Showing 393001 words to 396000 words out of 467220 words

Chapter 132 - MATAR MUTUM COMPLETED 1-3 BY MARYAM FARUK.doc

23 Sep 2025

12181

na amma na ?ure ninaje bango banzan iya cigaba da haWiyar ba?in cikinta ba, badan Allah yayi kwanaki na suna da tsayi ba na tabbatar da ban kawo haka ba, ko ban mutu ba da yanzu na nakasa".
"Wlh duk mun sani Alhaji, arzi?i nake nema mata ka janye furucinka za'a cika umarninka" Hajiya Ummun ta sake faWa, seya kalli tamfatsetsen agogon dake bangon gabas Win Wakin kafin yayi gajeran murmushi yace
"Hajiya Ummulkhairi ai wu?a da nama duk a hannunta yake, dama ai cewa nayi idan har ba'ayi abinda nace ba kinga da zarar ta saki anyi magana ta wuce dukda dai gaskiya, amma dai shikenan mu barshi akan hakan ta sahalewa Jafar yayi aurensa ta kuma yi al?awarin ba zata musguna masa ko matar ba shikenan ni bani da wata matsala da ita. Akwai ba?i da zanyi yanzu nasan idan basu ?araso ba to suna dab da shigowa, idan babu wani abun kuma zaku iya ?arasa a ciki" yana rufe bakinsa Waya daga cikin manajojinsa da suke zaune tare kafin Sarah ta gaya masa Ummun nason magana dashi ya le?o ya shaida masa ba?in sun ?araso. A sanyaye Hajiya Ummu ta bar falon, Binta dama ta daWe da tafiya tunda ya fara magana ta fice ta basu guri.

Bayan da suka koma cikin fushi tamkar Hajiya Ummu zata haWiye harshen ta take cewa "Badai ke baki da mutunchi ba? Shekaru ne kawai dake amma babu hankali. Banda dai ?wa?walwar ki bata aiki ace har yanzu ba zaki tuba ki koma ga Allah ke iya abubuwan da suke faruwa dake yanzu ba zasu zame miki ishara ba ko Binta se ranar da kika juya kija jiki a Waure ne zaki gane gaskiyar rayuwa ko kuwa? Hassada da son zuciya sun miki katutu a zuciya, ita Fatiman da zaki ce ba za'a aurota ba ai ba saboda matar Ahmad bace saboda talaka ce ke kuma a duniyarki kin ?i jinin talauci domin da yar attajirai ce a son zuciya irin taki ko Ahmad na raye ?addara ce ta rabasu tsaf zaki amince Wanki ya aureta to idan kin manta ne na tuna miki babu wanda aka haifa da arzi?i kowa a duniyar nan ya nema ya samu haka nan a nan ze mutu ya barshi sillin allura ba za'a binne mutum dashi cikin dukiyarsa ba ayyukanmu na gari ne kaWai zasu zame mana abokanan zama a kabari shaidar mutane kuma ta cece mu a ciki wanne ne baki gurSata naki ba?
Kin auri mutumin nan kin tarwatsa masa gida, kin kori wasu matan waWanda suka zauna kin hana musu sakat balle suji daWin rayuwar auransu kin lalata dangantaka tsakaninsa da yayansa kin dasa tsana da ?iyayya a tsakaninsu Binta shekarunki sittin a duniya me kima mora cikin arzi?in da ubangiji yayi miki? Ga kuWin ga yaya amma baki more su ba kin ?are lokacinki cikin ?yashi da hassada baki da buri a kullum daya wuce mugunta da burin ganin bayan wasu ta yaya zaki ga daidai a rayuwarki Binta?
Yanzu ?arshen Turai be zame miki ishara ba ita da kuke haWa kai shekara da shekaru kuna shuka sharri yau gashi an wayi gari tana raye amma ba zata iya amfanawa kanta ba balle ta amfana miki. A garin yawon asiri kin rasa ?afarki wanda badan Allah ya rufa asiri da yanzu ba wannan maganar akeyi ba, yayanki kinyi musu muguwar tarbiyya kin koya musu son kai gashi nan harke basu barki ba kowa tasa ta fishsheshi babu me tausayin wani a tsakaninsu guda Wayan da Allah ya shirya miki sila Ahmad Win da bakya ?auna kuma kin tsangwameshi kina nema kiyi masa baki idan ya lalace wa yake da asara? Kece. Shi kaWai yake tausayinki yake kuma gudun Sacin ranki yanzu zaki iya yiwa Naziru ko Zakariyya wannan cin kashin?
Nan ina takwaran Al?ali seda aka kai masa kuWin aure kafin ma kika san yar waye ze auro amma ko tari bakiyi ba se Jafar da yake gujewa Sacin ranki shi zakiyi amfani da haka ki muzgunawa ko? To karki fasa Binta ki tsinewa Jafar akan Afeeyah ke zaki shiga uku domin ita wani zata aura taci gaba da rayuwarta idan kuma ubangiji ya ?addara aure a tsakaninsu zaki mutu ayi, ko kuma da ran naki zaki gani idan yaso kiyi biyu babu daga nan se ba?in ciki se ya ?umeki kiyi bunga".

