Showing 129001 words to 132000 words out of 467220 words

Chapter 44 - MATAR MUTUM COMPLETED 1-3 BY MARYAM FARUK.doc

23 Sep 2025

12502

ta nemi Bus dan ba zata bimu ba"
"Tunda motar takice?" Ya mayar mata ba tareda ya kalleta ba, ya juya kan Aisha ya dan saki fuska yace
"Bismillah, muje ko?"

"Kuje ina? Au itama fitar zatayi?"
"Kinga Binta idan baki zuwa ki koma ciki suma duk Asibitin zasuje". Tana cika tana batsewa suka fita wajen tayi wuf zata shige gaba Audu ya dakatar da ita da cewa
"Shiga baya, Aisha ce zata zauna gaba"
Hadiza ta kwashe da dariya Binta ta sake ?uluwa ta lailayo Ashar ta watsa mata ita dai ta shige mota tana cigaba da dariyarta.

Bayan sun isa Asibiti tana tsammatar taga kowa ta kama gabanta dan a zatonta dubiya su biyun zasuje se gani tayi sun nufi bangare daya na yan Awo dan a waje ya ajiye su yace idan yaje kamfani Musbahu and juyo da motar ya jirasu ya mayar dasu gida.
Binta ta ringa binsu tana jira taga abinda ya kawo su gurin Awon ciki sedai daga yanda taga suna gaisawa da Ma'aikatan gurin tasan da sanayya a tsakani suka zauna gurin jira ana bin layi bayan an karbi Katunansu jikinta har rawa ya dauka sanda taga kowa ta zaro kati daga jaka ta mi?a kenan duk cikine dasu bata sani ba? Yaushe akayi? Tana zaman me?

Aka ringa kiran Binta Zakariyya ina bata ma jisu ba tayi nisa a duniyar tunani da zullumi karfa suma duk su haifi Maza dan taga kamar Audu bashi da ?wan haifar ya mace. Matar da take musu awon ta kallera tace
"Baiwar Allah tunanin me kikeyi haka duk kin firgice kalli fa har jininki ya Waga?"

"Kedai kiyi aikinki ki sallameni ina da abinyi" Binta ta gwaSa mata magana aiko matar ta harzi?o itama tace
"Se nice banida aikinyi ko ai bacci kika ga ina yi yanzu ko rawa"

"Kiyi ha?uri Sista" Hadiza ta tsoma musu baki aiko Binta tayi kanta da masifa ganin a waje suke yasa ta mata shiru se ma'aikatan ne suka haye itama Bintan kamar sa cinyeta Awon da ba'ayi mata ba kenan ta tattara ta fice ta haye Bus se unguwarsu Turai dan tana bu?atar su tattauna wannan matsala ta yaya za'ayi su biyu suyi ciki.

Audu kuwa isarsa kamfani ya tarar da wani mummuman Labari, motoci guda biyar da suka dakko masa Mai daga kudu haka nan wuta ta tashi sun ?one ?urmus harda direba guda daya dayayi ?undunbala saboda motarsa ce ta ?arsher sun tsaya zasuci abinci Abin ya faru tamkar Tsafi kawai wuta ta kama motar tsakiya kanka kace me sauran sun dauka an hanashi amma ya kafe ya tafi a zatonsa ze iya janye motar kafin wutar ta cimmata se gashi yana shiga ta kama gaba daya se tokarsa aka tattare.

Babban abin al'ajabi kamar yanda aka bashi labari ba iyakacin motocinsa bane a gurin mota tafi Ashirin da suka taho????      

                  ! " # $ % & ' ( ) * + , - . / 0 1 2 3 4 5 6 7 8 9 : ; < = > ? @ A B C D E F G H I J K L M N O P Q R S T U V W X Y Z [ \ ] ^ _ ` a b c d e f g h i j k l m n o p q r s t u v w x y z { | } ~  ? tare duk sukayi fakin suna cin abinci amma ibtila'in akan nasa suka sauka basu taba komai ba duk kuma iyakar ?o?arinsu na su kashe wutar abu ya gagara. Hankalin Audu ya tashi matu?a domin ba ?ananan kudade ne suka narke ba sannan ga Rai da aka rasa. Gaba daya suka Wunguma gidansu Direban daya rasu me suna Lawan sukayi musu Ta'aziyya, ya bawa Iyalansa kudade masu Wan kauri da kayan abinci yace kafin su yanke abinda ya kamata suyi musu. Wannan damuwar tasa ya manta da matansa na Asibiti a can kuma bayan sun gama har bayan Azahar shiru Musbahun dayace ze zo ya maidasu beje ba Hadiza tace su tafi kawai ta yuwu aiki yasha kansa ya manta.

