Showing 147001 words to 150000 words out of 467220 words

Chapter 50 - MATAR MUTUM COMPLETED 1-3 BY MARYAM FARUK.doc

23 Sep 2025

12214

masa shi da tabbatarwa seya gyara zama yace
"Se kum me?"
Muryarsa na rawa kamar a tsorace ya sake cewa
"Sannan idan da hali a gina mun, se muyi lissafi a yankemun abinda zan ringa biya duk shekara har na mallakeshi ya zama nawa".

Shiru ya ratsa tsakaninsu fin tsahon minti goma sha biyar har Ahmad ya yanke ?auna daga samun Amsa me daWi Alhajin kuwa kallonsa yakeyi yana nanata kalmar Aro da yace ya bashi na guri sannan ya yanka masa abinda ze ringa biya kuWin hayar daya ambata tun yana yaro kenan ze ringa biyansa, kenan a matsayinsa na Mahaifinsa baze iya ro?arsa ya mallaka masa gurin kyauta ba ko kum????? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? 
a ya gina masa irin yanda sauran Yaransa Yayan Binta sukeyi ko su Wauki abinsa ma suyi amfani dashi ba tareda saninsa ba?
"Idan ya tambayekan zaka yi masa hakan ne?" Zuciyarsa ta tambayeshi se ya rasa amsar da ze bawa kansa dan haka yaja numfashi yace

"Shikenan, ina fatan kana da Lawyer? Ka haWa duk wata takadda data kamata ka kaiwa Barr, kuyi magana dashi daga nan ka samu Mr Lee ku tsara yanda construction Win ze kasance da abinda za'a kashe daga nan se a tattara lissafin, darajar filin dai shekara goma baya an taya Miliyan dari ban siyar ba, nasan yanzu ya ninka haka sau goma ko fiye da haka tunda kasan inda yake kaima kwaWayin kyawun location Win ne yaja hankalinka dan haka zan bar maka shi a Dari biyu, ka gayawa Barr, sannan ka fara haWo kuWin filin tukunna koda rabine sannan zan yarda na fara gina maka".

Wani sanyi ya ratsa zuciyar Ahmad, ya shiga zuba masa godiya, seda ya gama kuma kwakwalwarsa ta shiga aiki na gaske, Miliyan dari biyu da Alhaji ya ambata kuWin fili seya biya sannan za'a fara gini a ina ze nemota? Tanadinsa ?ar?af idan ya haWa baze fidda kuWin filin ba, amma ya yarda a ransa Allah zeyi masa ze kawo masa hanyar da ze samu abinda ze cika burinsa.

*ALBISHIRINKU MATA YAN UWANA YAN KWALISA NAZO MUKU DA WANI DADDADAN LABARI!!!.*

*NASAN KUNDADE KUNA NEMAN FITACCEN GURIN DAZAKUJE AMUKU GYARAN GASHINKU DANA JIKINKU CIKI DA WAJENSA,TO YANXU DAI GA DAMA TA SAMU...*

*LABARI NAKE BAKUFA AKAN AFINTY QUEENS SHAHARARREN SHAGONMU NA SALOON DAYA HADA KOMAI DA KOMAI DA KOWACE MACE YAR KWALISA IRINA KE BUKATA,SANNAN MUNADA KWARARRUN MA'AIKATAN DASUKASAN KAN AIKINKINSU,KUZO AFINTY QUEENS KUBIYA KUDI MUKUMA MU BATA LOKACINMU DOMIN TSATSTSAFO DUK WANI KYAWU NA JIKINKU DA ALLAH YAYI MUKU...*

*A AFINTY QUEENS MUNA AYYUKA KAMAR HAKA:*

*- HAIR SALOON*
*-HENNA*
*-SPA*
*-DUKKAN*
*-PEDICURE*
*-MANICURE*
*-SANNAN MUNA DA TURARUKA IRIN NA AMARE YAN MATA DA KUMA MAI KANKAT DAN UWAR GIDA TA TURARA GIDANTA JIKINTA DAMA KAYAN SAWARTA ITA DA YARANTA,,HARMA ZAWARAWA DUK MUN TANADI KOMAI*
*DOMINSU SUMA*

