Showing 324001 words to 327000 words out of 467220 words

Chapter 109 - MATAR MUTUM COMPLETED 1-3 BY MARYAM FARUK.doc

23 Sep 2025

12102

ba'a kyauta masa ba, me yasa za'a ce kar a gaya masa ma? Ko so akeyi sedai kawai a kirashi ace yazo Yah Ahmad ya mutu" Salim ya faWa, Dr Hassan ya girgiza kai ba tareda yace komai ba, Fatima dai tana jinsu bata tanka ba har suka isa Asibitin ita da Salim suka zauna a gurin zaman jira na Sangaren matsananciyar kulawa (ICU) Dr Hassan kuma ya tafi gurin likitan da yake kula da case Win Ahmad saboda sa?on daya samu kan cewar yana nemansa.

A main reception Jafar ya tsaya bayan daya shiga, ya tsayawa matashiyar budurwar dake zaune gaban computer akai yana muzurai ita kuwa se murmushi take doka masa tana tambayar sa meyake da bu?ata, da?yar ya iya ambato sunan Ahmad Bechi ya shaida mata shi yazo gani. Seda tayi yan danne dannenta a kwanfuta kafin ta kalleshi tana murmushi tace

"Kayi ha?uri babu damar ganin marasa lafiya da suke a Wakin matsananciyar kulawa".

Ya zura mata ido, cikin rashin fahimta yace mata
"Ahmad Win ne a Wakin matsananciyar kulawa? Meya same shi?"

Kallon ?alau kake kuwa tayi masa kafin ta mayar da kai kawai taci gaba da abinda takeyi ba tareda ta sake bashi amsa ba, harya buWe baki ze saka mata magana se kuma yayi shiru, kujera ya nema ya zauna be daWe ba ya hango Dr Hassan yana fitowa daga cikin Elevator harya mi?e ze nufeshi se kuma ya fasa ya koma ya zauna. Yana kallonsa yaje gurin matar daya baro sukayi maganganu tayi danne danne a kwamfuta ta bashi wata takadda kafin ya wuce da sauri ya sake shiga elevator, gilashi ne me garai garai dan haka ya bishi da ido yana irga hawan benen a hawa na huWu ya fita sa sauri ya tashi yabi bayansa, jikin allon da aka rubuta taswirar guraren da suke a hawan ya duba, zuciyarsa tafi aminta da inda Wakuna na musamman suke dan haka yabi gurin da kibiya tayi alama.
??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????
Daga mesa ya hango Fatima tsugunne a ?ofar wani Waki Salim kuma na le?en cikin Wakin ta wundo. Kallo Waya yayi mata gabansa ya yanke ya faWi a hankali ?afafunsa sukayi sanyi la?was har suka fara gardamar Waukar sa seda ya dafe bango kafin ya iya tsayuwa sosai. Yana tsayen ya hango nurses guda biyu tareda likita suka fito fuskar likitan Wauka da murmushin ya?e ya bubbuga kafaWar Salim daya fi kusa dashi kafin suka wuce.

Yana kallonsu suka shiga, Fatima ce a gaba sannan Salim se Dr Hassan a hankali yabi bayansu kamar kazar da aka tsoma a mai yana shiga cikin Wakin idonsa yayi masa mummunan gani. Ahmad na kwance akan gado tun daga goshinsa zuwa ?irjinsa tareda wasu Sangare na hannayensa jone da wayoyin da aka ma?ala jikin tarin kwamfutocin da suke Wakin ga bututun sha?ar iskar osijin da alama ba'a daWe da cire masa shi ba. Idanunsa a buWe yana kallon ?ofa, ya saki murmushi ganin Fatiman ta shiga kafin ya motsa hannunsa da?yar ya mi?a mata ta ?arasa a hankali ta kama hannun tana kallonsa.

"Jafar" Ahmad ya faWa a hankali yana kallon ?ofa, duk suka juya, Jafar Win na tsaye tamkar an dasa Shi ya kasa gaba ya kasa baya, mi?a masa hannu Ahmad yayi kamar wanda ya janyo da mayan ?arfe haka ya taho, Fatima ta janye masa ganin yana neman faWa mata tamkar ma be lura da tsayuwarta a gurin ba. Seda ya isa dab da Ahmad Win, ya ri?e hannunsa daya dawo kamar na yara saboda siranta ya ringa kallonsa daga fuska zuwa ?afafunsa kafin ya buWe baki da niyyar magana sedai kuka ya rigayi maganar fitowa.