*Assalamu alaikum*
*Yar uwa kina da labarin UMMU_MAHEER COLLECTION kuwa?*
*Kasuwar online inda zakiyi siyayyar kayan ado da kwalliya kama daga kan suturun sakawa, mayafai, hijabai, kayan shafe shafe dana tsafta na kamfanin Oriflame, kayan yara na sakawa dana kwalli duk muna dasu masu kyau da sau?in farashi daidai da aljihunku*

*Muna da kayan back to school wato dangin su Lunch box, school bag, lunch pack da sauransu*

*Sannan akwai kayan kwalliyar Waki, muna yin gadaje, kujeru da duk wani abu daya danganci gida se wanda kika zaba kuma wanda kudinki ya baki*

*Kayanmu garantee ne, idan kinyi kasuwanci damu zaki dawo har ki kawo wasu da yardar Allah. Muna kano muna kuma tura kaya ko ina a faWin cikin ?asar nan da wajenta*
*Kai tsaye kiyi joining WhatsApp group dinmu ta kan wannan link Win*
https://chat.whatsapp.com/FKsWield4wPKepHDZwtPUP
*Ko kuma ayi mun magana akan number 07061838488*
*Nagode*

Kasa ce mata komai Hajiyar tayi banda matsar ?walla babu abinda takeyi har tayi shiru ta tashi ta shige Wakin Bintan cikin sanyin jiki Nazira tace
"Saboda Allah Hajiya duk akan me? Me yasa kullum aka tashi ke za'ace se kace ke kaWai ce mata a cikin gidan nan? Hajiya me yasa idan ba zaki duba kanki ba mu ki duba mu? gaba Waya kin gama zubar mana da mutunchi a duniya, bamu isa muyi wani katabus ba a gidajen auranmu se an zage mu da halinki duk akan me saboda Allah me yasa ba zaki bar zuciyarki ta huta ba ki samu ki ?arasa sauran shekarun da suka rage miki a duniya da cikakkiyar lafiya?"
"Ke da Allah rufe mun baki shashasha mara zuciya, ai wlh nidai nayi asarar haihuwa, duk abinda nakeyi ba don ku nakeyi ba? Se yanzu da rayuwar ku ta kyautata kowa ya kama madafa shine har zaku shiga sahun masu zagina kuna cewa ban kyauta ba duk dan saboda wa nayi komai a rayuwata?" Hajiya Binta ta katseta, taci gaba da kukanta tana cewa
"Saboda dai na zama kamar wata mujiya kowa ya tsane ni kowa ya kasa ganin cutar da aka mun laifina ake gani to wlh da numfashina bazan taSa bari na tozarta yanda ake fata ba, duk kuma me nufina da sharri abinsa sedai ya koma kansa masu dariya duk ranar kukanku tana tafe wlh harda ku munafukan banza munafukan wofi ni an ya ma kuwa da cikina na haifeku ba canza mun ku akayi ba".

