Showing 429001 words to 432000 words out of 467220 words

Chapter 144 - MATAR MUTUM COMPLETED 1-3 BY MARYAM FARUK.doc

23 Sep 2025

12103

komai, yanzu wannan ba sababbi bane aka saka miki su? Menene laifi idan yayiwa Hajiyarsu Dr ko ni idan nayiwa Aafeeyah su da suke sababbi akan ku?"

Hajiya ta ringa kallonsa kawai ta rasa me zata ce masa sega Faisal ya shigo ya zauna yana kallonsa yace
"Wai ka dawo yawo da excort ne?"
"Excort?" Ya tambayeshi cikin rashin fahimta. Faisal Win ya Wauki ruwan da aka ajiyewa Jay be kai ga sha ba ya buWe yana cewa
"Eh, naga wasu bouncers ne a waje na Wauka ko tare kuke"
"No, ni kadai ne. WaWannan nima a wajen na gansu nayi zaton ma ko tareda Yah Hussani suke dana ganshi a cikin gida" ya bashi amsa. Faisal Win ya mi?e yana cewa
"Toh inaga, yawwa dama ina son nazo ka taimaka ka tayani ro?on Baba Al?ali yaje ya karSo mun kayana na fasa auren yarinyar nan".
"Amma dai kayi hauka, ina saura sati uku ne bikin?" Jay ya faWa yana kallonsa. Hajiya ta taSe baki tace
"Wai ciki ne da yarinyar" a kiWime yace
"Ciki? Na waye?"
"Wlh ba nawa bane, dama yaudarata taso tayi ta la?a mun Allah ya tona mata asiri". Jafar ya ringa kallonsa, ya sani sarai Faisal baya ji dalilin da yasa Hajiyar da kanta kenan ta matsa se yayi auren yanzu kuma yace yarinyar nada cikin ya za'ayi ya yarda ba nasa bane?
"Amma dai idan kasan naka ne tun wuri kayi admitting base ka janyowa mutane Sacin suna a duniya ba, ayi postponing auren idan ta haihu can ku ?arata dan wlh baka isa kace ba zaka aureta ba in har kai ka mata cikin nan" Jafar ya faWa a fusace, Hajiya ta buWe baki zata bashi amsa Hussani ya shigo Wakin hakan yasa tayi shiru.

Hannu Hussanin ya bawa Jafar suka gaisa daga tsaye yace
"Hajiya barka dai, Jay zo mana" ya juya ya fita Hajiya ta bishi da wani mugun kallon tsana, da tana da ?arfin mur?ushe shi da tayi ta tsani ta buWi ido ta ga yayan Zubaida, ita fa duk cikin yayan gidan bayan Ahmad babu wanda ta tsana kamarsu. Tayi ?wafa, badan tsayuwar da yayi akan masu jere ba da tuni ta watsa gayyar niyya tayi seta lalata duk wani abu da suka ajiye a Wakin sau dubu kuma in za'a kawo sau miliyan zata lalata amma yanzun ma bata ha?ura ba tunda duk tsiya baze kwana a gidan ba.

Can babban compound Hussani ya fita Jay yana biye dashi a baya, ya tsaya ganin motar Maimuna data shigo tareda su Amal suna hangoshi kuwa suka fara ihu dole tayi parking a inda take ta buWe musu suka fita da gudu suka baibaye shi, ya Waga Ahmad yana kallon sauran ya tambayi Maimunan daga ina suke tace masa a gidan Sarki ta Wakko su jiya suna gidanta. Da?yar Ahmad ya sauka daga jikinsa saboda Hussani da ?wala masa kira ya fita can waje inda ya nufa. Da mamaki ya ringa kallon ?arfafan mutane huWun dake tsaye gabansa. Hussanin ya kalli wanda da alama shine ogansu yace
"Gashi kuyi masa bayani.
Zufa ta ringa keto masa tamkar wanda yake cikin Wakin gasa buredi, jikinsa har Sari yake seda ya jingina da motar da suka zo a cikinta. Ya kalli Hussaini dake tsaye ko a jikinsa yace
Laifin me yayi?"
"Ba gasu a gabanka ba ka tambaye su mana? Ni kawai dan kar su shiga haka nan a samu abin yin surutu damu a gari shiyasa kawai na ce su tsaya ba kira musu kai. Yanzun dai salin alin ba se kowa yasan me ake ciki ba idan yana nan kaje ka fito musu dashi kawai su tafi"
"Baya gidannan, Libya yace zeje" Jay ya faWa murya a sanyaye, ogan yayi murmushi yace
"Ina fatan gaskiya ka faWa mana, saboda informers Win mu sun tabbatar mana nan ne last location da aka ganshi kuma tunda ya shigo gidan nan be fita ba".

