Showing 132001 words to 135000 words out of 467220 words

Chapter 45 - MATAR MUTUM COMPLETED 1-3 BY MARYAM FARUK.doc

23 Sep 2025

12232

hade masa su ze turo wanda ze Wauka ya wuce da sauran.

Binta data tsammaci Audu bazeyi murnar samun ?aruwar ?iya mace ba se taga akasin haka, murna sosai ya ringayi, kwanan Aisha uku da haihuwa ta tafi wanka gida wanda da?yar Audun ya bari gida ya rage Shida Binta se yara. Binta ta shiga zullumi, tunda Aisha ta haihu walwalar Audu ta ?aru haka bashida wata hira seta yar jaririyar me suna Amina taci sunan Mahaifiyar Najibullahi yayiwa kara, basuyi sati biyu da tafiya ba ya kwashi yaran duka ya kaisu su gano Laila kamar yanda suke kiran yarinyar wannan ya Waga mata hankali ta kuma shiga zullumin to kodai itama ta haifi Mace ne saboda bata so ace wani ?a yafi nata shiga zuciyar Audu, amma da ta zauna tayi dogon Nazari seta watsar da waccen shawara, ita tana lissafine ne da abinda za'a mutu a bar mata, Yara Maza sune masu Gado duk wannan soyayyar da yakewa Lailan a banza tunda baze Wauketa ya Wora akan dukiyarsa ba da wannan ta watsar da tunanin haihuwar Mace taci gaba da lissafin zazzago Yara Maza.

Tsiranta da Aisha kwana goma sha tara ta haihu a Asibiti ta samu ya mace kyakykyawa da ita tamkar Laila dan yarinyar na fadowa Nurse din data karbeta ta dagata tana cewa
"Masha Allahu zankadi kin samu kyakykyawar yarinya da gani da Mahaifinta tayi kama dan ta fiki kyau" Nurse din ta gaya mata magana dan Binta ta gallabesu se dai idan bataje Awo ba amma tabbas se tayi faWa da wata daga cikinsu.

Zabura Binta tayi ta fizgi ?afar Yar kamar wadda ta fizgi leda ko wani abu mara rai, tawara ?afafun tana so ta tabbatar dagaske Mace ta haifa ko kuwa tsokanarta sukeyi data tabbatar din kuwa seta saki yar Nurses da basu gama dawowa daga mamakin fincikar da tayiwa ?afar yarinyar ba suka dulmiya cikin na sakinta da tayi ba taredadamuwar zata faWi a ?asa ba. Kuka ta fashe dashi bayan data koma ta kwanta. Nurse Win data cafe yar ta kalleta cikin Sacin rai tace
"Amma kedai anyi yar ku*****ba, banda ke mahaukaciya ce dabba ki fizgi ?afar Jinjira haka bakya ko tsoron ki ji mata ciwo sannan ki saketa a ?asa? Wlh badan mu muka karSi haihuwarki ba da nace sato yarinyar nan kikayi"

"To kice mana, idan ma kina sonta ki ri?e na baki kuma karki sake zagina wlh dan na fiki iya tashanci" Binta ta hayayya?o mata, matar zata sake magana sauran suka tareta sukace ta barta da alama tana da taSi a ?wa?walwarta.
"Sedai uwarku ce me taSi a ?wa?walwa bani ba" ta bisu da zagi sanda suka fita taci gaba da kukan ta.

Haka suka tattaro suka dawo gida abin dai babu daWi yanda Binta ta ringayi kamar me taSin hankali duk saboda ta haifi Mace wannan fincika da tayiwa ?afar Nazira ita tayi sanadiyyar Nakasarta wanda ba'a gane ba har seda ta kai munzalin tafiya sannan bayan dogon bincike likitoci suka gano wasu ?ananan jijiyoyin dake ri?e Sangalalen ?afa da tafin ?afarta ne a tsinke shiya nakastata ya zama ?afar bata Waguwa sedai ta jata a ?asa.

