Showing 297001 words to 300000 words out of 467220 words

Chapter 100 - MATAR MUTUM COMPLETED 1-3 BY MARYAM FARUK.doc

23 Sep 2025

12255

hankalin Ahmad yayi ba, be taSa jinsa yayi magana cikin raunin zuciya kamar haka ba, yanda yayin se kace ma mutuwar ce a gabansa tazo Waukar sa. Cikin sanyin murya yace masa

"Akwai sauran lokaci da zaka iya gyara komai Alhaji"
"Ta yaya?" Ya sake jefa masa tambayar se yayi shiru dan be san me zece masa ba kuma. Tun kafin a haifeshi yalalata komai ta yaya kuma ze tambayeshi yanda ze gyara yanzu, numfashi ya ajiye kafin ya sake cewa

"Ta yanda aka lalata nan za'abi a gyara Alhaji. Idan har ka yarda cewar kayi kuskure karka duba girma ko ?an?antar wanda ka Satawa, ka nemi yafiyarsu nasan ba zasu gagara yi maka afuwa ba in Allah ya yarda kuma komai ze dawo yanda ya kamata ace ya kasance".

Shiru Alhajin yayi yana sauraron Ahmad tareda auna kalamansa, kusan minti goma falon ya Wauki shiru Alhajin be ce komai ba Ahmad har yasha jinin jikinsa yayi zaton ko maganar daya faWa tayiwa Alhajin zafi ne se yaji yace masa

"Na sani Ahmad, amma ta yaya?"
"Ikon Allah" Ahmad ya raya a ransa a fili kuma ya gyara zamansa yace

"Kayi ha?uri Alhaji amma ina zaton ka fini sanin hanyoyin da zaka bi gurin gyara abinda kake ganin kuskure ne, idan kuma lallai kana bu?atar wanda zakayi shawara dashi ka nemi Baba Al?ali, akan idonsa komai ya faru nasan ze fini sanin dabaru da hanyoyin da za'abi a gyara"

"Shikenan, tashi kaje Allah yayi Albarka" Alhaji Audu ya faWa yana komawa cikin kujera ya kishingiWe, Ahmad yayi masa sallama harya kai bakin ?ofa ya sake dakatar dashi yana cewa
"Me yake damunka? Wannan ramar da kake yi ta lafiya ce kuwa?"

"Lafiya lau Alhaji, nadai yi zazzaSi kwana biyu toh ban gama warwarewa bane" ya bashi amsa yana shafa kansa. Alhaji ya tsare Shi da ido na wani lokacin kafin yayi masa alamar ya tafi da hannunsa. Bayan fitar Ahmad kogin tunani ya faWa, yana nan zaune har akayi kiran Azahar kafin ya tashi yayi Alwala ya fita masallaci.

HAJIYA BINTA
Guraren sha biyu hankalinta ya koma jikinta bayan data gama sharSar kuka kai kace nata mijin ne ya mutu, tana katarar Turai itace me karSar gaisuwa dan Turai babu baki, mutuwar Alin ta shammaceta kwarai kuma ta kaWata har zuwa lokacin ba za'a iya tantance halin da take ciki ba, ita batayi kuka ba amma bakinta gum ko gaisuwa akayi mata sedai ta amsa da kai Binta ce ta zama bakinta amma fa kana kallonta kasan tana cikin wani yanayin domin farat Waya ta zabge idonta yayi wuri wuri duk ta firgice abin dai se a hankali.

Abinci da aka fara rarrabawa yasa ta zabura ta fita waje ta hau kiran Sarah, shaf ta manta da wurwuri suka fito ko abin kari bata samu ta bawa Audu ba ga Azahar tayi yanzu. Sarah na kwance tana bacci dawowarta kenan daga makaranta taje Exam dan bata ma san da rasuwar ba se bayan data dawo ta kwanta akan idan an gama abincin da Momy tasa ayi za'akai se tabi Direba taje toh bata kai ga hakan ba sega wayar Hajiya.

