Showing 15001 words to 18000 words out of 467220 words

Chapter 6 - MATAR MUTUM COMPLETED 1-3 BY MARYAM FARUK.doc

23 Sep 2025

12196

Yakubu tasa dole ya tattara komai suka tafi masauki. Seda sukayi sallar Magriba da isha, ya rasa ma me ze ajiyewa Yakubun, ya kwaso Wasu yadika dinkakku kala biyu kowanne saiti uku a ajiye masa sannan ya sake dakko Shadda dinkin babbar riga shima guda biyu ya ajiye yana cewa
"Na Baballiya ne ba'a gama ba, daman Juma'ar nan nake cewa idan Malam Mudan ya shigo zan hada masa yayo mun gaba dasu kar kaya suyi mun yawa idan na tashi tahowa"

"Yanzu dai duk ka ajiye wadannan ka saurari maganar da nazo maka da ita" Yakubu ya fada yaba tattare kayan gefe, Audu ya zauna yana kallonsa se a sannan ma ya lura da cewar Yakubun bashida walwala dukda dai shi daman bame hayaniya bane sosai. A taqaice Yakubu ya bashi Labarin daya gigitashi jin cewar an sakawa Bara'atu rana da wani dan uwanta ya shiga share zuba dukda qofar Shagon a bude take ga iska na busowa amma Audu zufa yakeyi kansa ya shiga sarawa jin ze rasa Bara'atunsa macen daya gama kwallafa duk wani buri na duniya akanta. Shikadai yasan irin tanadin da yakeyi akan auransu shine yanzu Babanta zece ya bawa wani ita.

"Shiyasa kullum Dada take maka magana akan kasan me kake ciki saboda gudun haka, ban dama Inna Hajara tana tataka ai kasan tuni Bara'atu ta dade a daki Bilki da suke sa'anni kana gani da ciki yana tsaya mata ai tayi yaya biyu ko uku yanzu tunda dai ga Aisha nan da ciki Auran bana se ita kake so tayita zama har se sanda ka gama shirinka duk sa'annin ta sunyi Aure har an fara zundenta a gari " Yakubu ya fada. Audu dai bece masa komai ba haka suka kwanta amma fa be iya bacci ba, cikin daren ya hada yar jakarshi, Asubar fari suka dauki hanya dan yace baze tsaya ganganci ba dole yaje a san me ake ciki amma da ransa baze bari wani ya auri Bara'atu ba.

Bayan dogon tirka tirka da yayyensu daga qarshe suka yarda zasuje tambaya masa Auran Bara'atun, sunje da fari Babanta yaso yayi gardama akan shi ya rigada ya amshi maganar wani ya basu haquri suka taho gida Hashimu har yana Allashi qara ai gara haka, seya koma can Birnin da ya liqe yagani idan ze samu macen da zata aure shi babu wanda yasan saga inda yake kujifa. Kwana biyu tsakani Audu na kwance yana jinya tunda yaji cewar baza'a bashi Bara'atu ba sega dan aike daga gidansu akan Babanta yace ya turo yau a daura musu Aure ashe wai Rijiya ta durfafa dagaske zata fada idan ba'a fasa auranta da wancan ba, harta tsoma qafa daya babanta yaga dai dagaske bata hayyacinta shine yace ya janye amma fa sedai Audu ya turo yau a daura Aure dan muddin aka kai ranar daya saka da wancan tofa sedai ta mutu shine Innarya ta tashi Yayanta ta aikoshi, Audu najin batun ya miqe beyi wata wata ba ya kama hanyar Gona inda su Yakubu suke can suna gyaran kunya kamar wani yaro ya zube yana basu labarin abinda akace.

