Showing 207001 words to 210000 words out of 467220 words

Chapter 70 - MATAR MUTUM COMPLETED 1-3 BY MARYAM FARUK.doc

23 Sep 2025

12189

masu ha?uri basu iya fushi ba yau kuwa gashi ta tabbatar.

Ahmad kuwa seda yayi dagaske kafin ya danne abinda ya ringa cin zuciyarsa, yana da kishi matu?a musamman akan abinda yake so kamar Fatima. Koda yake binta yana lallaSata dan yasan kawai ra'ayinsa ne batayi bawai wani saurayi ne da ita daban da yasa take ?insa saboda shi ba. Yasan bata double dating, shiyasa ya nace yake ta ro?on Allah yana kuma ?ara cusa kansa gurinta amma yanzu ya fahinci ta samu wani saurayin da take ra'ayi shiyasa harta iya ci masa fuska ta ringa waya dashi a gabansa shi ga sakarai wato bazeji komai a ransa ba.

Seda aka kwana biyu da Wakkota da yayi be sake kiranta ba, dan ya yanke dole ya koyawa zuciyarsa ha?uri da ita tunda har ya fahimci da wani bayan shi yanzu komai yana iya faruwa kenan. Da safe ranar Asabar kwana biyu kenan da dawowar tata yana kwance a Wakinsa se gashi ta kirashi. Ya ringa kallon wayar kamar wanda yayi loosing memory saboda ya kasa yarda Fatima ce take kiransa da karan kanta yau. Rejecting yayi kafin yabi bayan kiran duk da zuciyarsa nace masa karya amsa ya bar wayar tayi ringing ta gama harta sake kira dan ya tabbatar da gaske shi take kira ba tuntuSen number tayi ba.

"Ina kwana?" Ta faWa a sanyaye bayan da yayi mata sallama ta amsa. Ya amsa gaisuwar yana jin tamkar ya taka rawar murna, dahgaske kenan idan mutum yaja aji za'a mutuntashi tunda gashi fushin kwana biyu ya juyo masa da hankalin Fatima.
"Kayi ha?uri akan abinda ya faru ranar nan banyi da wata niyya ba" ta sake faWa a sanyaye. DaWi ya sake kamashi, har tasan ta kirashi kenan ta bashi ha?uri ai kuwa akwai haske a cikin tafiyar. Ya wani mula yace
"Babu komai kawai dai na gaya miki idan kika sake sena fasa wayar tunda bazan iya fasa miki baki ba"
"Ai dai nace kayi ha?uri" ta sake nanatawa yace
"Na ha?ura na kuma yafe miki Alhakina da kika Wauka kika sa nayi fushi dake".

"Uhm" kawai tace, suka Wan taSa hira kafin sukayi sallama bayan yace mata zeje da yamma tace tana gidan Anty Sauda ya sameta a can dan kwana zatayi.

"Toh ko kefa? Nifa harga Allah zancen wani ?an Ball be kwantamun a rai ba. Haka kawai zaki kwasarwa kanki abinda ze saka miki ciwon rai idan ya aureki Win ma kenan. A matsayinki nawa Afeeyah zakice zaki auri world class Celebrity? Ai Wagen yayi yawa, irin waWannan ai ba kowacce mace ba, kuma duk ma ba wannan ba na tabbatar wlh fuskarki ce kawai ta ruWeshi, babu tabbacin idan yasan wacece ke ya yarda ya aureki a haka gara miki Ahmad Win. Mutumin nan ga Hankali, nutsuwa, mutunchi, karamchi uwa uba yana matu?ar sonki kuma ya sanki ciki da bai yasan Mahaifanki a hakan kuma yace yaji ya gani yana sonki ze aureki na rasa wace masifa ce tasa bakya son Bawan Allahn nan Afeeyah wlh in guje miki kiyi nadanar da ba zata amfana miki komai ba a gaba" Anty Sauda wadda ita ta tursasata kiran Ahmad bayan data shaida mata abinda ya faru tsakaninsu ta faWa.

