Showing 270001 words to 273000 words out of 467220 words

Chapter 91 - MATAR MUTUM COMPLETED 1-3 BY MARYAM FARUK.doc

23 Sep 2025

12192

GARI

*Assalamu alaikum*
*Barkan mu da wannan lokaci Ina maku fatan alheri*

*Toh Nazo maku Da kayan arziki*
*Kudai kunsan mata sai da gyara*
*Macen da Bata da gyara ta zama yar kallo a gidan ta*
*A katafaren kamfanin mu na BEENAD HERBAL MEDICINE*
*Mun shahara wajen kawo maku ingattatun magunguna mata da na gyaran jiki,kayan mu guarantee ne*
*Muna da*
*Tsimi*
*Zuma*
*Mallaka*
*Farin jini*
*Niima*
*Gumba kalla kalla da dai sauran su*
*A BEENAD HERBAL muna da turarukan wuta da humrah kalla daban daban sai Wanda kika zabba*
*Ga kuma maganin slimming*
*Gyaran nono*
*Maganin hips*
*Maganin Kara kiba*
*Da dai sauran su*
*Kayan mu tested and trusted ne*
*Muna maraba da masu siyan Daya ko sari*
*Muna Nan cikin garin kaduna*
*Kuma muna tura Kaya duk inda kike da yardan Allah*

*Ni ce taku har kullum*
*AMINA GACHI*

*CEO BEENAD HERBAL MEDICINE *&INCENCE*
*Ku tuntubemu kai tsaye akan 07034404975*
*Location KADUNA muna nation wide delivery*


*MATAR MUTUM*
*NA MARYAM FAROUK (UMMU MAHEER*

*FIKRA WRITERS ASSOCIATION*

*LITTAFIN KUDI NE*
*PAY 500 A ASUSUN*
*7061838488*
*OPAY DIGITAL SERVICES*
*MARYAM FAROUK*
OR
*0709290797*
*ACCESS BANK*
*SE A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488*
*IDAN KATINE A DAUKI HOTONSA A TURA ZUWA LAMBAR SAMA VTU KUMA A TURA A 08142548705*

*Kuyi following dina a Arewabooks @Maryamfarouk01 inda zaku karanta wannan littafin tareda sauran littattafaina*
*NAGODE*

*BOOK 3*
*PAGE 4*


Daren jiya ya zamo dare mafi tsayi a rayuwar Afeeyah, Jay harma da Ahmad. Shi Ahnad farin ciki da zumuWin wayewar garin da ze samar masa da cikar burinsa ne ya hanashi runtsawa. Afeeyah da Jay kuwa Al'amarin da yake cikin zukatansu me tsananin girma ne, dukka su biyun abin a jajantawa suka zama a wannan dare, babu wanda ze fahimci halin da suke ciki se wanda ya taSa riskar irin daren a rayuwarsa.

Da suka bar gurin Cocktail party BECHI GUEST PALACE suka wuce inda Alhaji ya sauke jama'arsa, ya cika Al?awari ya haWa Gala night shida abokanansa masu burin warwasawa, basu jima a can ba dalilin Jay da yake ta ?orafin kansa yana ciwo suka wuce Bristol inda nasu sauran Jama'ar suke. A can ma sabon hidima ce ta tashi dan already Abokanan Jay da sukazo daga Uk sun shirya masa Bachelor's party dan sunce ba zasu yarda ace the great Jay is getting married amma babu wani light ba, dama be gaya musu cocktail Win Ahmad ba silalewa yayi ya barsu da suka dawo kuma dolensa dukda yanda yakeji kamar zuciyarsa da gangar jikinsa zasu kama da wuta tsabar zafin da suke masa, duk yanda ya daure daga ?arshe ganin yana neman yayi breaking down a gabansu yasa ya sulale ya koma Waki ya kulle kansa ya kwanta akan gado, damuwa cacin a zuciyarsa, can cikin vault Winsa inda ya Soye pictures Winta ya shiga, ya ringa binsu WaWWaya yana musu kallon ?arshe tareda goge su haka ya kwana be runtsa ba, ga sa'oin sun?i gudu be san tsayin lokacin daya Wauka ido biyu ba kafin bugun da akeyiwa ?ofarsa da kuma ringing Win waya suka tayar dashi sanda ya duba lokaci ?arfe tara tayi harda minti biyar, mintoci tamanin da biyar kenan suka rage a Waura auran Ahmad da Afeeyarsa kafin su wuce Mambila inda za'a Wauro nasa auren.

