Showing 252001 words to 255000 words out of 467220 words

Chapter 85 - MATAR MUTUM COMPLETED 1-3 BY MARYAM FARUK.doc

23 Sep 2025

12372

kwanciyar hankali a zaman aure? Kaifa kace ka tsaneta kamar mutuwarka" Ahmad ya sake bauWewa daga daga barin bashi amsar abinda ya bu?ata, cikin yanayi kamar na ?ufula Jay yace

"Toh ai baka amsa mun tawa tambayarba" se Ahmad ya saki sanyayyan murmushi yace
"Babu abinda bazan iya sadaukar maka ba ?anina amma ina son Fatima sedai son da nakeyi mata be kai wanda nake maka ba dan haka indai ita ce burinka zan bar maka ita". Da saurin gaske Jay yace

"Wasa nakeyi, kawai so nakeyi na gwada tsakanin nida ita wa kafi so amma Allah ya kiyaye me zanyi da wannan yarinyar? Ya za'ayi ma naso abinda kake so? Ai ko ina sonta na gane tilas na ha?ura bazan taSa takarar wani abu a rayuwar duniya da kai ba ko menene koda rayuwata zata salwanta a dalilinsa zan ha?ura na bar maka shi".

Sukayi shiru na wani lokaci, a zuciyar Ahmad lissafi yake dalilin daya kawo Jay ya soko wannan maganar? Zancen Afeeyarsa sukeyi me yasa ze kawo maganar ya bar masa Fatima kuma? Shi ya kasa tattara abubuwan ma ya gane me suke nufi. Jay kuwa sake auna nauyin soyayyar da Ahmad yakeyiwa Fatiman yake a zuciyarsa, idan har ya zama silar rabashi da ita beyi masa Adalci ba amma be cancanci Azzalumar mace irinta ba mara tsoron Allah muguwa, Allah kaWai yasan dalilin wannan haWi.

"Yau na haWu da matata" Jay ya katse musu shirun, Ahmad yace
"Uhm, da wurwuri haka?"
"Dama ya kamata ace ita ce, rabon na sja wahala ne yasa na barta kuma yanzu Allah ya sake dawomun da ita cikin rayuwata bazan bari kuma ta kufcemun ba"
"Ikon Allah, ita kuma wacece ita?"
"Fatiyyah Mu'az" ya bashi amsa, Ahmad ya maimaita sunan da alama so take ya tuna koya santa can kuwa yace

"Fatiyyah Fatiyyah dai? Daman kuna tare har yanzu? I thought ma tayi aure itama kamar Maryam?"

"Nop batayi ba, we met not so long ago"
"Ayyah tana France kenan?" Ahmad ya tambayeshi, se yayi jumm daya tuna ashe ya kusa ya kwafsa kafin yace
"Eh, Aa, a Abuja muka haWu kafin na wuce ai ta koma Nigeria ta gama karatunta"
"Allah ya tabbatar da Alkhairi" inji Ahmad da sam be gane kan Jay ba.

Washe gari yaje gidansu Fatiyyah kamar yanda yayi mata Al?awari, Mamanta, Babanta da duka siblings nata sun sanshi sun kuma saba tun a lokacin da suke tare dan haka da yaje normal suka gaisa sukayi hira da Mamanta kafin ta basu guri. Sister ta ce ta Waukesu video a wayarsa da Fatiyyan ta karSa ta bata sanda suka fito rakashi. Fatiyyan da kanta ta shiga tiktok tayi uploading video da Caption Win ~FATIYYAHJAY~, shi bema san dashi ba se bayan daya koma Hotel ya kunna router yaga messages Win friends Winsa da suka sanshi da Fatiyyan a da, kowa tambayar da yake masa "sun dawo tare ne?" Wasu suce they will make a perfect couple. Daman be bi takan comments na tiktok Win ba shiyasa ma bega sa?on Afeeyah ba dan normally idan yayi posting turning off comments yakeyi saboda bashida lokacin dubawa, washe gari ya koma France yayi resuming field har sannan kuma zuciyarsa ba'a sake take ba.

