Showing 408001 words to 411000 words out of 467220 words

Chapter 137 - MATAR MUTUM COMPLETED 1-3 BY MARYAM FARUK.doc

23 Sep 2025

12155

lokaci domin ki tuba amma kullum maimakon gyara ?ara nausawa kikeyi Binta se kin wayi gari kin ganki a rami sannan hankali ze zo miki ki gane gaskiyar wannan rayuwar ba matabbata bace ba?"
Wlh ku zama shaida daga yau ba zan sake tako gidan nan ko na jibanci duk wani lamari na Binta ba muddin bata amince ta karSi umarnin mijinta ba kuma nima bana maraba da ita a muhallina ko mutuwa nayi na yafe karta kuskura tazo kan gawata" Hajiya Ummu ta faWa cikin kuka Munirah ma tace

"Nima haka, na yafe ki wlh na yafe zumunchi dake dan ba zan cigaba da mu'amala da shaiWan a suffar mutane ba. Iya kacin nadamar da kika jefani a rayuwa ta isheni, shekara da shekaru kullum da tunanin baiwar Allahn nan nake kwana nake tashi haka kawai na biyewa son rai na biyewa shaiWaniyar zuciyarki kika kaimu kika baro gashi nan ha??in ta ya kanainaye ni shekarata hamsin a duniya babu aure har na cire rai ina fatan Allah yasa wannan ya zame mun kankarar zunubin da kika saka na kwasa, Allah yasa iyakar wahalata a duniya ce" yeeee suka cigaba da kuka.

Binta tayi tsilli tsilli da ido tana kallonsu, Allah kaWai yasan abinda take ji a cikin ranta. Audu ya saketa gashi kuma babu wanda ze fahimceta ya gane halin da take ciki yan uwanta da duk kalar tsiyar data tata a rayuwa basu gujeta ba, ga auranta na arba'in da motsi ya mutu sanadiyyar Fatima dukda dai ta san da saka hannun su Aisha amma ta yaya za'ayi taso wannan yarinyar?

Ummu da Munirah suka mi?e ganin SaSatun banza ma sukeyi kamar bata jinsu, ta zabura ta ri?e zannuwansu ta fashe da kuka tace
"Shikenan babu wanda ze fahimce ni? Ku da kuke jinina ba zaku tayani ba?in ciki da jimami ba kune zaku ce na sakarwa ma?iya suyi galaba akaina? Akan auran yarinyar fa ya sakeni sannan ya sake kafamun sharaWin in dai ina so in cigaba da aure na se na yarda an aurota ta yaya zan so wannan yarinyar a duniya ta? Ashe ba banza ba ubangiji ya kinsa mun tsanarta me tsanani, ashe ita ce babbar ma?iyata ita ce garkuwar dake ?o?arin hanani kaiwa ga cikar burukana. Tunda ta shigo rayuwar ahalin gidan nan ta zame mana jaraba, data kama Ahmad bata sake shi ha seda ta kaishi kushewa ita kanta Aishar gata nan kullum a Waki ciwo ya lafketa a haka kune so na yarda Jafar ya rakito nana ita ta zagaye mu da mugun dafinta?"

"Kiyi duk yanda kike ganin zakiyi Binta amma wallahi tallahi muddin na saka kafa na fita daga gidan nan ki saka a ranki na mutu baki da sauran wata yar uwa Ummu a duniya Binta na sallamaki dama Allah nake dubawa da kuma iyayenmu har naci gaba da zumunchi dake badan haka ba shekaru da dama na daWe da sutakeki daga cikin Ahalina" Ummu ta faWa tana fizge zaninta, Munirah ma ta ?wace tana cewa
"Ya za?????"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"?"#ki ringa faWar kanki ke kaWai? Ai jam'u zakiyi domin na tabbatar har Yaya Sakina da Salima sun fita a sabgarki Binta se ki cigaba da rayuwarki daman tafi kama da ta wanda ba shida masu gaya masa gaskiya a duniya".

"Yanzu shikenan kowa ya juya mun baya? Mijina, yayana yanzu kuma yan uwana kun juya mun baya?" Ta faWa tana fashewa da kuka, babu wadda ta waiga cikinsu suka cigaba da tafiya, da rarrafe ta bisu tana cewa
"Shikenan na amince". Su ka tsaya cak kamar yanda numfashin Jafar ya tsaya na wucin gadi kafin yaci gaba. Ya rufe idonsa yana sauke ajiyar zuciya a jajjere, Hajiya Ummu da Munirah suka juya suna kallon Binta da son tabbatar da abinda ta faWa tana kuka tana gyaWa musu kai tace
"Na amince, amma wlh bazan taSa sonta ba kuma auran bazeyi albarka ba".