*MATAR MUTUM*
*NA MARYAM FAROUK (UMMU MAHEER*

*FIKRA WRITERS ASSOCIATION*

*LITTAFIN KUDI NE*
*PAY 500 A ASUSUN*
*7061838488*
*OPAY DIGITAL SERVICES*
*MARYAM FAROUK*
OR
*0709290797*
*ACCESS BANK*
*SE A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488*
*IDAN KATINE A DAUKI HOTONSA A TURA ZUWA LAMBAR SAMA VTU KUMA A TURA A 08142548705*

*Kuyi following dina a Arewabooks @Maryamfarouk01 inda zaku karanta wannan littafin tareda sauran littattafaina*
*NAGODE*

*BOOK 3*
*PAGE 22*



A cikin ?asa da kwanaki biyu Jafar yabi sahun Fatima gurin zama wani abin tausayi, dukda jarumta irin ta maza da yake gwadawa amma jiki da zuciyarsa sun gagara bashi haWin kai yanda kowa yayi zaton zeyi masifa yayi bala'in me yasa aka Soye masa ciwon Ahmad se gashi ko tari beyi ba, to yayi faWa akan me bayan aikin gama ya gama? Abinda kawai yake a gabansa samuwar lafiyar Ahmad ce.

Dukda tsarin Asibitin na ba'a barin me jinya kafiya da bala'in nacin Jafar tasa tilas suka Waga masa ?afa, shi yake kwana dashi sauran zasu wuni idan dare yayi su tafi gidan Jafar na nan London daya saka aka buWe musu. Villa ce me katafarun Wakuna guda uku se falo da wasu gurare na sha?atawa da kuma gurin motsa jiki harda ?aramin filin atisayen ?wallo. Da ace lafiya ce ta kaisu da babu abinda ze hanasu shagala da ?awatuwar gidan amma yanayin da suke ciki ya saka gadajen bacci kaWai suke iya ganewa a cikin gidan.

Kwanansu biyar da zuwa jikin Ahmad yayi sau?i sosai dan har an rage masa tarin wayoyin dake zagaye dashi yana kuma iya tashi da kansa har sallah yayi a tsaye har yaci shinkafa abarda ya kusan wata guda be WanWana ta ba tun ma jikin be kai haka lalacewa ba abu me ruwa ruwa kawai yake iyaci ya zauna lafiya idan ba haka ba ciwon cikin ya dirar masa.

Farin ciki da murna a gurin mutanen gida ba'a magana ranar da aka tura musu video sa yana cin abincin har sukayi video call da wasu daga cikinsu, abincin sadakar da akeyi ranar seda aka ninninkashi, sannan suka sake rarraba sauka da barar addu'oi a masallatai.

Duk budurin da akeyi a gidan seka rantse Alhaji Audu be sani ba saboda tun bayan tafiyarsu Ahmad ya koma kamarwata Amarya kullum yana Waki sallah kaWai take fitar dashi da fari ma mutanen gidan sun Wauka ko tafiya yayi shima seda akace ana ganinsa a masallaci tukunna. Ranar da Baba Al?ali ya kirashi yace masa yanzu sukayi video call da Ahmad jikinsa da sau?i dan har yana iya tsayuwa yayi sallah da ?afafunsa, suna gama maganar ya kira wani yaronsa da yake a kamfaninsu na alawoyi, umarni ya bashi akan a fitar da cakulatin data fi kowacce daWi a bi unguwanni suyi ta rabawa ?ananun yara sannan ya tashi ya shige Soyayyiyar ma'ajiyarsa. KuWe ya Wiba bandiran da besan adadinsu ba. Shida Amintaccen direbansa ya fita, magriba tayi har duhu ya fara rufawa.

Lunguna suka ringa bi gidaje ya aika direban yayi sallama gida kawai ko babba ko yaro duk wanda ya fito ya bashi yace gashi inji wani bawan Allah, yana da bu?ata a gurin Allah su taya shi da addu'a Allah ya amsa masa.

Kafin wayewar gari labari ya bazu ko ina wani mutum yayi rabon kuWaWe cikin dare. Har gidajen radio mutane suka ringa shiga suna Addu'oi da fatan Alkhairi. Wasu mutanen da bakinsu baya taSa faWar abin kirki se na tsiya kuma suka ringa cewa ?ila dan yankan kai ne.