*-MUNADA SHOES AND BAGS SBD ISASSUN MATAN DA SUKA AMSA SUNANSU MATA*=?
?
*- MAKEUP NA BRIDAL ND CASUAL...*

*IDAN KINSAN KINAJIN LABARIN SHAGON SALOON NA AFINTY QUEENS AMMA BAKI TABBATAR DA YADDA AIKINSU YAKE BA TO YAR UWA GADAMA TASAMU MEZAKI TSAYA JIRA MAZA KEMA KI ZARGAYO SHAGONMU DAZAN JERA MIKI ADDRESS DINSHI A KASA DOMIN KEMA KI TABBATAR DA KALAR IRIN NAMU KWAZON DA MUKA KWARE AKANSHI GURIN GYARAN JIKIN YAN UWANMU MATA KUMA MUKE GABATAR MUSU DA JAKUNKUNA DA TAKALMA HARMA DA TURARUKAN WUTA DANA SHAFAMA JIKINSU DON NISHADIN ZUCIYARSU DANA MAZAJENSU....*

*AFINTY QUEENS DISCOVER BLISS IN BEAUTY =؅?=د?*

*Address =?G?=?G?:*
*KU ZIYARCE MU A SHOP NO.9&10 SHEMA PLAZA,BEHIND SHEMA FILLING STATION KASUWAN BACCI KADUNA*
*TEL:08133379628.*

*MATAR MUTUM*
*NA MARYAM FAROUK (UMMU MAHEER*

*FIKRA WRITERS ASSOCIATION*

*LITTAFIN KUDI NE*
*PAY 500 A ASUSUN*
*7061838488*
*OPAY DIGITAL SERVICES*
*MARYAM FAROUK*
OR
*0709290797*
*ACCESS BANK*
*SE A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488*
*IDAN KATINE A DAUKI HOTONSA A TURA ZUWA LAMBAR SAMA VTU KUMA A TURA A 08142548705*

*Kuyi following dina a Arewabooks @Maryamfarouk01 inda zaku karanta wannan littafin tareda sauran littattafaina*
*NAGODE*

*BOOK 2*
*PAGE 3*


Daga gidan gona kai tsaye gidan Anty Manfusa Inda ya ajiyw Momy dan tare suka fito. Yayi masu bayanin yanda sukayi da Alhajin dan Anty Manfusan na cikin waWanda zasu saka hannun jari idan Allah yayi buWewar shopping mall Win.

"Wato uban nan naku lamarin sa yana matu?ar bani mamaki, yanzu ba'a rufa wata guda ba Yayansu Nihal (Dan Mijinta ne) yake cemun Anyi musu ?arin kuWin hayar shaguna a plaza, da aka kawo musu takaddu yaga an canza sunan da yake jiki wai yanzu ta zama ta NAZIRU BECHI, a yanda akace wai siya yayi gurin Alhajin wasu kuma sunce bashi yayi, nima yana faWa nace wlh ?aryane bashi yayi saboda rashin tsoron Allah duk girman plazar nan ace ya bawa Naziru shikaWai shagunan ciki fa sunyi hamsin? nifa da nice a matsayinki wlh da tuni gayyar ta watse dan bazan zauna ana wannnan kutumar ubancin inyi shiru ba"

"To banda abinki Manfusa Naziru ai ?ansa ne yana da damar mallaka masa duk abinda yayi niyya" Momy ta bata amsa. Manfusa ta harzu?a tace
"Shi Ahmad Win ai Agola kikaje masa dashi shi yasa ze kasa bashi kyaitar fili, tsabar zalunci kuma ya lafta kuWi har Miliyan Wari biyu ce masa akayi Ahmad Win barawo ne irin sauran Yayansa da ze mallakin waWannan kuWin a shekarunsa? Ko kuwa saboda yana rayuwarsa cikin rufin Asiri bai taSa neman wani abu a hannunsa ba?"

