Showing 231001 words to 234000 words out of 467220 words

Chapter 78 - MATAR MUTUM COMPLETED 1-3 BY MARYAM FARUK.doc

23 Sep 2025

12185

Magrib suka shiryi tafiyar dan Jafar baya ditar rana muddinba hayaniya da cunkoso yake so ya haWa ba. Tsaf suka shirya kamar tagwaye, kaya iri Waya suka saka Shadda Cream Color ta karSi jikin kowanne duk iya hassadar mutum sedai ya kallesu yace Tabarakallah badai ya kushe shigar wani daga ciki ba. Jafar ya sake jefa turaren jiya a Aljihu dan karya manta. Suka jero suna tafiya Ahmad na tsokanarsa har suka zo daidai part Win Alhaji.

"Ba zaka shiga kayiwa Hajiya Sallama ba?" Ahmad ya tambayeshi se yayi saurin cewa
"Kai Aa muje kawai, tun fa dana dawo maganar da take tayi mun kenan wacece nake so a ina nake neman Aure, kasan matsaltsalun Hajiya yanzu setace ba haka ba shiyasa nake so ayi komai a sirrince se an kai kuWi idan Allah yasa an Waura auran kawai se taji labari".

Ahmad ya ringa dariya yana cewa
"Lallai ka shahara, to wlh na barka da Allah idan ka janyo mun magana dan cewa zatayi ni na zugaka ka Soye mata"

"Ina zakuje haka?" Muryar Alhaji Audu daya fito da shirin fita masallaci ta dakatar dasu. Ko wanne ya tsume kafin suka shiga gaishe shi.
"Se ina haka kuka kafa huluna kamar sababbin Angwaye?" Alhaji ya tambaya. Ahmad ne ya bashi amsa yana shaf kai yace

"Gaisuwar surukan Jafar zamuje". Kamar Alhajin zece wani abu daga yanayin kallon daya bisu dashi se kuma ya canza da cewa
"Amma da kun jira kunyi sallar Isha'i a Jam'i ba lallai inda zakuje ku tarar basu idar ba" ya wuce is suka bishi a baya. Bayan an idar da sallah suka sake rankayowa tareda Alhajin suka shiga gida. Har Ahmad ya tada mota Balarabe guda daga ma'aikatan yaje da sauri yace masa Alhaji na magana seya bar motar a kunne ya wuce yanajin Jafda????ananun tsaki, har mamakin irin zumuWin da yakeyi akan yarinyar yake kamar ba Jafar da Mata ne suke zigilli akansa ba se gashi wata ta zargeshi tsaf tana ja a ?asa.

"Yanzu na samu waya Alhaji Munzali yayi hatsarin mota kuma jikin babu daWi ina so naje na ganshi" Alhaji ya faWa bayan da Ahmad yaje. Cikin jimami yayiwa Abokin Alhajin jaje da fatan samun lafiya. Alhaji ya sake cewa

"Bari na shiryo seka rakani mu duba shi" ya wuce sama ba tareda ya jira amsarsa ba. A waya Ahmad ya kira Jafar ya shaida masa, ya fara balbalin bala'i,
"Ai se kazo ka sameshi da kanka ka tuna masa fita zamuyi, nasan ba mantawa yayi ba yana sane tunda ya bu?aci na kaishi kayi ha?uri kawai kaje ma koma tare wani lokacin" Ahmad ya faWa da Jafar yace wai ya gayawa Alhaji fita fa zasuyi.

"Amma ni kaWai zanje gaida mahaifin nata kamar wani mara galihu?" Ya faWi kamar ze masa kuka, Ahmad ya sake cewa
"Duk ni sanda nake zuwa nawa gaisuwar dawa mukaje? In baka iya zuwa kai kai kaWai ka kira ko Sadik ko Anwar su rakaka"

"Ni dakai nake so muje"
"Shikenan seka jira na kai Alhajinmu dawo se mu tafi"
"Salon Babanta yace I'm not serious ba? Allah kawai dan ta riga da ta gaya masa ina zuwa da fasawa zanyi kawai naje muyi hira idan yaso daga baya se muje gurin Popsyn nata da kai" Jafar ya dira mita daga ?arshe ya kama hanya ya tafi shi kaWai Ahmad kuma ya kai Alhaji AKTH duba Abokinsa. A hanya Alhajin yake cewa Ahmad

"Babanku ya gaya mun iyayen yarinyar sun dakatar da zuwa tambaya sunce a basu sati huWu ko?"
"Eh haka yace Alhaji" ya bashi amsa ba dan yaso ya tado masa da maganar ba. Alhaji ya sake cewa
"Ka bincika kaji dalilin daya saka suka ce hakan ne?"
"Eh, kawunta wanda ze bayar da auran ne baya nan yayi tafiya shine dalili" Ahmad ya yanko ?arya ya lafta masa.

