Showing 387001 words to 390000 words out of 467220 words

Chapter 130 - MATAR MUTUM COMPLETED 1-3 BY MARYAM FARUK.doc

23 Sep 2025

12169

tayi a tsaye saboda yanda maganar sa ta daketa, wani abu me masifar Waci ya cika mata ma?oshi zuwa bakinta. Ta ringa kallonsa kamar idonta zasu zazzago kafin tace
"Ni ka bawa zaSi tsakanin aurena da na waccen shegiyar yarinyar Audu?"
Be amsa ta ba dama kuma bata tsammaci amsar ba se kawai taci gaba da cewa
"Kayi kaWan ka sakeni Audu. Aure kuma ko bayan raina aka Waura shi ban yafe ba, idan Jafar yana da wata uwar bayan ni kuma zan gani" ta tafi a fusace ?afafunta suka harWe kafin ta kai ?asa Jafar da duniya tayiwa zafi ya tareta, ta fizge bayan da taji ta daidaita ta fice daga falon kamar iska.
Gaban Alhajin Jafar ya koma ya dur?usa, kafin ma yace ta wani abu Alhajin ya dakatar dashi yace
"Wlh dagaske nakeyi, kuma babu mahalukin daya isa ya sa na canza maganata. Badai ni ta cewa matsiyaci ba? Zataga tsiya ganin idonta" yana gama faWar haka ya shige Waki ya barshi a dur?ushe.
Sama da mintuna goma sha biyar Jafar na dur?ushe bayan da Alhajin ya tashi ya barshi, hankalinsa yayi nisa da jikinsa ya lula gurin neman mafita cikin wannan sar?a?iya. Yanzu shi yaya zeyi? Hajiya bata kyauta ba amma wannan hukuncin na Alhaji babu abinda ze sake jawowa se tashin hankali saboda yanzu zata sake Wora Alhakin komai ne akan Afeeyah tunda ta silar tane har ya bata zaSi akan auranta.
Momy data gaji dayi masa magana ta taSashi yayi firgigit ya kalleta. Tafi minti biyu akansa tana kiran sunansa be amsa ba da farko data shiga falon ma ta Wauka sallah yakeyi seda ta kula da zaman da yayi da kuma yanayin fuskarsa sannan ta matsa kusa dashi tayi masa magana amma be amsa ba seda ta taSa shi.
Ya sauke ajiyar zuciya me ?arfi, da?yar yake kallonta saboda yanda kansa yake masa ciwo. Tace
"Lafiya Jafar inata magana ka zubawa guri Waya iso tunanin me kakeyi?
Daga cikin Waki Alhaji ya kirata, ta amsa tana kallon Jafar daya mi?e jiki babu ?wari ta sake cewa
"Jafar lafiyarka kuwa? Meya faru? Kaga idonka yanda yayi?"
"Babu komai Momy kaina ne kawai yake ciwo" ya bata amsa da?yar ya fara tafiya Alhaji ya le?o cikin fushi yana cewa
"Wai ba Kiranki nakeyi ba Aisha?"
Momy tayi ajiyar zuciya tana kallon Jafar dake tafiya kamar wanda yayi mankas, ta tabbatar ba wai ciwon kai bane yake damunsa kamar yanda yace dole wani abu ne ya haWa shi da Alhajin.
Ko zama batayi ba Alhajin ya balbaleta da masifa akan meta tsaya bayan shiya kirata?
"Wai me yake faruwa ne Alhaji? Meya samu Jafar?" Ta faWa a sanyaye ba tareda tabi ta kan faWan da yake mata ba. Alhajin ya zauna yana huci, daya shiga Wakin kasa zama yayi duk yanda yaso ya yakice kalaman Bintan ya kasa, abun ya masa ciwo matu?a ya sosa masa rai. Binta tasan ma'anar matsiyaci kuwa da har take kiransa da haka? Ya kira Al?ali a waya be sameshi ba shine ya kira Momyn yace taso yana son ganinta.
"Alhaji kayi shiru, wai me yake faruwa ne dan Allah" Momyn ta sake faWa. Ya saki numfashi me zafi kafin ya kalleta yace
"Na saki Binta saki biyu"
"Innalillahi wa'inna ilahi raji'un wane irin saki kuma Alhaji? Ita Hajiya Bintan ka saka me tayi maka?" Momyn ta faWa da sauri tana kallonsa da tsantsar mamaki shimfiWe akan fuskar ta.
