Showing 339001 words to 342000 words out of 467220 words

Chapter 114 - MATAR MUTUM COMPLETED 1-3 BY MARYAM FARUK.doc

23 Sep 2025

12099

da ganin fara'arta to babu shi babu gidan Ahmad balle ya kula sabgar matarsa ko yayansa.
"Koda wasa na sake ganin ka shigo gidan nan ka kalli ?ofar Aisha se na saSa maka, sannan wallahi tallahi in na sake ji ko ganin ka shiga gidan Amadu harka kula wannan shegiyar yarinyar sena Waga maka Nono Jafaru, ba kai babu su na raba. Banda ubanku Waya babu wani abu daya haWa ka da Amadu, ba kalar masifar da ban gani ba yana raye sannan ya mutum ma baze barni na samu nutsuwa ba ka gama wahalta masa ka koma kan yayansa da matarsa ko to ahir ban kuma yafe ba naira biyar idan ka sake kashe musu".

Tunani ya ringayi a ransa bayan ya baro gidan ya zeyi, besan yanda zeyi da Hajiya ta fuskanci abinda takeyi ba daidai bane ba ba kuma zeyi mata biyayya gurin bijirewa umarnin ubangiji ba. Zumunchi ai umarni ne daga Allah ba zaSi bane balle ta hanashi, kuma amana ya karSa. Ya sani idan da shine ya mutu ko da Hajiya zata hura wuta ta jefa Yah Ahmad baze fasa kyautata mata a matsayinta na mahaifiyar sa ba. Amma duk da haka kuma baze bijirewa umarninta kai tsaye ba, ze bita ta lallami da siyasa ze kuma cigaba da yi mata Addu'a Allah yasa ta fuskanci gaskiyar abinda take aikatawa ta gyara tun kafin lokaci ya ?ure mata.

Wannan tasa ya yanke shawarar dena zuwa gurin Fatiman a Asibiti dukda daman da haushin shareshi da tayi waccen ranar abin ya kasa ciwo ya kuma siyi duk abinda yasan zasu bu?ata nan kusa ya ajiye musu sannan ya bawa Baba Bilki kuWi ya kuma nemi yaro can a wani guri, ya bari idan suka koma gidan zeyiwa Baba Bilki bayani yaron shi ze zama a tsakiya duk abinda suke da bu?ata ze ringa samar musu dashi ta hannunsa babbar damuwarsa Waya ce yanda Hajiyar take so ta yanke mu'amalarsa da Yaransa. Dole ya nisance su wannan ne kuma abinda yake ganin baze iya ba amma dai ze nemi mafita zuwa lokacin da komai ze daidai ta.

Tun ana gobe za'a sallame su tasa su Anty Sauda da wasu cousins Win su sukare gidan suka haWa musu kayansu. Duk wani abu da yake nata suka haWe shi guri guda daga kan kayan sawarta dana yara se kwanukan kitchen suma ba komai suka haWa ba iyakar abinda taje dashi gidan duk wasu abubuwa da Ahmad ya canza mata daga baya basu taSa shi ba. Kayan gadonta da kujeru ma basu taSa ba tunda ya canza mata komai haka kayan da Jafar ya jibga a gidan gefe suka tattare masa abinsa suka kwashe wanda zasu iya suka Kai gida suka bar mata wanda zasu Wan yi amfani dashi kwana biyu kafin su tafi gaba Waya.

Mama Balaraba ce ta gayawa Baba Al?ali Fatiman ta kwashe kayanta da sukaje da daddare bayan an sallamo su sun koma gida. A daren ya kira Alhaji Audu ya gaya masa shi kuma yaje har Waki ya samu Momy yake tambayar ta waya ce ayi haka.

