Showing 357001 words to 360000 words out of 467220 words

Chapter 120 - MATAR MUTUM COMPLETED 1-3 BY MARYAM FARUK.doc

23 Sep 2025

12175

kiyayeni da wannan shegen rawar kan naki idan ba haka ba tam". Dogon Hijabi ta saka suka fita tare dan tana so taga waye ze ringa kaisu makarantar kafin wani lokaci ta karSa dan ba zatayi saken barin musu raganar yaranta ba karma dalili yasa su kawo wani tsarin. So takeyi gari ya ?ara wayewa ma ta kira Momy taji zancen Islamiyya tunda wadda suke zuwa acan unguwar take tayi nisa daga nan gara bokon dama a tsakiya take ita babu damuwar ace se an canza musu.

Turus tayi ganinsa tsaye ya buWe booth yara suna sauke kayan daya lodo a ciki, ta haWe fuska kamar hadari abinda baze yuwu ba kenan. Duk yawan direbobin da suke a gidan se shine ze ringa kai mata yara makaranta salon ya sace su wannan bama abu ne me yuwu ba. A bakin ?ofa ta tsaya tana kallon yanda yaran suka nufeshi da gudu ya tsugunna ya rungume su gaba Waya se kuma taji wani abu ya taSa zuciyarta, Wauke kai tayi gefe da sauri ganin ya kallo inda take, bata san ya matso ta ba se jin muryarsa tayi dab da ita yana tambayar ina Ahmad.

Kamar zata taSo sama haka ta cuna baki ta koma ciki, minti biyar tsakani yayi sallama yaran na biye dashi a tsakar gida ya gaida Umma ta bashi Ahmad be Sata lokaci ba yaran daya saka aiki na gama shigar da kayan ciki ya kwashe su suka tafi bayan yayiwa Umma sallama ya shaida mata yau ze wuce Abuja nan da kwana biyu kuma ze koma France.

Umman ta ringa masa addu'oi, ta ?walawa Fatima kira amma ko gezau tana ciki duk tana jinsu murna ce ta cikata jin ze koma ya sakar mata mara tayi fitsari mutum da shishshigi duk ya addabesu abunda ba ha??in sa ba amma ya kanainaye saboda iya neman suna. Duk mitar da Umma ta ringa mata bayan ya tafi bata tanka ba, tana jinta tana magana akan ubannin kayan daya lodo musu babu ce kawai ba'a sako ba tun daga kan kayan ciye ciye dana sha harda buhun hunan abinci, sabulan wanka dana wanki ashana ?aramin abu seda ya siyo musu se wata envelope Umman ta bata kamar ba zata bude ba jin babu nauyi tayi zaton wasi?a ce a ciki, ga mamakinta data buWe ATM card ne da ?aramar paper ya rubuta pin a jiki. Tsaki tayi ta jefashi cikin bedside drawer, saboda an ce masa tana fatara shine ze wani kwaso kayan abinci ya kawo musu badan Umma zata hau kanta ba wlh da seta saka an fita da kayan idan ya dawo ya kwashe abinsa.

Direba ne ya maido da yaran ya kuma gaya mata kullum ze Wauke su ?arfe bakwai a dawo dasu ?arfe biyu hakan yasa ta kira Momy ita tace tace mata a nema musu islamiyya nan kusa me kyau zefi sau?i akan suci gaba da zuwa waccen Win, hakan ya mata daWi, washe gari ta saka Yah Malam Winsu ya karSo musu form a Mai tasa, ranar Asabar aka kaisu akayi musu interview aka basu aji shikenan aka Winka uniform suka fara zuwa, idan aka Wakko su daga boko direban ze jira su ci abinci ya sauke su a islamiyyar idan an tashi kuma akwai yayan Umma Halima Yammata da suke can tare suke tahowa su rako su gida kafin su wuce. Duk sati biyu ranar Alhamis daga boko gidan kakanninsu ake wucewa dasu se ranar Asabar da safe za'a maido mata dasu saboda suna zuna zuwa tahfiz.