Mixed feeling yake dashi akan Afeeyah, Soyayyar da yake mata na neman ta hana tsanarta daya fara tun usuli cigaba dayin tasiri a ransa. Sabon babin da suka buWe na ?auna da Fayiyyah ne yake Webe masa kewa. Fatiyyah na sonsa, so na gaske, a gefensa zece yana sonta amam ko rabin yanda yakejin Afeeyah har a yanzu cikin zuciyarsa bata kamo ba amma kuma yana jin a ransa ze iya auranta yanzu musamman da yake neman ruwan kashe gobara shiyasa yake iyakar ?o?ari gurin ganin ya maida mata da kwatankwacin soyayyar da take gwada masa. Abu guda da yake haWa shi da Fatiyyah rawar kanta kuma tun asali abinda yayiwa tarayyarsu tasgaWo kenan yar gata ce da bata san komai ba se a tattalata a jiyar da ita daWi, irin soyayyar da sukayi da Afeeyah wadda da acw a baya ne ko wani ya gani yana kalarta cewa zeyi ba?auye ne a yanzu ita yake muradi a gurin Fatiyyan sedau wayewarta tayi yawa nata salon soyayyar na manyan yara ne masu buWaWWun ido irin wadda take burgeshi a da kenan yanzu kuma soyayya me tafe da sirkin kunya data WanWana a baya ita yake muradin sake samu amma Yah Ahmad ya yi masa tsakani da ita.

A ta gefen gidan Alhaji Audun Bechi kuwa rayuwa ce take ta gurgurawa yau fari gobe ba?i, Malam Hafizu ya cika maganarsa kamar yanda yace a bashi sati huWu shida kansa ya kira Baba Al?ali ya shaida amsa ya shirya suna iya zuwa sannan. Da Al?alin ya gayawa Alhaji Audu se cewa yayi ba za'aje ba, wai yar ta gwal ce da har se ya bawa mutane lokaci sanda yaga dama sannan za'aje neman auranta?

"Kota zubardaji ce ba Gwal ba wannan ba matsalarka vace ba, ma'aurin yace yaji ya gani seka kawo idanu ka zuba yanda ka sabayi a lamarin auran sauran yarorinka, karka cusa bakinka ciki muddin ba Alkhairi zaka saka musu ba" Al?ali ya dakatar dashi. Alhaji Audu yace
"Nifa kawai auran yarinyar be kwantamun a zuciya ba, tunda yana jin maganarka ka bashi baki ya nemi wata ga yayan manyan mutane nan yan Asali ko yaushe ne seda Alhaji Madari yamun maganar yarsa yace ko shi ko Jafaru..."
"Ai kasan shi Jafaru uwarsa ma ta isheka shiyasa ba zaka somo dashi ba wannan kuma daya zama karkatacciyar kukar kowa me daWin hawa dole ka nemi hanashi abinda yake so. Ni daman na daWe da sanin bawai Binta ce kaWai shaiWaniya ba, hali ne ya tarar da hali kaida itan shiyasa zamanku yayi tsayi.. To ni duk ba wannan ba, zancen muhalli a ina zauna?" Cewar Baba Al?ali.

Alhajin Bechi ya karkace yace
"Yanzu Ahmad kake tambayar i

FATIMA
Kafin cikar wa'adin da Baffah ya yanka ta tattara ta koma makaranta kowa ya ganta seya tambayi me yake damunta se tace musu rashin lafiya tayi saboda yanda ta fita a hayyacinta kana ganinta kasan bata da nutsuwa sam. A bakin Anty Sauda taji cewar Baffah ya kira Kawun Ahmad kamar yanda ya ro?i su bashi sati huWu lokaci ya cika kuma ya gama uzurin da yake a gabansa yanzu dan haka duk sanda suka shirya suna iya suje.

Anty Saudan dai ta sake shaida mata Ranar Juma'a yan gidansu Ahmad zasu zo, Ranar kwana tayi tana kuka har wani zazzaSine ya sake saukar mata ta ringa sake gwada kiran Jay da tura masa sa?onni ta kowacce kafa da ta san tana samunsa a baya amma a banza kamar me aikawa lahira. Sanda ta samu sa?on sunje har an tsayar da maganar auransu watanni shida masu zuwa kusan suma tayi dan a tsaye take ta sulale ta zauna seda aka jijjigata kafin ta farka daga suman zaunen ta kuma fasa musu kukan da tun suna bata baki da tambayar meya faru har kowa ya gaji ya rabu da ita, Maman Minal ce ta kira Anty Sauda dan taji ko mutuwa akayi a gida akan sanar mata, bata fiya zafi ba amma ranar seda ta warwarwa Afeeyah tayi mata tatas wai dan ma Badar bata nan ta tafi Kd dan har sannan Jikin Babansu se a hankali an dawo dashi dai amma duk weekend a gida takeyi Friday basa komai ranar take tafiya ta dawo Sunday bata ma san da zancen kawo kuWin ba yanda Afeeyar bata gaya mata ba itama yanzu ta dena damun kanta da matsalarta, ta dai gaya mata yanda suke ciki da Jay ta kuma jimanta mata ta sake nusashsheta abinda ake mata hasashe kenan sanda suke ce mata karta saki jiki dashi shikenan ta kama kanta ta rabu da ita tunda bata ga alamun zata hankalta ta gane Allah guda bane domin har sannan cewa take Ahmad ne ya janyo mata zuwansa ne ranar ya ruguza komai.