Nazira bata sake cewa komai ba Sarah daman batayi magana ba banda Wauke ?walla ba abinda takeyi. Ruwa ta kaiwa mijinta jiya bisa kuskure a garin buWewa ya zube haka ya ringa zaginta har yana ce dama ai ba zatayi nutsuwa ba tunda sauran hauka ce ta raineta da wannan ba?in cikin ta kwana tana tashi kuma ta Wora da wani. Suna zaune suna sauraron hajiyar dake kuka tana sakin maganganu mara sa daWi aka kira sallar Azahar, Nazira ta mi?e Saraha ma ta tashi se Nazirar tayi mata alama data zauna dan haka ta koma dan ta fahimci nufinta kar su bar Hajiyar ita kaWai ta sake fita taci gaba da tijara a tsakar gida, Hajiya Ummu ta fito tana waya ta mi?awa Binta tana cewa
"Salima ce"
"Ni babu wanda zanyi magana dashi bayan duk bakin ku Waya yanzu duk babu Allah cikin lamarinku" ta faWa ba tareda ta amsa wayar ba, Ummu tayiwa Salima sallama akan zata sake kiranta idan kuma da hali kawai ta shigo Kanon domin suna da bu?atar su haWu tunda Munirah tana Kanon dama ita. Sallah ta tayar nan cikin falon, tana raka'a ta biyu Fathiyyah ta shigo da kuka wiwi kamar wadda ta kawo sa?on mutuwa. Ta zube a gaban hajiya, Sarah ta buWe baki cike da mamakin jin maganganun da take faWawa Hajiyar. Ashe ita take sake tunzurata, dakyar Hajiya Ummu ta idar da sallah, daga gefenta idonta ya kai kan wani gwangwanin malt ta Waga taji da nauyi alamar ba'a buWe ba ranta na tafasa bata san sa'adda ta jefashi saitin Fathiyyah ba Allah kuma ya bata sa'a ta sameta a goshi. Tayi ihu ta mi?e tsaye a razane tana kallon Hajiya Binta dan ta zaci ita ta buga mata abu tunda sun fi kusanci dan ko Sarah bata lura da ita a gurin ba balle Ummu dake can gefe.

"Kika buga mun? Mena miki?" Ta faWa tana sakin kukan gaske kan na ?aryar da ta shigo tana yi dan taji zafin bugun sosai. Cikin tsananin fushi Hajiya Ummu ta taso tana cewa
"Nice nan na buga miki, kuma a bakin kawo gulma da munafuncin naso ma sameki na sauke miki ha?wara yar banza me suffar munafukan farkon zamani kawai. Ke dak bakiyi sa'ar hali ba, ko wacce macen kirki burinta ta rufawa mijinta asiri amma ke baki da buri daya wuce ki ringa kitsa sharri tsakanin mijinki da mahaifiyarsa saboda baki da asara idanta masa mugun baki ya lalace ko? Da alamu dake da shashashar surukar taki zamui jera kuyi zawarci karki shiga hankalinki kici gaba da biye mata. Idan ita uwarsa ce bashi da yanda zeyi da ita ke yana da zaSi akan zama dake, tashi ki fita ki bamu guri tun ban saSa miki kamanni ba duk ai jidalin ki ya janyo yara kowa da kalar tarkacen daya kwaso a matsayin mata ta ?arasa tana hararar Binta da ta sake shiga ruWu dalilin maganganun da Fathiyyah ta gaya mata.
Wato Jafar ya Wauki maganar Alhaji yana tareda waccen yarinyar? Kenan baya gudun tayi masa baki kamar yanda ta ambata ya zaSi Fatima akanta kenan?

