Showing 342001 words to 345000 words out of 467220 words

Chapter 115 - MATAR MUTUM COMPLETED 1-3 BY MARYAM FARUK.doc

23 Sep 2025

12384

falon yayi shiru banda sababin Binta bakajin komai tana ta kashewa Hussani da uwarsa Albarka kafin Alhajin ya zaburo yana cewa
"Wallahi tallahi Binta idan baki bar falon nan ba se kinyi nadamar abinda zan aikata miki tunda ke baki da hankali dabbace baki kuma san mutunchin kanki ba balle kisan na yayan da suke gabanki"

Tsit tayi na Wan lokaci kafin cikin maWaukakin mamaki tana nuna kanta tace
"Ni kake cewa Dabba Audu?" Hannayenta Jafar da duk abinda akeyi tamkar baya nan ya kama ya ce
"Muje Hajiya" ta fizge tana sake nanata
"Ni Audu ni kake kira Dabba a gaban yayanka da barorinka?" Cikin muryar da tafi ta farko kaushi yace
"Na faWa, a cikin Dabbobin ma ke tinkiya ce Binta baki san abinda yake miki ciwo ba, ina sake jaddada miki da ki fita daga gurin nan kafin ki tunzurani zuciya tasa na aikata miki abinda ba zakiji daWi ba".

Kuka ta fashe dashi Jafar da Yakubu suka sakata a tsakiya suna so su fitar da ita amma fafur ta tirje kamar wata yarinya ta?i fita, ta dai yi shiru dan hannayenta ta saka ta toshe bakinta dan ta hana sautin kukan fita dakyau. Shidai Jafar ya saketa ya fice abinsa daga falon zuciyarsa kamar zata kama da wuta saboda ba?in ciki.

Cikin fushi Alhajin ya kwashi takardun dake ajiye gefensa ya watsasu tsakiyar falon yana cewa

"Da yawanku kun saka idanu kuna jira kuji me zance akan maganar ginin super market Win Ahmad. Tabbas fili nawa ne kuma da kuWi na na gina masa shi akan ze ringa biyana a hankali har zuwa y???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?a mallakeshi ya zama nasa baki Waya bayan wannan babu ko tsinke da yake a ciki mallakina idan banda kayan da suke siya a hannunmu bani da hurumi da komai da yake ciki. Sannan maganar fili, kafin a iza harsashin ginin seda ya biyani kaso hamsin cikin Wari na kuWin ?asar ya kuma cikamun a ?asa da shekara Waya bayan buWewa. KuWin gini kuma ya cigaba da biyana kaso goma a duk shekara, shekaru takwas kenan kuma naira miliyan Wari biyu ce tayi saura abinda ze cika mun.

A ranar da zeyi tafiyar da be dawo gare mu a raye ba a nan gurin kafin su tafi ya kirawo lauyan sa da manajansa na banki yazo da adadin kuWin dayayi saura bashi tsakaninmu. A gaban Al?ali, Aminu yana nan ga Hassan da lauyan sa da kuma manajansa, dukkaninsu sun saka hannu a takardar yarjejeniya na kuma dam?awa lauyansa takaddun gurin dan tuntuni na daWe da sakawa an canza sunan mallaka zuwa nasa. A ta?aice abinda nake so na tabbatarwa masu shirin tayar da tarzoma shine wannan kantin da duk abinda yake a cikinsa mallakin Ahmad ne ba nawa ba.

Abu na biyu kuma shine, tun a lokacin dana bashi fili dan yayi gini har zuciyata kyauta na bashi bawai siyar masa nayi ba. Abinda yasa na karSi kuWin nayi ne saboda hakan zesa ya sake mayar da hankali sosai ya gina kansa, naci gaba da juya masa kuWin, amma a yanzu na canza shawara, a maimakon shi da nayi niyar yiwa kyautar na mayar da ita ga yayansa. Da akwai gidajen sabon estate Win da zamu buWe a watan gobe a Abuja, kunsan nawa akayiwa kowanne gida ?iyasi, na ware musu gidaje guda goma, yaya matan kowacce zata tashi da guda biyu shi kuma Ahmad ze Wauki guda huWu. Abu ma ?arshe shine ni Audu na yafe kaso na gadon Ahmad a matsayina na mahaifinsa na barwa yayansa.