Sallahu ta bata akan ta dafawa Alhajin farar shinkafa da miya,
"Da akwai markaWaWWen tattasai a firinji ki Webi iya wanda ze ishe shi kar kiyimu Almubazzaranci, kifi zaki saka ai kinsan wasa yake ci shima gunduwa biyu zaki saka a ciki, tumatirin yana da tsami ki duba a Waki na cikin wannan durowar ta saman mudubi da akwai kanwa ki Wakko ta ki zuba isashshiya karki manta ki tabbatar kin zuba da kin gama kuma ki mayar mun da ita inda kika Wakko kuma ki haWa masa salak da man zaitun, dan ubanki kiyi wani abu da ba haka nace ba zaki gamu dani idan na dawo" ta kashe wayar tana sake jaddada mata akan ta Wakko kanwar ta saka a miya.

Kamar yanda Hajiyar ta sakata nan da nan ta tashi ta fara haWa abincin dan daman ita tana son girki Shi yasa take son zuwa gidan Yaya Ahmad dan Fatima ma gwanace gurin iya sarrafa abinci, seda ta fara dafa Basmati rice Win ta yanka kayan hada salak Win kafin ta fara haWa miyar, harta zubawa tattasan mai ta tuna da kanwa da Hajiya ta ringa nanata ta zuba dan haka ta tafi ta Wakko ta robobi uku ta gani cike da ruwan kanwar ta koma kitchen a ranta ta tunanin wai me yasa Hajiya take amfani da kanwa ne a komai da zatayi? A ganinta bema kamata ace ana sakawa Alhaji kanwa a abincinsa ba saboda yanayin shekaru ga kuma Bp da yake dashi amma tun suna yara tasan Hajiya ko ruwan shayi zata dafawa Alhaji seta zuba kanwa kamar yanda take ce musu magani ce tana ?ara ?arfin ?ashi ?arya likitoci sukeyi da suke cewa a dena amfani da ita, tasan idan bata saka ba yau ba zataji kunne a gidan ba muddin Hajiya ta WanWana miyar nan tajita ba yanda ya kamata ba ta kaWe.

Da mugun sauri ta kawar da robar kanqar daga fuskar ta bayan data buWe ta saboda wani mugun Woyi da hankali da duk wani abu mara daWin sha?a daya kaiwa hancinta ziyara nan da nan yawu ya fara tarar mata a baki zuciyarta ta shiga hautsinawa duk yanda taso ta ri?e kanta kasawa tayi seda tayi amai kafin ta samu salama. Tana mayar da numfashi tana kallon robar dake cike da ruwan bala'i dan ba zata kirashi kanwa ba, ta cire dankwalin kanta ta Waure hancinta dashi kafin ta sake daukar jarkar tana ?o?arin son gane abinda yake ciki, ruwan nada dan kauri da yau?i tamkar Yawun bacci, da ido take kallonsa amma take zuciyarta ta sake juyawa ba shiri ta shiga tuttular dashi a cikin sink, Wakin ta koma ta Webo sauran jarkoki biyu duk abu Waya ne a cikinsu take ta zubar dashi ta fita da robobin can bolar tsakar gida ta watsa su ta koma ciki tana maida numfashi.

Ba kalar disinfectant da bata saka ta wanke sink Win ba kafin ta sauke ajiyar numfashi ta feshe kitchen Win da freshener ta kunna turaren wuta, kayan miyar data dora ma wankesu tayi suka bi rariya, ita kanta seda tayi wanka kafin ta iya sake diban wani ta fara haWa miyar a ranta tana mamakin tsayin shekarunta da wannan kanwa ta Wiba a ji?e da har ta koma Acid, ungurnu ta ji?a bayan ta gama miyar ta samo wasu robobin ta cika mata su da ruwan saboda tasan halin Hajiyar babu lallai tasan kanwar ta lalace ba kuma zata bata damar tayi mata bayani ba gara kawai ta maida mata abinta baki alaikum, ranar wuni tayi ko abinci ta gagara ci saboda warin kanwar Hajiya daya gagara barin tunaninta duk uban turaren data fesa bata dena jinsa a hancinta. Da taje gidan rasuwar abinda Hajiyar ta fara tambayarta kenan ta dai zuba kanwa a miyar ko tace mata eh, Momy ce ta karSi girkin dare amma duk da haka Hajiyar tace mata idan ta koma ta dafawa Alhajin shayi ta kai masa.

