Showing 399001 words to 402000 words out of 467220 words

Chapter 134 - MATAR MUTUM COMPLETED 1-3 BY MARYAM FARUK.doc

23 Sep 2025

12150

sukayi sanyi karsu kayar da ita a gurin. Ganin yanda tayi ladab yasa ya tattaro duk wata jarumtar sa da mazantaka ya aza ya gyara zama yana tamke fuska yace mata

"Kin barni a zaune bayan kin san bana son jira, sannan kin shigo haka nan babu sallama balle ki gaisar dani sannan ki zauna ni kike jira na farayi miki magana ko me?"
Ta zaburo ta kalleshi sedai ganin idanunsa na kanta har sannan yasa ta kasa bashi amsar data so seta Sige da murguWa masa baki ta kalli gefe. Yanda tayin ba ?aramin shagaltar dashi yayi ba ya ringa kallonta. Allah shine shaida yana son Afeeyah, kallo Waya yayi mata ta shiga ransa ya kuma rasa ta yanda zeyi ya cireta. Ya ringa kallonta yana sakin murmushin da be san ma yana yi ba, seda tayi ?aramin tsaki kafin ya hankalta take kuwa ya haWe rai fin na farko yana zare ido yace
"Yauma kin sake yimun tsaki, wlh Afeeyah ki kiyayi ranar da zaki shiga hannuna sena sauke miko duk wani abu da kike fama dashi akanki" yaja ?wafa. Yanda ya birkice lokaci Wayan ya koma Asalin Jay data sani yasa ta daidaita zamanta tana kallon ?asa cikin taka tsantsan tace
"To me zanyi maka? Akan me zaka zo inda nake bayan ni ban bu?aci hakan ba? Nifa bana son mutumen da basa gaba na sun ringa shishshige mun haka kawai".

"Keee" Jay da idanunsa suka canza taje ya faWa yana kallonta, fuskar sa bata Soye Sacin ran daya ziyar ceshi nan take ba, wato baya gabanta kuma shine shishshigi take nufi?
Ya sassauta murya kaWan dan karta Wauka maganarta ta dameshi harta Sata masa rai yace
"Kina zaton jin daWi ne ko son raina ya kawo ni gurinki?" Ya faWa yana zura mata ido kamar me jiran ta bashi amsa, seya girgiza kai yana wani murmushi irin na rainin wayo yace
"Karki yaudari kanki bake bace a gaba na yanzu Aafeeyah i have already moved on with my life. Abinda yasa nazo gurinki yanzun na san kin rigada kin san abinda yake faruwa. Ba'a nemi yardata ko amincewa ba Alhaji ne ya zartar da hukunci a matsayina kuma me son yayi koyi da kyawawan daSi'un Yah Ahmad dan haka bazan iya musa masa ba. Na karSi umarninsa sedai akwai wani hanzari ja gudu ba" ya dakata ganin kamar bata jin me yake cewa. Yanda take kallonsa babu ko ?iftawa zakace ta suma ne a zaunen da take.

Ya kaWa yatsunsa biyu a fuskarta tayi firgigit kamar wadda ta farka daga bacci, ko a jikinsa ya ci gaba da cewa
"Nazo ne na tunasar dake idan kin manta Hajiya bata son ala?ata dake, ni kaina kamar yanda nace miki babu amincewata, yanzu haka maganar da akeyi abun yayi tsamari har Alhaji ya gindaya mata sharaWin saki muddin bata sahale mun na aureki ba, yanzu zaki so ace auran mahaifiyata ya mutu saboda ke?" Ya ?arasa maganar cikin sauti kaWan, ta girgiza masa kai alamar Aa ba tareda tasan tayi hakan bama. A hankali ya tashi daga kujerar da yake ya koma kan two sitter inda take, be matseta sosai ba ya kama hannayenta biyu cikin nasa yana murzawa a hankali yace
"Nasan zaki fahimce ni Aafeeyah. Hajiya bata da sau?in sha'ani haka Alhaji me magana Waya ne. Duk su biyun babu wanda zan iya bijirewa na bi zaSin Waya dan haka nake neman alfarma a gurinki. Nasan kina sona shiyasa ma har kika yarda da tayin Alhaji ko kuma ke kece kika takurawa Baffa yayi magana ban sani ba, amma dai koma yaya akayi ba wannan ne a gabana yanzun ba. So nakeyi ki gayawa Baffa kin fasa bakya ra'ayina yanzu"
"Nasan Baffa yana girmama ra'ayinki baze miki dole ba ze kuma sanarwa da Alhaji ya fasa bani auranki dama kuma haka yace muddin ba Baffanki ne ya canza magana ba babu abinda ze saka ya janye tasa. Kinga idan kika ce bakya so shikenan ba ze ga laifina ko ya zargi na bi maganar mahaifiyata na?i jin tasa ba komi ze gyaru maganar zata wuce kuma auran mahaifiyata ze kuSuta sannan Alhaji bezeyi fushi dani ba".

