Showing 462001 words to 465000 words out of 467220 words

Chapter 155 - MATAR MUTUM COMPLETED 1-3 BY MARYAM FARUK.doc

23 Sep 2025

12387

yayi pecking goshinsa ashe shima yana da rabon ganin irin wannan ranar. So yayi ya shareta ya nuna ta masa abinda beji daWi ba amma kasa, ya koma kusa da ita tareda babyn ya haWa su ya rungume yana ce mata sannu.

A asibitin ya kwana tare dasu rungume da baby in har ya ajiye shi to ya bu?aci abinci data shayar dashi kuma ze sake karSa ya cigaba da jijjigensa washe gari da yamma aka sallamesu suka wuce gida, kwananta biyu da haihuwa suka wuce Nigeria har sannan kuma babu wani nasa daya sanarwa da zancen haihuwar ita dai ta kira yan uwanta ta gaya musu ba kuma ta tambayeshi dalilin ?in sanar da nasa yan uwan ba, ranar da suka dawo kai tsaye a gidan Alhaji Audu suka sauka, yana ri?e da babyn taba binsa a baya suka shiga falon Alhaji suka tarar dashi da Baba Al?ali, Alhaji Audu ya ringa murmushi yana kallon yaron Al?ali yace
"Allah kenan, yanzu da ina Binta take so akai wannan rabon?
A cikin gida kuwa irin kukan da hajiya ta ringayi bayan da aka baya jararin ya saka kowa a mamaki domin basu fahimci dalilin sa ba, gashi dai ta ?wa?wume yaro kamar zata maida shi ciki kuma tana rusa kuka har seda Baba Bilki tace

"Ke dai bakya gajiya da barin abin magana Binta. Ga dai Wa kin rungume ko makaho ya shafa irin wannan ru?o yasan na soyayya ne to shi kuma kukan na uban meye kikeyi saboda Allah kuwa dan ba wadda kike so ce ta haife shi ba?"

Cikin kuka ta girgiza kai murya bata fita tace
"Kukan murna ne Bilki, na godewa Allah da ya sa naga Wan Jafar a hannuna, koda ban so uwarsa ba ai shi jinin Jafar ne dole zan so shi babu kuma abinda ze saka na ?ishi tunda babu abinda yayi mun"

"Hali zanen dutse, Binta ba zaki taSa sauyawa ba. To se ki bamu mu Wauka mu da muke son Wan da uwarsa se ki jira idan wadda kike so ta haihu se ki ri?e wannan namu ne" Baba Bilki ta faWa tana ?o?arin karSar yaron daga hannunta amma ta?i sakar mata kamar zasuyi kokawa a tsugunnen da take ta babbake ba zata bada yaron ba seda ya canyara kuka saboda wujijjigar da suke masa kafin ta mi?awa Jafar dake tsaye zuciyarsa cike da mix emotions. Yanda Baba Bilki ta faWa ne ?arara kowa yaga soyayyar yaron a bayyane ga hajiya amma furucin da tayi na ko bata son uwarsa ai shi zata so shi be masa daWi ba, at least ko ba zata iya yin shiru ba ba a gaban Afeeyah ba bayan abin kirkin data musu ta haifa musu sanyin idaniya babu sannu ai bata bita da wannan maganar ba. A sanyaye ya karSi yaron ya mi?a mata shi ta amsheshi seta mi?e daidai nan Hajiya Zubaida ta shigo fuska a washe tana cewa

"Yawwa toh muje gashi can na gyara miki Waki se kiyi wanka ki huta" ta karSe babyn ta fita Afeeyah ta bita a baya hajiya ta rakasu da harar ?asan ido. Allahya fita sanin dalilin ?in mutanen nan guda biyu ta rigada da karSi ?addararta ba yanda ta iya Allah yayi Fatima ce uwar Wan Jafar na farko babu yanda ta iya. Kafin yamma gidan se kace ranar ake suna, har dare Afeeyah nata jiran taji Jafar yace suzo su tafi amma shiru sema akwati daya ciko mata da kayanta ya kawo kayan baby dama ta ware na amfani cikin siyayyar da suka taho da ita dan sunyi dashi akan can gurin Ummanta zata zauna ko na sati Waya ne yanzun kuma ya canza baki amma dai da sau?i tunda ba Wakin Momy aka ce ta zauna ba balle kuma gurin hajiya wannan kam kai tsaye zata ce ba zata zauna ba.