A hankali ya sulale ya fice se sannan dukkansu suka an kare dashi a falon ma, cikin fushin daya goge yar fara'ar data saukarwa Hajiya Ummu ta kalleta tace
"Ai ba zaki taSa canzawa ba Binta, wace irin magana ce haka kice auran bazeyi albarka ba anya wai kina tunani da ?wa?walwar ki kafin ki furta magana kuwa?"

"Nace na amince bisa dole badan ina so ba kuma babu wanda ya isa ya tilastani naso wannan yarinyar ko na sakawa auranta da Jafar Albarka, iyakata ake so a nunamun in sha Allahu kuma sedai suga ?arshensu. Ni dai ku kirashi ku gaya masa na amince shikenan" Binta ta faWa ?asan ranta tana ?issima abinda ita kaWai tasan menene.

*Shafuka kaWan suka rage, ku gafarceni bisa jina shiru hakan ya faru sanadiyyar wani al'amari daya fi karfina. Kuyi ha?uri, ina nufin waWan da suka saka kuWin su suka siyi littafin MATAR MUTUM. Nagode ?warai da jumurin bibiyata.*

*MATAR MUTUM*
*NA MARYAM FAROUK (UMMU MAHEER*

*FIKRA WRITERS ASSOCIATION*

*LITTAFIN KUDI NE*
*PAY 500 A ASUSUN*
*7061838488*
*OPAY DIGITAL SERVICES*
*MARYAM FAROUK*
OR
*0709290797*
*ACCESS BANK*
*SE A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488*
*IDAN KATINE A DAUKI HOTONSA A TURA ZUWA LAMBAR SAMA VTU KUMA A TURA A 08142548705*

*Kuyi following dina a Arewabooks @Maryamfarouk01 inda zaku karanta wannan littafin tareda sauran littattafaina*
*NAGODE*

*BOOK 3*
*PAGE 40*

*Assalamu alaikum*
*Yar uwa kina da labarin UMMU_MAHEER COLLECTION kuwa?*
*Kasuwar online inda zakiyi siyayyar kayan ado da kwalliya kama daga kan suturun sakawa, mayafai, hijabai, kayan shafe shafe dana tsafta na kamfanin Oriflame, kayan yara na sakawa dana kwalli duk muna dasu masu kyau da sau?in farashi daidai da aljihunku*

*Muna da kayan back to school wato dangin su Lunch box, school bag, lunch pack da sauransu*

*Sannan akwai kayan kwalliyar Waki, muna yin gadaje, kujeru da duk wani abu daya danganci gida se wanda kika zaba kuma wanda kudinki ya baki*

*Kayanmu garantee ne, idan kinyi kasuwanci damu zaki dawo har ki kawo wasu da yardar Allah. Muna kano muna kuma tura kaya ko ina a faWin cikin ?asar nan da wajenta*
*Kai tsaye kiyi joining WhatsApp group dinmu ta kan wannan link Win*
https://chat.whatsapp.com/FKsWield4wPKepHDZwtPUP
*Ko kuma ayi mun magana akan number 07061838488*
*Nagode*

"To madallah, Allah yasa hakan ya zama silar shiriyarta da samun daidaito cikin al'amuran. Ku dai cigaba da sakata a addu'a ku kuma ringa nusar da ita gaskiya idan da rabo zata gane" Al?ali ya faWa bayan da Jafar ya shaida masa cewa Hajiya ta amince da sharaWin Alhaji.
Yayi ?asa da kai kamar yana gaban Al?alin yace
"To Baba se kayiwa Alhajin magana, wlh harda yanda yake shareta yanzu yasa komi ya lalace ni ina tsoron kar ciwon damuwa ya kamata kawai dan hajiyar tana da dauriya ne amma da wata ce da yanzun ta kai ?asa saboda abubuwan nan".