Afeeyah ta zumSura baki, kafin tayi magana wayarta ta shiga ?ara, ringing tune data sakawa Jay ne dan haka ta mi?e da sauri da wayar a hannunta ta shige Waki Anty Sauda ta rakata da ido tana cewa
"Idan kina da rabo Allah ya ganar dake amma wlh nasan wannan Jay yake kowa yaudararki yakeyi ba auranki zeyi ba gara tun kina da sauran dama kiyi amfani da ita amma ba takanki zanbi ba, Baffa zan samu tun wuri asan abinyi baze yuwu shekara biyu ki gama yaudare bawan Allah kizo kice ba zaki aure shi ba" taja wayarta ta shiga kiran Baffansu sedai wayarsa a kashe. Tayi ?wafa a fili ta sake cewa
"Har gidan zanje, gara ko auran dole ne miki tunda baki da hankali" ita dai Afeeyah na kan gado tana malele kuwa Jay na kasheta da kalaman Love, tunda suka shirya ta manta komai. Hatta maganar dake ta azalzalar zuciyarta ta mahaifiyarsa bata tayar ba tama manta da batun ta sake zama daram akan Al?awarurrukan madarar ?aunar da yace ze shayar da ita idan sukayi aure. Ya mata Al?awari nan da watanni shida zezo Nigeria musamman saboda ita, ya kuma ce mata zuwan da zeyi zeje ya gaida Mahaifinta daga nan iyayensa suzo dan ya rigada ma harya gayawa Yayansa maganarta shima shirin Aure yakeyi tare za'a haWa da nashi dan haka ta fara duk wani shirinta da idan yazo tana iya yuwuwa daga tambaya taji an Waura musu aure kawai sedai taji ana fito kibi Mijinki.

Ranar tayi dariyar maganarsa yace tasaka wasa zata gani da gaske yakeyi, Alhajinsu bashida wasa ko yau yace masa zeyi aure muddin ya yarda da inda ya nemo auran magana ta ?are tambaya kawai za'aje ayo. Wannan tasa ta yanke shawarar sanar da maganarsa a gida tunda wuri ba wai se rana tsaka ba, ta fara takan Anty Sauda domin itace tsanin da ze kaita gasu Baffa. Muddin tayi na'am da abin tasan komai ze zo da sau?i sedai daga yanda ta karSi maganar tasan ko zata yarda se an yi ?waibai da ita dan tamkar Badar itama Ahmad ya lashe mata zuciya sonsa suke nasa son abinda ze taSa shi. Daga ce mata sunyi faWa tace seta kirashi ta bashi ha?uri idan ba haka ba ta gayawa Baffa ta samu wani saurayi yana hure mata kunne harta kori Ahmad ta masa wula?anci shiyasa ta kirashi.

****************
Hajiya Binta zaune kan carpet tana zubawa Alhaji Audu faten Accar da tayi masa saboda tana da bu?atu yau da kanta ta tsaya ta masa girki me kyau ta kashe gayu da wata kamfalarta shadda ta saka daham, lallen bikin da aka mata tun yau litinin yayi raWau a hannayenta da ?afa dukda na Salatif ne me yankan Siga amma da yake fatar da sauran Armashinta ya mata kyau. Humrar da akayiwa Amarya Hafsatu ta bulbula abinta ?amshin har hawa kai yakeyi dan seda Alhajinya kunna fanka bayan Ac dake falon saboda Atishawar da turaren nata ya saka ya fara jerawa.

Hira take masa wadda duk labarin irin tsaruwar gidan Hajiya ?aramar take zayyana masa. Jiya su Turai suka dawo daga jere, dakyar da ro?on Allah ma ta yarda ta zauna dan cewa tayi da da ita za'aje.
"Wannan wane irin abune babu kunya kawai Binta ki bimu se a ganki tsalam ace ga uwar Amarya a ina kima taSa ganin anyi haka? Ita Aisha data aurar da Yaya biyu gata uku wanne kika gani a ciki tajewa jere baku ne kuke zuwa ba se kece zakice se kinje salon ki zubarwa da yarinya ?ima tun bata kai ga shiga cikinsu ba? Abujar ce baki taSa zuwa ba ko kuwa ance za'a rufe shigarta ne idan bakije yanzu ba?" Turai ta ringa zazzaga mata bala'i dan lamarin ?awar tata ya fara kaita bango.