Ya girgiza kai yace
"Why would i lie to you officer? Tabbas yazo gidan nan dan ranar ina nan in fact motarsa ma tana nan ya barta ya karSi ta brother na da ita ya fita, zaku iya shiga ku tambaya securities may be kufi gasgata maganarsu"
"Oh, he tricked them" Ogan ya faWa yana shafa gemunsa kafin ya mi?awa Jay hannu yace
"Thanks for your cooperation, we may likely come back if there is need for that" ya bawa Hussani hannu shima daga haka suka shige mota suka tafi.

"To dai tun wuri idan kasan inda yake ka mi?a musu shi tun be janyo maka ba sun haWa da kai sun Waure" Hussanin ya faWa yana kallon Jafar dake tsaye, shidai bece masa komai ba ya wuce cikin gida. A sanyaye ya shiga falon hajiya ta ringa kallonsa har ya zauna yace mata
"Hajiya ina Yah Naziru ya tafi ne?"
"Amma kana falon nan ranar yazo yace ze tafi libiya ko kaima ciwon mantuwar ya kamaka?" Ta faWa tana hararsa. Yayi ajiyar zuciya yace
"Amma bakiyi waya dashi ba tunda ya tafi ko ya gaya miki ya sauka?"
"Kai ni bamuyi waya ba be kirani ba uwar meye ne da zaka zo ka fara mun tambaya akan wani Naziru yaron goye ko me? Ai lafiya ce take Suya dama kuma ai ya saba shiga duniya se sanda yaga dama ya dawo" Hajiyar ta katse shi cikin faWa. Yayi shiru kamar baze sake magana ba se kuma yace
"Amma hajiya babu wani abu da yake aikatawa na badaidai ba da yake Soyewa?"

"Jafar, ka tafi kai tsaye ka faWi abinda yake bakinka bana son wannan kwana kwanar ta iskanci" Hajiyar ta sake faWa se ya mi?e tsaye yana cewa
"Ya wuce kawai, na manta in gaya miki naje gidansu Fatiyyah akan ta dawo amma mahaifiyata tace ba zata dawo ba"
"Can su ?arata su suka sani" ta bashi amsa ba tareda ta kalle shi ba, seya koma ya zauna yayi ?asa da murya yana cewa
"Dama an kirani ne ina so zan koma France shiyasa ma naje gurin nata amma kuma sun?i saurarana. Ina ganin zan tafi kawai, idan na bata space ta gama fushin kafin sanda zan dawo komai ze koma daidai in sha Allah kan sannan ma an kammala ginin wancan gidan kinga se su tare duka a tare". Banza Hajiyar tayi masa ya sake cewa
"Idan komai ya kammalu zuwa alhamis zan tafi" se sannan ta kalle shi tace
"Da ita zaka tafi kenan?" Yayi ?asa da kai yana shafa gashin kansa bece mata komai ba tayi ?wafa tace
"Toh ban amince ba"
"Amma hajiya idan na tafi fa zan Wan daWe kafin na dawo at least zanyi kusan 3 months kuma.."
"Tashi ka fita ka bani guri" ta faWa a fusace tana nuna masa hanya. Yana fita ta fashe da kuka, Alhaji ya tarkata Zubaida sun bar ?asar shine shima ze kwashi waccen yarinyar ya tafi da ita shikenan ita tayi biyu babu an ?wace mata miji an ?wace mata Wa.