Lokaci daya Hadiza da Aisha suka dawo, tafiyarsu lamuran Asare Asaren da Audu yakeyi ukayi sau?i, suna dawowa tamkar an watsawa wuta fetur abu ya koma sabo farfaWowar daya fara aka sake kwanciya rigijin harma abin yafi nada muni. Akace zuciya bata da ?ashi balle kuma irin ta Audu me cike da wasi wasi a hankali se famfon da Binta take masa akan ya auro masu fararen ?afa ya fara tasiri a zuciyarsa. Ya fara tsangwamar Hadiza da Aisha domin a cikinsu ne yake ganin akwai silar taSarSarewar Arzi?insa, kyara, hantara, wula?anci ya fara yawa, Hadiza bata shiru idan ya mata ramawa takeyi daman Binta bata isheta kallo ba dan tasan gamonsu Aisha ce take masa shiru dan haka diban Albarkar tasa yaso yafi yawa akanta musamman da Binta ke yawan cewa daman an fi samun masu farar ?afar cikin mata masu shiru shiru kuma ai data tafi wankan gida abubuwa sun farfaWo amma tana dawowa ta dawo da tsiyarta.

Abu dai gaba yakeyi kullum ba baya ba, idan yayi kamar yabi ta Binta yaje ayi masa istahara a fayyace masa wwacece silar rugujewar Arzi?insa se kuma ya tuna nasihar Yakubu dayace jarabawa ce saga Allah idan yayi ha?uri a sannu komai ze zama tarihi seya kanne yaci gaba da Addu'ar neman Wauki daga ubangiji. Cikin wannan yanayi aka cinye shekara guda wanda a kullum ta Allah abin zama yake jiya tafi yau, Audu da harya fara mance lissafin abubuwan daya mallaka se gashi a hankali ya fara Waga kadarorinsa yana siyarwa a ?o?arinsa nason farfaWo da harkar Mansa dake neman dur?ushewa baki daya ya saki komai ya mayar da hankali akanta domin itace ?arfin tattalin Arzi?insa.

Binta ce takai wa mahaifinta rahoton abinda yake faruwa da Audun, shiri tayi ta kwashi kayanta domin tafiyar da tayi bata saka ran zata dawo ba, to ta dawo tayi me? Arzi?in da take zaman gadi yana shirin bin rariya wahala na doko musu sallama ita kam bada ita za'ayi wannan zaman ba. Alhaji Zakariyya ya tashi Wan aike takanas aka kira masa Audu, sun tattauna amma a duk maganar da sukayi ya kasa gano musabbabin wannan Asara dake hawan Audu kamar wanda akayiwa Baki haka nan be bi takan shirmen Binta ba ya sake daukar Kudade masu kaurin gaske ya bashi yace kuma duk in wata matsala ta tashi karya jinkirta ya je gareshi, wannan karamci na Alhaji Zakariyya ya ?ara samarwa da Binta gurin zama a zuciyarsa domin ya sani Allah ne ya haWa shi da Alhajin amma Auran Binta na daga abinda ya ?ara dankon zumunta a tsakaninsu kuma duk abinda zeyi masa zeyi dan Allah kuma saboda yana auran yarsa, wannan tasa ya ?ara kulla aniyar ri?e Binta dakyau domin bashida wata hanya da ze sakawa da Alhajin sama da hakan tunda duk sanda zwje gurinsa se yayi masa tanbihin ya kula masa da Binta karya dubi halinta.