Fafur tace Anty Rabi da Momy ba zasuje mata jere ba, Baba Bilki ma da tace ba za'a da ita ba dake har yau na sanyi tayi ba tace ai uban Binta ma yayi kaWan balle ita ta hanata zuwa gano gidan Yar Audu. Saboda neman suna tace wai Hajiya Balaraba tazo aje da ita tace Aa saje kai Amarya daga ?arshe dai bisa tursasawar Turai suka tafi da ita da Momy wadda bata so zuwa ba se Hajiya Zainab da Munirah ?anwar Binta wadda har yau sama da shekaru hamsin kenan tana zaune bata samu Mijin aure ba bayan rasuwar Mamansu ne ta dawo nan Kano da ta fara zama gidan Binta zama ya?i daWi se kawai ta siyi gida take zaune abunta tana kasuwancinta tana cigaba da ro?on Allah daya yanke mata dukda ta san cewar ba komai ya janyo mata shiga halin da take ciki ba se ha??in baiwar Allah da bataji ba bata gani ba suka la?a mata sharrin da harta mutu wasu na kallonta dashi. Suka hanata zaman lafiya a gidan auranta harta koma ga Allah.

A can Kaduna suka haWe da sauran yan uwan Binta akaje akayi jeren wanda babu wani abin arzi?i data siya. Kayan Gado dai a BECHI FURNITURES yace aje a Waukar mata duk abinda uba yakeyi saSanin su Khadija dayake ?ayyade Adadin kuWi yace a Wauki kaya na kaza. Su Turai ne sukaje suka zaSa suka darje kaya na ?arshen mutunchi a shagon, da Alhaji yaga Invoice ya ringa surfa masifar da bata da Amfani domin dai shiya nada dama kuma sun rigada sun Wauka har an jera dan a Branch Winsa na Abuja suka kwasa ?arshe abin ya ?are akan Aslamiyyah yace Gado biyu kujera biyu za'a Waukar mata saSanin Hajiya ?arama da aka sakawa huWu, Waki biyar ne a gidan da faluka biyu manya se ?arami Waya wanda yake haWe da Master Bedroom a sama shine na Megidan iyayensa sun gyara masa dan haka hatta Wakin da me aiki zata zauna Royal aka saka saboda samun guri da nuna akwai.

Kayan Kitchen dai daman yace musu a Al'adar Hausawa uwa ce takeyi to yana kan wannan magana har akan Hajiya be saketa ba dan haka ita tayi kayan kitchen tarkacen banza da wofi wasu matsiyatan kuloli da fulasai ta bakin Turai. Yanda ta ringa zuzuta ta gama siyan komai dan ?in yarda suje siyayyar tare tayi, haka ta nuna mata kayan ta?i se randa zasu tafi Jere da za'a Wiba aka tattara kaya ko cika buhu biyu basuyi ba amma faWi take
"Kinga kaya ko Turai? Dama na gaya miki sena baki mamaki ai bikin Nazira shammatata akayi amma wannan na shirya"

"Billahillazi Binta idan baki fitar da kuWinki kinci kin morawa kanki ba se kin mutu kina kwance a ?asa zakiga yayanki na wada?a dasu, yanzu wannan kayan kike zuzutu akai? Abinda ko Talaka me zuciya se yayi ninkin abinda kikayi wannan abin kike so akai ace daga gidan Bechi suka fito? Turai ta ringa masifa kamar zata ari baki tana kafa mata hujja da kanta yanda takeyi idan zata aurar da Yayanta da sauran ?awayensu, ta kawo mata Misalin Momy, auran Khadija da Annah ita da kanta tace har seda suka maido da wasu abubuwan gida dan seda aka kai sukaga an siya an ?ara siya tasan kuma yanzu ma na Aslamiyyah haka zata fitar da kanta kunay.