"Hakan ma da yayi nagode Anty dan wlh idan a gurin wani ne darajar filin nan ta zarce haka ko a haya za'a bani a gine dai a shekara Miliyan Hamsin sen bayar da ita wlh kinfa san location kafin ni nasan manyan Organization da suka nema ya hanasu har Gwamnati seda taso ta kwace gurin Baba Al?ali ne ya tsaya masa Allah ya taimaka aka bar masa in sha Allahu in har muka samu abinda muke so shekara biyar tayi yawa zamu mallakeshi ya zama namu kawai dai kuyi ta tayamu da Addu'a" Ahmad ya yayyafawa wutar masifar data fara ruwa, dole tayi shiru tunda uwa da ?an da take ha?ilo akansu abinma.be damesu ba.

A hanyar komawa gida Momy take ce masa
"Nifa ubana ina tsoron mutanen gidanku akan maganar gurin nan, ban manta ba Yayanku Zakariyya ya taSa nemar ya bashi ya gina Hotel ya?i, baka tsoron idan sunji suyi maka lamSo se ka saka kuWinka su zugashi ya kwace?"

"Momy, dan Allah ki kyautata zato akan abin nan ki cire duk wani wasi wasi daga ranki. Nida ke duk mun sani Alhaji kaifi Wayane, idan da beyi niyyar bani ba koda ace duniya zata taru akansa wlh baze bayar ba haka nan yanzu daya ce ze bada bana tsammanin da akwai abinda ze canza masa ra'ayi akan hakan, ki kwantar da hankalinki"
"Ai shikenan, Allah yasa tabbatar da Alkhairi"
"Amin Momy, abinda ya kamata ki faWa kenan" daga nan suka shiga wasu hirarrakin harya sauketa gida ya juya yana so yaje yaga Barr Ansaruddeen Kalam, Childhood friend Winsa ne kuma shiya Aminta dashi da zama Lawyersa, a gidan Barr yayi Magriba da isha suna tattauna yanda za'ayi da takardun daya kamata su haWa kafin su zauna da Lawyer Alhajin.

Cikin hukuncin Allah yarjejeniya ta ?ullu tsakanin Alhaji Audu Bechi da Ahmad Bechi, kowanne bangare ya gamsu da tsarin da akayi har kuma BECHI CONSTRUCTIONS sun aza harsashin gini bisa Jagorancin Mr Lee, Injiniyan da yake shugabantar bangaren gine gine da ?ere ?ere na BECHI GROUP OF COMPANIES kujerar da Hajiya Binta take hari domin kuwa tuni ta matsantawa Faisal tafiya bangaren Engineering Win yanzu haka yana shekara ta biyu ne a Civil Engineering, burinta daya gama kuma a tunSuke Mr Lee ya koma ?asarsu Faisal Bechi ya maye gurbinsa.

Ubangiji ya sirrinta Al'amarin ta yanda har gini yakai Linta Hajiya da Yayanta basu san abinda ake ciki ba, koda yake Yakubu Bechi ya sani saboda bu?atar fitar da kuWin da aka kai kan Teburinsa dan tuni ya maye gurbin Aminu Bechi.

Yakubun be fiya shiga sabgar da bata shafeshi ba, a barshi dai da son kansa dan haka muddin Abu ba wai ya shafi personal Interest nasa bane baze ce komai a kai yanzun ma haka ce ta faru yayi shiru ya saka hannu kawai kamar yanda aka bu?ata be kuma tattauna maganar da kowa ba.

