Showing 249001 words to 252000 words out of 467220 words

Chapter 84 - MATAR MUTUM COMPLETED 1-3 BY MARYAM FARUK.doc

23 Sep 2025

12237

ina jira" ta faWi kafin ta sauke wayar ta doka tagumi tana jiran taga an kira kamar yanda yace, tunani take tana ?arfafawa kanta guiwa dukda hankalinta ya tashi dajin bashida lafiya, ta yuwu ma beje ba jiyan ba ganinta da Ahmad bane ya Sata masa rai, ?ila ma ko be hau Online bane shi yasa taga kamar yayi blocking nata a WhatsApp amma ba haka bane. Shiru tana ta tunani har minti kusan ashirin ya wuce ba'a kira ba kamar yanda wanda ya amsa wayar ya ce mata ze kai masa yanzu se kawai ta yanke shawarar ta sake kira kodan taji ya jikinsa da kuma abinda yake damunsa.

AHMAD
Sau biyu kenan da yake jin muryar budurwar Jay tamkar ta Fatima, daya isa Wakin ya tarar da Manager shi tareda sauran jama'arsa wannan tasa be bashi wayar ba ya ajiye masa ita kawai akan Drawer ya fita zuwa gurin Dr Hassan, Jay kuwa bayan ya sallami ba?insa ya Wauki wayarsa da through out yau be ri?e ta ba. Missed calls Winta ya fara gani, wani abu ya soki ransa, daga safiyar zuwa yanzu yayi ?o?arin ganin ya rage damuwarta a ransa, a maimakon matsantawa kansa da son gano dalilinta na aikata musu wannan abun seya mayar da hankali gurin tunanin ta yanda ze hukuntata dan ba zata ci banza ba tilas ya maida mata da mugun nufinta akansu. Tunaninsa Waya yanda Ahmad ze karSi Al'amarin idan ya sanar masa, baze bari taci gaba da cutar da shi ba daga ?arshe ta karya masa zuciya tamkar yanda tayi masa.

Shi yana da taurin ran da ze shanye damuwarta amma baya tsammanin Yah Ahmad ze iya, he is so much into the girl.
"Kaima kana sonta" zuciyarsa ta raya masa, se yayi saurim kawar da tunanin daga ransa domin shine rauninsa. Allah ya sani yana Son ta, so na gaskiya saboda Allah badan wani abu ba amma kuma kash koda ace babu wata manufa game dasu a ranta, ya zama ace abinda ya faru Arashine daga Allah tilas shi ze ha?ura da ita domin Ahmad ya rigashi zuwa gurin kai ko ba haka ba ko da ace tasa ce Yah Ahmad yace yana so ze bar masa. Ringing da wayar ta fara ya katse masa tunani, yana kallo harta katse kafin ta sake kira yayi adding nata to blocklist, a fili yake so ya wanke ta, face to face yake so ya warware mata komai ta yanda zata fi ji a jikinta.

Haka yayi jinyar kwana biyu aka sallameshi kullum a Asibitin Hajiya da jama'arta suke wuni tamkar wani biki se dare Ahmad kuma yaje ya kwana dashi. A ta?in kwanaki biyun yayi rama fuskarsa kuma ta gagara Soye abinda yake ransa amma se yake boyewa da sunan ciwo. Kwanansa biyu da dawowa gida ya fara shirin komawa France. Da niyyar sati huWu yazo gida, sati huWun da yake cewa kafin cikarsu za'a Waura musu Aure da Afeeyah se gashi komai ya canza ko cikakken sati biyu beyi ba yana cewa ze koma. Hajiya daman cewa tayi gara ya tafi, Turai tace anyi ?ai?ayi koma kan mashe?iya shiyasa ma ya samu sau?i ya tashi saboda an san ko an bashi magani ko haya?i bayi zeyi ba se aka masa aikeb kai tsaye wai Malam ya saka hadimansa sun saka maganin a jikinsa.