Sati tsakanin zuwarwa Ahmad tambaya akaje na Jay, a bazata batun ya zowa kowa harda Ahmad da ita kanta Hajiyar seda aka saka ranar zuwa taji labari a bakin Alhaji Zakariyyah, data zabura zatayi bala'i se kuma tayi la?was kamar TarwaWa taji gishiri ta shiga zare idi dajin Yar wacce za'aje tambayowa Jay auranta. Se gani kawai Alhaji Zakariyyah yayi ta fashe da kuka, a zatonsa kukan bata sani bane kamar yanda ta tasammayin tijara a farko seda yaji tana cewa

"Ashe dai burina ze cika, Jafaru ze farantamun ya wanke mun takaicina Allah na gode maka kace dai ya gidan gwaunan bankin Najeriya ce ko ubana?" Zakariyyah murmushi kawai yayi dan yanda Hajiyar ta keyi kamar wata yarinya, daya tana neman ta ishe shi da tambayoyi ya fice ya barta ta shiga bige bigen waya tana sanarwa su Turai abin Arzi?in daya samesu. Ahmad kuwa Baba Al?ali ne ya kirashi yace ya shirya zasuje Abuja neman auran Jay, yayi mamaki, ko awa guda basu cika da gama magana da Jay ba amma beyi mentioning masa zancen auran ba koda yake duk Jay Win ya canza ya kuma kasa gane kansa balle abinda yake damunsa. Daya samu labarin shiru yayi be ce masa komai ba, a ransa yayi murna zasuyi aure lokaci Waya kamar yanda birinsu yake tun suna yara.

Juma'a Baba Al?alin yace zasu tafi su kwana a can Asabar idan sun gama abinda ya kaisu su juyo a ranar shi kuma yayi niyyar tafiya Zaria gurin Fatima wadda tun bayan Baikonsu Al'amura suka fara sauyawa a tsakaninsu, a yanzu base ya kirata ba takan kirashi da kanta dukda dai babu sakewa ko soyayyar da yake fatan samu daga gareta amma a hakan shi ji yake kamar yafi kowa farin ciki ba kuma shi da wata damuwa dan haka ya kirata ya sanar mata da baze samu damar zuwa ba zasuje Abuja neman ma Jafar Aure, bata nuna taji ba balle ya saka ran zata sakawa lamarin Albarka. Ita kuwa sunan Jafar daya ambata mata tamkar fami ya zamar mata kan nata Jafar Win da har yau bata dena kukan rasa shi ba, dangana tayi ta ta kuma buWe zuciyarta ta fahimci abinda aka daWe ana nusashsheta amma ta doWe zuciyarta da idanu??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????nta ta?i fahimta a yanzu ne ta ke godewa Allah domin nacin Ahmad ya mata rana domin da ace ya barta tamkar Jafar bata san wa zata kama ba.

Ita da kanta ta yarda haWuwarta da Jafar da soyayyarsu har zuwa rabuwarsu ha??in Ahmad ne, ta godewa Allah daya bata damar gane kurenta harya yasa tana da sauran lokacin da zata iya gyarawa, sedai aka ce So Wayane, har yau har gobe tana son Jay, bata sani ba ko se ranar data tabbatar da ta zama mallakin waninsa sannan zatayi jana'izar soyayyarsa ta binneta badan ta mutu ba.