Wannan kudi da Alhaji Zakariyya ya bawa Audu basuje ko ina ba yana dawowa Kano wani Abokinsa yayi masa tallar Farin wake, a shekarar an samu ?arancinsa acan wani ?auye suka samoshi yace su siya da yawa su ajiye zuwa A kwana biyu idan farashi ya hau su fitar su siyar dashi su samu riba. Audu be taSa yin irin wannan kasuwancin ba dan ko wani yaji ze siyi kaya ya Soye zuwa yayi tsada sannan ya siyar se yayi magana ya nuna masa rashin dacewar hakan amma a halin da yake ciki yanzu ta yanda ze farfado da jarinsa kawai yakeyi shiyasa ba tareda dogon tunani ba ya siyo wake aka jibge a suto, ba'a rufe watanni uku ba wake yayi muguwar tsada ya ninka kudinsa sau biyu akan abinda suka siyeshi lafiya lau Alhaji Mala Abokin Audu ya kwashe wakensa ya kai Kasuwa ana bude store din da kayan Audu suke aka tarar da wake dai babu na moro ?wari sun masa kaca kaca dayawa har ya fara yin gari tsabar yanda ya lalace kamar wanda ya shekara biyar a ajiye.

Hankalin Audu yayi ?ololuwar tashi da wannan Al'amari, Alhaji Mala da Bashir suka sake jaddada masa tabbas idan ba Asiri ba to cikin matansa akwai me Ba?ar ?afa a tasu falsafar. Mala yace ya shirya ze kaishi gurin Malaminsa duk abinda ake ciki ze fayyace masa, yace Malamin yayi tafiya nan da sati ze dawo shima daman zeje dan akwai tafiya da zeyi yana so a bashi sa'a.

"Ai Ba'a zama haka Alhaji Audu yanda mutane suka Saci da jefw jefe wani ido kawai ze saka maka kaga komai naka ya tasamma lalacewa idan kayi sake magauta se sun kaika ?as wlh kana kallon dai yanda abubuwa suke tafiyar maka kai base an ce maka da wani abu a ?asa ba, idan ka biye ta wannan Yayan naka kana ji kana gani sedai ka koma jiran wa wani shago ana sammaka na cefane sunanka ya tashi daga sahun matasan masu kudi ka koma layin yan karayar Arzi?i" Inji Mala.

Yana komawa gida ranar Binta ce take da girki, damuwa ta masa yawa yanzun shiyasa abu da yawa ba s an tambayeshi ba yana zaune zeyita rattabo zance kamar wanda kansa ya kwance.
"Ina za'a jira har nan da sati ai ka tashi kawai kaje nan gurin Malam Salisu Mijin Lantana, ba tuntuni nake gaya maka ba amma ka?i jin ta tawa ai yanzu da aka faWa maka a waje ka yarda. Bari kaga inje in gano maka idan yana nan ai ba'a bori da sanyin jiki wlh gara asan abinda ake ciki" Binta ta faWa tana saSar Hijabi.

Audu bashida zaSi a wannan gaSar ruwan kashe gobara kawai yake bu?ata shiyasa be hanata ba, Hadiza na zaune tsakar gida kan tabarma tana cin Abinci garin da dan zafi zafi ga tsohon cikin da take dashi ya ?ara mata jin zafin Binta ta wuceta tana cewa
"Maza kici gobe sedai kici a gidan me dattin hula".

Can ta samu Lantana suka gama ?ulla yanda za'ayi Lantana ta shiga ta zayyanewa Malam Salisu yace babu damuwa duk yanda tace hakan za'ayi. Seda sawu ya fara daukewa Sha daya saura kafin Audu ya tafi gidan Malam kamar wani munafuki, Malam Salisu ya tambayeshi sunan sa dana Matayen nasa gaba Waya ya gama zana ?asarsa yana jan wani kwandalelen carbi se muzurai yake da ido yana motsa baki yayi zane ya share yafi sau biyar kafin ya kalli Audu yace

"Gaskiya Alhaji akwai gagarumar matsala, wai ma ya akayi haka wannan Aure babu bincike?"
"Kamar yaya? Anyi bincike mana" Audun ya bashi amsa yana kallonsa a wani Wage, Malam Salisu ya murmusa yana cigaba da zanen sa yace
"Ba binciken halayya ko Asali nake nufi ba, Aa burujin ?asa. Ya kamata ace in za'ayi Auran Alhaji a ringa bincikawa aga taurari matar ya suke zasuyi daidai da naka ko kuwa? Kamar dai yanzu kaga ita ta farin Fatsuma Binta kace sunanta ko? Wannan mahadin Arzi?i ce.