Kallonsa kawai ta ringayi kamar wata shashatau har ya gama magan se kuma hawaye suka Salle mata. Ya ?ara ?arfin ri?on da yawa hannunta cikin sigar rarrashi yake cewa
"Kuka kuma Aafeeyah? Me yasa zakiyi kuka? Nasan kina sona amma ki duba al'amarin ki saka kanki cikin yanayin da nake zaki fahimci bani da zaSi, ceton rayuwata zakiyi ko zaki so ki zauna dani babu albarkar iyaye a tareda mu?"

BuWe baki kawai tayi ta fara kuka me sauti dan ya fiye mata sau?i. Saboda dai ita tafi kowa lalacewa a duniya shine za'a tallata ta gurin Alhajinsu har ya tilasta masa ya aureta wannan wane irin cin mutunchi ne? Ai ko tana masa soyayya irin ta da sedai ta mutu sanadin haka badai mahaifinta ya kai tallarta ba sannan saboda dama shi gadon rashin mutunchi yayi harya dubi idonta ya ringa gaya mata baya sonta, abin ya mata ciwo matu?a da gaske.
Jafar kuwa daurewa kawai yake amma kukan da takeyi ya taSa shi ji yake kamar ya rungume ta ya lallashe ta sedai bazeyi hakan ba, ba yanzu ba lokacin da ze mata lallashi na gaske yana tafe yanzun dai fatansa kawai bu?atarsa ta biya. Yasan ta hanyar tunzurata har Baffa ya magantu da kansa ya janye baikon shine abinda ze saka Alhaji ya ha?ura da nasa ?udirin idan yaso daga baya duk ze gyara kwaSar sa ya lallaSa ta tunda dai tasu ?addarar kenan.

Ya zaro hankici daga aljihunsa yayi amfani dashi gurin Wauke mata hawayen dake zuba kamar zeyi kukan shima yana ce mata
"Dan Allah kiyi shiru haka kice wani abu akan bu?ata ta"
Cikin kukan tace
"Wlh ban yafe ba tunda har kayi mun ?azafin Baffana yayi tallata. Ni me zanyi dakai? An gaya maka ko acan bayan da na yarda dakai a rashin sani ne dan a duniyata ka sani bani da abinda na tsana tamkar wanda ya raina mun iyaye wannan kuma tambarinku ne kaida Hajiyarka"

"Karki kuskura kije nan, nidai dana karya bille nake ro?on alfarma a gurinki ki zageni amma billah karki ce zaki raina mahaifiyata" ya tareta cikin hasala, hakan be saka ta naba'a ba kamar ma ya ?ara mata ?aimi ne tace
"Idan ?arya nayi seka faWa, tun ban sanka ba baka sanni ba kake zagina kana zagin iyayena. Mahaifiyarka har cikin gidanmu ta taka ta ci mutunchin mahaifana har tana i?irarin zata daki Ummata bayan duk irin tozarcin da takeyi mun alhalin babu abinda na haWa da ita a haka har ?wa?walwar ka zata baka tunanin ni Afeeyah zan so ka har nayi ?ulafucin auranka?" Ta girgiza kai tana share hawaye bayan data ?wace hannunta daga nasa taci gaba da cewa
"Karma ka yaudarar kanka. Tabbas na soka a baya a matsayin Jay amma a yanzu bazan taSa sonka a matsayin Jafar ?anin Ahmad ba. Kamar yanda kace ?arfa ?arfa aka maka bada yardarka ba sammakal dan nima babu yardata ka kuma saka ranka a inuwa dan ko baka ce haka ba bazan aureka ba" tana gama faWar haka ta wuce ciki da sauri tana kuka wiwiwi kamar wadda aka doka.