"Uhm kodai basu shirya ba dai kuma suna jin nauyin su gaya maka ka saka musu hannu a cikin shirin nasu?" Alhaji ya sake faWi yana kallon Ahmad da yanayinsa ya nuna he is not comfortable da maganar da maganar da Alhajin ya tayar. A sanyaye yace kawai yayi shiru be bashi amsa ba hakan tasa shima Alhaji ya kama kansa can kuma ya sake soko wata maganar yace

"Wato shi gaban kansa yakeyi babu wanda ya saka cikin lamarin auransa daga kai se Uwarsa ko?"
Yasan da Jafar yake dan haka yace
"Jiya ya fara zuwa gidansu Alhaji, tsarin Babansu ne kuma se yaga mutum kafinya bashi damar neman auran yarsa shiyasa zeje yau ya gaishe shi amma ba wai maganar auran ce ta taso ba".

"Dama aiba zaka taSa faWar laifinsa ba, shi kuma yar waye yake nema?"
"Nima ban sani ba yanzun zamuje daman kuma ya tafi shi kaWai" cikin yanayin ?osawa da tambayoyin ya bashi amsa se Alhaji ya ?aro radion Mota yayi shiru.

Jay kuwa be fahimci kwatancen da Afeeyah ta turo masa ba dan haka tace tayi sharing masa live location Winta haka kuwa akayi yana biye da Map tiryen tiryen se gashi a cikin gari tsukin unguwar Marmara. A bakin titi yayi parking mota yana ?arewa gurin daya zo kallo, dukda darene amma Jama'a nata kai kawo yanda kasan kasuwa ga surutu kaya kaya banda ?arar ababen hawa da suke karakaina akan titi.

He couldn't believe it a wannan unguwar suke zaune. Ya ringa zungura kai yana le?a yan hanyoyin da yake gani, gurin da Map Winza yake pointing lungune da babu alamar Mota tana iya shiga.
"Ta yuwu Babansu irin mutanen nan ne da basa son canza muhalli shiyasa ya ke zaune a nan ?ila da akwai wata hanya kota can baya da suke bi da mota har ?ofar gida" ya shiga baiwa kansa ?warin guiwa. A waya ya kirata ya gaya mata yana bakin titi besan ta inda ze shigo ba tace masa zata bawa Yayanta wayarta seya zo ya tafi dashi haka kuwa akayi ta bawa Yaya Malam wayar sukayi magana harya gano inda yake.

Seda ya rufe fuskarsa da Facemask kafin ya fita daga motar, sukayi musabiha sannan suka tsallaka Titi, suka ringa bin lunguna suna tafiya shidai bin Malam kawai yakeyi a baya a ransa yana mamakin wannan unguwa daya zo yau, a rayuwarsa be taSa shiga makamancin lungun ba, iyakarsa da nan haka gidan Sarki dan kafin ya tafi Turai yayi nacin son Doki da sallah ko idan an gayyaci Alhajinsu wani taro yakan biyo shi saboda yaga Doki shi be san akwai irin lokunan nan bama a Kano.

Tun yana hasashen ganin gida me Gate harya saduda domin dai gidajen jar laka yake tacin karo dasu wanda Hasken Nepa da Sololin da gwamnati ta ?awata lokunan dasu suka taimaka masa gurin ganinsu tsaf kamar da rana. Seya saki tunanin gidan Gate ya kama na kodai Babansu Basarake ne? Tunda akan samu gidan Sarakai cikin lungu. Bashi da me bashi amsa haka ya ringa jefa ?afafu har suka isa inda yaga Malam ya dakata da alamu nan ne gidansu Afeeyah.

Ya ?arewa gidan kallo cikin abinda befi sakan biyar ba, da fulasta lulluSe dan haka bayace ginin ?asa bane kona sumunti. Filin dai dukansa baze wuce taku Ashirin da biyar a kwance ba idan ma ya kai, be san ya zurfinsa yake ta ciki ba. Zuciya da sa?e sa?e take ta ayyano masa ai Akurkin da Alhaji Audu ya watsasu a gidansa ma yafi wannan gidan girma da yalwa.