****************************************
ZAM ZAM HOTEL, MAKKAH.
Tsayin kusan minti goma kenan Alhaji Audu na ri?e da waya a kunnensa, yanayin fuskarsa ne ze tabbatar maka da duk ma abinda ake gaya masa a wayar bame daWi bane ba. Hajiya Zubaida ta ajiye yar ?aramar butar shayi haWe da saucer a gabansa ta wuce inda wata yar container abin sha'awa me Wauke da zuma take ta dau?o ta ta ajiye a gabansa kafin ta zauna ta buWe ledar da suka shigo da ita ta fitar masa da wani biscuit da ledarsa kaWai ta isa ta tayarwa da mutum kwaWayi. Tunda suka gaisa da wanda ya kirashi a wayar bata sake jin yace komai ba banda um um da yake ta faWa, duk ta ?agara ya gama taji menene domin fuskarsa ta gama bayyanar da damuwa. Tana kallonsa ya saki ajiyar zuciya kafin murya a dakushe yace
"Nagode ?warai commander general, kuma kuna da goyon bayana 100% duk wani abu da kuke bu?ata daga Sangarena baku da matsala. Yara ne ka haife su baka haifi halin su ba amma babu komai, duk inda ya shiga a faWin duniyar nan zan fito muku dashi domin ba zan taSa goyon bayan rashin gaskiya ba. In har yanda yace he is innocent me yasa ze gudu? Da se ya tsaya shari'a ta tabbatar da hakan, karka damu zan kira uwarsa yanzun nan duk ma inda yake ta sani zata fito dashi" daga nan ya katse wayar ya ajiyeta yana huci.

Cike da damuwa ta shiga tambayar sa meya faru, be amsa mata ba ya tashi ya fita duk taji babu daWi. Tunda suka sauke Umarah suka shiga cin duniyarsu da tsinke. Tamkar wasu matasa sabon aure haka suke tattalin junansu, kullum cikin farin ciki da shau?i yanzun tun suna hanya bayan sun dawo daga harami suna shagon da suka tsaya siyan biscuits Win aka kirashi be samu sukunin amsawa ba seda suka koma masauki. Bata ce masa komai ba harya fita.

Alhaji Audu kuwa can kan barandar ya tafi ya zauna ya kira Al?ali. A gajarce suka gaisa ya shiga kora masa bayanin da Controller General na NDLEA ya kirashi yanzun ya masa akan Naziru. Nemansa suke ruwa a jallo, ?ima da darajar Alhajin tasa CG Win da kansa ya kirashi ya sanar masa tun kafin maganar ta fita ya zamana ya shafi mutunchinsa. Al?ali yace
"Tun sanda nake haska maka girman matsalar me kace? Ai cewa kayi duk abinda ya Webo ta tsaya iya kansa babu ruwanka. Baka san illar da al'amarin nan zeyi maka ba domin wata ?afa ce da magauta suka samu da zasu iya sukarka da ita amma muna fatan Allah ya tsare ya kuma kiyaye. Yanzun nan Jafar ya bar gidan nan yazo ya gaya mun sunje can gidan nemansa. Abinda baka sani ba shine kayan da suke nema a hannunsa suna cikin gidanka a Wakin uwarsa". Seda Alhaji yayi baya kamar ze faWi daga kan kujerar da yake saboda kiWima, baki na rawa yace
"A gidana u Soye ?wayar? Ita Bintan tayi hauka ne data bari aka shigo mun da kayan laifi gida?"

Al?ali yayi murmushi yace
"Ai se idan tana da zurfin tunani sannan zata sani zalama da son zuciyarta yasa an kawo mata masifa har cikin Waki tana gadinta daloli ya zuba a saman kayan yace mata kuWi ne ita kuma ai kasan ?iris ya rage ta fara bautawa kuWi. Nima Yakubu ne ya gaya mun yace da kansa ya duba kayan kuma yana da tabbacin ba ?waya kaWai bace a ciki".