"To Jafar damuwa ai ita ta Worawa kanta ba wani ba duk cikin abubuwan da take ha?ilo akai wannene take akan turbar gaskiya? Babu. Ai duk wanda yace tukunyar wani ba zata tafasa ba tohla shakka tasa ko Wumi ba zatayi ba dan haka ita zakaje ka gayawa waWannan maganganun ta cire ?yashi da hassadar da suke neman zautata daga ranta kota samu nutsuwar morar lokacin daya rage mata a gaba tunda dai tayi asarar na baya". Yayu shiru domin dai gaskiya Al?alin ya faWa Hajiya itace matsalar kanta ba wani abu na daban ba. Al?ali na shirin kashe wayar yayi ta maza yace
"To Baba yanzu yaushe za'aje kenan?"
"Za'aje ina?" Al?alin ya tambayeshi kamar be san abinda yake magana akai ba. Vike da sangarta yace
"Gidansu Afeeyah mana tunda ai hajiyan ta yarda".
"Wannan kuma ai ya rage naka Jafar tunda mun maka auran farko muka sake zuwa nema maka na biyu ka zame kaje kace kai bada yardarka ba, yanzun da ka yarda ai ka isa a shari'ance ka nemawa kanka aure ka kuma yiwa kanka wakilci. Idan kun tsayar da ranar Waurin aure seka sanar mana muzo muyi shaida idan kuma baka bu?ata ma ka hutashshemu se mu tayaka da addu'a daga gidajen mu ko?" Al?ali ya faWa.
Ya marairaice kamar ze saka masa kuka yace "Amma Baba kasan dai komai nayi saboda neman mafita ne kuma ai na gane kuskure na tunda daga ?arshe abinda nayi gudun shiya faru".

"Wannan ai kai ta shafa kuma Jafar. Yanda ka iya yin gaban kanka ba tareda shawara ba ka lalata komai seka sake komawa idan sunga zasu iya su karSeka karma ka kuskura ka sakoni a shirginka domin bazan shiga ba. Ni ban ma san kai din soko bane mara lissafi seda uban yarinyar nan ya kirani. Ta yaya zaka kalli idon macen da kake so kace baka sonta saboda dai kai kafi kowa gaSunta sannan yanzu saboda rashin kunya ka koma ka ?aryata kanka kome kake shirin yi? Yanzu da wanne ido zaka koma biko?"

Yayi ?asa da murya feeling guilty yace
"Ha?uri za'ayi a shiga maganar nan Baba, Baffa nada fahimta nasan idan kayi masa bayani baze ga laifi na ba"
"Oh saboda kawai mahaifinta sau?a?e??en mutum ne shiyasa kake taking nasa for granted? Kaje kace baka son yarsa sannan yanzu ka zagayo kana cewa ai yana sa fahimta to se kaje ka fahimtar dashi amma bani ba. Karka yarda ka sake kirana in dai ba har kaje kun daidaita su da kansu suka ce aje ayi maganar aure ba, mutumin banza kawai a haka kamar namijin gaske ashe huhun ma'ahu ne" Al?ali ya kashe wayarsa ya bar Jafar ri?e da tasa cikin jimami.

Daya fito daga Wakin hajiya jin sa ya ringayi tamkar wanda akayi beli daga kurkuku. Duk wani nauyi da takura da yake ji a zuciyarsa sun sauka, farin ciki da annushuwa suka maye gurbinsu. Dukda cewa be so al'amuran suka kasance a haka ba yaso ace anyi komai ya faru cikin salama ba tareda rayuka sun Saci ba to amma babu yanda ya iya da abinda ubangiji ya tsara. Lamarin hajiya bame sau?i bane, shawo kanta ta yarda da lamarin cikin laluma ba abu bane da ze yuwu a lokaci kaWan amma yanzun da haka ta kasance yana fatan ubangiji ya ida yayyafawa abin ruwan sanyi, hajiyar ta karSi ?addararta kamar yanda ya rungumi tasa. Zuciya cike da muradin cikar buri ya kira Al?alin da zummar ya gaya masa hajiya ta yarda da sharaWin dan haka kome ya tabbata sannan idan ze yuwu a cikin satin aje a bawa Baffa ha?uri ayi komai a wuce gurin amma Baba Al?ali is acting stubborn, ya samu matsalar hajiya ta kau shi kuma ze shigo da wani abu daban banda haka me yasa zega laifinsa cikin abinda ya faru? Tun farko ai gurinsa ya fara zuwa neman mafitar be bashi ba kuma yayi abinda yake ganin shine daidai an samu matsala se kuma Wora masa laifi?