Daga muryarsa zaka karanci Wacin da zuciyarsa takeyi yace
"Ni Binta ta kira da matsiyaci, ni Binta take gorantawa cewa mahaifinta ne yayi mun sutura shine silar arzi?i na. Ni Binta ta kalla take cewa cikin yayana akwai waWanda sukayi gadon tsiya ta uwa da uba saboda nace Jafar ya auri matar Ahmad a gaban Wana Binta take kirana da matsiyaci" ya ?arasa cikin Waga sauti jikinsa har rawa yakeyi. Momy tayi shiru kawai taja jinsa kafin a hankali tace
"Bata kyauta ba, amma kuma dukda haka bata cancanci hukuncin saki har guda biyu ba Alhaji. Binta ce fa, tayi abinda yafi wannan a baya balle Wan wannan kuskuren gaskiya ka janye maganar ka. Ya ma za'ayi ace aure shekaru hamsin da yan kai ka saki mace ai duniya ma seta zageka, yanda kuka saba kashewa ku binne yanzun ma haka zaka shanye Sacin ranka ka yafe mata amma saki babu daWin ji ai be kamata ba".
Kallon Momyn ya ringayi, se yaga kamar da biyu ba?ar magana take gaya masa ya sake tamke fuska yace
"Nidai na gaya kiki, na saketa kota amince ya auri yarinyar ko bata amince ba na rigada na yanke hukunci na gama zama da ita".
"Da dai ka nemi wani dalilin daban ba wannan ba, dama ka saba, duk sanda zaka auri wata mace seka saki wata. Kuma Alhaji ina tunanin kace Jafar yace bashi da ra'ayin auran Fatima, akan me zaka tilastashi har hakan ya zama silar mutuwar auran mahaifiyarsa? Wannan rashin adalci ne. Sannan ita kanta yarinyar nasan babu yardarta, fin ?arfi kawai ake so a nuna mata haka kawai a sakata a rayuwar da aka san zata cutu a ina ake haka?".
"Saboda ina so na tabbatar da wasiyyar da Ahmad ya bari shine kema kike kirana da mara adalci Aisha? To ki faWi duk abinda zaki faWa bazan canza magana ta ba, na saki Binta, idan kuma har kika ga Jafar be auri Fatima ba to mahaifinta ne ya hanashi auranta baya ga haka mutuwa ce kaWai zata saka a fasa auran nan" Alhajin ya faWa cikin fushi. Ta watsa hannaye tace
"Ai ba yanzu aka fara gwada son kai a gidan nan ba, sanda Ahmad ya kawo yarinyar yace yana so ai so akayi a hanashi, ka dena ma fakewa da wasiyyar Ahmad yanzu da yake Jafar ne shi yasa ka tsaya se inda ?arfinka ya kare akan samar masa da abinda yake so, haka kawai salon ka saka yarinyar mutane a bakin duniya ace dalilinta ka saki matarka" tana gama faWar haka ta fice ta bar masa Wakin ba tareda ta jira abinda ze sake cewa ba.

HAJIYA BINTA
Da?yar ta iya ri?e kukan daya taho mata harta ?arasa cikin falonta tana shiga tayi zaman dirshan a ?asa ta saki kuka, Naziru na tsaye, be daWe da shigowa gidan ba yazo Waukar abu cikin ajiyarsa badan ya tarar da Wakin a kulle bama da ba ze zauna ba, ganin yanda Hajiyar take kuka yasa ya cewa masu aikin dake duba guraren da za'ayi gyara su fita. Duk sunyi cirko cirko suna kallon Hajiyar, seda ya kullo ?ofar falon kafin ya dawo ya zauna yana tambayarta meya faru?
"Wani abun ne ya samu Alhajin?". Bata bashi amsa ba se kukanta data cigaba da sharSa baji ba gani jikinta har jijjiga yakeyi shidai Alhaji Zakariyyah tagumi kawai yayi yana kallonta. Kusan minti biyar tana kukan kafin murya bata fita sosai ta shiga cewa
"Ni Audu ya tashi cima mutunchi a duniyar nan? Ni Audu ze tozarta? Ni, ni Binta Audu zeyiwa haka?".
Gajeran tsaki Naziru yayi ya duba wayarsa dake vibrating kafin ya mayar aljihu yace
"Wai Hajiya meya faru? Kin zauna kina kuka se kace wadda aka aikowa da mutuwa".