Muryar Malam ta dawo dashi daga tunanin daya tafi yana cewa
"Bari na sanar mata ka iso" ya wuce cikin siririn soron gidan Jay harda tura wuya yana le?awa. Ya saki ajiyar zuciya me ?arfi bayan da Malam ya dawo yace masa Baffah yace ya shiga. A baya ya bishi cikin taka tsan tsan dan kar ?ofar gidan ta rafke masa goshi dan ya lura shima Malam Win da yake dogo ne sosai seya ran?wafa yake shiga.

Tilas ya yabawa tsaftar matar gidan domin dukda darene ko ina tsaf yake babu tarkace, a fakaice ya kalli ?ofofi guda huWu da suke cikin gidan wanda yake tsammanin Wakuna ne, ya hango kitchen da kuma inda yake zaton makewayine saboda ga famfo nan se siririn lungu ya shiga ciki. A cikin barandar dake gaban Wakuna biyu suna kuma kallon ragowan biyun ya zauna kan shimfiWar babbar darduma da akayi. Harda standing fan a ajiye a gurin. Malam ya shige Wakin Baffah ya sanar masa ga Ba?on wanda tuni ?amshin turarensa ya sanar musu da shigowarsa.

Dattijon daya tabbatar shine mahaifin Fatima ya fito, fuskarsa a sake yake yiwa Jafar da duk yaji ya rikice kamar wanda yaje gaban Sarki Maraba. Ya zauna daura dashi, Jafar ya du?e yana gaida shi amma Baffan ya bashi hannu sukayi musabaha. Tattaunawar tasu batayi tsayi ba, ya tambayeshi waye shi sana'arsa data mahaifinsa. Daga yanayi na kamala da kuma tambayoyin da Baffah yayi masa be ga wata matsala a tattare dashi ba. Baffan yace masa

"Da akwai wanda yake neman Afeeyah kafin zuwanka sun jima dashi amma ta tabbatar mun da kai take so, ina fatan a shirye kake domin bana so maganar auran taja lokaci, zan baka daga nan zuwa sati biyu ka turo magabatanka domin muyi magana, da zarar ta kammala karatu a Waura muku aure"

"In sha Allahu Baffah" Jay ya faWi yana goge zufar data tsatstsafo masa daga goshi. Baffah ya karkato masa da fanka saitinsa yana cewa
"Garin da akwai zafi sosai dan ma an samu wuta kasha ruwan ko zaka samu sau?in zafin" ya nuna masa ruwan pure water da ZoSon gora wanda Umma take siyarwa Malam ya ajiye masa tun zamansu. Umma ce tace pure water za'a bashi domin su na famfo ma suke sha ai kuwa har kuka Afeeyah tayi akan hakan.

Jay ya kalli farantin ruwan yayi murmushi kawai ba tareda ya sha ba, Baffah ya mi?e yana cewa
"Bari naje, an gayyaceni Mauludi anan ?asanmu zuwan kane ya dakayar dani da tuni naje dan bana so nayi dare a waje" se shima Jay ya mi?e tsaye yana laluba Aljihunsa. Bandir na dubu Waya ya zaro ya rage tsayi kafin ya mi?awa Baffan yana cewa
"Gashi babu yawa a siyi goro". Baffah ya kalli kuWin yayi ?aramin murmushi kafin yace
"Nagode Allah yayi Albarka" ya wuce ba tareda ya karSa ba yana cewa Umma ta le?o su gaisa. Malam ne ya fito daga falo yace ya shiga can kawai, yayi masa jagora Umma na zaune kan kujera tana kallon Arewa 24 a yar Plasmarta da Baffah ya saka mata kwanannan da Hijabinta har ?asa Jay ya kai ya gaisheta ta amsa a mutunce tana cewa ya hau kujera sw ya sake kalmashe ?afa ya zauna sosai akan Centre carpet kansa a ?asa.

"Kira masa ita" Umma ta faWa tana mi?ewa ta fice daga falon sega Malam da Afeeyah, ya baje a gabansa daman Baffa yake jira ya fita dan ta Umma me sau?i ne. Kamar wanda za'ayi wa ?arin karatu haka ya zauna bakin nan har kunne yau gashi ga Jay a gidansu.