Idan Allah ya kaimu da yamma za'ayi musu rabon, ina fatan ubangiji ya sanya musu albarka a cikin abun tamkar yanda ya albarkaci neman mahaifinsu" yayi shiru yana mayar da numfashi kafin yaci gaba da cewa

"Allah ya ji?an Ahmad ya jaddada rahma a gareshi, Allah ya dubi bayansa ya cika masa burinsa ma ganin kan zuri'arsa ta haWu guri guda. Daga abinda na gani a yanzu na sake yarda da nayi rashin Wa me biyayya.

Shi kaWai ne yake yimun uzuri koda akan kuskure na ne. Be taSa Waga mun murya ba, haka ko a fuskarsa be taSa bayyanar da Sacin ransa ko rashin jin daWi akan duk wani hukunci da na yanke ba koda ransa be so ba zeyi. A kasancewarsa ?arami a cikinku ya nusar dani abubuwan da dayawa hankali na be kai kansu ba sannan ya buWe mun idanu akan kurakuraina na baya da har zuciyata na shirya na gyarasu da taimakon sa sedai ubangiji be lamunce mun hakan ba ya Wauke shi a lokacin da nake da tsananin bu?atar sa.

Ina so nayi amfani da wannan damar na furta abinda naso ace na furtashi da ran Ahmad. Ni Audu ina neman yafiya da afuwar kowanne daga cikinku akan duk wani abu da nayi muku tun daga yarinta har zuwa girmanku, ku samu sararin da zaku yafe mun a cikin zukatanku. Babu mace dana aura da bana sonta haka dukkaninku yayana ina sonku kwatankwacin abu Waya. Kuyi mun uzuri akan ajizanci na da zuciya data taka rawa gurin sakani zartar da hukunce hukuncen da ni da kaina ina nadamar da yawa daga cikinsu.

A baya hankalina yana kwanciya idanna tuna ko bayan raina na haifi Wa irin Ahmad, a yanzu da babu shi kullum ina kwanciya da fargabar kar ya zama ban tashi ba na mutu na bar zuri'ata a wannan ?adamin da muke kai. Banida matsala da Yayana mata domin kansu a haWe yake, sun ajiye banbancin uwaye da duk wani abu da suke gani sun rungumi junansu ina ma ze yuwu kuma kuyi koyi dasu ku zamto abu guda ku amsa sunanku na kasancewa jini Waya?" Muryarsa ta sar?e tamkar ze fashe da kuka, seya mi?e yana haWa hanya ya haye samansa ba tareda ya kalli kowa a cikinsu ba.

Tamkar mutuwa ta gifta haka falon ya Wauki shiru lokaci me tsayi kafin ihun da Hajiya Binta ta fasa tamkar wadda ta hau bori ya fargar dasu cewar har sannan tana falon. Hannu biyu ta Wora akai tana zunduma ihu da kiran ta shiga uku ta lalace takamaimai ma babu me iya cewa ga dalilin ihun nata se kace wadda zata haukace. Alhaji Abdullahi ya cewa Zakariyya
"Idan ta kama ku Wauke ku fitar mana da ita daga nan da wanne zamu ji saboda Allah?" Zakariyya da Naziru suka jata jiki ba laka suka fitar da ita daga falon maganganu take babu kan gado yanda jikkunan su yayi sanyi ma babu wanda yabi ta kan abinda take cewa.

A sanyaye Baba Al?ali ya kalli sauran yace
"A shekaruna tamanin a duniya ban taSa ganin Audu ya bawa wani mutum ha?uri ba komai kuwa girman laifin daya aikata masa, ku bashi dama bance lallai se kun mu'amance shi ba amma alfarmar da kaWai ya nema kuyi masa. Ku goge cewar baya son wasu ko ya fi son wasu a cikinku. Ku yarda ku duka yayan sa ne abubuwa da yawa sun faru tun kafin a haifi kowanne daga cikinku. Ba komai kake iya al?alanci akansa ba musamman idan ba akan idonka ya faru ba. Gaba Wayan ku kuna manta cewar biyayya ga iyaye wajibi ce bawai zaSi ba,

Sannan baku da wani uzurin da zaku kare kanku a gurin Allah wanda zaku jingina dashi har ya zame muku hujjar ?in kyautatawa mahaifinku ko iyakar abinda ubangiji yayi muku ya rayaku ya baku lafiya da rufin asirin da baku rasa komai ba dukda kuna ganin cewar an tauyeku hakan ya isa yasa ku tabbatar da koda soyayya ko babu soyayya babu abinda ze hana al'amarin da ubangiji yayi nufin afkuwar sa kasantuwa.