A sannu kwanaki suka fara tseren gudu aka dena lissafin satika aka koma na watanni, rayuwa ta dau?i sabon babi, yara sun zama yan lungu sun ware sosai suna sabgoginsu dan daman sun saba da unguwar tunda suna yawan zuwa yanda suka saki jiki basu bata matsala akan komaai ya rage mata kaso mai yawa cikin abinda ya dameta domin tana fargabar yanda zasu karSi sabuwar rayuwar se gashi komai yazo mata da sau?i hakan kuma ya taimaka mata itama gurin fara saituwar nata al'amuran, kewar mijinta dai abu ne da baze taSa barinta ba amma baro can gidan da sukayi ya taimaka mata sosai gurin sake dangana, ta barwa Allah komai a kullum dare da rana kuwa bata gajiya da yi masa Addu'a ta nema masa rahmar ubangiji a inda yake, tana tsananin kewar sa, tana kuma tuna alkhairansa da lokacin da yake raye bata san muhimmancinsu ba se yanzu.

Idan sukayi sallah zata cewa yaran suyiwa babansu addu'a se su ce mata ai dady ya gaya musu koda yaushe su ringayi masa base lokacin sallah kawai ba idan suka faWi haka seta wani haWe rai, har sun gane bata son zancen dadyn kuma basa mata har mamaki takeyi yanda basa nacin ta kira musu shi yanda suka saba a lokutan baya, a ranta ta ringa jin daWi dan ba wani son sha?uwar tasu takeyi ba balle ya koyawa yaranta ba?in hali irin nasa. Abinda bata sani ba, duk safiyar Allah a wayar direbansu ze kira suyita hira har a kaisu makaranta haka idan an taso, da daddare kuma tana can zaman Wakin data wajabtawa kanta zasu kirashi a wayar Baffa ko ta Umma.

**********"
Hajiya Binta zaune a falon ta ta rafka tagumi da hannu biyu tana sauraron Naziru bawai dan tana gane abinda yake faWa ba, abin duniya ya isheta, kamar wadda ta zagi sama lokaci Waya komai ya lalace ta rasa ina zata kama.

"Shine nake so na kawo su nan na ajiye kafin komai ya daidaita, duk inda zan kai suna da ido a gurin nan gidan kuma nasan ko sun sani babu wanda ya isa yace ze shigo yayi bincike" Nazirun ya faWa yana kallonta. Ta janye tagumin da tayi tace

"Wai kayan menene haka da duk store Win da kake dasu basu isheka ba seka kawo su nan?"

Seda ya waiga kamar me tsoron aji su kafin yayi ?asa da murya yana cewa
"Daloli ne da wasu yan kayan aiki. Kinsan gwamnati ta sako mu gaba akan ha?an ma'adanan da mukeyi saboda mun?i yarda muyi raba daidai dasu shine suke so su ?wace lasisin da muke dashi da duk ma'adanan hannunmu, shine na tattara komai na siyar aka bani daloli dukda haka basu kyale ni ba akayi mun shunen EFCC to yanzu na kwashe komai daga account Wina ne nake so na kawo miki ki ajiye dan ba zasu barni ba yanzu haka fa unguwar gidana zagaye take da jami'ai suna ta bincike jira kawai suke na shiga da wani abu su kamani".

Dake taji zancen masoyanta kuWi harda gyara zama tace
"Kai dan Allah? Wannan gwamnati ta najeriya ko Azzalumai. Ba dama aga mutum Allah ya buWa masa yana samun arzi?i se a tasoshi a gaba se an ga bayansa to ta Allah ba tasu ba.
Yanzu dai kafin komai, ina kuWaWe na na kusan shekara goma daka turmushe yau ne gobe ne har yau ban gansu ba?" Ta faWa tana zare masa ido, sake ?asa yayi da murya yace

"To ai duk sune Hajiya, kin fa san na gaya miki ita wannan harkar bawai daga an zuba kuWi ake kwashe wa ba Aa tana bu?atar jari me ?arfin sannan rainon ta akeyi ta girma ta bun?asa yanda idan lokacin moro yayi har jikokin mu se mun barwa. Duk masu wayo yanzu abinda sukeyi kenan daka samu kuWi ka zubasu a harkar ma'adanan ?asa amma ita sabga ce ta masu ha?uri shkera goma zuwa sama kafin ta tsaya da ?afarta yanda ko ka fara zarar kuWi ba zata girgiza ba".