Baba Al?ali, Alhaji Babangida, Alhaji Abdullahi, Zakariyyah Bechi, Naziru Bechi, da Ahmad Bechi da se Aminan Alhaji Audu na ?ut da ?ut Alhaji Mu'azzamu da Alhaji Aliko sukaje neman auran saSanin na Ahmad da Baba Al?alin ne tareda Alhaji Abdullahi sukaje, ya sanarwa Alhaji Babangida lokacin ya bashi uzurin ranar ze tafi Umarah dalilin daya saka ba'aje dashi ba. Harka akayita girma, aure ake shirin yi irin wanda ake kira ?warya tabi ?warya. Shima kamar Ahmad watanni shida aka saka, suka dawo Kano ni?i ni?i da kayan arzi?in da aka haWo su dashi. Hajiya bata iya bacci ba, tun daren Juma'a take dokawa Naziru kira daya gaji da amsa ma yayi restricting number, yanda kasan zatayi tsuntsuwa ta tafi can haka tayi ta kasa zaune ta kasa tsaye har seda suka dawo abubuwan da suka zo dasu suka gigitata haka ta fita tsakar gida tana taka rawar murna tareda sakin habaici wa Momy da ko biskit ba'a kawo mata daga gidan Surukan Ahmad ba sanda akaje neman aure sun dai kawo tukucin naira dubu hamsin wadda aka cire musu daga dubu Wari biyar da suka kai kuWin aure da saka rana. Shima Jay Wari biyar Win aka kai dukda Hajiya tace tayi kaWan Baba Al?ali dashi ya bada kuWin daman yace haka yayi niyya kuma baya isa ta saka a ?ara ba ko Zinariya ze auro.

Bayan sun dawo Ahmad ya kirashi murya a sake sam be ri?i cewar Jay ya zame shi daga abubuwa da yawa da suka shafi rayuwarsa a yanzu ba ya shiga tsokanarsa da Ango Ango. Seda suka gama barkwanci kafin yace masa
"Amma fa na Wanji babu daWi, ni ya kamata nayi breaking news na auranka bawai naji labari daga sama ba, amma ya wuce ,I'm happy for you, I'm happy for us, at long last mun kusa mallakar muradan zuciyarmu"

"Ka kusa mallakar muradin zuciyoyinmu nida kai dai" Jaya ya raya a ransa a fili kuma ya marairaice yace masa
"Kunya nakeji, bansan taya zan gaya maka ba". Dariyar da Ahmad ya ringayi har seda ya sauka daga kan kujerar Momy da yake zaune, seda yayi me isarsa kafin yace
"Amma bakaji kunyar kanka ba da kake faWar wannan maganar? Ni zakace kana jin kunya ba zaka iya gaya mun za'aje neman maka aure ba? Ai shikenan amma ko na ji tausayin Afeeyah ne sunanta ko? Allah kaWai yasan yanda zataji idan labarin nan ya iske ta".

A fusace Jay yace
"Allah yasa ya zama silar Ajalinta ma kowa ya huta Annamimiya me fuska biyu munafuka kawai"
"Jafar me yake damunka? Me yasa baka da magana seta fatanma wani mutuwa haka kawai san kana da matsala dashi? Babu kyau tsananta ?iyayya, ina jiye maka tsoron kar a jarabceka da abinda kafi ?i a rayuwarka wlh seka gwammaci kida da karatu" Ahmad ya faWa in a serious tune se Jay yace

"Na nawa kuma? Jarabta ai an mun sedai nayi addu'ar Allah ya bani ikon cinyeta kawai amma batun wai wani waye tuni an wuce gurin"

"To karkayi saSo Malam nikam se anjima, daga kira muyi farin ciki kar ka jawo abinda rayukanmu zasu Saci, haba, kanka aka fara kasa Namiji a neman aure da zaka Wauki abu da zafi ka hana rayuwarka sakat? Duk ka canza daga Happy Jay ka koma wani Aggressive person akan me? Ita rayuwa daman ai tilas akwai samu akwai rashi ba kuma dole duk abinda mutum yaso ace ya same shi ba. Nasan zafin So amma idan ka kasance me neman zaSi da yardar Ubangiji cikin dukkan lamuranka koda zakayi fushi da wani abu daya sameka a rayuwa ya zama na Wan lokaci, Allah ya fika sanin dalilin daya saka ya hakana samun wannan abun naci da dagiyarka se ta janyo maka abinda zaka zo kana dana sani da nadama mara amfani a rayuwarka se Allah ya barka da abin yaga iyakar gudun ruwanka. Ga rabonka nan ka dace da ita, kayi addu'a Allah yasa ta zamo maka sanyin idaniya macen da kowanne Namiji yake fatan samu"