Share zancen yayi ya kama hanyar gida ransa fes domin yasan kome Al?alin ze faWa ze sakko ya wuce masa gaba tunda ai suma suna son auran. A parking lot ya tarar da Fatiyyah Liman yana goge mata mota tana ta zazzaga masa masifa kamar zata dakeshi, ya mata kallo Waya bayan ya fito daga motarsa ya wuce ba tareda ya ce mata komai ba amma ransa ya Saci da yanda tunda taga lako lakonsa ta dawo da daSi'arta ta fita ba tareda ta nemi izininsa ba sau da yawa yanzun wata rana kafin ya tashi ta fita ko ya fita ya barta a gida baze dawo ya tarar da ita ba rashin nutsuwar da yake ciki tasa baya kulata tunda daman abinda take nema kenan ya biyeta suyi Satacciya shi kuma yana Waga mata ?afa ne kawai saboda yanda al'amarin yazo mata yasan da wata ce daban ake wannan dambaruwar akanta ba zata damu kamar ace tsohuwar faccalarta ce Fatima Afeeyar da take tsananin adawa da ita saboda sanin da tayi itace rayuwar mijinta.

Wanka yayi ya shirya seda aka kira sallar azahar kafin ya fita daga gidan daga masallaci ya wuce gidansu Afeeyah bayan ya tsaya yayiwa su Nayla tsaraba ya haWa da food stuffs dukda wata be ko yi tsakiya ba kuma a farkon watan yayi musu siyayyar kayan abinci. Tare suka shiga gidan da Malam da zuwansa kenan shima. Umma na kitchen tana ?arasa aikin girki tana ta sauri dan za'a kaiwa su Layla tahfiz Waya suke fita break gashi har biyu saura Ahmad na cikin motarsa me chaji yanata yawo a tsakar gidan gwaranci da dariyarsa da ta jiyo tasa ta le?a ta window ta hango Jafar tsugunne a gabansa dan hankalinta yayi nisa bata ma ji sallamarsu ba.
?auke kai tayi taci gaba da zuba abincin a kula, a ranta tana jin idan akwai abu guda daya saka take Wagawa Jafar ?afa akan lamarin Afeeyah be wuce tarin ?aunar da yake nunawa marayun jikokinta ba.

Son da yake musu a bayyane yake, ta tabbata kuma babu wani mutum da Afeeyah zata samu a yanzu da ze ?aunaceta ya ?aunaci yayanta tamkar sa zata so ace yaran su samu gata da soyayyar uba wadda a gurinsa kaWai zasu samu sannan ta bar hakan a matsayin ishara ga ita Hajiya Binta duk yanda ta ?yamace su take wula?anta su saboda banbancin matsayi na wadata da ubangiji yayi musu se gashi suna nema su zame mata ciwon ido babu kuma yanda ta iya dasu. Ta tuna sanda tazo har cikin gidan tana ja mata kunne akan ta raba Afeeyah da Jafar a lokacin ma yana hidimta musu ne kawai a matsayin amanar yayansa be rigada ya fito da ainihin manufarsa ba zata so taga idonta a yanzu da al'amura suka canza salo kuma kodan ta nunawa Hajiya Bintan iyakarta zata bari ayi auran idan yaso ta haWiye zuciya ta mutu saboda ba?in cikin haWa jini da talaka.

Malam ya ?arasa kofar kitchen Win ya gaisheta ta amsa ta fito da kwandon data saka musu kayan abincin tana cewa
"Yawwa taimaka ka mi?a musu abincin nan makaranta, seda nazo Wora girkin na tarar gas ya ?are da?yar aka samo mun kaWan a bakin titi suma babu dama jira nakeyi kazo seka tafi da tukunyar gidan mai a zubo". Jafar ya gaishe ta ta amsa babu yabo babu fallasa hakan yasa yabi bayan Malam suka fita da Ahmad dan yanda ta amsa masa gaisuwar yasa jikinsa yayi sanyi kamar Umman na fushi dashi dukda dama ba wai tana sakar masa fuska bane tun da ya fara zuwa gidan.

