Showing 372001 words to 375000 words out of 467220 words

Chapter 125 - MATAR MUTUM COMPLETED 1-3 BY MARYAM FARUK.doc

23 Sep 2025

12184

Ahmad shine yasa ya zama shiru shiru ya koyi ha?uri. Seda ta tabbatar taji fitar sa da mota bayan Azahar kafin itama ta fice ta tafi gidan Adasiyyah dan tace ba zata zo ba ita, acan suka cigaba da ?ulle ?ulle abinda ya kamata tayi.
Tun a jiyan ta kira Mamanta ta gaya mata abinda ya faru, maman ta kaWu da jin wai Fatima faccalarta ita ce Afeeyar Jay amma ta sake jaddada mata kar tayi komai.

"Malam yace in gaya miki karki yi komai yanzu idan ba haka ba zaki dagula lissafin ne ki jangwalo sama da kara saboda al'amarin ne me matu?ar girma a tsakani, ki tattara hankalinki guri Waya karki kuskura kice zaki cewa kowa komai yanzu ki bari kawai shi zeyi komai za'a sabunta wancan aikin da akayi aka rabasu da farko yanzu ma kina zaune zaki nemi labarinta ki rasa kedai ki yi ha?uri kawai na Wan lokaci bu?ata zata biya" Maman ta gaya mata dan bata bata labarin ta'asar data rigada tayi ba.

*ASSALAMU ALAIKUM*
*YAN UWANA MATA MASU BURIN A KODA YAUSHE SU KASANCE CIKIN GYARA, JIKINSU YA RINGA TAFIYA DA ZAMANI TA FANNIN KYAU DA KAYAN MARMARI MASU HANA IDANUN OGANNI LE?E-LE?E TO KU MARMATSO DOMIN DAI TAFE NAKE DA ABIN ARZI?I KUMA DOMIN KU KA?AI*

*INA GABATAR MUKU DA GADALIN MUTAN NINGI, INGANTACCE KUMA SAHIHIN MAGANI WANDA MUKAYIWA LA?ABI DA TULA-TULA 3 IN 1*

*INGANCCE KUMA SAHIHIN MAGANIN MU TULA-TULA NA GYARAN NONO, IDAN HAR NONO NE MATSALARKI YAR UWA DA YARDAR ALLAH SE DAI KI BAYAR DA LABARI DOMIN TULA-TULA YANA GYARAWA TARE DA TAYAR DA DUK WATA KOMADA YA MAYAR DA SU CAS ABIN GWANIN SHA'AWA. BAMU CE NONONKI ZASU TASHI SU TSAYA KAMAR NA BUDURWA BA, A'A ZASU DAI SU CIKO SUYI KYAU DUK YANDA?????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????? SUKA YAMUTSE DA YARDAR ALLAH ZASU ZAMA ABIN SHA'AWA GA MAI GIDA. DALILIN KIRANSA TULA TULA E IN 1 KUMA BAYAN GYARAN NONO YANA MAGANIN SANYI TARE DA SAUKAR DA NI'IMA*

*AN SAMAR DASHI DAGA NAU'IKAN ABUBUWAN DA JIKI YAKE BU?ATA, MAI CIKI BATA SHA AMMA MAI GOYO ZATA SHA DOMIN YANA WANKE NONO SANNAAN IDAN ZA'AYI YAYE YANA HANA CIWON NONO*

*KAI TSAYE A TUNTUBI MAMAN ILHAM KADUNA AKAN 08135613021, Muna kaduna muna aika Kaya ko ina a faWin Nigeria cikin Aminci. Kar a manta siyanna gari mayar da kuWi gida TULA-TULA tabbas ne bawai ya?ini ba*

*MATAR MUTUM*
*NA MARYAM FAROUK (UMMU MAHEER*

*FIKRA WRITERS ASSOCIATION*

*LITTAFIN KUDI NE*
*PAY 500 A ASUSUN*
*7061838488*
*OPAY DIGITAL SERVICES*
*MARYAM FAROUK*
OR
*0709290797*
*ACCESS BANK*
*SE A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488*
*IDAN KATINE A DAUKI HOTONSA A TURA ZUWA LAMBAR SAMA VTU KUMA A TURA A 08142548705*

*Kuyi following dina a Arewabooks @Maryamfarouk01 inda zaku karanta wannan littafin tareda sauran littattafaina*
*NAGODE*

*BOOK 3*
*PAGE 34*

Tun Fatiyyah tana Wari Wari harta saki ranta ganin har an kwana uku Jay bece mata ta tafasa ba kuma saSanin ya da tayi tunani ze ?aurace mata yanda ya saba idan yana fushi da ita se taga ba haka ba, ita ce ma take janyewa tana kama kanta daga ?arshe kuma ta saki saboda Mamanta ta bata tabbacin Malam yayi aikin daya ce zeyi mata ya rage nata tayi amfani da salo da dabaru ta ?ara jansa jikinta ta rabashi da kowa wannan sararin data samu ya sake bata damar baje kolin tijarar data durfafi yiwa Fateema.