Mi?ewa tayi tabi bayan Fatiyyan, da?yar take takawa saboda jiki da ruhinta duk sun jikkata dalilin masifar data Worawa kanta ?arfin hali kawai takeyi amma dab take da kaiwa ?asa. Sarah ta yun?ura zata dakatar da ita Ummu ta hanata tace
"Barta, tunda bataji karatun mu na tabbatar duniya zata bida ita, rabu da ita".
A bakin mota ta cimma Fathiyyah har ta shiga tana ?o?arin tayarwa fuskarta fes tana murmushi tamkar ba ita ta fito daga cikin gidan tana kuka ba. Ta buWe gaba ta shiga da?yar tana cewa
"Kaini gidan Hassan".
"Gidan Dr Hassan kuma Hajiya? Baki da lafiya ne?" Fathiyyah ta tambaya seta zaburo mata tace
"Idan ba zaki kaini ba na sauka zaki tsareni da tambayoyi karki ?ara Sata mun rai". Fathiyyah ta taSe baki irin ke kika sani kafin ta tada mota suka fita.
**********************************
"Ni banga duk wani abun tayar da hankali har azo ana samun saSani irin haka ba, tun da dai baka son yarinyar babu dole ai itama ba wai ta rasa masu sonta bane balle ace kuma ai baze yuwu ace ka bijirewa mahaifiyarka akan mace ba auran ma ai be zama lallai yayi albarka ba.
Karka wani damu zanyi magana da Alhajin, babu dole a rayuwa idan kuma maganar yara ne ni zan karSe su na ri?e badan ma yarinyar zata ce nayi mata tsufa ba da nizan aureta ta ri?e yaranta shikenan magana ta ?are" Alhaji Babangida ya faWa bayan daya gama sauraron Jafar. Cikin kaWuwa tareda tsantsar mamaki Jafar Win ya ringa kallonsa jin saSon da yayi, wai shi se ya aureta ta ri?e yaranta. Kenan ma yana da interest akan Afeeyah all this while. Saboda yanda zuciyarsa ta harzu?a, be iya sarrafa bakinsa ba ya kalle shi yace
"Kenan ma Yaya kana son ta kaima?"
"Ko bana sonta Jafar ai zan iya auranta saboda ta ri?e yaranta. Ni ba kamar kai bane daka tashi tsakanin soyayyar uwa da uba, nasan zafin maraici domin rayuwar da mukayi muna yara muda marayu bamu da banbanci kafin ma mu zama marayun na gaske so ba zanyiwa yaran Ahmad sha'awar rayuwa ba tareda mahaifiyarsu ba nasan kuma shima Alhajin tunanin da yake ransa kenan ze so a samu wanda ze auri yarinyar ta rayu tareda yaranta. Kuma banda abinka mace kamar wannan a kwana nawa ne mutum ze fara son ta? Idan zata yarda tsaf zan aureta na mori ?uruciyarta ba ga babanmu da yake tsoho bama ze angwance kaga da gida zan ware mata ita kaWai tayi zamanta...."

"Nagode se an jima" Jafar ya katse shi yana mi?ewa tsaye idonsa kamar yayi kwalli da barkono tsabar yanda sukayi jaa, idan ya cigaba da zama yana sauraron sa tabbas ze saki ashar, to kuma Alhaji Babangidan ba sa'an sa bane balle yace zeyi masa tijara shiyasa kawai ya tashi baki alaikum ya bar masa gidansa. Ya za'ayi daga kawo masa kukansa kuma ze soko masa wani zance mara kan gado? Kenan kowa na gidan son ta yakeyi be sani ba?.
Alhaji Babangida kuwa dariya ya ringayi bayan da Jafar ya fita a fili yace
"Ja'iri kawai, gara kaje kayita addu'a Allah ya sassauta halin uwarku ya Wora ka akanta shine mafitarka a yanzu amma babu wanda zaka yaudara akan baka son yarinyar nan".
Kai a ?asa ya shiga falon hajiya dan bama ya so su haWa ido da ita, badan Mama (Hajiya Ummu) data kirashi kan dole ba da besan sanda ze sake taka ?afarsa yaje gidan ba har se randa Hajiya ta huce ta neme shi da kanta abinda ya ?udurce a ransa kenan. Babu kowa a falon, seda ya zauna ya fahimci hajiya batanan domin da kodai tana zaune a falo ko kuma ya jiyo karaWinta daga cikin Waki, ya sauke ajiyar zuciya kafin ya zaro wayarsa da niyyar kiran Maman sega Sarah ta fito daga Wakin Hajiyar ta gaisheshi a sanyaye kafin tace masa Maman na ciki.
Suna zajneyda Munirah suna jajanta abin ya shiga ya zauna kan carpet, Munirah ta kalleshi tace
"Dan Allah dubi yanda yaron nan ya koma, tun rasuwar Ahmad be mayar da jikinsa ba ga alhinin rashin Wan uwansa ga jarabar Binta ita bata ko tsoron wani ciwon ya kamashi? Kowa yana tattalin yayansa yana gudun su shiga damuwa amma ita da hannunta take ingiza nata a wuta".
Hajiya Ummu tace "uhm" dan ta fara rasa abin faWa kuma akan lamarin Binta. Yanzu jajen inda ta tafi sukeyi dan an duba ko ina bata nan ga kuma wayarta a falo ta barta balle a kirata.