Ahmad ne yake kiransa yana daga kwancen ya amsa
"Jafar lafiyanka kuwa? Tun asuba ake buga ?ofanka baka buWe ba bana ma zaton kayi sallah sannan ka duba lokaci ka gani yanzu tara harta gota baka tashi ba"

"Na tashi yanzu ai, bari nayi sallah" ya bashi amsa murya a dakushe kafin ya aje wayar Ahmad yace
"Dallah buWe ka karSi kayanka idan yaso ka koma baccin". A hankali ya taka ya buWe masa ?ofar, ya galla masa harara kafin ya mi?a kayan ya juya. Jafar yayi murmushi ya koma ciki. Seda yayi wanka yayi sallah kafin ya fara shiri.

"Da azaba, ciki tsaba, kan'a saba, zafin rabuwa da masoyi. ?addara rubutu take, faruwar ta wajib yake zata bika ko ka fake bata gane kuka kake.
Dama mafarki nake, buga zuciya ta ake, so yayimun fiffike, sai kace film ake" Baitukan wa?ar da Asharab ya saka repeat kenan tunda suka fita daga masallacin Sarki inda aka Waura auran Ahmad da Fatima har suka kai Aiport tamkar karatu bai canza ba. Yanda motar tayi shiru tamkar babu bil'adama a ciki ya sake tasirantar da kalaman mawa?in a raunananniyar zuciyar Jay, se yakejin kamar dashi yake kuma da ace Ashrab yasan abinda yake faruwa dashi se yace da biyu ya kunna wa?ar.

"Excuse me, let me call my wife" ya faWawa Asharb sanda suka isa inda ya aje mota,
"Su masu wife manya, amma kai har yanzu wife to be zaka kirata Ahmad ne yayi sealing deal" Ashar ya tsokaneshi.
Kifa kansa yayi jikin dash board bayan da Asharab ya wuce, duk yanda yaso ya daure ya kasa a hankali ya saki kukan da idan beyishi ba yana tsammanin zuciyarsa zata iya bugawa, wayarsa da take ta ?ara ce ta sakashi lallaSa kansa yayi shiru, seda ya gyara fuskarsa kafin ya duba wayar, Fatiyyace, tun jiya da yamma rabon da suyi magana ya bi kiran nata

"Yanzu Jay abinda zaka mun kenan? Ba yanda ban ro?eka ba akan kazo koda event Wina guda ne amma ka?i, tsabar wula?ancibse kawai naga hotonka da wata random girl looking like the best couples wacece ma?" Fatiyyan ta haushi da masifa. Ya runtse idanunsa kafin ya buWe su murya can ?asa yace mata
"Please Fatiyyah I'm not in the mood karki ?aramun damuwa akan wadda nake ciki, we are on our way now idan nazo zamuyi magana" ?it ya kashe wayar.

Cikin private Jet din Audu Bechi dana sauran abokanansa akayi jigilar zuwa Wauro auran Jay da Fatiyyah. A hanya Ahmad ya ringa masa mitar ?in tsayawa suyi hoto da Fatima har yana cewa shima idan sunje ba zeyi hoto da Amaryarsa ba, shidai se uhm da murmushin ya?e yakeyi, ba'a Sata lokaci ba ana Waura aure bayan yan gaishe gaishe da Waukar hotuna suka juyo dan daman suna can masu kawo Amarya a shirye suke tunda an sanar musu da anzo za'a juyo da ita. Gaba Waya ?awayen Fatiyyah suka rikita social media da pictures tareda zafafan videos da sukayi musu bayan an Waura aure, dama ce da suke ta jira se yau tazo daman sun gama shiryawa Dinner da za'ayi a nan suke so su huce haushin sauran events Winsu da beje sun samu sun baza capacity ba.

Fatima na kwance kan Gadon Maman Hanan ma?ociyarsu ce a nan gidan suka zauna da ?awayenta tun safe bayan da aka Waura auranta da Ahmad ta kasa gasgata abin, ji takeyi kamar mafarki ko kuma kamar bada ita Fatiman ba wata daban ce. Tunda ya kirata ya shaida mata ta zama matarsa shikenan duk wani sauran laka sa kuzarinta suka ida zagwanyewa, koda sukaje da Abokanansa yin hotuna Badar ce take ri?e da ita tamkar ra?uma da akala har aka gama ta nemi guri ta zauna bata tashi ba seda akayi kiran sallar Azahar Anty Sauda tayi aike yafi sau nawa harda kanta taje akan su fita su shiga can cikin gida dangi ana ta cigiyar Amarya amma ta?i tashi data dameta ta fasa mata kuka dole ta rabu da ita.