"Shegiyar ?arya kullum haka kake cewa. To nidai na gaji a bani kasona. Tsinannun kuWin ma kamar bakin rabo tunda muka Webe su suka zame mun jarfa, wlh duk sune silar lalacewar komai" yayi murmushi yace

"Ke dai kika ga haka Hajiya ni kuwa wannan kuWi ai su suka mun silar arzi?i, yanzu dai yaushe ya kamata a shigo da kayan? Sedai kuma fa ba iya mutanen waje ba har na cikin gidan ma bana so a san da zaman su musamman Alhaji bansan ya zamuyi ba"

"Yo ba gara bala'in waje da wanda yake cikin gidan nan ba? WaWannan annamiman matan guda biyu ai gara EFCC da koma waye dasu ka bar komai a hannuna kawai ka faWi sanda za'a kawo zan shirya komai, Alhaji kuma ai naji yana zancen zasu tafi Umarah daga can wai Aisha zata je ganin likita, Allah yasaa idan ta tafi karta dawo wannan mata ta zame mun ?aya a ?ahon zuci na rasa yanda zanyi da ita. Kaga tunda Amadu ya mutu ko rana baya ganin idonta kullum tana Waki kai daga tashinka zuwa yanzu sau nawa ka taSa ganin Alhaji a Wakunan mu amma wai yanzu a rana se ya shiga Wakin Aisha sau uku ban ko ishe shi kallo ba ita kuma waccen yar matsiyatan ta zame mata baiwa tana ?ugunta koda yaushe suna ?ulla munafunci". Yanda take magana zaka fahimci tsananin zafin da takeji akan abun.

Naziru ya mi?e yana cewa
"Yanzu dai duk ba wannan ba Hajiya mu fara gamawa da maganar kayan nan komai da ze biyo baya me sau?i ne. Bari naje, yaushe Alhajin ze tafi? Saboda naje nayi duk tsare tsaren daya kamata kafin nan, amma dai bari baje kawai ma yi waya" yana gama faWar haka ya fice daga falon be jira amsarta ba.

A mota ya zauna ya kira waya, seda ya gama tsara yanda za'ayi kafin ya tada motar ya bar gidan kamar an sauke masa wasu kaya haka ya ringa jinsa damuwar data dabaibayeshi ya kau dan yasan muddin kayan nan suka shiga gidan ya tsira se dai yayi ?o?arin fita da sauran ya kaiwa masu su kafin lokaci ya ?ure masa.

Hajiya kuwa bayan fitarsa tagumin data cire ta mayar, ji take kamar tayi ta zunduma ihu ko zata samu sau?in abinda takeji a ranta. Dama daman da taji yanzu da Naziru yace ze kawo mata ajiyar kuWi, zata nuna masa itama yar kanta ce ba shi kaWai ya iya damfara ba, idan ya kuskura ya kawo kuWin biyar ba zasu sake fita ba be san tafi gwamnatida EFCC da yake tsoro hatsari ba, zata ga da yanda ze dawo yace ta bashi kuWaWen.

Tashi tayi ta tafi falon Alhajin dan ta jiyo yaushe zasu tafi ayi a kawo kuWin ko ta ji sau?i idan tana jin Wuminsu, yana kishingiWe akan carpet idonsa akan kwamfuta ya saka gilashi se kayan abinci da be ko taSa ba a gefe,bata lura da Momy a gurin ba sedata zauna ta haWe rai kamar wadda taga mutuwarta kafin kuma ta saita fuska kaWan tayi masa sannu ya amsa ba tareda ya kalleta wannan ya sake tunzura zuciyarta ganin ya rufe kwamfutar ya mayar da hankali kan Aisha da alama magana sukeyi kafin ta shiga.

Tana shirin ta musu taratsi wayarta dake cikin aljihun doguwar rigar data saka ta fara ?ara, a fusace ya janyo ta ganin sunan Fatiyyah na yawo ya sake hasala ta ta Wauka tana cewa

"Wai wace irin yarinya ce ke me ba?in naci haka? Sata ko maita da zaki ringa bibiyata ko akwai bashi a tsakaninmu ne da ban san dashi ba?"

Daga can Sangaren saSanin muryar Fatiyyah se taji ta babbar mace, ta gintse fuska jin matar ma cewa
"Yi ha?uri Hajiya ba Fatiyyar bace mamanta ce".