Ahmad ne kaWai ya damu da konawar da zeyi domin ya gagara yarda wai Malaria ce take damun Jafar, akwai wani abu daya Soye masa kuma ya gagara tambayarsa kamar yanda shima Jay ya kasa furta masa abinda yake ci masa zuciya. Yayi ?o?arin magana da Ahmad tun yana Asibiti, ya tambayeshi kan yanzu ace masa Fatima yaudararsa takeyi bayanshi da akwai wani da take kulawa kuma shi take so yaya zeji?
"Already na sani, bayan ni da akwai wani da take tare dashi kuma shi take so bani ba, ya ci ace na ha?ura da ita Jafar, amma na kasa. Ni da kaina bansan irin son da nakewa yarinyar nan ba kawai dai ina cigaba da addu'a idan rabo na ce Allah ya bani idan ba tawa bace Allah ya musanya mun da wadda ta fita Alkhairi" amsar da Ahmad ya bashi kenan data sanyaya masa jiki tasa kuma ya fasa faWa masa gaskiyar abinda ya faru to ta ina ma ze fara? Ya Ahmad zeji? Se kawai ya shanye damuwarsa shi kaWai ya kuma cigaba da addu'ar Allah ya tarwatsa tarayyar su da Ahmad domin ita ba Alkhairi bace a rayuwarsu.

Ranar talata data kama saura kwanaki biyu Jay ya wuce Baba Al?ali ya kirashi akan yaje gida ya same shi yana son magana dashi. Shi kaWai ya tafi yauma daman Ahmad baya nan ya tafi Jigawa inda yake noman shinkafa dan da tare ma zasuje Hajiya ta hanashi binsa.

"Shiru baka sake cewa komai ba dangane da full address da nace ka samo na gidansu yarinyar da kake nema" Baba Al?ali ya faWa, ya sunkuyar da kansa yace
"Amm daman an samu matsala ne Baba so kuma na manta ban dawo na gaya maka ba"
"Matsala wace iri kenan?"
"Ita yarinyarce da akwai wanda suke tare kafin ni kuma bata gayamun ba se daga baya nayi finding out so i felt thar she betrayed me kuma bata da gaskiya if she could hide such important things to me may be bada gaske take so na ba nima".

Baba Al?ali ya ringa kallonsa kafin yace
"Kodai uwarka ta shiga tsakani ba?"
"Wlh babu ruwanta Baba bata san komai ba har yanzu kawai wannan dalilin yasa nayi blackout saboda ni bana son ?arya a rayuwata" Jay yayi saurin defending Hajiya. Al?ali yayi murmushi yace

"Amma ko zaka daWe kana bincike kafin ka samu budurwa da take kula saurayi guda Waya, daman ai se anyi takara wanda yafi ?arfi ya kayar da yan uwansa" cewar Baba Al?ali. Jay yayi murmushi, kamar ya sanarwa da Baban abinda ya faru amma baze so ya zama silar raba Ahmad da abinda yake so ba dan Baban baze bari ya aureta ba ya sani, gara ace ita da kanta taji kunya tace ta fasa tayi biyu babu so that bazeyi blaming kowa da cewar shi ya hanashi auranta ba.

"Ai ita Baba har iyaye sun san maganar fa for almost 3 years suke tare yana wahalta mata amma bata gaya mun ba seda naje gurin Babanta and from the way yayi maganar se naji kamar yafi son wancan ma akaina"

"Allah ya baka ha?uri ya musanya maka da wadda ta fita Alkhairi, shikenan zamu jira daga gurin mahaifin yarinyar da ?an uwanka yake nema shi saura sati ?aya wa'adin daya bamu ya cika, idan kuma duk an kasa ku ne se ku Wauki ha?uri mu tafi Bechi a nema muku mata" ya ?arasa maganar cikin raha Jay yayi dariya.

GIDAN MALAM HAFIZU
Kamar yanda na sanar miki sati biyu na bawa wanda kika kawo a matsayin zaSin ranki, yau kwanaki goma sha biyu kenan tun zuwan da yayi be sake dawowa ba, ina sake tuna sar dake kwana biyu rak ya rage miki idan suka cika ba tareda ya gabatar da kansa ba karkiyi kuka da duk hukuncin da zan yanke domin na baki dama a matsayinki na Ya dan haka nima zan gwada iko na na uba akanki" Baffah dake tsaye akan Fatima ya faWi.
"Kinji me nace ko?" Ya sake jaddada mata seta gyaWa kai alamar taji ya juya ya fice daga Wakin. Kwanciya tayi kan katifa ta fashe da kuka amma mara sauti, bata sake samun Jafar a waya ba tun ranar da wani ya amsa yace ze haWasu. Ta tabbata kuma yayi blocking nata a WhatsApp da sauran social media handles Winsa dan duk inda ta masa magana bata tafiya sedai ta gaji da jira ta ha?ura.