"Ta yaya za'ayi na sani ni ina nan? Amma dai koma menene ai ba laifi tayi ba daman ai zaman takaba aka ce tayi kuma ta gama me zata cigaba da zama a gidan kuma tayi ana zuwa ana ci mata mutunchi ita da iyayenta kuma babu wanda ya Wauki mataki ?" Momyn ta bashi amsa ba tareda ta kalle shi ba. Yayi shiru ya rasa me zece mata se kawai ya fita, a tsakar gida ya tarar da Hajiya sun fito da Fatiyyah Hajiyar na cewa

"Dake dai Aisha shashasha ce in ba haka ba ai kamata yayi ta tura aje a tsaya mata idan ma ba zataje da kanta ba a tabbatar matsiyatan basu saci komai ba yanzu kuwa ai se iyakar abinda suka manta ba zasu Wauka a gidan nan ba"

"To dai akwatuna kawai naga ana fita dasu se kayaj wasan yaran kamar har kayan gadonta da kujeru bata Wauka ba ko se zata tafi gaba Waya tukunna oho" Fatiyyah ta bata amsa, Hajiyar ta buWe baki zata sake magana taga Alhajin a gabansu, ko a jikinta tace

"Yo a akwatin kika san me aka kwasa? Yanzu dakakkun shaddoji da boyel Win nan da Amadu yake sakawa ke hulunansa da takalmansa kaWai ta kwashe kuWi zatayi dasu kuma nasan yana aje kuWaWe a gida wannan ko tuni an gama kasafinsu, to dai duk wanda yaci da rabo na Allah ya isa tunda dai arzi?in nan uba na ne silar sa an kwaso mana irin tsiya suna wada?a a ciki".

Duk yanda fuskar take a haWe seda maganganun nata suka sakashi murmushin da be shirya ba, wato dagaske Binta uzuri ce taci kai biye mata ma Sata lokaci ne kawai mutum shima ze zama irinta. Wuce su yayi ya shiga Sangaren sa ta ?aramar ?ofa Fatiyyah nata sunkuyar da kai tana Soyewa a bayan Hajiya saboda shigar jikinta fitted gown ce ta lace da wayafin net ga kuma gulmar daya kamata ta kawo, Hajiyar ta harareta tana cewa

"Dallah fito ai gara yaji tun wuri in ma ze tura aje a tare su a caje komai gara, yi maza kije dai kici gaba da sakamun ido, ina dai Jafaru baya shiga harkar su?" Se tayi ?asa da murya tace

"Koda yake ai nasan ma aikin Malamin nan yaci, kedai na gode miki yar nan. Ni da nasan kina da malamai me zan zauna jira tunda shegiyar yarinyar can Saratu ta zubar mun da dafa'i ita kuma Turai ta haukace shikenan na tagayyara na rasa inda zan kama, ga can wani tsinannen Malami da Mw sunan Alhaji ya kaini gurinsa ba biyan bu?ata ?arshe ya zajamun masifa na rasa ?afata shi kuma ya zama wani sususu, Miliyan goma haka suka mun fashinta billahillazi da zan gane hanyar garin ba abinda ze hanani komawa se an biyani kuWi na dan dai ni ba asararriya bace amma dai Allah ya isa ban yafe ba".

Kamar Fatiyyah ta rusa kuka wannan terere na Hajiya har ina a tsakar gida take musu hansfiri dukda wai ta rage murya amma fa tar ake jinta dan Hajiyar badai murya ja kamar lasifi ?afa. Ita bata san ma tsautsayin daya sa har ta buWewa Hajiyar cikinta ta kaita gurin Malaminta na, ita da daman har yau kamar me shuka dusa ayyukan nata sun?i ci yanda take so to ai yanzu ta samu wadda zata kasa komai a faranti ya Sare gayyar ta ?arasa watsewa. Sum sum tayi ta fice daga gidan tunda ta lura aljanun zazzaga ne da Hajiyar tun bata kwance mata zani a tsakar gida ba tunda dai ita ta ?una bata shayin ?auri, a fili take komai nata nata sakayawa.

Da Alhaji ya koma falonsa Baba Bilki ya kira yace ta haWashi da Fatima, video call suke da Badar tana shayar da Ahmad Jr, ubansa Jafar yace ba za'a Soye masa suna ba manya su kirashi da Ahmad yara suce junior Baba Bilki ta mi?a mata wayar bayan da suka gaisa da Wan uwan nata.

"Alhaji ne" ta faWa tana mi?a mata wayar seta katse tata wayar bayan da tacewa Badar Win zata kirata sannan ta kara wayar kunnenta a sanyaye tayi sallama.