"To madallah ya akayi?" Ta faWa cikin isa kamar ba Bintan dake yi tamkar zata kwantawa maman Fatiyyah idan suna waya ba, ita dai Hajiya Fauziyyan bata damu ba ta gaisheta ta amsa a ciki kafin ta karanto mata dalilin kiran.

"Ya Wauke passport Win ta kinga babu halin ace ya bishi sannan idan ta kirashi a waya baya Wauka ni kaina tunda mukayi magana sau Waya yace ze kira an fi wata ban jishi ba ga babanta yayi fushi bamu san me yace masa ta aikata daya saka ya tafi ya barta ba gaskiya asan abinyi hajiya wata uku fa ba kwana uku ba idan sakin yarinyar nan yayi ai seya fitoya faWa tayi iddah ta nemi wani mijin ba wai ya jingine mun yarinya ita ba sakakkiya ba ita bame aure ba".

"Ai hakan shine ya dace da ita, badai baki mata tarbiyyar girmama na gaba da ita ba? Gara ta zauna idan ta koyi darasin zama a gidan miji seta dawo. Kowacce matar arzi?i rufawa mijinta asiri take amma ita bankaWa nasa takeyi to ta zauna seta shekara ko ze dawo sannan a zauna idan zaman zeci gaba mu gani kuma kar wanda ya sake kirana a cikin ku tunda baku haWo mun da waya a kayan gara ba balle ku ce ku kuka siya" Hajiyar ta faWa kafin ta kashe wayarta tana huci.

Dariya ta basu dan seda Alhajin yayi ta kaWan bedai kalleta ba, a ransa yake cewa wato ashe Binta tasan tarbiyya da girmama na gaba?
Hajiya ta harareshi kafin cikin fushi tace

"Da zaku zigashi ya tattara ya bar ?asa ko sallama beyi mun ba in sha Allahu duk wani ?ulle ?ulle bazeyi tasiri ba duk mugun abun da ake shiryawa sedai ya ?arewa mutum. Jaki na haifa muku ko bawan uban mutum ne da za'a asirce shi a mayar dashi boyi boyi ana nema a ?arar masa da dukiyar daya tara da gumin halak? Mutum ma ya dena dariya idan ana zaton kurciyar da ake ta so a masa ce ta kamashi murnar ku ta koma ciki dan nice nan nace ya ya tafi kar kuma ya kuskura ya dawo seya shekara" ta ?arasa tana murguWa baki da buga cinya kamar yarinya.

Momy dai ta mi?e tana kallon Alhajin tace
"Ina sauraronka" ta fice ta basu guri. Da harara Binta ta rakata kamar idonta zasu zazzago seda ta ?urewa ganinta kafin ta maida hankali kan Alhajinta takwarkwashe fuska kawai ta fashe masa da kuka.

************
Ranar litinin jirgin su Alhaji Audu tareda Momy ya daga ?asar saudiyya, ba a son ranta ta bishi ba, badan yan uwanta da suka danneta ba bata yi niyyar cinye kwanaki Arba'in na rasuwar Ahmad a gidan tafiya taso tayi amma suka hanata duk wata rawar jiki da Alhajin yake mata a banza take Waukar komai domin ya rigada ya fice mata daga kai rayuwar ma gaba Waya bata mata daWi, wanda yake samar mata da farin cikin Allah ya Wauke shi bata kuma inkari da hakan domin dai daman Allah baya barin wani dan wani yaji daWi.

Kwanansu biyu da tafiya Naziru ya kawo ajiyar kayansa kamar yanda yace. Da daddare aka shigo da matoci sha?e da kayan ta ?ofar baya aka ringa shiga da kayan ita kanta data ga yawan kwalaye da buhunhuna seda tasha jinin jikinta ta tsareshi akan ya gaya masa gaskiimeye a ciki.