Yanzun ma sune akanta ita da Anty Hauwa suna zabga mata masifar ta tashi tayi wanka ga masu Waukar Amarya can har sun iso, kanta kife kan katifar data ji?e da hawaye tun bayan da tayi katari da video Jay da Fatiyyah a Ig, yanda taga ya ri?eta a jikinsa da murmushin da yake mata da irin kallon da yake jifanta dashi yasa ta sake tabbatar da yaudararta yayi a baya zuwa kawai yayi ya ruguza farin cikinta kuma yayi nasara. Ga dai matar sa nan a yanda ta ganta ta kereta a komai, farace kyakykyawa wadda ko shafa jikinta kayi zaka tabbatar daga gidan Ac ta fito domin hutu ya gama ratsa jikinta. Duk suffofin da yake yawan nanata mata yana so da mace ta haWasu to daman idan banda wauta irin tata ta yaya Mutum kamar Jafar ze so yar loko irinta? Itama ta yaudari kanta a baya data kasa hango fifikon dake tsakaninsu, ta yuwu Ahmad ne yasa take ganin ta kai ajin kowanne Namiji harda irinsu Jafar Bechin.

Tana wanka tana kuka harta shirya balle da suka shiga cikin gida zatayi sallama da su Umma nan ta samu dama ta ware baki ta ringa kurma ihu kamar wadda aka aurawa kidnapper tun ana rarrashinta har ta basu haushi suka fara balbaleta da masifa se Yan ?aukar Amarya su Hajiya Balaraba ne suka koma rarrashin Amaryarsu a haka suka kwasheta se gidan Audu Bechi kamar zata shiWe saboda kuka.

Tarba me kyau da mutuntawa yan uwanta suka samu daga yan uwan Momy da kuma Yan Bechi dan duk a nan suka tare suka bar Binta da Halinta kamar yanda sukace. Tana can tana kai kawon shirya abubuwan tarbar Amaryar Jafar harta su Turai yau zuba mata ido sukayi saboda Wigimin nata yayi yawa ta?i bari su suyi abinda ya kamata ta shige kinini da ita ake komai abun ba tsari shiyasa suka zame hannu suka barta tunda ta raina iyawarsu duk maganar da yan uwanta suka mata kuma ta?i taji ta shiga hankalinta suma se idon suka zuba mata. Ta cancare abinta tasha kwalliya da wata Madam getzner da Hajiya ?arama ta Winka mata tayi kyau sosai ga Gwalagwalai kamar zasuyi magana ta ko ina a jikinta, daman da akace tazo aje W???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?auko Amaryar Ahmad cewa tayi Umma ta gaida Ashsha ita babu ita cikin harkar tsiya ba zata ba.

A Sangaren Alhaji daga gefe akwai guest room, Wakuna biyu ne ciki da madaidaicin falo. Yawanci yanzu da baya zagayen kamfanunuwansa idan suka tashi lissafin shekara yafi so suyi a gida su kanyi dare dalilin daya saka aka tada ginin kenan Manajoji da lauyoyinsa suke kwana a ciki idan hakan ta kama nan gurin aka gyarawa Amare zasu zauna da ?awayensu kafin lokacin Dinner saboda cikin gidan babu masaka tsinke ko ina ya cika da bil'adama daman kuma daga can gurin dinner kowacce zasu wuce gidansu da Mijinta babu yan kai amarya wannan tsarin Baba Al?aline. Basu wani jima sosai da zama ba Fatima da tsirarun ?awayenta da sukayi Abu tare suna zazzaune suna cin abincin da aka gabatar musu, Badar na gabanta tana lallaSata kan taci abinci. ?asa ?asa take ce mata