Ta shiga share hawaye amma suka ?i tsayawa tace
"Da abinda aka mun gara ace mutuwa akayi ko yanzun ina fatan kafin ni naga tozarcin da ubanku yake shiryamun Allah yasa ya mutu se in ga ta yanda ze aiwar da abinda yake shiryawa. Ni Audu ze dubi tsabar idona yace mun ze dawo da Zubaida, wannan ?wan?wararriyar karuwar ita ze dawo da ita cikin gidan nan?" Seta sake rushewa da kukan daya fi na farko. Naziru ya mi?e domin bega ta inda matsalar Hajiyar ta shafe shi ba ga waWanda suje jiransa se kiransa sukeyi a waya ya nufi hanyar Wakinta yana cewa
"Hajiya a ina kika ajiye key Win Wakin can ne? Zan Wauki abu kuma sauri nake ana jirana?"
Tana kukan tace
"Yanzu Naziru ina gaya muku abinda ubanku yake shirin yi shine zaka tashi irin abun ma be dame ka ba ko?"
"To dan Allah Hajiya me kike so muyi miki yanzu? Ke fa ke kike Worawa kanki damuwa a duniyar nan yanzu ina ruwanki dan Alhaji ze dawo da Zubaida akanki zata zauna ko ke zaki aureta? Wlh abubuwa da yawa Hajiya ke kike mayar dasu wani abun, ga manyan damuwoyi a gaban mu amma ki ringa shigo da wasu abu da sam basu da amfani. Kece baki san zeta dawo ba, ni tun randa ya fara zuwa biko na samu labari to ina ruwana naga aure zeyi ba wai zaman dadiro zasu ba da kuWin mutum da lafiyarsa se kuma a hanashi abinda yake so? Dan Allah ni a ina key Win nan yake na Wauki abinda zan Wauka tun baki sakani a gagarumar matsala ba" Nazirun ya faWa yana shigewa cikin Wakin ta ya fara binciken abinda ya kawo shi. Zakariyya dai kallon Hajiya kawai yake tana rusa kuka, can yace
"?azu muka je Kai kuWin auren Jafar gidansu tsohuwar matar Ahmad".
Naziru daya fito daga Waki bayan ya samu ya gano mu?ullin da ?yar yace masa
"Kana zaune se anyi magana ka ringa zare ido ka manta amma ka iya kawo gulma, to Allah dai ya tsinewa me tada husuma".
Ashariya me mai?o Hajiyar ta lailayo ta aunawa Naziru tana cewa
"Wato kaima ka zama munafuki ma ?etaci dakai ake haWa baki ana zaluntata ko?"
Fasa buWe Wakin yayi ya dawo ya zauna kan kujera yayi ?asa da murya yace mata
"Hajiya, wlh sau da yawa lissafinki kaucewa yakeyi. Akwai ba abubuwan da dama ce Allah yake baki da kansa ta kiyi yanda kika so amma se ki kwaSar. Nifa banga aibu cikin maganar auran Jafar da yarinyar can ba cikin ruwan sanyi duk abinda mukayi ya zama namu ne ze dawo hannun mu da yayan da dukiyarsu duk hannun Jafar zasu dawo kinga se abinda akayi dasu sannan tunda Alhaji nada ra'ayi cikin abun yardar da zakiyi zata saka kema ?imarki da kika rasa a gurinsa ta dawo, haka burin da kike dashi na Jafar ya zama ja gaba akan komai yanzu duk ze tabba amma kin zauna kina wani abu haba dan Allah".
Maimakon kalamansa suyi mata daWi se ma sake tunzura sukayi ta harzu?a matuka tace
"Allah ya tsinewa dukiyar, in dai se na haWa zuri'a da waWancan matsiyatan zan samu arzi?i gara Allah ya kasheni a haka ni zaka cewa na kwantar da kai na bari Jafar ya auri waccen yar yarinyar Naziru? Yarinyar da kaf duniya bani da ma?iyi bani da abinda na tsana sama da ita?" Ta fashe da kuka tana cigaba da cewa
"Akanta Alhaji yace in zaSa ko aure na ko in yarjewa Jafar ya aureta. Akan matsiyaciyar nan Audu yake i?irarin ze sakeni to billahillazi huwarrahamanu kuji da kunnenku ban yarda ba kuma ko bayan raina Jafar ya auri yar shegiyar yarinyar nan ban yafe ba. Sena tsine masa gara ya shiga duniya nasan lalacewa yayi da dai ya kwaso mun waccen annobar ya cakuWa mun a cikin zuri'a kuma Audu ze san dani yake zance, ko zanyi yawo tsirara a garin nan se na Wauki fansar abinda yayi mun".