Ku ya?i zuciyoyinku, ku jajirce gurin manta baya ku kalli gobenku. Shekara Waya baya duk muna rayuwa cikin farin ciki, yau kwanaki hamsin kenan da muka rasa mutumin da kowa nan a cikin mu yana cike da alhinin rashin sa domin shi kaWai ne ya yarda da dukkanmu abu guda ne be kuma bambamta ba. Yanzu Ahmad muka rasa bamu san cikinmu waye ze bi bayansa ba, idan har baku zubar da komai kun rungumi junanku ba ta yaya zaku cika wasiyyar daya bar muku ta kulawa da Ahalinsa? A nan gurin ya ro?eku da ku dabaibayesu da soyayyar Ahali ta yanda sedai suyi maraicin mahaifi badai kukan rashin uba. Zarewada kukeyi da daddaya kuna dubasu ba shine abinda yake fata ba, na tabbata abinda yake so ku zauna tare kamar haka su faWa cinyar wannan su tashi a ta wannan su haWu da sauran yayayenku suyi wasa bawai mutum Waya ya zagaya ya gansu ba gobe wannan yaje.

Yanzu ku dubi yaron nan Jafar babu wanda ya damu dashi a cikinku, dama can a ware yake rayuwar sa da Wan uwansa kaWai yake dariya, yayi kuka yanzu daya rasa shi na tabbatar a cikinku babu wanda ya taSa zama dashi ya tambayeshi halin da yake ciki har ya samu ya rage alhinin dake cike da zuciyarsa bayan kunsan irin sha?uwar da take tsakaninsu ba abu ne me sau?i ya iya dangana nan kusa ba dole yana bu?atar wanda ze ja shi a jiki amma kun banzatar dashi ga bala'in uwar da Allah ya jarabce shi da ita hatta da amanar da aka bar masa tana neman tayi masa katanga da ita. Ku dubi Allah ku sadar da zumunchi duk wata ni'ima da ubangiji zeyiwa mutum yayi mana ita ku taimaka ku haWa kanku kuyi alfahari da yawan da Allah yayi muku ba ya zama abinda ze janyo rarrabuwar kawuna a tsakaninku ba".

*MATAR MUTUM*
*NA MARYAM FAROUK (UMMU MAHEER*

*FIKRA WRITERS ASSOCIATION*

*LITTAFIN KUDI NE*
*PAY 500 A ASUSUN*
*7061838488*
*OPAY DIGITAL SERVICES*
*MARYAM FAROUK*
OR
*0709290797*
*ACCESS BANK*
*SE A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488*
*IDAN KATINE A DAUKI HOTONSA A TURA ZUWA LAMBAR SAMA VTU KUMA A TURA A 08142548705*

*Kuyi following dina a Arewabooks @Maryamfarouk01 inda zaku karanta wannan littafin tareda sauran littattafaina*
*NAGODE*

*BOOK 3*
*PAGE 27*

"Wai dan Allah Hajiya menene kikeyi haka? Ji yanda kike iface iface kamar wata wadda iskokai suka bige, ni wlh idan ba zakiyi shiru ba musan abinyi tafiyata zanyi haba da wanne mutum zeji?" Naziru ya faWa cikin fusata. Tunda suka samu da?yar suka shigar da Hajiyar falonta take zunduma ihu tana tumami a ?asa. Cikin kuka fuska yare yare da majina tace

"Ai dole nayi kuka, Naziru bakaji abinda ubanku yake faWa a Wakin can ba? Ni Binta ina gidan nan Audu ya zartar da wannan hukuncin ba tareda na sani ba lallai Aisha ta gama dani. Ta cuceni ta illatani ina kwance na sakankance kuma billahillazi bazan yarda ba. Ko zanyi yawo tsirara sena ?watowa kaina yanci a cikin gidan nan, bata isa ba wlh kai ?arya ce ma, ba zata saSu ba" ta mi?e fuuu seta koma rigijib ta zube a ?asa saboda yanda ta tashin da alamu ta manta ?arafun nata yanzu se da dabara, aiko taji zafin faduwar da tayi sosai dan har bayan ta seda ya amsa seta sake fashewa da kuka.