A motarsa suka tafi a hanya ya rasa yanda ze yiwa Malam magana akan zancesa da Afeeyah se kawai ya ha?ura suka shiga hirar duniya, seda yayiwa malamin su Amal Win magana akan a rage mata aji tunda tace hadda tanayi mata yawa kafin suka dawo. Be shiga ba yacewa Malam a samo yara su kwashe kaya a booth, aka gama shiga dasu ya sauke Ahmad ya saka kuka Malam ya tambayeshi baze shiga bane yana shafa kai yace
"Naga kamar Umma fushi takeyi dani"
"Haba dai wane irin fushi kuma? Babu komai inaga dai aikin da takeyi ne yasa ka ganta a haka" Malam ya faWa, kafin ya sake cewa wani Abu Baffa ya Sullo dole ya sake komawa cikin gidan badan yaso ba saboda Baffan yace. Tare suka ci tuwon shinkafa da miyar gyaWar da Umma tayi haWe da zoSo me sanyi wanda har yanzu bata dena siyarwa ba. Yanda Baffa bece masa komai ba akan maganar da sukayi da Afeeyah yasa duk ya tsargu kuma ya kasa yi masa zancen shima. Ya gama yayi musu sallama ya tafi da Ahmad daya saka kuka seya bishi Umma ta Webo masa kaya kala Waya da diaper akan ko ze Sata na jikinsa suka wuce gidan Alhaji.

Tun a babban compound barorin gidan suka Wauke Ahmad wannan ya cafe wannan ya karSa yanda mahaifinsa yake da farin jini a gurinsu haka suke son yaransa musamman Ahmad Win da kowa ya ganshi zece tamkar marigayi. A falon hajiya ya tarar da ita sun haWa kai da Fatiyyah tamkar ?awaye suna ?us?us yana shiga kuma sukayi shiru Hajiya ta harare shi ita kuma Fatiyyan ta Wauke kai tana haWe fuska. Tamke tasa fuskar yayi ya zauna akan kujera yana fuskantar Fatiyyan yace
"Sau nawa zanyi miki kashedi akan Wakko maganganu kina zuwa kina tayarwa da mahaifiyata hankali?" Kafin ta bashi amsa hajiyar tayi tsugul tace
"Tazo Win, ai ni wlh a yanzu ta fiye mun kai sau dubu tunda ita ta san ?ima da mutunchi na tana kuma gudun duk abinda ze taSa su. Wato ni ka munafunta Jafar da kai aka haWa baki ake so aga bayana kai ka jagoranci kashe mun aure" ta fashe da kuka. Cikin tashin hankali ya zame ?asa gaban ta yana cewa

"Ya zakice haka hajiya? Ta yaya za'ayi da sanina na kashe miki aure?"
"Ai ta gaya mun komai. Ashe baki kuka haWa da Yakubu kaje ka saka matsiyacin mutumin nan ya kira Audu yace na je naci musu mutunchi ba zasu baka yarsu ba, har ina bugun ?irji akanka ina cin laya akan dama nasan ba zaka watsamun ?asa a ido ba ashe kaima ma?iyi nane ban sani ba. Amma nayi maka uzuri, sharrin ma?iya ne su sukayi tasiri gurin juya maka tunani amma ka sani koda nace na amince da auranka saboda kawai sharaWin da Audu ya gindaya mun kenan kuma ba zan yarda nayi asarar shekarun da nayi ina dakon lokaci in badan ma?iya da mahassada suna gurin kuma sun rigada sunji maganar bama da wlh ko sama da ?asa zata haWe bazan yarda da na sak....."

"Amma hajiya wannan ba maganar da za'ayi ta a gaban kowa bace ba" ya dakatar da ita sannan ya kalli Fatiyyah data baza kunne tana kwasar magana ya nuna mata ?ofa yace
"Tashi ki tafi gida, kuma wlh kika sake fitowa ba tareda na baki izini ba ki nemi inda zaki wuce badai gida na ba"
Cike da rashin kunya da kuma ta?amar a gaban hajiya suke ta ce masa
"Ban gane ba gidanka ba? Kana nufin sakina zakayi kome?" Ya mi?e tsaye yace
"Kin bawa kanki amsa. Duk yanda nake Wauke kai ina miki uzuri bakya gani, karki bari ki kaini bango kin sani sarai bani da kyau" ya faWa yana nunata da yatsa. Hajiya dai baki ta saki kawai tana kallonsa ta shiga tafa hannaye tana cewa
"Tabbas annoba ta tarar damu har gadajen baccinmu, yanda ubanka ya gindaya mun sharaWin saki kaima shi ka saka mata? Lallai dodonsu ya iya tsafi to wlh tallahi koda ba?ar jaka suka tsafance ka sena warware ba zasu taSa yin galaba akaina ba nafi

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login