Jafar ya sandare a inda yake zaune, da hannu biyu ya dafe kansa yana nanata innalillahi wa'inna ilahi raji'un a fili shikenan a garin neman gira ze rasa ido. Daga Wan zungurarta tayi ?aramin fushi shikenan seta kambama abu ta ringa yaga masa maganganu son ranta. Yaji kamar ya bita yace wasa yake mata, to amma koya faWi haka ma ba zata yarda ba ya rigada ya hasalata. Ransa ya ringa Saci akan cewar da tayi bata sonsa ya manta shiya fara gaya mata haka, kusan minti goma yana zaune kafin ya tashi duk ransa a jagule, Hibban ya shigo da ?aton try sha?e da kayan ciye ciye ya kalleshi ganin yana shirin fita ya ajiye akan centre table yana cewa
"Momy tace a kawo maka"
"Kace mata nagode sedai wani lokacin" ya fice Hibban Win ya bishi yana cewa
"Uncle abokanaina su uku ne kawai, suna falon Momy dan Allah na kirasu?"
"But i told you I'm not in a good mood, ka barni dan Allah" ya faWa sounding pissed off se kuma dayaga Hibban ya tsay yana kallonsa ya sassauta murya yace
"Sorry, ina Antynka?"
"Ta wuce Waki tana kuka" ya bashi amsa. Ya cije baki yace
"Shikenan, idan na dawo i promise zanga friends Win naka, deal" Hibban yayi murmushi ya rakashi jikin motarsa seda ya fice daga gidan kafin ya koma ciki ya gaya wa Mamansa Jay ya tafi.

A Wakin ta ya tarar dasu Afeeyah na rusa kuka ita kuma tayi tagumi tana kallonta ya gaya mata Jay ya tafi da hannu tayi masa alamar yaje yaja musu ?ofar ya wuce yana mamakin wai ita Anty Afeeyah bata gajiya da kuka se kace wata Amal.
A Wakin bayan ya rufe ?ofar Anty Sauda data gaji da sauraron ta gama kukan ta gaya mata abinda ya faru tayi tsaki ta mi?e tana cewa
"Se kiyi ai, idan kina da rabo kuma Allah ya shiryaki" tayi ficewarta ta barta. Afeeyah kuwa seda tayi dagaske kafin ta iya tsayar da kukanta amma da ta tuna yanda yace wai baya sonta ta dena ?ulafucin sa se sabon kuka ya ?wace mata. Ta tabbata dagaske yaudararta yayi a baya domin idan da har son gaskiya ya mata ai baze mata wannan cin fuskar ba. Ta ringa raya abubuwa a ranta, da ace zata iya daure zama inuwa Waya dashi da seta aureshi ko dan ta nuna masa iyakarsa amma ba zata iya ba. Ta tsane shi tun bata sanshi ba ya zatayi rayuwar aure da wanda bega mutunchin iyayenta ba a bayan idonsu se yanzun saboda munafunci?

Ta ringa tunanin ta yanda zata tunkari Baffa da zancen, be zama lallai ya fahimce ta ba balle Umma da duk motsinta zata ce gulma ce ta canza mata fahimta tasan ko ita zata iya tsayawa ta hana Baffan yarda da abinda zata gaya masa dan gani take ma Umma so take ta auren Jafar ya zame mata kamar hukuncin zunubanta na baya shi yasa take murna da abin. Har dare ta kasa cewa Anty Sauda komi akan zuwan nasa itama kuma bata sake bi ta kanta ba. Bacci ma gagararta yayi dan tsakani da Allah kalamansa sun ba?anta mata ba kaWan ba duk juyin da zatayi seta tuno yanda yace baya sonta da tayi ?o?arin fahimtar da kanta meye a ciki idan yace baya son nata ?in gamsuwa tayi da maganar. Ta hakaito abinda ta gani cikin idonsa be canza daga wanda take gani a shekarun baya ba illah ?aruwa da ya sakeyi, a hakan kuma yace bata gabansa kawai seta samu kanta da ?aryata shi ta kafa hujja da maganar Alhajinsa da yace ze saki Hajiya muddin bata yarje masa ya aureta bace kawai tasa shi faWar duk abinda ya gaya mata saboda ya tserar da auran mahaifiyarsa ya kuma gujewa fushin ta akan amincewar da zeyi.
Haka nan kuma se zuciyarta tayi masa uzuri kamar yanda yace ta saka kanta a halin da yake ciki ta tabbata ko itace bata da zaSi illah barin koma menene tunda hakan shine maslaha cikin al'amurin, yanzu ace auran Hajiya ya mutu a silarta ta tabbata har gadon baccinta tsinuwa da jafa'in Hajiyar zasu ringa tarar da ita, ita bama zata so haka ba wannan ya bata ?arfin guiwar tunkarar Baffa tasan kuma baze gagara yiwa Jafar uzuri ba.