Naziru ya ja tsaki yana haWe hannaye yace
"Ni babu abinda yafi Sata mun rai irin yanda a gaban yan uba Alhaji yake muzantani, sannan har wancan yaron ya samu bakin gaya mun magana wlh duk laifinki ne Hajiya. Yanzu ina kallo ace super market Win dana gama saka rai dashi har na gama ciniki da wasu yan china da zan siyarwa gurin har ba kafin al?alami na karSa se kawai yanzu azo ace wai Ahmad ya gama biyan kuWi ya mallake shi? A ina akayi haka? Kai daga jin wannan abun ma kasan shiri ne" se Zakariyya ya maka masa harara yace

"Wato ka gama shiryawa zaka kwanta kan komai ka handame kai kaWai shine harda yin ciniki da wasu zaka siyar musu". Faisal da shigarsa gurin kenan ya zauna fuska tamkar hadari yana cewa

"Yanzu gida guda Waya nace a bani aka hanani, zan siya da kuWi na ma akace ba za'a siyar mun da guda Waya ba shine za'ace an bawa yayan Ahmad har guda goma kun san kowanne gida nawa akayi masa kuWi kuwa?"

"Ai ko sama da ?asa zata haWe wannan kyauta bata yuwu ba se kace ma ana hauka? Ai wlh zasu gani, badai anjima ze gayyato su suzo ayi rabon gado ba? Zan nuna masa dabbanci na gaske a gurin kuma tsinke mutum yaci a kayan da aka satar mana ya ciwa kansa masifa dan se na saka duk anyi musu ?ulla ciki, bam wayata kaga na kira Fatiyyah yanzu ba se an jima ba tazo ta rakani gurin malaminta ayi wacce za'ayi kawai bazan zauna ina kallo ba?in ciki ya kasheni a gidan nan ba" Hajiyar ta sake faWa tana kuka tana laluben wayarta. Cikin mamaki Naziru ya kalleta yace

"Hajiya Fatiyyah ba matar Jafar ba kenan?" Tana latsa wayar da aka gano mata a ?asan filo tace
"Ita, da kaga wannan ya fara dawowa saiti ai ita ta kaini gurin malaminta akayi karya asirin da akayi mana. Har hatsarin da mukayi duk ashe Aisha da Rabi ne Bilki ta rakasu can wani tsibiri suka mun asiri ai so sukayi motar tabi ta kanmu mu mutu Allah ta fisu mugun nufinsu be ci ba. Ka zata a hankalin Audu yake wannan abin? Sihiri ne me ?arfi yake Wawainiya dashi kai na tabbatar maganganun da yayi ma bashi bane, Aljani aka tura masa ya ari bakinsa ya ambata waWannan maganganun to ko bishiyar kuka Aisha ta dasa a kansa sena kakkaSesu zata gani, zan mayar mata da raddin da seta gwammace mutuwa da rayuwa".

Da sauri Naziru ya fizgi wayar Hajiyar da harta danna lambar Fatiyyah ya kashe yana cewa
"Amma dai Hajiya kin samu matsala. Duk mutanen duniya ki rasa dawa zaki haWa kai kiyi yawon malamai se da surukarki? Surukar ma wannan yar iskar yarinyar da daman haka nan ta raina mutane balle yanzu da kika sake baje mata faifan sirrin kowa ashe tsirara ma take kallon mu, Haba Hajiya gaskiya baki kyauta mana ba ni dama matsalata dake kenan baki da sirri shiyasa ba komai nawa nake gaya miki ba. Waya sani ma ko haWa baki tayi da Malamin a maimakon ayi miki maganin matsala tashi ya sake lalata komai?"

Se tayi sakare tana kallonsa kamar wawiya kafin a hankali tace
"Kuma fa haka ne, ko kuma yan damfara ba irin yanda wannan ya kaini aka cinye mun kuWi babu biyan bu?ata" se ta sake rushewa da kuka tana cewa

"Tun da Aisha tayi cikin Amadu jikina ya bani ta ?unso mana jaraba, gashi kuwa tunda dai ta haifeshi ban sake samun nutsuwa ba. Shekaru nawa ina juya duniyata hankali kwance ban taSa zuwa gurin shege na dur?usa da sunan ya taimaka mun ba se akan al'amuransa. Kuna kallo ko abu ne yasha mun kai sedai na aika Turai amma yanzu ni Binta ni ce duk inda naji Malamin zaure hankalina baya kwanciya se naje gurinsa kuma a banza kamar wadda take shuka dusa maimakon abubuwa suyi sau?i sema ?ara lalacewa sukeyi. Audun da kallonsa kawai nayi a baya hankalinsa tashi yakeyi amma yau shine a gaban shegun yayansa yake kirana da Dabba lallai lalacewa ta same ni ni Binta".