Da "In sha Allah" Jay ya amsa masa shikenan aka gama wayar saboda ya sake goga masa gishiri akan rauni. Tun haWuwarsa da Afeeyah yake hasaso yanda wannan ranar zata kasance musu, ranar da za'ace yarjejeniyar aure ta ?ullu tsakaninsu, yaci burin zuwan lokacin har party yace ze shirya se gashi tazo masa da wacce be taSa koda hasaso zata zama matarsa ba. Gaba Waya ma yanda abubuwa suke faruwa shi baze ce ga shi ba kawai dai komai yana faruwa ne tamkar shirin film kamar wasa yanzu an tasarma zuwa No going back stage
"Ya rayuwarsa zata kasance da watan Afeeyah???" Tambayar da ke kara kaina cikin zuciyarsa.

Shirin biki ya kankama a gidan Alhaji Audu Bechi. Shiri akeyi tamkar a wannan karon ne za'a fara aurar da ?a a cikin gidan dukda shirin tsakanin Yayan cikin gida ne na waje dai nasu ido. Hajiya Binta tamkar zata haukacw saboda yanda ta azawa kanta tashin hankali akan wannan aure da Jay zeyi, Turai da Hajiya Zainab ne kan gaba akan shirin Komai, su suke haWa Lefe, kuWaWe masu nauyin gaske ya aika musu na haWa lefen. Me hali baya fasa abinsa, duk irin zumuWi da zirgillin da Hajiya takeyi akan shirin Bikin da aka zo batun haWa lefe taga uban kuWaWen da ake narkawa domin Turai tsakani da Allah ta tsaya take abun nan Hajiya ta rikice tace bata san zance ba ta yaya za'aje ana siyan Lesuna na dubu dari biyar zuwa sama ai Almubazzaranci ne.

*MATAR MUTUM*
*NA MARYAM FAROUK (UMMU MAHEER*

*FIKRA WRITERS ASSOCIATION*

*LITTAFIN KUDI NE*
*PAY 500 A ASUSUN*
*7061838488*
*OPAY DIGITAL SERVICES*
*MARYAM FAROUK*
OR
*0709290797*
*ACCESS BANK*
*SE A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488*
*IDAN KATINE A DAUKI HOTONSA A TURA ZUWA LAMBAR SAMA VTU KUMA A TURA A 08142548705*

*Kuyi following dina a Arewabooks @Maryamfarouk01 inda zaku karanta wannan littafin tareda sauran littattafaina*
*NAGODE*

*BOOK 2*
*PAGE 25*

"Ga Lesunan a Legas nan masu kyau dubu Hamsin dubu sittin duk dai ?ure gayu ai sun isheta" Hajiyar ta faWa, saboda takaici Turai bata iya bata amsa ba se Hajiya Zainab ce tace
"Haba Binta, a lefen Jafar za'a saka Lagos Lace? Ke kin taSa ganin yarinyar da ?aramar sutura balle ki ringa lissafo mata Lashin dubu hamsin dubu sittin? To ai wlh ko Ahmad da yake shirin auro Wiyar Talakawa Lefe Hajiya Aisha ta zage tana haWawa na garari. A gurin *Maryam Hassan 07088361522* fa take siyan Laces matar nan kuma indai Lashi ake magana bata kawo na banza dama kin so gaskiya ne se kice a tafi gurinta a samo Lasuna na fita taro a ci da buguzun dan gasu nan kala kala iyakar kuWinka iyakar shagalinka"

"Kuma suna kaiwa nawa?" Binta ta tambaya tana gyara zama, Hajiya Zainab tace "daga ?ana dubu goma sha haka har zuwa Wari da Woriya"
"To a samu yan Hamsin sittin Win a gurinta kawai a mayar da waWannan wannan Almubazzaranci har ina ai se Allahya kamamu" Hajiyar ta sake faWi. Data ishi Turai seta dena ma kai mata kayan idan an siya tun randa tace zata kwasa da kanta taje a musanyo tunda ita ta?i mayar da hankali.
"Ai gara a rage kuWin ko Gona ce a siya masa tunda shi baya maida hankali gurin tara kadarori yanzu da zeyi aure ai yaci ya fara" Hajiyar ta faWa, Turai tace
"Dake shi ba irinki bane ai da baki da buri sena ki tara baki ci ba baki bawa wasu sunci ba gara ki ajiye su yi diddiga a share".

Ta gefen Momy ma shirin biki suke da yan uwanta babu kama

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login