Kaga kai Tauraronka wuta ne, ita kuma Iska ce, ya kaga wuta a lokacin bazara yanda iska take fifitata inta ringaci balbal ai Allah kadai ke iya kasheta to haka ne hadin naku taurarinta suna ingiza Arzi?inka zeyita hauhawa ne to kuma se akayi rashin dace ita Aishatul Humaira taurarinta na ?asa ne, wuta kuwa da an yafa mata ?asa ai mutiwa takeyi to me kankat kuma Hadizatul kubura ita taurarin ruwa ne shiyasa da suka hadu su biyu se ?arfinsu ya danne na fatsuma suke neman nakastaka kuma in har ba'a dauki mataki ba gaskiya Alhaji abin bazeyi kyau ba dan abinda ?asar nan take nunamun idan ba'ayi da gaske ba har rigar sawa ka fita seka wayi gari baka da me kyau abinci kuwa wata rana se an kwana ba'a ci ba sannan yawan haihuwarsu yanwan Talaucin da zasu cigaba da saukar maka a gida".

Ranar kwana zaune Audu yayi yana ?ullawa da kwancewa, Binta bata tambayeshi yanda sukayi ba domin ita ta tsara komai se dariya take a cikin bargo dan ta sadda?ar gobe daga Hadiza har Aisha kwanan gidajen tsoffinsu zasuyi. Washe gari da duku duku ya mata sallama yace ya tafi Bechi, be ko bi takan sauran matan ba, yara da suke gaidashi ma be iya amsawa ba ya fita burinsa ya isa Bechi ya samu Hashimu domin wannan sabgarsa ce shine yasan takan Malamai. Ya isa Bechi be zarce ko ina ba se gidan Hashimun yayi rashin sa'a baya nan amma inji Jamila ba dadewa zeyi ba dan yace a aje masa abincin rana. A tsakar gidan ya zauna kan Turmi tsabar halin da yake ciki ya gagara shiga turakar Hashimun da tace ta masa shimfiWa ta aje masa ruwa da fura.

Seda akayi Azahar Hashimu ya shigo, an gaya masa anga wucewar Audu amma be yarda ba dan har can gida ya ratsa be ganshi ba se gashi ya tarar dashi a tsakar gida kan Turmi fuskarsa ta gama bayyanar da tashin hankalin da yake ciki. A ta?aice ya masa bayani babu bata lokaci ya goyeshi a mashin suka tafi wani dan ?auye dake gabansu kadan. Bayanan Malam Salisu sunyi kamanceceniya da juna sedai an saSa lamba a wasu guraren kamar Taurarin Aisha da Binta dashi bafulatanin yace masa taurarinsu iri daya ne da nasa dan haka babu matsala a hadinsu Hadizan dai itace me matsalar kuma akasin da aka samu Taurarinta nada matu?ar haske shiyasa ta tasiranci duka su ukun suke karbar gashi.

Bala'un da Dan fulani ya jere masa je afka idan ne rabu da ita ba sun zarce na Malam Salisu, Hashimu yace
"Dama a garin aure aure tun mutum na kwaso Arzi?i harse ya Webo tsiya gashi dai ka gani ai se ka san abinyi tunda wuri dan duk abinda Malam Sallau ya faWa da wuya kaga be faru ba, seda ya hanani Auran Saude na?i gashi ko ina karbar sakamakona"
"Aishi ba Allah bane bare kace duk abinda ya faWa seya tabbata" Audun ya bashi amsa. Hashimu yayi dariyar rainin hankali yace