Dukda tayi blocking Win layinta tun a ranar data je gidan bata ha?ura ba ta siyo wasu layukan ta ringa kiranta dasu ita kuma data Waga taji ita ce zata kashe tayi blocking number daga ?arshe ma ta dena amsa number da bata sani ba. Ranar da akayi kwana ukun bayan sallar Magriba Jafar ya shirya yace mata zeje gida gurin Hajiya, tana zaune a falo tana cin mangwaron data saka aka yanka mata ya Wan zauna gefen kujera yana tambayar ta ko zata shirya suje tare tace Aa bata jin daWi sosai ya tafi kawai ba zata iya zuwa ba. Warsa na aljihu tayi ?ara ya cirota ya amsa kiran a ta?aice ya mi?e tana gani a ?o?arin ya zura wayar a aljihu bata shiga ba ta zame kan kujera ya wuce ba tareda ya sani ba. Ya kai minti kusan ashirin da barin gidan kafin taji ringing tone irin nasa yana tashi a falon, ta ringa dube dube daga baya ta gano wayar a inda ya zauna. Cike da tsananin murna ta Wauke ta, kiran ya katse ta wuce da sauri ta kulle ?ofar falon da key kafin ta shige Waki saboda murna harda rawarta.

Kai tsaye ta lalubi number Afeeyah ta kira, a daidai lokacin Fatima na tsaye daga cikin get Win gidansu, fuskarta kirtif kamar hadari ta ri?e ?ugu da hannu Waya tamkar zata rufe Jafar da duka. Yana tsaye ya jingina bayansa da katanga hannaynesa harWe a ?irji yana kallonta ba tareda idanunsu sun haWu ba take cewa
"Banyi mamakin abinda ta aikata ba domin dama ai zaren kalar yadin ne ta yaya ma za'ayi tana tare da mayaudari, ma?aryaci kuma me zamba cikin soyayya me ?as?antar da halittar ubangiji da ganin yafi ?arfin su kuma ace zara san mutunchin babba?
Wlh abun daya fi mun ciwo ma yanda jahilar matarnan ta saka Ummana take tunanin har yanzu akwai wani abu da yayi saura tsakanina daku, me zanyi da mijinta? An gaya mata har wani abin so ne shi banda a gurinta da bata san me takeyi ba? Rayuwar da nayi a baya ma nadamar ta nakeyi kuma da ace kuma ina da damar sauya ?addara ta da na goge sanadin daya haWa ni dashi.

Na tsane shi na tsani duk wani abu da ze dangantani dashi. Tun da wuri ma ta sani ba abinda zanyi da mijinta dan ita taga abin so a tattare dashi kuma zuwan da tayi har cikin gida ta ciwa mahaifiyata mutunchi bata zagi banza ba wlh sena rama, zan mayar mata martani da abinda zeyi mata ciwo sama da wanda tayi mun" wayarta ta dakatar da ita daga bambamin da takeyi har haki take numfashinta na neman sar?ewa saboda masifa.

Da mamaki ta kalli wayar ta kalleshi, ya na nan yanda yake tunda ta fara maganar be motsa ba haka idanunsa basu dena yawo tsakanin bakinta dake magana da jikinta da take jijjigawa ba saboda tsabar abinda ke cin ranta. Ya mi?e tsaye dakyau fuska babu yabo babu fallasa ya mi?a mata hannu alamar ta bashi wayar tata, bata mi?a masa ba ya saka hannu ya zareta sannan ya Waga kiran da harya katse wani ya sake shigowa ya saka wayar a speaker. Muryar Fatiyyah tar a kunnuwansu tace
"You matsiyaciya yar matsiyata. Wato kinyi blocking layina kin kuma dena Waga unsaved number ko kin zata hakan ze saka na barki? ai ba zaki ?i Waga kiran dadironki kinga nima ba zan?i Waukar wayarsa na isar miki da sa?on da nayi niyya ba".