Hakan ko akayi suka kamo hanya suka dawo gida, sun sauka a bakin titi Hadiza tacewa Aisha
"Ko zamu ?arasa gidan Yaya Yakubu dan naji Babansu Baba yace sunzo gari muje muyi Bikon Yaya Balaraba be kamatu ace bama zumunchi da ita ba gaskiya"
"Amma bazeyi faWa ba?" Aisha ta faWa cikin sanyinta. Hadiza tayi murmushi tace
"Haba dai gidan Yaya Yakubu ne fa babu faWan da zeyi kuma tunda ba girki zamuyi ba kinga bamu da matsala da anyi la'asar se mu wuce gida idan ya dawo se mu sanar masa da munje".

Faran faran Balaraba ta tarbesu daman ta dan wayi Hadiza sukan hadu idan tazo gidan Yayarta lokacin da suke can unguwar suma Aisha ce bata sani ba dan bataje gidan ba Yakubun dai yaje yaga Amare da yace suje tace Aa ai bata da sauran dalilin zuwa gidan Audu kuma. Se da sukayi sallar La'asar sannan sukayi haramar tafiya ta hada musu tsaraba cikin abubuwan data zo dasu, Dada da jininsu ya haWu da Aisha tana ganin sun tashi tacezata bisu

"Ki bari muje da ita idan yaso se Baffansu ya maido ta anjima da daddare" inji Aisha suka tafi da ita.
Sun riga Binta komawa gida itace da girki kuma, sun tarar da yaran sun dawo daga makaranta Abdullahi ya tafasa musu taliya sunci da sauran miyar da yace ya gani a Kicin, shidin yana gida yanzu sun gama jarabawar fita daga sakandire da Audu yace ze fara zuwa kasuwa se kuma yace ya zauna ya huta dan ?asar qaje yake da burin turashi idan takardar sa tayi kyau.

Binta bata dawo na se guraren biyar da rabi ta shiga gidan tareda Lantana da alama ko ta biya ta gidan tane ta kirata shigarsu babu jimawa Mairo ma tazo ta fara shirin dora abincin dare. Shiru shiru har akayi Isha'i Audu be dawo ba, Binta ta sake cika tayi dam saboda ita keda girki shiyasa yayi zamansa a waje da waccen yar shilarce ai da tuni a gidan ma zeyi Magriba jikinsa na rawa se kace nata Matancin na Gwal ne. Har tara ta buga shiru babu Audu, Hadiza ta le?a falon Binta dake zaune tana kaWa ?afa tana kuma ayyana tijarar da zatayiwa Audu yau idan ya dawo taji muryar Hadizan na tambayarta ko ya shigo.

"Ke matarnan ki fita daga sabgata wallahi tallahi idan kika ti?eni sena miki abinda bakiyi tsammata ba. Wato kunga gurin zama har kun bude mara kun Wauki ciki to wlh ku kwana da sanin zaku haifesu a gidajen ubanninku kuwa" Binta ta faWa tana mi?ewa tsaye. Hadiza da fuskarta ke cike da damuqa tace

"Ni ba tashin hankali ya kawoni gurinki ba, gani nayi ya zarta lokutan daya saba dawowa kuma idan ma zeyi dare irin haka yana sanar mana shiyasa hankalina ya tashi. Mijina na fari daga irin wannan fitar shiru shiru se bugamun ?ofa akayi na buWe aka shigo da gawarsa"

"Keta shafa wannan ni tsakanina da tsohon mijin naki ai Allah ya isa ce da be mutu ba ai da Mijina be kwaso mun ke kinzo kin addabeni ba, ki barmun ?ofar daki kuma Audun ai ba Ji njiri bane da za'ace ya bata" Binta na rufe baki sujai dirar mota mintina kaWan ya shiga fuskar nan kamar wanda aka aikowa da sa?on mutuwa be kulasu ba ya durfafi sama harya fara hawa meya tuna kuma ya sakko ya wuto ?akin Binta.