Idan ba haka ba waye zeyi rabon kuWaWe haka a marrar nan kamar besan ciwonsu ba? Kawai duk wanda yaci kuWin nan to ya fara shirin zuwan mutuwar sa dan ya rigada ya amshi sadakin kansa.

Haka dai akayi ta yamaWiWi ana surutai shidai Alhaji be fasa rabon kuWin ba Almajirai da miskinai haka Alkhairi ya ringa tarar dasu wasu a yawon barar su wasu suna zaune har kuma sannan Allah besa wani yasan daga inda kuWin nan suke zuwa ba.

Sanda Ahmad ya cika sati cikin kulawar likitocin da suka san ?ima da mutuncin ?an Adam. Sosai jikinsa ya fara karSar duk wani magani da ake bashi har likitocin suka ringa mamaki matu?a domin a yanda suka karSe shi babu wanda cikinsu yayi tsammanin se ?ara cikakkiyar awa ashirin da huWu a raye se gashi har yaci sati guda.

Cigaban da aka samu ya saka Dr shirin komawa gida kamar yanda Ahmad ya bu?ata.
"Ya kamata ka koma gida haka Yaya, ku tafi tareda Salim ma ga Fatima ga Jafar nasan duk wani abu da nake da bu?ata zasuyi mun" Ahmad Win ya faWa.

Jafar ya kalli Fatima da tun zuwansa tsayin kwana shida sau Waya sukayi magana seya kalli Ahmad Win yace

"Itama ya kamata ta tafi gida, zamanta bashi da wani muhimmanci a nan"

"Har a gurin Allah a yanzu Ahmad bashida wani sirrin daya fini, a Sangaren abinda ya shafi kulawa dashi ko iyayen da suka haifeshi a yanzu se bana nan layi ze tsallaka kansu ballantana kai karan kaWa miya" ta bashi amsa ba tareda ta ko kalli Sangaren da yake ba.

Shiru yayi ya zuba mata idanunsa da suka canza launi suka koma ciki saboda azabar damuwar dake ransa,

"Ya isa haka duk kuyi ha?uri. Kamar yanda Ahmad yace ni zan tafi amma ina ganin Salim ya zauna tareda ku hakan ze fi" Dr Hassan ya kashe maganar ya kuma hana Jafar amayar da maganganun daya gama tattarowa ze watsa mata.

A daren ranar Dr Hassan da Salim da Ahmad ya kafe kan seya tafi suka siyi tikiti, da akwai jirgi da ze tafi Nageria jibi Juma'a da safe shi zasu bi dukda da sukayi magana da Baba Al?ali be so tahowar tasu ba, a cewarsa su zauna tunda dai jikin Ahmad Win yana samun sau?i su jira har Allah yasa a sallameshi se su taho baki Waya amma kuma tunda Ahmad ya kafe dole aka ha?ura dan lallabashi akeyi komai ya faWa a yanzu ya zauna kawai.

Daren Alhamis gaba Wayan su a Asibitin suka kwana, raba dare sukayi suna hira duk yanda likitan da yake da alhakin kulawa da Ahmad ba yanda beyi ba akan su barshi yayi bacci amma basuji ba har seda akayi sallar Asuba sannan sukayi masa sallama suka tafi shi kuma akayi masa allurar bacci.

Jafar ne ya kaisu filin jirgi tareda Fatima, seda fasinjoji suka fara shiga jirgin kafin suka baro Airport Win shida ita. Ganin ya nufi hanyar gida yasa murya a ciki tace masa
"Asibiti zaka mayar dani"
"Daga yau sau Waya zaki ringa zuwa Asibiti, a gida zaki ringa zama ki kula da abinda yake cikinki tunda ke baki damu da taki lafiyar ba shi ina sonsa ba kuma zan zuba ido ki salwantar dashi ba kamar yanda kikayi wasa da lafiyar Yayana" ya bata amsa ba tareda ya kalli shashen da take zaune ba yana kuma jin idanunta a jikinsa da alamun kallonsa takeyi ta kuma gaza samun kalmomin da zatayi amfani dasu gurin bashi amsa, har suka isa gidan kuma bata iya ce masa komai ba tamkar ma ya rufe mata baki da kwaWo harya gama abinda zeyi tana zaune a falo ya fita ya kulle kofar bata motsa ba.