Jay ya rintse ido saboda yanda kalmar da Fatiyyan ta faWa ta dake shi, Afeeyah dai shi take kallo ita kuma taci gaba da cewa
"Dafarko dai salon wasanki ya burgeni, da ace ana bayar da kyauta ta wadda tafi kowa iya yaudara a duniya da tabbas sena kai sunanki. Wato karkiyi biyu babu ba se kika haWa yaya da ?ani kikayi soyayya dasu, da kika fahimci zaki fi tara abin duniya a jikin Ahmad se kika fara auransa kikayi yanda kikayi kika kashe shi kika ci gado yanzu kuma shirinki ki auri mijina kenan ki mori soyayya kome? To bari kiji wlh kinyi ?arya kuma ke baki san komai ba a tsageranci da duniyanci ni nan na dama ki na shanye. Ba dan ba se nace Allah ma yasa kiyi kuskuren auran mijina ta yanda zanfi samun damar gwada miki kuskurenki da kyau yarinya" tayi shiru tayi wata dariya irin ta yan duniya kafin ta sake cewa

"Nima dai na tsaya ina Sata yawun bakina da lokaci na, idan har ke kin haifu cikin fa?irin ubanki da wannan koWaWWiyar uwar taki ki cigaba da kula Jafar, ki aure shi, na tabbata tijararriyar uwarsa kaWai ta isheki. Wlh Fatima se kin gane baki da wayo, se kin tsinewa kwaWayi da son zuciyar da suka ?awatawa zuciyarki Jafar har kika yi sha'awar auransa, dan Allah karki fasa idan harke kin cika Fatima Afeeya me fuska biyu ki auri Jafar" tana kaiwa nan ta kashe wayar.

Cikin kukan da ta kasa ri?e shi tana kallonsa tace
"Ka zageni, kaci mutuncin iyaye na mahaifiyar ka ta aibatani ta aibata iyayena yanzu kuma matarka, wlh Jafar nayi nadamar saninka a rayuwata domin tarayyata da kai bata amfaneni da komai ba se ba?in ciki da dana sani. Akan me kaida duk wanda suka shafeka zaku tsaneni? Ka shiga rayuwata kayi amfani da raunina kayi mun ?aryar so daga ?arshe ka yaudareni na kuma fahimci dalilin hakan, baka sona da Ahmad kasha faWar in har kana rate bq zaka bari ya aureni. Na auri Ahmad burinka na farko ba cika ba amma yanzu kuma ya mutu ya bar duniyar ma baki Waya ba wai ni kaWai daka tsana ba me kuma yayi saura da kake bibiya tare dani? Me kake nema? Na bar zuri'arku akan me kuma zaka cigaba da bibiyar rayuwata kana janyowa iyayena zagi da Satanci akan me? Me kake so dani Jafar?" Ta ?arasa cikin Waga sauti tana sake fashewa da kukan daya fi na farko.

Ashe ma da sanin sa akan abinda Fatiyyah tazo tayi mata kuma hakan beyi musu ba shine ya bar mata wayarsa a gida ta kirata sannan ya kwace mata waya ya amsa kiran saboda ta saurari cin zarafin da suka shirya yi mata.

Jafar ya sauke ajiyar zuciya ?arfi bayan ya gama tattara kalaman da suke da muhimmanci a gurinsa cikin maganganunta. Idanunsa sun kaWa sunyi jajir jijiyoyin kansa har bugawa sukeyi. Ya kalli ?ofar tsakiya data raba harabar get Win da cikin gidan a rufe take sannan ya kalli ?ofar get Win itama a rufen take, a hankali ya cike sararin dake tsakaninsa da ita, kanta yana ?asa tana kuka tamkar zata haWiye zuciyarta kafin ta kai ga fahimyar me yake shirin yi har ta janye ya tarairayota gaba Waya yayi mata masauki a ?irjinsa. Cak kukan da takeyi ya tsaya, ta gwalalo ido zuciyarta ta shiga bugu kamar wadda taga mutuwa muraran, so take ta ?wace amma irin ri?on daya mata da kuma tsoro tareda mamakin da suka dirar mata lokaci daya yasa ta kasa koyin ?wa?w?waran motsi se juya idanu kawai take tana kokawa da numfashinta dake barazanar tafiya hutu.