"Ki ci ko babu yawa kinga fa tun safe babu abinda kikaci kinata ba?in rai da kukan banza da baze amfana miki komai ba, nidai ba zan gaji da tuna miki yanzu kin zama matar aure ba, kici gaba da tunanin wani ?ato a ranki har kina masa kuka mala'ikun Allah nata rubuta miki zunubi shi kuma yana can yana lole soyayya da zaSin ransa ji gara ma kici abincin ki samu fuskarki ta marmaro kar kwalliyarki ta?i kyau wlh dan ku biyu ne yau kinga dai shi ya gama ciyar da matarsa tun a jirgi abinsu" Badar Win ta ?arasa tana kanga mata wayarta video Jay da Fatiyyah ke playing yana bata abinci a baki se wani narkewa takeyi rabin jikinta akan nasa, murmushi me ciwo Fatiman tayi kafin ta karSi plate Win shinkafa da Kazar data saka mata ta faraci badan daWi ba, ta sani gaskiya Badar da duk sauran mutane suke gaya mata ita ma kuma tasan hakan amma ya zatayi? Sun gagare gane ita ba kukan son Jafar takeyi ba kukan yaudararta da cutar da zuviyarta da yayi takeyi ita me kuma zatayi dashi yanzu da har zatayi kuka akansa badan ma bata da iko da zuciyarta ba ai da tunin ta daWe da goge duk wani tunani nasa a ?wa?walwarta da zuciyarta baki Waya.

Tana cin abincin Ahmad ya kirata ta amsa, muryarsa me taushi me cike da shau?i da mayen sonta yace
"Mun dawo kizo ki tarbe ni". Ta saki murmushin da bata shirya masa ba saboda yanda yayi maganar kafin cikin sanyi tace
"Daga gobe ba se ka ro?a ba, a bakin ?ofa zaka ringa tarar dani ina jiranka"
"Dagaske Babe?" Ya faWa muryarsa cike da farin cikin da ko ba'a faWa ba na jin daWin amsar data bashi ne, ta kaWa kai kamar yana gabanta tace
"Dagaske"
"I can't wait, Allah ya nuna mana anjima daman da akwai karatukan da nake so na fara biya miki dan ki haddace su da wurwuri ki shirya mun sosai fa kinji" ya sake faWa, bata amsa ba saboda zuciyarta data raya mata abinda yake nufi, shima ace haka yake, be damu da shirunta ba yace mata I lobiyu kafin ya kashe wayar ta ajiye taci gaba da cin abincinta.

Shirun da taji Wakin ya Wauka yasa ta Waga kai ta kalle su tayi zaton ko sun fita ne se taga ashe duk ita suka zurawa ido suna kallonta, Fatima Adam tace
"Almura, wanda be san halinki ba kin cuceshi Afeeyah"
"Haka Almura ma take? daman mena gaya muku tsabar iskanci ne tana so tana kaiwa kasuwa koda yake ai epizy ya ?are dan uban mutum dole ya bada kai bori ya hau koya?i Allah" inji Islam suka saka dariya gaba Waya ita kuma ta hararesu tana cigaba da cin abincinta.

?wa?wa?was takun takalman yan gayu da shewa da hayaniyarsu ya karaWe kunnuwansu kafin aka buWe ?ofar falon da suke zaunen yammata suka fara shiga kana ganinsu kasan shafaffu ne da mai, sun kai su goma sha biyar kowacce taci ado da suturu na Alfarma sedai Winkunansu ya bayyana rashin wadatar tarbiyya a gidajen da dayawansu suka fito dan abin ba'a cewa komai, Amarya na tsakiyarsu jikinta lulluSe da laffaya fara wadda suka ganta da ita cikin hotuna da videos Win da sukayi a hanyar tahowa.

Ido cikin ido suka kalli Juna ita da Fatima, babu wani yanayi a kan fuskokinsu da ze nuna abinda yake zukatansu, kusan a tare kowacce ta Wauke kanta gefe, su Badar dai kallon yammatan sukeyi yayinda su kuma suke ?arewa falon kallo.

"Wai Fatiyyah a nan zamu zauna duka da mutanen nan kamar wasu prisoners duk girman gidan nan ace ba'a ware mana inda zamu sauka ba daman? Jifa gurin" wata wadda da alamu tafi sauran Waukar duniya da zafi ta faWa tana wani taSe baki tana kuma kallon su Badar kamar taga kashi, wadda ke ri?e da hannun Amarya tace

"Ke kin fiya matsala Amal wayace dole ko zauna a nan?"
"Aa fa ba Amal kaWai ba Hanan nima bazan iya sharing room ba gaskiya i thought they will offer us single rooms shiyasa na biyo ku banbi su Mom Hotel ba amma yanzun nan tafiya zanyi gurinsu" wata tsigalalliya ta sake faWi, kusan mutum bakwai cikinsu suka sake mara mata baya suna maganganu ita dai Amarya na tsaye bata ce komai ba se wadda suka kira da Hanan ce take musu magana amma basuji ba suka ja Akwatunan su fiii suka sake ficewa,
"Kuyi ha?uri dan Allah" Hanan faWa kafin taja Amarya Fatiyyah suka zauna tareda sauran ?awayenta uku da sukayi saura basu bi waWancan ba, sudai basa cewa komai amma kana gani kasan suna jin kansu da yawa.