A Wan lokaci ta fita a hayyacinta, zuciyarta zafi take mata ga ciwon kan da tayi ?aryarsa ya aureta da gaske me azaba irin wanda ko idanu idan ya tasar mata bata iya buWewa. Yanda Umma tayi banza da ita tamkar ta manta da wanzuwarta a gidan ne yake sake ta'azzara mata ciwo da damuwa, bata da wanda zata tattauna dashi, Anty Sauda ma ta juya mata baya, Badar Babansu bashida lafiya har an fita dashi India suna can dukansu tunda ta mata sallama basu sake magana ba kusan kwana goma bata san layin da zata sameta acan ba shi kansa Ahmad da take ganin ya zame mata ?uda ta rasa yanda zata yaki ceshi a yanzu da take bu?atar Sangaren da zataji sanyi shima ya kaucez tun randa yaje be sake komawa ba haka waya befi sau huWu sukayi ba saboda ayyuka da yace mata sun masa yawa baya samun lokaci sosai wannan shi ake cewa rana zafi inuwa ?una babu inda zata tsoma ranta taji daWi ga wani sabon batu da Baffah yazo mata dashi ita ya zatayi????

Daga kwancen da take ta janyo wayarta ta buWe Tiktok, a can ne take zaton be rufeta ba kai tsaye tayi searching account Winsa ta shiga profile Win. ?irjinta ya buga dum da ganin video da yayi pinning a farko, hannunta har yana rawa ta buWe, videonsa ne da wata yarinya, Jaa ce dan kalar fatarta farace irin me sirkin jini. ?irarta irin jikin yayan madarar nan da zaka gansu fatarsu luf kamar an hura musu iska a cikinta, kyakykyawa ce bata cika tsayi ba, tana da cikar ?irji sosai da mazaunai wanda fitinannen Winkin doguwar rigar data saka ya bayyanar dasu. Hannayensu sar?e da juna tana masa magana yana doka murmushin nan nasa me tsada. Ta ringa maimaita karanta Caption Win daya rubuta
# FatiyyahJay#
*ASSALAMU ALAIKUM*
*Kande lafiya kika zabga tagumi kamar wadda tasha ruwa da jin kiran La'asar?*

*Kedai barni tsahira, gobe za'a fara azumi amma kin ganni ko sabon cokali da zan sakawa Baban Lantana bani dashi, na aika kasuwa kaya sunqi siyuwa tsada kamar ka kurma ihu*

*Ayya kice Kande bakida labarin KLC KITCHEN WORLD*

*KLC KITCHEN WORD? WACECE HAKA?*

*Hadiza Lele kenan ne kayan amfanin kitchen, kayanta akwai kyau da inganci duk abinda kike nema zaki same a gurinta cikin rahusa maza ungo number ta nan 08165121716 ko kuma ki isketa har gida a*

*Ring road Naibawa bayan gidan gwangwan*

*Karin Albishir tana Adashen kayan kitchen kinga hankali kwance zaki fara yiwa Lantana tari base rana tazo ana ki fito da kaya ki hau zare ido*

*KLC KITCHEN WORLD*
*08165121716*

*MATAR MUTUM*
*NA MARYAM FAROUK (UMMU MAHEER*

*FIKRA WRITERS ASSOCIATION*

*LITTAFIN KUDI NE*
*PAY 500 A ASUSUN*
*7061838488*
*OPAY DIGITAL SERVICES*
*MARYAM FAROUK*
OR
*0709290797*
*ACCESS BANK*
*SE A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488*
*IDAN KATINE A DAUKI HOTONSA A TURA ZUWA LAMBAR SAMA VTU KUMA A TURA A 08142548705*

*Kuyi following dina a Arewabooks @Maryamfarouk01 inda zaku karanta wannan littafin tareda sauran littattafaina*
*NAGODE*

*BOOK 2*
*PAGE 24*
Comment section ta shiga, hawayen da suka lulluSe mata ido suka saka bata iya ganin abinda aka rubuta. Tana kuka tana typing
"Unblock me and answer my calls Jay dan girman Allah I'm going to explain ba abinda kake tunani bane" Tana turawa ta fita ta shiga gurin message nan ma ta fara jera masa maganganganu amma harta ha?ura cire tsammani be amsa ba, kuma official account Winsa ne babu batun ace be gani ba. Wacece wannan yarinyar? Menene haWinsa da ita? Ta ringa tambayar kanta. Kuka tasha har seda taji tana neman shiWewa sannan tayi shiru amma hawaye basu dena zubar mata ba.