Alhaji Audu ya ringa salati yana nanatawa jikinsa ya shiga tsatstsafo da zufa gaba Waya gani yayi garin yana juyawa a idonsa. Da?yar ya iya ce masa
"Amma meyasa baka gaya mun tunda wuri ba? Yanzu yaya za'ayi?"
"Nima ban daWe da sani ba, washe garin da ka tafi tana Asibiti ya buWe Wakin ai babu me shiga daga ita se shi ibilishin daya ajiye mata kayan. Yanda za'ayi kuma yanzu ka saka rana ka dawo ka tattara komai a sirrance ka haWa da ita da kayan ka mi?awa hukuma duk ma inda ya shiga idan yaji sun kama uwarsa ai ze fito ya faWi ainihin masu abin ko?" Al?ali ya sake faWa. Alhaji Audu dai yayi shiru dan ya rasa me ze sake faWa, tunani kawai yake sanda aka shigar masa da kayan kaifi gida kuma da sanin Binta. Murya kamar ta wanda akayiwa mutuwa yace
"Binta ta cuceni, banyiwa matar nan komai a rayuwa ba se Alkairi amma ga abinda ta saka mun dashi. Ina nadama da ba?in cikin haWa zuri'a da Binta, Allah ya sani bazan iya cigaba da zama da ita ba ganinta kaWai a matsayin matata ze iya ?arasa ni zuciyata ta buga na nidai na s...""

"Aa fa ha?uri zakayi karka ka fara wannam maganar. Abinda ya faru ai ya rigada ya faru se dai ayi addu'ar Allah ya kare wanda zezo a gaba. ?addarar ka ce kayi fatan Allah yasa ta zame maka kaffara kawai shine magana yanzu ka kumayi gaggawar dawowa domin idan maganar nan ta fita ina jin tsoron abokanan hamayyarka na kasuwanci suyi amfani da damar gurin ya?ar ka dan haka ka dawo asan abinda za'ayi kawai shine" Al?ali ya katse shi daga nan sukayi sallama ya kasa tashi daga gurin hasashe kawai yake dame dame Binta ta ajiye masa a cikin gida domin shi baze taSa yarda wai bata san komai ba, a yanda bayani yazo masa asalin kamfanin da su Nazirun sukayi Sadda kama da sunan pharmaceutical company filinta shi da kansa ya mallaka mata shi a lokacin tace gidan gona zatayi tunda a wajen gari yake ashe miyagu ta bawa suke aikata ta'addanci a ciki. Wata lamba ya lalubo ya kira.

***************************************
Afeeyah na kwance akan gadonta bayan ta idar da sallar isha'i, basu jima da gama magana da Badar da akayiwa Cs a safiyar ranar ta samu yarta mace da tace Nurain yace Bestynsa zeyiwa takwara, a daddafe sukayi maganar suka gama dan bata cikin yanayi me daWi. Tun ranar daya karSi passport Win ta yau kwana uku kenan be sake zuwa ba haka kuma be kirata ba tun tana basaarwa a zuwan bata damu ba har abin yafi ?arfin ta. Yanzu tunda yana ganin taje hannunsa shine ze fara lale mata katinan rashin mutunchi ko kuwa dama wancan daren yaudara ce zancensa na farko da ya gaya mata bata gabansa a yanzu shine gaskiya?
Abin ya haWe mata biyu, ga damuwar Jay ga mitar Umma da wadda ta ita take karin kumallon safe tayi na rana dana dare duka ba dare ba rana goranta mata takeyi ai gashi nan, zirgillin daya kaita ta bashi kanta babu jan aji babu komai gashi nan tun ba'aje ko ina ba har yaci moriyar ganga ya yarda fata. Tace
"Dama abinda yakeyiwa kenan tunda ya samu a banza ai kuma se yanda Allah yayi dake. Mutumin da a rana se yazo gidan nan sau babu adadi amma ace ya jera kwana uku babu ko Wuriyarsa ko da yake me ze zo yayi? Ni dai wlh in har kinyi ciki sedai ki tafi Wakin uwarsa ki zauna duk randa ya waiwayeki shikenan amma ba zaki mun rainon ciki a gida ba".