Daga qarshe dai Yaya Baba da wasu Abokanan wasansu biyu ne suka sake zuwa dan Hashimu yace ba inda zeje, an samu Baban Bara'atu ya haqurq da zancen daura aure ranar aka tsaida magana akan rana daya dana Yakubu. Da wannan farin ciki Audu ya koma Kano, dukda ba haka yaso ba. So yayi ace se yayi gida a Kano sannan zeyi aure dan biki yake so yayi irin wanda akeyi A Kano yayiwa Bara'atu lefw na yargata wanda ze zama abin tarihi a garinsu harda kewaye, amma yanzun ma bata baci ba, zeci gaba da qoqari kuma ko ba yanzu ba seya biya bashin duk abinda ya qudurci yi mata. A haka kwanakin Biki sukazo, a zatonsa za'a daura aurene kawai tunda kowa yasan bashida Mahalli yayi qoqari ya siyowa Bara'atu kayayyakin fitar Biki daga Kano aka dinko harda takalma da mayafai kala hudu yayi mata na yan birni. Ana saura kwana hudu daurin Aure ya tafi Bechi bayan yayi sallama da Abokanasa na kasuwa dana unguwa dukya shaida musu zeyi aure, amma biki ba yanzu ba suka hada masa gudummawa kuwa sosai har seda yayi mamaki, koda yake shidin ba daga baya ba gaskiya bashida rowa ko kadan, haka Biki, suna, ta'aziyya sedai idan beji ba suma duk sun masa Alqawarin idan biki ya tashi zasuje tunda yanzu abin yazo a qurarren lokaci basu shiryi tafiyar ba.

Ranar Juma'a aka daura Auran, na Yakubu aka fara daurowa da safe a can Rigarsu Balaraba suka dungumo da Amarya da yan uwanta, se bayan sallar Juma'a aka daura na Audu da Bara'atu. Murna kam ba'a cewa komai a gurin Dada da tasha kwalliya cikin kayan da Audu ya dinka mata, haka qannensa Bilki da Aisha sun sha Anko Baballiya kuwa shaddarsa iri daya data angwaye wanda dama Audu ya dinka musu da niyyar suyi fitar bikin Yakubu se gashi abu yazo a daidai. Qarfe tara suna can Majalisa da Abokanai ana ta shaqiyanci sega Baballiya da gudu yake fada musu wai an Kawo Amaryar Yaya Audu. Kowa yayi mamaki dan ko jiya da yaje gurinta seda suka sakeyin maganar tace masa Innarta tace se daga baya zata tare tunda abin yazo babu shiri Babanta kuwa Magriba nayi ya tada ballin se an kaita, an ce masa babu daki yace ta rakuba a na Babarsa da ya san be shirya auran ba yayi haka yan uwa suka rakota ita kam ko a jikinta dan ko cikin Rumbub gidan aka ce ta zauna shiga zatayi tunda dai burinta ya cika ta Auri Audu.

A dakin sa aka sauketa da qawayenta da zasu kwana, daren ranar Audu tunanin yanda zeyi kawai yake, da yasan za'ayi haka da ya ququta ko babu dabe itama an tayar mata da daki ko ciki dayane, haka dai gari ya waye, da hantsi yan uwan Balaraba suka gama mata jere tsaf irin na yar gata harda Kumbo nan suka fara shirin tafiya bayan sun qara damqa Amarta a hannun yan uwan Yakubu. Daga bangaren Bara'atu dai babu wanda yazo se qawayenta da suka kwana.

A can gidansu ana ta taqaddama tsakanin Babansu da Innarta akan yace ko tabarma baze kai mata ba tunda bata bi abinda yake so ba, ita kuma ta rantse se yayi, da yasan haka ne seya bata lokaci ita da take son auran zatayiwa yarta komai amma yanzu banda kwanuka babu abinda ta tanada dan haka dole ya fito da kayan gado danbaze barwa yarta abin gori ba bayan ba rasa abinda zeyi mata yayi ba gashi tun rana bata daga ba labarin jeran da akeyiwa Balaraba ya fara bazuwa a gari dan itama Babanta Attajirine a rugarsu kuma itace Auta a mata dan haka sun mata bajinta.

Hayaniyarsu har dakin Ilu Abokin Audu da suka kwana a gurinsa maqota suke dasu Bara'atun kuma dakinsa jingibe yake da dakin Soron su Bara'atu inda Innar tata da Baba suka shiga wai suna sirri saboda yan biki dake ciki se gashi Audu yaji komai, sulalewa yayi ya tafi cikin garin Kumbotso saboda yafi masa kusa akan yace ze tafi Kano, yasan gurin lokaci lokaci yana zuwa dan har Aboki yake dashi kai tsaye gurinsa ya tafi bayan sun gaisa be bata lokaci ba ya zayyane masa abinda yake tafe dashi na batun kayan daki saboda garinsu Babu Kafinta meyin kayan katako, gadon qarfe kuma a gurinsa shi da yake zaune a birni yake ganin kayan gado da akeyi na Alfarma ya fitar masa yayi.