"WaWannan uban kwalaye da buhu ace kuWaWe ne bajat Win ?asar duka ka sace ko yaya? Kaga kar ina zamana ka jefani a masifa gara ka gayamun gaskiyar menene ta yanda ko sahu aka biyo zansan yanda zan kare ka" ta faWa tana kallon kayan bayan an gama saukewa. Cike da iya yaudara ya buWe buhu Waya yana nuna mata Wanyun daloli dake ciki yace
"Dagaske kuWaWe ne Hajiya ba wani abu ba". Jikinta har rawa ya Wauka da ganin kuWin tace

"Naziru kodai kungiyar shan jini ka shiga?" Ya maida buhun ya sile sannan ya shiga kunna manyan Ac na tsaye da aka haWa a Wakin tun kafin a kawo kayan yana cewa
"Wlh matsalarki kenan Hajiya, nidai ga ajiya nan idan kikayi wasarere da su kuma bani kaWai zata shafa ba".

Ranar ko bacci kasa yi tayi, da taji motsi zata fara haske haske, kusan kwana uku a jere ko shara ta hana ayi mata kafin daga baya ta saki ranta taci gaba da gadin dukiya.


*ASSALAMU ALAIKUM*
*Matan kwarai matab albarka ina gaisuwa. To kunsan dai ba iya shafa mai fata yai kyalli shine cikar kyawun mace ba, a ganki dumur-mur, jiki duk tsoka jiki duk laushi ko ina oga ya kama yaji shi tibis shi ne magana.*

*Ina farin cikin gabatar muku da ingantacciyar SABAYA wadda zata cike miki gurbin wannan ramar ta kuma tabbatar miki da mafarkinki na zamtowa matar sakawa a gaban mota*

*Kiran waya kawai zakiyi ko chat, a tuntubi Maman khadijah mai garin kunun sabaya, tana Palladan anguwan Fulani Zaria Kaduna state tana kuma aika sa?o duk inda kuke a faWin tarayyar Nigeria, kar a manta siyan na gari mayar da kuWi gida*

*Phone no.-08033411249 OR 07037777442*

*MATAR MUTUM*
*NA MARYAM FAROUK (UMMU MAHEER*

*FIKRA WRITERS ASSOCIATION*

*LITTAFIN KUDI NE*
*PAY 500 A ASUSUN*
*7061838488*
*OPAY DIGITAL SERVICES*
*MARYAM FAROUK*
OR
*0709290797*
*ACCESS BANK*
*SE A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488*
*IDAN KATINE A DAUKI HOTONSA A TURA ZUWA LAMBAR SAMA VTU KUMA A TURA A 08142548705*

*Kuyi following dina a Arewabooks @Maryamfarouk01 inda zaku karanta wannan littafin tareda sauran littattafaina*
*NAGODE*

*BOOK 3*
*PAGE 31*

Kwanci tashi a sarar mai rai, kwanaki ma shuWewa, satuka na kaucewa tun ana lissafin watanni se gashi yau ake addu'ar cikar Ahmad da shekara guda da barin duniya. Kafatanin yaya da jikokin Alhaji Audu sun hallara a cikin gidan wasu matan daga ciki tun ana gobe addu'ar wasu kuma da safen haka nan mazan kowa yazo tare da matarsa da yayansa.

A katafaren Alhajin suka zauna kamar koda yaushe, abin al'ajabi, saSanin zaman jungum jungum da aka saba kana hararata ina hararka wai se gashi yayan Alhaji Audu maza sun haWa kai suna hira, muryoyinsu har cikin guda suna dariya sun rabu gida biyu suna musu akan wasan zakarun nahiyar turai da ake gab da kammalawa, masu goyon bayan arsenal sunayi, waWanda sukr bin bayan sauran clubs da babu su a cikin masu jan wasan kuma sun haWe suna fatan man city ta samu nasara.

"Gaskiya ya kamata ka koma gida Jafar, nifa idan nine kai ba zan taSa iya buga wasa a wani gida da ba Arsenal ba tunda dai suna sake zawarcinka ka amsa, ko shekara biyu ka ?ara ka saki harkar haka ka barta ana marmarinka base an gaji dakai manyan clubs sun dena neman ka ba" Alhaji Hussaini ya faWawa Jafar dake zaune a ?asa ya jingina da kujera. Jafar yayi murmushi yace
"Akwai abubuwa da yawa a rayuwata da nake son su har raina amma tunda har na barsu bazan iya sake koma musu ba, ni ?wallon ma duka barinta zanyi na gaji, gida nake so na dawo na huta nayi training waWanda zasu gajeni".

"Haka ne kam,

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login