"Au da hankalinka ya gushe can zakayi kenan an maka kiranye ka shigo kamar wanda aka jefo baka ko gani dakyau ai seka tafi can Win" Binta ta faWa tana babbake ?ofarta. Hadiza tayi masa sannu da zuwa ya Waga mata hannu yana cewa Bintan
"Matsa na shige"
"Ai sedai ka koma inda da ka niyyaci zuwa" inji Binta. Tsaki me ?arfi yaj ya juya ya haye saman Hadiza tabi bayansa Binta ta kwarma Ihu murya a sama tana kiran yau akwai tashin hankali a gidan ashe.

A saman kuwa harya fara cire kaya Hadiza ta isa, a tausashe take cewa
"Da alama gajiya tasa ka manta ba a nan kake na yau"
"Ina sane, sedai in kema korata zakiyi se in tafi" ya bata amsa.
"Ba haka bane, rigimar Maman Zakariyya ce bana so kana jiyowa gata can tana masifa bana son tashin hankali ko ?o dazun a Asibiti seda aka ce mu guji yawan hayaniya" ta sake faWa cikin taushin lafazi. Audu ya rafka tsaki, da matan nan sun san me yake ciki da sun Waga masa ?afa. Rigarsa ya raruma ya sauka sukayi kiciSus da Binta na hawowa ya raSeta ya wuce Wakin Aisha.

Ganinsa ba yanda ta sababa yasa ta masa sannu da zuwa ya shige Waki ta bishi da ruwa, tana jiyo hayaniyar Binta dukda bata jin me take faWi sosai. Abincinta ta kai masa beci ba yana kishingiWe ya harWe hannaye ya zurawa guri daya ido, ta ajiye, tana so ta tambayeshi ko lafiya amma ta kasa se kawai ta fita ga Dada da tayiwa mamarta al?awarin za'a maidota hartayi barci yanayinsa kuma ya nuna ba lafiya ba balle tayimasa maganar.

Tana zama Binta ta faWo kamar jifa, ta mata kallo daya ta maida idonta kan Talabijin yanayin kallon Hadarin kajin da tayi matan ya saka Binta yin shiru dan kwarjini yarinyar ta mata, tabbas Sarauta ba ?arya ba. ?akin data san zata samu Audu ta tura ta shiga, Aisha bata san ya sukayi ba taga Binta ta fito sumi sumi ta wuce. Data sake le?awa se taga kamar yayi barci dan haka ta shige dayan dakinta suka kwanta tareda Dada.
*PROMO PROMO PROMO*
*Nace kina da Labarin MOMMY MOROCCO ME KAYAN MATA KUWA?* *Ko kuwa dai kina nan zaune baki wangale kina fama da masu niqa Kuka da Citta ko su qulla miki Garin Masara da sunan Magani*? *To ki karkade kunnenki Yar uwa ki kuma maza ki dauraye qafarkin nan da tayi furu furu domin MOMMY MOROCCO Ta diro Nigeria kuma tafe take da Abin Arziqi Niqi Niqi*

*Ina mai farin cikin shaida muku Moommy Morocco zatayi BONANZAr kayanta na kwana biyu*.
*Tazo muku da zafafan magungun wanda ya taba amfani dasu ne kadai ze baki labari Ingantattun magunguna na gani na fada ajin farko wanda aka hadasu cikin tsari da kula daga Ganyayyaki da kayan abincinmu masu qara lafiyar jiki da saukarwa Mace Ni'imar da take buqata kayanta babu Algus babu abinda ze cutar dake da yardar Allah*
*1-Da akwai hadin First ladies exclusive VIP package*
*2-Qafarka qafata package*
*3-Kankat package*
*4-Da kuma Mini package*

*Tazo muku da gangariyar maganin SANYI sadidan na Jiki dana Mara wanda In sha Allaahu ba ke ba sanyi kuma za a iya ba wa Yara, Maza ma suna sha*

*Bata tsaya iya nan ba tazo da Turarukan ta na ban mamaki se wanda ya gwada ze bada labari, Kedai kada ki bari de wannan damar ta wuceki domin ta zabtare Farashin kayanta har zuwa kaso 50% discount! Kyaso wannan gara basa ta wuce ki kuwa Indai ba Bintan Audu kike ba* >?t?>?t?
*A tuntubeta a WhatsApp:09086233009*
*Ko kiran waya a 08029988065*

*Siyan Nagari Maida kudi gida*

*MATAR MUTUM*
*NA MARYAM FAROUK (UMMU MAHEER*

*FIKRA WRITERS ASSOCIATION*

*LITTAFIN KUDI NE*
*PAY 500 A ASUSUN*
*7061838488*
*OPAY DIGITAL SERVICES*
*MARYAM FAROUK*
OR
*0709290797*
*ACCESS BANK*
*SE A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488*
*IDAN KATINE A DAUKI HOTONSA A TURA ZUWA LAMBAR SAMA VTU KUMA A TURA A 08142548705*