Washe gari yan uwanta suka zo, babyn na gurin hajiya tun da aka masa wanka da safe ta turo aka Wauke shi yana hannunta idan ta gaji da ru?o ta bayar a kwantar dashi a dan gadonsa da aka haWa duk wanda ya shigo sedai ya le?a can yaga baby tayi mirsisi ta?i kula Hussani daya zauna ya ringa zuba mata tsiya yana cewa
"Billahillazi hajiya Allah ya so ki, yanzu ke da wannnan sadaukin kika so ki hana a haifa? Kin ganshi dai beyi ruwan wanda ze zo a shege ba to da kin matsa haWe budiri suna zamuyi da addu'ar wata taranki dan bama zamu jira se kin cika shekara ba amma dai Allah ya so ki, dama na siyo miki wheelchair irin me motor Win nan tana nan za'a kawo kya samu ta shiga filin rawa ki Wan taka daga zaune" ya Wauke yaron ya fita dashi dan dama Alhaji ne ya turo shi ya Wauke shi akwai wasu mutanensa da suka zo ya gaya musu anyiwa Jafar haihuwa zasu ganshi. Yana fita ya fashe da kuka kuwa, dagaske ba da ace ta matsa ?ila da Yanzu babu ita se ?addarar ta tsaya a kan aurenta.

Kwanan Afeeyah huWu da haihuwa Fathiyyah ma ta haihu namiji, tunda Jay ya tura mata hoton baby wai Fatima ta haihu take kuka kusan abinda ya taso mata da haihuwar kenan daga ?arshe ma se CS aka mata ta samu yaronta kyakykyawa kamar yayansa, yanda suka ci buri akan haihuwar tun ba da aka ce mata namiji bane ta gama shiryawa ita zata zama uwar magaji amma lokaci Waya shirinya ya wargatse ace Fatima ta haihu kuma namiji ta ringa tunanin toh ya akayi bata lura da tana da ciki ba sanda suka dawo kuma tsabar munafunci me yasa be taSa gaya mata ba amma ita duk motsin nata cikin seya labartawa Fatiman. Ta ringa fushi da Jafar Win yaje ma ko kulashi batayi ba shi kam ko a jikinsa shima ya shareta yana ta lelen Wansa farin cikin da yake ciki ma baze bari ya biye mata ta Sata masa rai ba yayi musu kwana biyu sannan ya koma Kano ana gobe sunan babyn Afeeyah da yayiwa huWuba da Ahmad ba yanda Al?ali beyi dashi akan ya saka masa wani sunan ba yace Aa, al?awari yayi tun be san kansa akan Wansa na farko Yah Ahmad zeyiwa takwara kuma Allah ya amsa masa ya bashi namiji ace ba ze saka ba ai haka baze yuwu ba.

Randa????''''''' '
' ' '
''''''''''''''''''' '!'"'#'$'%'&'''(')'*'+','-'.'/'0'1'2'3'4'5'6'7'8'9':';'<'='>'?'@'A'B'C'D'E'F'G'H'I'J'K'L'M'N'O'P'Q'R'S'T'U'V'W'X'Y'Z'['\']'^'_'`'a'b'c'd'e'f'g'h'i'j'k'l'm'n'o'p'q'r's't'u'v'w'x'y'z'{'|'}'~''?' Fathiyyan ta haihu Alhaji yace masa shikenan se a canza tunda ita Fatima tana da Ahmad to ya sakawa babyn Fathiyyah kai tsaye yace masa shi fa Aa ranar suna kuwa aka raWawa babyn Afeeyah Muhammad Ahmad, taro sosai iyalan gidan sukayi babu wanda be zo ba maza da mata haka yan uwan hajiya Binta ran Fathiyyah da Mamanta ya ringa suya da suka ga hotunan sunan har kuka seda tayi Maman ta ringa cewa wai hajiya ta munafunce su in har dagaske ne bata ?aunar Fatima ya za'ayi ta bari ayi irin wannan bikin saboda ta haihu kuma ko barka bata jewa Fathiyyah ba dukda sun san a tsugunne take babu ?afa kuma ai yan uwanta sunje da ?anne da yayyen Jafar Win harda matan yan uwansa tun suna Asibiti wasu kuma sun bari se ranar suna. Saboda haushin budirin da akayi na sunan Ahmad ?arami hotunansa da Afeeyah duk in da ka shiga a social media zaka gansu Fathiyyah tace ita ba zatayi sunan ba yace ta huta dan haka ranar kwana bakwai duk wanda yayi niyar zuwar mata suna data Sangaren sa sukaje da kayan barka tuli suka juyo a ranar shima Jafar Win daga can ya koma Paris cike da kewar yaran sa.