****************
Kamar yanda suka tsara ?arfe huWu Malam Sani Aminin Baffansu Fatima da kuma Yayanta Jafar suka zo gidan a matsayin wakilanta. Baba Al?ali yace Sarki da Salim su zauna su wakilci mahaifiyarsu sai lauyoyin Ahmad biyu da Baba Al?alin daya jagoranci rabon. Basu wani Sata lokaci ba dan tuni daman an rigada an fitar da komai bayan da aka tattara abinda ya bari kusan kuka duk waWanda wata sabgar kuWi take tsakaninsu sun dawo dashi dan haka basu sha wahalar rabon ba na Alhajin Audun da be sanar dashi da wuri ya yafe bane suka tsaya sake kasawa kafin su zauna kuma har sun sake fitar da ?wafin takaddun da za'a bawa kowanne Sangare dan haka babu Sata lokaci bayan sun zauna sukayi abinda ya tarasu.

Anyi rabo na gaskiya yanda Allah yace ayi. a cikin kayayyakin gidansa kayan da suke Wakin sa da falonsa kaWai akayi lissafi dasu bayan nan duk wani abu da take amfani dashi daya siya mata Baba Al?alin yace ha??in ta ne kyautace tsakaninsu dan haka baya cikin gado haka motar hawanta ba'a lissafa da ita ba, kayan sawarsa da sauran kayan amfaninsa kuma duk sadaka akayi dasu.

Gida 24 aka raba, aka cirewa mahaifiyarsa kaso huWu mahaifinsa kaso huWu se matarsa kaso uku na dukiyar, sauran kaso goma sha uku daya rage aka raba tsakanin yayansa hudu mata uku da namiji Waya wanda ya samu ninki biyu na abinda matan suka samu haka kason Alhajin Audun wanda yace ya yafe aka sake rabashi daidai a tsakanin yayan tunda kyautace ya fita daga sahun gado.

Sarki aka bawa rabon Momy itama Fatima aka dam?awa yan uwanta kasonta tareda na yaranta amma Malam Sani yace Aa, Yara nasu ne su ri?e musu dukiyarsu har sanda Allah ze rayasu su mallaki hankulansu su kai minzalin da zasu iya juyata da kansu. Baba Al?alin ya yaba da dattakon sa domin dan daman abinda Alhaji Audu yace shi dukiyar yaran a bawa Jafar tunda shi ubansu ya barwa Amana se Baba Al?alin yace Aa ayiwa yan uwan mahaifiyarsu tayi saboda gudun abinda ze iya zuwa ya dawo domin ba'a wani ja lokaci ba yayi sasanci tsakanin wasu surukai.

Miji ne ya rasu kwana arba'in da Woriya da rasuwar sa uban matar ya maka mahaifinsa a kotu wai ya?i raba gado ya sallamar masa yar sa jikokinsa. To dukda dai yana kyautata zaton Malam Hafizun bashi da irin wannan zalamar tunda dai tun bayan da aka auri yarsa sau Waya be taSa taka gidanta ko gidan Alhaji Audun ba balle ya ro?i wani abu kwatankwacin abinda mahaifin Hajiya Rabi yakeyi wa Alhajin. Haka aka tashi taro Hajiya Binta dake cikin gida idanu duk sun koWe saboda kuka jira take taji ance an zauna rabon ta fita tayi tijara ta watsa taron se ji tayi Salim ya shigo yana gayawa Momy ai har sun tafi.

Salim Win ya zauna da takarda yana yiwa Momyn bayanin yanda akayi Hajiyar ta shiga falon kamar an cillata tana huci bata Sata lokaci ba ta fizgi takardar hannunsa ta ringa zazzaga maganganu marasa daWi se wanda ta manta wani abin ma tamkar wadda kanta ya kwance babu tabbacin ita kanta tasan me take cewa har kuma ta gama Momyn bata ce mata

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login