mata da wani aikin ka barmu mu sasanta a tsakaninmu mana" Binta ta sake fada kamar da gaske sasancin take so ayi. Yayi shiru kamar baze tanka mata ba kafin kuma murya a dake kamar ta Boss yace
"Ina jinki".

"Yauwa Nawan, yau akwai tukuici na daban ladan wannan Alfarmar daka mun" seta juya kan Bara'atu tace

Bara'atu da taja Hijabi ta rufe fuska dan ta kasa riqe kukan daya zo mata qasa qasa takeyinsa tana share hawaye wato dai ranakun baqin cikinta basu qare a gidan Audu ba, maidota yayi ya qara sauke mata buhun hunan rashin mutunchin da be ida sauke mata a baya ba, da sauri ta dago kai jin abinda Bintan take cewa

"Kin ga ya dage dole mubi tsarin da aka kawo da farko amma tunda kin nemi a canza, idan kin yarda ni a bangarena a maimakon sharar dakina zaki ringa yimun Wankin kayan Yara ke ma seki fadi abinda zan ringayi miki a madadin taki sharar" ta qarasa tana doka murmushi kamar wawiya.

Kasa cewa komai tayi, ta kalli Bintan kafin ta kalli Audu tana jiran taji abinda zece se ji tayi yana cewa

"Babu maganan ta zabi abinda zaki mata, sharar dakinta ita tace ta yafe kar kiyi na dakinki kuma wannan da ba zatayi ba kika musanya mata" ya juya kan Bara'atu da tayi fakare tana sauraronsu yace
"Zaki ringayi mata wankin kayan yaran duk ranar da baki da girki, My decision is final" aka jefo turanci daga nan ya shige daki ya barsu zaune.

"Yanzu wasan ya fara yarinya" Binta ta fito mata a sak ta fada kafin ta miqe tana juya Mazaune tabi bayan Audu tana wata shaidaniyar dariya irin ta wanda ya nisa cikin lamarin duniya.

https://chat.whatsapp.com/I8xKHGurk7EBf5ZqQdxHKG

*MATAR MUTUM*
*NA MARYAM FAROUK (UMMU MAHEER*

*FIKRA WRITERS ASSOCIATION*

*LITTAFIN KUDI NE*
*PAY 500 A ASUSUN*
*7061838488*
*OPAY DIGITAL SERVICES*
*MARYAM FAROUK*
OR
*0709290797*
*ACCESS BANK*
*SE A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488*
*IDAN KATINE A DAUKI HOTONSA A TURA ZUWA LAMBAR SAMA VTU KUMA A TURA A 08142548705*

*Kuyi following dina a Arewabooks @Maryamfarouk01 inda zaku karanta wannan littafin tareda sauran littattafaina*
*NAGODE*

*PAGE 28*

Kwana tayi tana juyi duk motsi abinda ya faru daren jiyan seya fadomata zuciyarta tayi mata nauyi, idanunta banda radadi babu abinda sukeyi dalilin kukan data sha, Ta rasa a wanne matsayi zata ajiye Audu dan bata ta Binta kwata kwata ta gama sallama mata amma shi Audu fa?

Son zuciya ko kuwa qin gaskiya ne yake saka shi aikata abubuwan da yakeyi ko yaya? Me yasa duk hukuncinsa yake kasancewa na son zuciya kuma bisa goyon bayan rashin gaskiya?.

Rashin baccin da batayi ba cikin dare yasa ta makara, dakyar ta iya tashi tayi sallah kanta na bala'in sara mata ta koma ta sake kwanciya tana jin yaran na qu qunin Yunwa dan Zakariyya harya fara kuka gashi bata jiyo motsin Bintan ba alamarbata sakko ba balle ta dora abin kari, Audun m yau be leqa su da Asuba yaga ko sun tashi ba kamar yanda ya saba haka daya dawo wucewarsa daki yayi tunda fushi yake da ita kuma yau din Lahadi ce baya fita da wuri daman se qarfe sha biyun rana shiyasa Bintan ta qara samun damar tsula tsiyarta.

Abdullahi ta kira tace ya share tsakar gida ya wanke saboda hadari ya taso daren jiya ruwa be sauka ba se Iska ta taho da qura ita kuma ta daure ta hada ruwan wanka ta yiwa yaran kafin Hajiyar gidan ta gama qailularta ta basu abin kari. Tana cikin shiryasu ta jiyo hayagagar Binta ta san baze wuce da Abdullahi take ba. Cikin kayan Babannan ta samarwa Zakariyya wanda suka masa tace su zauna nan bari ta kawo musu abin karyawa ta zura Hijabinta tana qoqarinfita ta jiyo sallamar Bintan a qofar dakinta, tayi A'uziyya a zuciyarta domin Binta ta zarce shaidan kaidi, sanin Audu na gida kuma zata yuwu wani bala'in ta sake zuwa ta hada mata dan haka tayi saurin fita kafin ita ta shigo mata cikin dakin.

Faran faran tamkar babu wani mugun abu a ranta ta gaida Bara'atun ita dai daga lafiya ta gagara qara ce mata komai saboda zuciyarta gaba daya ma tsinkewa takeyi, ita dai kaf a karkararsu bata taba ji ko ganin Mace irin Binta ba, to ko daman wannan abin shine wayewar da ake fada? Idan kuwa hakane ta godewa Allah da ta kasance bagidajiya akan ta zamo daga cikin munafukai.

"Kuyi haquri na barku da yunwa ko? Bacci ne ya kwace mun yau, Bari in maza ko ruwan shayi ne a tafasa se a soya wainar qwai tunda muna da burodi" Binta ta fada tana murmushi. Cikin sanyi Bara'atu tace
"Babu komai ai" ta bata amsa a sanyaye daga nan Bintan ta juya tana murmushin da Allah kadai yasan ma'anarsa.

Kusan Minti goma tsakani Binta ta sake dawowa da qaton Fulas din ruwan zafi tun wanda Dada ta bata ne lokacin Amarcin da ake zuba musu ruwan zafi a ciki. Yana da girma ga riqe zafi shiyasa take jin dadinsa sosai.

"Sannu da aiki" ta fada sanda ta kabi Fulas din, Binta tayi murmushi ta koma kitchen ta sake kawo mata Farantin data Zubo faya fayen wainar qwai.

A babban Jug din da take hada musu shayi gaba daya ta zuba Madara

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login