Cikin muryarsa me amo da izza Alhaji Audun ya amsa sallamar ta da gaisuwar data biyo baya. Tayi shiru tana jin kwarjinin da yakeyi mata yana ratsowa harta cikin wayar kafin taji yace

"Ki dakata da kwashe kayanki da kikeyi sannan idan Allah ya kaimu ranar Asabar zaku zo nan gidan gaba Waya zan ganku" ya faWa mata cikin sigar bata umarni" se ta amsa da
"Toh Alhaji"
"Ya Ahmad yana lafiya dai ko tareda sauran yan uwansa?" Ya sake tambayar ta, ta Waga kai kamar tana gabansa kafin tace

"Suna lafiya baki Waya"
"Allah yayi Albarka, se ha?uri kinji ita rayuwa haka take ba kowa ne yake samunta yanda yake so ba fatanmu dai Allah yasa muyi kyakykyawan ?arshe. Ita kuma Binta haka zakiyi ha?uri da halinta domin dai bamu san inda rana zata faWi ba" ya ?arasa da maganar da ta dabaibaye mata tunani daga nan sukayi sallama ya kashe ta mi?awa Baba Bilki wayarta ranta cike da tunanin akan me za'ace tayi ha?uri da halin Haajiyar Jafar? Rana kuma ai kowa yasan a yamma take faWuwa.
..



*MATAR MUTUM*
*NA MARYAM FAROUK (UMMU MAHEER*

*FIKRA WRITERS ASSOCIATION*

*LITTAFIN KUDI NE*
*PAY 500 A ASUSUN*
*7061838488*
*OPAY DIGITAL SERVICES*
*MARYAM FAROUK*
OR
*0709290797*
*ACCESS BANK*
*SE A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488*
*IDAN KATINE A DAUKI HOTONSA A TURA ZUWA LAMBAR SAMA VTU KUMA A TURA A 08142548705*

*Kuyi following dina a Arewabooks @Maryamfarouk01 inda zaku karanta wannan littafin tareda sauran littattafaina*
*NAGODE*

*BOOK 3*
*PAGE 26*

Baba Al?ali ya kira Baffan Fatima ya sanar dashi akan suna da zama ranar Asabar da yamma akan maganar rabon abinda Ahmad ya bari idan se samu zuwa ko kuma ya turo wanda za su wakilceta. Da farko Baffan cewa yayi Aa babu komai duk yanda sukayi daidai ne amma Baba Al?ali yace ai ba haka shari'a take ba, dole su gabatar da wanda ze wakilceta ayi komai a gaban sa gudun ?orafi daga baya.

Ranar Juma'a Alhaji Audu yaje gidan Baba Al?ali sun daWe suna tattauna maganganu dan haka yana barin gidan ya kira Alhaji Babannan yace yana so ya tara masa ?annensa maza washe gari da safe yana so ya zauna dasu.

"Kana ji ko, daman aka fara magana ka kwarkwance kace ka manta ke ake cewa na rantse da Allah se naci ubanka yau Alhaji. TaSarya zan samu na rotsa maka akai idan yaso ka manta komai da hujja. Tsabar iskanci se ana tsaka da maganar hankali se kayiwa mutane zuru idan an taSa ka kace me ake cewa kai ka manta to ka kuskura kamun hauka yau zan nuna maka a nono na ka tsotsa" Hajiya Binta ta faWa tana harar Alhaji Zakariyya.

Naziru yayi murmushi yace
"To wai Hajiya har se kin tsara mana yanda zamuyi? Kedai ki tsaya kisha kallo kawai da anzo daidai gaSar da zaki saka baki kawai ki shigo".

Hajiya ta dafa kafaWar sa tana cewa
"Idan duniya tamun zafi na tuna ina da kai se naji sanyi sanyi a raina Allah dai ya cigaba da she?a maka albarka kaji duk kitimurmurar da zasuyi sedai su gama amma billahillazi Aisha bata isa taci wannan kanti ba. Amadu yayi wahalar banza da wofi ya tara mana gwanjonsa za'ayi mu siye ya zama namu kawai, maza tashi kuje kar a fara bakwa gurin su kuma waWancan shegun da Yakubu da Faisal zasu zo su tarar dani. Yan iskan yara da ace nasan haka zasu mana mu cicciSa su su bulemu da ?ura ai wlh na barsu sunyi ta gararamba a gari babu madafa amma babu komai bari dai komai ya daidaita zan waiwayi kansu" ta ?arasa tana yin ?wafa.