Washe gari daga gidan Anty Sauda ta shirya ta shiga makaranta dan tana da test a ranar kuma take so taje Kaduna kamar yanda sukayi al?awari da Badar. Sha Waya ta gama abinda takeyi ta wuce gida, bata ji daWin ganin Motar Anty Sauda ba tasan harta je ta ?ulla abinda bata sani ba yanda Umma ta amsa mata gaisuwa ya tabbatar mata Anty Saudan ta shiga tsakani. Ta wuce ta hau haWa yan kayan da zata bu?ata dan ta rigada tun jiya kafin ta fita ta gayawa Umma zata Kadunan. Seda ta gama shiryawa tsaf ta fito jin muryar Baffa a tsakar gida dan sanda ta dawo baya nan da tayi niyyar bari se ranar lahadi idan ta dawo sannan ta masa magana se kuka taga lokaci ze ?ara ja, gara ayita ta ?are kowa yasan matsayinsa kawai. Su Sauda suka bita da kallo ganin ta fita, a Waki ta samu Baffa da alamu masallaci ze tafi dan da wuri yake tafiya dukda se ?arfe biyu ake sallah a babban masallacin.

Baffa ya ringa kallonta kawai tana magana tana kuka harta gama sannan yayi ajiyar zuciya yace
"Shikenan, zan kira Al?ali na gaya masaz duk yanda ake ciki zakiji"
"Nidai Baffa kawai gaya musu zakayi ka fasa karma ku tsaya jan magana balle aga laifinsa" bakin ta ya suSuce se da Baffan yace
"Au bakyaso aga laifinsa kenan ni kike so nayi dakon zunubin?" Se tayi saurin girgiza kai tana cewa
"Aa Baffa ba haka nake nufi ba. Idan Alhajin yasan yazo munyi wannan maganar ze iya cewa Hajiya ce ta masa dole kaga karya zartar da hukuncin daya ambata".
"Afeeyah kenan me abin mamaki, bakya son mutum amma kina gujin Sacin rai ya same shi, ai shikenan zan kira Al?alin ai shi me fahimta ne babu damuwa in Allah ya yarda" ta baro shi yana cigaba da shirinsa. Umma na tsakar gidan kallon da tayi mata yasa ta fahimci taji duk abinda suka tattauna da Baffan. Tayi sum sum ta shige Waki bata ko zauna da Anty Sauda ba ta Wakko mayafinta da jaka ta fito Ahmad ya saka kuka ze bita daidai nan su Layla suka shigo daga makaranta.

"Dady ne ya Wakko mu" Amal ta faWa cikin murna, tayi kamar bata ji su ba ko tambayarta ina zataje da sukeyi ta?i amsawa dan wani sabon haushinsa daya taso mata. Ya gama cewa baya sonta kuma ya ringa bibiyar rayuwar yayanta.
"Ba zaki jira a sakko daga juma'a ba?" Umma ta tambayeta sanda tace mata zata tafi tace Aa bata so tayi yamma Anty Sauda ta fito da Ahmad dake kuka har sannan ya?i shiru tace
"To ki tafi dashi mana"
"Haba dai" ta faWa kamar wata wadda aka ce tayi saSo, Umma ta harareta tace
"Guri ta samu ki rabu da ita. Idan baki auri ?anin ubansu ba seki nemo wanda ze ri?e ki tareda Wanki dan na gaji nayi rainon nawa yayan tuntuni bazan iya na wasu ba". Abin ma se ya bata dariya wai wasu, yau kuma ita ce wasu a gurin Umma. Ikon Allah.