Marar tace take mata ciwo dauriya kawai takeyi duka a jiya anyi mata scanning kuma babu wata gagarumar matsala a tattare da ita kawai dai sunce cikin ya koma baya, a wata na takwas yake a lissafinta na asali amma a bincikensu watanni biyar ya nuna. Ita harta cire rai da cikin ma dan bata zaton koda Allah ze nufa ta haifeshi yazo da rai, waya sani ko kuma abokin tata tafiyar ne ?ila ma ita zata riga Ahmad Win mutuwa.

Wanka tayi tasha shayi sannan ta kwanta dan tana da bu?atar hutu dagaske, bacci tayi irin wanda ta daWe batayi kamarsa ba, tun bakwai na safe ba ita ta farka ba se karfe uku har da mintinuna na yammaci.

Jikinta kamar wadda akayiwa dukan tsiya haka ta tashi ta zauna tana yamutsa fuska. Wayarta dake gefenta tayi kara ta mi?a hannu ta Wakko. Umman tace take kira, ta Waga cikin sanyi suka gaisa tana tambayarta jikin Ahmad, basu ja maganar ba ta bata uzurin zatayi sallah. Wanka ta farayi haWi da alwala ta gabatar da sallolinta.

A falon ta tarar da abinci soyayyen dankali da farin ?wai se ruwan shayi sune kaWai abinda take iyaci tun zuwansu, kaWan ta tsakura taci, da hannu ta irga awanni zuwa lokacin tasan yaci ace su Salim sun isa gida dan haka ta shiga laluben lambar Momy se sannan ta lura da ta kirata lokacin tana bacci dan haka tabi bayan kiran. Sun Wan jima suna magana da Momyn akan jikin Ahmad, hankalin Momy ya?i kwanciya tace gani takeyi kamar sun faWin yaji sau?i ne saboda su kwantar mata da hankali. Su Salim ma har sun sauka suna Lagas jirgin ?arfe tara na dare zasu bi zuwa Kanon.

Sake kwantar mata da hankali Fatiman tana bata tabbacin duk abinda ake gaya mata gaskiya ne, jikin Ahmad yayi sau?i sosai kuma yana karSar duk wani magani da ake bashi yanzu saSanin sanda suka zo. Sun dau?i kusan awa guda suna magana kafin sukayi sallama se lokacin ta lura da yar farar takadda a ?asan farantin kayan abinci ta Wauka ta duba, gajeran rubutu ne

"Idan kin tashi ki nemi tasi ta kaiki Asibiti" abinda aka rubuta kenan ta tabbatar kuma Jafar ne.

Hijabi saka ta Webi abubuwan da zata iya nema dan yau ko dame yake tafe be isa ya hanata kwana da Mijinta a Asibitin ba, daman nauyin Dr Hassan yasa takeyin shiru duk yabi ya kankane komai amma tunda sun tafi zata nuna masa iyakarsa yau.

******************
A can Asibiti kuwa bayan da Jafar ya ajiyeta ya koma ya iske Ahmad yana bacci, zama yayi a bakin gadon yana kallonsa yana goge ?walla. Har sannan ya lasa yarda dagaske abubuwa suke faruwa, ta ya akayi tsayin lokaci Yah Ahmad na tareda ciwo amma be sani ba har ya tsayin yaushe kenan Yah Ahmad ya fara Soye masa damuwarsa kenan?

Wayarsa dake cikin Aljihunsa ta shiga ?ara ya cirota da sauri dan ya manta be sakata a silent ba yanda ya saba duk sanda yake cikin Asibitin. Fatiyyah ce ta kirashi, tunda ya taho seda ya kwana uku kafin ta kirawoshi shima badan tana so taji lafiyarsa ko inda yaje ba, Aa bu?ata ce da ita ta tafiya Nigeria biki kuma tunda yayi mata abinda take so Win bata kuma neman sa ba se yanzun

"Ashe Ahmad ne bashida lafiya" ta faWa bayan yar gajeriyar gaisuwar ya kake da tayi masa se ya bata amsa da "Eh" kawai.
"Kuma shine ba zaka gayamun inda ka tafi ba? Yanzun ma fa daga zuwana Dady yake tambaya na jikinsa nace ni banma san bashida lafiya ba, kawai fa suka rufeni da faWa shida Momy to ta yaya zan sani bayan babu wanda ya kirani ya faWan mun?
Dama ka kira Dady tun wuri ka gaya masa da gaske ban sani ba ya dena ganin laifina yana zagina" Fatiyyan ta faWa cikin isa isa.