Naziru da Zakariyya suka mi?e zasu fita saga falon tayi saurin zaro takardar data linke ta cusa kasan cinya ta mi?awa Nazirun tana cewa

"Ka ri?e a hannunka koda zakaji an lissafo wani abu da bamu san dashi ba" ya karSi takardar da kwafin kadarorin Ahmad ne da aka tattara Nazirun ya siye wani lauya abokin lauyan Ahmad ya samo masa, saboda tsabar Worawa kai jidali Hajiyar harta kasafta komai yanda rabo ze tashi yanda kasan suna da kasafi a ciki hankalinsu gaba Waya kuma ya tattara akan rabon gadon ?yashi da hassada fal ransu saboda abinda suke ganin ya tara da guminsa ba na sata irin nasu baz koda yake tace ?arya ne Amadu be kai tsaikon da za'ace ya mallaki abubuwan da aka rubuta ba, yaushe mq ya fara kasuwar? Munafunci ne ya shiga jikin Alhajin ya wawuri na wawura shi yasa zata tsaya kaida fata se an fitar musu da ha??in su ba'a isa ayi aringizo suna kallo suyi shiru ba. Idan ba rainin wayo ba ko Jafar da ake biya miliyoyi da kuWaWen ?asar waje be aje wani abin azo a gani ba se Ahmad.

Acan babban falon Alhaji Audu kuwa Yayansa maza kaf sun hallara se Alhaji Audun, Baba Al?ali, Alhaji Abdullahi.
Baba Al?ali ne ya buWe musu taro da Addu'a kafin Alhajin ya fara bayanin ma?asudin tarasu da yayi.

"Duk muna sane da cewar Wan uwanku ya rasu ya bar iyalinsa da juna biyu, wannan ne abinda ya jinkirta sauke masa nauyi na ?arshe wato rabon abinda ya bari ga magadansa. To Alhamdulillahi, yau kwana goma kenan data sauka dan haka muka ga kamatuwar ?arasa abinda yayi saura to amma rabon gadon bashi ne ainihin abinda ya saka na taraku a nan ba saboda nan cikinku kaf babu wanda yake da koda gadon silin allura cikin abinda ya bari.

Dalilina na kiran ku a nan shine na farko ina so inyi jan kunne da kuma gargaWi, ina so wannan ya zama karo na ?arshe da wani a cikinku ze sake sake shiga wata sabga ta rashin Wa'a har ya jona sunana a matsayinsa na Wana. Anyi na farko anyi na ?arshe idan har aka sake maimaitawa da hannuna zan mi?a koma wanene gurin hukuma na kuma bada umarnin zartar da ko wane irin hukunci akansa.

Tsayin shekaruna na nemi dukiyata da gumina ta hanyar halal, ban taSa saka kaina a wata gurSatacciyar hanya ba har zuwa yau duk masu sharri da bita da ?ulli sunyi sun barni ba ze yuwu ace rana tsaka na haifi Wan da ze janyo mun Sacin suna ya tarwatsamun shekarun dana kwasa ina gina kyakykyawan suna bisa ganganci da son ransa ba".

Tunda Alhajin ya fara magana Naziru yayi tsam kamar an tsoma rayayyar kaza a ruwan zafi, ya sadda kai ?asa ilahirin jama'ar falon kuma suka zura masa idanu se kace shi yake maganar ba Alhajin ba.

Alhaji Audun ya ci gaba da cewa
"Abu na biyu kuma babu wanda muka haWa sisi dashi gurin gina dukiyata balle yace rabonsa yake Wiba, masu yiwa dukiyata Wiban karan mahaukaciya ku shiga taitayinku domin ina gab da juyowa kanku" karaf idanunsa suka haWe dana Aminu da ya saki wani malalacin murmushi se yayi shiru ya kasa cigaba da magabar. Lkacin da aka titsiyeshi akan abinda bashi da masaniya akai ya dawo masa. Babu gargaWi babu komai aka umarceshi daya ajiye aiki amma ya godewa Allah daya bar gurin kuma gaskiya ta bayyana dukda daman ko a lokacin yasan Alhajin yasan bashi da lafi, da yake shi ba ?an so bane shiyasa ba'ayi masa uzuri tamkar su da suka kwashe shekaru suna tafka bada?ala sedai a bisu da gargaWi kawai.