"Amma Hajiya wannan ba dabara bace, idan har da gaske Alhaji yayi wannan furucin na sa dagaske yakeyi kuma babu abinda ze saka ya janye muddin ba kece kika sakko kika canza naki ra'ayin ba. Yanzu Hajiya a wannan shekarun zaki zaSi aurenki ya mutu saboda wata can da ?arshe riba zakici idan aka auro ta Win ma? Duk tanadi da burin da kike dashi shikenan kin yarda ya tafi a banza? To nidai in har zakiji shawara ki ha?ura tunda dai shi kansa Jafar Win nan yana son yarinyar idan kuma kika ce zaki tsine masa saboda ita kanki kikayiwa asara wlh ba wani ba. Kuma magana ta gaskiya har idan ta tabbata Alhaji ya sakeki to nidai ba gidana ba, gara ma a fara dubawa cikin gidajen hayarki wanda kuWin su ya kusa ?arewa kawai a basu notice ko da yake ga gidan Zakariyya ko na Yakubu"
Zakariyya yayi zuruf yace
"Wa? Ai kasan gidana ya kana kaWan shirin canza wani ma nakeyi"
"Shikenan se ka shirya harda ita ka fitar mata da Waki dan nasan Yakubu ma ba yarda zeyi ta zauna masa a gida ba balle Faisal da ko auren be kai ga yi ba sedai ko ta tafi gidan su Nazira ko Hajiya ?arama".
Kamar wata sakarya haka ta saki baki tana kallon Nazirun har ya gama mata tijarar ya wuce Wakin ajiyarsa yana mita. Ta sauke ajiyar zuciya me ?arfi tana murza idonta da kukan da tayi yasa ya Wauki raWaWi kamar ta zuba yaji gashi a hakan ma ba wai kukan ya tsaya bane maganganun Naziru ne suka tsayar mata da hawayen, kasa ce musu komai ma tayi harya fito da yar jaka daya zubo abinda ya Webo ya wuce ?ofa yana mata sallama Zakariyya ma ya mi?e ya mata sallama yabi bayansa se lokacin kukan da ya fi na baya ya ?wace mata, kukan gaskr da yake tahowa tun daga can ?asan ranta tanayi tana tari ta dafe ?irjinta da yake mata zafi. Yayan da takeyin komai saboda su yau sune su ka fara gudunta kowa yana barranta ta da zaman gidansa.

************
Shiru Al?ali Yakubu yayi yana sauraron Jafar harya kai aya kafin ya gyara zama yace
"Abu beyi daWi ba gaskiya shima kuma Audu yayi gaggawar yanke hukunci da yayi ha?uri komai ze daidaita a hankali amma yanzu ya sake lalata komai ne kawai".
"Nima abinda na gaya masa kenan amma ya?i saurarona. Baba kasan halin Hajiya, bata duba maganar da take fitowa daga bakinta amma ai shi Alhaji tunda yasan yanda take da se yayi ha?ur ya sauke nasa fushin. Wlh bansan ya zanyi ba yanzu Baba bazan ma iya zuwa gurin Hajiya ba dan bana son ta sake gaya mun wasu magana marasa daWi dan Allah ka gaya mun meya kamata nayi?" Jafar ya faWa kamar zeyi masa kuka. Al?ali yayi shiru yana tunani kafin yace
"Abun akwai sar?a?iya Jafar, nafika sanin hakin Audu, duk rigimar da mahaifiyarka takejin ta iya ina tabbatar maka da koda ta dabaibaye shi dukda haka ?yaleta kawai yakeyi abinda yayi kuma yau ya tabbatar da ta kaishi bango bana tunanin kuma akwai abinda ze saka ya janye maganarsa domin idan akwai abinda kowa ze shedi Audu dashi shine baya magana biyu, wannan halin sa ne tun yana yaro muddin ya kafe to fa babu me tan?warashi. Yanzu komai yana hannunka ne kai kake sa zaSin abinda zaka yi, maslaha Waya kuma itace ka lallaSa Binta ta barka kayi abinda yace kodan ka cece auranta ko kuwa ka yarda ta sakun kamar yanda ya ambata?"