Cikin aminci Afeeyah ta cigaba da jego a Wakin Hajiya Zubaida, yanda matar take kula da ita ba ?aramin daWi takeji ba domin ko ita ta haifeta ?arshen abinda zata mata kenan. Hankalinta a kwance take jego tasha bacci ta godewa Allah tsakaninta da Ahmad se shayarwa safiya nayi aka masa wanka za'a kaiwa hajiya shi in dai ba kuka kuma yayi ba ba za'a dawo mata dashi ba kullum da safe itama tana shiga ta duba hajiyar bata dai zama data gaisheta zata fita dalilin babu fuska ko gaisuwar ba kullum take amsa mata ba sau tari ma dariya abin yake bata kuma dai tana yiwa hajiyar uzuri tunda a ?alla albarkacin baby Ahmad harsu Amal yanzu suna shiga Wakin hajiya su zauna tareda ?anin su ba kuma ta kyarar su ko hantara yanda take musu a baya har yasa suke tsoronta ko da yake ina lafiyar da zatayi hakan tunda magana ma kullum kamar ana sake zu?e mata murya wani sa'in ma ba'a gane me ta faWa seta maimaita kamar harshenta yana harWe, duniya dai abin tsoro aka ce gani ga wane kuma ya ishi wane tsoron Allah.

Haka rayuwa taci gaba da juyawa yau fari gobe ba?i, sun koma gidansu gaba Waya sakamakon Jafar yayi retire daga ?wallo ya dawo gida gaba Waya a lokacin kuma aka fara zama na gaskiya da gaskiya. Alhamdulillahi, shine abinda bata gajiyawa da maimaitawa a kullum cikin halin farin ciki ko akasin haka. Abubuwa da yawa sun faru, rayuwa ta girgiza tamkar zata kife amma cikin hukuncin Allah gashi komai ya zo ya wuce tamkar ba'ayi ba. Soyayyarta da Ahmad, shigowar Jafar rayuwarta zuwa rabuwarsu, auren Ahmad zuwa rasuwarsa abubuwan da suka biyo baya har zuwa yanzun da take amsa sunan Jafar wasu darusa ne masa zaman kansu mabanbanta. Ta san daWin so da auren soyayya ta kuma san daWin auren wanda yake sonka kuma da ace za'a sake bata zaSi a yanzu tabbas zata zaSi maimaita zama da Ahmad sama da Jafar ba kuma dan ta dena son Jafar ba ko ta raina irin kulawa da soyayya da yake gwada maya Aa se dan a yanzu da tayi hankali ta fahimci ainihin rayuwa da abinda ta ?unsa ta kuma gane ba iyakar zallar soyayya bace aure akwai wasu abubuwan da suka sha gabanta wanda hali shine kan gaba. Soyayya takan gushe hali shiyake zaunar da mutum ta kuma sake gasgata karin maganar da hausawa suke cewa zama lafiya yafi zama Wan sarki amma ba zata butulcewa ubangiji ba kullum cikin godewa masa take tana kuma ro?onsa daya cigaba da dafa mata badan halinta ba domin ba wayo ko dabararta bane ya bata komai.