Nura ya kaishi gurin wani Kafinta da ake ji dashi a Kumbotso dan a Kano ya koyo aiki wasu kayan ma daga can yake dakkowa ya kawo. Ya numa masa wani Gado Lamba 1 da Kobud dinsa me biyu ta yan gayu dan harda mudubi a jikin murafenta ga kuma mudubi shima me durowa uku a jiki kayan sunyi kyau gasu Ruwan Hoda irin kalar da Bara'atu take so sedai kudin da aka saka musu a yanayin da yake ciki sun masa yawa ga Katifa da ze siya da pillo, aka tirza aka tisa dakyar dai kaya suka siyu, shima seda Nura yayi masa ciko daga baya zasu warware tunda suna haduwa A Kano, aka loda masa su a A kori kura da dundumemiyar katifa da pillow biyu harda Abin shimfida dana rufa ya kama hanyar gida.

Sanda ya dawo yamma tayi rana na gabda faduwa, a waje ya bar masu mota ya shiga ciki nan ya tarar da Dada da yan uwanta da basu wuce ba suna ta kiciniyar kwashe yan kayayyakinta ana shigar dasu dakinsa nasa kuma suna waje da alama dakinta za'a mayar dasu daman ba wani shirgi ne dashi ba Gadon qarfe ne da wata Katifa da yake ta saka ranar canzata tunda ba kullum yake kwana a kai ba se yayi ta mantawa se akwatinsa guda daya. Kunya ta kamashi yanda aka faka kayan a gefe, kenan Dada dakinta zata basu kuma wannan Gadon za'a sakawa Bara'atu

"Yawwa ga Audu" Matar Yayan Dada da basu yada zumunchi ba ta fada dan tun safe ake nemansa an rasa shi ga babu waya bare aji inda ya tafi. Dada ta yafa gyale ta yafice shi suka yi soro, Goggo Fadi, Maryo da sauran Maqwafta yan tsogumi da suka baza tabarma, sun gama kallon dakin Balaraba suka fito aka kafa gulmar ana jira aga me za'a sakawa Bara'atu ita kuma,
"Koda yake ina dakin ma?" Fadar Goggo Fadi, Maryo ta karkace baki tace
"Dukdai qaryar Birnin ta qare, ayita zuwa ana burga a bikin jama'a ga nashi ya tashi ko dakin da za'a ajiye Amarya babu idan da gaske da kudin ai daga tsaida rana yaci a dora ginin Bulon sumunti ma bana qasa ba" suka tafa da matar Hashimu dake kusa da ita.

Dada kuwa suna zuwa zaure tace
"Ina ka tafi Audu bayan kasan halin da ake ciki babu inda dan uwanka bw zaga a garin nan ba amma ba'a ganka ba Jama'a har ana cewa ka gudu". Dariya ta kwace masa yace
"Na gudu kuma Dada naje ina kamar wani mara gaskiya?"

"Oho dai duk ba wannan ba, Hasiya tazo ta gaya mun Baban Bara'atu yace bazeyi mata kayan daki ba, da ace mun san da tariyar nan da tuntuni mun fara shiri amma yanzun ma se ayi amfani da abinda Allah ya hore, na bar muku dakina tunda kaga yafi girma ni se na koma na Malam, Babana kuma ya shiga cikinsu Idrisa (Yaran Yaya Baba da suke zama a gidan) kafin muga abinda Allah zeyi, idan an kwana biyu filin can na gefe seka shigo mata dashi ayi bandaki da gurin girki irin na Yayanka kaga shikenan a sannu Allah ze hore duk kuyi muhalli irin wanda kuke buri, wancan gadon naka ma gaskiya Audu ba'a bawa Amarya ba ga Katifa duk Babana yaci qaniyarta idan da sarari ko katifa ce ka siyo da ledar daki a shimfida mata".

"mma Dada da baki fita daga dakinki ba wancan dinma ya isa ta lallaba kafin muga abinda Allah zeyi" Audu ya fada, Dada ta juya tana cewa
"Kaje dai muga ko katifar da Ledar zasu samu" ya tsayar da ita yana cewa
"Shaf na manta da Ledar wlh sedai ko Bilki taje yanzu inda za'a samu, leqa kiga ga kaya nan dai na samu dukda dai nasan basu kai yanda akeyi ba".