Ba Aminu kaWai ba da yawansu taSe baki sukayi domin maganganun Alhajin babu ta inda suka shafe su. Abu ne tsakaninsa da yayan so shafaffu da mai. Hussaini daya fisu Wanye kai babu shakkar komai kai tsaye ya kalli Alhajin yace

"Ni daman nasan yaudarar mu kawai akayi da sunan Ahmad. Wlh dana san wannan soki burutsun za'ayiwa mutane babu abinda ze kawo ni gidan nan. To wai duk meye namu a cikin wannan maganganun naga abu ne daya shafi mutum da yayansa?
Sannan idan ma maganar ake so ayi a fito fili mana a kama suna bawai a ringa ?umbiya-?umbiya ba a nan waye besan Naziru na harkar ?waya ba su kuma waWancan kasurguman Sarayi? Ni indai iyakar wannan maganar ce wlh ina da abinyi can uwata tana jirana zan kaita Asibiti anzo an ajiye mutane ai ba se an sake nanata mana Yayan Binta sune yayan so a gidan nan ba abu ne da tunda aka haifemu muka taso muka san dashi".

"Yawwa ai idan bakayi haka ba Usaini ba'ace kilaki ce tayi cikinka ba" Hajiya Binta dake laSe a bakin ?aramar kofar falon tana jin duk abinda akeyi ta faWo musu tana huci,

"Meye haka Binta? Waya kiraki da zaki faWowa mutane babu izini babu komai?" Baba Al?ali ya faWa. Ta ri?e ?ugu kamar yarinya tace
"Har se an kirani? Kana zaune ai wannan tantirin tsinannen yaron me kama da Wan Allah bani yake zagina da yayana ai baka dakatar dashi ba se ni zaka tuhuma abinda ya shigo dani wato daman haWuwa kukayi kuyiwa yayana taron dangi to kunyi kaWan badai da raina ba wlh kai ko mutuwa nayi kurwata ba zatayi sanyin da har zata tsaya a ciwa jinina zarafi ba kai kuma dan uwarka ka faWa ka sake faWa yayana sune yayan so domin duk bazar da kuke rawa da ita albarkacinsu ce, kai badan ma ?addara ba har a haifeka a gidan nan kazo kana zubawa mutane rashin daraja? ?an hau" ta ?arasa tana jijjiga jiki.

Murmushi Hussainin yayi yana gyara hannun rigarsa yace
"Abu Waya nake so ki maimaita tsohuwa kalamanki na farko, kinga yanzu ?arfe Waya ne a jikinki ko? Na rantse da Allah se na miki dukan da kaf se an zare ?asusuwan jikinki an miki ciko da ?arafuna zaki san cikakken Wan hau ne ni na gaske"

Tsawa Alhajin ya buga masa yana nuna hanya yace
"Tashi ka fita tunda kai ba zaka taSa sanin ka girma kayi hankali irin na sauran yan uwanka ba"
"Ai dama Alaji yanzu zan tafi dan idan na zauna tsaf se lahanta mutum kuma na riga nayiwa uwata Al?awarin bazan dau?i maganar kowa a gidan nan ba har na fita to gara na kama gabana kafin zuciya ta Webe ni na karya wannan matar amma ko ba yau ba zamu sake haWewa tsohuwa" ya kwashe hularsa da wayarsa ya tsallakesu ya fice Hajiya ta shiga auna masa lita litar ashar bayan data tabbatar ya kai ?ofa base juya kanta ba".

"Kema ki fita daga nan kafin ranki ya Saci" Alhajin ya sake faWa yana kallon Bintan fuskarsa ta nuna Sacin ran da yake ciki Saro Saro. A duk sanda zama irin haka ya haWasu se Hussaini yayi abinda ya sosa masa zuciya sannan itama Binta tazo tana baje tata basirar rashin hankalin yanzu da ace akwai bare a cikinsu ai ba ?aramin zubar masa da mutunchi zasuyi a idon mutane ba.

"Babu inda zanje wlh se anyi komai akan ido na. Daman annamimanci aka shirya ai, to wlh bazan Wara daga nan ba se naji duk wata kitimurmura da aka zo da ita" Hajiya Bintan ta faWa tana zama akan kujera, Alhajin ya yun?ura ze sake mata magana Al?ali ya tare shi seya koma ya zauna yana haWiyar numfashi kamar wanda kunama ta harba, fuskar nan tayi kirtif kamar ta shanu. Seda aka kwashi kusan minti goma

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login