Tsayin mintuna uku tana ri?e a jikinsa kafin ya saketa a hankali, kallo Waya ta kara masa ta juya cikin gida da sauri har tana haWa hanya kamar zata faWi, ya saki murmushin da besan dalilin yinsa ba yana kallonta harta shige ciki. Gyaran murya dayaji a bayansa ya sakashi juyawa da sauri se yaga Baffa a tsaye, yanayin da fuskarsa ta nuna kuma ya tabbatar masa babu tantama yaga duk abinda ya faru.

Wata irin kunya ta lulluSe shi, a lokacin fata yayi inama yana da baiwar Sacewa ko kuma ace ?asa ta tsage kawai ya shige ciki ya huta da tsayawa gaban Baffan se yayi kasa da idonsa yana shafa kansa da hannu Waya kafin ya rage tsayi ba tareda ya bari sun haWa ido da Baffan ba murya bata fita sosai ya gaida shi. Yanda yaji muryar Baffan ya sake kashe masa jiki ya kuma tabbatar da gasken ya gansu. Yana ji Baffan yana cewa
"Malam Jafaru be kamatu mutum ya bari shaiWan ya ringayi zuciyarsa harya kaishi ga aikata abinda be kamata ba kuma, a ringa kiyayewa dan Allah".

Da?yar ya iya amsa masa da
"In sha Allahu Baffa" seda ya dena jiyo sawun takalman Baffan kafin ya mi?e jiki babu ?wari ya fita daga gidan yana waiwaye. Yafi minti goma cikin mota ya kasa tafiya, abu biyu zuwa uku suke masa yawo a rai a lokacin, sam beji daWin abinda

MaWaukakiyar kunyar Baffa da abinda ya ganshi yana aikatawa wanda Allah ya sani bada wata manufa yayi ba, ya sani idan ma yace ze rarrasheta da baki ko ya gaya mata wata magana ba zata saurareshi ba shi bema san ya akayi ya aikata hakan ba kawai ?wa?walwar sa tabi umarnin zuciyarsa ne ta baiwa jikinsa unarnin aikata hakan.

Abu na biyu kuma maganganun data furta masa a ciki ya samu amsar tambayoyin dake zuciyarsa tsayin shekaru tara, Afeeyah ta ?ullace akan ya shiga rayuwarta ne saboda ya rabata da Ahmad. Tana zargin ya yaudararta yayi wasa da zuciyarta daga ?arshe ya barta daya ga babu yanda ya iya ya rabasu a tunaninta kenan, tsayin lokacin kallon da takeyi masa kenan sannan ta ri?e shi da kuskuren da shi kansa yana nadamar hakan. Me yasa ta gagara yi masa uzurin duk abubuwan daya aikata mata a baya sharrin shaiWan ne da kuma ?uruciya?

Be aibata ahalinta da wata niyya ba, ko a lokacin haushi da kishin yanda Ahmad ya Waukake ta sama da kowa da komai ita kuma take wula?anta masa Wan uwa ya sakashi yin waWancan furucin data kama ta ri?e a zuciyarta shi ba har ransa ya faWi koma menene ba amma ta yaya ze fahimtar da ita hakan kuma ta yarda ta yafe masa? Babbar damuwarsa Allah yasa Ummanta da Baffa basu san komai akan wancan lokacin ba, idan har sun sani be san irin kallon da suke masa ba ta yuwu ma shiyasa kwata kwata Yayarta bata shiga sabgarsa, ko haWuwa sukayi ya gaisheta se taga dama take amsawa ?ilan ta gaya mata komai shiyasa take kallonsa da abin suma su Baffan ta yuwu dattako ne yasa suke nuna masa tamkar babu komai amma can ?asan ransu suna ri?e dashi idan haka ta kasance ta yaya ma zasu yarda da ?ulluwar wani al'amari tsakaninsa dasu?

Ya furzar da iska me zafi daga bakinsa kafin ya tayar da motar ya shiga tu?i a hankali kamar mara lafiya, Baya so ma ya tuna maganganun Fatiyyah tarata kawai yakeyi baya so kuma ta bari ya kai bango dan hukuncin da ze Wauka baze yi musu daWi. Har ya kusa titi sannan ya lura da ledar Ice cream Win daya siyawa su Amal da kuma Pampers da Frisco cream Win Ahmad dan yana lissafe dasu yasan sun kusa ?arewa daman sune dalilin zuwansa gidan yana shiga yaci karo da ita shine ta tsayar dashi ta fara zazzaga masa tsiya. Tunda ya kai mata ATM Win daya tsara ze ringa saka mata kuWin kula da yaran bata taSa cire komai a ciki ba hakan yasa duk wata yake turawa wani yaronsa kuWi da list Win duk abinda ya kamata a siya akai musu, daya dawo kuma ya cigaba da kansa.