Ya gaishe su suka amsa Nazira ta shiga tana kallonsa tace
"Jay ka kira matarka kaji ko tare suka fita da Hajiya ni na kira layinta da nake dashi a kashe yake" ya amsa da "toh" ya zaro wayarsa ya shiga kiran Fathiyyah. A speaker ya saka wayar, seda kiran ya kusa katsewa kafin ta amsa can ciki tace "hello". Strictly ya tambayeta
"Ina Hajiya?" Daga can Fathiyyan ta juya Ido kamar yana gabanta kafin tace
"Na sauketa gidan Dr Hassan" be ce mata komai ba ya katse wayar, Munirah ta dau?i salati tana cewa
"Lallai Yaya Binta ba zata taSa yin hankali ba, to faWa ta tafi suyi da Hajiya Zubaidar ko me?"
"Addu'a ta Waya ubangiji Allah yasa a ?arasa gurguntar mata da Wayar ?afar, ?ila idan ta tsugunna gaba Waya zata naba'a tasan annabi ya faku. Kai innalillahi wa'inna ilahi raji'un, Binta fitina ce ni dai ban san a ina amta gado wannan halin ba domin dai duk ahalin gidanmu ita ta fita zakka, yanzu ana ?o?ari a gyara Alhajin ya sakko shine ta tafi ta Wakko wata maganar ai shikenan ni kam na zare hannuna kai yi tafiyarka kayi duk abinda zuciyarka ta yanke maka na tabbata ubangiji baze kama ka da bakin wannan matar tunda ba umarni ne akan shari'a na zallar son rai da ?in Allah ne" Hajiya Ummu ta faWa tana mi?ewa ta shiga tattara komatsanta da niyyar barin gidan kamar yanda tace ta gaji ba zata iya da Binta ba kuma.
****************************************
Hajiya Zubaida na zaune cikin Wakin ta, gama mata dilka kenan ta fito daga cikin abin turara jiki ta zauna tana shan *TULA-TULA (Maman Ilham 08135613021)* da aka dama, a gurin Halima matar Dr Hassan ta samu bata ji nauyin komai ba ta tambayeta dan ta bawa Aimana Autarta tasha kuma ya mata amfani Labat Winta da suka zube sun tasa sunyi acan acan shiyasa tace itama ba za'a barta a baya ba domin dai Allah yayi mata baiwar jiki me kyau wanda kulawa da gyara suka taimaka mata ?warai ta yanda idan ka ganta ba zaka taSa bata shekarun da take dasu ba. Irinsu Hajiya Zubaidan su suke sake tabbatar da gyara shine mace. Duk kyan mace da ?uruciyarta idan ta zauna kara zube bata gyara jikinta to fa nan da nan zata lalace jikinta ya riga shekarunta tsufa haka kuma duk tsufan mace idan har tana gyara za'a dama da ita zata daWe tana morar duniyarta da tsinke.
Shekaru goma kenan da Mijin data aura bayan sun rabu da Alhaji Audu ya rasu wanda ta haifi yara uku dashi yan biyu mata se namiji guda Waya tun sannan kuma ta koma gidan Dr Hassan Win da zama saboda can unguwar da take tayi nisa kuma babu kowa tare da ita shiyasa ya maidota nan gidan kuma dukda bata da miji bata fasa kulawa da kanta tana gayu yanda ta saba ba wannan ya rigada ya zame mata jiki yanzun kuwa da tarihi ze maimaita kansa shiri takeyi bana wasa ba domin dai tana son Audunta, shi Win mutum ne da ba zata manta dashi a tarihin rayuwarta ba yayi mata halacci duk kuma abinda ta zama a yanzu shine sila, shi ya rabota da ?azamar rayuwar da ?addara ta jefata wannan abin ne yake sakawa koda ta tuna tozarcin daya sameta ta dalilin sa takeyi masa uzuri, a sikelinta alkhairinsa ya Wara sharrinsa domin koda ya rabu da ita gaba taci, ta samu miji dukda be kai shi arzi?i ba amma tayi rayuwar kwanciyar hankalin da tasan b
da tana gidansa ba lallai ta samu irinta ba.

kunnenta ma?ale da waya suna magana da Alhaji Audun, dalilin jinkirin rashin gama gyaran inda zata zauna har gashi saura kwana biyu Waurin aure wanda so yayi ace a ranar zata tare shine ya kira yake gaya mata babu fashi zata tare ranar amma Abuja zasu tafi suyi kwana uku kafin nan an kammala komai

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login