Idan Umma na mata tijarar se taji kamar ta haWa kayanta ta bar gidan to amma can gidan Anty Saudan da zata har gara Umman idan Baffa yana nan tana Waga mata ?afa can kuwa ita ta mata mijinta ya mata tunda ta koma washe garin da Jay ya maidota ko zaman awa Waya bata iyayi ba ta gudu saboda Baban Hibban daya tasata a gaba se kace wata abokiyar wasansa yana zolayarta.
Ta tashi zaune jin Umma na ?wala mata kira daga tsakar gida, ?aramin mayafi ta yafa akanta ta fita gaba Waya kewar yaranta ta cikata da suna nan kaWaicin baze mata yawa ba tana tunanin gobe zata kira Maimuna ko iya Ahmad ne a dawo mata dashi ta samu abokin hira. A tsakar gida ta tarar da Umma da Maman Zaliha ma?ociyarsu, ta gaisheta ta amsa tana tsokanarta Amarya ita dai tayi murmushi kawai. Umman ta tura mata madaidacin flask tace
"Gashi nan kaza ce ta dafa miki, akwai tsumi a fridge Win falo Zainab ta aiko miki dashi Wazun na manta ma dashi".

Kai a ?asa ta Wauki flask Win tayiwa Maman Zaliha godiya ta wuce tana jin Umma na cewa
"Magulmaciyar banza kawai" suka ci gaba da magana da Maman Zaliha. ?aki ta shiga ta buWe kazar, in dai dahuwar kaza ce Maman Zaliha ogace a gurin bata mantawa ita takeyi mata sanda tana gidan Ahmad duk kuma kazar da zata ci bata taSa jin daWin ta tamkar ta Maman Zaliha a lokacin Ahmad da kansa yake bata kuWi masu yawa yace ta kai mata a dafa musu kaza, ko zabo ko cicciSi haka yace cewa. Hawaye ya kawo idonta ta saka gefen mayafinta ta share. Wani lokacin zuciyarta se ta ringa hakaito mata yanzu fa Ahmad baze ji daWi ace ta auri Jafar ba ko? Tana yawan tunanin yanzu da ace Ahmad yasan rayuwar su ta baya da Jafar yayi zeyi a rayuwarsa? Ta kan godewa Allah daya rufa wannan sirrin har Ahmad ya koma ga mahaliccinsa be sani ba bata san da wanne ido zata kalle shi ba. Yanzun ma a haka ta kanji kunyar kanta musamman idan ta tuna wancan moment Win se taji sam bata kyautawa Ahmad ba. Bata manta yana yawan nanata yana addu'a ta kasance tasa shi kaWai daga duniya har lahira yanzu ya zeji idan yasan abinda ta aikata da Jafar Win sa?

Tana hawaye tana cin kazarta, dake cikinta da yunwa kazar kuma da daWi tas ta cinye ta shanye romon ta kora da ingantaccen tsumin da cousin Winta Zainab ta dafa musu gallon guda ta aiko mata dashi ga tula tula da take sha shiyasa jikinta duk yake mata se a hankali, dauriya kawai takeyi amma ita da kanta tasan ta kwantowa kanta ruwa haka nan ma tasan irin halittarta balle tayi amfani da abubuwan da zasu sake motsata, tun da Ahmad ya rasu ta Wauka ta rasa duk wani shau?i da yake tareda ita se gashi lokaci Waya ya tado mata da abinda ke neman ya sa ta ta shiga tara kuma ya tafi ya barta. Ta ture kwanon gabanta tana Sata fuska nadamar dalilin daya saka taci ta kamata. To ma akan me bayan ma mijin ba wani mijin azo a gani ba zata zauna tana Satawa kanta lokaci saboda shi.

Wayarta tayi ?ara tayi tsaki ta janyota, seda ta maimaita karanta numbers Win sau biyu tana mamakin Satan hanya yayi kome? Se yau sannan ze kirata? Bata Waga ba seda wayar ta katse ya sake kira kafin ta amsa tana tura baki kamar yana ganinta. A hankali kamar me raWa taji yace
"I tried to hide it underneath but i miss you so muchhhhhh i will do anything to hold you close wife". Ajiyar rai taja kamar wadda ta farka daga suma, ya sake yin ?asa da murya sosai yace
"I can't specify, i just missed everything about you babe as in every inch and detail of you komi nayi kewansa like mad. Ina waje come out quickly before i go crazy please" ya ?arasa kamar zeyi mata kuka. Kashe wayar tayi ta ajiye ta dafe saitin zuciyarta saboda yanda take bugu da sauri da sauri. For about two minutes kafin ta tashi a hankali ta zame cotton doguwar rigar

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login