Juya kan motar yayi ya koma amma beyi gigin shigar musu gida ba yayi amfani da wayarta da babu password akai ya kira Baffa. Yana zaune cikin motar yana bincika mata waya su Laylan suka fito, ya ?arasa goge numbobin da yayi marking kafin ya buWe musu motar. Sun daWe suna masa surutu nan suka sha ice cream Win dan ya fara narkewa har tara tayi kafin ya basu sauran kayan da wayarta suka shiga gida suna ta tsallen murna.

?walla ta cika masa ido amma be barta ta zubo ba, yanzu ta yaya Hajiya zata tilasta masa ya wofantar da zuri'ar Yah Ahmad bayan dashi kaWai yaran suka saba, shi kaWai suke sakewa dashi kusan sama da yanda ma sukeyi da mahaifinsu sanda yana raye. Tamkar Yah Ahmad yasab bazeyi doguwar rayuwa ba seda ya gina so da sha?uwa me girma tsakaninsa da yaran yanzu ta ina Hajiya take so ya fara koyar rayuwa ba tare dasu ba? Sannan waye ze cigaba da kulawa da yaran suji tamkar Abbansu yana raye idan bashi ba?

Ba'a son ransa ya bijirewa umarnin Hajiya ba amma Allah ya sani baze iya aiwatar da abinda take umartarsa dashi ba dan idan yayi haka ai Allah ma seya kama shi da laifin yasar da amana da kuma watsi da zumunchi. Kwanakin da yayi beje ya dubasu ba ba ?aramin damuwa yaran sukayi ba jiya da daddare kusan kuka Nayla ta kirashi tayi masa a wayar Baffa akan me yasa ya dena zuwa gurinsu suna kewarsa? Hakan ya warware mas aduk wata niyya ta ?aurace musu na wani lokaci kafin komai ya daidaita, yanda ta tambayeshi ko bashida lafiya ne yasa beje ba seda ?walla ta zubo masa, wato sun aminta rashin lafiya ce kaWai zata hanashi zuwa gurinsu dole yayi duk me yuwuwa gurin ganin ya samar musu mafita baki Waya, baze iya cigaba da irin wannan rayuwar ba.

Seda ya tsaya a wani masallaci yayi sallar isha'i data wuce shi kafin ya kama hanyar gidan Dr Hassan, akwai maganin daya ce yaje ya karSa kwana biyu ciwon kai ya matsa masa baya kuma iya bacci koya kwanta sedai yayi ta juyi idan ma baccin ya Wauke shi baya wani yi da yawa yake farkawa. Da mamaki ya ringa kallon sabuwar galleliyar motar Alhaji Audu ta fita taro a harabar gidan, abu biyu ya tabbatar masa da tasan ce ba wai wata daban ba na farko plate number sannan model Win motar guda uku ce duk faWin Kano kuma tasa ce fara sauran duk ba?a?e gare su kuma dai tunda ya siye ta baya jin ya hau ta ya kai sau uku ma balle kuma ayi batun aro ya bawa wani wannan bama me yuwuwa bane.

Ransa fal mamakin ya wuce Sangaren Hajiya Zubaida wanda yake a farko yana so ya gaisheta kafin ya wuce ciki dan yasan Anty Halima matar Dr Hassan ba lallai ta barshi ya fito yanzu ba da hirar ta da bata ?arewa. Tsam yayi a bakin ?ofa sallamar da fara ta ma?ale shi be shiga ciki ba kuma be koma da baya ba idonsa ?ur akan Alhajin daya gani zaune akan kujerar dake kallon me shigowa. Alhajin daya Waga kai jin anyi sallama ya kalle shi ganin ya tsaya be shiga ba yana ta kallonsa yace
"Idan ba shigowa zakayi ba ka koma ka tsayawa mutane kamar wani mutum mutumi" Hajiya Zubaida dake kujar data bashi baya ta waiwayo taga wanene, fuskar ta washe tace

"Aa Jafar kaine? Shigo mana ka tsaya a dokin ?ofa ga dare". Jiki la?was ya ?arasa ciki ya samu kujerar

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login