"Karki manta ki Wan saka kanwar kaWan a cikin shayin fa" Hajiyar ta faWa mata, ba ba?onta bane shayin kanwa tun suna yara suke sha seda sukayi hankali suka fara shiga kitchen da kansu sannan suka yayewa kansu jidalin Hajiya Alhaji ko babu fashi idan be ci a abincinsa ba zesha a shayi ko a lemo kai duk abunda Hajiyar zata bashi yaci se ta zuba kanwar nan a ciki ta yuwu shiyasa ma ta ji?a ta ta daWe harta lalace bata sani ba, tuno kanwar Wazun yasa zuciyarta ta fara tashi, haka ta ringa tauna cingan har Allah yasa ta kwanta.

Seda aka share kwanaki bakwai na karSar gaisuwa kafin Hajiya Binta ta koma gida gaba Waya taci gaba da addabar Turai da tambayar yaushe za'ayi musu rabon gado se kace tana da kaso a ciki. Sanda ta nutsu a gida girkinta ya wuce ranar Momy ta sake karSar, da daddare ta dafa shayi kamar yanda ta saba yi koma girkin waye, harta juye Shi a flask ta tuna da bata zuba abinda ya dace ba dan haka.

Seda ta jujjuya robobin a hannunta tana kallon ruwan ciki kafin ta Wauki Waya ta koma kitchen ta mayar da ruwan shayin ta buWe kanwarta ta kwarara a ciki tana murmushin mugunta sannan ta ?ara flavour data saba saka masa ta jira ya sake tafasa ta juye. Seta ji yanayin shayin beyi mata yanda ta saba ba amma dai taji daWin hakan ko ba komai ze sha kai tsaye ba tareda yayi mata ?orafin daya sabayi ba. Harda shafa hoda da turare dan akwai abinda take so ta aiwatar ta Wauki farantin kayan shayin ta wuce Sangaren Alhaji Audu.

Yauwa ko kefa, kwata kwata bana son wannan gahawar da kike zubawa a cikin shayi ke kanki ya kikaji ?amshin wannan da wanda kika saba dafawa?" Alhajin ya faWa bayan daya kurSi ruwan shayin, tayi dariya yana sha suna taSa hirar rasuwar Alhaji Ali tana labarta masa yanda Turai ta zama abar tausayi.
"Yan uwansa nacan sun kasa sun tsare so sukeyi su cuceta ba zasuyi musu rabon gado na Allah da annabi ba Allah sarki Turai musamman da duka yayanta mata ne se abinda aka yafita mata kawai kai wlh nayi takaicin mutuwar Mu'azzam da yanzu babu uban wanda ya isa ya tsoma musu baki a cikin gado" Binta ta marairaice tana faWa, Alhaji dai na kallon Tv yana shan shayi bece mata komai ba taci gaba da cewa

"Ni wlh da zaka shiga maganar ka tsaya tsayin daka se anyi mata Adalci in ba haka ba cutarta zasuyi" ta ringa nanata maganar shidai be kulata ba can ya tashi da sauri dalilin cikinsa daya murda masa ya wuce sama ya barta, abu kamar wasa yana shiga banWaki ya tsuge da gudawa, a Wakin ya kwanta yana maida numfashi lokaci Waya kanshi yayi zafi jikinsa yayi masa nauyi ga jiri na kwasarsa daga kwancen da yake kafin wani lokaci idanunsa sun fara duhu be sake sanin meke faruwa ba daga ?arshe se farkawa yayi ya ganshi kwance a gadon Asibiti Dr Charles na tsaye kansa yana duba ruwan da aka ma?ala masa.

Bakinsa Wauke da salati ya yun?ura ze tashi kansa ya sara dole ya koma ya kwanta, Dr Charles ya shiga jera masa sannu tare da tambayar me yake yi masa ciwo ya nuna kansa.

"Sannu Alhaji, ka kwanta kaWan karkayi motsi me ?arfi kan ze sarara" Likitan ya faWa masa cikin tabbatar wa seya Waga masa kai kawai a ransa yana tunanin meya sameshi har aka kawoshi Asibiti be sani ba?