Yanda akayi Labari ya isarwa Hajiya Binta kuwa hanya ce ta bida ita ta gurin da filin yake zataje gaisuwar Lantana wadda Allah yayiwa Rasuwa, Hajiyar bata yada Lantana ba a wannan bangaren kam tayi Al?awari dan Lantanar tsautsayi ta gamu dashi a shegen yawonta mota ta kaWeta shikenan ta gamu da ?afa, shekararta goma a zaune kafin Ajali ya sauka Bintan na le?ata lokaci lokaci duk kuma sanda ta wuce seta kalli wannan fili tana wassafa burinta akansa. A Zoo road yake, zuciyar Kasuwanci, kanta takeyiwa tanadi zata gina plaza ta zuba shaguna wanda ko iyakarsu me kadararta tasan ba ?ananan kuWaWe zata ringa sha?a duk shekara ba.

Jiki na rawa ta samu Alhaji Zakariyya da zancen waya tada gini a wannan filin?
"Badai siyar dashi yayi bamu sani ba? Ka nema ya hanaka ina fakonsa shine ze siyar? To duk wanda ya siya ma kuwa ya siyi Asara dan ciniki be yuwu ba" Inji Hajiya Binta. Alhaji Zakariyya da har ya fita shiga ruWu domin a halin da ake ciki a yanzun ya karSi kuWi a hannun Lebanese da suke son gurin zasu gina Hotel dan bashi zeyi ginin ba kuma ya musu Al?awarin kafin watan da ake ciki ya ?are zasu fara aikinsu se kuma yake Jin wata magana daban.

Bangaren Land and properties ya tafi ya samu Alhaji Musbahu, basa shiri saboda duk sanda suka tashi cefanar da wani abun muddin basu kai masa takadda ta gaske me Wauke da signature Chairman ba baya basu Approval, Zakariyyan kuma baya duba Girma ko Shakarun Alhaji Musbahun haka ze zageshi a gabansa yace ai bashida gadon ubansu balle ya ringa hanasu TaSa dukiyarsu, yau Win se gashi harda risinawa ya gaidashi kafin ya tambayeshi suwa aka bawa Filin da har suka fara gini"

"Ban sani ba, kaje ka samu uban naka kaitsaye, ku masu jiran Gado ma kuke Wauka kuyi yanda kuka so da guri balle me abun daya tara da guminsa?" Amsar da Alhaji Musbahu ya bashi kenan shima kuma ita ya mayarwa da Hajiya.

Ranar akayi dacen itace da Girki dukda Alhaji Audu baya gari ya tafi Umara amma a daren ranar ake saka ran dawowarsu shida Hajiya Rabi da Yammatan gidan duka suka tafi Umara wanda Albarkacin Tafiyar da za'ayi da Hajiya ?arama da Sarah, wanda ze buga musu Visa da karanbaninsa ya haWa da duka sauran Yara Matan da suke a gidan se kuwa gashi Alhajin bece komai ba akai. Amma fa seda akayi uwarka ubanka da Hajiya Binta kafin tafiyar ta yuwu harda Allah ya isa yanda kasan kuWinta aka Wiba akayi tafiyar dasu.

Babu shirin da tayi na cewar yau Megidan ze dawo tunda ya tafi ma sau biyu sukayi waya Albarkacin zata bashi sautin Dogayen Rigunan Gumama wanda take bulalawa a tsakar gida tayita yawo kamar Maro?iya, idan tacewa Hafsatu ko Sarah su siyo mata cewa zasuyi ta tura da kuWi shiyasa ta aikawa da Alhajin hotunan kalarsu kamar wani Yaronta tace guda biyar za'a siyo, da taji shiru be duba sa?on ba shine ta kirashi, na biyun ma tinin an siya tayi masa yace Eh Alhalin ko downloading yaga me ta tura beyi bama.

?arfe goma na dare jirginsu ya sauka kafin a gama dakko musu kayansu su tafi gida sha biyu saura shi Alhajin dama VIP lounge na Arrival ya shige abinsa yace idan sun gama a sanar masa dan baze tafi ya barsu su duka mata ba ga dare, Ahmad ne kaWai ya tsaya Tarbarsu a samarin gidan, a cikin gida kuma Momy ta musu Wan abin taSawa dukda dawowar darece amma tasan Alhajin baya cin abincin jirgi ko China zeje sedai yasha ruwa ko shayi shiyasa ta tanadar masa abinda zeci dukda ba girkinta bane sedai ganin Yau Hajiyar ko Hanyar kitchen bata kalla ba yasa tayi, kamar ma dai bata da lafiya ne dan karaWin da take isarsu dashi a gidan ma yau shiru kunnuwansu sun samu sa'ida.