Dada ta leqa, baki ta saki ganin kaya tuni kuma yara da matan Unguwa da sukazo shiga gidan suka baibaye motar ana kallo dan ba'a taba ganin irinsu a garin ba.
"Audu, Kano kaje har ka dawo wannan kaya haka?" Dada ta fada cikin mamaki, Audu yayi murmushi yace
"A turo Bilkin ta samo Ledar tunda ita akw fara shimfidawa ko anjima zan miki bayani.

Dada ta koma ciki bakinta a washe yaqi rufuwa ta tura masa Bilki. Gidanta ta tafi ta dakko ledar data siya take shirin canza ta dakinta bata rigada ta shimfida ba dama ta bari se an gama hidimar Biki nana da nan aka hadawa Amarya daki ga gado na Alfarma kamar wani gidan zoo haka mata keta leqawa masu gyaran daki na korarsu dan sun hanasu yin aikinsu yanda ya kamata tuni kuma labari yakai wa Innar Bara'atu, ta fashe da kuka tana cewa

"Allah na gode maka daka nunawa masu gulma da munafurci qarshensu" tun safen suke qullawa da warewa da yan uwanta akan yanda za'ayi, ta hada dan abinda ya samu, Gadon katako taso tayiwa Bara'atu dan ance Amaryar Yakubu ma shi aka mata amma abinda suka hada baze isa ba kuma wanda za'a tasa ya tafi Kumbotso a yammar shine aiki har sun saddaqar a dauki na qarfen anje shima me siyarwar wai baya nan abin duniya duk ya mata yawa sega wannan labarin farin cikin dukda tasan wata sabuwar gulmar za'a samu ace Miji ne yayi mata ko babu komai sabon salo ne dan babu yarda Miji yaso haka a garin har yayi mata kayan daki.
https://chat.whatsapp.com/Hi7n2ddpUxZ24e1tJyREqZ

*Assalamualaikum, My name is Maryam hassan, I sell Laces range from 35k to 250k beautiful n classic designs, kids clothes , materials, shadda gezner men materials range from 30k to 120k , women veils , 8k,12k,15k,25k,all available muna bada sari muna maraba da masu siyan daya, muna hada na lefe da kayan barka , location Kano, FREE DELIVERY NATION WIDE BI MA'ANA FA DILIBIRI KYAUTA A TSADAR KUDIN MOTAR NAN YAR UWA ME KIKE JIRA? MAZA KI TUNTUBE MU
*MATAR MUTUM*
*NA MARYAM FAROUK (UMMU MAHEER*

*MARUBUCIYAR*
*WATA KISHIYAR*
*RUBUTACCIYAR QADDARAH*
*HALIN KISHI*

*FIKRA WRITERS ASSOCIATION*

*LITTAFIN KUDI NE*
*PAY 400 (PROMO PRICE BAYAN KAMMALA FREE PAGES ZE KOMA 500) A ASUSUN*
*7061838488*
*OPAY DIGITAL SERVICES*
*MARYAM FAROUK*
OR
*0709290797*
*ACCESS BANK*
*SE A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488*
*IDAN KATINE A DAUKI HOTONSA A TURA ZUWA LAMBAR SAMA VTU KUMA A TURA A 08142548705*
*NAGODE*

*FREE PAGE 5*

Kafin dare dakin Amarya Bara'atu ya dauki haske bakin yan gulma yayi muqus qiri qiri Goggo Fadi ta kasa boye baqin ciki da wannan abu ta ringa yada magana wai Dada tadai tsananta binciken inda Audu yake samunkudi haka ya za'ayi ace daga fita ya dawo da irin kayan nan waya sani ma ko wasu ya bige ya dakko? Ita dai Dada tun tana mamakin lamarinta harta dena, a zamansu idan aka ce mata wata rana Goggo Fadin zata zama yanda take a yanzu qaryatawa zatayi se gashi da ido ta take gani bawai fada mata akayi ba.