JAY

Abuja yayi zango bayan ya bar Kano, sati huWu yayi niyyaryi tareda Afeeyarsa kafin ya koma, abinda yake ji a ransa yasa baze iya cigaba da zama a Kano ba kuma baze koma France ba dan ya san kewa ce zatayi masa yawa, damuwar da yake ciki nunkuwa zatayi. Ahmad ne ya rakashi Abuja as usual a ?o?arinsa na son nuna komai lafiya lau sedai Ahmad Win ya masa shiru ne kawai yana binsa a yanda yake so amma ya gano tabbas akwai abinda Jafar ya ke Soyewa, sanin menene kuma ya barwa Allah yana dai da ya?inin ko meye idan lokacin daya kamata ya sani yayi base ya tambayeshi ba ze gaya masa. Ya masa magana dai akan Afeeyah saboda sun fita da Alhaji yace masa Baba Al?ali ya masa zancen an fasa zuwarwa Jay tambayar aure kamar yanda aka shirya a farko, daya tambayeshi dalili yace masa

"Mayaudariya ce Azzaluma, tana da wanda iyayenta suka fi so yake wahalta mata for ages so tayi ta yaidareni Allah yasa na ganota da wuri" ya bashi sa. Ahmad yace
"Kuma da gaske kakeyi ka ha?ura da ita? Daman duk kurarin soyayyar nan a bakine ba gaskiya ba? Ai na zata se in har kaji an Waura mata aure da wani ne zaka sare ashe ma bada gaske kakeyi ba"

"Yah Ahmad kenan" abinda ya sake ce masa kenan daga nan suka bar maganar dan shima be jata ba. Daya kaishi Abuja a ranar ya juyo dan da sassafe suka tafi be kuma zauna ba ya masa sallama ya juyo dan akwai ayyuka a gabansa sosai da yake so yayi. Wannan tasa Jay ya kashe wayarsa dan baya so wani a gida ma yasan be tafi ba, seda ya shafe kwanaki biyu a Hotel room sedai yayi wanka yaci abinci yayi sallah ya kwanta yana tunani. Duk ta yanda ya ke lissafa ze warwarewa Afeeyah se yaga daga ?arshe abin akan Yah Ahmad ze ?are. Ranar daya kwana uku ya gaji da kwanciya da dare ya shirya ya fita, mota ya Wauka a Hotel Win ya fita ya ringa yawo a titin Abuja harya gaji, haka nan yaji yana kwaWayin Shawarma dan haka ya tsaya wani guri dake kan titin daya biyo.

Yana tsaye gurin cashier kamar daga sama yaji an kira sunansa
"Jayyy" yanda taja sunan ya sanar masa da wacece, ita kaWai take kiransa haka mamakinsa ya akayi ta ganeshi? Ya juya baya kuma kota gaba ta kalleshi fuskarsa lulluSe take da facemasks saboda tsaro. Ya juya sosai yana kallonta, FATIYYAH MU'AZ ce, fuskarta Wauke da murmushi me kyau take kallomsa itama, kafin yayi wani abu ta isa gareshi ta rungumeshi and he couldn't help it but to hug her back.

"When did you come back to Naija?" Ya tambayeta bayan daya raba jikinsu, hannunta sar?e cikin nasa tana binsa da kallo kamar mayya tace
"Since last month, mun ma dawo duka nan ai"
"Wow, at long last" ya faWa da wide smile. Ta kai hannu zata zare masa facemask ya ri?e yana girgiza mata kai ta Sata fuska,
"Excuse me sir, your order is ready" muryar wata waiter ta katse shi tana mi?a masa ledar kayansa ya amsa har sannan Fatiyyah na manne rabi a gefensa ya kalleta yace