Hajiya ?arama tareda wasu yan uwansu na Kaduna ne suka shigo da kayan abinci suka ringa sauke musu, seda suka gama kafin suka gaisa dasu Badar cikin mutuntawa tana kallon Fatima tace
"Yi ha?uri matar Yah Ahmad ni ya kamata na tareki amma kunzo bana nan naje taho da make up artist Win da zatayi muku kwalliya ne daga airport tana can zata ci abinci yanzu ta Wan huta kafin nan kuma kunyi wanka se a fara ko saboda lokaci ko?" Ta ?aras atana kallon Fatiyyah kafin ta mi?e tayi musu sallama ta fita. Basu ko taSa abincin ba kowacce se latsa waya takeyi kafin Fatiyyah ta fara waya da alama kuma da Angonta ne dan sunji tana cewa

"Gaskiya ka nema musu accommodation ai wannan ma zasuce nayi musu wula?anci suzo bikina amma ace sun rasa gurin kwana", ta cuna baki da alama kome yake faWa mata bame daWi bane kafi ta cire wayar daga kunnenta bayan data saki siririn tsaki, cikin masifa Hanan tace mata
"Akan me zaki kirashi? Nan Win bola ce da zasuce ba zasu zauna ba se kace kwana zasuyi a gurin naga zaman lokaci ne mu shirya kawai mu tafi gurin Dinner daga can gidan Anty Diyana zamu tafi mu kwana amma shine zasu tsaya sunawa mutane izgilanci ke kuma harda kiran Mijinki kice ya canza musu guri saboda baki da hankali wlh indai wannan halin zaki cigaba dashi biyyewa ?awaye zaki sha wahala" bata kula Hanan Win ba ta tashi ta wuce ?ofar da take zaton itace ta Bedroom, bata ma tsaya tambayan wannene nasu ba ta shige ciki dan ranta a bace yake da wayar da sukayi da Jay, ce mata yayi matsalarta ce data ?awayenta ba tashi ba.

Duk suka rakata da ido harda Fatima seda ta bugo ?ofa kafin kowanne ya Wauke idonsa ya cigaba da abinda yake a gabansa su Hanan da sauran jama'arta suka bita ciki Badar tace
"Ikon Allah inda ranka zaka sha kallo"
"Ai kuwa dai, wannan faccala taki da alama kanta yana haya?i se kin bita a hankali" cewar Fatima Adam Badar ta hayayya?o mata tana cewa
"Kamar ya ta bita a hankali? Ita ce mijinta ko kuwa gida Waya zasu zauna? Ke kina jina ko idan taso kuyi mutunchi kuyi karki kuskura ki raga mata in tazo miki da iskanci ehe tana tafiya tana wani kaWa ?ugu bayan ciko phone store ne"

"Badar jaraba, tsabar sharri da taya ?awarki kishi shine zakice cuko tayi kina kallo abubuwa masha Allah kakar ita ta zanawa kanta amma fa babu ?arya itama ta haWu jiki yaji hutu ku kam mazajenku sun iya zaSe ba wanda zeyiwa wani iyayi da mata" Mardiyya ta faWa Badar taci gaba da mitar abinda ?awayen Fatiyya suka musu.

Hajiya ?arama da Khadija ne suka rako me kwalliya da apprentice Winta bayan sun gama cin abinci, ta kalli Fatima tace
"Aa, Anty Fatima kina zaune bakiyi wankan ba? Ina Anty Fatiyyan ko ita za'a fara yiwa?
"Eh idan ta shirya a fara yi mata kafin muyi magrib se ayi mun" Fatima ta bata amsa a sanyaye se suka wuce ciki inda su Fatiyyan suke. Khadija ce tace su Badar dasu Hanan suyi sharing Wayan Wakin se su bar Amaren tare ayi musu kwalliyarsu su kuma ga Apprentice Win me kwalliyar idan da wadda take so ayi mata toh hakan sukayi Badar ta maidawa Fatima akwatinta Wakin da Fatiyyah take, sanda

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login