Innar Bara'atu ta aiko da kwanuka da tayi tanadi aka jere masu reras tun daga qasa har sama. Tana can bagaren Balaraba tun safe Dada tace suje can da qawayenta suyi wanka suka karya nan suka hade da qawayen Balaraba ana ta raha har dare kafin suka fara shirin tarar Angwaye. A bangaren Balaraban tayi wanka tsaf ta shirya cikin daya daga kayan daya dinko mata daga Kano, Balaraba ta bata Humra ta shafa dan ita dai babu shiri aka hankadota, suna zaune Aisha tazo tace au koma can an gama gyara mata daki suka bar Balaraba da nata qawayen can kuwa se santin daki sukeyi qaunar Audu ta sake linkuwa a zuciyarta ko banza ya fitar da ita kunya ya mata abinda tasan ko Baffabta bazeyi mata kamarsa ba.

Se qarfe Goma Aka rako angwaye, Yakubu aka fara rakawa tunda shine babba kuna duk Abokanan nasu daya, bayan barkwanci da abinda aka saba akayi siyan baki sukayi musu yar nasiha da tunasarwa akan aure da qalubalen dake ciki dan gaba daya Abokanan da sukayo rakiya su bakwai mutum daya ne mara aure wasu da yayayensu dan haka sun san yanda lamarin yake nan akayi addu'a suka sallami yammata wadanda zasu tafi gidan Fadima Amaryar da su Balaraban suka kawo garin harta hadu da Yakubu. Daga nan aka raka Audu, basu jima ba nan ma akayi addu'a kowa ya watse suka raka Abokanan qofar gida kamin suka koma ciki, Yakubu ya shige bangarensu bayan y??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????ayiwa Audu sallama ya sakace qofa, Audu ya tsaya kawai yana tunani, duk yanda yaci burin ranar auransa gashi bata zo masa a yanda yake mafarki ba.

Lissafi yake yanzu Yakubu Asirinsu a rufe suna da komai a bangarensu babu wanda ze san me suke ciki amma shifa? Rufin asirin ma bandakin da yake kusa da ace har yanzu da tsohon suke Amfani da tareren yayi yawa. Haka ya shiga daki jiki babu karsashi sosai ya saka a ransa bazeyi komai ba har se randa ya samu yanda yake so dangane da muhalli. Bara'atu ko harta fara gyangyadi akan sabuwar Katifa daman jiya ba wani baccin kirki sukayi ba kuma sun tashi da wurwuri motsinsa ya farkar da ita ta shiga jan mayafi tana boye fuska. Ya bude musu Kazar da suka shigo da ita dakyar ta iya ci saboda Yunwar da takeji taci kadan tasha ruwa tace ta qoshi.

Qofa yaji ana kwankwasawa, seda ya tambayi waye yaji muryar Inna Hasiya, ya bude ta miqo masa wani qaton Flask din ruwan zafi wanda ya siyawa Dada a Kano guda biyu saboda lokacin sanyi dukkansu cike da ruwa tana cewa
"Da akwai na sirki nan cikin bambu", ta sake miqo masa wani kantamemen baho irin na wankan Jego tana cewa "Allah ya tashe mu lafiya".

Kamar wani munafuki haka ya tattara bahon da fulasan gefe ya ajiye ya kalli Bara'atu data takure a gefen gado kamar jinjirar kyanwa yace
"Kiyi shiri ki kwanta dare yayi"
Da "toh" ta amsa masa ta miqe amma duk ta diririce ta rasa abinyi fahimtar kamar kunya takeji yasa ya fita ya tsaya daga qofar dakin, yana fita ta bude jakar da aka sako mata yan kayanta. Doguwar rigar yadi me laushi ta ciro da qaramin Hijabi. A gurguje ta shirya, ta ninke wanda ta cire kafin ta haye gado ta duqunqune kamar me bacci daidai nan Audu ya shiga dakin. Shirin baccin shima yayi, ya hau kan gadon yanajin wani banbara kwai wai yau shine gado daya da mace.

Dukda yanda yayiwa kansa Alqawarin baze tabata ba har se sunyi kebantaccen guri kamar nasu Yakubu amma ya kasa, cikin tattali da tsantsar So ya mayar da ita tasa, a cikin daren ya taimaka mata ta gyara jikinta kamar yar baby haka ta shige bahon ta gasa jikinta tsaf kamar

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login