"Na fika sanin haka, amma tunda muka yarda dashi har muka zo tambaya gabansa ai magana ta ?are, ya rahe naka ka Wauki matakin daya dace" a gurin sukayi sallama Audu ya juyo Kano zuciyarsa fal wasi wasi. Ya daukarwa Yakubu Al?awarin baze sake sakin wata mace ba gashi kuma yanzu dole ta saka zeyi sakin kuma ya san duk ta yanda zeyiwa Yakubu bayani baze taba fahimtarsa ba. Maganar gaskiya kuma baze zauna yanaji yana gani ya rasa komai nasa dalilin wata mace ba.

*ALBISHIRINKU MATA YAN UWANA YAN KWALISA NAZO MUKU DA WANI DADDADAN LABARI!!!.*

*NASAN KUNDADE KUNA NEMAN FITACCEN GURIN DAZAKUJE AMUKU GYARAN GASHINKU DANA JIKINKU CIKI DA WAJENSA,TO YANXU DAI GA DAMA TA SAMU...*

*LABARI NAKE BAKUFA AKAN AFINTY QUEENS SHAHARARREN SHAGONMU NA SALOON DAYA HADA KOMAI DA KOMAI DA KOWACE MACE YAR KWALISA IRINA KE BUKATA,SANNAN MUNADA KWARARRUN MA'AIKATAN DASUKASAN KAN AIKINKINSU,KUZO AFINTY QUEENS KUBIYA KUDI MUKUMA MU BATA LOKACINMU DOMIN TSATSTSAFO DUK WANI KYAWU NA JIKINKU DA ALLAH YAYI MUKU...*

*A AFINTY QUEENS MUNA AYYUKA KAMAR HAKA:*

*- HAIR SALOON*
*-HENNA*
*-SPA*
*-DUKKAN*
*-PEDICURE*
*-MANICURE*
*-SANNAN MUNA DA TURARUKA IRIN NA AMARE YAN MATA DA KUMA MAI KANKAT DAN UWAR GIDA TA TURARA GIDANTA JIKINTA DAMA KAYAN SAWARTA ITA DA YARANTA,,HARMA ZAWARAWA DUK MUN TANADI KOMAI*
*DOMINSU SUMA*

*-MUNADA SHOES AND BAGS SBD ISASSUN MATAN DA SUKA AMSA SUNANSU MATA*=?
?
*- MAKEUP NA BRIDAL ND CASUAL...*

*IDAN KINSAN KINAJIN LABARIN SHAGON SALOON NA AFINTY QUEENS AMMA BAKI TABBATAR DA YADDA AIKINSU YAKE BA TO YAR UWA GADAMA TASAMU MEZAKI TSAYA JIRA MAZA KEMA KI ZARGAYO SHAGONMU DAZAN JERA MIKI ADDRESS DINSHI A KASA DOMIN KEMA KI TABBATAR DA KALAR IRIN NAMU KWAZON DA MUKA KWARE AKANSHI GURIN GYARAN JIKIN YAN UWANMU MATA KUMA MUKE GABATAR MUSU DA JAKUNKUNA DA TAKALMA HARMA DA TURARUKAN WUTA DANA SHAFAMA JIKINSU DON NISHADIN ZUCIYARSU DANA MAZAJENSU....*

*AFINTY QUEENS DISCOVER BLISS IN BEAUTY =؅?=د?*

*Address =?G?=?G?:*
*KU ZIYARCE MU A SHOP NO.9&10 SHEMA PLAZA,BEHIND SHEMA FILLING STATION KASUWAN BACCI KADUNA*
*TEL:08133379628.*