Ta saSa Ahmad Win a kafaWa ta juya cikin Waki akan zata haWo masa kaya dan akan dai ta fasa tafiyar gara su tafi tare. Tana ciki ta jiyo muryar Baffa yana tambayar ina Ahmad. Nayla ta kinkimeshi ta kai masa shi seda ta canza jaka da zata ci kayan ba tareda ta raba ba sannan ta fito ko sallama batawa Anty Sauda ba ta fice. Tayi turus ganin Jay a ?ofar gidan ya dora Amal da Ahmad akan bayan mota Nayla da Layla kuma suna tsaye gefensa suna surutu. Baffa dake tsaye da wani ma?ocinsu yace mata
"kin fito? Ki hanzarta dai kar ko rasa mota, tafiyar yamma babu daWi".
Tayi kinini da fuska ganin Jafar na wani kallonta kamar ya samu Tv, tana ji yana tambayar Baffa
"Fita zasuyi ne?"
"Kaduna zata je can gurin yar uwarta Badriyyah. Ka santa da shiririta maimakon ta tafi tun safe shine se yanzu" Baffa ya bashi amsa. Tayi sakare jin ?aryar da yake shirgowa yace wai

"Ai nima Kadunan zanje yau, da se bayan la'asar ma zan tafi se kuma wanda zanje gurinsa ya kirani akan nazo da wuri". Ma?ofcin nasu yace
"Ai shikenan se ku haWa hanya bibbiyun ai ta fi daWi". Tamkar zata rusa kuka, Baffa daya tabbatar ?arya Jay yakeyi bashida shirin zuwa wata Kaduna dalilin Afeeyar zeje yace
"Ai ko se ku hanzarta indai tafiyar zakuyi". Amal ta dira tsalle tace
"Dady zanje, kafin yace wani abu Baffa yace
"Aa akwai hadda gobe ko kina so a zaneki idan kikayi fashi?"
"Dama duk sati se an doketa bata kai hadda Baffa idan muna tilawa seta kwanta tace bacci takeji" Layla ta faWa. Jay yaja kunnenta yana zare mata ido yace
"Bakya karatu ko?"
"Wlh inayi Dady haddar ake bani irin tasu kuma nacewa Malam yayi mun yawa amma ya?i ya rage" jin abinda ta faWa yasa ya sakar mata kunnen yana kallon Afeeyah dake tsaye fuska kamar hadari yace
"Zaki rakani na samu malamin nasu, ai ba shekarunta Waya dasu ba balle ace ?wa?walwar ta zata Wauki abinda suke Wauka". Ita dai bata ce komai ba, Baffa ya sake mayar da Ahmad ciki bayan daya sallami mutumin da suke magana tana ji tana gani haka ta shiga motar yaja suka tafi babu damar musu tunda Baffa ya kasa ya tsare.
Suna fita daga unguwar cikin tsiwa tace
"Sauke ni Malam" ya mata banza, ta ringa masa tijara kala kala amma be kula ba fuskar sa na kan titi ya ringa tsula gudu abin harya bata tsoro. Seda suka gota kwanar Wangora kawai taga ya gangara gefen titi ya tsaya, fuska a haWe ya kalleta yace "sauka". Ta kalli inda suke, ba jeji bane kuma rana ce amma tsoron gurin ya kamata dan a ta nan haka aka ce ana kidnapping.

Ganin ta?i sauka yasa ya daka mata tsawa yace ta fice masa daga mota, idonta ya kawo ?walla ta fitan ya fito shima ya fitar mata da jakarta ya ajiye kafin yaja motar yayi gaba se kuma ya tsaya gurin wani mutum da bata lura dashi ba se sannan yana siyar da kaji da zabi a gefen titi. Bata san me yacewa mutumin ba kafin yaja motar ya koma baya. Tsoro ya kamata ganin me kajin ya dawo dab da inda take seta ja akwatin tayi gaba ta ringa tsayar da motoci amma abu kamar tsafi duk wadda zata taho a cike, ita da in dai ta fita se masu mota sun tsaya suna so su bata lift se gashi yau da kanta take tsayar da motoci amma babu wanda ya saurareta yanda kuma me kajin nan yake ta kallon ta gashi se taga yana waya lokaci lokaci ba ?aramin tsoratata yayi ba, Allah yasa ba informer bane

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login