Kusan minti talatin yana kwance kafin nauyin da kansa yayi masa ya ragu lokacin kuma aka cire masa ruwan daya rigada ya ?are, a hankali ya tattaka yayiwo Alwala yayi sallar Asuba da Azahar da suk wuceshi yana kwance, Hajiya Rabi tazo da abinci ita ya tambaya ya akayi aka kawo shi Asibiti tace masa suma suna cikin gida kawai Hajiya Binta ta fasa ihu tace suzo ya mutu, da sukaje suka tarar dashi cikin gudawa kaca kaca shine aka tattaroshi aka taho Asibiti bayan an masa gwaje gwaje kuma likita yace musu Jininsa ne ya hau Sacin cikin kuma ya faru dalilin wani abu daya ci, Binta dai tana gida daman bata bisu ba Waki ta shige tana addu'ar Allah ya yanke mata ace dagaske Alhajin mutuwa yayi dan ita sanda akace Alhaji Ali ya rasu a ranta seda tace daman Audu ne ya rasu bashi ba sega Alhajin yayi jinyar kwana biyu an sallamoshi ya dawo gida bayan da likita ya sake gargaWin Hajiya Rabi wadda ita tayi zaman jinyarsa kan kula da abinda zeci da wanda ze sha.

Sannan da yaje gidan sake dubashi ya tara su ukun duka ya sake jaddada musu da su guji sakawa Alhajin kanwa da gishiri a abincinsa dan kanwar ce musabbabin kwanciyar tasa, sun samu trace Win ta da yawa a cikin jininsa dan haka a kiyaye. Hajiya tayi tsilli tsilli ganin yanda duk suka zuba mata ido har Alhajin domin dai kowa yasan itace take girki da duk abinda aka lissafa shidai likita ya musu sallama ya tafi, yana fita itama ta bar falon kamar zata kifa ta wuce Wakin ta ta fiddo da robobin ta shiga dubasu, kadan ta tsiyaya ta shanshana kafin takai bakinta ta WanWana gafin kanwa coiii daga ji ungurnuce kuma an ji?a ta da yawa.

Ashariya ta kwaso me mai?o ta lailaya ta buWe ragowar robobin suma dai kanwar ce a ciki tsabar yanda ranta yake tafasa bata san sanda tayi ball dasu ba duk suka kelaye a tsakar Wakin kafin ta shiga kwazarawa Sarah kira kamar ma?ogaronta ze tsage ta nufi Wakin da take. Seda ta fara yi mata Sarin makauniya kafin ta shiga jibgarta kamar Allah ya aikota tana zaginta,

"Dan abu ta kazanki me kika canza mun dashi? Ina kanwar da take cikin robobin uban meye wannan ki zuba mun?" Take faWa tana jibgar Sarah dake ihun neman agaji amma babu dama dan Hajiyar ta datse ?ofar falon a garin sauri sanda ta shigo kuma dole ta ciki ake buWe wa indai bada mu?ulli ba.

"Gani nayi ta lalace wallahi shiyasa na zubar na ji?a miki sabuwa" Saran ta faWa da taga Hajiyar na neman nakasata, aiko ta saketa tayi baya tana dafe ?irji da hannu biyu tace

"Kikayi me?" Ta lailayo Ashariya me naso ta danna kafin taciga da cewa
"Kin san menene kika zubar mun? Kin san wata nawa nayi ina wurudinnan shine kika rusa mun komai? Allah ya isa tsakanina dake Saratu kin cuceni bazan taSa yafe miki ba, shikenan kin sake maido dani farko rayuwata ta sake shiga tangal tangal, sati Waya ya rage mun na kammala aikin kin cuceni kin tarwatsa mun komai innalillahi wa'inna ilahi raji'un" Hajiyar ta faWa tana kuka shaSe shaSe kafin ta zube kan kafet kamar yarinya tana shure shuren ?afa kamar me Shirin hawa Bori, ita dai Sarah data samu ta saketa da gudu tayi ?ofa ta fice daga falon, a tsakar gida ta kwanta tana kuka dan ba ?aramin duka Hajiyar tayi mata ba.

Momy ta kamata ta kai tsaye ta kaita gurin Alhaji tana mamakin me tayiwa Hajiya Bintan haka da yayi zafi tayi mata wannan dukan, daga ita har Alhajin shiru sukayi suna sauraron Sarah data faWa musu abinda take zaton ya tunzura Hajiyar ta daketa,
"Wlh Woyi kanwar takeyi har yau?i ruwan ya fara shiyasa na zubar na ji?a mata sabuwa" Sarah ta faWa tana sake rushewa da kuka Momy na lallashinta ?asan ranta fal da tunanin wasu abubuwa da ta gani da idonta a shekarun baya wanda kuma sune musabbin daya saka ta dena WanWana ko farin ruwa ne ya fito daga Wakin Hajiyar kuma ta hana yayanta.