Jafar ya ringa kallon Baba Al?ali domin sam beyi tsammanin jin haka daga bakinsa ba, kenan yana goyon bayan abinda Alhajin yace kenan, baze shiga maganar ya yi gyaran da yayi tunanin zeyi ba.
"Kayi shiru kana kallona" Baba Al?ali ya faWa ganin ya zuba masa ido kawai ba tareda yace komai ba, Jafar ya sauke kansa ?asa yana jera ajiyar zuciya, a hankali yace
"Amma Baba koma yaya ne nasan Alhaji yana jin maganarka idan har kai kace masa ya janye nasan ze janye. Tabbas Hajiya bata kyauta ba amma da ya hukuntata ta wani Sangaren ba wannan ba, dan Allah Baba ka shiga cikin maganar nan, su Win duka iyayena ne babu wanda zan zaSa na bar wani a cikin su kuma koda auran zanyi ina bu?atar albarkar kowannensu kafin na samu nutsuwa da kwanciyar hankali a ciki. Dan Allah Baba ina ro?on ka ka taimaka mun ka shiga cikin maganar nan, wlh bayan kai ban san wanda zan kaiwa kukana ya taimakeni ba dan Allah Baba ka sa baki ya janye SharaWinsa nayi al?awari zan cika unarninsa amma ya bani lokaci".
Al?ali yayi murmushi yace
"To Jafar dama ai SharaWin idan bata yarda bane kaga kenan ita ce wadda za'ayiwa magana ta janye nata unarnin shikenan a zauna lafiya. Kaje ka sameta nasan ai da ?ananan shekarunta bayayi zawarci ba ai yanzu data tsufa ba zata so ace tayi ba".
Ya fahimci Baba Al?alin bashida niyyar yin komai akan maganar kuma bega laifinsa ba domin ko shine a matsayinsa be zama lallai yayiwa Hajiyar uzuri ba dan haka kawai yayi masa sallama ya tafi ba tareda sanin meya kamata yayi kuma ba.
****************************************
"Nifa ko ta yarda ko bata yarda ba na rigda na yanke hukunci ba kuma zan canza ba" Alhaji Audu ya bawa Al?ali amsa. Bayan fitar Jafar Win ya kira Audun yayi masa maganar shine yake gaya masa haka. Al?ali yace "a ta?aice dai dama neman hanyar rabuwa da ita kakeyi, idan ba haka ya za'ayi kace kota yarda ko bata yarda ba ka saketa ai ba a haka, kome tayi maka ai kawai taci gaba dacin Arzi?in abinda yasa tun talataini kake shanye duk Wibar albarkar da takeyi maka, se yanzu da bata da mamora ne zaka ce zaka saketa? Taje ina? To baze yuwu ba, ni bazan maka dole ka janye sharaWinka ba a yanzu amma muddin ta yi abinda kace dole ka janye wannan maganar banzar da kakeyi".
WASHE GARI
AFEEYAH
Tunda Umma ta sanar mata da abinda yafaru jiya take kuka ta shiga Waki ba kuma ta sake fitowa ba itama Umman bata bi ta kanta ba dan gani takeyi duk abinda zatayi yanzu munafunci ne, wane tijarace batayi a baya ba akan Jafar Win se yanzu saboda ya kawo kuWin auranta shine zata zauna tana kukan ?arya. Baffa ne ma da safe da beji motsinta ba kuma yasan tana da makaranta ranar ya shiga har Waki ya sameta ya ringayi mata nasiha.
"Ni dai Baffa bana so, ka taimakeni ka mayar musu da kuWin su bazan aure shi ba" ta faWa cikin kuka. Baffa yayi murmushi yace
"Anya ko bakin daya furta so daga baya ze rikiWa ya zama ?i Afeeyah? Kin manta ni dake munyi irin zaman nan yafi sau nawa kina jaddadamun Jafar kike so ba wani ba a lokacin ubangiji be ?addara rayuwa tsakaninki dashi ba, yanzun kuma da lokaci yayi se kice ba haka ba karfa ya zama kin yiwa Allah butulci"
"Ba haka bane ba Baffa, har zuciyata da gaske yanzu bana sonsa. Ko a baya na so shine a matsayinsa na Jafar ba dan nasan ainihin nufinsa akaina ba, sannan ko babu waccen ala?ar ni Baffa ba zanyi aure yanzu

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login