"Wai meye haka Yah Malam?" Afeeyah ta faWa tana tura baki. Jay ya kalleta bbau yabo babu fallasa yace
"Ina ruwanki? Yayanmu ne kuma Fan"
"Loyal Fan ma kuwa, dan Allah ina zuwa be kamata naci amanar Jay ba gara na fara sanar masa ya zo ya ganka inaga har suma zeyi yau saboda ?aWi" Yah Malam ya faWi kafin ya sake ficewa da sauri kiran Amininsa Sani. Tsabar yanda yake Son Jay ne sunansa ya koma haka, babarsa kanta ta tashi daga Mamansu Sani ta koma Mamansu Jay dako ka zagi Jay a gaban Sani gara ka ambato Babansa Malam Hamza ka zaga.

Bayan fitar Malam Afeeyah ta zauna yanda Jay yake binta da kallo kamar me neman wani abu a jikinta ne duk yasa ta tsargu. Atamfa ta saka yau A line gown Dark blue ce da fari se dan jaja kaWan a jiki kalar ta haska ta sosai ta mata kyau. Cikin sanyin murya ta gaishe shi, ya amsa bataji sautin muryarsa ba laSSansa taga sun motsa shine ta fahimci ya amsa mata. Jikinta yayi sanyi, murnar dake ranta ta yau Jafar yazo gurin Baffah alamar maganar auransu na dab da ?ulluwa ta disashe. Ta tsammaci ganin fuskarsa a washe kamar jiya koma tafi hakan amma se taga saSanin zatonta, ba yabo ba fallasa, ba wannan Fara'ar da ya ringayi jiya balle zumuWin taSata se binta yakeyi da kallon data rasa dalilin sa.

Sukayi shiru for almost 10 mins shi yana kallonta ita kuma tana wasa da zoben hannunta zuciyarta na dakan lugude. Meya kawo canji a fuskar Jay? Abinda take tambayar kanta kenan.
"Afeeyah" taji ya kira sunanta ta Wago a hanzarce kamar tana jira, idanunta da suka fara tara saboda tunane tunanen da takeyi ta sauke a cikin nasa daya zuba mata. Tana kallo ya taune Lips Winsa na ?asa kafin ya kalli gefe alamu sun nuna maganganu ne a bakinsa bama magana ba amna ya haWiye su se ya mi?e yana ?a?alo murmushin data tabbatar na ya?ene yace mata

"Muje ki rakani, kar Umma tace bani da kunya na shige mata falo nayi zamana". Yanda yayi maganar yasa dole ta murmusa lokaci Wauke ?wallar data ziraro mata duk akan idonsa. Ya cire rafar KuWin Wazu ya ajiye a inda ya tashi kafin ya juya ya fara tafiya tabi bayansa tana cewa
"Ka Wauki kuWinka indai ba faWa kake so ka janyo mun ba" be amsata ba ya sa kai ya fice. Umma na tsaye gaban ?atoton Fridge Winta tana jera Gororin ZoSo, dama yanzu take shiri a ranta ta le?a falon se gasu sun fito. Jafar yayi mata sallama tace ya gaida mutanen gida ta juya taci gaba da aikinta Afeeyah tabi bayansa zalo zalo jiki a saluSe.

A soro ya tsaya bayan ya tura ?ofar gidan ya jingina bayansa da ita ya harWe hannu a ?irji yana mata kallon da yake sakata faWuwar gaba. Ko a mafarki be taSa hasashen Afeeyan ta fito daga irin wannan gidan ba, ?irarta, fatar jikinta, kwalliyarta basuyi kama dana wadda take rayuwa cikin wanna lokon ba. Abubuwa da yawa suke masa yawo a rai amma yayi ?o?arin furzo wanda yafi tsaya masa a rai da Baffanta yace masa akwai wanda ta daWe tare dashi amma tace shi take so. Kamar saukar Aradu haka taji tambayar
"Wanene wanda Baffa yace kun daWe tare dashi?".

Seda tayi dagaske kafin ta iya danne firgicinta ta saita kanta ta hanyar marairaice fuska, yanayin da tayin ransa a Sace yake amma abin ya bigeshi se kawai ya Wage kai sama yana sha?a tareda furzar da iska me cakuWe da ?amshin turaren da a yanzu ya tabbatar a jikinta yake jinsa.