Da idonta biyu ta taSa ganin Hajiyar a kitchen ta kuskure baki ta zuba ruwan a cikin miya, na farko data gani Wauka tayi gizo idonta ya mata ba daidai ta gani ba, seda ta sake ganinta a karo ka biyu sannan ta tabbatar da cewar da gaske ne na farkon ma daga nan kuma ta haramtawa kanta cin duk wani abu da Hajiya ta dafa ko ta saka aka dafa, sannan ko ita take da girki ta dena matsawa daga kan tukunya harse ta sauke ta raba ta bawa kowa nasa sannan hankalinta yake kwanciya.

Sannan bata mantawa akwai sanda Jafar ya taSa ce mata Hajiya tana zuba yawu a abincin Alhaji dukda abinda ta taSa gani a baya seta Wauka dai wasu Walamisan siddabarunta take karantawa ta tofa masa ya ci...

"Kuje da ita tayi wanka tasha koda panadol ne, idan kuma ya kama se an kaita Asibiti ki haWata da Salim suje" Alhajin ya dakatar mata da tunani haka ta sake kama Saran suka wuce, data cire riga bayanta duk shatin yatsun Hajiya kamar na fuskar ta kai kace da bulala ta daketa ko wane irin ?arfi ne da hannun Hajiyar se Allah haka ta daddana mata da ruwan zafi ta bata maganin tasha da taji dama dama tace ba se an kaita Asibiti ba amma fa Wakin Hajiya tayi sallama dashi daga nan har zuwa wata biyu masu zuwa da za'a aurar dasu kayanta da suke can a taimaka a samu wanda ze Webo mata.

Hajiya kuwa bayan data sha kuka ta godewa Allah wayarta ta rarumo ta kira Turai, abin takaici se ?anwar ta ta Waga tace mata suna Asibiti Turai bata da lafiya.
"Me ya sameta?" Ta tambayeta daga can ?anwar Turai tayi ajiyar numfashi tace

"Toh abin ne dai gashi nan kamar bugun iska za'ace ko jifa, ana zaune kawai ta hau zabure zabure tana maganganu da kiran sunan marigayi, to yau da safe kuma abin ya ta'azzara kawai gani mukayi ta falla da gudu wai gurin Ali zataje ta nemi yafiyarsa shine fa aka rirri?eta da ?yar, munce akaita gurin masu ru?iyya Halima tace Aa shine aka kawota nan Asibitin Malam todai an mata Allurar bacci likitan ?wa?walwa ake jira yazo ya dubata"

"Na shiga uku ni Binta, likitan ?wa?walwa haukacewa Turai Win tayi? Lallai kice tawa matsalar me sau?i ce" Hajiyar ta faWa tana zare ido kafin ta ajiye wayar ta shiga safa da marwa a cikin Wakin, jimamin halin da Turai take ciki ta fara da kuma ta tuna Asarar da Sarah ta janyo mata seta fashe da kuka wiwi ta zauna ta haWa kai da guiwa tana rera kukan.
*MATAR MUTUM*
*NA MARYAM FAROUK (UMMU MAHEER*

*FIKRA WRITERS ASSOCIATION*

*LITTAFIN KUDI NE*
*PAY 500 A ASUSUN*
*7061838488*
*OPAY DIGITAL SERVICES*
*MARYAM FAROUK*
OR
*0709290797*
*ACCESS BANK*
*SE A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488*
*IDAN KATINE A DAUKI HOTONSA A TURA ZUWA LAMBAR SAMA VTU KUMA A TURA A 08142548705*

*Kuyi following dina a Arewabooks @Maryamfarouk01 inda zaku karanta wannan littafin tareda sauran littattafaina*
*NAGODE*

*BOOK 3*
*PAGE 14*

"Ahmad" Alhajin ya kira sunansa cikin sauti me rauni kafin ya ciga da cewa
"Ina tsoron nayi mutuwar farat Waya irinta Ali na tafi na bar zuri'a a ta a yanda take yanzu"

Yanda Alhajin yayi magana ba ?aramin dugunzuma hankalin Ahmad yayi ba, be taSa jinsa yayi magana cikin raunin zuciya kamar haka ba, yanda yayin se kace ma mutuwar ce a gabansa tazo Waukar sa. Cikin sanyin murya yace masa

"Akwai sauran lokaci da zaka iya gyara komai Alhaji"
"Ta yaya?" Ya sake jefa masa tambayar se yayi

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login