Zare wayar yayi daga kunnensa ya duba se sannan ya lura da lambarta ta Najeriya ta kirashi ya mayar da wayar yana cewa
"Indai ba wani abu me muhimmanci zaki gaya mun ha karki ?ara kiran wayata nan kusa ki bari har sena nemeki da kaina" kafin tace wani abu ya latse wayar gaba Waya ya kasheta.

Daga kwancen da Ahmad yake yana kallonsa tun shigarsa Wakin ya farka amma ya gagara motsa jikinsa balle ya iya magana ji jinsa yakeyi kamar wanda aka WaWWaure da igiyoyi a hankali kuma komai ya fara sakinsa harya iya motsa bakinsa yace masa
"Wai Jafar me yake damunka? Kai ka nemi auran yarinyar nan da kanka ba dole akayi maka ba amma tunda ka aureta babu wata mu'amala da take nuna so ko sha?uwa a tsakaninku, yanzu da take ita kaWai baka yi mata adalci ba inaga kuma ka haWa ta da wadda kake so?"

Kallon Ahmad din yayi kamar ba zece masa komai ba se kuma yaja iska ya fesar yace
"Tunda na rabubda ita na rasa komai rayuwata ta kasa daidaita tamkar ta tafi da duk wata nutsuwa da farin cikin da yake tattare da rayuwata"

"Kaci gaba da ha?uri lokaci ya kusa zuwa da zaka mallaketa" Ahmad ya faWa yana kallonsa Jafar da shima ya waiwaya ya kalleshi dalilin jin abinda ya ke cewa seya sake Wauke kansa gefe yana cewa

"Tafi ?arfina yanzu na ha?ura da ita, tun da ban sameta a farko ba ba rabona bace kuma ba zata taSa zama rabona ba har abada..."

"Kar ka manta da maganar hausawa da sukace *MATAR MUTUM KABARINSA?* sannan kuma sau da yawa jinkiri ya kan zamo Alkhairi, karka fitar da rai da tsammanin, jikina yana bani da akwai rabo a tsakaninku kuma yana kusa gab yake da samuwa" Ahmad Win ya sake katse shi. Shiru sukayi na kusan minti goma kowanne da abinda yake sa?awa a ransa kafin Ahmad yayi jarumtar amayar da abinda yake ransa, a hankali yace masa

"Kayi ha?uri da damuwar dana jefa zuciyarka a ciki na tsayin shekaru. Amma me yasa ka Soye mun Fatimata itace Afeeyarka? Me yasa ka rufeni ko kana tantama akan son da nakeyi maka? Kana zan ba zan iya sadaukar maka da koma menene ba koda kuwa dalilin hakan zan iya rasa raina?

Kayi kuskure Jafar kuma banji daWi ba har raina wlh da ace nasan kaine wanda Fatima taso kuma kaima itace wadda har a yanzu kake dakon soyayyar ta da bazan aure ta ba. Ina tsananin kaunarta amma na yarda soyayyar da kakeyi mata ta zarce tawa domin akanta ka shirya tunkarar kowa da komai sedai na kasance katangar data hanaka kaiwa ga muradinka, na kasance dalilin ?unci da zubar hawayenka me yasa ka zaSi ka jure komai saboda ni alhalin kasan zan iya seaukar maka da komai da na mallaka?"

Tamkar wanda ruwa ya cinye a zaune haka Jafar ya zama, dukda uban sanyin Ac dake Wakin zufa ce ta shiga keto masa ta abinda yake zaton kunya ce, ina ze tsoma ransa ace Ahmad ya san yanayiwa matarsa wani kallo na daban? Har tsayin wani lokaci Ahmad ya gano wannan gingimemen sirrin kuma yake kallonsa dashi? Ko shine dalilin daya zameshi daga jikinsa har lalura me girma irin wannan ta sameshi amma ya gagara sanar dashi.

Katse masa tunani Ahmad yayi yana cewa
"Kayi shiru, me yasa kayi haka Jafar? Meyasa ka zaSi rayuwar ?unci bayan ka tabbatar da itace cikon farin cikinka?"

"Abinda kakeji akaina da har ya saka kakejin zaka iya sadaukar mun da soyayyarka irin sane yasa na zaSi rasa farin ciki na muddin zan cigaba da ganin fuskarka da murmushi. Ka

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login