Hajiya Binta da ta zuba sharafi ta shimfiWa mulki tamkar babu ranar hisabi yanzu ta zama abin tausayi kusan duk waWanda a da suke da fushinta idan suka kalleta a yanzu gani suke ma to menene abin cigaba da ri?on ta a zuciyarsu shiyasa lokacin bikin Salim da suka haWu a gidan tana kuka ta nemi su yafe mata abubuwan da suka faru a baya kamar Hussaini ce mata yayi shi tunda uwarsa ta koma gidan ya yafewa kowa ma kuma shi dama be taSa mata kallon me hankali bama dan haka babu dalilin da ze saka ya tsaya yana Sata lokacinsa akanta, duk abinda ya faru a baya laifin wanda ya aurota ya kuma zauna tana juyashi ya gani domin idan da bata samu lasisi a gurin Alhajin ba ai da ba zatayi duk abinda tayi a baya ba. Yayan Hadiza ma dai sunce sun yafe mata abinda yake tsakaninta da mahaifiyarsu wannnan kuma Allah ya fisu sanin yanda zeyi dasu tunda dai ba zasu ari bakinta suci mata albasa.
Babban abinda yafi Waga mata hankali wanda kuma shiyafi damunta shine yayan Bara'atu suka ?i saurararta. Har Al?ali seda ya saka baki amma Babannan yace idan mahaifiyarsu zata dawo doron duniya to ze yafewa Binta. Har yau kusan shekaru hamsin ba'a dena goranta musu akan sharrin da ta bibiyi mahaifiyarsu da shi ba, ba'a daWe ba yarsa sukayi faWa da kishiyarta haka tace mata waye besan kakarsu ta kashe Wan kishiyarta ba shiyasa ta haWiyi zuciya ta mutu saboda kowa ya?i aurenta a garinsu seda yasa aka kulle mijin aka kulle kishiyar yan sanda sukayi musu tsakani kafin yarinyar ta samu sararin watayawa a gidan mijinta shi da yake zaune a Bechi shi yasan irin tasirin da tuggun da Binta ta haWawa mahaifiyarsu yayi akansu, labarin ya zama tamkar wani tarihi da ba'a so ya gushe kullum cikin tisa shi akeyi badan tsayayye bane shi Win da yanda mutanen karkarar zasu takashi su ringa goranta masa abin ai da ba za'a ce komai ba amma dake a tsaye yake yayi maganin duk wani shege daya nemi ya kawo masa raini. Har Jafar seda tasa ya ro?ar mata su yace baze iya ba, aikata ganganci a matsayin kuskure gurin mutane sun Wauke shi kamar wasa, mutum na sane zeyi abunda yasan bana daidai bane cikin ta?amar ze gyara wata rana ko kuma ya Wauka yaci banza a lokacin da kuma ze fahimci kuskuren sa be zama lallai yana da damar da ze gyara ba tamkar dai lamarin Hajiya Binta da Bara'atu a yanzu.

Bata tuna cewar irin wannan ranar zata zo mata da zatayi fatan gyara kurakurenta na baya ba a sanda Bara'atu zasuyi tafiyar da bazasu dawo ba har cewa tayi idan har ta fito ta faWi gaskiyar abinda ya faru zata yafe mata idan ba haka ba kuma sedai su ?arasa shari'arsu a gaban Allah a lokacin ai wasa ta dau?i al'amarin tayi biris yanzu da bulalar nutsuwa ta bugeta ta fahimci tana bu?atar afuwar mutanen data zalunta kuma babu Bara'atu iya kar ha??in ta kaWai ya isa ya wujijjiga rayuwarta sannan taje lahira ta karSi sakamako idan ta tuna wannan abun ji take kamar zuciyarta zata tarwatse saboda tsoro har mafarki take da Bara'atu tana sake jaddada ba zata taSa yafe mata ba wannan kuma shine musabbabin sake ta'azzara ciwon dake nu?ur?usar jiki da ruhinta.

**********************************
Conference hall, Bechi groups
Al?ali Yakubu ya share hawayen dake zuba akan fuskarsa muryarsa na karyewa yace
"Na godewa Allah daya sa nayi tsayin rai har naga irin wannan lokacin da zuri'ar Audu ta Winke ta zama abu guda Waya Allah sarki Ahmad nasan duk inda kake kana kallonmu kuma cike kake da alfaharin cikar burinka, abinda kayita ha?ilo akai a ?arshe ubangiji ya amsa ya kawo daidaito a tsakanin ahalin mu" ya kalli Alhaji Babangida yace
"Allah ya taya maka Tijjani, girman ya sake hawa kanka saman wanda kake dashi. A tsayin shekarun da mahaifinku yayi yana jagoranci dukda irin faWi tashi da zagon ?asan da wannan rukunin kamfanunnukan ya fuskanta be taSa dur?ushewa ba, babban jigon kuma daya kaishi ga wannan mataki shine gaskiya da amana domin duk wanda yasan Audu ya kumayi mu'amala dashi ze bada shaidar sa akan abu biyun nan ri?on gaskiya da kuma amana. Ina fatan ka gaji mahaifinku ta fuskokinsa na Alkhairi domin Audu mutumin kirki ne, ko wanne Wan adam yana da tasa tawayar sannan rayuwar mumini bata taSa cika har se an jarabci imaninsa Alhamdulillah ina taya Wan uwana murna da be bar duniyar nan ba har seda ubangiji ya haska masa kurakurensa kuma ya gyarasu gwargwadon damar da ubangiji ya bashi.