*Kuyi following dina a Arewabooks @Maryamfarouk01 inda zaku karanta wannan littafin tareda sauran littattafaina*
*NAGODE*

*PAGE 31*


Seda aka kwashi sati daya cikin wani yanayi a gidan, Audu ba magana babu murmushi bare dariya duk kuma wadda tayi kuskuren shiga sabgarsa ta jawa kanta tijara. Basu san me yake faruwa ba se randa zugar Yan Bechi suka zo Bus biyu ranar befita ba kusan kwana biyu ma kenan be fita ba sedai yaransa dake ta zarya a gidan kuma sedai su fita can inda yake ajiye mota suyi magana ko Binta duk iya labenta bata tsinto abinda ake ciki ba har seda yan Bechi sukazo jaje.

Ashe bayan motar Mai kwanaki Babbar Gonarsa da yake noman shinkafa ruwa ya shanyeta. Gonata ba yar ?arama ba. Shinkafar kuma tayi kyau dan har an saka ranar girbi Dam din dake kusa da inda yake Noman yayi ambaliya gana Waya ya shafe gonakin dake kan hanya abindai ya munana ba'a cewa komai.

Binta ta ringa kyarma jin Ma?udan kuWaWen da aka ce sun narke daga kan Mai zuwa shinkafar,
"Shikenan, a garin kwashe kwashenka ka kwaso mana me farar ?afa" ta faWa hannu biyu aka jiki na tsuma hawaye suna sakko mata. Duk akayi shiru aka zuba mata ido banda Audu dayaja tsaki dan maganar tata Sacin rai ta ?ara masa ya tuna da wani lokaci can baya sanda suna Yara tun Malam nada rai Goggo Fadi na ce musu yayan me farar ?afa, a lokacin abinda ya dauka saboda Dada Farace tar duk jikinta abinda take nufi kenan kalar fatar ?afarta shiyasa be taSa gayawa Dadan ba se bayan daya girma ya san ma'anar abin sannan ya fahimci zaginsu takeyi shiyasa duk inda yaji an faWa se ransa ya baci.


Binta ta ringa kuka tana maimaita an Auro musu me farar ?afa shikenan zasu tagayyare su shiga wani hali yan jaje suka koma wasu na ganin salonta data saba la?awa matan da yake aurowa sharrine wasu kuma sun yarda da abinda ta fada dan tun bayan Auran Audun abubuwa suka fara canzawa yanayin bun?asar Arzi?in tayi ?asa ba'a dai samu wani ibtila'i babba kamar wadannan ba.

A hankali rayuwar walwala da jin dadin da akeyi a gidan ta fara juyewa zuwa ?unci da tashin hankali dan zuciyar megidan a kusa take kullum ?iris yake jira a taSashi yayi zazzaga ga mata uku kowacce da ciki haihuwa kusa hatta da yanayin cima ta sauya dan samun ?asa yakeyi ba sama ba. An kwashi watanni cikin wannan hali, Audu nada shirin mallakar rijiyar Mai tasa ta kasansa a kwankin baya domin har ya fara harhaWa kudade sun gama tsara yanda za'ayi da Alhaji Zakariyya wanda ze siyar masa da daya daga cikin rijiyoyinsa sedai matsalar daya shiga a yanzu da harta girgiza masa jari ta tilasta masa karbo kudaden daya bayar matsayin kafin Al?alami ya sakasu cikin harkokinsa na Noma da kiwo wanda anan Ibtila'in yafi sauka, Amfanin gonar da ya noma a shekarar sama da kaso hamsin ?wari sun lalatashi haka dabbobinsa na gidan gona Kaji sedai a shiga basu abinci a tarar da au fululu a ?asa sun mutu ko a hangi Sa ya Tir?e?en Rago yana kakarin mutuwa sedai a danne a yanka.

Abu dai kamar wasa ana saka ran samu sau?i se ya zamana kullum kamar Tiri ?aruwa abubuwan sukeyi. Mutane da yawa sukace hannu aka saka masa, Asirine, jifansa akayi ya bazama shine waccen tsangaya ya kai sadaka shine waccen gidansa kuwa kullum cike yake da Gardawa anata saukar Karatun Al?ur'ani idan an gama ayi sadaka amma abin se godiyar Allah kawai.