*MATAR MUTUM*
*NA MARYAM FAROUK (UMMU MAHEER*

*FIKRA WRITERS ASSOCIATION*

*LITTAFIN KUDI NE*
*PAY 500 A ASUSUN*
*7061838488*
*OPAY DIGITAL SERVICES*
*MARYAM FAROUK*
OR
*0709290797*
*ACCESS BANK*
*SE A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488*
*IDAN KATINE A DAUKI HOTONSA A TURA ZUWA LAMBAR SAMA VTU KUMA A TURA A 08142548705*

*Kuyi following dina a Arewabooks @Maryamfarouk01 inda zaku karanta wannan littafin tareda sauran littattafaina*
*NAGODE*

*PAGE 32*


Bayan daya dawo a Wakin Hadizan ya sauka ta karbi girki, ya ringa kallonta ga Aminu dake da shekara daya da watanni biyu ga ciki da ko yau ko gobe zata iya haifeshi. Tausayinta ya kamashi duk da halin da take ciki amma tana ta kaida kawowa tana hada masa abinci. A zamantakewa Hadiza bata da laifi, mace ce ta gaske dan ze iya cewa a duk matan da ya aura babu tsayayya kamarta. Ta iya kula dashi haka tsakaninta da sauran Matansa tana mu'amalantar kowacce da sigar data zo mata. Duk bala'in Binta ta sarara mata sedai tayi a bayan idonta amma ya zeyi? Shidai baze cigaba da zama da ita ba domin ko ita idan zata masa Adalci inta san itace matsalarsa yaci ta nemi rabuwa dashi da kanta kawai su ha?ura da juna ze saketa badan baya sonta ba sedai dan hakan shine maslaharsu baki daya ze kuma cigaba da daukar nauyinta har iyakar rai ze cigaba dayi mata duk abinda ya kamata tamkar tana gidansa.

Da daddare harsun kwanta ya tashi zaune, cikin nutsuwar dashi kansa besan yana da ita ba ua shiga yiwa Hadiza bayanin halin da ake ciki.
"Kuma ka yarda? Tamkar fa kayi shirka ne Audu ka tara sani da Allah. Ya za'ayi ace maka nice silar Karayar Arzi?inka kuma ka yarda shin Allah baya jarabtar mutum haka nan dole se wani abu ya zama sila?" faWa hawaye ma zubo mata.
Audu ya murtuke fuska, yasan gaskiya ta fada to amma magana ta ?are tunda har aka gaya masa kuma ya yarda dan haka yace

"Kinga muyi ha?uri kawai nidai na rigada na yanke hukunci na sakeki saki biyu, kina da zaSi na kici gaba da zama a gidan nan ba se lallai mutane sun san na sake ki bama".

Kallon kayi hauka tayi masa kafin ta mi?e tana kuka ta shiga haWa kaya, se yayi fakare kuma yana kallonta duk yaji babu dadi, da ace da wata hanyar da ze magance matsalar sa ba lallai seta rabuqa da Hadiza ba daya bi amma babu yanda ya iya. Washe gari ta bar gidan, Binta ta ringa rawa tana shewa, satin Hadiza Waya da tafiya ta haifi Aliyu, tayi maza biyu kenan sunyi kankan kan da Binta wadda keda cikin da na biyar Aisha nada na biyu a sannan. Tun Binta na saka ran Aisha zata bi bayan Hadiza har suka haihu wannan karon ma kusan tare tsiran kwana goma tsakaninsu Binta ta fara haihuwa ta samu Yakubu takwaran Al?ali, seda Babanta ya shiga maganar kafin ta ha?ura da wannan takwara da aka mata da babban ma?iyinta Aisha kuma Abdullahi suna kiransa Sarki Al'amuran Audu kuma suka fara daidaita sannu a hankali Arzi?i yaci gaba da bun?asa harya fi nada.

Aisha da Binta sukaci gaba da jera haihuwa, bayan su Yakubu Binta ta haifi Aisha wadda Audu yayiwa ?anwarsa takwara ta rasu wata daya kafin haihuqar Bintan itama yarinyar watanta hudu ta koma

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login