Duk wanda yaga kayan gadonta da kujeru yasan ubanta ne yayi mata ke za'a zaga ace uwarta bata da zuciya dan wlh ko yar ri?o a gidan nanta wuci akaita da wannan tarkacen. ?arshe se Alhaji Zakariyya da Alhaji Naziru harda Yakubu Turan ta kira tace kowa yazo ya bada abinda ya samu, ta tattara ta bazama kasuwa tayo mata siyayyar kayan kichen na fita kunya suka kai ta barwa Binta tsiyarta da tace ta ajiyewa Auta Saratu ta huta ita tasan ba zata raina wannan Win ba toh fa tunda suka dawo aka kawo mata Video shikenan ta kasa nutsuwa labari data kai aya zata maimaito tun Alhajin yana ji harya gaji yace mata

"Binta yanda kike nanata mun labarin gidan nan ko zuwa nayi yanzu bazan Sata ba danna gama gane kowanne lungu da sa?o na gidan, ki bani abincin naci kafin ya huce dan Allah do nakeyi na fita zamu haWu da Al?ali mu tattauna yanda taro ze kasance kinga lokaci yana ?aratowa yau Litinin saura kwana huWu Waurin aure".

"Ai toh yi ha?uri wlh santin gidan ne ya?i ya barni, ai Hajiya dai tayi gida Allah ya tsole idon ma?iya yasa mutu ka raba" ta faWa tana bashi. Shida ya shiga cin abincin yana jinta dan batayi shiru ba. Ta gyara zama tace

"Dama Alhaji zancen gurin Kamu ne an gama magana da mutanen nan yanzu sun dawo sunce wai kuWi yayi kaWan se an ?ara kuma ni nayi ?ar?af dubu Ashirin yanzu se nayi da gaske zan fito da ita ai bikin nan dai ya talautani da gaske".

Ya kalleta ta gefen ido a ransa yana mamakinta, wai ta kashe kuWi kome ta yi se Allah bayan duk abinda ake ciki yana da labari. Zakariyya ya gaya masa su suka bada kuWin kayan kitchen bayan ta Wiora musu Alhakin abinda za'aci a gurin Mother's eve data shirya shi kuma nan be san Buhu nawa da galan na mai nawa da sauran kayan abinci data kwashe masa a Store tace za'ayi abincin biki ba. Kaji Wari biyu ya saka aka bata ita kaWai banda Sa da za'a yanka na abincin yini. Tunda aka fara zancen bikin nan Aisha bata ce ma ya bata sisin kobo ba, Bilki ce ta nusashsheshi har ya batan dukda be kai ko kwatan abinda Binta ta ?wamusa a hannunsa ba. Kayan gado kansu ya banbanta Hajiya ?arama cewa yayi su Wauki wanda ya musu Aslamiyya kuwa dalilin Sarnar da su Turai suka masa shiya faWi kalar wanda za'a Waukar masa an gaya masa Ahmad da Sarki ne sukayi cikon KuWaWe masu nauyi suka Waukar mata irin na Hafsatun kuma duk abinda ya kamata ace yayi wanda Aisha bata tambayeshi ba su sukayi yana kallo aka ringa sauke ruwa da lemo besan katan nawa bane inji Ahmad Jafar kuma shi ya siya Musu Cinema Tv su biyun nan cikin Yaya bila'adadin daya haifa ne suke da zuciyar bashi gudummawar auran ?annensu dukda sun san yana dashi ba babu ba amma yaji abinhar cikin zuciyarsa.

"Alhaji kayi shiru" Hamsha?iyar ta girgizashi. Ya aje farantin hannunsa ya mi?e tsaye yana cewa
"Ki karSo kuWinki kizo kuyi a nan cikin gidan kamar yanda su Aisha zasuyi ni banida wasu kuWi da zan sake baki kuma a yanzu nayi iya abinda zan iya"

"Ai shikenan, kana ji Jafaru wai baze zo bikin bako? Gaskiya ka kirashi kayi masa magana ta yaya za'ayi ace baze halarci Waurin auran ba? Ta ya mutane wai zasu san ?anka ne yafi so ayi ta kallonsa a ba kowa ba ai idanya fito kowa ya san ?anka ne darajar sa seta sake linkuwa a ?asar nan ko ya kace?" Ta sake soko masa wata maganar, ya mi?e yana shiga Waki yace
"Duk yanda kika ce Binta, bari na shirya na fita dai na baki guri" ya barta tana cizon yatsa. Daman ba Even centre data kama, tunda taji a gida Momy zatayi Kamunta zata kira masu Decoration taje kakarta ta yanke sa?a bari zatayi ta gama shirya komai se ranar tayi ta kankane ita da mutanenta dan ba zata iya zare Miliyan nawa ta kaiwa masu gurin biki ba, abinci ma da Turai tasa ta kashi kuWaWe ta bayar ciwon rai takeyi, so tayi ta bawa masu aikinsu ayi shi nan a cikin gida amma tace gun yan gayu zasu kai, so tayi ya bata kuWin ta rage asarar wanda tabayar shine yace bashida su yanzu duk kwalliyar nan da tayi ta tashi a banza kenan ai shikenan.