A ?akinsa Momyn ta shirya masa komai ta bari tayi masa sannu da zuwa daga bakin ?ofa ta wuce ?akinta da Yammatanta da suka ru?un?umeta suna faWin sunyi kewarta. Dukda darene haka ma'aikatan gidan Maza suka ringa shiga Babban Falo suna masa sannu da zuwa, Hamsha?ai kuwa, Yakubu, Faisal da Salim harda Mu'allim suna ?akunansu babu kuma wanda yake bacci a cikinsu daga masu chatting se masu waya da Yammata gara Mu'allim Win ya fita ya tarbi uwarsa ya rakata cikin gida kafin ya koma yaci gaba da Chatting, Tashen Balaga yake akayi rashin sa'a kuma Yayyensa da suke kewaye dashi babu wani gwani da ze kwafi abin Arzi?i a gurinsa shiyasa shima yake nema ya tashi da ?abi'u irin na gidansu da ya zame musu Gado wato halin ko in kula.

Hajiya Binta bata saurara ko Babbar Riga Alhajin ya cire ba yana sallamar Masu aiki ya hau sama ta dirar masa a ?aki, ransa a jagule da rashin ganin sauran Yaran dake cikin gidan tamkar yanda Ahmad yazo ya tsaya kuma yaga motar kowannensu a ajiye dan ya kafa dokar hana yawon dare ?arfe goma ake rufe masa Get ba shiga sedai fita duk kuma wanda ya kwana a waje shi yasan ta yanda yake hukuntasu kuma sun biyu suna bin dokar.

"Yawwa Alhaji sannunku da sauka, nace Wazu naje Goron dutse se nabi ta Zoo road zan karbi sa?o, base naga gini tsiriri a filin kaba? Ni na gaza fahimtar ma me ake ginawa yo bulune ta ko ina an tayar da katangu inaga hawa uku ma aka Wora bene a gurin" Hajiya ta faWa tana zama idanunta kuma akan kwanukan da Momy ta ajiye. Alhaji ya shiga kacaniyar zare kayan jikinsa, sati biyun nan yaji dadinsu ya samu lokaci da Amaryarsa dan har wani Wan kumari yayi yanzu ya dawo zata fara ?warzabarsa, ita bata tarairayeshi ba sannan ta addabi masu tarairayarsa ta hana musu sukuni.

Seda ya cire rigarsa ta rage singlet da Wandon dakakkiyar Gedzenar jikinsa kafin ya janyo teble ya bude Casserole Win da Momyn ta ajiye, Irin dankalin nan na yan gayu da ake soyawa sama sama sannan a gasa yaji Albasa da Koren tattasai da Yellow da zafinsa alamar yanzu aka gama ko akayi Microwaving ?amshi na tashi. Ya tsiyaya Shayin dake cikin yar buta yayi bismillah ya faraci ba tareda ya bata amsa ba. A daren take son jin yanda ake ciki dan haka tayi shiru ta tuno da tsohuwar kissa ta matsa tana cewa

"Yi ha?uri duk na sha'afa banma ce maka ga abinci ba, Allah sa be huce ba dan na daWe da gamawa".

"Da dai harshena ya dena tantance WanWano sena yarda, sannan yaushe kika fara siyan irin kwanukan nan? Ina cewa kikayi na yara ne sedai a siyawa su Dada ko kuma kin canza shawara kinbi sahun su Aisha tsofai tsofai daku kuna Asarar kuWi a siyan kayan kitchen?" Alhajin ya mayar mata da martani yana murmushin rainin hankali. Tayi tsam, har yar kunya ce ta kamata wato yasan ba ita ta ajiye ba kenan? Amma seta waske tajira harya cinye tas ya shiga banWaki ya kuskuro baki ya zauna a bakin gado yana duba wayarsa.