"Kai da kanka kana cewa baze yuwu ace mace kamata na rasa saurayi ba, haka ne amma kuma babu wanda nake so cikinsu" ta faWa cikin rawar murya
Idanunta akan fuskarsa, so takeyi ta fahimci abinda yake zuciyarsa amma ya?i bayyanar da hakan. Zuciyarta ta sake tsinkewa sanda taji yace

"Bana son ?arya Afeeyah na kuma tsani me yinta. I asked you everything that concerns you me yasa zaki Soye mun wannan? Kuma har Baffahnki yasan da zamansa tsakanin ni dashi wa kike shirin ki yaudara?"

"Amma kasan babu batun yaudara tunda har na kawoka gaban Mahaifina, idan ?arya nakeyi maka bazan taSa bari kaga tushe na ba zamu ?are soyayyar mune kawai a waya ba zaka taSa sanin inda zaka saneni ba idan na gama na sallameka"

"Shi da k ika fara kawowa shi kika yaudara kenan?" Ya tsareta da idanunsa da suka canza kala saboda abinda shi yaWai yasan menene. Tayi shiru dan gani tayi kamar ze iya kwasa mata mari idan ta sakw faWin wani abu. Ya dafa ?ofa yana nunata da yatsa yace

"Ki tabbatar da kin sallameshi, karna sake ganinki da duk wani abu daya dangance shi, i mean daga kan sutura, cosmetics har wayar hannunki ki cire Sim yanzu I'm going to send you another one. Ki nemi izini gobe or the next day I'm taking you out to shop, bana so na sake ganin duk wani abu daya siya miki a jikinki har wannan turaren da kike sakawa bana so na sake jinsa a jikinki".

Yanda kasan Ya da Uba haka yake nunata yana zazzaga mata maganganu, tunda take a rayuwarta bata tabajin ta tozarta irin na wannan lokacin ba, a tsaye take amma ji tayi inama ?asa ta buWe ta shige ciki ko kuma ta rufe idonta ta Sace Sat daga gurin. Maganganun Jafar suna nufin ita ko iyayenta basu isa su mallaka mata ire iren suturu da sauran kayayyakin da take ta'ammali dasu ba, yazo yaga gidansu dole ya samu bakin faWa mata maganganu ai. Yanda yake magana fushin dake cikin muryarsa ya zarta ace iyakar na disappointment ne, ya wuce ace na ?aryar da yake i?irarin tayi masa ne tabbas da akwai wani abu daya tunzurashi bayan wannan.

Jiki a saluSe ta shiga gida bayan daya sallameta ya tafi ta shige Waki ta faWa kan katifarta tana sakin kuka me sautin da ta kasayi a gabansa se hawaye. Muryar Umma dake kwarara mata kira da hayaniyarsu Yaya Malam ta sakata dole ta tashi, seda ta wanko fuska a bakin famfo kafin ta shiga falon da suke.
"Wannan kuWin fa na menene?" Umma ta tambayeta tana kallonta kafin ta Amsa Sanin Jay ya zaburo yana cewa

"Yana ina Afeeyah? Ni daman nasan ?arya kakeyi haka kawai ina gurin Babyta ka tasoni yanzu kasa na faWa mata magana yanzu nayi two zero, ni banyi hira da ita naji daWi ka yaudareni da sunan Hero".
Malam daya sha wahalar nemo Sani ya galla masa harara yace
"Minti nawa nayi ina gararanba a lokon nan kowa yace besan inda kake ba? Amma dai ko ?amshin da gidan nan yakeyi ai ya isa kasan yau anyi babban ba?o"

"Ji banza, wane kalar turarene Ahmad be baza mana a Lokon nan ba? Shifa idan yazo tun daga titi ake sanin ya iso gidan nan kuwa a ?alla yana kwana uku kafin ?amshin ya gama bajewa" inji Sani Malam yace
"Zubairu" Umma ta daka musu tsawa jin zasu kaure da musun da suka saba tace au fita su bata guri tunda basu san sun girma ba.

Afeeyah na tsaye har sannan ta sake nuna mata kuWin tana tambayar na menene
"Shine ya ajiye kuma seda nace masa ya Wauke zakiyi faWa amma be jiba" ta bawa Umman amsa. Murmushin takaici Umma tayi tace

"Ba laifi ai tunda shi naga

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login