Ina me yi maka nasiha da ka ri?e gaskiya ka kuma daidaita tsakanin yan uwanka, yanda suka Wauki amanarsu data iyayensu suka dam?a a hannunka ina fatan ubangiji ya taya maka ya baka ikon fita kunyarsu" ya juya kan sauran da kowanne ya sunkuyar da kai ?asa yace
"Dukkaninku akwai Sangarorin da kuke kowane yana da irin rawar da ze taka a cikin wannan tafiyar wanda kuna kuskuren Wayan ku ya shafi kowa da kuma komai. Jajircewarku ce zata sake tabbatar da legacy na wannan kamfanin, sau da yawa mutane sukan ?are rayuwarsu gurin gina wani al'amari a rayuwarsu amma da zarar sun gushe iyalansu sukan kasa cigaba da ri?e ragamar abinda aka bar musu daga nan kowanne irin kasuwanci ne seya dur?ushe. A ko ina tafiyar biyu tafi Waya, na sani a nan kowannenku tsaye yake da ?afarsa sedai akwai lokacin da za'a kai da mutum ze gajiya amma ya kuke tunani idan akace ?afofin nan da yawa dole idan wata ta gaji wata zata taffa mata toh amfanin haWi kai kenan ubangiji ya albarkace ku yayi muku yawan da zaku share hawayen junanku ba tare da kun nemi taimakon kowa daga waje ba. Ina fatan yanda kuka zaSi cigaba da tafiya tare ku tabbatar da hakan ta hanyar bayarda duk wata gudummawa da wannan tafiyar take da bu?ata. Ina ro?on Allah daya tsare ku daga shaiWan me burin wargaza aikin Alkhairi, ina ro?on Allah daya dawwamar da niyyarku ta aikata daidai, duk abinda ze kasance sharri a tattare da zumunchin ku Allah ya nisanta ku dashi walau mutum ko dabba ko wani abu duk abinda ze sanya wasi wasi, mugunta, ?yashi ko hassada a zukatanku Allah ya nisanta ku dashi. In sha Allah yanda muka taru a nan haka zamu sake taruwa a filin barka cikin farin ciki zumunchi kuma ya cecemu zuwa ga farin ciki madawwami.

Ta yuwu wannan ne zama na daku irin haka na ?arshe, bara Audu ne akan wannan kujerar da Babangida yake kai a yanzu yau gashi baya nan, Zakariyya ma yana tare damu shima yanzu babu zuwa baWi bamu san wanda ze kasance da wanda base kasance a nan gurin ba dan haka ina sake jaddada muku da ku kyautata mu'amala ku sadar da zumunchi, kuyi kyauta kuyi sadaka kuyi soyayya saboda Allah kada kuma ku tsananta ?iyayya domin al'amarin ubangiji me juyawa ne".

Shiru ya ratsa gurin, ya ringa kallonsu, kafatanin yayan Alhaji Audu maza da mata daga kan Alhaji Babangida har zuwa Abdallah Autansu suna gurin idan ka cire Naziru dake prison se Ahmad da Alhaji Zakariyyah waWanda Allah yayiwa Rasuwa. Haihuwar su Afeeyah da sati uku Allah yayiwa Alhaji Zakariyya rasuwa bayan yayi kwana biyar a coma sakamakon faWuwa da yayi, rasuwar ta gigita hajiya ba kaWan ba seda aka ringa mata rubutu tana sha ana mata wanka kafin ta samu dangana, da bakinta take cewa amma dai Aisha waliyyiya ce. Ashe abinda taji kenan sanda Ahmad ya mutu ita dai Momy sedai tayi murmushi kawai domin tasan hajiyar bataji ko kwatan abinda taji ba koma tace yake kan ji domin ba zata dena kewa da kukan rashin Amadun ta ba har se ranar data tarar dashi tukunna.

Tsiran wata takwas tsakaninsa da Alhaji Audu wanda a jiya akayi

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login