Maganar ta sakw soka masa hankalinsa naga sa?onnin da yake dubawa yace mata
"Ahmad ne ze bude kanti a gurin".
Ruwa take sha babu shiri ta ?ware nan ta shiga tuttula tari kamar zata amayo kayan cikinta Alhajin na jera mata sannu. Seda ya lafa mata ido da fuska sunyi jajir se sauke numfashi takeyi dan ta sha?u amma bata daddara ba ta kalli Alhajin tana zaro ido tace

"Ban fahimci Ahmad ne ze buWe kanti ba? Ka gane inda nake maka zance kuwa? Filin Mota fa nake magana bawai wani guri daban ba"

"Nan Win nima nake miki zance ai, ba kince kinga ana ta gini ba? Shopping Mall ze buWe a gurin" ya sake bata amsa. Yanzun ta tabbatar da ya gane inda take nufin kuma gaskiyar zancen yake gaya mata. A fusace tace
"Ahmad ze buWe shopping Mall ko zaka buWe masa? Ni zaka ninke a baibai wannan filin zakace ka bawa Ahmad ya bude kanti a ciki ina nan da Me sunan Alhaji yace yana son gurin cewa kayi da tanadin da kakeyi akai ashe ?an gidan Aisha kakeyiwa tanadi zaka buWe masa kanti?"

Hankali kwance dan seda ya kishingida kafin ya bata amsa yace
"Ko kaWan yanda dai kikaji nace miki shi ze buWe to hakan ne nidai na bashi fili mun kumayi Agreement harya biyani wani kaso zan gina masa gurin a hankali idan kasuwa ta kafu ze ringa biyana har mu warware"
Data rasa abin ce masa se kawai tace
"Ai shikenan" ta fice daga Wakin.

Da Asubar Allah ta tattago Naziru da Zakariyya ta shaida musu abinda akw ciki, suka ?ule a Waki suna ta ?ulle?ullen yanda za'ayi a rusa maganar amma sun gaza samo hanya domin a yanda Alhajin ya iya bata amsa jiya tasan ba wata magana da zata faWa yanzu ta samu shiga a gurinsa. Idan ya murWe barinsa takeyi domin a garin tace seta latsa dole se ayi rashin sa'a kwaSarta tayi ruwa shiyasa yanzun ma kamar zatayi kuka tace

"Kubar komai a hannuna zan barshi dai yanzu tunda naga kansa yana haya?i amma zan maidashi hankalinsa ne kuma wlh ba ?an Aisha ba ko ubanta ne yayi kaWan daya mallaki gurin nan se an karSeshi".

NAZIRU da yayi shiru yana ta tunani ya gyara zama yace
"Wani tunani nayi, tunda kince yace miki ba kyauta ya bashi gurin ba na tabbatar kuma dagaske ba kyautar bane, me ze hana mu bi abin a siyasance? Nasan dai a shekara goma Ahmad indai ba Naman mutane ze ringa siyarwa ba a gurin nan baze haWa kuWin filin nan da ginin da za'ayi masa ba..."

"Kai na rabaka, ka dena ganin yaron nan yana yawo tsalo tsalo dashi wlh neman kuWine ya hanashi ?iba, yanda kasan wannan tsohon haka yake babu sana'ar da baya gwadawa" Alhaji Zakariyya ya tare Nazirun. Seya ja tsaki yace
"Ka dakata Malam kaji point Wina, i know what I'm saying, kai kasan nawa ake taya filin nan Tsohon nan ya?i siyarwa? Kuma kaidai kasan riba kawai ya sani babu batun faWuwa ko mu da yake mana Gwanjon kayansa ai saboda uwarmu ta iya ?asarta ne, ni shirin dana hasaso yanzu as i was

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login