"Let's go". A tare suka fito daga gurin, motar daya zo da ita suka shiga suka zauna Fatiyyah ta shiga Waukansu hoto bayan daya zare facemask Win.
"Ki bari muyi magana mana" ya faWa yana kwace wayar ta sakar masa tareda maida hankali tana kallonsa harda yin tagumi da hannu biyu.
"Idanunta irin na Afeeyah" ya raya a ransa, ya san Fatiyyah tun kafin yasan ze haWu da wata Afeeyah a duniya. Yarinyar CBN governor ce, a London suka haWu, friend Winta ce Asali budurwarsa Maryam se kuma suka fara ?awance da Fatiyyan sosai daga ?arshe ma Maryam Win tayi aure wannan yasa ala?arsu ta fara canzawa da Fatiyyan saboda tana nuna so takeyi suyi soyayya. Yes tana da komai da ze saka Namiji ya sota amma beji yana ra'ayinta a lokacin ba, abinda ya burgeshi da ita har yasa ya kasa man tata yanda ta kama kanta taja ajinta ta rabu dashi tunda ya nuna baya ra'ayinta saSanin sauran yammata da suke naci suna binsa yana wula?antasu kamar mayu. Kusan three years kenan basu haWu ba suna dai chat jefi jefi se yau Allah ya sake haWasu.

Sunata labari a mota har seda Maman Fatiyyah ta kirata dan tace zata siyo shawarma ne yanzu ta dawo kuma tajita shiru wannan ya ankarar da ita daWewan da tayi a wajen sukayi sallama ya rakata motarta, Shawarman daya siya ma bata yayi suka rabu akan zeje gidansu da safe kafin ya wuce saboda yace mata probably ya wuce France zuwa jibi.

Bayan ya gama abinda yakeyi ya hau gado ya kunna Wifi ya shiga WhatsApp, status Winsa yayi updating da 'found a new love'. Badan yayi blocking Afeeyah ba tun a ranar zata gani, Ahmad ne ya fara buWewa ya masa replay da
"Who is the new catch"
"Some one that i deserve, and she deserves me" ya maida masa. Se Ahmad ya kirashi ta WhatsApp Win dan tunda ya tafi kamar yanda sukayi zato ta nan suke magana ya?i kunna wayarsa.

"Jay dagaske kake ka ha?ura da yarinyar nan wai?"
"Dagaske mana Yah Ahmad kasan dai sau Waya nake so kuma if i hate something and turned my back against it i never go back to it" ya bashi amsa. Ahmad yayi murmushi yace

"Amma ko, da zan baka shawara da nace kayi ha?uri indai abinda ze iya gyaruwa ne tsakaninku ka gyara saboda i can tell you truly love that girl Afeeyah dan ban taSa ganinka a irin yanayin da soyayyarta ta sakaka ba, kaga koda kake ganin kamar bani da zuciya akan Fatima ba haka bane ba, Ina sonta ne jikina da zuciyata ba zasu taSa samun nutsuwa da wata mace ba bayan ita shiyasa nake jure komai saboda na sameta"

"Yanzu a baka zaSi ni ko ita wanne zakayi choosing?" Jay ya tambayeshi, yayi murmushi yace
"Kai jinina ne ita kuma rayuwata ce"
"Ita zaka zaSa kenan?" Jay ya sake tambaya Ahmad yace
"Aa, rayuwa ba zatayuwu ba seda jini yana kwaranya a jikin mutum kaga kenan ku Win dafe kuke da rayuwata, rasa Waya daga cikinku tamkar rasa nine"

"Yanzu kenan ba zaka iya sadaukar mun da soyayyarta ba idan na bu?ata?" Jay ya sakeyi masa tambayar da se bayan ta fito yayi nadamar yinta. Ahmad yayi shiru har ya fara zaton ko wayar ta katsene kafin kuma yaji yace
"Zan kwanta cikin salama bayan na mutu idan har ka kasance kaine zaka maye gurbina ka tarairayi iyalina, amma fa dukda haka nasan se nayi kishi, amma karka sake faWar haka Alhalin ina raye amma da gaske kakeyi ko wasa wannan maganar?" Ahmad ya tambayeshi. Kamar wanda ake ingizawa Jay ya sake cewa

"Idan da gaske nakeyi zaka iya barmun ita?"
"Ta yaya wannan zazzafar ?iyayyar zata rikiWa ta koma soyayya har ta samar da kyakykyawan yanayi na

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login