Ana wannan yanayi Hadiza ta tashi da Na?uda cikin dare, Audu da Aisha ne suka fita kaita Asibiti dan Bibta cewa tayi Allah ya kasheta babu inda zataje da Aishar ta shiga kiranta Audu kuma tace masa Yara, be kamatu a barsu su kadai a gida ba. Haka kawai sun hau Titi suna tafiya mota ta tsaya, ya fita yayi yaj dube dube ya sake kunnata yana ja inji yayi wata ?ara Baammm mota ta cake kuma ko ba'a fada musu ba sun san Injine ya buga, tamkar Audu ya fasa kuka, ya fita nemo taimako Hadiza dai nan cikin mota ta haihu ta santalo danta Namiji ?ato.

Wani mutum ne ya taimaka musu ya ?arasa Asibitin dasu se safiya aka sallamosu bayan an tabbatar da ita da Jaririnta duk lafiyarsu ?alau motar Audu kuma akaje da Janwe aka dauketa.
Binta da taga Hadiza ta dawo gida da Da Namiji ba'a cewa komai, ba?in ciki kamar ta mutu ko zuwa tayi mata barka batayi ba har akayi sunan Aminu Hadizan ta koma gida saboda jikinta daya?i mata dadi tun bayan haihuwar Binta faWi take ta tafi kenan ba zata dawo ba.

Haihuwar Hadiza ta sake zuwar musu da sabon sauyin dayafi na farko dan Asara ce take afkuwa kan Asara duk abinda Audun ya taba seya lalace Binta ta samu nayi ta ringa kwakwazo ai damab ta faWa ya auro me Farar ?afa beji ba. Yakubu ya samu Audu yake tambayarsa
"Anya kuwa Audu kana fitar da zakka yanda take idan munyi lissafi?"

Cikin tsananin damuwa Audu yake ce masa
"Allah shine shaidata dukda bani da cikakken sani akan kasafin Zakka shiyasa ma bana fitarwa da kaina nake baka, kuma wlh Duk idan muka fitarda lissafin shekara yanda kace a fitar din nan haka nake cirewa da hannuna nake rabawa dan karma na bawa wani yayi ha'inci ya rage sannan ka san muna fitarda sadaka daban itama haka ake hadawa a rabar nidai na yarda wannan jarabawa ce kawai daga ubangiji ina kuma ro?on daya bani ikon cinyewa"

"Hakane, na godewa Allah daya sa ka yarda cewa duk wani tsanani daga shine haka kuma sau?i ma daga gareshi ne. Kaci gaba da Addu'a muma muna tayaka karka kuskura ka bari wata maganar banza tayi tasiri a ranka ace maka wani ya maka Asiri ko wani abu, ka ?addara Allahn daya baka Arzi?in shine ya jarabceka akansa".

Kwanan Hadiza Ashirin da bakwai da haihuwa Aisha ma ta haihu ta samu Mace. A gida ta haihu daga ita se Bilki da kuma Unguwar zoman da aka kira dan Audu baya nan kuma babu mota balle a kaita Asibiti kuma Allah ya bata da sau?i ta samu yarta Kyakykyawa me kama da ita. Binta na daki tana fama da kanta dan itama ta kusa Lantana ta kwaza mata zancen haihuwar, tayi wata dariya harda buga ?afa tana cewa

"Ita kuma da ?afar hagu ta shigo kowa na farawa da Magaji shine zata haifo mace? Koda yake na godewa Allah, Allah yasa in ma zata cigaba da haihuwar tayita jera irinta" Lantana ta tayata sukayita izgilanci akan Ikon Allah.

Da Audu ya dawo ya tarar da haihuwar, farin cikin jin Mace aka haifa ya wanke masa kaso hamsin na damuwar da yake kwana yana tashi a cikinta. Ya fita ya samo mota suka tafi Asibiti, su kadai yasa aka maido shi kuma ya tafi bakin Asibitin Nasarawa inda suke da zuwa Binta siyayyar Haihuwa dan rigar da aka sanyawa Jinjirar bashi ya siya ba be kuma san inda Aisha ta sameta ba halin daya shiga yasa duk ya manta da wai ana da bu?atar wasu abubuwan na haihuwa Hadiza ma se bayan data haihun ya basu kudi suka siyo abinda ya sawwa?a tunda ta san yanda Al'amuran suke wannan kuwa cewa yayi a hada masa kayan barka na Alfarma, aka ware masa wanda ze tafi dasu lokacin ragowar yace a

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login