Alhaji ya fito a shirye yana waya, bata san da waye ba abinda taji kawai ya fizgi hankalinta shine
"Babu damuwa nagode, bari mu gama da hayaniyar wannan bikin zanyi magana dashi. Idan son samune ya ha?ura da yarinyar ya nemi wata dan sam banji abin ya kwanta mun a rai ba amma bama so na hanashi abinda yake so saboda yaron nada biyayya nasan muddin nace Aa tilas ze ha?ura koda ace hakan ze cutar dashi amma yanzu zan samu Al?ali shima da maganar yanda mukayi zakaji".

"Toh fa wane yaro kuma ake magana akai?" Tayi tsalam ta tambaya bayanya kashe wayar. Yana tafiya ze sauka ?asa tabi bayansa yace
"Ahmad ne, ya samu yarinyar da ze aura. Kiyiwa wancan yaron magana shima ya dakata da shashancin da yakeyi ya fitar da mata dan tare zan haWu bana son Biki a rarraben nan"

"Yo naji kana cewa yarinyar bata maka ba? Halan kwashe kwashe yayo ko? Ni daman nasan za'a rina Allah yasa dai ba gidan matsiyata ya kwaso auran ba mu shiga uku su ?ara yawa bamu gama data gidan nan ba ya kwaso mana wata" Hajiya ta faWa shidai be bata amsa ba ya fice daga falon dan Malam Sadi Driver sa yana tsaye harya kunna mota.

Ta wuce ciki inda ta baro ?awayenta da sukazo ana ta tsara yanda biki ze kasance, Kamu dai rigar na Momy zasu shiga dukda ba haka su Hajiya Zainab suka so ba Turai kuma tace haka ne daidai tunda dai Yaran nan ubansu Waya toh ayi Kamun nan a tare idan yaso tunda kowacce gidan Mijinta sun shirya Dinner se suyi abarsu daban ga sauran events da kowacce Amarya zatayi da ?awayenta.

"Yanzu kawai sedai mu zama yan kallo mun raSe raSe kenan?" Hajiya Sha'awa ta faWa, Binta ta karkace tace
"Inji wa? Ai biki namune wahala kawai zasu mana su shirya komai. Da kunji ance ina uwar Amarya ku rufa mun baya mu shige, duk wani kira da za'ayi ku shike kuyi kinini karku basu wata ?ofa a gurin" akayi shewa aka tafa.

Se ranar Laraba Ahmad ya kaiwa Fatima ?inkakkun kaya, Atamfa me kyau da akayiwa Winkin zamani amma Modest Winki se wani shegen Lace da Anty Sauda tace ya haura dubu Wari biyu. Kowanne kaya da mahaWinsa, Takalmi, mayafi, jaka harda Sar?a da agogo. Zobunan gold guda biyu ya saka mata a ciki ganinsu ya tuna mata da ranar da yace ta nuna masa hannunta kenan measurement Win hannun ya Wauka. Yace mata Atamfar ta Ankon Kamun ce dan ya gaya mata zasuyi biki har Iv ya tura mata Lace kuma kawai Winka mata yayi na Dinner.

Tace ba zataje ba Umma ta goya mata baya a cewarta babu tsayayyar magana a tsakaninsu da har zata saka taje musu biki, idan kuma zuwan nata ya janyo wani abu da ba za'a so ba fa? Gara dai da ace anyi magana yan uwansa sun san da zamanta da sau?i ko cikin yan uwa tana iya samun wata suje tare su dawo. Baffa ma da aka gaya masa cewa yayi Aa. Da kansa ya kira Ahmad yace ba zataje ba, yayi kuma faWan zobuna har biyu da Umma tace masa zinare ne yace in yazo ya karSe su ya ajiye idanAllahyasa taje gidansa ya bata ya dai amsa da Toh amma koshi Baffan yasan baze

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login